Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci masa rai,ta yaya zaici gaba da zama da auren mace irin rufaida a kanshi,a kwana na hudu ya yanke shawara ya rubuta mata takardar sarki biyu ya ninke,da kansa yaje gidansu yasamu waliyyanta ya danqa musu,kowa yaji mutuwar aurensu amma banda rufaidan da bayan ta amshi takardar takoma daki rawa tashiga yi,kana takira dukkan wanda take tunani zai tayata murna ta gaya mishi,daga qarshe takirayi samarinta da suka mata alqawarin aure ta shaida musu
"Mun zama free yanzu,don haka abinda yarage min idda kawai,iddar ma aina gama yinta tuni,sai kawai kasoma shirya mana yadda aurenmu zai kasance"
"Da wuri haka?,karki damu babe" amsar da kusan suka bata kenan.

Ko kadan mmn amir bataji dadin sakin da jibrin yayiwa rufaida ba,saima tausayin rufaidan daya kamata sanda inna ke basu labarin abinda tazo har gida tayi musu,tasan ba shakka zallar quruciya ke dawainiya da ita,da kuma rashin cikakken hankali,tasan kuma tunda ta aikata haka jibril bai zama da ita,saboda girma da darajar innarsa tana saman komai da yake dashi a duniya,sai tayi addu'a Allah ya zaba musu abinda yafi alkhairi,mmn ummi kuwa cewa tayi
"Wai meye abun damuwa?,abinda ta shuka nefa ta girba,mu taso fiddawa Allah yaduba zukatanmu yaga bamu da haqqinta,ai indai a duniya ba zaka zama mai kwaikwayon aikin alkhairi ba saboda girman kai ko kana ganin kafi kowa to kana tare da wahala dakuma halaka"
"Gaskiyane" cewar inna,a fakaice tadinga yaba musu da qoqarin zama da yaronta da sukeyi duk da yanayin rayuwar da yake ciki hakan baisa sun juya masa baya ba kamar yadda rufaida tayi ba.


******************


*_MAHAƘURCI MAWADACI_*


Cikin taimakon Allah da addu'ar iyaye da kuma dafawa da addu'ar nagartattun mata Allah ya qaddara jirginsu jibril ya bayyana,kuma aka samu dukkan kayansu,harda qarin wasu kudade masu kauri naban haquri daga kamfanin jirgin na akasin da aka samu.


Cikin qanqanin lokaci rayuwarsu ta daidaita harma taso ta zarta na baya,don dama haka hukuncin Allah yake,a duk lokacin daya jarabci bawa yayi haquri da jarrabawar,to wala'alla yayi hakanne donya daukaka darajarsa yakuma maida masa mafiyin abinda ya amsa daga wajensa cikin kyautayi da karamcinsa,bai manta alkhairinsu ba,ya dunqule kudi da kansa ya baiwa kowa ta qara fadada sana'a da jarinta,don yaga amfanin sakarwa mace tayi sana'a qwarai da gaske.


Tare suka zauna suka tattauna abinda zasuyi dinga yi,inda daga qarshe suka yanke su dinga saida atamfofi da laces pieces masu kyau,sai takalma masu sauqin kudi daga 2k zuwa qasa,wanda yayan mmn amir da yake zuwa lagos suka tattara kudin suka baiwa,yasoma saro musu masu kyau da sauqin kudi.


Allah kuwa ya dafa musu,yasanyawa kasuwar tasu albarka,nan da nan sai gashi sun soma ganin sauyi,duk da haka mmn amir bata saki sana'ar saida ruwa da lemo ba,saita barwa yaranta mata suke hada lemon su gyara firjin su jera su kuma saida su adana kudin,aware riba su saka a asusu nasu ne,uwar kudin kuma a sake siyan kayan hadi,tayi hakanne don suma ta horesu da sana'a da neman na kansu,kuma alhmdlh tana ganin alfanun haka.


Zuwa wani lokaci bbn amir ya rushe fiye da rabin gidan yamasa gyara na musamman aka maida musu ginin xamani,rayuwarsu taci gaba da juya musu cikin farinciki saboda kowanne ya fidda hassada qyashi da mugun kishi daga ranshi,kowa yana kiyaye abinda dan uwansa bayaso,sannan duk abinda yasan zai cutar dashi a karan kanshi bai yarda yayiwa abokin zamansa.


