Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki,ina shirin ganin abinda ba haka ba daga gareki" fuska tadan yamutsa,saboda babu abinda zancan nasa suke mata sai bata mata rai,itafa arayuwa babu wanda ya taba mata kwatankwacin abinda jibril din yake mata yanzu,donko saurayi magana daya zai gaya mata yanzu ta sauyashi,bata lamunci a dinga gaya mata magaba kai tsaye ba
"Kaman yaya?"
"Kamar yadda nake gani" ya bata amsa shima kai tsaye
"Yanxu duk qoqarin da nakeyi kai baka gani,baka yabamin saima kusheni da kawo matsalolina,duk yadda nake haquri a gidan nan baka gani ba?" Ta fada cikin kuka,don ita harga Allah bata gano laifinta ko daya ba,sai tarin laifinsa dana matansa
"Tunda hakane saika fadi dame dame nake maka".


Tiryan tiryan ya lissafo mata komai,saidai cikin zuciyarta tsaki take ja kawai,tanason maida masa wata zuciyar na kwabarta,saboda tana lissafe nan da rana ita yau zata amshi kudin ankon bikin qawarta,kuma taji daga bakin qawayenta masu aure,idan kika sake wani abun ya hadaku yana iya hanaki kema abinda kike buqata,saboda haka ta faki idanunshi ta yatsina fuska sannan tace
"Shikenan naji,xan gyara"
"Da dai yafi,saboda na auroki ne don dukkaninmu munason juna,na auroki don dukkaninmu muyi farinciki datarayyarmu da juna har lahira,abu nabiyu,irin wadan nan kayan banaso kina yawo dasu cikin gida haka,saboda yarana da sauran masu shigowa wadanda suke ba hurammanki bane,a qa'ida ta addini bai kamaci ace suna ganinki haka na,bugu da qari tarbiyyar yaran gidan,kinsan yaro da riqe abu da fahimta,bare kusan dukkaninsu sun riga dasun tasa,balaifi zaki iyamin ado dasu sanda muke daga ni saike,don Allah ki lura ki kuma gyara" wani abune yasake tsaye mata a wuya,kusun uba,waime jibril yake nufi ne?,kwalliyarma da zata ringa da qananun kayan zai hanata,abinda taci vuri ta kashewa kudi,aqalla ita kanta batasan nawa ta kashe wajen siyan kayayyakin ba,gaskiya ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa,bataga uban wanda ya isa ya hanata shigar datayi niyya ba cikin gidan,wannan shine babban abinda zata daina suyi galaba muraran a kanta,ba shakka dole ta rage mishi son yaran nan ba,idan ba haka ba ita za'a cutar da yawa,kuma akwai dambarwa ba 'yar qarama ba,amma a fili saita cuno baki
"To naji" kai ya girgixa cikin mamaki,wasu lokutan halayanta kanyi kamanceceniya dana mmn ummi,mmn amir ce mace daya tak dakan saka gwiwoyinta a qasa ta bashi haquri a duk sanda tayi masa laifi.


Da wannan tasamu tasha kanshi,komai yawuce,don dama shi bamai daukar dogon fushi bane ko a baya,idan yayi dogon fushi to tabbas ka qureshi ne.


**** **** ****** *****


Washegari hakanan badon taso ba tatashi da wuri ta dafa mishi shayi da chips,kamar xata fadi haka ta dinga ji saboda tashin wurin datayi,haka ta dinga aikin takaici nacin ranta,saboda tariga ta saba a gida bata tashi a irin wannan lokacin,suma sun sani ba'a tashinta sai sanda taci baccinta ta gyatse,ko aiki zaiwa mamanta kanta kuwa ba ruwanta,idan ta tashinma batason aikin wahala,zata karbi aikin da zatayi daga zaune ne,shima idan yadauki lokaci saita kawo wani uzurin da zata aje aikin ta barshi.


