Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

secondry bata da komai?,wucenan wallahi"
"K'nnnn,to ai shikenan,yanzu yaushe zaki shiga kasuwar?" Dan shuru tayi sannan tace
"Ina tunanin anjima kadan,don akwai wasu magunguna da zan siyo wanda yakamata ace nashasu tun last week amma ban samesu ba,to tayimin waya ta kawo nazo na amsa" baki anty luba ta kama tana dariya
"Lallai rufaida,kurman tanadi kawai akewa auren nan" fari tayi da idanu cikin jin dadi
"Kedai bari kawai anty,burina kawai nazama tafisu,duk da yanzun ma nasan tafisu dince" dariya tayi ta juya tafice tana cewa
"Idan kin tashi tafiyar kimin magana inada saqo"
"Tohm" ta amsa mata tana maida kanta tasake gyara kwanciyarta,tanajin dadin yadda take juya jibril son ranta,kamar sitiyari a hannun driver ba tare da wata matsala ba,hakanan ba tare data nemi komai ta rasa ba.👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA* 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi *Musa Huguma*


*BABI NA UKU*


"Adawo lafiya,Allah ya tsare" maman amir dake miqewa daga duqen gogewa baban amir takalma da tayi ta fada
"Allah yasa,shikenan babu wani abu?" Ya fada cikin sigar tausayi,har cikin zuciyarsa yana jin tausayinta,girmanta da qimarta na kuma daduwa cikin ransa,sai a yanzu ya gane ba qaramin haquri tayi dashi ba a wancan karon da yake fagamniyar kawo maryam gidan,gashi yanzun maryam din ta kasa daya cikin goman haqurin da ita halima tayi dashi,bayan shi a karan kansa yasan cewa bai mata kwatar abinda ya aikata ga halima din ba wancan lokacin
"Babu komai,saidai awo kawai da nakeso naje" baice komai ba yashiga laluba aljihunsa,yaciro naira dubu daya da dari biyar,cikin mamaki ta saka hannu ta amsa tana dubanshi,yadan saki murmushi
"Kije kiga likitan,sauran canjin ki riqe kya sayi wani abun a hanya" da mamaki saman fuskarta take juya kudin,ba kasafai yake mata kyauta irin haka ba,duk da cewa dama itadin ba wani damuwa tayi ba,don tana sana'arta tasaida ruwa da lemo da qanqarar yara,kuma ta rufa mata asirinta sosai,tana ciniki ba kadan ba,don ada firji daya gareta ta sake siyan wani ya zama biyu,daya tazuba ruwa zalla,daya tayi lemo zobo ginger da kunun aya da qanqarar yara,daya daga cikin abinda yasake kawo rashin jituwa da kishinta a zuciyar maman ummi kenan,don tana tsammanin bban amir din ke boyewa yana mata abubuwa ba tare datasan cewa guminta bane,da farko burga ta dinga mata na ita ta girmi sana'a,don miji ya tsaya mata,bata neman komai ta rasa,lokacin ludayinta nakan dawo,maman amir din takanyi murmushi kawai don tasan qarshen labari ko ba'a rubuta mata shi ba,itama tahau wannan siradin,sai a baya ta gane ashe duka kurace da fatar akuya,tadauki darasi ta kama sana'a tana bidar na kanta,sai gashi a yanxu bayan wasu shekaru abun yana neman zamewa maman ummin dan zani,ya fara tara iyali,hakanan mata biyu gareshi gata uku nan zuwa,tilas abubuwa da yawa suka soma sauyawa,wanda basuyiwa mmn ummin dashi kanshi dadi ba,suka dinga samun sabani,ta riga ta sangarce da saidai ta tambaya a bata,bata iya nema ba,hakanan take zaune,duk abinda mmn amir din tayi kuma ta zargi baban amir shiya mata,tun tana qoqarin fahimtar da ita harta tattarata ta watsar ta qyaleta,daga bisani idanuwanta suka gane mata.