*************

Mmn amirce tayi sallama a falon mmn ummi,mmn ummi dake kwance tamiqe tana amsawa tana yamutsa fuska da alamu bata da lafiya ne,sai da mmn amir ta aje kwanon gabanta sannan ta tsaya tana dubanta
"Dole kici wani abufa,ga alalan nan dan kadan nayi miki ma yadda zaifi dadi,amma karki soma cemin yafita daga kanki irin na dazu,in kuwa baki cinye ba agabansu mubarak xamusa bbn amir yamiki dura,yadda kike musu fadan basuci abinci idan basu da lpy kema suga haka kike,kinga bakya qara ba ko?".
"Mmn yara,wallahi ji nake kamar yanzu na fara haihuwa,wannan cikin walahar dani kawai yake,haryau na kasa naji dadin jikina?"
"To ai dama kowanne da irin yanayinsa,aikin lada mukeyi,fatanmu Allah yabamu da sauqi yasa mu gama lafiya" tafada tana cire mata murfin kwanon,sosai alalan yayi mata don haka tasoma ci,ganin hakan yasa mmn amir tace bari taje ta qarasa girkin rana na yara suna gab da dawowa daga makaranta
"Mmn yara" mmn ummi takirata,saita amsa tana juyowa,cikin sanyin jiki da murya tace
"Don Allah ina neman afuwarki ki yafemin duk abinda na taba yi miki tun daga shigowata gidan nan zuwa yanzu,idan nazauna nayi bitar halayenki da zamanmu na yanzu duk sai naji kunya ta kamani da dana sani,ki yafemin don Allah don nasan na cutar dake a baya koda baki fada ba,nayiwa kalmar kishiya mummunan zato,na zaci saikin shigo da wuta da bala'i dakuma tsiwa sannan kike samun duk abinda kikeso,ki yafemin" murmushi tayi kana tadawo hannun kujera tazauna
"Ni a wajena tuntuni wannan yariga daya wuce mmn ummi,nasan cewa sharrin zuciyane dakuma rashin sanin dawar garin,dukkaninmu kuna kuskure daga amare har uwayen gida,yawanci ku amare kukan daukarma kanku wani abune,duk da cewa wata takan fara samun dama ne tun daga waje daga wajen wanda zata aura din,wala'alla shiya soma nuna mata matarsa ba wata abace bace,matarsa ta gaza dashi kodai wani abu makamancin hakan,wata kuma duka babu daya,abu daya take da tunani shine wannan mijin,burinta kawai ya watsar da matarsa da yaransa ya rungumeta,ta manta cewa itamafa wannan matar tasa macace kamar yadda take mace,itama tana da buri a zuciyarta,uwace tana da yaran da bazataso wani abu ya rabesu ba koya rabeta,tanason mijinta wala'alla fiye dake,saboda bakisan iya abinda ta hadiye tsahon xamansu ba,bakisan wacce wahala sukaci tare ba kafin sukai wannan matakin da kikazo kika samesu akai ba,kin manta cewa ya sameta ne kafin ke,ya sameta a sanda take zabi guda daya cikin rayuwarsa,tazauna dashi ta raineshi a duniyar rayuwar aure,tunda a sannan shidin cikin rayuwar auratayya tamkar jaririne sabon haihuwa cikin duniya,tafiki saninshi ciki dabai,maimakon kishigo da kyakkyawar niyya,saikiga Allah ya taimakeki ya miki maganinta koda tana da wani mummunan nufi a kank,amaimakon ta kwantar dakai tasan waye mijin ta hanyar kishiyar,tanutsu ta gane yaya gidan yake?,wacce rayuwa sukeyi,a'ah,duka saiki bata rawarki da tsalle,kice ke kin shigo da iyawarki ne,ki dauki labaran da wasu ke baki karance karance da kallace kallace kice dasu zaki hada kizauna da mijinki,bayan duka rayuwar wannan ta zahiri ce,tasha banban da duk yadda zaki hasaso koki tsarawa kanki,ki dinga takaici idan mijinki yana girmama uwargidansa,maimakon hakan yazame miki abun alfahari saboda kinsan cewa yacika nagartacce,kema aduk yayin da kika samu kanki a muhallinta zai mutuntaki ya darajtaki,sannan zaman lafiyarku cikin gidanku yafi komai kwanciyar hankali da riba a gareku gaba daya"