Bayan ta sallameshi saida ta koma takwanta din kuwa,bata tashi ba sai bayan goma na safe,yara tuni sun soma jin yunwa,tadora shayi a gurguje ta dora musu indomie,ta jibagata ta sauke sannan tashiga sharan gidan,wanda kafin tagama ta jigata ainun,haka ta dinga qorafi da surutai ita kadai,yaran kuwa duk wanda yayi kuskuren yin wani abu ba dai dai ba zaici gyatumarsa.


Mmn amir ce data fuskanta tayi hikimar tattare yaran a dakinta,don tasan tabbas idan mmn ummi ta fuska ta to yauma sai an raba abun fada,itakuwa sam batason tashin hankali,uwa uba kuma tasan hankalin jibril xai tashi fiye da jiya,abinda ita kuma bata fata kenan.


Haka taci gaba da karbar aikinta harna tsayin kwana biyu,wanda kafin sannan ta jigata qwarai,ta zaci abun akwai sauqi bata tsammaci haka ba,randa zata sauke girki tanason ta huta amma tana tsananin kishin miqawa mmn ummi jibril,babu yadda ta iya haka tasaki mmn ummi ta kama,saidai taci alwashi itama kafin mmn ummin tafita saita baro musu bacin rai.


Tunda gari ya waye ranar da zata karbi girkin take cikin walwala da farinciki,bini bini minti daya biyu kaji ta saki waqa wadda ke cike da habaici da baqar magana,sosai ran rufaida yabaci don ta gama yankewa da ita mmn ummi take,tayi qwafa ta quduri abinda zata mata ta huce yakai sau shurin masaki.


Mmn amir kuwa batasan ma me suke ba,tana kwance abinta tana duba wasu daga cikin litattafan marubuta masu ma'ana,sosai takejin dadin karatun,don tana qaruwa da abubuwa a ciki ba kadan ba.


Bayan yagama shirin fitarsa daga dakin rufaidan,yasoma leqa mmn amir din,tana zaune tafito da duka kayanta tana gyarawa da safen kasancewar bata da wani aikin yi,lemon siyarwar ma ta dakata dayi harsai ta sauka,sai ruwan pure water kawai da take saidawa yanzu,tanason bayan tasauka dinne tasake fadada sana'artata,ta qara wasu kalolin lemon da sauran abubuwan sanyi nasha.


Jin shigowarshi yasanyata fitowa falon nata
Kamar koyaushe suka gaisa ya tattambayeta jiki tace alhmdlh
"Idan nadawo ku shirya zamuje mu dubo hajiya bata jin dadi"
"Ashasha,me ya sameta?" Ta tambaya cikin nuna damuwa
"Ciwon qafarta ne yatashi"
"Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bata lafiya"
"Amin ya rabbi" ya amsa yana sanya hannunshi cikin aljihunsa.


Dubu guda yaciro
"Kekam kawaicinki kamar yaso yayi yawa"batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,kana tace
"Name fa?"
"Indai ba asibiti zakije ba,ko kin qure da yawa bazaki bude baki kice bbbn amir bani kaza ba,yanzu yadda baki girkin nan baki samun 'yar biyar da 'yar naira goma ya kenan?" Murmushi tasaki kawai ta kada kai,babu mutumin da zaice baison ace mishi ungo,to amma idan ya kasance bake daya bace wajen miji,sa'annan bani baninki tayi yawa to babu shakka zakifi kowa baqinji ne a cikinsu,bugu da qari Allah S W T ne kadai baya gajiya da roqo,wannan shine cikakken alfanun sana'a a wajen diya mace.


"Baka ganin ina saida ruwa da lemo?" Ta fada a tausashe
"Ah,kice hajjaju ce nan a gabana" yadda yayi maganar saiya bata dariya
"Duk da hajjajun ce dai ungo amshi wannan ki riqe,don nasan lalurorinku na masu ciki,kar a je a rugurguje ribar da jarin duka" hannu biyu ta amsa zata karba tana godiya saiga rufaida tashigo.


