Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dinta tacika ta da turaren wutarta tadawo falo tazauna tahada tea mai kauri tasoma sha kafin abba yatashi ya tsotseta,don bata dafa abun kari na gidan ba,iya na 'yan makaranta tayi tunda ba girkinta bane.


Cikin qaramin lokaci saqon qamshinta ya gauraye ilahirin gidan harda maqota,ya hadu da ragowar sanyin safiya yabada wani yanayi mai dadi,haka qamshin yacigaba da kutse har cikin hancin bbn amir dake kwance yana bacci,saiya soma bude idanunsa a hankali yana tuna a inda yasan wannan qamshin.


Sassanyan murmushi yasaki yanajin wani madaukakin farinciki yana ratsa zuciyarsa daya tuna yau kwanan halimatussadiya ne,saiya tashi yazauna sosai saman gadon,yawaiwaya gefansa saiyaga rufaida na sheqar bacci abinta,da sauri yakalli agogo,tara saura,yara fa?,waye yashiryasu zuwa makaranta?,yayiwa kansa tambayar,cikin hanzari yasoma tashinta.


Sai data gama miqa sannan tamiqe tazauna cikin ranta tana mita,tana kishinsa amma wani lokaci takan gwammace ba kwananta bane,saboda tafiyin baccinta ta more yadda ranta yakeso.


Tsaki taja ciki ciki bayan tasauke hamma sannan tace
"Lafiya?" Agogo ya nuna mata yana shirin sauka daga gadon
"Yauda makaranta,yara ba abinda aka dafa musu bare a shiryasu,yi maza ki tashi don Allah" yafada a gurguje yana dage labulen bedroom din yafice daga dakin,wata muguwar harara tabi bayanshi dashi sannan taja matsiyacin tsaki,cikin qunquni tasoma saukowa tana maganganu ita kadai
"Wai yara,ina ruwana dasu,kada Allah yasa suyi karatun ma,auren mai iyali auren jaraba auren masifa,baya ta taka kullum sune a ransa,kafin ya ambaceka ma ya ambacesu,baka haifa ba amma ka qare a bauta" ta dura ashariya sannan taja zaninta tayi daurin qirji kafin tafito falonta.


Da mamaki yake duban tsakar gidan yadda yake fes fes kamar wani lokaci can baya,saiya kauda wannan yanufi dakin mmn amir don yaji baiji ma motsin yaran ba.


Sallamarshi da lumshe idanunsa duka lokaci guda yayisu sabida qamshin daya mamaye hancinsa wanda yayi kewarsa fiye da tunani,sanda take amsa masa sallamar samun kansa yayi da zuba mata idanu,wani irin kyau tayi masa gamida daukar hankalinsa ba kadan ba,ga qamshinta daya cika mishi hanci,ita dinma ta lura da hakan,saboda haka tasaki murmushi,tasan cewa tun rana ta dana tarkonta,lallai yau zai wuni ne da tunaninta,hakanan dokinsa zai sake ninkuwa.


Amshe gaisuwar da take mishi yayi
"Ina yara?" Dan juya idanunta tayi
"Yara kuma aisun tsufa a makaranta" ajiyar zuciya yasauke
"Ina can ina na rude naga lokaci yawuce na zaci basu tafi ba"
"Haba kai kuwa abban amir,kawai saimu zauna jira bayan zamu iya sallamarsu" murmushi yasaki
"Hakane,amma wannan aikin nasan na halimatussadiya ne" yafada yana mata wani irin kallo,saita saki murmushi kawai tadan sadda kai alamun kunya,wanda hakan ya qayatar dashi sosai.


Ta bangaren rufaida kuwa tunda tafito tasaki baki galala tana duban yadda gidan yacanza gaba daya kamar bashi ba,gabanta yayi mummunar faduwa data tuna cewa yau baqar rana ce a wajenta,wato ranar da mmn amir din xata amshi girki,tana nan tsaye tana jimami har mmn ummi da tun sassafe ta saka lalle da salatif din da mmn amir ta bata tafito cirewa saboda yayi awannin daya kamata yayi,bata kalli rufaidan ba tawuce bakin famfon tawanke abinta,duk akan idon rufaidan
"Cabdijan,wai suna nufin kai zasu hademin,ita taje an mata lalle itama ta saka,kan uban nan kayyasa".


