Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koyi da wasu dabi'u nata ba,uwar gida itace ginshiqin gida,itace kuma kamar turken mai gida da dukka wani ahu daya mallaka,idan ka dace a ita saika godewa Allah.


Yanayin dayaga fuskarta yasa ya gaza wucewa,saiya soma kame kame,inda daga bisani yac"wannan zaman bazaki gaji ba?,kawo tazugen na qarasa saka musu kije ki huta"kai ta kada
"A'ah,barshi kawai,aiba lokacin hutu bane yanzu koda naso na huta din" haka ya tsaya yana ci gaba da tayata gyara kayan yaran har kowa ya sanya nashi sannan ya shige dakinsa donya shirya shima,ta bishi da kallo tanajin wani bacin rai da kishi yana taso mata,ta dauke idanunta taba karanta "hasbiyallau la ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim".


Mmn ummi dake bakin window din tana kallonsu ta saki labulen cikin tafasar zuciya,wato ta fuskanci wani dama dama yake da mmn amir,itace banza kenan?,fushinta banza farincikinta banza?,anya ko matar nan haka ta zauna?,sai wani sashe na zuciyarta ya gargadera,don tunda suke da mmn amir din nata taba ganin wani abu guda daya tattare da ita daya sata shakka ba,abu dayane tasan cewa tana da yawan azumi kamar ma bata damu da abinci ba,hakanan tana da yawan tashin dare harta dinga zargin ada wani abu take cikin daren,saita gane sallar dare ce.


Sai data zauna saman kujerar sannan ta qwalawa yaran nata kira da sunayensu daya bayan daya,usman ne ya soma shigowa
" gani umma"cikin dakinta ta nuna mas"shiga ka cire wadan nan kayan ka samu wasu cikin kayanka ka saka"dum yayi yana dubanta sannan kuma yace
"Amma umma,wajen daurin aure zamuje"
"Iyee,ni kake gayawa wajen daurin auren kishiyar uwarka zakaje?,to shiga kayi yadda nace maka tun ban tashi na zazzabga maka mari ba" hakanan yaron yashige ciki sum sum,ya sauya kayan yafito,zai fita ta tsaidashi ta nuna masa saman kujera
"Zauna nan" ta fada tana dubanshi,haka yakoma yazauna,yayi lakur saman kujerar har zuwa sanda usman yashigo.


Cikin murna yana nuna mata shaddar jikinsa
"Umma,kalli sababbin kayana zamuje unguwa mu dasu abba dasu ya amir"jawoshi tayi da sauri sannan tahau tube mishi kayan,saiya riqe rigar da hannunsa yana kallonta
"Nidai umma karki ciremin,karki batamin kwalliyata,mama ce ta sakamin unguwa zamuje"
"Unguwar ubanka ko?,maza ni kama min bakinka a nan" yaro da baisan hawa ba baisan sauka ba,ganin tacire kayan da gaske kuma tana niyyar sanya masa tsofaffi saiyahau kuka da ihu harda tsalle,haushi ya cikata,ta janyoshi tahau duka,tanajin mmn amir dake tsakar gida tana tambayarta lafiya amma tayi banza da ita tashiga takoma saman kujera tayi zamanta tana baiwa ummi da kukan usman ya tasheta nono.


