Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na rasa mafita,na rasa yazanyi da ita,tasan komai na auwal kama daga dukiya abinda yakeso da wanda bayaso,amma wallahi kinganni haryau ban gama sanin danginsa bama bare wani abu,wannan wacce iriyar masifa ce?" ta qarashe zancan kamqr zata saki kuka
"Turqashi,yo ai wallahi dole kowa yabi jam'iyyarta,na farko idan kashigo gidan saika tsinewa kanka itace amaryar saboda tsafta da gayu,nabiyu ni kaina tunda nashigo bangarenki ko baqin ruwa baki bani ba,ita kuwa har qoqarin doramin girkin rana take idan baki dawo ba,na uku sashen mariyar kamar wadda tayi haihuwa goma,komai a watse babu kintsi ko kyakkyawan gyara,duka q zuciyarta take wannan maganar,amma a zahiri saita saki ajiyar zuciya
"amma matar nan ta shammaceki mariya,matar datake kiranka ada kusha hira kotasa mijinta ma yakiraki?"
"Hmmmm,idan ana salla ba'a magana,ashe duka cutata takeyi?,ta nunawa auwal ne sam ita bata kishina,shi yasa duk wani abun tashin shina idan yataso kowa ke doramin laifi,sai ace nice sila,saboda hadiza tun kafin nashigo bata kishina bare yanzu da muka zama daya,ni kuwa wallahi babu matar dazan boyewa kishinta da nake saboda ba tsoronra ai nakeji ba,rufaida.....hatta da abinci fa matar nan ran girkina saita tsiri dafa wani abu da tasan yana jarabar so,saitasan yadda tajashi sashen ta cikin dabara,acan zaiga abun,idan yace zaici saita hanashi,daga qarshe saita zuba a flask tarakoshi ban,fuskarta da dariya da komai zakiga ta ajemin flask din tana cewa
"babu ruwana ga mijinki nan nadawo miki dashi,yadage saiya ci mana abinci,ni kuwa bazan batawa 'yaruwata raiba,kuma bazan bari yaci shi daya yabarki na,gashinan kwaci tare" tafada tana kwatabta salon magabar hadizar bacin rai nasake baibayeta
"Kuma wallahi rufaida a gabana zaicinye tas,daga lokacin nawa abincin saidai yakwana"aifa dole,irin wannan dabge haka?" Rufaida ta raya a zuciyarta sanda ta tuna da dandanon girkin hadiza datayi katari dazu dazu dashi.
"Yanzu fa haka siddan sai naji waya daga gida waita musu aike,mama tace na tayata godiya,shi kansa auwal din rabon daya siya singlet ko boxer ya manta,rannan fa haka tasiyosu set bibbiyu,tadauki set daya ta aikomin da daya waina aje yayi amfani dasu sanda yake wajena,don Allah kijimin wani cin fuska"

Shuru rufaida tayi,tashiga dogon nazari,to indai ko har hakane tata matsalar salamace akan ta mariya,amma duk da haka a yanzu babbar fargabarta randa mmn amir zata karbi girki,batasan ya zata kaya ba,tasan cewa akwai bannar qura a gaba,a yanzu kusan itace damuwarta,donta mmn ummi dasauqi,tana ganin bata da ajin da zata wani zama damuwarta,zasuci gaba da bugawa a haka kawai,burinta ta karbi jibril a hannunta yadda ya kamata.