Sanda mmn ummi tazo gifatata sai tahau yada waqar habaici,duk daba daidai take waqar ba
"Kayan aro abun banza ne......dole wataran kadawo naka" ita dariyama tabaiwa mmn ummin,bata isheta kallo ba ta wuce dakinta ta turo qofarta tabarta anan a tsaye,don a yanzu ta girmi wannan abun,bata sake ganin wautarta bama sai dataga yadda mmn amir din ke komai cikin aji da hankali.


Abun saiya tsayawa rufaidan a ranta,ita daya atsakar gida,ta kasa wucewa kitchen dinma bare tadora abinda zata dora,tana shirin shigewa saiga bbn amir yafito daga dakin mmn amir din,fuskarsa dauke da murmushi,don iyakar ganin da yayiwa haliman ya tabbayar yau a ango yake sak.


Da idanu ta tsareshi,zuciyarta kamar tafaso qirjinta tafito saboda kishi,taci gaba da kallonshi harya wuce dakinsa batare daya kula ma da abinda take ba.


Wannan bacin ran yasanyata ruwan tea kawai ta dafawa a gidan tsurarsa,tunda kowa nada bread dinsa a daki,yawanci da daddare yake shigowa dashi yabaiwa kowacce nata.


Tayi hakanne dabiyu donta batawa bbn amir din rai,abinda bata sani ba ko a qasan silifas dinsa,yasan yaudin ko babu komai zai huce duk wani bacin ranshi,yashirya abinsa ya biya dakin mmn amir din tana zaune tana baiwa abba nono yabata kudin cefane hade da muqullin dakinsa
"Rufaida tana ciki,idan tafita kya kulle" ya gaya mata,kyawawan addu'o'in data saba tayi masa,ya amsa cikin walwala kana yafice.


Sai data gama bawa abba nono sannan ta goyashi tafito,don tana son gyaran dakin bbn amir din,shi kadaine bata gyara ba saboda bata da dama a sannan,don girkin mmn ummine data gama ta baiwa rufaida,batason tashiga haqqinsu,ko baya ga haka ma batason tayi gyaranta wata ta bata mata.


Ga mamakinta har yanzu rufaida na cikin dakin,ta gane hakanne ba tare data shiga,takalmanta data gani kawai ya shaida mata,saita qyale bata shiga din ba,takoma ta hada ruwan wanka tayiwa abba,tashiryashi ta sake goyashi sannan takuma fitowa taduba ko zuwa yanzu tafita daga dakin,saidai har yanzu tana ciki,a karo na ukune data ga bata da niyyar fita ta yaye labulen falon kana tawuce uwar dakin,don tanason gamawa da wuri tadora abincin rana saboda yara 'yammakaranta da zasu dawo.


Shame shame tasameta saman gadon,daga ita sai kayan bacci masu shara shara sosai,wayarta a hannunta tanata charting,ta daga kai suka hada idanu,sai mmn amir din ta gintse kamar bata ganta ba tasoma tattare labulen bedroom din don so take ta sauya mishi wani data siya duk da mai sauqin kudine amma suna da kyau.


Harta gama cire labulayen bata motsa ba,don haka cikin dakiya dashan magani tace mata
"Ina buqatar space zan kintsa dakin" wata miqa tayi tana tashi zaune sosai
"Oh sorry.....wallahi....jikinane duk ciwo yake,a gajiye nake,kinsan halin maigidanne haqurinsa kadanne,baida wasa ta wannan fannin" juyowa tayi sosai tadubeta yadda taketa wani yatsina,murmushi mmn amir din tayi duk data motsa mata kishinta amma bata bari tagani ba koda saman fuskarta kuwa
"Qwarai kuwa,nizan bada labarin haka,ai Allah ya taimakeki ma da kikazo a qarshen lamarin,kina da mataimaka masu karbar miki shi ki huta,ni a lokacin da nake amarya ni kadai dagani saishi,dukka soyayyarsa babu wajen da zai raba ya rageta ni kadai nake tallafarta ai ansha gwagwarmaya,kice da kece bazaki iya ba,ashe nidin ba qaramar jaruma bace,shi yasa kinga yara hudu cas ga goyon na biyar a baya,banda jarumi wazai haka?" Dum rufaida tayi,saboda ta fuskanci bayan maida mata magana datayi harda habaicin bata mori soyayya ba ita kadai,don haka ta figi mayafinta ba tare data ce komai ba tafice a dakin
"Mara kunyar banza da wofi,mu zuba,nida ke shege ka fasa" taja qaramar qwafa taci gaba da aikinta.


