Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace “menene?”
Yace “fadamin zakiyi ya akai ranan? Ya akai su Sarki da Umma sukaje can?”
Ajiyar zuciya tai sannan ta fara bashi labari.
Kallan bakinta kawai yake tanata magana, murmushi kawai yakeyi.
Safiya wacce tazo dan suyi sallama ta tsaya a jikin kofa, jin yanda abin ke mai dadi ne yasa tasan tabbas da matsala, kwankwasa wa tai sannan ta shiga.
Binta na ganinta ta mike da sauri, Safiya ta kalleta Binta ta mike zata fita, Junaid yace “ina zaki?”
“Harira ke nemana.”
Tana kaiwa nan ta fita.

Safiya ta zauna tana cewa “ko kunya ta take?”
Yace “kila dan tanada kunya gata batada saurin sabawa da wanda bata sani ba.”
Safiya tace “hakane, zan wuce ne nace bari nazo dan nasan ba zuwa zakai ba.”

Yace “a’a bansan zaki wuce ba da zanshigo.”
Ta kalleshi cikin kulawa tace “Junaid!”
Kallanta yai bai amsa ba, tace “dan Allah ka dinga zuwa gun Umma, sannan kayi kokarin sakin jiki da ita, bakasan tashin hankalin data shiga na rashinka ba.”

Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan tacigaba “Umma duk duniya bata hada sanka da kowa, kowa yasan haka, kai kanka sanda kana karami sanda kake mata daban ne, ya kake tunanin takeji yanzu gaka a kusa da ita amma Kamar kana nesa da ita?”

Junaid yai shiru sai dai yanzu ya fahimci lalai bai kyauta ba, tace “kayi kokarin canzawa dan Allah.”

Insha Allah!
Abinda yace kenan, ta mike tace “zan wuce.”
Nan ya fito har waje ya mata sallama, akan sai ta taho da yaranta dan ya gansu.

Gana fita taji ana gulma akan Junaid ya taho da mata daga can wasu har da kari wai tana da juna biyu.

Hankalinta ne ya tashi ta nufi bangaren Azeema.
A zaune ta tadda ita akan kukerarta.
Safiya ta kalleta tace “Umma kinji abinda ke faruwa?”
Azeema ta kalleta tace “naji, ynzu Barira ta jiyo a waje.”
Safiya ta zauna cikin tashin hankalu tace “amma ya naganki haka?”
Azeema ta kalleta sannan ta dau madarar dake gefenta ta sha sannan tace “kin manta na basu kwana biyu?”
“Wani kwana biyu Umma ana cikin wannan yanayin?l
Azeema ta lumshe idanunta kadan sannan ta ajiye cup din tace “ki gaida Mahmud.”

Safiya ta zuba mata ido, kamar zata sake magana sai ta fasa, mikewa tai tare da yin sallama ta fita.

Azeema ce ta kalli Barira tace “matsan kafata wajen yatsuna.”
Barira ta kalli kuyangar dake gefenta tai saurin matsawa ta fara matsa mata.


**********************************

*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Goma Sha Takwas*


Kankace zance ya gama karade masarautar nan, ta ko ina zancen da ake kenan, wasu sunce ma ciki gareta, a cewar wasu ma wai ta haihu sun boye dan ne, zance dai kala kala.

Azi ne ya shigo da saurinsa ya nufi bangarensu Hari, suna zaune a waje suna tsincs shinkafa ya shigo.
Daga yanda yaha alamunsa ta fahimci da matsala, mikewa tai ta taso inda yake tace “Azi lafiya?”

Yace “Hari kinji abinda ake cewa?”
Name kenan? Tai tambayar cikin mamaki, Azi ya kwashe abinda yaji ya sanar da ita.
Gani yai ba alamun mamaki a tattare da ita yace “Hari kinsani ne?”
Ta kalleshi tace “bansani ba sai dai dama nasan za ai haka.”
Kamar ya?
Ta kalleshi cikin damuwa tace “Yanzu ba wannan bane matsalar, matsalar da zata biyo bayan wannan lamari shine abinji.”
Kallanta yai fuskarsa dauke da tambaya, ta kalleshi tace “indai munaso Junaid ya zama jarumi sannan ya karanci masarauta yasa abinda ya dace dashi dole sai ya shiga halin gagarin rayuwa, a yanda yake yanzu bazai taba yiwuwa ya kwace kansa ba, baka gani baya ji baya ganin komai? Abinda ya sani kawai Binta wanda a yanzu ya kamata yasan mutanen dake kusa dashi, makiyansa da kuma mutanen da zai taimaka, dan haka ka dauke ido, in har yaga Binta na neman shiga wani hali lokacin zan san abinda ya kamata yai, karka manta dan sarki ne jinin sarauta.”