Itama nan ta gayawa mariyan komai,saita sauke ajiyra zuciya tace
"Amma mazan nan 'yan abu ta kazar ubane,suzo suna fasa miki kai suna kambamaki,saikin gama dauka babu yake saikin shiga wasan yasha banban,wallahi rufqida ban taba daukan lamarin haka ba,ni da nasan hakane auren ma bazanyishi ba,idan ko nayi gwara na auri yaro irina dagani saishi babu abinda zai dagamin hankali,tunda suma nagidan ashe shegerune,kana musu kallon biri ne ashe suna maka kallon ayaba,yanzu jiya dana fita girki dasafe saida mukayi kaca kaca dashi,haka kawai yahanani barcin safe wainatashi na shirya masa abun kari,bayan kumaga bayan sallar asuba ya taramin gajiya nasamu bacci yadaukeni saboda rashin imani,wai saboda nayi banza naci gaba da barcina yatayarmin da hayaniya da gori,waishi tubda yake da hadiza bai taba cewa tayi ire iren wadan ba,kafin yace tayi tuni tahi,bai taba farkawa yasameta tana bacci ba idan ba bata da lafiya ba,danacemishi baida abinda yafaru ba yataramin gajiya ko wanka ban samu yiba waisai yace,hadiza sai nayi zagaye biyu,koda tana da tsohon ciki kuwa haka zata gyara jikinta takuma shiryamin komai,kinsan cikin maganganunsa maganar data tunzurani nafita neman mafita yau?"kai rufaida ta girgiza
"Cewa yayi,nifa dadin zama da ita yasa nayi tunanin akwai wata kamarta,bari na dado na rage mata wasu nauye nauyen,sai gashi ashe abun duka bige ne,qyalqyal vanza a waje" tana zuwa nan ta kasa daurewa sai ga qwalla.


Kai kawai rufaida ke girgizawa,ashe jibril yana da kirkinsa tunda bai tava gaya mata irin wannan kalmar ba duk iskancin da take masa?,to ai kuwa wallahi zata sake riqe wuta,bq zata yarda ma azo wanann bigiren ba,don duk sanda yayi gangancin gaya mata hakq saiya saki aurenta wallahi.


Rufaida riqe da habarta take kallon mariya sannan tace
"Turqashi,muna ruwa mariya,yanzu meye abunyi?" Saita goge qwallar tana dubanta
"Aini nayanke kawai zan nemi taimakon malamai masu zafi da aiki da sauri sauri su shiga lamarina,saboda na fuskanci abun bana qare bane,don wallahi da quruciyata dakyauna bazan zama baiwar namiji ba yadda ita tazama,nayi aurene don in sakata in wala,nayi aure don nasamu 'yanci na shaqata,badon na takura kaina da bauta ba,shegiya gajeriyar banza,ko rabin kyauna bata kai ba bazan zauna wallahi tadinga juya komai da komai ba,bayan nice amarya niyafi cancanta nayi wannan mulkin ba ita ba,kuma wallahi da ba haka auwal yakemin ba" juya kai kawai rufaida take tana tunanin zancan mariya,idanma tace zatabi malamai ina taga kudi?
"Tunanin me kike?,koke bazaki shiga sahun 'yan huce takaici ba,dama qawata tajima tana bani shawara wlh ninaqiji sai yanzu danaji uwar bari"
"Mariya,kudin da kake riqewa ada yanzu wallahi basa baka shi,akan dari biyu fa sai a titsiyeki ana tambayarki me kikayi da ita?,bayan ada sai a banki ninkinta koda watsarwa xakiyi babu mai tuhumarki" tabe baki mariya tayi
"Auke haka kika xauna?,tabdi to wallahi bari kiji,ke mazan nan matsiyata ne masu shegen romon baka,waisai ka tambaya kudi qiri qiri a hanaka?,da kuwa ko uwarsa zai saida saiya siyar yabaki kudin cas yadda kika buqata,ni dana masa zancan kudi da yadda naga hadiza na fantamawa waisai cewa yayi dama yataba cemin aina koyi sana'a tun a gida,saboda ita kanta hadizan sana'a take,duk abinda naganta dashi a kudinta ne take yiwa kanta,abinda yamana ta qara dashi,saina qyale banza,idan yadawo daga aiki daya rataye rigarsa xan lali na lala,idan bai dakina naji matsuwa saina bude store nazari taliya ko semo ko couse couse nakai shago nabugar subani kudina nayi gararin gabana,idan ba haka kamusu ba wallahi saikaji kunya koka mutu a tsaye,abinda kawai suka sani su ajema abinci,sus dinka maka kaya su baka" washe baki rufaida tahauyi saboda shawarar mariya ta wannan fannin da zata dinga samun kudi ta mata sosai.