Gyara tayiwa dakin na haqiqa komai saida tabi ta kanshi,hakan yadan ja mata lokaci,inda Allah ya taimaketa mmn ummi da taga bata komai saita tayata da gyaran su kayan miya da sauransu,tana bakin qofar sunayi suna taba hira,zuciyar rufaida kamar tafito,haka tadinga leqensu ta window dinta abun yana nata ciwo,daga qarshe data rasa yadda zatayi tahau group dinsu ba watsapp tasoma bawa qawayenta labari tana tsinewa su mmn ummin da basusan me ake ba,suka tayata suka zagesu tas,kana kowace tahau bata kalar tata gurguwar shawarar.


Tana da zafin aiki ba laifi,don haka tana kammala girkin baifi da minti biyar ba yaran suka shigo,a sannan qamshin miyar data sauke bai gama tafiya ba wanda taji spices din data tanada tun randa tayi siyayya,aikuwa suna sallama kowanne yasoma cewa yunwa yakeji,mubarak kuwa yaron mmn ummi dayaga itace akitchen saiya riqe cokali yahau rawa
"Yau zamuci girkin umma" haka Allah yayishi duk dabai wuce shekara goma ba amma yanason abinci mai dadi,yakuma san umman tasu ba baya bace,ko jallop ta sarrafa saikaji taste din har tsakar kanka.


Abinci tayi mai kyau ba kamar wanda mmn ummi kanyi ba koda yaushe da rana basa wuce dafa duka saboda gandar dora sanwa biyu,uwar gayya rufaida kuwa tunda tazo girkin rana fara da maice,maici yaci,mara ci ya haqura,ta hadawa mazan daban matan daban,tasa amir yadaukowa kowa lemo a fridge dinta,nan fa baki ya gaza yin shuru,sukayita surutu wanda idan kakula dakyau santi suke.


Mmn ummi na daga falonta wanda labulenshi ke a dage tana karantar taran,farincikin da suke da yadda suke enjoying abincin kawai ya isa ya gaya maka abunda ke cikin zukatansu,sai a sannan tayi picking wani kuskuren nata wanda tunda suke da mmn amir din batama taba fuskantar yadda suke zumudin abincinta ba sai yanzu,tasan dai yawancin lokuta zataga mmn amir din idan zatayi miya tana daka wasu abubuwa tazuba wanda ita a wajenta bata daukesu a bakin komai ba,hasalima ganin qoqarinta take idan tazauna tana yiwa miya dake dake,takance
"Bayan zaman bare maggi saikin wani zauna wani aikin bare bare na wasu abubuwa daban?,ai miya indai maggi da mai yaji shikenan an wuce wajen".


To ita kanta ayau datake cin abincin ranar tana cine tana karantar banbance banbance,babu qarya abincin ya mata dadi harta taya yaran suma.


Rufaida kuwa tun tana daki qamshin ya isketa,saita dinga tunanin daga maqota ne,amma sanda tazubo abincin saita gane daga ina ne,sanda tazauna tasoma ci taso taci da yawa saboda taste din yayi masifar kama mata harshe,amma data tuna shawarar da daya daga cikin qawayenta ta bata ba banzatar da abinci da yawan qorafi gaban maigidan kan girkin mmn amir din saita dannan babbar loma a matsayin lomar qarshe tamiqe da kwanon a hannunta ta isa kitchen.


Takuwa taki sa'a mmn amir din tana ciki tana kwabin wainar shinkafa,ta aika amir kan suwuce islamiyya cikin kudinta yasiyo tantaqwashi donta sake burge bbn amir din
"Nifa gasky qamshin dake cikin miyar nan yahanani cin abinci,don wallahi niban saba jin irin wannan ba,saikace an zuba mata turare,komai gauuuu a ciki,gasky bazan iya jurewa ba don ban shirya zama da yunwa ba wlh" ta dangwarar da plate din ta tsaya tana jiran taji me zatace.


Saidai banza mmn amir din ta baiwa ajiyarta,idan tukunyar dake kitchen din ta nuna tasan rufaidan tashigo to mmn amir tanuna tasan da shigowarta,saita maida kanta ga hanifa dake yanka mata alayyahu tana gyara mata yadda ake jerashi kafin a yanka,don yawancin yanzun tare suke shiga kitchen ranakun da babu makaranta,ko idan aiki yacabe mata kamar yau kafin lokacin shiga islamiyya yayi,tunda sai uku da rabi suke tafiya.


