Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka daya daga cikinsu taja tsaki tana cewa
"Muyi abinda ya kawomu,don da alama dakunan a bude suke" sanda suka juya zasu shige din mmn amir tafito.


A mutunce suka gaisa,wanda mmn ummi taji kamar ta shaqota,suna gama gaisawa takoma daki abinta,samira ta gabatar musu da abinci da ruwa takoma daki sukaci gaba da sabgarsu ba tare dako sun kao hankalinsu ko sun damu da abinda ke gudana a tsakar gidan ba.


A hankali xaman qaryar datayi a tsakar gidan yasoma gundurarta,duk wani abu da aka shigo dashi idanunta akai yake,a zahirin gaskiya rufaidan ta fita yawan kaya nesa ba kusa ba ko sanda akayi nata auren bare yanzu da yara suka lalata wani itama ta lalata wani,sai taji hankalinta yayi mugun tashi,lallai dole tasan abunyi,dole ta sabunta komai nata,dole ta tattara takoma daki har zuwa sanda yaran suka dawo daga makaranta.


Yadda suka wuni jere haka tawuni yawo tsakanin dakinta da tsakar gida zuwa bandaki,ranar kuwa yaran sunsha duka sosai,gashi dama babu islamiyya bare su tsira,abu kadan yaro zai mata ta kamashi ta kila ta kila,kusan a kansu ranar ta huce,saida suka guji suka gudo dakin mmn amir,wadda tunda tasaki labulenta suna ciki ita da samira bata sake ma fitowa ba bare tasan wainar da ake tonawa,ko abune take da buqatarsa a tsakar gidan takan aika samira ko amir yadauko mata.


********* ****** *********


"Yauwa nawa ne kudin lallen namu nida amaryar?" Zahra'u dake tsaye wadda tacire nata lallen ta fada
"Ku bada dubu da dari biyar harda baqin"
"Baji wannan amaryar ta musamman ce,ko nawa kikace a baki bayarwa za'ayi,angon ya tsaya mata,uwa uba gidan mutum biyu zata shiga itace ta uku,koba haka ba jama'a?" ta qarasa maganar dai dai sanda ta zaro kudin ta miqawa mai qunshi,kusan fiye da rabin dakin 'yammata ne,amare da qawayen amaren,maganar zahra'un ta ruda dakin kowa da abinda yake fada,wata daga cikinsu dake zaune daga can gefe an gama sanya mata lallen ta tabe baki
"Mata biyu?,tabdi,wallahi saita tashi tsaye tayi da gaske,itakuwa meya kaita?,aini wallahi ban auren mai mata ma sam" wadda ke fuskantarta itama tata qafar da qunshin tace
"Hhhhh,lallai hajiyata baki hadu ba,ni nan da kike ganina wallahi idan bame mace bama bazan auri saurayi ba,kuma yanzu haka burin nawa zan aura,ai bari kiji na gaya miki....." Ta miqe ta zauna sosai sabanin dazu da take kashingide
"Indai kin hadu kin cika mace,inda zaki nunawa duniya kedin kat ce,kiyi soyayya dame mata,ki guma mata baqinciki,tanaji tana gani halayen mijinta yasauya,ki karbeshi daga hannunta,ki morewa soyayya ya zama naki ke kadai,daga qarshe ki aureshi ki shiga gidan ki kafa sarautarki,ki watso taciki waje,idan kikaga wasa wasa ma ki hadota da yaranta"
"Shine magana!...." Rufaida ta fada cikin wani jin ixxa isa da ganin cewa tashiga layin wadanda suka cika mata
"Wannan dagani tafiyarmu zatayi kyau,badon lallene a hannuna ba damun tafa dake wallahi,amma bari nacire lallen ki sakamin number dinki,yaushe ne naki bikin"
"Cikin satin nan ne"
"Kash,naso ace akwai tazara daya yajewa dayanmu,amma duk da haka bata baci ba,kafin mu gama yaga amarcinmu zamu jone,zaki zomin koni naxo miki" dora bayani tayi
"Ke nifa tun kafin na shiga wallahi ta gama sanin matsayina a wajensa,ita kanta ta gama sallamawa,donko kishi dani bata isa ta nuna masa tanayi ba,ina kiransa duk sanda naga dama,wani lokaci ma ita zata daga,ta gaidani in amsa sama sama inashan qamshi,idan nasoma na datseta ince ta baiwa mamallakin wayar,ke wallahi saboda tasamu fada da soyayya a wajensa,data fuskanci saita kama qafa dani har kirana take tana gaidani,ta kuma bawa yaranta su gaidani,bari na taqaice miki zancan,ba yaranta ba har ita anty sama anty qasa take kirana dashi" dariya rufaida ta kwashe dashi,labarin ya mata dadi,har taji kamar dramer dinma tafi tata
"Dole muje dake wallahi,amma wannan matar tasa anyi jahila" dariya itama matashiyar me suna jamila tayi
"Kamar kuwa kin sani,daga primary aka liqa masa ita daga can qauyensu,tun bashi da komai har yayi arziqi,kinga kuwa yanzu dole yanemo ta gaban jirgi,kada babban abu ya tashi ta kwafsa masa" suka sheqe da dariya suda sauran wadanda kejin dadin hirar a dakin.