Hira suka dingayi kala daban daban,kowacce na gayawa 'yar uwarta sirrinta,wanda batabar gidan mariya ba sai data wuni sur,sun yanke cewa ita mariyan tasoma xuwa wajen maganin,idan tasamu nata kudaden kuma taga aiki yayi kyau saita rakata,da haka suka rabu.


Sanda tashiga gidan saota hade girar sama data qasa don kada kowa yamata magana,mmn amir kan dauke kai tayi saboda ba xamanta take ba,hakanan ba ita tayiwa laifin ba bare ace,yar neman magana ce mmn ummi tana girki amma tahau waqe waqe
"Kamota nan.....mai qafar tafiya ce....eh fa....mai qafar yawoce....ungulu kinsan gidan kowa" tajita sarai kuma taga ba zata iya tankawa ba,ta fito burum daga daki hannunta akan qugu,tayi tsaye kan mmn ummi tana cewa
"Dawa kike wadan nan waqe waqen naki?",dagowa tayi ta jefeta da harara
"da wanda yatsargu"tsaki rufaidan taja
"Aikin banza,idan mutum ya isa yafito fili yafada mana"
"Dake nake,an gaya miki tsoronki nakeji,ko kedin wata tsiyarce?" Aikuwa bata rufe bakinta ba tasa hannu ta ingixa mmn ummin,takuwa qume qum a goshi da bango,itama kuwa tana waiwayowa takama rufaidan da komawa rikica.


Mmn amir na daki a sannan yaran suna islamiya,tiri tirinsu yasa tafito,saita kama salati cike da mamakin hauka da wauta irin nasu,dambe kamar wasu qananun yara,itakam bazata iya rabonsu ba suje su make mata dan cikinta,saita soma musu maganar kan su rabu,amma qememe sukayi kunnan uwar shegu da ita,ganin haqilon ya mata yawa saita koma daki takira bbn amir tashaida masa,yace tayi xamanta a daki,karta sake kula kowacce a cikinsu
"Amma abban amir sunata fa...."
"Haka nace kiyi ko kema musu zakimin?"
"Allah yabaka haquri" bisa umarnin bbn amir tayi zamanta a daki,haka sukaci suka gode Allah,kowacce tayiwa yaruwarta tabo,don kuwa mmn ummi bata haqura ba itama sai data kumburawa rufaida baki.


Afusace kowacce tazauna tana jiran dawowar bbn amir din yadauki mataki kan abinda 'yaruwarta tayi mata.


Ranshi babu dadi yadawo gidan,ranar wuni sukayi sur maganar batan container dinsu.


Yana sallama tsakar gidan mmn ummi tayi hanzarin fitowa daga dakin,goshinta liqe da auduga,tana wani cika tana batsewa,ji take bazata iya jiranshi ya qaraso dakinta ba
"Gwara da Allah yadawo dakai,kazo kayiwa tufkar hanci indai kanason zaman lafiya a gidanka,wallahi wallahi kayimin katangar qarfe...." Ai bata qarasa ba rufaida itama tafito fa kumburarren bakinta
"Ayimiki katangar qarfe dani koni ayimin katangar qarfe dake tun ban miki mummunar illaba,banza shashasha ballagaza,wadda tun kafin ashigo gida kike hauka da hayagaga da dabbanci"
"Ni kike cewa dabba...."sai tayo kan rufaidan,itama rufaidan tayo kanta,tsawa ka tasa musu sannan cikin fushi yace
"Kowacce tawuce tatafi gidansu"
"Subhanallah" mmn amir wadda tafito jin sallamarshi da sabuwar hayagagarsu ta fada
"Ko a jikina wlh"
"Oho tafi nono fari" haka kowaccensu tafada,duk da jikkunansu yayi sanyi sannan suka juya zuwa dakunansu.


A nutse mmn amir tanufi dakinsa,sanda tashiga yana tsaye kawai hannayensa cikin aljihu ya baiwa qofa baya,a sanyaye tace
"Don Allah bbn amir kayi haquri,bai...." Da hanzari ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu
"Karki sake kibani haquri,ki koma dakinki,banason tsaiwarki a nan" yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata yayi matuqar fusata,saboda haka bata sake furta komai ba tajuya a sanyaye tafice a dakin.