Azi ya jinjina kai cikin gamsuwa yace “Nagane Harira Allah yasa komai yazo da sauki”tace Ameen

Junaid na kwance a kan kujerar dake falan ya mike zaune ya kalli Binta dake zaune a kasa tana ninke kayansa da aka kakkawo mai.
yace “zo muje mu gaida Umma, jiya banje ba.”
Ta mike tace “kai kadai ya kamata kaje yaya, bai kamata muje tare ba.”
Dan ajiyar zuciya yai yace “bari na kira Azi muje to.”
Ya mike ya shiga daki ya shirya sannan ya fito yai waje.
Da kallo ta bishi a hankali tai murmushi jin dadi, domin ganin Junaid cikin kwanciyar hankali shine kwanciyar nata hankalin.

Azi na dawowa daga gun Hari ya hango Junaid cikin hanzari ya matso, Junaid ya kalleshi yace “muje gun Ummah.”
Azi da sauri ya amsa tare da cewa “ka kyauta yarima.”
Tare suka fito sai dai duk inda suka wuce sai nuna shi ake ta gefen ido, mutane sai kallansa suke suna gulma.

Kallan Azi yai kamar zai tambayeshi sai kuma ya fasa dan gani yake suna kallanshi ne akan basu sanshi ba.

Azeema na zaune kuyangarta ta shigo da gudu ta sanar da ita Junaid ya taho.
Kallan Barira tai tace “Barira sa a aikata can.”
Barira ta juya da sauri ta fita ta bayan kofa, Junaid ne ya shigo ciki, Azeema na zaune a kilisarta gabanta kayan marmari ne, kamar yanda ta saba yauma cikin kwalliya take tasha ado sai dai fuskarta ba kwalliya, sai ma alamun damuwa data nuna s fuskar.

Junaid ne ya shigo ta gyara zamanta tana cewa “Junaid kaine?”
Cikin halin kulawa ya taho gunda take da sauri yana cewa “lafiya?”
Kuyangar dake tsaye agunce ta kalleshi tare da zubewa ta durkusa tace “Yarima tun jiya Gimbiya bata jin dadi, sai dai tana fitowa ta zauna anan saboda bataso kazo kaganta a kwance.....”
“Fita daga nan, banace karkiyi zancen nan?”

Da sauri ta sake durkusawa tace “tuna nake Gimbiya sai dai ganinki cikin wannan hali ne ya sani na fada, ga rabanki da abinci tun jiya.”
Wani kallo ta mata wanda yasata fita da sauri, Junaid ya kalleta jikinsa yai sanyi, haushin kansa ya kamashi, yace “kiyi hakuri Umma kina nan bakida lafiya ni kuma ina can ina bacci hankalina a kwance.”

Murmushi tai na karfin hali tace “karka damu Junaid ba wani abu bane dan ko Takawa bai sani ba, gajiya ce kawai kila.”

Kallanta yai sannan yace “zaki iya daurewa ki tashi? Kamar gwara ki shiga ki mike akan zama anan.”
Mikewa tai a hankali, ya dauki kayan marmarin da kansa ya shigar mata dasu ciki, bayan ta zauna ne yace “kina san wani abu?”

Murmushi tai tace “bakomai Junaid ganinka ma ya isheni.”
Kansa ya saukar kasa yace “ki daure dai kici wani abin.”
Tace “shikenan bari nasa a kawon madara nasha.”
Da sauri ya mike yace “zauna anan bari nasa a kawo miki.”

Yana fita ta bishi da kallo tace waya isa shiga tsakanin d’a da mahaifiyarsa bayan wata tara yai a cikina ni kadai.
Cikin ruwan sanyi zaka dawo inda ya dace dakai Junaid.