"Allah ya rufa asiri,amma dai kubi a hankali,bigiren da uwargida tahau wataran shi zaki hau kema,wala'alla tasu ma tafi taku kyau" wata mata dake tsaye tana zarowa me qunshi kudinta bayan ta cire nata ta fada,duk sai idanunsu suka koma kanta,
"Malama waya saka dake,nifa dama tunda na fuskanci kedin uwar gida ce ko zama kusa dake naqi,saboda haka ba ruwanki da sabgarmu,jeki ji da damuwarki"
"Sannu sannu dai bata hana zuwa,kuma *HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BANE* daga haka ko waiwayowa ta dubesu batayi ba ta dauki diyarta dake bacci tafice,nan suka dasa yi da ita,wanda daga bisani suka watsar kuma sukaci gaba da sauraren labarin da jamila take basu,wanda baqaramin dadi yakewa rufaida ba da sauran masu ra'ayi irin nata.

_muje zuwa masu karatu_. 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_



Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*


*BABI NA BIYAR*



Aqalla ya kusa minti ashirin tsaye gaban mudubin yana dudduba kanshi yaga inda baiyi ba a jikinsa,shaddace 'yar ubansu ya saka sky blue,ba abinda take sai sheqi da walqiya,hakan hular kansa itama babu abinda take sai daukar ido,komai na jikinsa daya sanya mai tsadane,kasancewar jin kansa da yake yaudin rana ce ta musamman,kuma yanason ya fitar da rufaida kunya ita da qawayenta ranar dinner din kamar yadda tace.


Wayarsa dake gefe ce tadauki burari,da hanxari ya dauka yaduba,rufaidan ce cikin hanzari ya daga ya kara a kunnensa,yayin da fuskarsa ta yalwata ta kuma wadatu da fara'a kamar wanda aka yiwa albishir an 'yantashi daga wuta
"Dear...inata jira fa"
"Karki damu baby ina kan hanya,ganinan zuwa karki fushi don Allah,yanzu ba lokacin fushinki bane kinsan ya...." Maganarshi ta maqale sanda yaga shigowar mmn amir dakin.


Kanta tadauke kamar bataji abinda yake fada ba din na,shi yasa sam bataso ma shigowa dakin ba a irin wannan lokacin donta kaucewa ganinsa da kuma kaucewa ganin abinda zai motsa mata kishinta,saidai ba yadda zatayi Allah ya qaddara saitaji din.


