Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakanbi girma girma ne,zaune yasameta itama ga abun karinta ta saka a gaba,saidai bata taba komai ba,sai usman da mubarak dake karyawa abinsu.


Qafarta na dore daya saman daya tana karkadata,kana kallonta sau daya zakasan akwai abinda ke cin zuciyarta kuma tanason ta amayar,da qyar ta iya amsa sallamarsa kamar wadda aka shaqe takuma bishi da banzan kallo,bai wani lura ba harsai daya gama biyewa yaranshi yana yiwa ummi wasa sannan ya dubeta
"Mun tashi lafiya" yasoma gaidata maimakon ita ta gaidashi
"Gashi nan kaga alama"
"To madalla" ya fada a taqaice,tunda yaga yanayinta da yanayin gaisuwarma yasan wani abune kuma na daban,bata rabo da qorafi sam a rayuwarta,kullum cikin matsala daga wancan sai wannan,shi yasa bai fiya jimawa a dakinta ba,hakanan ko ranar girkinta ba wani doguwar hira suke ba idan ba ita taso ba.


Da dafari sanda yake dokinta yana ganin tafi mmn amir iya komai saboda karatunta ya dara nata bai ganin illa da aibun dukka wadan nan halayen nata,saida tafiya tayi tafiya sannan ya tantance tsakanin aya da tsakuwa.


Yana dire ummi yace
"Xan fita,akwai wani abu?" Ya qarashe zancan yana dire mata kudin cefane,da harara tabi kudin kafin ta maida dubanta kanshi
"Wallahi wallahi kana bani mamaki jibril,bansan rainani dakayi dukka cikin matanka yakai haka ba,ku gama tiqa dariyar kaida waccar me zubin karuwan,kashig dakin mmn amir ka kusa kashe minti goma sannan nika shigo a wani tsaitsaye kabani kudin cefane,wato bauta itace aikina ko?" Yaran yaduba,baison wani cecekuce gabansu,wanda wannan dabi'ar mmn amirce takoya masa ita,da fari bai dauki hakan a bakin komai ba,sanda yake ganiyar neman auren mmn ummi yakan iya fadata da fada gaban yaran,koya caccaba mata maganganu,iyakaci tayi shuru,idan sun mata zafi da yawa tayi kukanta ta goge hawaye.


Sannu sannu sai Allah ya canzashi,wanda yasan ba komai bane yakawo hakan face addu'a data saka a gaba babu dare babu rana.


Yasha raba dare suna waya da mmn ummi suna kwance gado daya da mmn amir,baya shayi ko shakkarta,takan tashi ko kallonshi ba zatayi ba,tun a sannan bata da bandaki cikin falo sai tsakar gida,nan zata fito ta daura alwalarta ta koma falo tayi shinfida tahau sallarta,tabarshi shi kuma cikin dakin ya qaraci wayarshi har yayi bacci,wani lokacin bai sake ganinta sai zashi sallar asubahi.


Yakanyi mamaki idan washegari tatashi wasai tashiga sabgarta da yaranta,fuskarta cike da annuri,wanda duka hakan bai rasa nasaba da wannan sallar dare data kusa kwana yi.


"To tashiga hankalinta,idanma tanayine saboda muji n bata a gabana,saidai idan ita bata da tarbiyya mu muna da ita ehe" bai saurareta ba sai yunqurin danne zuciyarsa da yake,yasa kanshi yafice daga dakin.


Ya tabbatar da cewa kura ce tayi lafiya,ko kuma yakoma kan tarbiyyar mmn amir ne,inda ta sameshi a lokacin da yake a bbn amir dinsa bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman ba yana kallonta,koda bada shi take ba,saidai mmn amir ta zame masa mudubi,hakanan yakanji a karan kanshi bai kamata yayi wani abu naba dai dai ba,kobanza a yanzun iyali yake tarawa.