Ganin taqi ko dubanta saita buga tsaki
"Bari shi jibril din yadawo,yasan matakin dauka wallahi" tafice faran faran daki,haka ta haqura tacika cikinta da ruwa tana jiran dare sadda maigidan zai dawo.


**********


Kafin magariba ta gama komai,gidan yadauki harama,hatta iskar gidan kamar an canzata saboda qamshi take bayarwa,tayi wanka hade da alwala tashige uwar dakanta,bayan ta baiwa su amir dake assigment riqon abba,ta tura qofar tarufe saboda idanun yara,kana tasoma kintsawa,duk wani loko da saqo na jikinta tayi mishi abinda ya kamata kafin lokacin bacci yayi,ta duba cikin kayanta ta fidda riga da skert na atamfa da dinkin ya mata cas yafidda kowanne komada ta jikinta tashirya kanta a ciki.


Bata fiya damuwa da sanya qananun kaya ba idan ba gown haka ba ko skert budadde saboda yara,tayi imanin cewa basai kin saka kayan da qirjinki zai fito koya kasa rufe miki cibiya,koya shaqe miki wuya ko hannu sannan zaki kyau ba,a'ah,shi ado da kwalliya iyawa ce,saidai duk sanda tayi shigar wala atamfa ko gown takanyi wani kyau,saboda kowanne lokaci takanyi duba da yanayin da kwalliyar zata dace dashi.


Sosai tayi ruwan tararewa kanta,sannan taduba wata after maikyau cikin kayanta tadora saman kayan saboda sundan matseta,amaimakon ta bata mata kwalliya saita sake qawatata,kamar baqar balarabiya,ta yafa qaramin mayafin after din tafito zuwa dakin bbn amir donta aje wasu kayyaki da zata iya amfani dasu a kwana biyun da zatayi,dazun saboda idanun mutane yasa bata shiga da komai ba tabari sai duhun magariba yashiga.


Kusan a idanun rufaida kome yake wakana,don tunda tazauna bakin window dinta takasa tashi,addu'a kala daban daban tadinga yi,har bata qaunar taji sallamar bbn amir yau cikin gidan.


Fes ta hangi mmn amir din saboda akwai wutar nepa,qirjinta yahau suya da wani irin kishi,harta shiga tafito idanunta yana wajen.


Haka kawai yaji yau bazai iya shiga gidan hannunsa haka ba duk da babu isashshen kudi a hannunsa saboda har yau basu fita daga matsalar batan kayansu ba,kawai dai ana jalauta rayuwar cikin rufin asirin Allah,dama kuma jibril din ba baya bane wajen riqo wani abun yashigo gida dashi,ba kasafai yake shigowa gida haka ba.


Kifi ya tsaya yasiya musu mai kyau mara qaya ragon ruwa kana yawuce gida.


Yana sallama dukka yaran dake dakin mmn amir suka fito suna masa oyoyo,kasancewar sunfi zama a can har yaran mmn ummi,basu wani damu da dakkn mmn nasu ba sosai,don mmn amir din tafi dadin sha'ani,hatta da ummi da yanzu tasoma wayo tafison tafiya can,wani lokaci saisu bar mmn nasu ita kadai.


Ummi dake itace qarama yasoma dagawa sauran yana shafa kansu yana amsa sannu da zuwar da sukeyi masa,dai dai lokacin da rufaida ke labe bayan labule tana kallonshi gabanta na faduwa,kishi fal ranta.


Tunda yashigo yashaqi qamshin gidan gaba daya hankalinsa ya karkata wajen mmn amir din,amma dole yayi adalci yadda yasaba,mai girki dakinta ne qarshen shiga,wannan karon mmn ummi ce a matsayin babba,don haka yanufi dakinta.


Tana zaune a falonta tana goge kayan yaran yashigo,fuskarta ba yabo ba fallasa ta aje gugar tana masa sannu da zuwa da tambayarshi ya kasuwa kamar yadda taga yawanci mmn amir din nayi,ya amsa ciki jin dadin yadda take sake sauyawa,yana addu'ar Allah ya dorar da ita,yana kuma qara ganin qimar halima don ya tabbata kusan itace silar wannan nasarar data fara samuwa.