Hakanan ya diririce,yar kunya ta saukar masa,saiya hau kame kame
"A'ah,mmn amir ba zaku bane?" Murmushin qarfin hali tasaki tana zama gefan sabon gadonshi sakamakon nauyin da takeji cikinta yayi,wanda ta tabbatar an sauya gadonne saboda amarya,saidai bata taba nuna masa ta gane hakan na,mmn ummi ce tayi qaura da kwana a dakin,tace dacan bai sauya saboda su ba saidon wata,to tabar kwanan dakin,tanajinsu amma bata saka musu baki ba
"A wannan yanayin da nake ciki hutu nafi buqata aiko?" Ta fada don ta baiwa kanta kariya,don tanajin koda ace lafiya lau take bataga abinda zaya kaita wajen bikin ba,kai yashiga kadawa
"Hakane kam,haka ne,Allah ya raba lpy"
"Amin,dama hajiyace tace kafin ka fita ka bada sauran kudin cefanen abincin wuni,saboda ba lallai ka kwana gida gobe ba ko saboda baqi,da sassafe kuma za'a je 'yan kaba a siyo kayan miyan"
"Toh...ba damuwa" ya saka hannunshi cikin aljihu ya fito da sabbabin kudi wanda ya tanada saboda liqi wa amaryarsa ya irgo ya bata,hannu biyu tasa ta amsa kana tamiqe ranta na mata suya,zuciyarta na zafi amma tana qoqarin ganin ta danneta ta hana mata tasiri,a hankali ta juya tafice,saiya bita da kallo kunya da tausayinta na ratsashi.


Dakin mmn ummi tawuce donkai mata kudin saboda ita hajiyar tace ta baiwa saboda ranar tafado ranar girkinta.


Zaune ta can uwar dakanta,saman gefan gado tama fuskantar mudubi,saman gadon baje yake da kaya kala kala,daga na kwalliya zuwa na sakawa,da alama ta bajesu ne tana zaben wadanda zata sanya ne,ta kuma gama zaba din,don lace ne ta wareshi gefe hadi da mayafin da takalmi masu tsini,awarwaraye xuwa sarqa da dan kunne.


Cikin mamaki mmn amir ya qarasa shiga dakin gamida sallama idanunta a kanta,daga kai tayi daga shafa jambakin da take tana amsa mata sallamar sannan ta sake maida kanta,ta mudubin mmn amir take kallonta,tasha makeup sosai wanda tajima rabonta dataga tayi kwalliya irin haka
"Da alama fita zakiyi ko?" Mmn amir ta tambayeta cikin shakku,da mamaki ta waiwayo tana dubanta
"Ya kike tambayata kamar bakisan meke faruwa ba,wai tsayama,ba zakije bane banga alamun kin shirya ba?" Kai mmn amir ta girgiza cike da mamaki,saboda abinda yafarun kafin yau bata tsammaci mmn ummi xatace zataje partyn ba.


Rufaida ce ta rarrabawa qawayenta number wayar mmn ummin suke kiranta suna zaginta tun randa sukayi hatsaniya da rufaidan ta wayar bbn amir din,a rana sai a kirata sama dasau talatin,data gane sune tayita mita har kunnen bbn amir din,toya danyiwa rufaidan magana,tace yace tana bata haquri,a hado da katin dinner guda biyu tace abasu tana gayyatarsu ai duka mijinsu ne.


Sam hakan baiwa mmn amir ba a nata tsarin,amma ga mamakinta saitaga mmn ummin yanzun na shirin zuwa
"Yanzu keda gaske kike zuwan xaki?" Sake waiwayowa tayi ta dubeta
"Qwarai kuwa,aiso nake naje naga shegiya da qawayenta,kuma na tabbatar zuwana zai quntata musu,ya hana bbn amir rawar gaban hantsi,sai naga tunqwal uwar daka"
"Kiga tunqwal uwar daka ko ko gano abinda zai tashi hankalinki ya hanaki barci?" Mmn amir ta fada cikin ranta,don tasan wanda yayi nisa bayajin kira,koda ta gaya mata baji zatayi ba,saboda haka ta aje ajiyar zuciya tana miqa mata kudin hannunta
"Allah ya kyauta,gashi inji hajiya tace zata kiraki" kudin ta harara kafin daga bisani ta amsa
"Nifa ku daina sakani cikin wannan sabgar taku,wadan nan sabbin kudinma da alama amaryar xai baiwa ya tsakuro a ciki ko?"
"Bansani ba wallahi,saidai idan kun hadu ki tambayeshi" baki ta tabewa mmn amir din sannan tace
"Yanzu ba zakije din ba?"
"Saikun dawo Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya,amma ki dauki ummi kawai basai kinje da yaran ba bare su bata miki kwalliya"
"Kin kawo shawara kuwa" ta fada har cikin zuciyarta,ita kuwa mmn amir tayi hakanne saboda kada aje a tafka wani abun kunyar gaban yaran,batason duk wani abu da zai sakawa yaran negative tunani kan iyayensu ya dinga giftawa ta idanuwansu.


