Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita yace “Azeema!”

A hankali ta juyo saitinsa yanda ya kira sunantane yasa ta kasa amsawa.

Kallanta yai yacw “nasan Azeema da rashin hakuri, rashin yafiya, daukar fansa, rashin barin wani yai nasara a kanta.”

Murmushi tai tace “shaidar dakamin kenan? Duk ba shaidar arziki?”

Yace “Sai dai macece wacce tasan kanta, bata shiga hakkin wani, bat taka na kasa da ita, bata yin abinda zai jawo mata zagi gun mutane.”

Dariya tai tace “to naji menene ke faruwa?”

Shiru yai tare da kura mata ido, tace “menene? Kasan halina banda hakuri ko na jira ne.”

Dariya yadanyi kadan sannan ya mike tsaye da sauri yace “dama fada miki zanyi jibi ki shirya zamu wani guri dake, sai dai mu biyu zamuyi tafiyar sai dakaru guda uku.”

Kallansa tai cikin mamaki tace “ina zamu haka da sai a boye zamu?” Yace “in mun je kya gani sai dai wannan karan duk rashin hakurinki dole ki hakura sai munje can.”

Murmushi tai tace “ya na iya? Na hakura.”

***********
Ga duk mai bukatar siyan littafin nan ya tuntubi 07084161619.
**********



Zama tai daga inda aka tanada dominta, yarima na zaune ya kalli Junaid yace “dan bamu guri ko?”

Junaid ya juya zai fita, Zeenatu tace “ni nace ya tsaya.”

Cikin mamaki Yarima yace “kinsan gobe zan koma ina bukatar muyi sallama ne.”

Muyi sallamar a haka dan ni wlh bacci ma nakeji.

Shiru yai yana kallanta, murmushin rainin hankali ta saki, Junaid ya fahimci amfani take sanyi dashi hakan yasa ya juya kawai zai fita.

Jiyai tace “ina zaka?”

Junaid ya juyo yana kallanta, Yarima Sulaiman ya hade fuska sosai, balle dayaga Junaid ya kalleta ido cikin ido, kallanta yai yace “meye tsakaninki dsshi? Dan ba bawan dazai kalli Uwar gijiyarsa ido cikin ido.”

Junaid ya kalleshi yace “Tuba nake Yarima amma ina da aure.”

Ya juya y fita rai a bace, mexaiyi da wannan? Wallahi ko aura masa ita akai sai san yanda zaiyi ya gudu daga gunta.

Binta ce ta fadomai, gwaibar hannunsa ya kalla,yai ajiyar zuciya anya binta taci abinci ma kuwa? Jiyai gaba daya kansa ya rike, ko ya gudu daga nan tunda ba mai kallansa.

Kafin ka fita kofar masarautar ma an kamoks.

Dole ya lalabata inta fito tabashi damar tafiya.

A ciki kuwa Sulaiman ne ya kalli Zeena yace “wai Gimbiya meke damunki? Sai yaushe ne zaki tsaya muyi magana ta fahimta?”

Kallansa tai tace “kafi kowa sanin bana sanka to akan me zaka damu da sai ka aureni? Akwai yan mata a gidan mu ka zabi wacce kake so ka aura amma bani ba.”

Cikin mamaki ya kalleta yace “saboda yaran can?”

Dama dalilin tahowa dashi datai kenan dan ya korar mata wannan cingan din.

Kasa tai da kanta batace komai ba.
A zuciye ya mike yace “saboda bawa? Kamar ke? Ina ganinki me aji da hankali? Tir da wannan kazantar.”

Yana fada a zuciye ya fito, banko kofa yak wanda Junaid ya mike daga gun da sauri, wani kallo yamai sannan ya zubar da yawo a gefensa ya wuce.


Junaid ya bishi da kallo.

Zeenatu ce ta fito tana yar hamma, kallansa tai tace “ashe kanada amfani.”

Jin haka yasa yace “dan Allah ki barni na koma gida.”

Tace “zan barka dan in ban barka bama rayuwarka anan tana cikin hatsaru.”

Bai fahimci me take nufi ba amma bai damu ba yace “ki barni na tafi yanzu.”