*********

Barira kuwa tana fita ta shige bangaren Junaid cikin sanda, kamar yanda Azeema ta zata kuwa Binta na zaune a fadar sa.
Bata ma kula da abinda takeyi ba tace “Binta ashe kina nan, Yarima ne yace ki sameshi a raga.”
Raga? Ta tambaya cikin mamaki, Barira tai dariya tace “bakisan gun ba nasan muje na nuna miki, dan shiyasa ma yace na raka ki.”

Tai dariya kadan tare da cewa “da yace zaije gun Gimbiya?”
Eh bandai san me yake nufi ba kamar cewa yai kije kamar kuma cewa yai ki dauko mai abu, kiyi hakuri kwakwalwar tawace ta fara tsufa.”

Binta tai dariya tace “nunamin gun in naje na gani in baya can sai na dawo.”

Barira tace “nagode Binta, suna tare da Gimbiya bansan ko sunje ba.”
Binta ta mike ba tare da dogon nazari ba.

Barira na fita Binta tabi bayanta, Hari taga alamar wucewar Binta sai dai bata hango wanda ya fara wucewa ba, hakan yasa bata kawo komai ba.
Barira ta nuna mata ragar daga nesa tace “bari taje Azeema ta aiketa.

Binta ta wuce ta shiga, ba kowa agun harta shiga, katan guri ne wanda yake a killece, daga alamar yanayin gun kamar an dade raban da wani ma ya shiga ciki, a hankali tace “Ya Junaid?”

Ta shiga cikin dakin tana cewa “Ya Junaid? Yarima?”
Jitai an kulle kofar, da sauri ta juyo ta kalli kofar sannan ta kalli ciki, wanda ba alamar mutum, dawowa tai da sauri ta tura kofar, sai dai me? Jinta yai tai a karkame, hankali a tashe ta fara bubuga kofar yana turawa, sai dai ba alamar zata bude.

Da sauri ta juya ta kara kallan cikin dakin wanda sai yanzu ta kula da yanda yana ta gama zagaye gun tace “ina ne nan?” Tashin hankali da tsoro ne suka shiga ranta.

**********

Gani duk yanda tai hankalinta ya kwanta ya kasa kawai ta fito daga bangarenta ta nufi bangaren Hajjo.

Hajjo da Ramatu na zaune tana bata labarin yanda labari tasan kafin gobe ya isa gun Mai martaba, Zeenatu ta fado ciki.

Kallan Ramatu tai sannan ta kalli Hajjo tace “Hajjo inada magana dake.”
Harara ta kifa mata tace “ke harkina da wani magana da zakiyi dani? Fadi anan.”

Zeenatu ta kara kallan Ramatu, wacce yanzu ta mike tace “ni na wuce Hajjo sai gobe.” Ta rusuna alamar girmamawa ta fita.

Tana fita Zeenatu ta zauna kusa da Hajjo tace “Hajjo nayi tunani na samo mana mafita.”
Cikin kallan rashin damuwa tace “ke harkina wani tunanin neman mafita ne bayan kin kasa samosa kanki?”

Zeenatu ta riko hannunta tace “me kike tunani in muka raba kafa?”
Raba kafa? Hajjo ta fada tana kallanta.
Zeenatu tace “Idan Ya Zubair bai samu mulki ba a kalla ni ma samu matsayin matar Sarki.”

Yanda Hajjo take kallanta ne yasa tace “Hajjo?kinajina?”
Mikewa Hajjo tai tace “wai na tabbatar bakida hankali.”

Zeenatu cikin rashin fahimta tace “bangane ba Hajjo?”
A zuciye Hajjo ta shiga dakinta ta rufe kofa.

Zeenatu ta dafa kanta......

**********



*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Goma Sha Tara*


Mikewa tai daga gun ta fito waje inda Fure take, tace “Fure muje bangaren Gimbiya Umma karama”
Mamaki ne ya bayyana karara a fuskar Fure tace “muyi me?”
Zeenatu tace “meye damuwarki da abinda zan?”
Nan tai gaba tana yar mita.

A can bangaren Azeema kuwa Barira ce ta shigo dauke fa tire ta ajiye sannan ta gaida Junaid, kallanta yai ya mika mata hannu ta mikamai.
Sannan ta rusuna ta gaisheshi tace “bansan ka iso ba yarima naje sanarwa wanzan rashin lafiyar Gimbiya.” Ta kalli Azeema wacce itama ta kalleta alama ta mata da ta aiwatar, Junaid ne yace “Allah sarki sannu.”