Bai gaji ba yazauna dirshan yaci gaba da kukanshi,har bban amir yagama shiryawa,ya gaji dajin kukan saboda haka ya daga lebulen yashigo yana kallonta
"Me aka yiwa yaron nan ne wai?" Sai idanunsa ya fada kan ahmad dake zaune kan kujera yana rarraba idanu
"A'ah,kai kume me kake a zaune duka 'yan uwanka sun shirya?,ina kayan naka?" Sai daya saci kallon uwar yaga ta maka masa harara sannan ya maida kallonshi ga uban,usman daya dakatar da kukan ganin shigowar uban shiya bashi amsa
"Abba umma taciremin sabbabin kayana" daga kai yayi ya dubeta,bai tanka mata ba yasanya kai cikin dakin ya debo kayan kayan yaran yadawo yasanya musu
"Karka fitarmin da yarana,babu inda zasu gayyar arna a idi" dai daya kada kansu tana rsaye a bayanshi tana yada magana sannan ya juyo yace
"Idan 'ya'yankine saiki hanani zuwa dasu ai"
"Ai wallahi kaima kanka kasan na fika iko dasu ehe,kuma ba'a canzawa tuwo suna duk juyin da zamani zaiyi sunanshi tuwo" taci gaba da daga murya tana zazzaga ruwan masifa harya yaran zuwan 'yar farfajiyar dake gidan wanda anan yake aje motarshi.


Surutun duka suka damu mmn amir,wanda itama kanta a quntace take,ga hayaniyar baqi tasoma jiyowa maza 'yan daurin aure,wanda ta tabbatar ba za'a rasa mata masu shigowa ba,saita saki abinda take tabar tsakar gidan ta hada ruwa tayi shigarta wanka.


Tana bakin madubi tana kwalliya taji shigowar maqotansu su biyu,a gurguje ta gama shiryawar tafito ta samesu,suka gaisa sannan sukace sun shigone koda wani aiki
"Ai kuwa akwai,samira naketa jira ta iso,gasu innarma har yanzu basu qaraso ba" abinda za'a rarrage ta nuna musu,sannan tashiga taci gaba da shiryawa.


Duk da cikin jikinta amma tayi kyau,kwalliyar ta dace da ita,ba jimawa samira ta iso,ita da qanwar ummanta da qannenta biyu da yaransu,nan suka shiga cikin maqotan akaci gaba da aiki.


Ba'a jima ba innar jibril ta iso itama da qannenshi duka mata,da kanta mmn amir ta tarbesu,tayi musu duk wani abu daya dace sannan sukaci gaba da sabgarsu,kafin wani lokaci gidan yadan soma cika da tashin hayaniya,awa daya da wasu mintuna da zuwan innar hafsa ta iso ita da qannen maman ummi,saida suka soma tsayawa ga jama'ar tsakar gidan aka gaisa sannan suka nufi dakin mmn ummi,wanda tun dazun datashiga dakin ko leqe bata sake ba,kai kace babu dan adam cikin dakin.


Jiddace ta waiwayo ta dubi mmn amir
"Tabdi,wai dama mmn ummi na gidan nan?"
"Abinda zan tambaya kenan nima" innar jibril ta fada fuskarta cike da tsantsar mamaki,sai mmn amir ta rasa amsar da zata basu
"Eh...me yiwuwa ko bataji zuwanku bane"
"Wanne irin bataji zuwanmu ba?,awata nawa zaune a nan,sannan duka yaran ai suna tsakar gida,idanma bataji zuwana ba ai bazata rasa jin muryar daya daga cikinsu ba,ashe duk abinda ake fada kan yarinyar nan na rashin arziqin da take tunda jibril yatashi aure da gaskene,ban gasgata ba sai yau" sababi sosai innar take,mmn amir na tausarta
"Kiyi haquri inna ki mata uzuri,ba lallai taji ba" shine abinda taketa fada tana fatan zata sassauto,bata da abin cewar daya wuce haka,saboda shekarun baya iwar haka ita ake tsinewa ake zaga sanda maryam din ke gab da shigowa gidan,bata da wani katabus bata da abin cewa,babu abinda zatayi tayi fari a idanunsu,sai gashi yau da yake ance duniya juyi juyi wai kwado ya fada a ruwan zafi maryam dince abar zagi
"Jeki kiramin ita" innar tace da jidda,saurin dakatar da ita mmn amir tayi tace
"Bari nayo mata mata magana dakaina inna" saboda tana tsoron kada jiddan tashiga ta tunzurata su raba abun fada,abu yazo ya kwabe,don ita kanta yau ta kanta take,ba zata iya daukar kowanne tashin hankali ba.