"Mu kuma iyayen gida namu kuskuren muma daban,kamar yadda kika dinga tafka kuskure alokacin kika baiwa rufaida dama ta rainaki tun bata shigo ba,sa'annan kika dinga qoqarin lallai saikin tilasta mijinki yafasa aure,bayan kin manta bayanke yana da damar sake qara wasu biyun ras,kina yunqurin ki haramta halas,ki soke fadin Allah,kiyi fito nafito da ayarsa,hasashenki na gaba kuma ki cutar da amaryar idan tashigo,kiyi amfani da jimawarki cikin rayuwar aure da rayuwar gidanki ki xalunceta,kisa miji ya qasqantata,ki dora mata dukkan laifi,ki hanata sakat,wasu daga cikinmu su bibiyi malamai su raba auren kamar yadda ake samun wasu amaren dake bibiyar malaman suma su raba uwargidan da mijinta da yaranta dakuma gidanta ma baki daya,gaba daya mata mun zama maqiyan junanmu,muke yaqar junanmu da haifarwa junanmu matsala,kullum damuwar itace,kishiya ta hanani zaman lafiya,uwar miji ta hanani xaman lafiya,qannen miji sun hanani zaman lafiya,faccala tasani a gaba,matan waje yake nema dukka dai matsalar MATA ne matsalar yan uwansu mata,mafitar daya ce,kowa ya tsarkake niyyarsa,kowa yadora rayuwarsa bisa mizanin abinda Allah yace yakuma umarcemu,karka cuci wani kamar yadda bakason a cuceka,sai kowa yazauna lafiya,mu fita daga matsala,kakata ta taba bani labari,a baya idan aka qara miki kishiya kunyarki takeji,kunyar hada idanu take dake,saboda tana ganin ta aure miki miji,yayin da ke kuma a naki fannin uwargida kike riqeta hannu bibbiyu,kikemata kallon qanwarki,yadda zaki mu'amalanci qanwarki bazakiso ta cutu ba haka kike mata itama,to ayanzunfa?,haka muke?auren mai mata ba matsala ko kuma laifi bane,amma dole kisan cewa zaki ga banbance banbance,wataqila ma ki hadu da wasu 'yan qalubale,hakanan dare daya bazaiyiwu kice zaki zama ita ba,kamar yadda itama ba zata taba komawa ke ba,kamar dan makaranta ne,a ranar daka shiga bazai taba yiwuwa kace so kake ka kamo dan aji shida kana aji daya ba,ko so kake kayi suna farinjini irin na dan aji shidan nan ba,komai na rayuwa mataki mataki ne,haquri kuma shine matakin dukkan nasara"cikin gamsuwa mmn ummi take kada kai
"Ba shakka muna kuskure kam,ko yaushe mune matsalar junanmu" mmn amir ta gyada kai
"Qwarai kuwa,duk da suma mazan suna da tasu mihimmiyar rawar da suke takawa,saidai mu namu mijin alhmdlh,yana bakin qoqarinsa tunda can bare a yanzu" hararar wasa mmn ummi ta jefa mata
"Eh mana,kyace haka mana,kullum dama ai bai laifi a wajenki" dariya tasanya tana miqewa
"To dama ta yaya,kema bai laifin ai wajenki" suna dariya dukka mmn amir tafice,mmn ummi tasaki ajiyar zuciya,tana godewa Allah daya ganar da ita da gaggawa,da ayanzun yadda mmn amir ke hidima da ita da taji kunya.


*_RUFAIDA FA?_*


Tun daga lokacin data amsa takardarta sai tayi tsammanin zata sake bude sabon babin rayuwa ne,tayi aure da mutumin da bazai daina nuna mata qauna da tattali ba kwatankwacin yadda take samu a yanzu ba.