A tsakar gida akayi clashing da bbn amir da mmn ummi,sai aka hau kallon kallo,kowa da abinda yake saqawa a ranshi,ran mmn ummi fal kishi take dubanshi,ko ran aurenta gani take baiyi kwalliya irin haka ba,yayin da gabanshi ya fadi,yayi tsammanin ba zataje na kamar yadda mmn amir tace,yanzu ya zaiyi kenan?,ga rufaida nacan tana jiranshi,duk saiya daburce,duka basirarsa tadauke
"Na shirya" ta fada tana tsareshi da idanu
"Toh....toh,ina zuwa" ya fada yana juyawa da sassarfa yafita daga gidan.


Daya daga cikin abokansa yakira ya gaya mishi abinda ke faruwa
"Kaga kasan ya za'ayi?,bari nazo na tuqaku,idan yaso sai aje a dauko rufaidan ka zauna dasu duka a baya nina kaiku wajen" dan jim yayi saboda yana tunanin yadda zata kaya,yasan yadda rufaida taci burin lokacin nan
"Yanzu hakan xa'ayi?"
"Kana da wata mafiyar ne bayan wannan?,idan akace za'akai wata sannan axo a dauki wata za'a bata lokacine kawai"
"Shikenan,sai kazo"



Cikin minti ashirin murtala abokinsa ya iso ya daukesu a motar,suka zarce gidan kwalliya inda tacan za'a dauki rufaidan.


Yana zaune a cikin motar yakirata yace gashinan ya iso ta shaida masa gata nan fitowa,a sannan anata kiciniyar rufe mata zip din gown dinta,saita aika qawarta ta sanya mata jakarta da kayan data cire cikin motar kafin tafito.



Da sauri xahra ta dawo
"Ke rufaida?,garin yaya,naga kamar bashi daya bane,shida wata mata ne harda yarinya a hannunta"
"Mata kuma?,yarinyar hannun tata macace?"
"Eh ba zata wuce shekara biyu ba" wani mugun ashar rufaidan ta lailayo ta maka
"Amma bansan matar nan jaka bace sai yau,zuwa zatayi wajen kenan?,lallai lallai yau zatasan da rufee take zancan,rabi'ah qyale rigar nan basai kin zugeta ba,shi zai qarasa zugewa da kansa" ta fada tana qwace jikinta,saita ciro wayarta daga jaka ta kirashi,bugu daya ya daga,ta narke masa sosai
"Kaga kasa qawayena sunatamin dariya wai bakaji dani tunda baka iya shigowa ciki mu fito tare" sosai ta rikitashi,saiya hau kallon mmn ummi dake qame a gefe ta gefan idanu
"Haba dai?,bari naxo to" ya fada yana kashe wayar
"Ina zuwa" kawai yace musu ya fito,saiya zagaya gefan murtala ya masa rada a kunne sannan ya wuce.


Tare suka jero shida ita,mmn ummi ta juya don gyarawa ummi xama a jikinta ta hangosu,wani abu taji yariqe mata wuya,ta zuba musu idanu sanda suke tahowar,sarai rufaida taga cewar ta gansun,hakan ya sanya tasaka hannunta cikin na bbn amir gami daci gaba da janye masa hankali har suka kawo bakin motar,idanunta nakan maryam din a fakaice,don babu laifi kwalliyar datayin ta mata kyau sosai,bata tsammaci ta iya ado yakai haka bama.