Suna daki dukka shuru ita da yara,saidai su amir din kallo suke,yayin da ita kuma tashiga nazari,saiga usman da mubarak sun shigo dakin,da alama mmn ummin ta tafi kenan,su kuwa dayake yarane kuma akwai shaquwa tsakaninsu da mmn amir din sai basu damu ba,suka shiga sabgarsu dasu amir din.
[10/3, 3:02 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA BAKWAI*


*har yanzu dai litattafaina nakan youtube,a tashata ta SAUTIN HIKIMA,shiga donki sauraresu kai tsaye*👇đŸŊ👇đŸŊ👇đŸŊ👇đŸŊ

https://youtu.be/8LI1DTRwdaM

*Daurin boye*
*Alqawarin Allah*
*Mutuncin mace*
*Dangantakar zuci*




Cikin tausayi da qauna yake dubanta sanda take duqe tana goge masa takalmansa,gaba daya sai yakejin gidan sakayau kamar kadda yadawo dasu,har zuciyarsa tasoma raya masa meya kaishi ga qara aure aure bayan mmn amir din bata rasa komai ba?,qaddara da kuma *hangen dala* wanda yake *ba shiga birni* bane,a sannan ganin nawajen yake kamar zai samu fiye da abinda yake samu wajen mmn amir din,kamar suna da abubuwa da kuma qualityn da ita mmn amir din bata dashi,uwa uba da zugar abokai da suke ganin a yadda yakedin da yadda Allah yamasa budi lokaci daya a sannan yafi qarfin mace daya,ashe dukka kuskure ya tafka,amaimakon yayi taai da hankalinsa yayi dogon nazari,yakuma dora duk wani abu bisa doron doka da oda da kuna dacewa,sai yanzu yake ganin duka ashe ba haka bane.


Hannunta data motsa saman fuskarshi ya fargar dashi
"Tunanin me kake yallabai?,tunaninsu mmn ummi ko?,ko nima wlh kullum idan natashi sai naji gidam ba dadi,sabo turken wawa,ga yara idan naga sunyi wajen dakin ummansun wlh duk sai naji babu dadi,don Allah baban amir......"
"Toh....zaki fara ko?" Yafada yana dubanta,yasan kwanan zancen,baisan me yasa duka tadamu yadawo dasu din ba
"Wallahi ba haka bane....kawai"
"Kinga idan kin gaji da dawainiya danine ki fadamin,ni wallahi sai yanzu ma nake dana sani,bansan wanne tsautsayi bane yasa na yadda kika aje girkinki,sai yanzu na sake gane ashe cutar kaina nayi"
"Duka ba wannan ba bbn amir,don Allah kodon yaran kaduba mana" harara ya watsa mata,yana tsaka da morewarshi hankali kwance tanason dawo masa da tension.


Har yaqarasa abinda zaiyi yafita bai bata amsa ba,saita dawo tazauna jikinta a mace,itakam ko sau daya bata taba buri kishiya tafita tabar mata gida ba,saboda indai tashigo kuma magana ta gama qarewa ai,zata fita tabarmiki yara kiyita wahalarsu,ita ko uban ko jama'ar duniya ba lallai kowa yagani ba,wani ya yaba maka,wani yazageka koda bilhaqqi tsakaninka da Allah kake,sannan su kansu yaran babu yaron da zai girma yaso ganin mamarshi ba'a gidan babanshi ba,idanma babu yaran tafita ai tabar miki tabo,tunda ko ina za'aje za'ace tsohon mijinta ne,uwa uba yasanta tasanshi saidai kawai a kalli juna,idanma akayi rashin sa'a saisu sake dinkewa a waje,ke kina cikin gidan kina kwasar takaici da baqinciki.


Haka ta dinga shan kanshi yaje amma qememe yaqiya,duk da yasamu kira daga dukkanin gidajen rufaidan dana mmn ummi,amma baije ba sai da akayi kwanaki kusan uku bisa tursasawar mmn amir din.