Saiyadan zauna mata nadan wani lokaci donya faranta mata,kana ya fice zuwa dakin rufaida usman rabi'a da ummi suka bishi.


Tana ganin tahowarsa takoma takwanta rigingine tabaiwa qofa baya,da qyar ta amsa sallamarshi yaqarasa shigowa idanunshi kanta
"Lafiya dai ko?" Ya tambaya ganin yanayin nata,saita yatsine fuska tana wani gyara kwanciya daqyar
"Tunda kafita bani da lafiya ne" tayi maganar tana hararar yaran ta qasan idanu,saboda takaicin hawar mata kujera da sukayi
"Ayyah,Allah ya sawwaqe,kin sha magani ne?" Saita kada kai,anzo wajen,dama kudi take nema daga wajensa,tana so tacika kudaden da take fafutukar hadawa don ta yaqeshi shida matansa gaba daya
"Asibiti nakeso naje gobe" shuru yadanyi don yasan kudin hannunshin yanzu basufi suyi masa lalurar gobe ba,inda yasan zata buqaci zuwa asibitin da ya haqura da siyan kifin,amma yasan goben Allah bazai hana yadda za'ayi ba
"Ba komai,Allah yanuna mana goben,duk da babu kudi hannuna amma Allah bazai hana yadda za'ayi ba zuwa goben" wani qarin takaicine yacikata sanda yamiqe zai fita yana mata sallama,na farko ta tsammaci yadda taketa juye juye zai tsaya ya bata lokaci sosai wajenta fiye da yadda ya bata yanzun,nabiyu kuma baqincikin yadda kullum babunsa take qara gaba take,ta zabeshi cikin manemanta ganin duk yafisu abun hannu,ashe zata bare da ita,taja wani matsiyacin zaki tana kashingida gamida zaro wayarta,a sarari ta furta
"Mtswee,tsautsayin takaba auren shidadde" saita koma grp dinsu tana duba chart din da aka gama dazu,ana hirar wani dan grp dinsu da yake buga wani game,yayi kudi lokaci guda sanadiyyar hakan,harma ga motar daya siya nan falleliya an turota group.


Bata mantawa sa'idu na daya daga cikin masu sonta a sannan,amma saboda bashi da komai taga tafi qarfin ajinsa,me zatayi da saurayi wanda a yanzu yake fafutukar nema,mena sama waci bare ya baiwa na qasa,gwara dai ready made
"Allah dai yasa ba rabon wahala bane yake kirana,gudun qaddara guzurin taddata,Allah ya kiyaye" tafada bayan tagama duban hirar tasu.


Sanda yashiga falon nashi komai ready yasameshi,hatta da cokali da tsumman dazai goge hannunshi,murmushi yadan saki saboda yayi missing irin wannan,gyaran falon kawai yasake kwantar mishi da rai,ya fuskanci kamar yaudin wani dan jan aji takeji dashi,don sanda yashiga da yaran dakin nata sai ya tadda tana bandaki wai,don haka yayi dakinsa cike da daukin ganin isowarta.


Tana sallama yacira kai da sauri,ya amsa mata yana qare mata kallo,tana qarasowa dab dashi xatayi masa sannu da zuwa yayi caraf ya janyota cikin jikinsa,saiya sauke ajiyar zuciya yana jin yadda yayi rashinta da yawa,qamshinta yake sansana loko da saqo na jikinta yana lumshe idanu
"Yau an 'yantani halimatu" dariya tadan kubce mata,kafin tayi magana yasake cewa
"Qamshi kike mmn amir,qamshi mai dadi,gaskiya na yadda yau ango nake" nanma dariya yabata,saita zame jikinta tana cewa
"Kasoma wanka tukunna bbn amir" ta tuna masa abinda yaso mantawa,don bayan barinta dakin babu wadda tadamu dawai yayi wanka bayan yadawo daga kasuwa,saidai wani lokaci shi a karan kansa idan yaji yana da sha'awar yin hakan.


Kusan kome yake hankalinsa yana akanta,haryayi wankan yafito,sai yace sai yaje yayi sallar isha'i sannan zaici abinci,don haka ya hada kan yaran mazan suka wuce masallaci.