Shiya soma bude murfin motar yashiga sannan rufaidan
"Thanks my zuma" rufaidan ta fada tana kashe murya,murmushin yaqe yayi saboda mmn ummi dake motar,cikin tabara saikace qaramar yarinya soma tittirjewa
"Shine kayi shuru ba amsa?,wallahi kaci bashi,zaka sani"
"Yi haquri karki tasarmin yarinya" mmn ummi ta fada cikin matuqar tunzura,tanajin zuciyarta kamar zata fito,saita dan dago tana duban mmn ummi fuskatta cike da murmushin cusa takaici
"Au,ayyah antyna,kiyi haquri ai bansan kina ciki ba,ina yini?" Ta gaidata tana jefa mata wani kallon raini.


Lallai rainin hankalinta yakai,ita zata faki idanun bbn amir ta dinga jefawa kallon banza,sannan ta gaidata daga bisani,dauke kanta tayi tayi banza da ita,sai bbn amir din da baisan me ake ba ya waiwaya yana duban mmn ummin
"Ana gaidaki fa maryam" juyawa tayi ta jefawa rufaidan harara da kuma kallon banza sannan tace
"Lafiya" sama sama cikin shan qamshi,hakan ya batawa rufaidan amma saita share saboda tasan cewa lallai zata fanshe.


"Zugemin dear don Allah,tun daxu muke fama amma yaqi" sai kuma ta dubi mmn ummi
"Ki haquri anty zan dan ari mujinmu xai rufemin zip" wannan qaton asharne yazo bakinta,amma wanzuwar murtala a wajen yasa ta kasa furtawa,don tana ganin mutuncinsa kamar yadda shima yake ganin mutuncinta,hakanan tanajinsa yana zuge mata zip din tana wani shagwaba gami da cewa
"Yimin a hankali dear da zafi".


Maganar murtala yasanya mmn ummin taji kamar ta ciro zuciyarta
"Malama rufaida wannan shagwaba ai a bari mudan kauce ko?"fari tayi da idanu,maganarsa ji tayi kaman an qaramata qaimi ne
"Kai haba malam murtala,normal nefa,wannan aiba wani abu bane,na saba indai ina gaban dear,wani abun aisai an shiga daga ciki wannan kam ba wanda zaiji ba kuma wanda zai gani sai wanda yakai ido ko kunnensa"
"Hakane kam" ya fada yanason rufe maganar don ya fara shanshano wani abu.


Sanda suka fara tafiya qawar rufaida na gaba,hira suke ita da qawar tata suna kwasar dariya abinsu ganin kamar bbn amir din hankalinsa ya kasu kashi biyu,duk da tayi qoqarin janyr hankalin nasa donta cusawa mmn ummin haushi.


Suna gab da shiga wajen taron mmn ummin ta dora masa ummin datayi bacci saman cinyarsa
"Dan riqemin ita bari naje na kama ruwa nadawo" ta fada tana balle murfin motar tafice abinta,abun ya batawa rufaida rai sosai,don su kawai ake jira aga shigowarsu,ga qawayenta daga can qofa suna tsaye sun shirya kansu suna jiran shigowar tasu,sanda tasoma masa qorafin sunbar mutane na jiransu saiya dubeta
"Komu shiga ta tadda mu"
"Kan ubancan kayyasa" ta fada cikin ranta,a ranar auren nata,ranarta rana ta musamman kawai saiya wani sungumi 'ya su shiga dakin taro da yarinya a kafada,dan hoton da zatayi na amarya a kafadar ango shikenan yasha ruwa yake nufi ko kuwa,sam ba xata lamunta ba.



Wayarta ta dauka ta turawa zahra dake zaune gaban mota tex,ba'afi minti biyar ba zahran ta juyo cikin nuna kulawa
"Ita kanta babyn kidan gurin nan zai tasheta,gashi da alama taji dadin baccin,ko zaka kawota na sami zani na goyata ta kwanta sosai?"hakan sai yaga kamar yafi,hakan ya masa,saboda haka zahra ta zagayo ta amshi ummi,yayin da su kuma sukabi ta cikin ayarin masu tarbar amarya da ango suka dunguma dakin taron.