Shiru tai tana kallansa, kafin tace “bari nai tunani.”


*********

Azeema ce ta kalleshi tace “sosai fa suke kama Allah, daka ganshi kaima zakai zatan Junaid ne.”

Yace “Tsabar kina san ganinshi ne amma taya Junaid zai zama bawa a masarautarsa?”

Tace “kana tunani?” Tai maganar cikin sanyin jiki.

Yace “sosai, duk inda Junaid yake ai bazai taba zama bawa ba, sarauta a jininsa take.”

Mirmushi tai sannan ta jinjina kai alamar gamsuwa..........

*Ayusher Ce*


*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma


Suna isa kilisarta ta kalleshi ta taradda Fure a bakin kofa tana jiranta,

Tana ganinta ta sauko da gudu ta matso kusa da ita tace "Gimbiya kije inji Hajjo?"

A daren nan? Ta fada sannan tace "bacci nakeji naje da safe."

Tayi wucewata zata shiga ciki, Junaid yace "Gimbiya."

Juyowa tai ta kalleshi tace "da safe."
Haka kawai tace tai wucewarta ciki.

Junaid ya bita da kallo rai a bace, yace laifina ne ma dana yarda zaki ce na tafi.

Tana shiga tai kwanciyarta tai bacci, shikam Junaid yunwa ma ta hanashi baccin daya dace, koya kankalli idanunsa zaka fahimci yana cikin wani hali.

Da safe bayan gari yai haske aka sake zuwa mata da umarnin taje inji Hajjo, yanzu kam ta san menene dalilin, ta fito tana neman zuwa, Junaid ya tareta tare da tsugunnawa yace "dan Allah ki barni na tafi."
Kallansa tai tace "jeka, ta kalli Fure tace "fitar dashi."

Tai gaba, dan itama tana san yabarnan ko dan kar bincike yasa a gano shi.
Suna kokari fita sai ga dakarun bangaren Hajjo nan, shikam Junaid matsa musu yai yana neman wucewa.

Jiyai an cafkoshi, cikin mamaki ya kalle gabjejen mutumin daya kamashi yace "lafiya?"

Mutumin bai tsaya wata wata ba ya dauremai hannu ya sabashi a kafada ya fita dashi ba tare da ya bar Junaid ko magana yayi ba.

Suna fita daga gun aka sashi a budu akai gana dashi, duk yanda yaso magana ya kasa saboda karar da aka sa mai a baki, ina za'a kaishi? Me kuma yai? Wannan tunanin sune suka sashi ya yake ta shure shure.

Zeena ta kalli Fure cikin mamaki tace "me yai?"

Fure ta girgiza kai alamar bata sani ba, nan sukai ban garen Hajjo dan tana san taji meke faruwa.

Tana bude kofa a ka kwado abu saitinta, da sauri ta goce cikin tsananin mamaki ta dago rai a bace.

Hajjo ta gani, gefenta Zubair.

Hajjo sai huci take ranta a bace, Zeena na shigowa ta sallami kowa dake kilisar ya raga daga ita sai Zeena sai Zubair.

Hajjo ta kalleta cikin takaici tace "ni zaki zubarwa da mutunci a idan duniya?"

Zeenatu ta kalleta a gabanta na faduwa me tayi?

Zubair ya kalleta rai a bace yace “dan iskanci kijewa Sulaiman da bawa kice shine kike so?”

Yanzu ta fahimci meke faruwa wato saboda haka ne kenan aka kama Wali?

Zatai magana Hajjo tace “Wlh baki isa ina zaune cikin mutunci na ki zubar min ba, kuma daga wannan lokacin ki dawo nan ki zauna, dama na barki kin koma can ne saboda na dauka kinyi hankali, amma tunda harni zaki zubarwa mutunci ki fara soyayya da bawa......”

“Wai Hajjo ke kin yadda? Wasa fa nake mai wlh.....”

Hajjo a fusace tace “wlh idan baki rufemun baki ba sai na fasashi, kuma wanda kika kira da saurayinki kin jamai, dan a dalilinki zai fiskanci kabarinsa”

Zeena tai shiru tana kallan Hajjo, Hajjo ta cigaba “kuma ki lalaba Sulaiman tun kafin mai martaba yaji halin da ake ciki, kinfi kowa sanin abinda zan biyo baya in yaji.”