Gidansu mmn ummi yasoma zuwa,aka saukeshi a soron gidan,bayan jin tabakin bbn amir aka saurari mmn ummi wadda dama keta son abata dama,don tanata tsomamasa baki yayanta yana kwabarta,sai kuwa tasaki kuka
"Wallahi ni dama bayasona,duk cikin matanshi ni yake nunawa banbanci da rashin soyayya qarara,zaluntata kawai yake...." Duka yayan nata yakai mata wanda yasanyata katse zancan,nan yahau bambamin fada yace ananma saikin nunamin halin naki,tashi kaje jibril sai tayi hankali kazo kadauketa.


Dama ba wani damuwa yayi tadawo din ba,saboda tasire masa da halayanta data nuna masa fes,tun daga neman auren rufaida kama yanzu,ba haka taso ba ita dinma,donta soma qosawa da zaman gidan,amma saita maze tayi cikin gida fuuuu.


Sashin rufaida kuwa itama tun tana zuba idanu da zaton zuwan jibril har taji dif,abun ya sosa mata rai da bata mamaki
"Lallai jjbril,ni zai wulaqanta,wato yakoremu yazauna da baqar matarsa kenan ko?" Sai mmn amir ta tsaye mata a rai,duk abun saiya soma damunta da bata mata rai,ta zaci daga zuwanta babanta zai kira jibril amma sai taji shuru,bai kira ba bai kuma yi zancanshi ba,sabida bayanan yayi tafiya,taci alwashin wallahi saita nunawa jibril kalarta,duk zaman haqurin da take da kauda ido amma bai gani ba,ita wallahi da tasan haka auren yakema ba zatayishi ba,ashe babu abinda yafi 'yammatanci dadi?,kawai matsalarta bata son yadda komai ake hadata da qannenta ne,hatta da dakin kwana,hakan yasanya takan tuno dakinta da gidanta akai akai.