***** ***** ***** ******


Cikin kwanaki amarci sosai rufaida takeci yadda takeso,tasamu kusan duk abinda takeso daga wajen bbn amir din,don idan yadawo daga kasuwa babubinda yake sake fita yana tare da ita,hakan yakan mata dadi yana faranta ranta,takanyi kowacce shiga da take tunanin zata ja ra'ayinsa da hankalinsa,ta kuma samu yadda takeso,zub da habaici jirwaye da kamar wanka,dariya da darrarku na cusa haushi da takaici dukka ta baje abinta.


Babu wanda ke qunsar takaici irin mmn ummi,nafarko bata da wata sana'a da takeyi face zaman dabaro,zaman hira,zaman charting ko xaman kallo,uwa uba gaba duk wani motsi na rufaidan idanunta yana kai,kome take tana sane dashi tana biye dashi,hakan ya sanya tunda rufaidan ta fuskanci hakan saita qara qaimi,kullum burinta ta bullo da wani sabon abun dazai basu takaici.


Saidai ta bangaren mmn amir ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,wasu abubuwan tana sane dasu itama,amma data fuskanci zuciya na neman janta saita dawo da sana'arta,nan da nan taci gaba da saida ruwa da lemonta,kasancewar ta iya sosai,ga uwa uba tsafta,hakanan idan bata komai takan zauna tayi tilawar qur'ani,idan ta gaji ta kunna kallo ta taba,dama ita ba charting take ba,idan tagaji da kallon kuma takan kunna karatun qur'ani yadda zai cika dakinta ya hanata jin motsin kowa da komai,yara kam har yanzu bata daukosu ba,don haka wuni takeyi daki abinta,idan dare yayine takan nemi izini wajen abban amir tadan fita tayi tattaki kadan tadawo gida,takan leqa wani sa'in gidan mmn laila maqociyarsu,kuma qawarta qwaya daya da take da ita,bata fiya shiga gidan tayi fitowar banza ba,takan qaru da ita ta fanni da dama,kusan halinsu yaxo daya,hakan yasanya suke abota sosai.


Abu biyu zuwa uku ke damun rufaidan,yadda ta fuskanci jibril din mutum ne mai son yara,uwa uba baya yarda da wulaqanta kowa cikin matansa,amma ta fuskanci kamar mmn amir din yafi kaffa kaffa da lamarinta akan mmn ummi,hakan yasanya tasake daura damara gamida cin alwashi.


Cikin haka kwanakin amarcin amarya rufaida sukaci gaba da turawa,har mmn ummi tagama girkin yazamana a yanzun rufaidan ce zata karba.


******* ******** *******


Karfe bakwai na safiya ya farka daga baccin daya daukeshi bayan dawowarsa daga sallar asuba,yazauna saman gadon sosai yana kallon rufaida daketa sheqar baccinta,donko sallar asuba batayiba kasancewar tana hutun sallah.


Hannunsa ya saka saman filon da take kai ya bubbuga yana tashinta,daqyar ta iya bude idanunta da sukayi jaa saboda bacci,mugun dadin baccin takeji sosai
"Tashi ki doramin ruwan wanka,saiki dafamin wani abu,zan fita daurin aure qarfe tara da rabi nakeso nafita" lumshe idanunta tayi tanajin wani yaji yaji na bacci,ta yaya tana baccinta me dadi zaice tawani tashi tadora masa ruwa da abinci?,ruwanne bai iya dorawa ba ko abincin ne dole sai yaci,itafa ba abinda tatsana tun a gida irin ka hanata baccin safe,daka hanata bacci da safe gwara kayi mata koma meye
"To" kawai tace dashi ta maida idanunta ta rufe,ya zaci taji,saboda haka yamiqe yafita falo yashiga bandaki don ya rage cikinsa kafin ruwan yayi zafi.