Zeena idanunta ya ciciko tace “Allah wasa nake.”

Hajjo tace “damuwarki ce, amma tunda Sulaiman ya san fuskar yaran bazan yadda wani abu ya faru akan wani bawa ba.”

Zeena tai shiru batace komai ba.


*************

Junaid kam ba’a saukeshi ba sai a wani daki wanda babu komai a ciki sai yayi, cillar dashi ciki akai suka ja kofa suka sa key suka fita, duk yanda yake biga kofar yake magana akan a bude mai amma ba alamar akwai wani a kusa, yayi bugun har ya gaji wanda yunwa da wahala suka sashi yin bacci.

Yanzu kam gaba daya garin Biram ya gama fita masa akansa, da mahaifiyar data yadda shi, da yan uwan da basuda mutunci sam bai ga abin birgewa a cikin sa ba.

Yanzu kam gaba daya idanunsa sun daina ganin daidai, yana kwance kamar mara rai.

********

Gaba daya Azeema ta kasa samun nutsuwa, ta aika Bari bangaren Zeena tace mata ba yaran nan, shiru tai a cikin daki, itadai tanata mafarkai kala kala wanda yanzu kam nemansa take ido rufe domin ta duba bayan kansa, in har taga bashida bakin tawadar da Junaid ke dashi ba to zata cire ranta.

Safiyyace ta turo kofar bayan tayi sallama, Azeema ta kalleta tare da cewa “kingama zaki wuce?”

Zama tai kusa da ita sannan tace “Umma ni yaushe kika fara bari kowa na sanin halin da kike ciki?”

Azeema ta kalleta tace “sharesu kinsan bana damuwa da abinda bai shafen ba.”

Safiyya tace “Sarki ya aiko a fada miki wai karki manta.”

Dame? Ta fada tana kallan Safiyya.
Safiyyah tace “ni ina na sani? Da alama abu ne tsakanin ku.”

Auu ta fada tare da cewa to sai da safe.

Ganin yanda tai shiru da maganar yasa Safiyyah tasan batasan fada ne.

Safiya na fita ta shirya bayan tayi sallar magrib ta fiyo daga dakinta.

Bangaren Mai Martaba suka nufa, suna shiga ciki ta taddashi a shirye yana zaune da alama tunani yake yi.

Shikam tun jiya yake tunani anya abinda yake shirin yi shine mafita garesu? Duk da umarni ne na Sarki Zubair sai dai yana tunanin bazai iya cigaba da ganin Azeema cikin kunci ba, zai lalaba inta ganshi ta barshi a can yanda Yayan sa ya nema.

Jin an tabashi ne yasa ya dawo daga tunaninsa, ko muryar Zagi baiji ba sanda yake sanarda isowarta.

Juyowa yai ya kalleta sannan yace “muje?”
Kai ta daga alamar eh, nan ya riketa suka shiga wani daki, suka saki bude wani suna shiga ya bude kofa sai gasu a waje.

Cikin mamaki ta kalleshi tace “a yaushe akai wannan barauniyar hanyar?”

Yace “tun yaya.”

Suna fitowa suka shiga motar dake gefen kan hanya wanda dama jiransu suke.

Tana shga ta kalleshi tace “yau na fara shiga abar nan.”

Murmushi yai yace “zan dinga daukanki a boye ina yawo dake.”

Murmushi kawai tai batace komai ba, dakaru biyu ne a gaban motar daya na ja daya kuma yana zaune.

Sunyi shiru a mota kowa da tunanin da yake, sam bata damu da inda zasu ba saboda ba shine a gabanta ba, sunyi tafiya mai nisa kafin yadan fara janta da hira, sama sama suke hirar ganin haka ya sashi yin shiru.

A bakin wani kauye yace su tsaya, kallan Azeema yai yace muje?

Cikin mamaki Azeema ta kalleshi tace “ina ne nan?”