Daga can dakin mmn ummi kuwa hafsa da jamila qanwarta ne suka sanyata tsakiya suna faman lallashi,yayin da taketa faman sharbar kuka duk sanda ta daga kai ta kalli agogo taga lokacin da aka sanya na daura auren harya gota,yanzu kenan abban amir din ya zama nasu su uku?
"Wallahi wannan abun da kikeyi bayi bane yaya,tun yanzu kin karaya gaba daya tun kafin anjima azo kawota?,baki ganin mmn amir ita saikace abun bai dameta ba?" Tabe baki hafsa tayi
"Uhmmm,kinga maryam,ki tashi ki shirya tun kafinma a gane a haka kike zaune".


Sallamar mmn amirce ta sanyasu yin shuru,tashigo fuskarta sake tana duban mmn ummi
"hala bakiji zuwan inna ba?"
"Naji,me zanyi mata?,nafito taga na damu ko ban damu ba?,to ta Allah ba tata ba munafuka" sosai maganar ta baiwa mmn amir mamaki,a nata tunanin furfura ko bata tsohonka bace ka girmamata,jamila ma kama baki tayi,daurewa mmn amir tayi
"Amma dakin leqo kun gaisa,kin san idan ba leqowa kikayi ba zata yita qorafine"
"Tayita yi,uwata ce?" Kai mmn amir ta girgiza,sai taga tafiyarta yafi alkhairi akan ci gaba da tsaiwarta,don kada tsautsayi ya debi mmn ummintace zata aikata wani lafazi naba dai daiba a kanta.


Tabe baki hafsa tayi
"Kekam haryau baki da siyasa,tashi ki shirya din kije ku gaisa ki dawo,saime idan kinje?,gutsurarki zasuyi" da qyar suka lallabata tashirya din kana tafito,saidai duk wanda yakalli fuskarta yasan cewa babu walwala ko fara'a a fuskarta kona gamin gafara,haka ta dinga gaisawa da mutane daqyar harta isa dakin mmn amir.


A daddake tagaida innar ta amsa itama tana mata wani kallo
"Wato ke isassa ba'a isa kizo ki gaida mutane ba kenan sai an kiraki ko?"
"Banji shigowarku bane,inacan ina lallaba ummi tana rigima"
"To ai yayi kyau" daga haka shuru ya ratsa tsakani,minti biyar taqara ta miqe abinta tafice.


Da kadan kadan baqi ke zuwa wasu suyi Allah yasanya alkhairi su tafi,wasu kuma su zauna zaman wuni,ko sau daya mmn ummi bata sake leqowa ba tana cikin daki abinta,duk meson su gaisa saidai yashiga.


Daga can sashen rufaida kuwa lokacin da angon yashigo gaida surukai bayan an gama daura auren idanunta a kanshi,wani farinciki takeji yana ratsata,yau Allah ya cika mata burinta,kunyar ragaggiya ce ko sanda akazo daukan hotuna tsakanin amarya da ango,style take badawa kala kala,har wata kakarsu ta ankara,daga bisani ma tabar tsakar gidan tashige daki ta zauna.


Kusan duk hotunan da ake musu yaran saida suka shiga,usman da yake qarami yana hannunshi,tun bata lura ba harta lura,sai abun yasoma tsaye mata a wuya,data sake lura sosai saitaga hatta da shaddar jikinsu ma iri daya ce,qwafa taja can qasan ranta,wato bayan iyayensu suma akwai tasu qurar kenan?,zataji da kowa ta raya haka a ranta.