Saidai abun mamaki koda yafito wajen minti ashirin saiya sake samunta kwance abinta,babu alamun tatashi ma,sake tashinta tayi,ta dago kao cikin fusata,wanda har taja tsaki ba tare data tuna a inda yanzun take ba
"Wai meye?,nifa gaskiya bacci nakeji,kabari idan natashi saina dora maka mana" tana kaiwa nan tasake maida kanta
"Ya zakici haka,tashi da Allah,ina gayamiki zan fita ne qarfe tara da rabi fa" cikin qunar rai kamar ta kutuntuma ashar tatashi tazauna,fuskarta a dinke tsaf,bacin rai kamar tayi me?,ta kalli agogo taga takwas saura
"Haka kawai saboda rashin sanin muhimmanci mutum a akama a tasheshi,toko a gida ni iyanzu ina kwance,babu kuma wanda yake tashi na,sai kawai yanzu azo a hau tashin mutum" ta sake jan tsako bayan ta gama qunquninta.


A falo ta wuceshi fuuu ko kallonshi batayi ba,ya bita da kallo kawai harta fice,mamaki yadan kamashi,na meye quncin tashin?,wani lokaci kafin suyi aure iwar haka yana shirin fita waya na maqale a kunnenshi suna shan hira,kullun dawuri take tashi saboda shi,yanzun kuma na meye nauyin?.


A kitchen kuwa bayan ta dora ruwan wankan saita samu waje tazauna,bacci nacin idanunta kamar takifa,ba zata iya tuna yaushene tatashi iwar haka daga bacci ba a gida,idan ba rashin lpy take ba zata asibiti,ko wata lalura ta daban.


A daddafe tagama dafa ruwan tajuye masa tashiga dakin ta dire masa
"Yauwa,shayi xaki fara dafamin,saiki soyamin doya daqwai,ta isheni,idan ita zakuci kiyi duka gidan,idan kuma wani abun zaki dafa muku to" idanu ta fiddo,kusun uwa,bayan shayin ma sai an dafa wani abun na daban?,na daban dinma sai ta dafa da kowa cikin gidan?wallahi ba zata iya wannan tsiyar ba,ganin yashige bandaki sai kawai tajuya takoma kitchen din tadora shayin shima tana Allah Allah ya dahu,cikin zuciyarta kuwa haushi cike fal na hanata baccinta.


Tana gama juyewa ta dora ruwa,ta farke indomie ta tsumbulata cikin ruwan,ta farke maginta ta zazzage mata ta rufe
"Babu wani doya da qwai da zan iya da sassafen nan kamar wata 'yar daudu,yaci indomie kawai,gwara dana hade mata kayan hadin bari naje na kwanta nadan sake matsewa kafin ta dahu,aikin banza,banson tashin safiyar nan" tasake yin tsaki tana ficewa daga dakin.


Gadonta tawuce tafada kai,ta sake jan bargo ta lulluba abinta,batayi minti daya cikakke ba baccin yasake awon gaba da ita.


Daure da towel yashigo dakin yana goge jikinsa,ga mamakinsa saiya sake ganinta kwance tana bacci
"A'ah" ya furta ranshi nadan sosuwa,bubbuga qafafunta yasoma yi
"Rufee,tashi mana ina abincin?" A zabure ta farka tana mutstsika idanu,yasake maimaita mata tambayar
"Au,tana wuta bari nazuba maka"
"Doyar?" Ya fada cikin mamaki,bata amsashi ba tayi gaba da sauri,saidai ina ta makara,sanda taisa kitchen din har mmn ummi da qauri ya isheta tafito tasauke tukunyar,wadda tuni taliyar ciki ta qone qurmus.


Turus tayi tana kallon tukunyar tana kuma kallon mmn ummi da tukunyar taliyar ke gabanta.........👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA DAYA*



*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*


*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_






Idanu suka hada da mmn ummi,sai kawai ta waske tana bata rai ta isa bakin tukunyar tasa hannu tabude murfin,ganin yadda tayi baqiqqirin saita saki tsaki,dai dai sanda bbn amir yashigo kitchen din saboda ya zaqu ya fita,yana neman makara ne
"Ina abincin?" Ya tambaya yana duban rufaida da tukunyar taliyar dake gabanta
Sautin dariyar mmn ummi ya karade kitchen din,wanda hakan yasanyasu dukka suka waiwaya suna dubanta,sai kuma ta gimtse kamar ba itace tayi dariyar ba,ta soma 'yan waqe waqenta tana ciro wasu fulasanta tana sauya musu waje.