Hannunta ya rike bayan dogaran sun fita daga motar yace “ ki yafemin akan duk abinda zaki gani, na sani ban kyauta miki ba, sai dai zan yadda da duk hukuncin da kika yankemin”

Kallansa tai cikin rashin fahimta sannan suka fito.

Dogaran na gaba su kuma suna baya, yana rike da hannunta kasancewar dare ne.

A bakin wani gida suka tsaya wanda ke bayan gari, cikin mamaki Azeema ta kalli gidan gini ne na sarauta, kallansa tai ya dan murmusa mata.

Bubuga kofar dogarin yai daga ciki akace wanene?

Azi fa fada tare da bude kofar kadan, yana fatan gani Junaid.

Idanu ya zaro cikin tsananin tashin hankali, gani dogarai, shikenan an kashe Junaid.

Abinda kawai yazo mai kenan, yana neman sa hannu aka ne yaji ance “Azi!”

Da sauri ya kalli inda yaji maganar, Azeema ta kalli wanda aka kira da Azi cikin rashin fahimtar wanene.

Azi cikin rawar jiki yace su shigo.

Nan suka shiga cikin gidan, yarinyace a bakin rariya take kwara amai, Bari na dan bubuga bayanta? Jin motsin mutane yasa suka juyo.

Binta ta dauraye bakinta tareda kokarin mikewa.

Ido Azeema ta zaro ganin Bari ta matsa da sauri inda take ta riko kafadarta tace “ba bari bace?”

Bari jikinta ya fara rawa ta zube a kasa tana cewa “Gimbiya.”

Hankalin Azeema ba karamin tashi yai ba data kalli Takawa tace “meke faruwa?”

Nan ya umarci dogarawan da su fita, Azi ya nuna musu hanyar falan Junaid.

Gaba daya Azeema neman zaucewa take tana cewa “ina yarona?”

Sarki ya rike kafadarta ya jijigata sannan yazaunar da ita yana cewa “ya isa ya isa.”

Hawaye ne suka zubo mata ta kalleshi tace “‘meke faruwa?”

Binta dake tsaye jikin kofa rashin karfin jiki yasata tsugunna a gun.

Nan AbdulSalam ya kwashe komai ya fada mata ya daura da cewa “Azi ina Junaid din?”

Azeema kam ji take kamar mafarki takeyi, sai zare ido take tana neman danta.

Azi ya tsaya daga bakin kofa ya zube a kasa yana cewa “Ranka ya dade yana Masarauta.”

Masarauta? Suka fada a tare cikin tashin hankali.

Azi ya sanar dasu abinda ya sani, dan dama bai san me yai ba waya wa laifi da sauransu.
Azeema jin wannan yaran shine Junaid ta tuno sanda ake zubamai ruwa jitai bata gani sosai, luuu tai ta zube a kasa.

Binta kam hawayene kawai ke zubo mata, yanzu kam jin halin da Junaid yake ciki ya kara tadda mata da hankali, hawaye ke zubowa kamar wanda ake korosu......

Ba karamin bacin rai Mai Martaba ya shiga ba da jin zancen nan, had uban waye ya isa ya taba Junaid a gidan sa? A masarautar da take hakkinsa?

*******


*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma Sha Daya


Azeema tana dawowa hayyacinta ta tace su tafi maza kafin wani abu ya sami danta.

Mai Martaba ne ya kalli Azi yace "ku shirya gobe da asuba ku biyo motar ice.
Azi yace "to Takawa."
Sun fito AbdulSalam ya tsaya yana kallan Binta datake ta share hawaye, yanzu kam bayan tausayin harda tausayin kanta take? Ta tabbatar yanzu batada inda zata zauna.

Kallan Hari yai yace "wace?"
Zubewa tai a kasa tace "wanda yarima ya taimaka ne, tun tana karama anan ta taso, mamanta ta rasu."

Shiru yai sannan ya kalli Azeema, bata fahimci me yake nufi ba hakan yasa batace komai ba.

Kallanta yai da alama rashin Junaid ne yasata shiha halin nan, yace "ta fito mu tafi, in kuma bata shirya ba kwa taho gobe."

Da sauri Azeema ta kalleshi sannan ta kalli Yarinyar, itakam Binta jin haka ne yasa ta dago ta kalleshi, hawaye ne suka zubo mata ta sunkuya tace "nagode Mai Martaba."