Sai data tabbatar ta bata lokaci me yawa sannan tafito daga inda take boye,dab da zata wuce securityn dake wajen taji ance
"hajiya,ko wannan diyarki ce?" Da sauri ta waiwayo,saiga ummi kan kafadarsa tanata baccinta,wani irin bacin rai take taji ya sauko mata,ranta yabaci sosai,har wani daci daci takeji saman harshenta,qarasawa tayi ta amsheta tana tambayarsa wanda ya bashi ita
"Watace ina tunanin qawar amarya ce"
"Na gode" tace dashi tana amsar ummi,cikin bacin ta durfafi dakin taron tana qiyasta cin mutuncin da zata yiwa bbn amir da rufaidan ma gaba daya,ita zai wulaqanta?,ya bada 'yarta kuma 'yarsa ajiya?,yana nufin budurwarsa ta fita tafi 'yarsa?,ashe haka bbn amir din yake sai yanzu ainihin kalolinsa suke dake bayyanar mata,lallai da gaske,bataga laifin matan da suke cewa duk wadda ta riqi namiji uba ta mutu marainiya,da gaskene namiji hankakane,gabansa fari bayansa baqi,ko a mafarki bata taba tsammatar haka daga baban amir ba,ta zaci ko a fuska kadai ta nuna batason abu ya barshi kenan har abada,ashe ita biqin jegon jaka takeyi.



Gab da xata shiga hall din daya daga cikin samarin dake gadin qofar yasa mata hannu
"Hajiya ina zuwa?" Daga kai tayi tana dubanshi cikin mamaki
"Ciki mana,ina zan shiga idan ba nan ba"
"Saidai ki koma gaskiya,an hana shiga"
"Kamar yaya?,kasan me kake fada kuwa?,kasan wace ni?" Dariya taga sun sanya gaba dayansu bayan sun hada idanu
"To hajiya ko wacece ke kuwa saidai ki haqura ki koma".


Nan ta tsaya musu bayani amma suka watsar da ita a wajen sukaci gaba da hirarsu,abinda yasake bata haushi yakuma daure mata kai shine bayan ita wasu da yawa sun shige,ta musu magana sukace sudin ai an gayyacesune ansan da zuwansu,wani azababben bacin rai yadinga cinta,kunyar yadda suka tozartata ya kamata,saita koma inda suka aje motarsu,abin takaicin a rufe take,murtala kenan shima yana ciki.


Wayarta taciro a gaggauce tasoma kiran bbn amir,lallai ba shakka dukkansu saisun gane kurensu,da saninsa kenan za'a wulaqantata?,ta kirashi a qalla ya kusa sau ashirin saidai bai daga,kasancewar yawa da qarfin hayaniyar dake wajen ba zata barshi yaji ba.


Kamar zata saki kuka haka ta rungume ummi ta soma takawa zuwa titi donta samu abun hawa ta wuce gida,don ba zata iya zama har sai an tashi ba,bacin ran da takeji ita kadai tasan irinsa,inda Allah ya taimaketa da jakarta ta fita,da a cikin motar aka kulle batasan ya zatayi ba.



Kai tsaye dakinta tawuce ba tare da kowa yasan tashigo ba,yaran duka suna dakin mmn amir sunma yi bacci abinsu,kayanta tasoma cirewa tana watsarwa,jin zuciyarta take kamar anyi gobara,xani tasamu ta daura ta zauna jiran dawowar baban amir.



Awa guda harda rabi wayarra tasoma ruri,data duba saitaga baban amir ne ke kira,wani mugun tsaki taja,tanajin wayar harta gama rurinta ta katse,ya sake kira har sau biyu amma wayar bata isheta kallo ba bare ta daga.

Qarfe sha biyu da rabi na dare yashigo gidan,sanda yarufe qofar tana jinsa,miqewa tsaye tayi tana sauraren qarasowarsa.