Sosai rufaida ta qulu,ta sani sarai da ita take,amma sata a gidan barawo rance ne,kuma duk wanda yaci tuwo da ita miya yasha,ba zata lamunya ba,kuma saita fanshe dariyar data yi mata din
"Ka ganta qonewa tayi wallahi" ta fada cikin salon shagwaba tana wani yarfe hannu,wanda hakan ya qular da mmn ummi wadda kunnuwanta suke kansu
"Qonewa kuma?,garin yaya zaki dora taliyar da bata wuce minti takwas ko goma ta gama dahuwa harta qone?"
"Na dora ne bacci yadan rinjayeni naje na kwanta kanta qarasa".


Dariya mmn ummin tasake kwashewa da ita cikin salon waqa tace
"Kayan kitchen mama tasiya min,abinci dahuwar 'yan gayu,wani kalarma sai an dandana,ayye sama mata,mata" daga haka ta sanya kai tafice abinta tana sheqa dariya.


Sosai rufaida ta qarasa qulewa,a zafafe ta waiwayo tana duban bbn amir
"Kanajin matar nan ko?,nifa take tsokana,wallahi kaja mata kunne niba sa'arta bace,idan ba haka ba nixan dauki mataki a kanta dakaina" nan take yaji ranshi yabaci,ita sam bata abinda zaici da barna da kuma bata mishi lokaci take ba,sam bashi ya dameta ba?,bacin rai ya hanashi magana,sai kawai ya rabeta ya isa gaban gas din.


Qwai uku ya dauka ya fasa ya kada,yana neman frying pan ta qaraso wajen
"Ina maka magana amma kayimin banxa kamar bada kai nake ba?" Ta fada itama ranta yana baci sosai,tana ganin kamar ya wulaqanta ko kuma yana bayan cin fuskan da mmn ummi tayi mata kenan.


Kai ya daga ya dubeta kawai,sau tari a kwanakin nan idan tana wanu abu sai yaga kamar ba rufaidanshi daya sani ba,kamar wata rufaidan ce ta daban,sai yaga kulata ma bata bakine,tunda ita batasan ya kamata ko bai kamata ba.


Har yagama soyawa yajuye yadauka yawuce tana tsaye,shurunsa saiya sake bata mata rai gamida kuma tunzurata qwarai,fuuu tabi bayanshi dakin,ta sameshi zaune harya soma karyawa da ruwan tea din data dafa mishi,da kuma qwan data soya.


Kanshi ta tsaya cikin bacin rai,don tana jin ya kamata tanuna mishi bacin ranta sosai
"Ni zaka wulaqanta jibril a gaban matarka?,ni rufaida ni zaka yiwa haka,na kawo.maka qararta amma kayi kunnen uwar shegu da qorafina,wannan shine kulawa ta musamman da kayi alqawarin bani,shine darajar tawa da kace zaka daukaka fiye data kowacce diya mace?,jibril tunda nashigo gidanka nake ganin abubuwa na cin fuska da wulaqanci,dama haka kake?,ina duka alqawuran daka daukarmin?".


Kai ya tada ya dubeta
" ke bakisan kinyi ba dai dai ba?,bakisan abinda kikayi shi yafi cancanta ki maida hankali akansa ba ba wani shirmen banxa ba?,ga abinda yafi muhimmanci sam ke bashine a gabanki ba,kawai ta abinda aka miki kike na daukar miki fansa?,hakan shine dai dai a wajenki kenan?"ranta yasake baci,wato shi baima ga abinda akayi mata ba kenan,abinda aka mata din shine shirmen banza
"Amma dai aiko yaya kayi magana ko kodan saboda ta rainani,idan yaso mayi solving wannan issue din daga baya" shuru yayi yaba kallonta,wato bata fahimceshi ba kenan har yanzu?,sai kawai yamiqe daga cin abincin yana qoqarin danne bacin ranshi da mamakinsa,yadauki jakarsa da muqullin motarsa ya gewayeta yana fadin
"Saina dawo"
"Jibril" ta kirashi cikin bacin rai daya riqe mata wuya,amma saiya wuce baiko waiwayo ba.