Saida azahar abbansu yasaukesu a gidan,innarshi kawai ya gaida yafice daga gidan,mmn amir na falon sanda yashigo,saita dauke ido kawai taqi kallonshi tana jin wani kishi na taso mata,ta tsiri hira da mmn ja'afar matar abokinsa,shima daya dubeta saiyaga hankalinta bai kanshi don haka ya juya da hanzari yafice.


Bangaren mmn ummi kuwa sanda yaran suka shigo ji tayi kaman ta kamasu ta gada da uban tayita duka,shaddar jikinsu ta dinga ganinta kamar daga wuta aka cirota,don haka ta korasu waje tace su bata waje.



*BAYAN AWA SHIDA*


Tsaye take cikin dakin tana shiryawa cikin atamfa,kayan kwalliyane baje a gabanta tana makeup,zahara dake zaube tana miqo mata abubuwan da take buqata,dakin ya bade da qamshi kai kace barin turare akayi,ba abinda kakeji sai hira da shewarsu,a haka kakar rufaida hajiya kaka tashigo dakin.


Cikin mamaki take duban rufaida daketa zuba baki rai rai batama lura da shigowarta ba
"Ke aku,samu waje ki zauna" sai a sannan ta waiwayo,ta dakata daga saka dan kunnen da takeyi tace
"Kefa tsohuwarnan kin iya takura wlh" tafadi tana samun waje ta zauna kamar yadda hajita kaka ta buqata,saita itama tasamu waje tazauna tana dubanta
"Duk fitsarar da kike da rawar qafar da kike ina lura dake,to bari na gaya miki gaskiya idanma uwarki bata gaya miki ba,wannan mu a wajenmu abun kunyane aga amarya tana haka,don haka ki kama kanki karkice zaki shiga cikin matansa kina musu wannan rawar kan,idan kikai hakan kai tsaye za'ace ba daga gidan tarbiyya kika fito ba" dariya rufaida ta bushe da ita ita da sauran qawayenta na makaranta dake dakin masu irin tunaninta
"To hajiya yanzu so kike naje nayi ta sussunne kai ina abu kamar banje makaranta ba ko kuwa yaya?,nifa auren soyayya mukayi da mijina,kuma babu wadda zanwa biyayya tunda yadda suke matanshi haka nake,haba hajiya nafa fisu da komai,idan ba'a bini ba ai kuwa bi ba'ace nabi mutum ba" ta fada tana juya idanu,sai hajiya ta kama baki ciki mamaki
"Ni tarasulu,ke rufaida akul ki shiga hankalinki,mu idan muka aurarwa mace miji kunyarta mukeji,mukan jima bama iyama hada idanu da ita saboda abune me nauyi da girma,hakanan abokiyar zamana harta rasu ke har yanzu da nake miki maganar nan ban iya fadar sunanta yaya nake ce mata,haka itama bata taba batamin raiba ko sau daya,suna na kuwa nima ban tabaji ta fada ba,saida nayi haihuwar fari take kirana da sunan dana" sake kwashewa tayi da dariya har suna tafawa da zahra
"In gaya miki gaskiya hajiya?,wallahi bazan iya wannan rayuwar ba,banma tanadeta ba ko a mafarki,kishiyar zan shiga ina kwantarwa dakai ina yiwa biyayya?,bayan nasan cewa na fita da komai?,ai tsakanina da ita kawai shine nasaita mata hanya ta bani waje na sarara nida mijina,matan nashi gidadawa kada ma uwar gidan taji labari" da yatsa hajja ta nunata
"Ke wallahi ki kiyayi kanki,mu dukka din nan da kukewa kallon gidadawa da haka muka fiku iya riqe miji,me bokon taku ta tsinana muku banda tabarbarewa lalacewa da rashin iya zaman aure?,iyee ki gayamin?" Shuru dukka sukayi saidai rufaida tasan halin mutuniyarta,saita hau lallabata
"Aikin banza aikin wofi,duk bokon da kuke haryau sunqi karanta muku iya zama da miji da kishiya lafiya lau,kunawa aure kallon abu mai sauqi,bayan bakusan cewa *HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BA* ne"
"Kiyi haquri hajja nima tsokanarki kawai nake,zauna ki gayamin ina saurarenki" ta fada don kada hajjan ta ballo mata ruwa,ita ta haifi babanta tasan kuwa yanzu idan zance yashiga kunnensa sai ya bata mata ranta,fur hajjan taqi zama tace taje tagwada bokon tata.