Saidai kuma abu na farko daya soma bata mamaki shine yadda suke mata kauce kauce a duk sanda tayi maganar aure,kowanne saiya soma yi mata yawo da hankali,daga qarshe ma manufofinsu suka fito,kowanne so yake kawai suyi rayuwa a waje,data nuna qin amincewarta basu takura mata ba,saidai sun soma janye duk wani kudi da suke kashe mata da tallafi da suke bata,sa'annan sukaci gaba dayi mata goce goce kan turowarsu gidansu ayi maganar aure,sannu sannu sai suka soma guduwa daya bayan daya,da taga haka itama saita watsar dasu ta kama wasu,su dinma duk kanwar jace,abinda yakawo wadancan shiya kawosu,hakanan abinda yakori wadancan shi yakoresu suma,tun abun baya damunta harya soma damunta,tafi tafi sai maneman suka fara ja baya,saitayi kwana da kwanaki bataga walqin kowa ba,hakanan ba'a nemeta ba.


Jikinta yafara sanyi sanda tasoma shiga zawarci dan gaske,don kowa ya zuba mata idanune,hatta da kakarta wannan karon tayi watsin tsiya da lamuranta,mmnta ma da take dan samun goyon baya daga wajenta yau dadine gobe akasinsa,don babu dana ta tambaya koda klien na wanki bare kudin kashewa zata hau fadan tagaji da hidima da ita,ta fidda miji tayi aure,to ina taga mijin ma bare ta tsaidashi?.


Jikinta bai sake sanyi qalau ba sai ranar da taje asibiti batajin dadi zataga likita,mata babu wahalar sabo a tsakaninsu,kafin zuwan likita wajen zaman jira hira ta barke,ashe matan aurene da zawarawa,sai taji rabin hirar kamar da ita akeyi,maganar wata mata ta qarshe ita taja hankalinta
"Shi zaluncin aure tun a duniya Allah yake sakayyarsa,duk wanda ya cuci wani walau mata ko miji,indai kikace bazaki haquri ba auren zamani saidai kiyita fita ana irga miki aure,kowa haquri yakeyi,indai an sauke miki haqqoqin da duk Allah ya shardanta musu to duk abinda zai biyo baya mai sauqi ne,saidai idan an take dokar Allah ne ko akwai cutarwa mabayyaniya".


Duniyar tunani tafada maizurfi,tana nazarin iya zamansu da jibril,basu taba kwana sun tashi babu abinda zasuci ba,bai taba hanasu sutura sanyawa ba,hatta da ruwansha basu shan na fanfo saidai idan yaqare ne kafin yadawo daga kasuwa,ba zaki tambayeshi abu yana dashi ya hanaki ba,ta lissafa abubuwa da dama game da jibril din ita daya tana zaune.


A hankali sai hankalinta yakoma gareshi,saidai duk wata hanya da zatabi don samun damar kowa gareshi lokaci yariga daya qure mata,ashe dama sau daya take zuwarwa mutum a rayuwa?,saimai matuqar sa'a ne yake samun dama ta biyu,koda ta fuskanci 'yan gidansu da zancan babu wanda ya tsaya ya kulata,yayanta nema yace da ita
"Ban sake yarda baki da kunya ba sai yau rufaida,to bari kiji na gaya miki,kaf cikinmu mu muna da kunyar da bazamu iya tunkarar jibril ba,keda baki da ita to bismillah" kakarta kuwa duka takai mata,abun duka saiya taru yayi mata yawa.


Tabbacin data samu cewa jibril yayi mata fintikau kuma ta rashi yasa tasoma koyawa kanta yadda zata fuskanci rayuwa,tasan cewa tagane kurenta a qurarren lokaci,don haka tasoma qoqarin gyara dukkan wani kuskure nata.


*_GASKIYA ƊAYA CE_*


Hakanan tasamu kanta da shiryawa zuwa gidan zahra qawarta.


Hannu bibbiyu ta amsheta amma tana mamakin ganin rufaidan a gidanta,saboda sam bata zuwa tunda ta fuskanci zahran na gaya mata gaskiya.