Ganin ya makara da yawa ya sanya bai shiga dakin kowa ba yawuce,yayanke aranshi idan ya isa kasuwa yakira yaji lafiyar kowa,duk da yariga daya ga mmn ummi,mmn amir ce baiji motsinta ba,kuma ya kyautu ya leqata din kafin yafita kodon yanayin da take ciki.


Nan ta zube a kujerar falon nata ranta na mata suya,bata tsammaci zai bari mmn ummin tayi mata haka a gabanshi ba,kuma har tayi magana ya nuna ba wannan ne damuwarshi ba,damuwarshi wato cikinsa kadai?.


Ta jima zaune anan cikin bacin rai,tana saqa yadda zata rama abinda mmn ummin tayi mata,hakan yasanya har rana tasoma dagawa,lokqcin cin abincin yara da matan gidan yayi amma babu amarya babu dalilinta,kitchen wayam ba abinda aka dora,haka tsakar gidansu yana nan tun yadda yake daren jiya,baisamu arxiqin shara ba,wanda aikin amarya ne,kuma bata fito ba bare ta share din.


Dai dai lokacin mmn amir na daki kwance bayan ta idar da sallar walaha,bata wani jin yunwa sosai saboda tunda sassafe data tashi taji tana jin yunwar ta debi cake ta hada shayi mai kauri tasha abinta,tunda cikinta yasoma tsufa cin abincin nata ba wani mai yawa bane,shi yasa wanda tacin bai gama narke mata ba har yanzu.


Qarar wayarta yadauki hankalinta,tamiqa hannunta tadauko tana duba mai kiran,saita saki murmushi,din yanzun haka tunaninsa take taga bai shigo ba kamar yadda yasaba,har kishi yaso taso mata ko rufaida ce ta riqeshi?,sai tayi ta'awizi ta kori shaidan tayi istigfari,ta kuma gargadi kanta kan zato zunubi.


Sallama tasoma yi masa ya amsa mata
"Yanxun nake tunaninka,naji shuru yau babu motsinka nake cewa Allah yasa ya lafiya" ajiyar zuciya yasaki a boye,har kullum naya rasa samun wani abu dazai sanyashi farinciki daga bakin halimatunshi,kome yayi mata,kowanne yanayi suke ciki bata fasa nuna kulawa da damuwa dashi,daya daga cikin abubuwan daya sanya shima ko yaushe yakan qara qaimi wajen ganin yanuna mata kulawa kamar yadda take mishi,koda nashin baikai nata ba
"Nima kina raina,naso leqowa naga ya kika kwana keda baby,to na makara,ayimin afuwa" murmushi takuma saki
"Tunda naji shuru nasan babban lalurane ya tareka,babu komai yau da gobe sai Allah,ina kwana?"
"Lafiya lau,da fatan kin tashi lpy ke da babyn?"
"Lafiyarmu lau alhmdlh"
"To ma sha Allah,su amir basa nan bare na tambayesu,qiri qiri kin koremin yarana" murmushi tasaki kawai,don ita ason ranta ma yaran suyita zamansu a can,koda zasu dawo din gaskiya bata buqatar dawowarsu gida nan kusa,cikin nutsuwa da taushin harshe tace
"Ni na isa na raba yara da gidan mahaifinsu?,kawai dai nafi samun hutu da nutsuwa yadda ya kamata ne abban amir shi yasa,kuma nasan can din babu matsala,koda makaranta aka koma koda qafa suna iya takawa suje,tunda tamafi kusa dasu akan nan din" ajiyar zuciya yasauke
"Aishikenan,tunda anmin qarfa qarfa yana iya" murmushi tasaki mai sauti kadan
"A'ah wallahi,bankai wajen ba"
"Babu komai Allah ya raba lafiya dai"
"Amin ya Allah"
"Shikenan?,saina dawo?"
"To Allah ya tsare,ya bada sa'a,yayi jagora yakuma bada abinda aka fita nema"
"Amin ua hayyu ya qayyumu" ya amsa yana jin dadin addu'ar har cikin zuciyarsa,duk da wannan ba sabon abu bane wajen mmn amir din,abu daya dahar yau mmn ummi takasa koya daga wajenta,abu kadan xai hadasu tana kallo xai fita ma amma ba zata iya bude baki tace masa a dawo lafiya ba,ita a lallai saita nuna masa sai kuma yasan cewa taji haushi,abinda bai taba gani daga wajen mmn amir din ba,kome ya hadasu kome sukayi bata fasa ce masa a dawo lpy,ko Allah ya tsare.