Sanda qawarta zahra tazo sunsha hira sosai(qawarta tun ashafin farko da take musu fada kan mummunan ra'ayinsu suke jin haushinta)zahra itama tayi aure,mai mata ta aura itana ikon Allah,saidai suna zamansu lafiya,don bata shiga da wani mummunan niyya ko nufi ba,haka itama matar bata da wani mugun quduri akanta,kallo daya zaka yiwa zahran kasan hankalinta kwance yake,harda ma yaron cikinta,suna tsaka da hira tadauki waya takira kishiyar tata
"Auntyn salama dame dame ma kikace nasiyo?" Rufaida naji tana lissafa mata,sai data gama sannan tace
"Me zakiyi da kayan fruit haka zahra?" Murmushi tayi tana aje wayar
"Maman salma ce zata koyamin wani abunsha da abban salma yakeso sosai,haba ni naga duk ran girkinta shi kadaine abinda yake shanyewa tas ashe yafisonshi ne niban sani ba inata masa wasu kalolin lemukan" tabe baki rufaida tayi
"Wace haka zata koya miki abu zahra?" Murmushi tasakeyi
"Abokiyar zamana mana" kama baki rufaida tayi cikin ta'ajjubi da mamaki
"Amma wallahi zahra bansan lalacewa ta sameki har haka ba sai yanzu,yanzu duk duniya ki rasa wanda zai koya miki abu sai kishiyarki?,wallahi kozan mutu da jahilci bqzan yarda kishiya takoyamin komai ba,wallahi kin fado zahra" murmushi kawai zahra tayi ta dafa rufaida
"Wato dai mai hali bai fasa halinsa,dawowarki gida rufaida ni nasan da walakin,bari na gayamiki wani abu da baki sani ba,macen data cika itace wadda ke jiran aikatawa da neman sani kan duk wata hanya da wani abu dazai sake daga darajarta wajen miji,dakuma qara soyayyarta cikin zuciyarsa,wannan abun da mmn salma zata koyamin ba wani abu bane ban kuma fado ba,abune da mijina yakeso ni ban sani ba,saboda nidin sabuwace cikin rayuwarsa,itadin tafini sanin komai nashi,iya abun dayi masa da zan dinga yi zai sake samamin fada cikin zuciyarsa,da zarar na iya an wuce wajen na kwashe ilim me yayi saura?,sai samin daukaka daga wajensa,wala'alla ma nazo nafita iyawa kona qara tawa fasahar akai,rufaida...bari kiji,duk wanda yariga kwana dole yarigaka tashi,babu yadda zamuyi qaddararmu ce auren mijin wata,mijin da suka dauki shekaru tare,tun bansan wayeshi ba,itace tasoma bude masa idanu da duniyar auratayya,ita tahoreshi kan abubuwa da dama wadanda ko uwarshi data haifeshi bai koya wajenta ba,ta dabi'antar dashi,to ta yaya keda kika shigo jiya ko yau zakice tashi daya saikunyi kafada da kafada da ita idan har ba kin samu banzar uwar gida ballagaza ba?,dole ki koyi siyasa da kwantar dakai bana cutarwa ba,wanda zaki zauna ki dauki darasin waye mijinku a wajenta,wanda ita tafiki shan wahal ke a bagas kika samu,tunda sanda tasoma zama dashi ba wanda yasan dukka halayensa na zahiri dana badini bare yagayamata ,bare takiyaye,sai dataci wuyarshi wala'alla kafin ta gama fuskantarshi a daidaita,ke kuwa ga satar amsa ga leakage kin samu,ruwanki ki kwantar dakai ki samu ilimi,ruwanki kita hauka darajarki na raguwa maimakon tayi sama,ba naki bane shiga da qafafa da nuna qarfa qarfa,bayan kedin cikin duniyar aure kamar jinjirin da aka haifane yau yashigo duniya,ta yaya zaice yafi dan shekara goma ashirin,ashirin da wani abu sanin kan duniya?,idan kabi komai sannu a hankali duka rayuwar bawata mai zafi bace" tabe baki rufaida tayi tana sosa qeya
"Me zafice ni a wajena indai akan kishiya ne,tunda gashi ita tayi sila da har wai jibril xai iya kallon qwayar idanuna yacemin nataho gida" ta qarashe zancan da alama abun na mata zafi haryau,nan ta kwashe komai ta gayawa zahra,murmushi kawai tasake yi
"Rufaida kenam,to wallahi na raina wayonki mayau,waya gaya miki ana dambe da kishiya?,ana harka ta masu aji meya kawo akuyanci a ciki?,ai yanzu kishin masu aji ake,mijin da kuke neman fada da matsayi a wajensu ku tsaya gabansa kuna dambe kamar awakin da aka sako sunajin yunwa?" Sai zahran tamiqe saboda ganin kiran maigidanta da tayi,da alama yana kan hanyar zuwa daukarta
"Ni wannan zancan wallahi kunya ma yabani wai dambe kamar wasu 'yan nursery?" Saita kwashe da dariya saboda harta hango su suna kici kici da juna,harara rufaida ta watsa mata tana dariya dariya
"To 'yar wulaqanci,awajenki ne wani abu,ni a wajena fidda raini ne wallahi,saboda na fusakanci yaren datafi ganewa kenan jakar"
"Towai ina uwargidan naku?,ita bata cewa komai ba abinda ke hadaku?"
"Uhmmm,rabu da wannan wadda haryau nakasa gane dame zan karya lagonta,kome nayi mata yi take kamar bata gani ba kobai bata mata rai ba,na rasa me zan mata ya tsaya mata a wuya"
"Dakyau,da alama tasan abinda takeyi"
"A hakan?,kishiya na maka amma ka nade hannu,wallahi ba'a haifi 'ya ba"
"To ai kuwa kinga yanzu ta tsira da mutuncinta a idanun mijinta,tana dakibta asirinta rub a rufe" da wannan hirar ta raka zahran waje tawuce gidanta bayan ta mata nasiha duk da tasan ba lallai tadauka,tunda bayau aka soma ba.


Kwana uku tsakani saiga kakarsu,tunda taji sallamarta hankalinta yatashi,tasan halinta sarai,macace da bata daukar wargi ko raini,barema tasu tasake tsami tun randa za'a kaita data mata fadan tabi abokan zamanta su zauna lpy tamaida abun wasa,hakanan dai aka gaisa,tana ta mata fara'a da nan nan da ita don kada tayi wani ba dai dai ba.