Waje yai Azeema ta kara kallan yarinyar cikin rashin gamsuwa sannan tabi bayansa.

Binta ta mike da sauri ta kalli Hari tace "Hari ki taimaka ki tahon da kaya na."

Bari ta fahimceta hakan yasa tace "yi maza kisa takalmi ki bisu."

Takalmi tasa da sauri ta kalli Azi tace "sai kun taho." Tai waje.

Mai martaba ne ya kalli dakarun nan biyu yace "daya ya zauna gobe da asuba ku taho dasu Azi, zamu tafi da yarinyar can."

Nan suka amsa daya ya zauna, Binta ta fito ta tsaya a bayansu suka nufi wajen gari.

Suna zuwa ya mata alama data shiga gaba ta shiga ta zauna tana tunanin zancensu kenan da Junaid akan suna san su hau mota, yau gashi ta hau.

Azeema kam ko kallanta batai ba dan sam abin bai mata ba.

Suna shiga mota tai shiru, tana tuno abinda Zeena tamai, idanunta ne suka ciciko tare da zubo da ruwa.

Sarki ya kalleta yace "tunda mun san inda yake dan Allah ki kwantar da hankalinki."

Kai ta daga tare da cewa "Amma me ya kaishi zuwa a matsayin bawa?"

"Ko ma menene dalilinsa bazai wuce ke yaje gani ba."

Idanu ta runtse cikin takaici tana kallo aka wahalar mata da danta da akai, lalai sai ta dau mataki dan bazata taba barin wannan abin ba.

Har suka isa batace komai ba, haka shima daya fahimceta baiyi magana ba.

Meyasa Sarki Zubair zai mata haka? Abinda kawai ke yawo a kanta kenan.

Suna isa suka shiga ta lungun da suka fito, Binta na binsu a baya, sun isa ana alamun kiran sallar asuba, Sarki ya jata zuwa turakarsa yace "Azeema ki jira gari ya waye sai a nemeshi, ki zauna anan."

Kai ta girgiza alamar rashin yadda tace "bani na tafi inasan kadaicewa ne."

Saketa yai jiki a sanyaye yasan tana ganin laifinsa ne shima.
Kallanta yai yace "ki tafi da yarinyar."

Fita tai taga ta a inda suka barta, kallanta tai sannan tace "biyoni."

Binta tabi bayanta sumu sumu, tana shiga bangarenta Bari ta fito da gudu, Kallan Bari tace "bata guri."

Ta wuce daki, Bari ta kalli Binta wacce gaba daya ko kayan jikinta a wahale suke saboda ita kanta ma ba'a hayyacinta take ba.

Nan ta shiga da ita dakinsu, tana kaita ta fito ba abinda tace mata, Binta ta zauna a kasa tadan sa kanta a saman gado tare da lumshe idanunta tana tunanin abinda ke faruwa? Bata san sanda bacci yadan zare ta ba.

Azeema tai shiru a daki tana tunanin wannan lamari, hawaye kam sun kasa daina zubowa daga idanunta.

Gari nayin haske ta fito kilisarta, Bari ta mike daga zaman datai da sauri tace “Gimbiya me kikeso?”

Azeema tace “Ina Zeenatu?”

Cikin mamaki tace “Gimbiya Zeena? Naji ance tana gun Hajjo.”

Hanyar fita yai wanda yasa Bari matsowa da sauri tace “Gimbiya can zaki da safen nan?”

Wucewa tai batace mata komai ba, da sauri Bari tabi bayanta.

Bangaren Hajjo suka nufa, Hajjo na dakinta tana kishingide tana bacci taji ana buga kofarsa, ranta bace ta mike zaune tare da bada izini, kuyangarta ce ta shigo tace “Ranki ya dade kinyi baki.”

Cikin mamaki Hajjo tace “da safen nan?”

Eh su Gimbiya Azeema ne.

Cikin mamaki ta zura alkyaba dinta ta fito.

Azeema na zaune, ta fito sai da ta zauna sannan tace “Azeema lafiya da safen nan?”

Azeema ta kalleta tace “Zeenatu nake nema.”