Da wannan tunanin yakashe wayar yakira mmn ummi,ya kira wajen sau uku bata daga ba,tana gani kuma tana sane tayi dagawar saboda abu biyu,na farko tana jin haushi yafita bai leqo ba,gashi tana son amsar wasu kudade data shirya qaryar amsa daga hannunsa,nabiyu kuma batason ya mata magana ko fada kan dariyar data yiwa rufaida dazu,haka yagaji ya haqura da kiran tunda yafita haqqinta.


Har zai aje saiya tuna bai ajewa rufaida kudin cefane ba,amma sanin akwai kudi daya aje dakin yasa ya lalubi lambarta.


Dai dai lokacin tana kwance saman doguwar kujerar falonta,tasha tea da bread cup din yana aje gefenta,tunda yafita ko dakin bata samu ta gyara ba,tana miqe tana latse latsen waya abinta,charting take a grp dinsu wanda yake cike da qawayenta,tana ta basu labarin yanayin rayuwarta a gidanta,da kuma abinda yafaru dazu tsakaninta da bbn amir din,ashariya wasu ke qundumowa suna sake dorata bisa layin matakij da zata dauka,hirar tayi mata dadi,hakan yasanya zuciyarta yadan rage fushin da takeji.


Kiran bbn amir din yashigo,takalli lambar taja tsaki,tayi minimizing kiran takoma kan watsapp dinta harta katse,wani kiran yasake shigowa sannan ta daga,murya a dake tayi masa sallama ya amsa
"Afwa na sha'afa ban aje kudin cefane ba,ki duba qasan kayana akwai kudi ki dauki dubu daya"
"Dubu daya?" Ta fada cikin izgili izgili a muryarta,ya tsammaci jine batayi sosai ba,don haka yasake maimaita mata
"Eh dubu daya" tsaki taja yadda bazaiji ba ta kashe kiran,takoma grp dinsu tana gaya musu nawa ne kudin cefanen nasu,kasancewar kowa yasan yadda take cika baki da kurari kan bbn amir din sai sabuwar hayaniya ta barke,wasu na rainawa wasu suna babu laifi,kowa yashiga bata irin tashi shawarar,saita koma ta kwanta sosai tana sake duba saqonnin a tsanake daha bayan daya.


Dai dai lokacin da mmn amir tasoma jin yunwa,saboda haka ta katse carbin da takeja din ta yunqura tamiqe tafito daga dakin bayan ta aje hijabinta,kamar hadin baki mmn ummi tafito itama dauke da ummin tana magana ciki ciki a hade,da alamu mita take,usman na biye da ita yana kuka kuka
"A'ah,lafiya dan fodiyo?"mmn amir ta fada tana shafa kan usman din,ita kadai ke kiranshi da sunan wani lokaci cikin gidan,saiya maqe kafada cikin kuka sanda mmn ummi ta tura kitchen tashige
"yunwa nakeji"
"Bakaci abinci bane?,gashi har sha daya saura?"
"Inafa zaici abinci?,bayan babu abinda aka girka cikin gidan,zokiga kitchen din qwalam babu komai sai qonanniyar taliya" ta fada cikin daga murya ta yadda tasan rufaidan zataji.