Dariya sosai ta dingayi suna tayata sanda hajiyan tafita,haka tajuya taci gaba da diban kwalliyarta.


Lullube amarya rufaida take cikin shigar atamfa da yalwataccen mayafi kamar yadda akasan kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mamanta wadda rafito da ita daga dakin mamarta zuwa dakin dakin da dangin ubanta suke don yi mata fada,qasa qasa tace da zahra dake kusa da ita
"Ke nifa na gaji da wannan qabli da ba'adin nasu,wai meye baka sani bane a auren nan da aketa damunka?,kwanciyar aurece kawai fa ta rage,kosu wlh saina koya musu wani abun,amma sun dameka da zantattuka wani sai haquri sai haquri suke cewa kamar ance musu anmin mutuwa" dariya zahra ta kwashe da ita cikin qunshe bakinta kana tace
"Salon bata lokacine kawai da al'adar da suka daukaketa,kedai kawai ki bisu a haka suyi su gama mu qara wuta" da wannan zancan aka qarasa dakin,sun mata nasiha daidai gwargwado,wanda wajen rufaida kallonta take a matsayin ita da babu duk daya,ta kunnen data shiga haka take fita ta dayan,har suka gama aka tattaro aka fito da ita don danganata da gidanta.👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*Haske Writers asso*💡

*BABI NA BAKWAI*




"Allah ya kawo mu gidan gimbiya rufaida,lokaci yayi,gamu gidan rufaida,mata mai cikakken iko a gidan jibrila" wata zabiya dake cikin tawagar amarya taketa faman fada tana sake nanawatawa,gami da hadawa da guda mai shiga tsakar ka,su kansu wasu daga cikin 'yan uwan amaryan basusan wace ita ba,suna dai biye ne,har suka wuce farfajiyar gidan zuwa babban tsakar gidan,wanda ke dauke da varender da dakuna manya a jere.


"Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" mmn amir take maimaitawa sanda takejin wata faduwar gaba da fargaba na saukar mata
"Uhummm,sun iso kenan" daya daga cikin matan qannenta ta fada
"Da alama" samira ta fada tana dawowa kusa da mmn amir din,qoqarin kauda duk wani surutun masu shigowa da amaryar take daga kunnuwanra,da kauda duk wani furuci da zaya iya fitowa daga bakinsu.


"Na shiga uku,hafsa sun kawota,wallahi gasunan" mmn ummi ta fada tana dora hannuwanta saman ka,hawaye yana balle mata,da sauri hafsan ta sauke mata hannun tana cewa
"Haba don Allah mana maryam,ki nutsu,a haka kikeso su shigo su taddaki?,haba don Allah" hafsan ta fada tana sauke mata hannun data dora din aka,jamila tamiqo mata mayafinta tace ta yafa,don wala'alla suce zasu shigo da ita nan din.


"Ku fara shiga da ita dakin uwar gidan" yayar maman rufaida ta fada sanda taga suna yunqurin shiga da ita dakinta,wani takaici yacika rufaidan,taji kaman ta dakatar dasu,saidai ba yadda ta iya haka tanaji tana gani aka sauya akalarta zuwa dakin mmn amir.


A mutunce suka amshesu,sannan suka gabatar da itawa mmn amir din gamida danqa amanarta a hannunta kamar yadda al'ada ta tanada,cikin matuqar dakiya da nuna juriya mmn amir tace
"Toh,amana abune mai nauyi,amma duk da haka muna fata da addu'ar Allah S W T yabamu ikon riqewa,yashige mana gaba ya kauda fitina" dukka suka amsa da amin cikin yabawa da halayyar mmn amir din.