"To na gode,Allah ya qara budi"
"Amin amin" ya fada yana sanya kai zai fice daga gidan,duk abinda ke faruwa mamn ummin tana bakin famfo duqe tana wanke kayan da yaranta suka cire,qasan zuciyarta tana jin kamar ra kama mmn amir ta daka,tana ganin duk ita ke daurewa baban amir gindi,har wani durquson goge masa takalma take da tsohon cikinta?,tana masa addu'a?,mutumin da zai musu kishiya aoba masoyinsu bane,kamata yayi su hada kai su yaqeshi harsai ya gaji don kanshi ya janye,amma tafi yarda da zancan hadixa data gaya mata idan ta tona zuciyar maman amir din qila fal take da farincikin za'a yiwa mmn ummin kishiya,tunda kishiya tabiyu tana bin wada kebi mata ne ba matar farko ba.


Tana kallonshi amma qyashi take tace masa a dawo lafiya,har yakai soro wata zuciyar ta tunzurata,donme zai baiwa mmn amir kudi amma ita data aika yara jiya suka gaya mishi ya bata cikon kudin me takalmi yace bashi dashi?,wuf ta miqe ta rufa masa baya.


Dab da zai fita ta rafka masa kira,da mamaki yajuyo yana kallonta,ta qaraso dab dashi fuskarta kamar tasowar hadari hannunta aqugu
"Wannan rashin adalcin da kake gwadamin ya isheni hakanan,jiya jiya nace ka bada cikon kudin takalmina kace babu amma yanzu ita ka narka mata kudi zataje awo,toni ka gayamin a wacce bolar ka auroni ne?" Sakato yayi kawai yana dubanta cike da dimbin mamaki,ta manta lokacin da yake bata ninkin kudin da ake buqata a asibitin,kuma yadauketa cikin motarshi ya kaita yadawo da ita,wani lokaci harda qwalama ta masu ciki amma mmn amir din koda ta nuna damuwa a fuska badai kaji abakinta ba,ta manta sanda take tsiro da ankon qawaye na babu gaira babu dalili ya dauka kudin ya bata ba tare da mmn amir din tace komai ba.


Kafin ya furta komai kira yashigo wayarsa dake gaban aljihu,ya zaro yana duban me kiran,rufaida ce,murmushi ya subuce masa wanda ya tunzura mmn ummi
"Ina magana dakai kayi banza dani kana kallon waya kanamin dariya kamar wata tababba?" Daga kai yayi ya dubeta sannan ya maida kansa kan wayar yana shirin dagawa fuskarsa washe da fara'a
"Baki da amsa ne ai" kafin yakai ga kara wayara a kunne tasa hannu ta warce wayar cikin fushi da fusata tana duba me kiran,dama jikinta ya bata ashe kuwa itace,a cike take da ita dama,wancan kwanakin ranar girkinta data turowa baban amir din saqonni har guda biyu,wayar na kusa da ita tadauka ta karanta,ta mata reply na zagi itama ta maido mata,kafin ta sake maida mata baban amir ya karbi wayar,da sauri ta kanga wayar a kunnenta,kafin tace komai kalaman sun daki kunnenta
"Honeeeyyyyyyy" muryar rufaida ta ratsa dodon kunnenta cikin shagwaba
"Honey din uwarko kona ubanki,shegiya karuwa,masifa annoba,to bari kiji na gaya miki,wallahi sai kinyi danasanin shigowa gidan nan in gaya miki,banza shashasha kawai,ballazaga mebin mazan jama'a" ta qarashe maganar tana barin soron da sauri saboda amsar wayar da baban amir ke qoqarin yi,ta saka sakata a qofarsu ta tsakiya cikin hanzari,ma'ana ta rufe baban amir din daga can soron do ta samu damar cin karenta babu babbaka,wata dariya rufaida tasaki kaman taba kallonta ta tabe baki
"Tooo....yau kuma da haukar da aka tashi kenan?,bari na soma tambaya cikin gawarwarkin daya aje gidan wace ke a ciki,ta farkonce kome bi mata don insan yadda zan ciwa mace uwa dakyau"
"Ta uwarkice,nace ta uwarkice wadda bata ramin kanta saina wani stupid" dariya takuma yi saboda tunda taji ta jefo kalmar bature to ba shakka maryam ce
"Kice dai bama ramin kanmu saina wani,ina cewa kema saura kika tarar shi yasa zan shigo na tayaki muci tare,to bari kiji,ni bana fada a waya,ki tanadi duk wata masifa da bala'i da makamanki da bomabomai saina qaraso gidan,don waya tayimin kadan wallahi,wawuyar mace wanda batasan inda yake mata ciwo ba,saikin gane uwarki bata koya miki komai na game da yadda zaka mallake miji,ki jirayi shigowar rufaida zaki gane komai da babban baqi" daga haka ta kashe wayar qit
"Abu ta kazar uba,ni zata zagawar uwa?,wallahi yau saita gane shayi ruwa ne" mmn ummi tasoma kumfar baki tana banbami tare da qoqarin sake kiranta,cikin haka Allah ya bawa baban amir damar bude qofar wadda sabida sauri sakatar bata gama shiga ba dai dai bata sani ba,yana shigowa yakai hannu ya finciki wayarsa
"Ka bani,wallahi saina rama zagina"
"Bazan bayar ba ki qwata idan kina da qarfi"
"Allah ya isa ban yafe ba wallahi,da ita da wanda ya daure mata gindi,macuci azzalumi,aina haka mukayi dakaiba sanda kaje zaka auroni,Alla ya isa ban yafe haqqina ba,kuma zagina da tayi sai Allah ya mana hisabi dakai" juyowa yayi yana dubanta cikin matuqar bacin rai,zaiyi magana kiran rufaida yasake shigowa
"Kiyi haquri don Allah my rufeee...." Abinda yasona cewa kenan cikin kwantar da murya kana yayi shuru na wani sakanni,wanda hakan yabaiwa rufaida damar jiyo bambamin da mmn ummi wadda ke tsaye a bayanshi takeyi,murmushi yasaki yana cewa
"Yauwa dear....na gode" baiko waiwayeta ba ya saka kai yafice yana ci gaba da wayarsa da rufaidan,wanda tana sane tajanyeshi dama,hannu maman ummi ta dora aka ta zube a wajen,tana jin kamar zata tayar da bori,ita baban amir yayiwa haka?,mutumin dako bacin ranta baison gani shine a yanzu zai watsar da ita yawuce abinsa?.