"Toh,garin yaya?" Mmn amir tafada bayan taduba kitchen din ta tabbatar ba'a dafa komai din ba
"Oho,tsabar iskancine da iya shege,da kuma daurin qarqashi data samu wajen mai gidan,nina tabbata da nice yau a gidan na na kade idan na aikata haka,gwara ke da yake anayi dake tunda kin daure masa baya yayi yadda yakeso"
"Dakata,duk wannan bata taso ba,ko wani uzuri ne dai ya hanata fitowa,karki gaggawar hukunci" mmn amir ta dakatar da uta,don batason tasoma sakin zancan nan nata wanda idan kishin ya tsikareta kamar wadda aka dorawa wuta saman ka saita saukeshi
"Koma uban meye bari naje nagani" mmn ummin ta fada tanayin gaba xuwa dakin rufaida,da ido mmn amir tabita kawai tana addu'ar Allah ya kade fitina.


Sai data shige dakin sannan ta maido dubanta kitchen din,gaba daya yakoma wani irin tunda tasaki harkar girkin gidan,kamar yanzu da yake cike da kwanukan girki,saita duqa a hankali tana tattaresu waje daya.


Da qarfi ta bankada labulen dakin tayi tsaye tana duban rufaida wadda ke kwance dafa'an tana faman charting,ganin haske daya dadu a dakin yasanyata daga kai ta kalli bakin qofar,suka hada idanu kowacce ta tsuke fuska
"Ina abincin safiyarmu?" Ta jeho mata tambayar kanta tsaye,wani kallo ta watsa mata sannan tamaida kanta a charting dinta kafin ta bata amsa
"Ban dafa ba,don babu wanda ya ajiyeni"qarasa shigowa dakin mmn ummi tayi,wanda ada batayi niyya ba
"kamar yaya?,me kike nufi?,mu mugama dafawa mu baki kina lafe a daki keda miji kuci sannan yanzu kice mu bazaki dafa ki bamu muda namu yaran ba?", sosai tatashi tazauna tana duban mmn ummin
"Kinga tsaya,karki cikamin kunne da hayaniya,abincine banga damar dafawa ba saboda haka ki samamin salama malama" sosai mmn ummi ta tunzura,ai kuwa cece kuce ya barke tsakaninsu,wanda hakan yaja hankalin mmn amir dake kitchen din
"Ya salam" ta fada tana miqewa daga durquson da tayi,bayanta ya amsa mata,tayi tsai donta huta tanajin kuma yadda harshe ke tashi daga dakin rufaidan.


A daddafe ta qarasa qofar dakin ta daga labulen tashiga
"Haba don Allah,meye haka?,saikace wasu qananun yara?,harshenku yacika gida?wannan aiba mutunci bane wallahi"
"Kinsan me wannan 'yar rainin hankalin tace?" Mmn ummi tafada tana nunata cikin zafi,kafin mmn amir ma ta amsa ta gaya mata duka yadda sukayi,sannan ta dora da cewa
"To wallahi bata isa ba,yadda muka dafa muka bata itama saita dafa ta bamu"dariya rufaida ta sheqe da ita
"xakiga isar tawa kuwa,naga wanda ya isa yakaini kitchen"
"Zaki gamu da wanda kike ganin ya daure miki gindi kuwa" daga haka mmn ummi ta juya fuu tafice daga dakin tafada dakinta tasoma lalubar wayarta,yayin da rufaida tadauki wayarta tawuce bedroom dinta tana ci gaba da zagin mmn ummi gamida lalubar number bbn amir,tana ganin gwara tatareshi da zancan tun kafin yazo a rigata lauya maganar.