Kafin yadawo ta gama da yaran,har abba dake bacci tabar musua dakinta,bayan ta kunna musu cartoon a mbc 3 bayan ta tabbatar da cewa basu da wani assigment na makaranta,saboda haka yana dawowa ta tattara mishi dukka lokacinta,wani sabon amarci sukeji dukkansu ita dashi,don a jikinsa take tana bashi abincin da kanta,bai sake sanin yayi missing komai nata ba sai daya soma cin abincin,lallai ba shakka yayi rashi mai yawa,ya rasa taste dinta na musamman
"A ina aka samu nama yau a miya?" Ya tambayeta sanda yaga nama a ciki,murmushi kawai tayi
"Allah ne yabamu yau" shima murmushin yasaki,yasan halinta tun ba yau ba,kusan takanyi hakan lokaci zuwa lokaci,musamman idan taga kwana biyu bai siya ba,koda yana da kudi,idan tayi hakan saiya zama kamar tuni ne a wajensa ba tare datayi magana ba,baya rufa kwana uku bai siya ba kuwa daga ranar,dukka hankalinsa yana kanta,musamman yadda dinkin ya fidda qirjinta dake a cike
"Nikam abban amir kada ka cinyeni mana,wannan kallon fa" tafada adan shagwabe kamar ba ita ta aje amir da ahmad ba,murmushi yasaki kana yace
"Ba zaki fahimta ba uwar gida sarautar mata" daidai lokacin rufaida ta turo qofar gamida yaye labulen,dukka suka maida dubansu gareta,sai sannan tayi sallama zuciyarta kamar zata tsinke saboda yadda tagansun ko ita a kwanakin amarcinta ba zata iya tuna sanda suka zauna kamar haka ba ita dashi
"Lallai matarnan ta cika qaramar karuwa" tafada a ranta.


Janye jikinta mmn amir tayi gefe,saidai bata ko daga kai ta kalli rufaidan ba,hakanan bata tashi daga wajen ba,don zuciyarta da jikinta ya bata da gangan tayi hakan,bai kyautu tafado kai tsaye ba ba tare data tsaya daga bakin qofa ta nemi izni ba,tunda daga ita har mmn ummi haka sukeyi idan zasu shiga wajensa indai harda wata a ciki.


"Lafiya?,qaraso bismillah" abban amir din yafada cikin mamakin ganinta,ya tsammaci ko jikinne,saidai sanda tazauna tana harhada rai,kishi na sake kamata,bata taba tsammanin haka mmn amir din keda kyan jiki ba,a yadda tasanta tana da ciki duk ciki ya bata yanayinta ta zaci a haka take,kota haihu ba zata canza ba,saboda tana jin labarin haihuwa tana lalata shape da kyan jikin mace,amma saitaga sabanin haka,uwa uba ma bata da rabin structure na jikin mmn amir din,tana ankare da kallon da take mata,saima tasake daidaita zamanta dakyau tana basarwa itama,qorafi tasoma cikin bacin rai
"Qara nakawo maka jibril?"
"Qarar wa?" Ya tambaya cikin mamaki
"Wadda tayi girki yau,ni gaskiya ba'a kyautata min ba,ya za'a bani wani abinci duk qamshi,an cika abinci da abubuwa wanda ni na kasa ci bazan iya cin abinci mai qamshi ba"
"Qamshi?,wanne irin qamshi ne a girki halimatu?" A nutse tace
"Nima dai ban sani ba,amma gata nan ka tambayeta".


Bai sake cewa komai ba saiya daga waya yakira mmn ummi,babu dadewa tashigo ya tambayeta
"Qamshi kuma?,agirkin namu?,indai qamshi take magana saidai irin na wannan miyar da kake ci" tafada tana dora idonta ga rufaida
"Kasan dai yanayin girkin mmn amir din,qamshin girkinta daban yake" kai ya jinjina don yafi kowa sanin hakan
"Ai dama nasan baza'a gaya maka gaskiya ba,saboda ni aka tsana,anason hademin kai a musguna min,to nidai nawa abincin banda qamshi kamar na turare turare ko hoda babu abunda yake,saidai idan iya nawa kawai aka zuba saboda kada naci" dubanta kawai mmn amir tayi
"Ina zuwa" mmn amir din tafada tana fita,babu jimawa yadawo da farantin da rufaidan tasoma cin abincin,yana nan yadda ta maida kitchen din,hatta da cokalin bata cire ba,takuma ajene saboda abinda kaje yazo,sai gashi kuma abinda take zaton din ya tabbata.