A qofar dakinta yaga takalmanta,hakan ya alamta masa ta dawo kenan
Dakin mmn amir yashiga ya taddata sunyi bacci duka ita da yaran,yau duka yaranma na dakin,mazan na falo ita da matan suna uwar dakinta saman gadonta,saiya koma da baya ya rufe musu qofar yadda ya ganta ya durfafi dakinsa.



Yana tsaka da cire shaddar jikinsa ta bankado labulen tashigo,saiya daga kanshi yana dubanta tare da karantar yanayinta,har saman fuskarta takejin zafi saboda bacin rai,ta tsaya gabanshi tana dubanshi.


"Basai kayi haka ba zaka tabbatarmin da cewa kai namiji ne,lallai ka nuna halinku da ainihin kalarku,jibril kai munafiki ne maciyin amana da zakaci mutuncina,ku hada baki da budurwar da zaka aura ku wulaqantani,nayi nadama da danasanin aurenka,ba abinda zance tsakanina dakai sai Allah ya isa!" Ta qarashe fada cikin daga murya da zafin rai,daidai lokacin da wayarshi ta dauki ruri,hannu yakai zai dauka tayi hanzarin rigashi kana ta daga tasa handsfree ganin sunan rufaida
"Dear,na manta kayana dana cire a motarka"
"Allah wadaranki kwarkwasa fidda me giji,baqar daga qarshenki ya kusa zuwa" ta fada tana katse kiran,sannan ta daga wayar zata kwadata d qasa,duk kuwa da cewa tasan tsadarta sarai,da hanzari ya tsaidata
"Karki soma,bani wayata!" Ko kadan bata saurareshi ba ta daga wayar ta makata a qasa,take ta tawarwatse saman tiles din.


Cikin bacin rai ua durfafota,zaginsa da fasa wayar suka hadu suka masa zafi sosai
"Idan ka iso karka barni da raina" ta fada tana tsaye qyam tana jiran qarasowarsa,yana isowar kuwa ya dauketa da wani lafiyayyen mari daya sanyata sakin qara saboda yadda ya ratsata,take rigimar ta sake zama sabuwa,ta soma masa jaye jaye cikin dakin naduk abinda hannunta yakai tahau bannatarwa.


Wannan qarar ita tatashi mmn amir,cikin tashin hankali ta fito daga dakin ta nufi dakin bbn amir din inda tajiyo hayaniyar tana tashi.


Daidai lokacin daya sake daga hannu xaikai mata mari mmn amir tashiga tsakani cikin hanzari,wanda kadan yarage yasameta
"Bban amir,meye haka?,meya sameka?"
"Ki qyaleshi ya aikata abinda yayi niyya,zai auro wata dama babu abinda bazai aikata ba!" Mmn ummi ta fada da madaukakin harshe,fuska jazur,saita waiwaya tana dubanta sanda bbn amir yace
"Idan bata ficemin a daki ba zan aikata duk abinda yazo raina" qin fita tayi sukaci gaba da sa'insa,harsai daya kusa sake kai hannu jikinta sannan mmn amir din tayi nasarar fitar da ita.


Cikin fushi yake furzar da iska me zafi,yasamu gefan gadonshi ya zauna yanajin yadda kanshi ke sake daukar caji.



Gefan gadonta ta zaunar da ita sai kuma mmn ummin ta fashe da kuka tana rufe fuskarta,ji take gaba daya duniya ta mata zafi,kamar duk wata qofar walwalarta da farinciki an tosheta,tsayawa kawai mmn amir tayi tana dubanta,tome xata gayawa maryam?,kome zata gaya mata ta jima da gaya mata shi,ita kanta tagaji da ganin wannan bala'in,tayi a qalla minti ashirin tsaye a kanta kafin tace
"Allah ya kyauta,ya sawwaqe" ta juya tafita daga dakin.👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*


*BABI NA SHIDA*




Tunda safiyar garin asabar ta waye tasake shiga fita hayyacinta,tunda ta idara sallar asuba ta kasa komawa bacci,sai zirga zirga da take tsakanin tsakar gidan soro zuwa nata dakin,idanunta kacokam yana kan dakin baban amir,wani mahaukacin kishi takeji,yanxu nan da wasu awanni kenan yaxama nasu su uku?,tashin hankali,saita dora hannunta aka tana neman inda zata sanya zuciyarta da ranta taji dadi,wani irin radadi da zugi gamida qunci takeji cikin zuciyarta,saita dauki wayarta ta kirayi hafsat.


Bugu hudu ta daga
"Ya akayi mmn ummi,mun tashi lpy"
"Babu batun tambyar lafiya game dani,tunda kin san babu ita,yaushe zaki shigo,wallahi hafsat jin gidan nan nake kamar wata qiyamata ko lahira"
"Karki damu ina sallamar babansu minal zan shirya na taho"
"Don Allah karki dade"
"In sha Allahu" aje wayar tayi tana furxar da iska daga bakinta.


Wayar tatace tasake ruri,data duba sai taga lambar qanwarta ce,ba jinkiri ta daga sai taji muryar mahaifiyarta,kuka ta sanya
"Meye haka maryam?"
"Umma yaune daurin auren fa?"
"Sai kuyi haquri ai,haka Allah ya dora muku"
"Don Allah umma kixo,don Allah"
"A'ah,nikam bazanzo wannan gidan naku ba,zandai turo miki ruqayya da zakiyya,sai yayarku duka zasu taho tare"
"Toh umma"
"Zasu taho miki da saqo,saiki sawa ranki haquri,tunda haka Allah ya dora masa" daga haka sukayi sallama,saita danji sanyi da maganar da sukayi da ummantata.


Qarfe takwas tasoma jin motsin yaran a tsakar gidan,tun cikin satin suma yaran ta sallamasu gaba daya,mmn amir ce keta hidima dasu,hattasu abun ya shafesu,ita kuwa maman amir ko a jikinta,saboda kai kawon yaran da kula dasu da takeyi ya dauke mata hankali gami da debe mata kewa da bacin rai,idan tana tare da yaran sai taji ta manta da wasu abubuwan.


Miqewa tayi ta isa bakin window tana leqen abinda yake faruwa a tsakar gidan,mmn ummin ce zaune saman kujera 'yar tsugunno,gabanta sabbabin shaddodine ruwan omo,saman cinyarta wasu daga wandunan yaranne tana saka musu tazuge,mubarak na tsaye a kanta da alama yayi wanka ya shafa mai yana jiran ta gama saka masa tazugen tabashi ya saka,yayin da mmn amir din ke aikin tana gyarawa hanifa wankan da takewa usman.


Wani baqinciki da bacin rai ya kamata,wato har wani anko ya yiwa yaran na xuwa daurin aurenshi kenan,ita batama sani ba?,kafin tayi kowanne yunquri baban amir din yayi sallama yashigo gidan,hannunshi dauke da wata shaddar kalar ta yaran,da alama tashice ya amso.


Qurawa fuskarshi idanuwa tayi sanda yake qarasowa gaban mmn amir,fuskar da ada babu wata fuska da takeso da qaunar gani amma a yanzu babu fuskar data tsana take jin haushi da takaicin gani irinta
"Sannu da aiki maman yara" ya fada yana murmushi,har cikin ranshi kuma yanajin dadin yadda take shirya yaran zasu daurin auren tare dashi
"Yauwa" ta fada ciki ciki fuskarta sam babu wannan fara'ar daya saba gani,duk sai yaji jikinsa yayi sanyi,tayi qoqari matuqa kuma tana kanyi,yasani cewa baiwa Allah yayi masa da uwar gida,wadda ta tsaya kai da fata wajen ganin ta hade kan gidan waje daya,ya tabbatar da maryam ce uwar gidansa tofa sai abinda hali yayi,yasani sarai cewa suk maigidan da yayi rashin dacen uwar gida toya kade ya gama yawo,duk wadda zai aura daga baya mawuyacine idan batayi

Please Login or Register in order to submit comment