"Idan kagama inada magana" ta fada idanunta akan kudin hannun mmn amir da take niyyar ajewa,wani takaici ya kamata,ai ita datake kan ganiya ita yafi cancanta yadauki kyauta irin haka ya bata,wayasanima ko kullum sai ya bata?,shi yasa baya fashin shiga,kuma dakinta kullum yake fara shiga
"Ganinan zuwa muje" ya fada yana nuna mata hanya,yadda bata kula mmm amir din ba itama saita sake tsumewa,tayi kamar nata ganta ba,tunda aqa'idance ita yakamata tasoma gaidata,na farko ta girmemata a wajen miji,nabiyu kuma har dakinta ta taddata
"Shikenan saina dawo"
"Allah yatsare" ya amsa mata kana yafita.


Yana fitowa sukayi kacibus da mmn ummi wadda aketa gyare gyare tun safe za'a karbi miji,yayin da rufaida ke daga kitchen tana diban abincin kari,saidai duka kunnuwanta na tsakar gidan,gaisawa sukayi itama sannan yamiqa mata kudin cefane,ta amshe cikin walwala ta rakashi da addu'o'i,kana itama yashaida mata zasu duba hajiyan idan yadawo,wani murmushi rufaida tasaki,anzo wajen,plan dinta zai tafi dai dai kenan
"To Allah yakaimu" ta amsa ba tare data tambayi me zasuje yi din ba.


Fitowa rufaidan tayi daga kitchen din,itama gaya mata yayi
"To" tace kawai itama tayi gaba,ganin batayi magana kan nemanshin da tace tanayi ba saiya sanya kai yafice daga gidan,yayin da rufaidan tawuce dakinta tana waqar
"Ahayye sama ruwa qasa ruwa..." Tana wassafa tsiyar da zata tsula anjima.


*kuci gaba da haquri dai,duk sanda kukaji shuru ba shakka wani babban uzuri ne ya kawo tsaikon,sannu sannu bata hana zuwa,jigon ko manufar labarin dai daukar darasi da koyi da kyawawan halayen ciki*.....[10/3, 3:01 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA HUDU*





Sannu a hankali rayuwa tacigaba da garawa tsakanin wadan nan mata uku masu mabanbantan hali ra'ayi da kuma alqibla qarqashin inuwar miji guda daya,wanda ya koyi darasi daga kuskurensa nafarko daya tabayi a yanzu yake ganin ya gyara komai ba tare dayaci tura ba,saidai hausawa nace,tun ran gini tun ran zane,yariga daya dora maryam mmn ummi akan keken bera,ta sangarce ta tsammaci daga ita yarufe qofa,babu wata diya mace dazai sake aura a matsayin mata,tayiwa mmn amir duka cin kashin dataga dama,ta manta da cewa duk jisan jifa qasa zai fado,hakanan idan gemun dan uwanka yakama da wuta to sai kayi gaggawar shafawa naka ruwa,babu burgewa ga mace tashigo tasamu 'yaruwarta cikin halin qunci da matsantawar miji tabuga tsalle da shewa taga saboda ita yake haka duka,a'ah fa,kamata yayi idan kemai zurfin tunani da hangece kiyi tunanin gobenki,kiyu tunanin ya zata kasance a dake duk sanda kika bude idanu kika ganki kan bigiren da ita waccar take?,ya zata kaya ke dake din?.


Wannan dalili na tunanin itace zata kulle mishi qofa yasanya duk sanda tabude idanu taga rufaida ranta ke bala'in baci,ta gaza boye kishinta,ta bada dukkan qofar raini,takuma bawa rufaidan gudunmawa wajen karantar abinda kw tunzurata da bata mata rai,ta bawa wannan bangaren himma.


Ta sashin rufaida kuwa duka yadda ta tsammacin abun sai taba wankin hula yana neman kaita dare,waishin ina duka tarin kalaman soyayya qauna lallabawa da bbn amir yake mata a waje?,ina duka tarin kalaman idan bake ba sai rijiya dayasha furta mata?,ina kalaman kinfi sauran mata suka maqale?,ina kambamatan da yakeyi?,ina dukka kudi da yake bata?,kanta yakan daure tamau da mamaki,kada dai ace *HANGEN DALA* take irin na wasu 'yammatan wanda hausawa sukace *BA SHIGA BIRNI BACE?*,sam ko daya ba zata yarda tayi faduwar baqar tasa ba,qudurinta ko daya ba zata yarda ya salwanta ba,idan kuwa tabari haka ta kasance to tamkar ta zama lusara kenan,meye amfani meye kuma ribar auren me mata kenan?.


Ta sashin mmn amir kuwa tsuntsu biyu ta jefa da dutse guda,tafiyar yaranta zuwa gidansu ba qaramin taimaka yayi ba wajen bata sarari da damar tsara doro da bigiren da zata dora rayuwarta akai,ta sake karanta da kuma hasashen yadda rayuwar gidan zata iya tafi mata nan gaba,ta shiryawa komai bisa tsari da hikima irin na nagartattun mata masu tsaftataccen kishi,dimbin wayo da siyasa.



Ta bangare guda kuma kosau daya batayi wasa da addu'a da gayawa Allah yadorata kan dukkan wani wanda yake qin jininta ba,ya hasakakata idanun maigidan fiye da kowacce mace,ya sanya mata kwarjini da hasken fuska,lokaci lokaci takanyi waya gida tasa ayi wake da shinkafa koda nacij mutum biyar ne tace ayi mata sadaka.


Ta gama dukkan wani shirinta na haihuwa,ta karbi adashinta wanda tayi da ribar sana'ar da takeyi ta hade abinta tsaf,abinda duka bbn amir din yaga dama yayi mata bata da kaico,tunda tana sana'arta ta gama nata shirin,saboda batason cikin mata uku tafita zakka,ya zamana tahadu da tambarin bani bani wadda ke karya qima da darajar mace,ya kuma gusar da dukkan soyayyar mace a zuciyar mijinta,musamman a wannan zamanin da talauci yasoma qwanqwasa qofar jama'a da yawa,wasu mazan kuma zukatansu suka mutu,har wasu daga ciki suka yanki tikitin nade hannayensu matansu su dauki nauyin kansu su dauki nasu nauyin sukuma dauki nauyin 'ya'yansu dukka a kafadarsu.


Raunannar kafada da annabi yace a killace,a tausaya musu,sa'annan yabada lambar yabon zamantowa mutum mafi alkhairi matuqar iyalanka suka maka shaida da cewa kaine mafi alkhairi a wajensu.


Duk da tasan ba haka jibril yake ba,tunda mutum ne jajirtacce,mai qoqarin sauke dukka nauyin dayahau kanshi,saidai Allahne kadai baya gajiya,kuma shine kadai baya buqatar taimako.


*BAYAN WASU LOKUTTA*



Satittika qididdigaggu suka rage ma haihuwar tata,wanda tasan cewa tazarar dake tsakanin haihuwar da babbar sallah ba yawa gareta ba.


Yau ya kama ranar girkin rufaida ne,ta gama abincinta yadda tasaba wanda yazama alaqaqai ga jama'ar gidan da basu saba cinsa ba,bayan kaiwa dare da takeyi sai tsabar kura kurai cikin girkin nata,wanda kosau daya ita bata ganiba bare ya dameta tayi qoqarin gyarawa.


Qarfe bakwai na dare wansa tuni an idar da sallar magariba,dai dai lokacin da mmn amir ke zaune saman abun sallarta wadda ta gamafa azaune tana jan carbi,tanabin dakin nata da idanu tana duba meye bata hada ba.


Kayanta take kwashewa a hankali a hankali cikin satin tana dauresu waje guda ba tare da kowa yasan ma me yake gudana ba cikin dakin sakamakon sabbin kayan daki da zata sauya na haihuwarta,wanda wani cikin kudinta ta bayar,wani kuma lokacin bikin rufaida da bata siya komai ba ta adana abinta ta hada,cikin sati mai zuwa takeso a kawo mata takintsa komai koda haihuwar zata iya zuwa mata kafin cikar EDD dinta.


Sosai tasake sauya salonta,tasake zama mai sirri sosai fiye da sanda suna zaune ne itada mmn ummi,saboda ta karanci rufaidan macace mai shegen sanya idanu da bin qwaqqwafin abinda bai shafeta ba,shi yasa data karanci haka tasha maganin zama da ita,duk qwaqwwafinta sai mmn amir din taso take gane wani abu tattare da ita.


Sallamar mmn ummi yasanyata daga kai ta amsa mata tana dubanta,saitaga itama hankalinta naga dakin,da alama tana mamakin yadda komai yake a hargitse wani kuma hade waje guda.


Tana qoqarin zama bayan ta ture kayan tace
"Yausje kikayi wannan aikin mmn amir?,ko alama banji motsinki ba" murmushi tasaki kawai tana shafa addu'a
"Kinacan kina fama da yara"
"Mtsweew,wallahi bari kawai,kekam gashinan kin huta sosai abinki,babu mai saki bari bari"
"Wani satin suma zasu dawo ai,don na fahimci karar babansu tasona qarewa yasoma qananun qorafi"
"Yanzunma shi yace namiki magana yanason ganinmu"
"To Allah yasa lafiya"
"Da alama" tafada taba miqewa
"Yanzu zan fito" ta bata amsa bayan ta yunqura tamiqe,fitowarta kenan daga wankan dare,saita sake shigewa uwar dakin nata ta laluba kayan da zata sanya.


Duk da tsufan da cikinta yayi da rashin girki da batayi amma bata yarda tana zama haka wargazaza ba,shi yasa idan ba sanin mai tsohon ciki kayi ba kazo ka sameta a zaune haka zaka tsammaci ba ciki gareta ba,don hatta da jan lalle ciki baya hanata bare kitso,tariga tasaba ya zame mata jiki.


Doguwar riga tafitar ta wani yadi mai taushi ruwan hoda maidan turuwa wanda yahaska chaculet colour fatarta wadda tasake kyau saboda yanayin ciki,duk da dama kalar fatarta haka take,ko sau daya bata taba gigin gwada sanya mata man qara haske ba wato bleaching,bata da ra'ayi ko kadan,masu yima qyanqyami suke bata,dalili kenan daya sanya ba kasafai tafiya cin abincin rufaida ba,don tana taba shafa man duk da fara ce amma hakan bai mata ba.


Gashinta mai tsaho da laushi irin na baqaqen fulani ta tajeshi ta daureshi da qaramin ribbom tashafeshi da mai,ta maqala qananun dankunne fashion sannan tafeshe jikinta da turare bayan ta mutstsike jikinta da kuallacture mai qamshi,dauri tayi sosai daya sakeyi mata kyau tafito haka ba tare data damu da yafa mayafi ba.


Sanda tashiga yanacin abinci,idanunshi kanta yana sakin murmushi,hakanan duk sanda yaga haliman yakejin wani kwanciyar da nutsuwa na saukar masa,baisani ba ko tsananin biyyayarta da rashin sin hayaniya da rashun shiha duk wata kwaramniya ko tashun hankali shiya haifar da hakan?,rufaida na daga ciki bedroom din,a nutse tasamu waje tazauna tana ambatar sunan Allah
"Sannu halimatussadiya" myrmushi ya qwace mata,cikin fara'a tace
"Kai za'a yiwa sannu da kwaramniyar neman halal,Allah yasaka da alkhairi,yarufa mana asiei duniya da lahira" addu'ar ta masa dadi sosai,duk da cewa ma'abociyar addu'a ce ita
"Ameeennn ya rabbil izzati,Allah yayi albarka" ta amsa mishi da amin,dai dai sanda rufaida tafito daga dakin,sanye take da wando lages da riga tshirt wadda tadan sauko kadan,kanta sanye da hula data dace da kalar kayanta,fuska ta tamke tsam ganin suna magaba da juna da alama tattaunawa suke,hakanan tatsani taga yana hira da mmn amir din,wani lokaci harta gwammaci yayi da mmn ummi,saboda itadin batasan wanne malamine yake mata aiki ba,duk qanqantar magana sai taga tana tasiri har zuciyar jibril din,yanzu haka idan ba'ayi sa'a ba har gari yawaye yana cikin walwala,ko kuma yadauko wani labari na abun alkhairi data taba yi masa yahau bata,tayi fushin sunyi fadan yafi sau a qirga amma ya kasa dainawa,ta fuskanci wani lokaci ma baisan yasako mata zancanta ba,kamar ana tsirarsa yayi maganarta.


Bata taba tsammanin akwai wani abu da zatayi shakkarsa ba game da matar,amma yanzu tana shakka dari dari da tunani kan idan ta karbi girki kuma ya lamarin zai kaya?,tunda gashi yanzun ma suna nesa nesa da juna amman haka na kasancewa?,inaga ta shigo turaka?.


Har yau ta rasa meye yake baiwa mmn amir din haushi,canki canka take,ta gwada duk wani abu dake baiwa mmn ummi haushi akanta amma bataga wannan fushin ba kan fuskarta bare akai ga tankawa,hasalima ba wata hira suke tsakaninsu ba,sai magana ta kama sannan take hadasu,sai kuma gaisuwa da sallama,amma ba zata iya tuna sau nawa tazauna hira ba tsakaninsu,sabanin mmn ummi wadda da wuya rana tafito ta fadi basuyi 'yar tankiya ba.


Kawai saita gwada sarar zama tasanya hannu cikin kwanon bbn amir itama tasoma cin abincin bayan tayi bake bake a gabanshi.


Itama macace kamar kowa,kishin hakan yataso mata,amma saita tuna cewa ba haramci rufaidan ra aikata ba,bugu da qari kuma itama matarsa ce kamar yadda itama take,don ita kanta tare suke cin abinci a sanda take girki,don haka saita soma furta YAHAYYU YA QAYYUMU BI RAHMATIKA ASTAGIS,ASLIH LI SHA'ANI KULLAHU,WALA TAKILNI ILA NAFSI DARFATA AININ,A'UZU BULLAHI MINASHSHAIDANIRRAJIM,hakan ya hana komai yin tasiri saman fuskarta,saima ta sanyo musu hira sukaci gaba dayi.


Sosai hirar ke sukar zuciyar rufaidan,cin abincin dai kawai takeyi,uwa uba ga turaren mmn amir din saya dumame falon nashi,wanda takejin kamar tatashi tafidda ita daga dakin,tun wata rana da wani abu yafaru tasake tsanar turaren.


Ranar taje gida,sai aka kawo mata kaya gugarta,mmn amir din ita ta amsa,mai wankin yace abashi dankwalin daya daure kayan a ciki,hakan yasanya bayan tabashi tasaka nata dankwalin tadaure mata,data dawo tasa mubarak yadauka ya miqa mata,ta amsa tadora saman kujerarta.


Ranar ita keda girki,bayan baban amir yadawo yazauna kan kujerar da kayan suke,kusa dasu yana danne dannen waya,tunda yazauna qamshin yadinga kai mishi ziyara,saiya daga kai koya waiga kadan kana yaci gaba da danne dannensa.


Dai dai sanda tashigo taji yace
"Haba,nifa ince" ta qaraso wajen tana tambayarsa
"Mefa?"
"Daa har zance ina kika samo irin turaren halima,ashe dankwalinta ne kusa dani" sak kawai ta tsaya tana dubanshi cike da kishi,shi kuwa baima kula ba yaci gaba da abinda yake,take ta warware dankwalin tacire kayanta,tafita tsakar gida saman igiya ta dora mata,sai data fito taganshi kana tadauki abinta.


Babu jimawa mmn ummi tashigo,daidai sanda yagama cin abincin yagyara zama yana dubansu
"Yauwa,inaso kubani aron hankalinku nan....dukkaninku nasan cewa kun sani halima da maryam,lokaci iwar haka na gabatowar babbar sallar cikin taimakon Allah nasiya abun layyata da kuma sitturunku kuda yara,to wannan karon al'amuran duka sunzo sai addu'a" shuru yadanyi kana yadora
"Duk da banso gaya muku ba,to amma kudin iyalina ne da babu wanda yakaiku kusanci dani,dadi da wuya ya kamata ace kunsani,na tattara kudaden hannuna da kudaden dakayan da muka siya a shago na bayar za'amin sari,to cikin hikima ta ubangiji jirgin ruwan daya dauko kayanmu igiyar ruwa takadashi wani waje wanda ba'asan nahiyar da yayi ba,kusan har yanzu babu labarinsa,duk sa cewa ana nan ana bincike to bazamu cire rai ba,saidai muyita addu'a da fatan Allah yasa muna da rabo".


Cikin tausayawa mmn ummi ke kallonshi,ba shakka taga damuwa sosai tatare dashi,har tayanke tsakanin yau da gobe tatsaya ta bincika jin yaja bakinsa yayi shuru,ba shakka asara ba qaramin abu bane,kota sile biyarce bata da dadi bare ta maqudan kudade haka
"Subhanallah,ya salam,amma bbn amir shine kayi shuru da bakinka muna zaune abinmu munata walwala bamusan halin da kake ciki ba?"cewar mmn amir kamar zatayi kuka,don abun ya tabata,tasan cewa ba qananun kudi yazuba,tabe baki rufaida tayi,cikin zuciyarta tace
"Makira,indai pritending din nan ne kowa aiya iyashi,yau zakiga aikin makirci" murmushi baban amir din yayi,harga Allah yana yabawa da yadda take damuwa da lamuransa
"Banda abinki idan na fada aiba magani zaiyi ba,saima saku damuwa da zaiyi,musamman ke da kike wannan yanayin"
"Amma atleast ko a addu'a ma sanyaka ko?" Kaiya jinjina
"Gaskiyane,da wanann don wannan,to amma yanzunma ba'a makara ba aiko?"
Kaita jinjina
"Hakane,ubangiji ya bayyanasu cikin aminci,yasa rabonkune,yakaresu daga dukkan abinqi"
"Amin summa amin"
"Tofa,ana wata ga wata,to Allah ya bayyana" inji mmn ummi tana sanyawa ummi mama a baki,ta soma saqa tunane tunane iri iri a ranta.


Rufaida kuwa saitahau salati tana matsar hawaye,wanda hakan yaja hankalinsa zuwa kanta
"Yanzu dama a wanann halin kakeciki amma ba wanda yasani,ya Allah yadubeka,ga nauyin iyali gana iyaye,gashi kuma kowanne saikayi babu mataimaki sai Allah,ga hidima kala kala a gabanka" murmushi yasakeyi
"Babu komai,ai Allah yana tare da bawa kowanne lokaci,hidima kuwa wadda tasamu ai ita za'ayi,wadda tazama wajibi ba mustahabbi ba,shi yasa ma na taraku na gaya muku,wannan karon saidai kuyi haquri da layya,hakanan suma kayan salla,amma su kayan suna kaina in sha Allahu,da zarar komai ya warware zan biya bashi".


Ai gaba daya sai wutar rufaida tadauke,tashin hankali,wannan wanne irin bala'i ne?,ita da taci burin wanna sallar?,qawaye da 'yan uwa za'azo aci a raqashe a gidanta itama tayi aure?,sallar saura sati uku amma harta lissafa ya kama ranar suyar hanji da washegari duka ran girkinta ne,tabdijan.


Ta fannin mmn ummi ma sakato tayi tanajin wani dan takaici takaici na tabata,duka lissafin bogi da tayi zata qara ma bbn amir din kan qunshi da kitso da kudin dinki ya tashi kenan
"Haba bbn amir,ko wanda baisanka ba yaji wannan aiya sauke maka komai,bare mu da muke masu rufa maka asirine,shekara nawa ana abu,don yanzu kawai Allah yakawo wata lalura harsai ka taramu kabamu haquri?,kayi fata kawai Allah yawarware ya tsaga da rabonku koba haka ba?" Ta fada tana dubansu mmn ummi,don ita a tsammaninta suma haka yake cikin zuciyarsu
"Hakane" mmn ummi tafada a taqaice,rufaida kuwa kai kawai ta gyada na ganin ido,ji take kamar ta shaqo mmn amir tayita zabga mata mari,kawai don ya fadi hakan babu wannan dan boren ma na yayi qoqari yanemo saita wani kama ta sauke masa?,koda yake itace a cikin ruwa zundum ita da zata haihu,billhillazi sai tafi kowa jigata,itakam kod yage da fige saita samu wani abu jikinsa,bacin ranta kawai ace tana cikin amarci wai ace gidanta ba'ayi layya ba?,wannan shine babban tozarci,bayan ya gama sanya mata rai tun tana waje,ta gama baje lissafi,saboda ta sani dik shekara gidansa sa yake yanka musu,ita kuwa ba wanda yake najikinta sa baisan da wannan ba tun kafin suyi auren,don kasonta mai yawa yake kaimata a lokacin.


"Shikenan,na gode qwarai da fahimtata da kukayi,Allah yayi muku albarka yasake hada kanku,yakuma hore kafin sannan ayi duk abinda ya kamata"
"Amin amin" suka amsa kowa da abinda ke qasan ranta,kana yasallamesu suka tafi.


A daki mmn ummi haka abin yadinga mata qwaqur qwaqur arai,tadinga juya zancan cikin ranta,hakanan tadinga zancan zuci ita daya.


Ta fannin rufaida kam tsaf walwalarta ta janye,harya lura da haka,daya tambayeta tace kanta ke ciwo haka suka kwanta,saidai kafin bacci yadaukesu yajiyo maganarta
"Amma banda sakaci da wasa da dukiyar mutane jirgi sukutum da guda ace wai an rasashi ya harba wani gun?" Ya zaci zancanne yadameta kan asarar da suke gab da tafkawa,saiyace da ita
"Eh,hakan na faruwa idan ruwa yayi yawa,amma idan akwai rabo saikiga Allah ya bayyanashi"
"To Allah ya bayyanashi kafin nan da sallah,koda irin sallah saura sati dayane,komai ai zai iya warwarewa,saboda sallah ba layya aisai aslow" shuru yadanyi yana son shinshino inda ta dosa,sai kawai yabita da amin,saboda yanzu shiba wannan ne duka agabanshi ba.


******* ****** ********



Sati guda da faruwar hakan aka kammala mata duka kayan gadonta harda kujeru da showglass,sallah saura sati daya kenan,tayi waya aka turo mata salima da khadija da kubra 'ya'yan qanwar innarsu sukazo suka tayata aka shirya kaya komai tsaf dashi,tsaffin kayan saita maida dakinsu amir wadanda ranar suma aka dawo dasu gida gaba daya.


Tunda aka shigo da kayan rufaida tagansu ta kasa zaune takasa tsaye,bacin rai kamar tasanya kuka,wato munafurtarta bbn amir yayi kenan?,yace babu kudi ga asarar da suke shirin yi amma ya narka mata kayan daki haka.


Bata iya jure bacin rai ba,saboda haka tadauki wayarta tahau kiransa,saidai ta buga babbar rashin sa'a duka layukansa switchoff,takai takawo cikin daki ita daya bacin rai yacikata,tanajiyo hayaniyarsu ita da yara da yammatan dake tayata aikin amma ko leqe,saima tasake sakin labule tunda dama girkin mmn ummine,don dole datagaji dakai kawon takwanta saman kujera taba wassafa yau tashin hankalin da zasuyi dashi,don wallahi da sake an baiwa mai kaza kai,wannan rashin adalcin dame yayi kama?,ya zagayesu yaje yamata kaya saboda zata haihu?,watafi cikin haihuwa,hakanan dai tawuni ita daya baqinciki fal zuciyarta.


Ta fannin mmn ummi kuwa duk da tasan cewa kudinta ne na sana'a da wadanda batayi hidima dasuba auren rufaida amma saidataji ranta yasosu,duk da ta dake tanata yaqe,takuma leqa dakin taga kayan,amma sai taji duk ta quntata,hakanan nata kayan dakin saita rainasu,taji itama babu abinda

Please Login or Register in order to submit comment