"Haba mmn ummi,wai sau nawa zan gaya miki wannan?,yanzu meye amfani ko ribar abinda kikeyi,maqota da masu wucewa duka sunajinki?,kafin a tsinewa baban amir sau daya an tsinemiki sau goma koda mala'iku kuwa" harara tayi kaman zata watsa mata saita fasa,cikin qunar rai da fusata tace
"Kome baban amir yayi yasamu goyon bayanki ne,tunda kinsan hannu daya baya daukar jinka,ba yadda banyi dake mutare abinnan ba amma kika qi bada goyon baya,yanzu kinsan muggan kalamai da alwashin da yarinyar takeci a kanmu nida ke?,to nida ke mu shirya kayanmu dukanmu gaba daya saita fitar damu" murmushi maman amir tasaki tana kada kai
"Kome ta gaya miki maman ummi kece kikayi babban kuskure,ina ruwanki da budurwar mijinki?,meye hadinki da ita?,kin fita kusa da mijinki,kin fita daraja koda ba haka bane to a wajen Allah haka ne babu kuma wansa ya isa ya kankare,koda tashigo gidan kuwa karki manta zata jima bata cimma matsayin dake kike kai ba,tunda ko banza kin rigata samunshi,kin rigata samar masa da diya,to me yayi saura?,me zai daga miki hankali?,maman ummi...." Ta kira sunanta cikin nuna da gaske zata furta mata maganar
"Inada yaqinin nafiki son abban amir,na kuma fiki kishinsa" saitayi jagale tana kallonta,magana takeson gaya mata kenan kome?
"Qwarai,ina tare da abban amir tun auren saurayi da budurwa,tun baida wani abun azo a gani,amma daga sanda yasoma neman aure na sanyawa kaina salama,inajin kishinsa kamar na mutu,ina kuka saboda kishi,ina kasa ci in kasa sha saboda kishi,amma dana fuskanci wanda nake abun saboda shi shi jin ransa yake kamar sallah saina sawa raina haquri da dangana,na kawo idanu na zuba akan duk wani abu da zaimin cikin sani ko rashin sani,wanda zumudi da rawar kaine ya sanyashi dama wanda yayi saboda radin kansa,yanzu gashi an wayi gari na barshi da kunyar abinda ya aikatamin a baya,na tsira da mutuncina da darajata a idanunsa saboda ban aikata duk wani abu da zai nuna rashin nutsuwata ba,babbar zubewar girma ko daraje a wajenki na matar gida budurwar miji ta zageki,bari na tambayeki..."shuru ta sakeyi tana dubanta
"Tunda kuke da baban amir har kika shigo gidan nan kin taba kiransa na daga wayar?,kona taba kiranki dai dai da rana daya?,kin taba jin muryata ko ganina?" Kai mmn ummi ta girgiza sannan tace
"Duka ban taba ba,amma Allah yagani ni mmn amir bazan iya koda rabin abinda kikayi ba,wayar dare,kiran dare amma ace duka baki nuna ko daukan mataki ba?,bazan iya ba wallahi,babu wata shegiya data isa ta takani wallahi ko wace saina maida mata,duk wadda ta nunani da yatsa saina karyashi" ajiyar zuciya mmn amir tayi tana kallon mmn ummin,shi yasa a rayuwa duk abinda kasan bakaso kada kayima wani,idan ba haka ba kuwa,watan watarana saiya fado a kanka,sai an maka,sai an ramawa wanda ka cuta ko ka cusgunawa koka zalunta.
"Shikenan,Allah yabada sa'a" ta fada tana miqewa gami da bar mata dakin.