Gabanshi ta aje farantin tabude masa,kowa yakalli abincin yasan ba sabon zubi bane,an dade da zubashi kuma akaci kadan aka barshi
"Bismillah" mmn amir tace masa,saiya dauki cokalin ciki yayi loma har uku,baiji komai ba face qamshin spice dai irin na miyar da yake ci yanzu kamar yadda mmn ummi tace masa.


"Indai kinci wannan miyar irin ta gabana to babu abinda yaraba taste dinsu,babu wani qamshi a cikinta daya saba"
"Ai dama nasan haka zaka ce,to miyar yau qashi daya tsoka daya aka bani saikace wata mayya"
"Ban bada kudin nama ba,adalcinta ne yasa tasiya tasaka muku" sai kuma tayi shuru,mmn ummi tamiqe tana danne dariya,saidai bata yiba illa cewa
"Uhmmm" datayi
"Allah kyauta,Allah yabamu alkhairi" tafada tana ficewa daga dakin.


Gwiwa a sanyaye ta miqe tana qananun maganganu tafita itama tafita,sam ba haka taso ba,dukka yadda takeso bata samu ba,amma ba zata taba haqura ba,don abinda idanunta suka gani tattare da abban amir da bbn amir din bata taba tsammani ko a mafarki zataga kusanci da qaunar juna tsakaninsu haka ba.



*YAN BIYAR*๐Ÿคš๐Ÿฝ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ


*_RUMBUN FASAHA SUNAN WANNAN TAFIYAR_*๐Ÿค™๐Ÿฝ๐Ÿค™๐Ÿฝ๐Ÿค™๐Ÿฝ


*WANNAN KARON TAFIYAR TA BAMBANTA DA SAURA*

*KOWANNE LABARI YADAUKI SABON SALO*


*SABON SALON DA BABU KWATANKWACINSA*


*ZAKI GASGATA HAKAN IDAN AKAYI TAFIYAR DAKE*


*BILLYN ABDUL*
_SARAN BAYA_

*HAFSAT RANO*
_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_

*HUGUMA*
_SIRADIN RAYUWAR BILKISU_

*MAMUHGHEE*
_MIN QALB_

*MISS XOXO*
_KIBIYAR AJALI_

_dukkan ruguntsumin gamayyar wadan nan litattafan zaki samesu kan farashi na_700

5 ๐Ÿ‘‰๐Ÿพ700
4 ๐Ÿ‘‰๐Ÿพ500
3 ๐Ÿ‘‰๐Ÿพ450
2 ๐Ÿ‘‰๐Ÿพ400
1๐Ÿ‘‰๐Ÿพ300

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

ACCOUNT NO-
*0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

ย 0903ย 234ย 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR
[10/3, 3:03 PM] Hadiza Tanko: ๐Ÿ‘๏ธโ€๐Ÿ—จ๏ธ๐Ÿ‘๏ธโ€๐Ÿ—จ๏ธ *HANGEN DALA*๐Ÿ‘๏ธโ€๐Ÿ—จ๏ธ๐Ÿ‘๏ธโ€๐Ÿ—จ๏ธ
_Ba shiga birni ba_


ยฉ๏ธยฎ๏ธ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso ๐Ÿ’ก

*BABI NA SHA ASHIRIN*




Kafin ta kwanta Sai data tabbatar ta sallami yaran bayan ta sanyasu sunyi addu'a kowa ya kwanta,sannan tadauki Abba tawuce zuwa dakin bbn amir. Cikin Pampers ta shirya Abba ta sauya Masa Kaya masu nauyi sa'annan itama tashirya cikin Daya daga cikin kayan baccinta,tun Tana shiryawar tagama tafiya da bbn amir din,Allah ya Sanya a lokacin abban yayi bacci,saboda haka ba Bata lokaci Suka Lula zuwa duniyar ma'aurata. Fadar yadda Daren ya wakana man Bata bakine,kewa ce ta hadu da gyara,Sai bbn amir din ya tsinci kansa cikin wata duniya ta daban,zai iyacewa bai taba tsintar kansa cikin wanna situation din ba. Koda asuba da Suka tashi salla bayan ta hada musu ruwa Mai dumi sosai sunyi wanka,saiya rasa me zayace Mata,Tana zaune gefansa Tana lazumi "Allah

Please Login or Register in order to submit comment