A falonta ta cimmata tazauna tanata huci gamida maimaita kiran lambar bbn amir
"Wa kike kira?"mmn amir ta tambayeta sabida sanda tafito ta fuskanci itama rufaidan bbn amir din take kira
"Shi wanda ya daure mata gindin nake nema yakwana da sanin abinda yafaru" kai ta girgiza tana duban mmn ummi,batasan sai yaushe zata soma gane dukkan lamura ba,idan rufaida farin shiga wadda batasan ciwon zamantakewar aure da ciwon jibril din gaba daya da qimarsa ba ita ta aikata,ita mmn ummi da yake uban yaranta kuma wadda tadan dauki wasu shekaru cikin mu'amalar aure,tasan ciwonsa yaci ace tayi?
"Yanzu abinda zaki aikata din kina ganin kinyi dai dai kenan?" Dubanta tayi cikin jin haushi tace
"Kamar ya?"
"Yanzu kinwa uban yaranki adalci kenan?,ya fita neman abinda zaici gaba da tufa miki asiri keda yaranki,amma ki rasa dame zaki saka masa saida kiransa ki daga masa hankali?,ke kina kira ita tana kira?"
"Auto,me kike nufi?,na qyaleta kenan tatakamu tabarmu da yunwa taci karenta babu babbaka?"
"Idan tabarku da yunwa baki da hannun da zaki sarrafa abinda zakici koda dai dai cikinkine?,ki jirayi dawowarsa idan yaso kya kai masa qorafin?"
"Au....to ko bakinku daya?" Da mamaki take duban mmn ummin harta gane hakan saman fuskarta,duk da tadanji nauyin abinda tafada din saboda ita kanta tasan ba hakan bane,amma da yake idanunta a rufe suke saita dora
"Idan ba haka bane toki qyaleni,don wallahi saina gaya masa yasan sa saninsa,ai dama duk qanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa,niba irinki bace dazan zauna inaji ina gani a cuceni na qyale,duk wanda ya cuceni saina qwaci haqqina koda tsiya koda tsiya tsiya ne ehe,tunda ya jajibo wata toya shirya tarbar duk wani qalubale"
"Allah ya bada sa'a" mmn amir din tafada tana miqewa tabar mata dakin.


Kitchen din takoma sharp sharp tayi jallop din taliya da tattasan leda,da yake gwanar girkice tayi dadi qwarai kuwa,ta diba tazubawa usman da ahmad tawuce da saura daki,donko gyaran dataso yiwa kitchen dinma saita fasa,hakaza tsakar gidan,takoma daki abinta ta sakaya qofarta.


Dai dai sanda kowacce cikinsu ta taqarqare tana zabga mishi kira,sam bai sani ba,wayar tana a silent kuma cikin aljihunsa yana fama da custumers,sai daya sallamesu sannan yasamu waje yazauna yaga kiran,hankalinsa yatashi ganin kira wajen sha biyar na rufaida da mmn ummin,saiya rasa ma wazai soma kira,hankalinsa ya tashi yana fatab Allah yasa ba wani mummunan abu bane yasamu iyalin nashi.


Yana cikin wannan taraddadin kiran rufaida yakuma shigowa,babu jinkiri yadaga
"Lafiya meya faru?" Shine abinda yasoma fada
"Mmn ummi tayi kiranka ne?"
"Me yafaru?,naga miscal dinta"
"Yauwa,kome zata gaya maka karka yarda da zancanta,idan kadawo gida zakaji komai" shuru yayi yana nazari,tunaninsa nason hasaso masa abinda ke faruwa,jin yayi shuru ya tabbatar mata bata fada masa komai ba,saboda haka cikin jin dadi tace
"Saika dawo,i lov you" ta katse wayar takoma ta kwanta abinta saman gado tana juyi hadi daci gaba da charting dinta.


Jin maganar da rufaidab ta fada yasashi jan mugun tsaki,ya gama hasashen komai,haushi yacikashi,wanne irin kira ne wannan haka na rashin tunani?,yana shirin maida wayar kiran mmn ummin yashigo itama,saiyaqi dagawa yamaida wayar yaci gaba da sabgoginsa,amma sai hankalinsa yagaza kwanciya,ya fiddo wayar yanemi mmn amir
"Lafiya lau,ba wani abu daya faru,kowa lafiyarsa qalau" tace dashi sanda ya tambayeta,don tunda taga kiran tasan bai rasa

Please Login or Register in order to submit comment