Hajjo ta sake kallanta cikin mamaki, Zeenatu? Nan ta tura a kirata tana cewa “Laifi tayi ko?”

Zeena ce ta fito cikin abin bacci tana hamma.

Azeema tana ganinta ta mike tace “Ina yaran da kika zubama ruwa rannan?”

Da sauri ta kalleta, gaban Hajjo ya fadi shikenan har magana ta kai? Amma meya sa taga Azeema cikin damuwa me makon tai murna? Badai wani munafircin ta kullo ba?

Azeema rai a bace tace “yana ina?”

Zeena ta zaro ido ta kalli Hajjo da sauri, Hajjo tace “ya tafi, cikin dare ya gudu.”

Azeema tai wani murmushi sannan tace “ya gudu? Yaran dake kulle?”

Hajjo tace “fada mata bakin sakeshi ba?”
Da sauri Zeena tace eh na sakeshi.

Azeema tace “ko?”

Zeena tace “eh.”

Azeema ta kalli Bari tace “Bari, jeki sanarma mai Martaba abinda Zeenatu tace a gama da inda Junaid yake.”

Cikin mamaki Bari ta kalleta, Hajjo cikin rashin fahimta tace ta fada mishi inda Jun......”

Sai yanzu kwakwalwarta takai dakyau tace “Junaid?”

Ta fada hankali a tashe, Azeema tace “ina d’ana? Ta kalli Zeenatu wacce idanunta suka firfito, Azeema ta runtse ido cikin fada tace “idan na kara magana baki fadamin inda yake ba duk abinda ya biyo baya karkiyi mamaki.”

Da sauri Hajjo ta rike hanunta, yauce rana ta farko dataga Azeema haka. Tace “Azeema me kike san cewa? Wai bawan nan Junaid ne?”

Azeema ta kwace hannunta tace “wuce?”

Ta fada tana nunawa Zeenatu wacce gaba daya hankalinta ya tashi hanya.

Zeenatu ta kalli Hajjo tace “Hajjo ce ta kamashi bansan inda yake ba.”

Azeema ta kalli Hajjo, Hajjo tace “zauna bari nasa a kawoshi, tashin hankalin na menene?”

Gaba tai tace “ya na ina?”

Hajjo ta kalleta da sauri, ta sa takalmi tace “bari muje tare.

Suna fita waje, ta kalli Hajjo tace “na manta da abu a ciki, nan suka tsaya ta dawo ciki.

Zeena tana tsaye inda suka barta, gaba daya kokarin jera abinda ya faru takeyi a kanta.

Ji tai an kifa mata mari, yanda taji marin ne yasa ta gigice, Azeema tace “duk garin nan ba wanda ya isa ya marar min da, duk matsayinsa kuwa.”

Ta juya, Zeenatu ta zube kasa kawai tasa kuka, dan taji marin nan har kanta.

Tare suka tafi har inda aka kulle Junaid gaban Hajjo sai faduwa yake tana fatan Allah yasa yanada rai.

Bawan da ya rakosu ne ya bude kofar, ido Hajjo tadan runtse dan jikinta y gama bata ya margaya lahira.

Ana budeshi Azeema ta hango danta a yashe akan yayi, hankalinta a tashe ta shiga ciki da sauri tasa hannu ta dagoshi, jin yana numfashi ne yasa ta saki wani ajiyar zuciya hawaye ya biyo baya.

Kallan Hajjo tai wacce tai tsuru. Azeema ta shiga jijigashi tana hawaye a hankali yadan bude ido, baya gani sosai sai yaga kamar Binta ce kusa dashi dan sam bai kawo Azeema mahaifiyar sa ba.

A hankali yace “bin.....bin.....”

Idanunsa ne suka rufe wanda ya kasa ko bude ido, Azeema ta kalli bakinsa duk ya tsage alamar yunwa da kishin ruwa.

Wanda ya bude kofa ne yazo ya daukeshi suka fito.

Azeema ba abinda tace sai hawaye da takeyi.

Bangarenta suka nufa Hajjo zata shiga Azeema tace “mun gode da rakiya.”

Tana fada ta kalli Bari wace ta rufe kofa.

Hajjo tabi kofar da kallo tashin hankali, yanzu a wani hali zata tsinci kanta? Ita? Zeenatu? Da Zubair dan tasan yanzu ko za’a mutu Azeema itama cewa zatai Junaid ne zai gaji mulkin nan.


Suna shiga Binta na tsaye a waje tana shan ruwa saboda gaba daya jikinta ba karfi, tana ganin an shigo da Junaid ta yadda kofin, da sauri ta isa gun tace “Junaid.”

Ciki ya shiga dashi ya kwantar dashi dakin Azeema.

Binta hawaye kawai take ganin yanda duk ya canza, ta kara cewa “Junaid.”

Azeema ce ta kalleta tace “Yarima Junaid.”

Binta ta daga kai alamar to, Bari ta kalla tace “yi maza ki kira wanzami.”

Nan bari ta fita da sauri, Azeema ta fito falo dan bada umarnin abincin da za’amai da kayan sawa.

Binta suna fita ta tsuguna gefen gadon tana kuka, dagowa tai tana kallan yanda duk ya canza, hawayen da takeyi ne ya diga a kan fuskar sa, a hankali ya dan bude idansa sama sama.

Kallansa tai tace “Junaid!”

Binta? Ya fada tare da kokarin murmusawa sai dai a hankali idanunsa suka koma suka rufe.....

Tausayinsa ne ya kara kamata hankalinta ya kara tashi, hawaye kawai take.


*Ayusher*



*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma Sha Biyu


Azeema ce ta turo kofa, dauke da kofi a hannunta, kallan Binta tai tace "bamu guri."
Mikewa Binta tai zat fita, a hankali yace "Binta!"

Juyowa tai ta kalleshi, murmushi ta sakar mai hawaye suka gangaro tace "Yarima kagane ni?"

Kai ya daga sannan yace "Yarima?" Dan yaune rana ta farko data kirashi da haka.

Azeema ce ta kalleta wanda ya sa juyawa zata fita, mikewa ya shiga kokarin yi yana cewa "Binta ina za......."

Kallan mahaifiyarsa a gabansa ne yasa ya kalli dakin da yake ciki, sake kallanta yai cikin mamaki, kofin hannunta ta mika mai wanda madara ce a ciki ta shanu, mikamai tai saboda yanda yakejin jikinsa ne ya amsa ya kafa kai bai sauke kansa ba sai da ya shanye ta duka.

Ajiye kofin yai sannan ya kalleta yace “meke faruwa?”

Kallansa tai cikin tausayawa ta zauna a gefen sa tace “Junaid!”

Shiru yai yana kallanta yana san jin abinda ke faruwa, hawaye ne suka zubo mata ta gogesu tace “kasan kullum dakai nake kwana nake tashi? Amma Junaid kana ganina kaki sanar dani kai wanene?”

Abinda ke bakinsa ya hadiya, kallanta yai kamar zaiyi magana ya fasa, mikewa ya shiga kokarin yi yana cewa “ni zan wuce ni da Binta.”

Hankali a tashi ta mike tace “Junaid zaka koma ina?”

Kallanta yai yace “yanda kike rayuwarki hankalinki a kwance nima a can hankalina a kwance yake, tunda kin gani na ganki zan koma.”


Da sauri tace “kana tunanin zan barka ka koma wani gun? Junaid? Baka tausayin mahaifiyar data rasa danta tun baigama wayau ba? Shekarata nawa rabona dakai? Ka rasa abinda zakacemin sai zaka tafi?”

Juyowa yai ya kalleta, zuciyarsa ce ta karaya, shi kanshi yana kewar mahaifiyarsa amma gani yake kamar mantawa sukai dashi.

Karasowa tai inda yake tace “ka koma ka huta na sa akira wanzami ya dubaka, Junaid bansan meke yawo a ranka ba anma ni mahaifiyarka ce, babu uwar dazata ajiye danta a wani gun tai rayuwar datakeso.”

Shiru yai baice komai ba, ganin haka yasa tace “ kana san wani abu ne?”

Kai ya girgiza alamar a’a yace “Binta tana ina?”

Kallansa

Please Login or Register in order to submit comment