Sai data gama hirarsu tamiqe zata fita sai tace
"Me kikeyi ne a gida,kamarma bayau kikazo ba ko?" Waigowa tayi,tayi wuqi wuqi da ita,suka hada ido da mamanta,saita dawo tazauna tana fara'a
"Banajin dadine,shine nazo,amma na warware,ina saka ran komawa ma da zarar abba yadawo" washe baki tayi sosai cikin fara'a
"A'ah,toko kishiya ko miji aka samar mana?" Dariyar jin dadi tayi na yadda qaryarta takarbu tace
"Uhmmm,to gamu nan dai"
"To Allah ya inganta" mamar na wajen natace komai ba,irin matan nan ne da basu da yawan magana,sanyi da shuru shuru,amma akwai shegen son 'ya'ya,da dauke kai akan wasu kusakuran da suke da buqatar a gyara musu amma sai tayi biris.


Tunda tsohuwa harira tazo gidan rufaida bata da sukuni,addu'a kawai take Allah ya tattarata takoma inda tafito kafin abbanta yadawo gari,aikuwa addu'arta bata amsu ba,saboda kwananta uku saiga abban nata yadawo,wanda bayan yakirata sunyi magana bai shawarceta ba yanemi ganin jibril,hankalinta yatashi sosai bayan daya shaidawa baaba harira wadda take mahifiya ce wajensa,ranar kuwa anga sauka da hawa na masifa da bala'i
"Eyiii,yo baga abinda nake gayamiki ba,'yar bokon qarya,bokon asara,kin gama cika baki da tutiya amma baki iya zama da miji lafiya lau ba,aure duka duka watanni ba'a cika shekara ba amma gaki a gida,to billhillazi baki isa ba,ni bazan dauki kowanne iskanci ba,ki kuka da kanki idan yaron nan yazo naji akasin abinda kika fada" baki ta turo tana sake jin haushin ma yadda jibril din yayi burus da kiran da aka masa kwana biyu kenan
"Ni wallahi hajiya bazan zauna yana maidani tuwon cushe ba,yayimin matansa suyimin,mena qaru dashi ne a aurensa,can mata sun zira maka ido,ga hayagagar yara,baka huta ba ko kadan" duka takai mata aikuwa taci nasarar samunta a baya,ta gantsare saboda taji dukan,tsohuwar akwai qwari,sannan akwaita da zafi
"Haka kikace?,to muzuba nidake don ubanki,ni yaran wasuma saita musu sahu nake bare nawa".


Kwana uku saigashi yazo,a dakin baqi dake soron gidan aka saukeshi,rufaida da mamanta na gefen hajiya harira,sai abba kusa da jibril din,kamar gidansu mmn ummi nan ma basu tauye kowa yafadi abinda yasani ba,saidai rufaida kamar mmn ummin itama ta tsagalgale tadinga qarawa zancan armashi,wanda hakan yasa hajiya tayiwa jibril umarnin yatashi yayi tafiyarsa tun ba'akai ga qarqare zancan ba,dukkaninsu babu mai magana yatashi yamusu sallama yafuce abinsa kuwa kamar dai gidansu mmn ummi,shi kansa a hanya mamaki yadinga yi,abinda sukayi din sai suka sake sane masa arai,tunda har basa iya tausa harshe gaban manyansu ta yaya zasu iya zama da miji?,shi dinma kawai soyayyar da suke masa ne yasanya tun farko suka yiwa halayen nasu ado suka biye aibukansu.


Bai mantawa sanda akwai sanda yake neman auren mmn ummi,sabani yahadashi da mmn amir,a sannan yana tashensa da ganin rashun haquri da kishine yasa take abubuwa saboda zai qara aure,shi kuma babu uban daya isa ya hanashi,yaje yakai qararta,har gida wanta yazo yamata tas har kamar zai daketa ma,daga kai batayi ta kalleshi ba bare tamaida masa magana,sai qas da kanta da tayi tana sharar qwalla,daga ranar kuma bata kuma bari tayi abunda zaikai qarar tata ba,ajiyar numfashi yasaki,yana godewa Allah da shaidan da kuma 'yan tunzura basuci nasara a kanshi yarabu da nagartacciyar uwargidansa ba.


"Nace ba,ajiya ai ba'a haka,dakin barta itama tagama fadar matsalarta duka sai a taru a gyara" cewar mmm rufaida,wata harara hajiya harira ta banka mata wadda tasanyata sadda kai qas
"Eh tabbas haka yake,tana da ra'ayi fa da 'yanci,ke rufaida!" Ta qwala mata kira
"Ki hada kayanki tsaf gobe dake zan wuce gida" ita sai hakan yamata dadi,can gidan hajiyan babu yara,tana ganin acan din sai tafi sakewa,tunda babu yara aiba wani aiki mai yawa ba kamar gidansu ba,kana babu mai takura mata,saboda haka babu jinkiri tasoma hada kayan nata washegari tabita suka tafi.

**** ******* ******


Ganin yaje dukka gidajen biyu amma bai mata zancan kowacce zata dawo ba yasa dole ta sake tunkararshi da maganar
"Bbn amir,dadai kayi haqurin dai,duk abinda haquri bai bada ba,rashin haquri bazai badashi ba,kayi haqurin kadawo dasu,tunda kaga ni yanzu nasoma jin ciwo,wanda dagashi yana gaba gaba saina naquda fa,ka dawo dasu kodon 'ya'yanka" shueu yayi bai tanka ba,yana nazari cikin ransa,idan akwai wadda zai dawo da itama yanzu bata wuce mmn ummi ba,itace yaran ke bashi tausayi duk da babu abinda suka nema suka rasa,asalima sunfi kyau wajen mmn amir din saboda kulawa da suke samu,saidai cikin satittikan nan tacika masa waya da saqonnin ban haquri dana nadama(meye amfanin aikata hakan?,duk abinda kikasan daga qarshe ke zaki fado qasa warwas kadama ki soma aikatashi),kira kuwa saidai yayita rejecting,shi kansa yasan halin yayan nata,baida sauqi,bazai qyaleta ba.


Sai da aka qara sati daya sannan yadawo da ita,a sannan sallah saura kwana daya ranar jajiberi da daddare,jinta tayi kamar a aljanna,ashe duk dadi gidan uba idan ba dole ko mugun matsi cutarwa takura ko masifar dakan iya nakasta rayuwa ba gidan miji yafishi.


Ta sauke numfashi a dakinta sanda take tuna nasihar qanwarta jamila
"Tun baya dama mmn ummi aikin yaudari kanki,idan gemun dan uwanka yakama da wuta naka kake shafawa ruwa,duk macen dake da cikakken hankali wallahi bai cancanci kiyi murna ba saboda kina amarya ana fifitaki akan 'yar uwaki ba ita ana wulaqantata ba,kuka ya kamata ka zauna kayi da hawayenka,ka kokawa kanka saboda watan watarana,abinda yaci doma bazai bar awai ba,toke ki godema Allah ma,bai miki abinda yayiwa mmn amir ba,kafin tashigo Allah yaganar dashi ya sauya halayyarsa,to saiki godewa Allah daya kawar miki da kwasar naki sakamakon,ki kuma sawa ranki haquri kan kishi,ki tuna haka mmn amir taji sanda zaki shigo,ke fiye da hakanma,saboda ita tasoma samunshi a farko,tana tsaka da rayuwarta daga ita saishi sai gako ciki,gwara ke kin taddata baki zauna ke kadai ba,amma saikika zauna kika biyewa zuciyarki,yanzu na tambayeki don Allah?" Shuru tayi tana kallon jamila,wadda take mamakin hankalinta wani lokaci kamar itace yayar ba maryam din ba
"Dake da mmn amir data kwantar da hankalinta ta iya allonta kuma taketa wankewa waye yafi wani samun kwanciyar hankali da riba?,banda samun qima a idanun miji?,kin taba tunanin meya siya mata dukkan wadan nan?,zaki iya tuna yaushe

Please Login or Register in order to submit comment