******* **** *******


"Wai maman amir mu mmn ummi zata wulaqanta?,har ta ganmu ta dauke kai tawuce daki?haka ta koma?,to do n yaya zai qara aure shine me?,me za'a fasa?"
"Mtseweeew,kice fa kika damu wallahi,ni tayita kumburinta idan taso ma ta fashe,qarin aurene babu fashi sai yayishi ehe" murmushi kawai halima tasaki tana zama bayan ta aje musu kwanon abincin da ita da kanta tashiga kitchen tazubo musu,ganin mmn ummi dake da girkin bata da niyyar basu din,shuru tayi na sauraron qorafinsu da yadda kowacce ke zuba baqar magana kan mmn ummin,dubansu kawai take don bata data cewa,zuciyar musulunci da ilimin addini kadai daya ratsata yasanya taci gaba da mu'amala dasu,a shekarun baya babu tamkar ya maryam a wajensu,a sanda ya niyyaci qara auren babu abinda bata gani ba daga gunsu,basa boyewa har a gaban idanunta
"Na qagu wallahi maryam tashigo"
"Wai kinga matar yaya kuwa?,tabdi,wallahi yaya yayi zabe"
"Ke ai wannan kankat ce,tayi a rayuwa,ga ruwan mutunci zallarsa,bakiga yadda takesonmu muda umma ba"
"Kinga kyautar data aikowa umma da ita kuwa?,ke yaya kanshi fa yamato,donta iya soyayya"
"Nce gareta mafa,wallahi da yaya zai barta tsaf zata dinga fita aiki,amma tace masa ma ita tafison tazauna gida takula dashi" ire iren wadan nan maganganun dama wadansu wanda ba zata iya tunasu ba ba wanda basu fadi ba a gabanta,babu kara alkunya ko kawaici,sunsa qafa sun shure duk wani alkhairi nata kyautatawa da haba haba da take dasu,a lokacin ambaton Allah datake yawaita yi shi kadai yazame mata haske,uwa tagari kuma da take da ita tayi mata jagora,matakin farko data soma mata dannar qirji,ta kuma kwabeta,a yanzun taga alfanun hakan
"Wallahi maman amir ni yadda kike yafi komai burgeni" cewar jidda qanwar baban amir,sai a sannan tadago ta dubeta
"Kishi na hankali da nutsuwa ba irin nata ba na jakan mata,ai rannan rufaida ta gayamin komai,wallahi ta burgeni data rama abinda tayi mata" cewar jidda tana ci gaba dacin abincinta
"Indai rufaida ce dai dai da ita take,yarinyar da takejin quruciya da karatu akanta" dariya haula tayi
"Nifa harso nake naga ya zatayi idan rufaidan tashigo,gaskiya tana ruwa,maman amir kedai wallahi kinyi a rayuwa da kika iya kama girmanki,kaman baki da kishi" kai ta girgiza kawai tana fidda dan qaramin murmushi,sa'annan cikin nutsuwa ta dubesu
"Babu wata mace da bata da kishi,duk matar datace bata kishin mijinta toba shakka an samu matsala,kuma idan aka zurfafa bincike akwai wata a qasa,zan muku maganar daban taba muku makamanciyarta ba,abinda kawai zanja hankalinku akai shine,ku gane cewa dukkan mace macace,kuma ba'a cewa jifa idan yawuce kaina yafada kan uban kowa,koda baku da aure ke jidda kina dashi,kuma kuma wataran matan wasune,gidan wasu zaku je,cikin dangin wasu,Allah yasa kun fahimceni"
"Eh hakane,amma wallahi kawai dai duk wanda yadebo da zafine bakinsa,ni banga abun wannan kishi hakaba ina dalili?" Cewar jidda tana watsa hannu,sai kawai mmn amir din ta watsar da maganar tadauko musu wadda ta kawosun,wunin da za'ayi cikin gidan.