Ta cikin mayafin rufaida ke tabe baki sanda mmn amir din ke karanto addu'o'i suna amsawa,qaramin tsaki taja qasa qasa cikin ranta sannan ta furta
"Bagidajiya,kawai zata batawa mutane lokaci" sai data kammala suka shafa sannan suka miqe da ita suka fice zuwa dakin mmn ummi,har cikin zuciyarta taji sanyi na sauka sanda take shafa addu'ar,ta saki sassanyar ajiyar zuciya gami da sake maida kanta cikin sabgogi ta hanyar sallama da maqotanta wadanda suka soma haramar komawa gida ganin an kawo amarya.


Idanunta qir a kansu sanda suke shigowa dakin nata,baqiqqirin take ganinsu,kallon da take musu tamkar ganin abokan gaba ne a sansanin yaqi.


Wani irin tafasa zuciyarta take,kaman ta tashi ta koresu,amma dole tazauna tanaci gaba da dubansu,saboda maganar da jamila tayi mata tun kafin su shigo.


Yadda sukayi bayani dakin mmn amir haka sukayi mata,zuciya ta ciyota,taga zallar rainun wayonsu,ita za'a baiwa wani amanar kishiya?,duk yadda taso ta danne tayi shuru saita kasa
"Dacan baku bata tarbiyyar zaman gidan miji ba da bazata iya ba har sai kun bada amanarta?" Da mamaki suke kallonta,idanunta qyar akansu tana jiran wata ta tanka musu,ware idanu rufaida dake cikin mayafi take,inama daga ita sai ita tafadi wannan maganar,lallai wannan matar saita gane kurentq,dama tana sane da ita sarai,bata manta daduk wani cin fuska data mata ba kafin shigowarta gidan ,ta kuma ci alwashi ta lashi takobi saita rama,saita bada mata yaji a rayuwarta mai radadi
"Ikon Allah,to adai dinga haquri" yayar umman tata ta fada,sai duka suka miqe tare da rufaidan don barin dakin
"Da ba'a haquri ai da ba'a kai yawar haka ba,da bata shigo bama" ta fada ranta na mata zafi.


Dubanta jamila tayi bayan sun fice
"Gaskiya baki kyauta ba mmn ummi,abu na 'yan mintina ki barsu suyi su gama su fita shine kika kasa shuru,nikam gida zan wuce" ta fada tana miqewa ta dauki jakarta ta rataya
"Madalla,Allah ya raka taki gona,tunda na taba qanwar umma uwarmu" bata tanka taba tafice a dakin,ta leqa dakin mmn amir da tuni baqinta suka yoye saura 'yan qalilan suma daketa hada karonsu zasu wuce,sai qanwarta salima da zata kwana gidan donta tayata hidimar gobe ta gidan.


Zuwa awa daya gidan ya yoye babu kowa,hatta da amarya sai ita kadai,don qawayen nata duka angon yasa an kwashesu an maidasu gida,don yace bazaiyi wani siyan baki ba,saboda yana bala'in jin nauyi da kunyar mmn amir,bazai iya tsayawa yayita wannan yarintar ba da qawayen amarya ana jinsu,duk da hakan bai yiwa rufaida ba,amma haka ta haqura suka tafi suka barta.


Dukka yaran mmn amir ta sanyasu suka canza kayansu,salima ta gyara musu wajen da zasu kwanta tasaka su sukaje suka kwanta,hatta dasu usman basu kalli qofar dakin mamansu ba,don sunsan qarshen zancan wala'alla kafin bacci ya daukesu sai sunci na jaki.


Dai dai lokacin da amarya rufaida take kewaye dakinta tana dubawa,ba laifi komai yayi mata yadda takeso,duk da tasan cewa data yarda bbn amir din ya raba musu gida to dakin nata sai yafi haka,saidai sam ita bata da sha'awar wani raba gida,tafi sha'awar a hadesun yadda zataji dadin nuna musu cewa ruwa na sa'an kwando bane,wannan ma hakan ya mata.


Babban falo ne mai hade da bedroom,sai wajen dining wanda kusa dashi kuma qofar toilet ne,duk da ita kitchen taso a mata a wajen,duka sauran falukan matan nashima haka yake,gini ne mai kyau wanda yasha tiles da fentin mai kala biyu,kalar da kowacce cikinsu ita tazaba da kanta.


Tana zaune tun dazun inda take,ba inda ta motsa,jikinta gaba daya ya mata nauyi,ga wani ciwon dako ina na jikinta ke mata,hakanan zuciyarta sam babu wani sauran karsashi ko qwarin gwiwa tattare da ita.


A haka taji shigowar baban amir din gidan,tanason ta tashi tabar falon amma ta kasa,a haka harya shigo gidan,sai daya tabbatar ya kulle ko ina sannan yashigo tsakar gidan bakinsa dauke da sallama,shuru tsakar gidan yake,saidai a kacame yake,ko baqone kai zaka tabbatar cewa lallai anyi wani sha'anine cikin gidan.


Idanunsa kan qofar dakin rufaida,wanda yake tarwai da haske kamar yadda dakin mmn ummi yake,sabanin dakin mmn amir da nata hasken baikai nasu ba,da alama ta rage qwayayen dakin nata.


Kai tsaye dakin mmn amir din yanufa,ya yaye labulen bakinsa dauke da sallama,amsa masa tayi a sanyaye bayan ta daga kanta da niyyar kallonshi,saidai ta kasa,saboda wani abu daya takore mata wuya,hakanan taji cikinta yasake nauyi
"Sannu da zuwa" ta furta daqyar tana kuda kanta gefe,idanunshi a kanta yana karantarta ya amsa mata
"Kun yini lpy ya yaran duka?"
"Sunyi bacci" ta bashi amsa a taqaice,shuru daiya ratsa tsakaninsu,hakanan yadinga jin nauyinta,yana tuna wancan shekarun da suka shude a rana irib wannan,kusan hakan tayi masa,yaga zallar kishi da bacin rai a fuskarta amma tazabi yin shurun kamar wannan lokacin,duk sai yaji nauyin tashi yafita din,yana ganin kamar ya cutar da ita a rayuwa har sau biyu,cikin son nade tabarnar kunya yace
"Na tsammaci zuwa yanzu kin kwanta,don nasan kunsha kujiba kujiba ko"
"Yanzu nake shirin tashi" ta fada tana yunqurawa da qyar
"Yi a hankali" ya fada sanda tadan koma baya kamar xata zauna sai kuma ta sake miqewa,ledar hannnunshi yamiqa mata ganin tana niyyar shigewa uwar dakinta
"Babu wani abun da kuke da buqata?" Ya tambayeta yana kallon bayanta sanda take dab da shigewa dakin nata
"Babu komai" ta fada bayan ta dakata ba tare data waiwayo ba
"Haka akeso" sai yasake yin shuru na wasu sakanni sannan yace
"Halima.....don Allah ki kwanta kiyi baccinki sosai kodon abinda yake jikinki,karki sakawa ranki damuwa don Allah"kai ta jinjina tana qoqarin hadiye abinda ke taso mata sannan ta sanya kai cikin dakin.


Kusan sakan goma sannan ya taka ya juya yafice yana jin tausayinta sosai cikin ranshi,ta nuna dukkan wata jarumta da haquri,ba shakka haliman baiwa ce da Allah yayi masa na macen da ba kasafai ake samun irinsu ba,maryam kawai ta zame masa ishara.