Da kallo takebin zahran ganin yadda tayi qalau da ita,ko bata fada ba kasan bata nemi komai ta rasa ba,ta saka shuru sai data tanka
"Qiba kike kawai abunki zahra,kamar ba wadda ke gidan kishiya ba" murmushi tayi sanda take zuba mata lemo
"Ni ai ba kishiya gareni ba,abokiyar zama ce dani,kuma don kana da abokiyar zama saika dinga ramewa kaqi kumari?" Kaita juya tana murmushi itama
"Har yaudai kina nan da aqidarkin nan akan kishiya rufaida" tafada tana dan dariya
"Mun rabu da jibril fa watanni kusa tara" da mamaki take duban rufaidan,bata boyewa zahran komai ba ta gaya mata,dakuma wanda yanzun yafito yake neman aurenta wanda shi dayane yake da niyyar aure cikin manemanta,ajiyar zuciya mai nauyi zahra tasaki kana tace
"Tun farko ne rufaida tunaninki ya gurbace,kinsan ta ina?" Saita girgiza kai
"Da farko yadda kika tashi cikin unguwa wata ta musamman yasa kika dorawa kanki abubuwa da yawa,kika zauna kika tsarawa kanki yadda kikeso rayuwarki ta kasance,kina jin kamar dole hakan zata kasance miki,manemanki suna miki hidima sosai saboda kowa so yake ya kaiki gidansa,hali koda ba nashi bane ya ara ya yafa ma kansa duk don ya burgeki yaja ra'ayinki zuwa ga amincewarki,duka saikika dauka a haka,kikayi amannar cewa hakanne,baki taba sakawa ranki cewa wataqila ba haka yake ba,wataqila ya arane ya yafa don yasamu soyayyata,bari na sanyawa raina bayan munyi aure zan iya ganin canji iri daban daban,zan iya haduwa da qalubale,bari na cire tunanin zamu dore da mu'amalarmu ta waje,bari na sanyawa raina ibada zanje,bari na saka tunanin cewa zan iya haduwa da qalubale nau'i daban daban,soyayyar kadance,haqurin juriya da kawaici yafi yawa,qauna da tausayi shine zaici gaba da riqemu,saikika sawa ranki wannan halayya da dabi'a ta waje ita zata dore,dukkan abinda kika samu a waje a ciki ninkinsa zaki samu,baki taba tunaninma zaki samu dai dai da haka ko qasa da haka ba,daga sanda kika shiga kikaha komai ya canza sai a soma samun matsala,don baki tunanin faruwar hakan ba bare kiyi shirin tarbarsa,sai a soma samun sabani,saboda an lallabaki an kuma daukoki kamar sarauniya,kinyi tashe a media unguwa da makaranta,kina ganin kinfi qarfin daukan wulaqanci ko rashin kyautatawar namiji,saikiga kanku daya bai isa ba bazai kuma taba isa ba"


"Ta fannin matansa na gida da yawanmu sanda mai.mace yazo aurenmu,abu nafarko da mukesoma darsawa ranmu wanda shike kashemu shine,ta gaza ne,jaka ce,babu abinda ta iya,ta gaza hanashi kallon kowacce mace bare ya nemi qarota,mun manta cewa zukatan maza Allah ya haliccesu ne da qarfin ikon daukar soyayyar mace hudu,wai wasu suka ce,halin maza 'yan china suka kalla sukayi waya mai sim hudu" sai suka danyi dariya gaba daya sannan zahran tadora
"sannan an qawata zuciyoyinsu da son mata,duk yadda kikagai ga qwarewa da iya komai na fannin rayuwa da zamantakewa baki isa ki hana zuciyarsa so ko kallon wata ba,jarrabawarmu kenan,yayin da kike yunqurin shiga burinki waccar ta tozarta ta wulaqanta,kin mata adalci kenan?idan qanwarki ce yayarki ko qanwar mahaifiyarki zakiso ta tozarta haka?" Kai rufaida ta girgiza cikin sanyin jiki
"To koda yaushe tunaninmu kenan,bama tuna cewa idan mune bazamuso haka ba,son kawunanmu ya mana yawa,munyi watsi da maganar ma'aiki faufau ta fannin kishi da yake cewa muso junanmu,musulmi dan uwan musulmi ne,kada ya cuceshi kada ya xalunceshi duka muna manta tarin hadisai da ayoyin muna gaban kanmu,shi yasa muketa wahala muna fagamniya a duhu,inda zamu koma bisa tsari da turbar koyarwar addini qafa da qafa da ayau munyi dariya munyi shewa kuma kowa ya rabu da matsalarsa,muna jahiltar rayuwar aure mazanmu da matanmu,muna kuma kaucewa turba"