*BAYANA AWANNI*


Tunda ta kawo masa abincin ta tattarashi ta watsar,banda ma 'yan nasihun da maman amir tayi mata da babu abinda zai sanya ta saurareshi,shima cike yake da ita,hakan ya sanya baibi ta kanta ba yaci gaba dacin abincinsa,yana wasa da ummi daketa sabgarta saman carfet,lokaci lokaci yana diban abincin yana bata da cokali harya kammala,yasha ruwa yadauke ummin ya karkade mata jikinta yadorata saman cinyarsa sannan ya dubeta
"Me dame kike da buqata keda yara,inajin saura baifi sati uku ko biyu ba tariya" wani kallo ta watsa mata,kishi na tokare mata a qirji,ta rasa ma me zatace masa
"Kaje ka qarawa amaryar inaga hakan yafi armashi"
"Ohkey" kawai yace ya saba ummi a kafada yafice,binsa tayi da kallo,watoma bashi da lokacin lallashinta kenan barema ya biye mata suyita ba ko zata samu sassauci cikin ranta.


Kai tsaye dakin mmn amir yanufa,tana kwance saman doguwar kujera sanye da doguwar riga mara hannu,yaran duka na zaune qasa suna kallon tv,sallamarsa yasa kowanne maida hankalinsa bakin qofar yana fadin abba,abba,miqewa tayi daga kwanciyar datayi tana gyara zamanta,bayan ya gama da yaran ya dubeta
"Sannu" yace da ita yana dubanta,murmushi tadanyi sannan tace
"Yauwa"
"Ammm....nace dame dame kuke buqata kedasu ahmad gaba daya dasu ummi" ganin ya bata dama yasa lissafa masa iya abinda take ganin tana da buqata din,aljihunsa ya lalubo ya qirga kudi ya miqa mata,hannu biyu tasa ta karba sannan tayi masa godiya,ya sake qirgo wasu ya miqa mata
"Wannan nasu ummi ne,a musu siyayyar duka abinda ya dace" hannu tajanye tana kada kai
"A'ah,ka bawa ummansu ina ganin ta fisu sanin me dame suke buqata"
"Karbi nan,nasan da itadin ai nabaki ko?,banason jan zance" haka tasa hannu ta amsa badon son ranta ba,ta sake masa godiya,ya dubi amir
"Dauki ummi ka maidata wajen mamarta ta soma bacci" ya miqe yadauki yarinyar,shima yarufa masa baya.


Kudin ta irga,ya wucema yadda ta tambayeshin,tasan zai isheta tagama duk wata siyayyarta harda ma qari a sama,saita hada da kudinsu ummin ta adana da zummar gobe tasamu mmn ummin,da alama tamasa halin nata ne shi yasa ya watsar da ita shima.

*mrs muhammad ce*👑👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA* 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *safiyya Abdullahi Musa Huguma*


*BABI NA HUDU*



Gidan babu kowa yayi shiru kasancewar yaran dukka sun wuce makaranta maman ummi tana dakinta wanda tun sape bata gilmawarta ba itam tana nata dakin saidatagama kintsa duk abunda xatai na ayyukanta sannna ta dauko kudin da baban amir yabata sannan tanupi dakin maman ummi akwance ta tarar da ita tana kallo ummi najin sallamarta tararrafo gunta tadauketa tana cewa xoki naushi dan uwanki na ciki yadda kikasaba sannann tai sallama takarasa parlourn tashi tai maman ummi tai tazauna fuskarta babu walwala maman amir takarasa tasamu daya daga cikin kujerun parloun tazauna tanacewa muntashi maman ummi murya acushe ta amsa tanacewa lafiya lau to madallah tafada tana mika mata kudin dake dake hannunta amsa tai sannan tace wannan kuma namaye maman amir tadubeta tace kayan siyayyar yarane jiya baban amir yabasu"
"Jiya da yaushe?"
"Sanda kike can kina sake kashe kanki wajen mijinki,mmn ummi bakyajin magana,amma Allah yagani nayi iya abinda zan miki,shine shaida" daga haka bata jira taji me zata fada din ba ta miqe tafice a dakin.


Da kallo mmn ummin ta bita takaici na cikata,wato kudin siyayyar 'ya'yan nata ma yafi qarfinta?,yafi qarfin yabata da hannunta saiya kaiwa kishiyarta?,qwafa taja ta dauki kudin ta irga,saita rabasu biyu tana ayyana abinda zatayi dasu,rabi kawai zatayi musu siyayyar dasu,saura kuwa zubin adashinta zatayi dasu,ribar qafa kenan ta fada cikin ranta.


******** ****** *********


"Wallahi wallahi babu shegiyar da zanwa girki,girki?,ni nace ka qaro auren kenan,idan sunsoma su rube saboda basuci abinci ba" ta qarasa maganar tana kashe famfo gami da daukar botikin wankanta tashige bandaki ta banko qofar.



Shuru ne ya ratsa tsakanin baban amir da mmn amir dake tsaye cirko cirko,bacin ran mmn ummi yana kamashi qwarai da gaske,cikin halayen datake masa bai taba ganin daya daga ciki mmn amir ta gwada masa ba,koda a sanda take neman auren maryam din,kunya duka ta dabaibayeshi,musamman daya tuna sanda babu kunya ba komai ya baiwa mmn amir kudin cefanen abincin 'yan jeran mmn ummin a wancan lokacin,yace lallai ta girka,a sannan batajin dadi ta gaya masa amma yarufe idanu ya caccaba mata magana,yana ganin kamar tsabar kishi yasanyata tace bata da lafiya qalau take,baiso akai girkin gidansu ne,azo aga kamar bai isa da gidanshi ba,ko kan gidansa ba a hade yake ba,kasa magana ya motsa zaibar wajen
"Ka kawo kawai sai ayi kamar na wancan karon" yajuyo yana dubanta,farinciki ne qasan zuciyarsa,saidai yana ga bai mata adalci ba ayadda tayi nauyi haihuwarta nan da satittika ya bata abincin masu jere,ga wadda takw ziqau ma tace ba zatayi ba inaga ita
"Ki barshi kawao,zankai can wajen gwaggwo sai ayi a kawo musun" ko daya batason yakai wajen mahaifiyarsa kafa wata sabuwar maganar kuma ta bullo,tasan halin surukar tasu qwarai da zafin rai da fada,,wani sabon bacin ranne kawai
"Babu damuwa,tunda anyi wancan wannan ma bazai gagara ba" kai yake jinjinawa,qimarta da nauyinta na kamashi,a sanyaye yace tabiyoshi daki ta karba.


Kudi ya irgo masu yawa ya miqa mata,ta amsa tana dubanshi tare da kallon kudin
"Sauran kiyi amfani dasu" ya furta yana kallon idanunta,godiya tayi masa kana ta miqe ta fito,sai data nutsu ta lissafa kudin da zai isa ayi komai,sauran canjin suna da yawa ba laifi,data lissafa taga sun kai mata kudin datake na cikon da zata sauya plasma dinta.

******** ***** ********



Zaune take a falon qafafunta na amiqe,gefe wata matace wadda a qalla ba zata wuce shekara talatin ba,kana kallonta zakaga kamar da suke da mmn amir,hira suke jifa jifa har dayar ta jefo magana kan gidansu mmn amir din
"Yaushene tariyar amaryar taku ne?"
"Saura kwana goma inajin ko sati,don cikin satin nan masu jere xasuxo" baki ta tabe sannan tace
"Wannan karon kamar ba kishiya za'a miki ba anty halima,shi kuma mijinku haka Allah gada masa" itama nata bakin ta tabe
"To yaka iya da abinda yafi qarfinka?,idan fada yafi qarfinka ai wasa kake maidashi samira,wancan karon da hankalina yayita tashi me aka fasa?,meye kuma ya sauya?,tunda ya gingimo yakuma dauki aniya aisai ka tayashi da idanu da kuma addu'a ko?" Kai ta girgixa
"Haka yake,amma banga kina wani shiri ba" qaramin murmushi tasaki
"Nice kuwa me shiri,amma yanzu ta abinda yake cikina mu rabu lafiya nake tukunna,bama wannan ba,bari na dauko miki kudin plasma din nan ki tafi dashi,yanzu abinda ya rage kawai kiyi xancan labulayena da mutumin,kudin sun samu shi nake jira,yayimin masu kyau sosai don Allah kalar kujerun,zan dauko miki dinkunana ki tafi dasu duka ki ajemin"
"Amma dai anty halima aiko kala biyu kya dauka ko saboda zuwan amarya"
"Xan dauki uku ma,amma nikam yanzu batasu nake ba,ta lafiyata nake"
"Allah dai ya raba lafiya"
"Amin amin,don Allah idan baban abba zai barki kizo mana jibin ki tayani girkin 'yan jeren,yaran duka suna makaranta kya tayani zama ma"baki samiran ta kama
" au wannan karonma keya hada da girkin?,bai baiwa waccar ba taji yadda kikaji?"
"To meye a ciki?,ko nayi ko banyi ba zaikai wani guri ayi,kuma a hadamu duka a zaga,sannan kuma babu wani abu da zai fasu,kinga ni mubar wannan xancan don Allah muje na lissafa abinda yarage na baki" daga haka ta yunqura tamiqe samiran ta bita tana sake jinjinawa juriya da qarfin halinta.

********* ***** *********



Tunda safiyar ranar bayan mmn ummi ta sallami yan makaranta tafito tasoma hada duka kayan girkin da zatayi amfani dasu,maman ummin nata shige da fice gami da sabgoginta,batace ma maman amir din kanzail ba,sai itama tadan bata iska don ta fuskanci yau a cike take fam,su kansu yaran sun daku kafin Allah ya taimakesu su wuce makaranta.


Duk wasu kan kayanta ta hadesu tsaf,tsinkenta bata bari tsakar gida ba,duka mmn amir din ta ankare da ita amma bata tanka ba,hakan yasake qular da mmn ummin,a yanzun tafi yarda da zanxan hafsa datace ita tabaiwa baban amir goyon baya,kuma tabashi goyon bayanne saboda su quntata mata don tazo ta taras da ita itama a gidan,ta wuce yafi a qirga amma ta rasa dame zata takali mmn amir din da zance,har daga qarshe tace
"Hmmm,sannu da aiki" saita daga kai ta amsa mata kawai taci gaba da aikinta
"Kekam da daurewa qarya qarqashi kike,yanzu masu zuwa yiwa kishiyarki jere kikewa wannan hidimar,wallahi ko 'yar sarkin santanbul ce bata isa ba" murmushi ya kubcewa mmn amir
"Ba saboda su nake ba,saboda mijina nake albarkacinsa sukaci,kuma wannan din ba komai bane ni a wajena,tunda ba yanzu na saba yiba" sai ta tabe baki
"To madalla,Allah ya taimaka" bata amsata ba taci gaba da aikinta,a haka samira ta cimmata ta kama mata sukaci gaba.


Kafin lokacin isowarsu harsun kammala,tayi wanka ta sauya kayanta masu kyau wanda suka sake fito da ita dukda tsohon cikinta,tuni mmn ummi an dauki kwalliya kamar wadda aka gayyata wani babban taro,ta samu kujera ta dasa bakin qofar dakinta wanda yake fuskantar dakin amaryar,duk da yadda takejin zuciyarta kamar zata faso amma haka ta daure don tanason ganin tunqwal uwar daka,hakanan tanaso taga idanun kowacce shegiya da nasu salon.


Mmn amir kuwa tana daki suna hira abinsu da samira,tana ta taya samiran aikin duwatsu na hannu da akewa kaya beadwork,ba'a wani jima sosai ba sallamar baqin ta ratsa tsakar gidan,gaban mmn amir yafadi,saita kira sunan Allah tana tattara nutsuwarta,mmn ummi dake tsakar gidan kuwa wayarta a hannu tana danne danne,tana jinsu har suka qaraci sallmarsu suka shigo babu wadda ta tankawa,sai sukayi turus ganinta a tsakar gidan suka hau kallon kallo a tsakaninsu,daya daga cikinsu ce tasake maimaita sallamar waiko ji ne batayi ba ganin kota dago ta dubesu,wannan karon dagowa tayi ta musu wani banzan kallo ta watsar,ganin

Please Login or Register in order to submit comment