Daga nan dakin mmn ummin yashiga,itama da sallamar yashiga,tana tsakar falon tana kai kawo goye da ummi a bayanta wanda ta jima dayin bacci,fuskarta kawai zaka kalla kasan bala'i da tashin hankalin da take ciki.


Dauke kanta tayi sanda taga shigowarsa,qirjinta yaci gaba da zafi,ko sallamar ma bata da lokacin amsa mishi
"an yini lpy" ya fada itama yana zama hannun kujera,banza tayi dashi,saima tasoma tattare kayan dake zaune d'ai d'ai tsakar falon kamar batasan Allah yayi ruwanshi ba,qoqarin danne bakinta take ta hana kanta ruga masa ashariyar daketa yawo saman harshenta,data gama saita wuce dakinta tarufe qofar tabarshi nan zaune.


Yasan cewa lallai anzo gabar da duk dauriyarki dole gazawarki ta bayyana,saboda haka baiyi qasa a gwiwa ba yanufi qofar dakin yasoma qwanqwasa mata
"Bude mana maryam"
"In bude inyi uwar meye?,jibril kafice min daga daki wallahil azim idan nafito ba zamu kwasheta da dadi ba,maciyin amana kawai,Allah dai yayimin sakayya" saita rushe da kuka sosai mai fidda sauti,kanshi kawai ya girgixa saiya koma da baya ya aje mata ledar ya juya yafice zuwa sashen rufaida.


Cikin so da qauna ta taryeshi,cike da nuna wayewa da sanin me rayuwa take ciki,hakanan ya biye mata,saidai can qasan ranshi yana mamaki kadan kadan idan tayi wani abun,sabida ko maryam daren farkonsu batayi ba bare halima,daga bisani saiya share shima,komai ya kauce daga ranshi ganin cewa ba wani abu daya tadda tattare da ita wanda ba dai dai ba ko zai saka zuciya ko rai cikin zargi.


Wanka mmn amir tasamu tayi cikin bandakinta sannan tasauya kaya,ganin idanunta yasoye,tunani yana neman hanata bacci,saita dauko qur'aninta da dama kullum bai rabo da gefan gadonta,ta bude wasu shafuka tasoma karantawa,babu jimawa taji bacci yazo mata,idanunta har rurrufewa suke,tasamu ta maida qur'anin batayi wata wata ba taja filo ta kwanta.



Mmn ummi kuwa a iya cewa kwanan zaune tayi,sai zirga zirgan shiga bandaki data sameta saboda tashin hankali,tayi kuka har batasan iyaka ba,haka tazauna tasaka agogo a gaba tana kallo,duk daqiqa daya da zata wuce tana lissafawa gamida qissima yanzu abu kaza baban amir din yake,yanzu yaci ace yayiwa rufaidan abu kaza,saita sake rushewa da kuka,haka takusan kwana,kafin wani lokaci kuwa kanta yadinga ciwo,da qyar gefin asuba tasamu bacci yayi awon gaba da ita cike da tarin baqinciki da quncin zuciya.


Qarfe biyar da rabi yashigo dakin,a lokacin tana zaune saman abun sallarta tana jan carbi,duka yaran sun gama sallarsu sun koma baccin,itama jira take ta gama addu'o'inta takoma ta kwanta din kafin gari ya qarasa wayewa,saboda tasan gidan a kacame yake sosai,gashi yaudin tanason zuwa awo ranar da zata likita ne.


Kallo daya tayi masa ta dauke kai,saidai abun ya bata mamaki,batama tsammaci shigowarsa ba adai dai wannan lokacin,don kuwa zamanin maryam bataga idanunshi ba sai goma na safe.


Shi yasoma gaidata har taji abunma bambarakwai,saita amsa kawai,ya tambayi yaran tace sunyi sallah sun koma
"Sannu da qoqari,Allah yayi albarka"
"Amin" ta amsa tana ci gaba da jan carbinta

Please Login or Register in order to submit comment