"Kibar hangen gidan wata,duk matar da kika gani cikin gidanta tadauki wasu shekaru haqurine yakaita ga wannan bigiren,kyanki ko matsayinki ko nasabarki yabar rudarki ki dinga ganin cewa idan kika fita tarin maza suna jiranki ko suna sonki,a'ah sam,wadan nan din dakike gani duka na bogine,wallahi wallahi kika bari son zuciya yakaiki ga kashe aurenki kika zalinci mijinki ki guji ranar da Allah zai hukuntaki,ki godewa Allah dayasa kika samu daya ma daya zauna,abunda zaki dora shine istigfari kada Allah ya jarrabeki a sabon gidan aurenki sanadin kuskurenki na baya,ki rabu da dukka qawar da bazata baki shawara bisa turbar musulinci ba".


Sosai jikin rufaida ya ida mutuwa,takuma gano kurakurai masu tarin yawa data tafka cikin rayuwarta,kusan dukkan abinda zahra tafada hakane,koda can abinda ya rage kusanci da shaquwarsu da zahra fadan gaskiya irin na zahran,ita kuma a sannan duniya tana mata guda akai.


Gidan zahran tawuni sai yamma sannan takoma gida,tana sake jaddawa kanta zata gyara dukkan wani kuskure nata don tayi kyakkyawan qarshe takuma rabauta kamae yadda sauran mata suke rabauta.


_ƘARSHE!_


_MARUBUCI a kullum tamkar kyandir ne da yake qona kanshi donya haskaka al'umma,a duk sanda marubuci yadauki alqalaminsa burinsa shine yayi rubutun da xai zama darasi ga al'umma,yasoma labarinsa yakuma kammalashi shida kansa,labarin yafi cizon marubuci fiye dakai dake bibiyar labarin,domin yakanji wani nauyi mai girma a tsakiyar kansa har sai sanda ya kammala rubutun yazama cikakken littafi_


_kyakkawar kalma sadaka ce,annabi S A W yace duk wanda bai godewa mutane to baya godewa mahaliccinsa_

_masulmin da yafi falala shine wanda musulmai suka kubuta daga cutarwar hannayensa da kuma harshensa(aikinsa da maganarsa)_

_mu'amalarka itake nuna waye kai?,daga wanne gida kafito?,wanne nau'in tarbiyya kasamu?,harshe yanzu zai daukaka darajarka yakuma sauke darajarka cikin qanqanin lokaci ya qasaqantaka,mu kula da harsunanmu_

_ka guji zalunci,saboda shidin duhune a ranar qiyama_

_littafin HANGEN DALA banyishi don cin mutuncin wani bangare ba,nayi ne don wayar dakai da samun daidaito da fahimta a garemu gaba daya_

_ina roqon Allah ya karba,yakuma datar damu_🙏🏽🙏🏽🙏🏽


_mu hadu a zafafa biyar da zasu fara zuwan muku a jibi in sha Allahu,litattafan namu sune kamar haka_


_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_
Hafsat rano

_SUKAR BAYA_
BILLYN ABDUL

_KIBIYAR AJALI_
MISS XOXO

_MIN ƘALB_
MAMUHGHEE

_SIRAƊIN RAYUWATA_
HUGUMA

_GUDA BIYAR DIN RANKATAKAF ZAKI SAMESU AKAN_

5=700
4=500
3=450
2=400
1=300


*Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki*👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

_saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)_👇👇

 0903 234 5899

*IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU*👇👇


09033181070

*SABUWAR SHEKARA*
*SABON SALO*👌🏽👌🏽

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment