Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki ta ta6e, dan hakan bai dameta sosai ba, ayanzu burin gyara rayuwar d'anta ne a gabanta, dan nan kusa take buk'atar dawowar mulki hannunsa, tunanin yanda zatai da Abdulsalam ne ya darsu a ranta, dolene ta san yanda zatai.




Nace, "turk'ashi, wannanfa shine ga akuya ga kura🤭🚶🏻♀".







***************
Ayusher 27
***************


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*


{28}


Bude idanunsa yai a hankali ya daurasu akan Azi dake durkushe a gefensa, Littafin dayake nazari na hannunsa ya kulle.

Azi yai murmushi yace "yauma bazaka fita bane?"

Junaid ya kalleshi yace "zuwa yamma."

Azi ya jinjina kai cikin gamsuwa sannan ya mike, haryaje kofa ya juyo ya kalli Junaid, Junaid ne ya kalleshi kallo mai dauke da tambaya.

Azi ya kara rusunawa yace "Binta fa ta zama 'ya, jiya dana ganta, da alama Gimbiya ta zareta daga gun bayi."

Kai Junaid ya jinjina bai ce komai ba, Azi wanda ya fahimci jin dadin Junaid ya fita daga falan.

Shiru Junaid yai a hankali kuma wani lalausan murmushi ya zagaye fuskarsa, baiyi niyyar fita ba saboda yana jiran aike daga bangaren Mai Martaba sai dai jin haka yasa ya mike.

Ciki ya shiga ya fara shirin fita, harya gama shirya wa sai kuma ya koma ya zauna.

************

Kallan Barira tai tace "Anji daga gun Junaid?"

Barira tace "tuba nake ranki ya dade amma haryanzu ba labari."

Shiru Azeema tai, tace "Binta fa?"

Dazu wai zata fita, Azeema ta kalleta tana mata alamar ina?
Kai Barira ta girgiza tace "bansani ba Gimbiya."

Shiru Azeema tai tana dan kada hannunta, badai dan ta bata matsayin 'ya ba take neman zagayewa ta dinga zuwa gun Junadi ba tare da saninta ba?

**********

Mikewa naga ya sake yi sannan ya fito daga cikin dakin nasa, da sauri Azi ya matso yace "Yarima zaka fita ne?"
Kai Junaid ya daga cikin kasaita ba tare da ya amsa ba.
Da sauri suka matso dan yima Junaid rakeyi.

Zeena wacce ta nufi bangaren Junaid ce ta tsaka cak, daga nesa wanda akala yakai taku goma sha biyar tsakaninsu.
Itama ja tai ta tsaya daga inda take.

Zeena ranta yakai matuka gun baci, tun daga sama ta kalleta zuwa kasa, da alama kenan ta fita daga matsayin bayin da take?
Cikin isa ta daga hannu tayima Binta alama da ta zo.

Binta ta kalleta sannan ta karasa inda take.
Wani banzan kallo ta sake mata sannan tace "daga ina?"
Binta ta kalleta tana tunanin wannan tambayar fa?
Zeena ce ta katseta da cewa "ina zaki kuma? A iya sanina kin bar bangaren Ya Junaid."

Binta ta dago ta kalleta sannan tace "zanje gun Harira ne."

"Harira? Wace kenan?"
Shiru Binta tai ganin batasan me zata ce ba, Zeena jin bata tanka mata ba yasa tace "banaji dai mace wacce tasan mutuncinta zata dinga zirga zirga bangaren namijin da batada alaka dashi ba."

Binta ita kanta batasan sanda ta kalleta ba, hatta Fure sai data guntae dariyar data taso mata.

Ganin yanda Binta ta kalleta ne ya harzako Zeena dan dama neman abinda zata mata takeyi, Binta bata nufa ba taji an wanketa da mari.

Kallanta tai cikin tsananin mamakin laifin datai, Zeena tace "me? Zaki rama ne?"

Binta tai shiru, ke yanzu in har kinada hankali ba tattarawa ya kamata kiyi ki dau kafafunki ki koma mahaifarki ba?

Binta yanzu kam ta fara zargin san shi Zeena takeyi.

Junaid wanda ya fito yana tsaye daga bayansu yanajin abinda ke faruwa, ransa yakai matuka gun baci duk da a fuskarsa bazaka gane ba, Binta ce ta dago zatai magana ta ga Junaid, ido ta kuramai ta kasa cewa komai.

A kufule Zeena ta juya dan taga meke faruwa, Junaid suka gani a tsaye yana kallansu.

Gaban Zeena ne ya fara dukan uku uku, wanda idanunta suka firfito waje, a hankali cikin kasaita da takama ya fara taka kafafunsa zuwa inda suke.

Binta kam kallanshi kawai take gaba daya ya canza, ya sake kwarjini, dama haka Junaid yake ko dan ya dawo inda ya dace dashi ne?

sauke idanunta tai daga kansa ganin ya nufo daf da inda suke, Zeena a rude tace "Yaya."

Kallanta yai yace "Zeena? Me kikeyi a nan?"

Ta kalleshi cikin fargaba tace "dama nayi tunani zuwa ne gunka."

Guna?"
Kai ta daga,yace "me kike anan to?"

Kallan Binta tai wacce ganin bai kalleta ba yasa gaba daya taji kafafunta sun fara rawa.

Idan na kasa dake ya miki laifi me zai sa ki kaskantar da kanki a ciki mutane?


Mamaki ne ya kamata ta kalleshi da sauri, Binta kam gaba daya jitai kanta ya fara wani sarawa, juyawa yai zuwa bangarensa, Zeena ta kalleta ta dafa kafadarta tace "dan an sa saban kaya ba'a canza asali."

Tabi bayansa, Azi kam wannan lamari shi kanshi ya daure mai kai, meke faruwa?

Suna shiga cikin falansa kallo kadai yama Azi, suka bar falan dukansu.

Yana tsaye dama bai zauna ba, ita kanta Zeena a tsaye take, cikin salo tace "Ya Junaid."

Bai juye daga inda yake ba yace "ke kika nemi hadin aure tsakani na dake?"

Gabanta ne ya cigaba da faduwa, ta rasa me yasa yau take jin shakkar Junaid haka.

Juyowa yai ya kalleta sai kuma taga ya saki wani murmushi wanda ya kara sata cikin wani yanayi.

A hankali ya tako zuwa inda take yace "me? Bake bace?"

Kallansa tai idanunta duk sunyi jaa, kai kace marinta akai, a hankali tace "nice."

Murmushi ya sake yi yace "kinasona da har kike tunanin zaki jure duk matsalar da zata fito ta bangaren Hajjo da Ummana?"

Yawun bakinta ta hadiya sannan tace "Eh."
Yadan jinjina kai a hankali yace " hakan yayi, sai dai in har kinaso na aure nima sai kinbi sharadi na."

Sharadi?
Ta fada a dan tsorace, yace "eh sai dai in zan aureki tare da kawarki."

Kawata?

Cikin mamaki tai tambayar, yace "wacce kuke hira da ita a waje dazu, na tabbatar yanda kike yar sarki bazaki daga hankalinki akan hakan ba."

Rainin wayau, bayan yasan abinda sukai a waje harya tambayeta yanzu kuma yazo mata da wani rainin hankali? Wai kawarta? Sannan me? Ya hadasu da wannan yar iskar da ba'a ma san tsatsonta ba?

Junaid ne ya kalleta yace "kina so ki aureni wannan ce kadai hanya in kuma baki amince ba kowa yasha zamansa."

Shiru gai tama rasa ta ina zata fara kamo abinda ya kamata.

Junaid yace "ki sanar da Mahaifinki haka dan nasan zai kira ya tambayeki, in kuma baki amince ba kowa yasha zamansa."

Yana kaiwa nan ya fita daga falan ya barta a tsaye kamar gunki.

Binta kam kasa ma shiga gun Hari tai tana tsaye a gun kamar wacce bata numfashi, abun daya faru sai kara dawo mata yakeyi.

Ganin Azi ya fito yasa ta fahimci sune, da gudu tai kwana ta labe, sai dai kafin ta karasa kwanar Junaid ya hangota, tsoransa ma kartaje garin gudu ta fadi taji ciwo.

Haka suka zo ta saitin inda ta boye ya dan kalleta ta gefen ido ya basar, kiyi hakuri Binta idan har banyi hakan ba bayanda za'ai na dawo dake gareni.

Bangaren Azeema ya nufa wacce ganin Junaid baizo ba yasa tasa a kara kiran Jakadiya.

Suna zaune Jakadiya na mata bayani akan binciken da akai, Azeema kowacce aka nuna mata aka mata bayani sai tadan kushe.

Jakadiya tasa dariya tace “Gimbiya taya za’a samu wacce zata dace bayan duk wacce aka baki bata miki ba?”

Azeema tai murmushi tace “bawai basumin bane Junaid dine kamar basu dace dashi ba.”

Barira ce tai dariya tace “A idanun Gimbiya, Junaid ne kadai ya cika yanda ya kamata .”

Azeema ta kalli Jakadiya tace “Me Takawa yake a ‘yan kwanakin nan?”

Jakadiya tace “nikaina bansan meke faruwa ba, da alama wani nazari yakeyi.”

Matsowa tai cikin gulma tana san sanar da ita har Junaid ya kira bayan sun zauna dasu Shammaki aka sanar da isowar Junaid.

Da sauri ta suka tattare Barira ta nunawa Jakadiya hanyar baya ta fita da sauri.

Azi ne ya kalli wacce tai ison ya sake mata alama dan ta sake sanarwa.

Barirace ta karaso da sauri ta bude kofar, sannan ta basu hanya.

Junaid ya shiga ciki, kallan Azeema yai wacce ta gyara zama kai kace ita kadaice dama a gun.

Zama yai ya gaisheta cikin kulawa.

Kallansa tai cikin wani jin dadi tace “Barka da isowa Yarima, har ina tunanin aikawa kazo, ganin kwana biyu banganka ba.”

Junaid ne ya kalleta yace “Tuba nake Umma na.”

Wani dadi ne ya kamata, tace “Ya zanyi, ai ganinka ya wanke komai.”

Murmushi yai cikin jin dadi.

Barirace ta sunkuyo tace “Yarima, Gimbiya ta maida Binta matsayin ‘ya.”

Kallan Azeema yai sannan ya sunkuyo yace “tana godiya Ummana.”

Shikenan? Abinda yazo mata ranta kenan, ganin ba wani farin ciki a fuskarsa yanda ta zata.
Sai dai hakan ya mata dadi ta wani bangaren.

***************

AbdulSalam ne yai shiru, yau ya gama tattare duk wani hukunci da zai dauka.
Shammaki ne ya kalleshi su biyu a cikin falan, yace “Ranka ya dade ka gama tunanin?”

Abdulsalam yace “eh. Dole ne mubi abinda yakeso inhar munasan abinda mukeso ya samu, sannan inhar munaso mu binne abinda yake tattare da rayuwarmu.”

Kayi shawara mai kyau Ranka ya dade, kayi hakuri mu bashi abinda yakeso, ni inaga wahala ma kadai ya isheta a gadan nan da batada kowa.


Kai Abdulsalam ya jinjina yace “inka fita kasa a kira Zeena.”

Nan Shamaki yai sallama, a waje ya bada sakon Takawa sannan ya tafi.

Zeena wacce tunda ta shigo bangaren Hajjo ko kala batace ba, duk kuwa da maganar da Hajjo ta mata bata iya tankawa ba.

Zubair ne ya kalli Hajjo yace “Hajjo kin bincika mai Junaid suka tattauna da Mai Martaba?”

Hajjo ta kalleshi tace “Zubair sau nawa zaka tambayeni ne? Menene matsalar ka ne nikam? Bantaba ganin ka cikin wannan yanayin ba.”

Ya kalleta fuska a kumbure yace “Hajjo bakiga yaran nan bane shi yasa.”

Tsaki taja tace “kaidai kayi kokarin bin karatun ds akema karka kuskura ka bari yaran nan ya sake wulakantani dan wlh bazan taba yadda ba.”

Baki yadan kara kumburowa sai dai baice komai ba.

Harara ta bugawa Zeena tace “Ke bansan iskamci kinshigo ko kala bakice ba.”

Fure ce ta shigo da sallama ta zube tace “Gimbiya Mai Martaba yana nemanki.”

Wani murmushin jin dadi Hajjo tai da alama Sarki ya yanke hukunci akan maganar Sulaiman datamai.

Mikewa Zeena tai kamar mara rai ta nufi kofa.

Hajjo ta sake wani murmushi jin dadi.

Nace Zai zama kuka😂🚶🏻♀

*******
Zeena ce dukufe a gaban Mai Martaba ya kalleta yace “Zeena!”

Kallansa tai tace “Naam Abba.”

Shiru Abdulsalam yai kafin yace “maganar Junaid namai magana.”

Kallansa ta sakeyi sai dai batace komai ba dan ta riga tasan me zai karasa ce mata.
Sai ji tai kuwa yana cewa “Yace inhar zai aureki sai dai ya hada da yarimyar daya taho da ita.”

Shiru tai wanda hakan yasa Sarki yace “Zeena! In kinsan bazaki iya ba ki hakura ki auri Sulaiman.”Yai maganar cikin kakkausar murya dan ya fahimci inya mata lago lago zata lalata komai.

Kallansa tai tace “a’a na amince.”

“Kin tabbatar zakisa Hajjo ta yadda da abin nan?”

Kanta tsaye tace “eh.”

Yace “jarki fadawa kowa maganar Binta, sannan Hajjon ma karki mata zancen ki da Junaid harsai munyi magana dashi.”

Tace to, mikewa tak ta fito gaba daya jikinta ba karfi kai kace wacce ta tashi daga jinya ce.........

Hmmm🚶🏻♀

*******
Ayusher🏌🏻♀


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*


{29}


Zeena tana fita Abdulsalam yai shiru yana nazari, Junaid ya kamata yasa a kiramai ko Azeema?
Dan tabbas yana san al’amarin nan ya faru cikin gaggawa tunkafin Junaid ya gama fahimtar masarautar.

Idanun Junaid ne suka fadi masa a lokacin daya mai zancen indai zai auri Zeena to lalai sai dai ya hada da Binta.
Bari ya shawo kan Azeema ya tabbatar ita bazata taba yadda da wata Binta ba, dole yai amfani da ita.


A daren ranar sarki Abdussalam ya buk'aci ganin Azeema a matsayin wadda zata kwana a sashensa.

Tunda yammaci jakadiya ta Isar mata da sak'on mai martaba.

Bata wani ja lokaci ba ta amsa kiransa itama, dan tanason jin wane zamane yayi dasu wambai kwana hud'u da suka wuce, sannan tana san tamai magana akan auran Junaid da takeso ayi.

Sai wajen tara Na dare ta kimtsa cikin shiri Na alfarma da baza k'amshi, ta d'ora had’ad’iyar alk'yabbarta, barira ce kawai tamata rakiya sashen mai martaba.

Bayan sanar da zuwanta jakadiya tamata iso.

Tana shigowa cikin turakar tasa ya mike a hankali ya tako zuwa inda take.

Azeema ta kalleshi cikin kulawa tace “Takawa!”

Abdulsalam ya mika mata hannunta, hannu tasa ta rikoshi, ya jawota har jikin gadansa sannan ya zaunar da ita akan gado, dagowa tai ta kalleshi sannan tai murmushi.

Zama yai kusa da ita shima sannan ya jawota jikinsa ya rungume.
Murmushi ta sake yi sannan tace “AbdulSalam!”
Bai saketa ba har sai daya biya bukatarsa.
Jawota yai jikinsa ya sake rungumeta, tadan tureshi kadan tace “Menene?”

Hannu yasa akan fuskarta yace “Me kike tunani in muka hada jinin mu aure?”

Jinin mu?
Ta maimaita tana kallansa, kai ya daga mata yace “Zeena da Junaid nake nufi.”

Yanda take kallan kwayar idanunsa ne ya sashi sake cewa “menene?”

Mikewa tai zaune da sauri tace “bangane Zeena da Junaid ba.”

Shima zama yai sannan ya kamo hannayenta yace “badai na tunanin Azeema zataki hada jininta da nawa, dan na tabbatar sirri na nata ne.”

Kallansa tai idanunta cike da tsoro tace “Abdulsalam?”

Yace “me? Ba hakan bane? Na tabbatar duk abinda nai a baya kin sani sannan baki taba furtawa wani mai numfashi ba a doron kasa ba, kinga hakan yasa nasan ni dake sirrinmu na juna ne kamar yadda nima duk abinda ya shafi ki sirri nane.”

Hannunta ta zare da sauri wanda gaba daya taji jikinta yana rawa.

Bakinta na rawa tace “zan wuce bangarena.”
A daren nan? Ya fada yana kara rike hannunta, me kike tsoro? Bayan komai a tafin hannunki yake? Ki kwanta kiyi bacci hankalinki a kwance.

Yanda take kallansa yanzo kallo ne mai cika da shakka.......

Ya d'auke Kai yana wani murmushin k'asaita, yasan wacece Azeema sarai wajen rik'o da ra'ayin kai, amma ya tabbata a wannan ga6ar yamata kamun da bata Isa su6ucewa ba.

Itama komawa tai ta zauna zuciyarta na sake maimaita maganganunsa, dolene tayi hak'uri sai asuba ta koma sashenta tamkar yanda sukeyi, dan inhar takoma yanzu hakan zai d'auki hankalin wasu, duk yanda taso bacci ya dauketa kasawa tai.

Idan ita ta amince Junaid fa? Ko kad'an bataga ta inda junaid ya dace da Zeena ba, sannan tama Yaya jininta zai kasance waje d'aya dana hajjo? Dukma ba wannanba, hajia iya zama ta amincene? Kai, wai miyasa Abdussalam yay wannan tunaninma?....

Wannan tambaya da zuciyarta tai matane ya sakata juyawa ta kalli Sarki Abdussalam dake kwance shima yana kallonta. Murmushi yamata. Batareda ta maida masa murtani ba tace. “Kozan iya sanin dalilinka Na wannan had'in?”

Murmushi yakumayi, sannan yatashi zaune yana matsowa jikinta. “Azeema ki tsaida zuciyarki waje d'aya, kinsan har abada banzan cutar da jininki ba, auren wad'annan yaran shine Makullin sirrinmu, ko kina tunanin duk randa shi kansa Junaid ya san sirrinmu zai d'aga mana k'afane? Bayanann ki tuna inada d'a Zubair, ya girmi Junaid, atunaninki shi mahaifiyarsa batason yayi mulki? Had'in auren Junaid da Zeena itace hanya mafi sauk'i wajen dank'a masa mulki da maganin tasowar duk wata k'ura da muka binne a baya”.

Ajiyar zuciya Azeema ta sauke, tad'an gamsu da jawabinsa, saidai gaskiya batason had'a zuri'a da hajjo, amma tasan matakin dazata d'auka, sannan tana a kan bakanta Na aura masa d'iyar mashahurin sarki.



******************

Washe gari Azeema da kanta ta buk'aci ganin Junaid. Anutse yai shirinsa cikin kayan alfarma, Azi yai masa rakkiya tamkar kullum.

Bayan an masa iso yasamu shiga har cikin k'uryar d'akinta.

A zaune ya isketa tayi shiru dan ko shigowar shi bataji ba tsabar ta shiga cikin tunani mai zurfi, kallo d'aya zakai mata kuma ka fahimci tana tare da damuwa. Da sauri ya k'arasa gareta, “Umma lafiya kuwa?”.

Hannunta ta janye tana sauke ajiyar zuciya, ta kalli Barira dake tsaye a k'ofa. “bana buk'atar motsin kowacce hadima, kowa yaje sai nan da awa d'aya Ku dawo”.

Barira ta jinjina kai da fad'in “angama ranki ya dad'e” juyawa tai ta fita zuciyarta na mamakin minene matsalar uwar d'akin nasu, tunda tadawo sashen mai martaba da asubahi batada walwala.

Azeema ta maida kallonta ga junaid dake durk'ushe gabanta, hannunsa ta Kama tana masa nuni daya zauna sosai. Bai musaba ya zauna, murya a raunane Yakuma mai-maita Mata tambayar d'azun.

Tad'an murmusa domin kauda damuwar fuskarta, “Ka kwantar da hankalinka Junaid, babu abinda ke damuna, yanzu natashi a barcine. Nakiraka ne muyi wata magana”.

“ina saurarenki Umma” Abinda yace kenan duk da bai gamsu ba.

“Junaid me kake tunani akan Zeena?”

Duk da yasan me take nufi amma sai yai kamar bai sani ba yace “Zeena? Me nake tunani kamar ya?”


Ta daure tace “Junaid zaka iya zaman aure da Zeena?”

Cikeda mamaki ya kalleta, ”Umma miyasa kikaimin wannan tambayar?”

“Saboda inason ka aureta”.

Y'ar zabura yai cikeda tsoro dan duk da yasan maganar amma bai kawo har an shawo kanta , ta yaya? Kwana daya kacal? Tabbas akwai abin bincikawa a wannan lamari.

Kallanta yai yace “Umma miya birgeki ga yarinyar data fara tozartani farkon shigowara masarautarnan, ama bar wannan rashin sanine amma gaba daya yarinyar nan batada tarbiyyar data dace, meya birgeki dahar kike tunanin had'a jininta da naki?”

Tambayar ta daki zuciyarta, amma saita danne, cikin dai-daita kanta tace, “Ka d'auki hakan matsayin kuskure Na rashin sani, sannan Zeena batada matsala matsalarta daya rashin uwa mai tsawatar mata.”

Shiru Junaid yai yana nazarinta, lallai zuciyarsa takuma yarda akwai sirrin dake tsakanin sarki da mahaifiyarsa, to amma nami? Miyasa zai zargi mahaifiyarsa da kansa? Ya salam zuciya wannan k'aryane, ummana bazata aikata komai na son zuciya ba duk da bai gama saninta ba amma yana mata fatan hakan............

Tunaninsa ne ya katse saboda dafashin da tayi.

Daidaita zamansa yai ya kalleta bayan ya canza yanayin fuskarsa.
“Zan amince da auren Zeena amma da sharad'in in har zaki amince ku hadata da Binta.”

Wata muguwar zabura tayi tana kallonsa cikeda tsananin mamaki. “Junaid kanada hankali kuwa?”

Murmushi yai cikin wani yanayi mai wuyar fassara yace “Ummana lafiyar d'anki k'alau.”

Bazai taba yiwu ba kai kasan bazan yadda ka auri Binta.

Kallanta yai yace “Na yanke wannan shawaran ne ba dan komai ba sai zargin da nake akwai manufar mai martaba na had'ani aure da Zeena, inhar y'ancinmu kike buk'atar mu k'wata, mulki yadawo gareni kamar yanda kike buri to lallai dolene na had'asu su biyun, inba hakaba zanbi tawata hanyar na bankad'o gaskiya, dan inada abubuwan da ban gansu dasu ba, inason sanin dalilin mahaifina na sakawa a maidani na rayu a ke6antaccen waje bayan yasan mahaifiyata nada ranta......”

Kallansa tai tabbas Junaid jinin Zubair ne wanda ya dace da mulki sai dai in har yayo halin Zubair tabbas ita kanta bazata tsira ba, hankalinta ne ya tashi ta kalleshi tace Junaid Na Neman k'ara Mata zafi akan Wanda sarki ya had'a Mata a daren jiya,

Daurewa tai tace “Amma Junaid hadin auren ba shi bane, yanzu na maida Binta ‘ya, zan samo maka wata ka aura.”

Ido ya kura mata yace “Me kikace a gaba da daraja abu mai daraja?”

Kallansa tai batace komai ba, yace “indai har bazaku amince da hadin auren da Binta ba to nima bazan auri Zeena ba inyaso kowa yasha zamansa.”

Ya fada fuska a hade.

Kallansa tai kanta taji ya fara sarawa, itakam sakayya ce take neman afkuwa da ita.
Mikewa yai yace “in kinyi nazari mayi magana, nabarki lafiya Ummana.”

Shiru tai haryabar dakin, meyasa komai baya tafiya yanda takeso? Haryakai kofa tace “shikenan!”

Da sauri ya juyo ya kalleta, murmushin yake ta kakaro tace “shikenan ka auresu, indai inaso in daraja abu mai daraja dole naso abinda abin da kakeso.”

Jikinsa ne yai sanyi, ya tako a hankali zuwa inda take ya durkusa yace “nagode Ummana.”

Shiru tai batace komai ba...


******
Binta kam gaba daya wani irin zazzabi ne takeji yana neman rufeta, tun abin da ya faru jiya, idanun Junaid take hangowa da yanda ya nuna bai damu da ita ba.


Wasu zafaffan kwala na dana sani ne ke zubo mata, da alama zamanta a gidan nan ya kare.
*****


Zeena kam abincin gabanta kawai take jujuyawa ta kasa ci, kallan Fure tai tace “Fure me kike tunani a kan matsayina gun Ya Junaid?”

Fure tai dariya tace “ai Yarima ya fara fuskartar kedin kece kika dace dashi ko baki ga abinda ya faru jiya ba, kiga yadda ya wulakantata saboda ke.”

Kallanta Zeena tai a ranta tace “inafa wulakantata ya jani falo dai ya wulakantani san ransa.”
Saura Hajjo abinda ta fada kenan a ranta, mikewa tai tace “muje gun Hajjo.”

Da sauri Fure ta taso.....


****


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{30}


********************

Ran Hajjo a 6ace ta kalli amintacciyar baiwarta. "kina nufin jiya Azeema a turakar mai martaba ta kwana?".

"Wannan gaskiyane ranki ya dad'e, lamarin ya girgiza kowa, dan ansan dai kwanankine jiyan...."

Zeena dake zaune tana karyawa tai saurin fad'in "To banda munafunci irinna bayi miya ruwanku? Shi Abba bashida damar kusanci da kowacce matarsa a lokacin daya so? Kunsan dalilin kwanan natane dazaku kawoma mutane tsirku"

Duk Harar da hajjo ke zubama Zeena batai shiruba saida takai aya. Sosai hankalin hajjo yakuma tashi, dan dama labarin zuwan Zeena sashen mai martaba sau biyu dukya zomata.

Da sauri tace, "inason a nemamin ison zuwa sashen mai martaba yanzunan".

"Angama ranki ya dad'e".


Babu dad'ewa da tafiyar baiwar tadawo da sak'on mai martaba yanada bak'i Na musamman. Dole hajjo ta hak'ura da zuwan.

Zeena ce ta daure bayan sun fita tace "Hajjo."

Kare hade rai Hajjo tai ta kalleta tace "ke kuma menene?"

Ganin yanayin Hajjo yasa ta kasa cewa komai.

Shikenan, dama cewa zanyi Ya Zubair ya fara karatun?
A kufule tace eh.
Zeena tai shiru tana tunanin ta yanda zatai ta mata bayani.


*********************


Yinin yau gaba d'aya mafi yawan masarautar sunyisane acikin rashin dad'in rai, dan kowa da tabon damuwarsa cikin zuciya.

Gimbiya Azeema, hajjo, Junaid, Zeena, Binta. Sai sarki daketa shirye-shiryen Neman mafita, dan kuwa yayi zama Na musamman da manyan fadawansa akan shirin auren Zeena da Junaid, da tu6e Zubair daga sarautar matawalle a nad'a Junaid.

Dukkan wani hukunci sun yankeshi akan auren Zeena da binta, Wanda za'a d'aurama Junaid arana d'aya, sannan amasa nad'in sarautar matawalle.

Fadawan dabasusan sirrin sarki Abdusslam ba mamaki yakamasu ainun, ganin ansaka bikin auren kusa, sannan zai tu6e d'ansa daga matsayinsa yabama Junaid rawanin bayan Zubair shine babba, shiya kamata afarama aure kafin Junaid. Basuda hurumin bin ba'asi dan haka sukai tsitt.
Lalai Sarki yana da adalci.

******************

Da yammacin ranar Azeema ta nemi izinin ganin sarki Abdussalam.

Kai tsaye yabada izinin shigowarta.

Kokad'an fuskarta babu walwala, sa6anin shi ta sarki dake a washe da farinciki. Koda ta zauna yai k'ok'arin ta6ata saita janye jikinta.

"Ba wannan ne yakawoniba Takawa."

Sarki ya dakata daga k'ok'arin ta6ata, sannan ya gyara zamansa, "ina saurarenki"

"Na isarma Junaid da sak'onka, amma shima yazo da nasa sharad'in".

"Sharad'i kuma? Name kenan?"

"Inhar zai auri Zeena saidai ya hadasu da yarinyar da sukazo tare."

Ta zayyane masa duk yanda sukai da Junaid.

Dukda shi Junaid yafara sanarma hakan saida zuciyarsa ta k'ara sosuwa, cikin danne yanayinsa yace, "To Azeema mizai Hana mu kar6i nasa za6in, watakila akwai nasa hangen shima?"

"Wannan had'in baiminba, amma Zan amince dashi, daga baya Na d'au mataki"

"Mataki?!"

"Wane iri kenan?"

Murmushin da tunjiya batayiba ta Saki, ta mik'e tsaye tana kallon sarki "zakaji koma wanene anan gaba, dan bazan had'a zuri'a da y'ar da batada asaliba"

Shima sarki abdussalam murmushin yayi, dan hakan yamasa dadi dari bisa d'ari. Kafin yabata amsa harta fice.



********************


Binta abin duniya duk ya isheta, gaba d'aya ganin Junaid yamata wahala, anbata y'ancin kanta amma an nisantata da yayanta, Wanda tasani tun a k'uruciya.

Shi kansa yamanta da ita gaba d'aya, hangensa ma da takeyi daga nesa yanzu ya gagareta, batada aiki saina kuka da zaman d'aki, ko wajen harira ma yanzu tabar zuwa tun randa Zeena ta mareta ya Junaid kuma yai halin ko in kuma da ita, ga zazzabi dake cin jikinta, abin haushi ba wanda ya damu da yanayin da take ciki.

Takanje wajen bishiyr kwanaki ta zauna taita tunani, kewar mahaifiyarta da Junaid na damunta, wanda ayanzu haka

Please Login or Register in order to submit comment