Ta mike sannan tace “ina waje Yarima in da akwai abinda kakeso.”
Ya daga mata kai ta fita, kallan Azeema yai ya dara tiren akan cinyarsa sannan ya sa spoon acikin dan karamin kwanan dake dauke da faten wanke wanda yasha kifi da alaiyahu wanda itace tace amata.

Amsar cokalin tai sannan a hankali ta debi abinci, loma daya tai ta ajiye cokalin tace ta koshi, Junaid cikin damuwa yace “Umma dan Allah kici abinci, tace “Allah banjin yunwa sai dai in nai bacci na tashi.”

Kallanta yai cikin rashin jin dadin abinda ya aikata yace “to ki kwanta in kin tashi kyaci.”
Kai ta daga sannan ta gyara kwanciyarta, bargo ya ja ya rufeta sannan ya kalleta, murmushi tamai mai sanyi sannan tace “tafiya zakai ko?”
Yace “a’a zan zauna ki tashi.”

Cikin jin dadi tace “nagode Junaid.” Ta fada tare da lumshe idanunta.

Zama yai akan kujerar dake dakin yana kallanta, gashi a dalilinshi mahaifiyarsa na neman shiga wani hali.

Wani littafi ya gani a gefen gadanta a hankali ya jawoshi, murmushi yai daya dubawa da alama rubutu take kokarin koya aciki.
A hankali yaji muryar Barira tace “Yarima!”
Mikewa yai sannan ya bude kofar dakin a hankali, ta sunkuya tace “Yarima dama Gimbiya Zeena ce tazo neman Gimbiya.”

Fitowa yai tare da rufe kofar a hankali, sannan yace “kice tana bacci.”
Tace “to Yarima amma Gimbiya dauka zatai karya nake mata saboda kowa yasan Gimbiya batasan baccin rana.”

“tana ina?

Nan ta nunamai inda take, tana zaune a kilisar Gimbiya, a bakin kofar ya tsaya ya kalleta.

Tunda ya tsaya ta zuba mai ido, tuno abinda ya faru tai tsakaninsu a hankali murmushi ya bayyana a fuskarta.
Kallan Junaid tai wanda ya kalleta shima yace “Gashi kinzo ta kwanta.”

Mikewa tai tace “Ya Junaid ka karaso ko gaisawa muyi mana? Ko na karaso?”

Kamar bazai karasa ba sai kuma taga ya nufo gun, zama yai fuskarsa a hade tsam, ta koma ta zauna itama sannan tace “Ya Junaid haryanzu baka huce ba?”
Dame kenan?
“Abinda ya faru tsakanin mu mana, daga yanda kake min magana kamar bakaso yasa nasan baka huce ba.”

Yanzu kam kallanta yai sosai yace “inban huce ba mai zai faru?”
Tace “hakan nake so nima ai.”
Hakan?
Tace “eh, nafisan ka rama yanda nan gaba bazanyi ta jin haushin kaina akan abinda na aikata ni kadai ba.”
“Ohhh tunda haka ne bari na nasa a rama.”

Murmushi tai tace “sai dai kai ka rama da kanka.”

Mikewa yai yace “bani da lokacin wannan, zan koma ciki.”

Da sauri ta mike tasha gabansa, kallanta yai cikin mamaki, tace “Ya Junaid me kake tunani in mukaje gun Hajiya Inna ka ganta?”

Kallanta yai kafin yai magana tace “baka santa ba ko? Ka gani? Ni zan kaika ka ganta.”

In zan ganta sai ta hanyarki?

Ta dansa yatsarta ya dan sosa wuyanta kadan tace “sosai, dan batasan Umma karama kaga nina dace na kaika.”
Bai bata amsa ba tai saurin cewa “ zanzo gobe ko jibi muje, in Umma Karama ta tashi ka gaisheta.”

Ta juya da sauri ba tare da taji amsarsa ba, wani kallo ya bita dashi sannan ya juya yai ciki, kamar yanda ya barta tana kwance tana bacci ya koma ya zauna yana kallan dakin.”

***********

Binta tuntana ihu tana kuka hartazo ta gaji da buga kofar ta gaji dayin kukan, Zama tai a jikin kofar ta takure tana hawaye.

Harira kam bata kawo komai a ranta ba saboda a tunaninta Junaid tabi, tunda bata fada mata ba shiyasa batai tunanin komai ba.

Mai martaba na dauraye hannunsa sabuwar Jakadiya tai sallama, hannunsa ya karasa daurayewa sannan ya kalleta yace “Jakadiya!”
Ta zube a kasa tace “
Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara

Murmushi yai tare da goge hannunsa sannan ya kalleta yace “meya faru?”
Ta sake kasa dakai tace “Takawa anata rade radin Yarima Junaid yana da aure a inda aka samoshi, matarma har ta kusa haihuwa.”

Kallanta kawai Abdulsalam yake kafin yai wata dariya wanda shikansa baisan tazo mai ba, yace “mata? Harda ciki? A ina kika samo shirmen nan?”

Kallansa tai kadan ta kara maida kanta kasa tace “wallahi Mai Martaba wannan zance har wajen masarautarnan ya zagaya.”

Yanayin fuskarsa ne ya canza yace “mene?”

Tace “tun jiya ake yawo da maganar, gudun kar hankalinka ya tashi yasa na jinkirta sai dai ance wai tare suke kwana a daki daya, shine naje na bincika kuma sai gashi na tabbatar akwai yarinya dake kwana dashi.”

Idanun Abdulsalam ne ya canza yace “mene?”

Ta sunkuya tace “gafara Takawa, laifina gagarumi ne ni na sani amma bazan bari wani abu ya sameka ba.”

Abdulsalam yace “Binta ce amma a bangaren Azeema take, me zaisa kice suna kwana tare?”

Tace “wallahi da gaske Takawa da kaina na bincika.”

Yanda fuskarsa ta nuna bacin rai tsantsa ne yasa ta kalleshi, a hankali ya saki fuskarsa sannan yace “a aika Azeema da Junaid suzo.”
Mikewa tai da sauri ta fita.

Abdulsalam yai shiru yana tunani, bazai yadda da hakan ba harsai yaji da kansa.

Azeema ta farka taci abincinta Junaid shima an kawo nashi yana ci.

Wani irin dadi take ji wanda tunda taga Junaid bata taba jin irinsa ba sai yau.

Kallanta yai yace “Umma ya akai?”
Murmushi tai sannan ta mike zaune tace “mamaki nake haryanzu kana nan.”
Yadan sunkuyar da kansa yace “kiyi hakuri, maimakon na duba yawan shekarun da kikai kina jirana, sai kawai na duba yanayi na na rashin sabawa dake dabanyi ba.”

Kai ta girgiza da sauri tace “sam ba haka bane na fahimceka nasan kuma a hankali zaka saba.”

Nagode.

Murmushi tai sannan a hankali ta mike ta shiga toilet.

Tana fitowa tace inka gama muje ka zagaya kaga yanayin gurina.

Zaki iya fita?

Tace “eh gwara nadan zaga ko naji karfin jikina.”

Murmushi yai sannan yace to.

Tare suka fita suka zagaya cikin fadarta, ga gefen shuke shuke, ga hanyar da zata sadata da wani bangare, tace “nan ne asalin bangarenka.”
Kallan gun yai kamar mai shirin tunowa sai kuma yai murmushi yace “a bude yake?”
Tace “eh muje ka gani.”

Nan suka shiga ciki, tsaf yake kamar wanda akwai mutum a ciki, ga komai akwai a bangaren.
Kallanta yai, tai murmushi tace “nasa an barshi a yanda yake ne akan tunanin kullum zaka dawo gurinka.”

Tausayinta ne ya kara kamashi, ya kalleta jiki a sanyaye yace “nagode Umma, Nagode da kullum nake ranki.”

Idanunta ne suka ciciko, ta juya kanta gefe tare da saurin fitowa.
Shima fiyowa yai Barira ce ta shigo gun da sauri, ta kalli Azeema tace “Gimbiya mai martaba na kiranku ke da Yarima.”

“Mai martaba?”

Ta fada tare da kallan Junaid, dakinta ta koma ta kara shiryawa, alkyabarta mai launin ruwan kasa ta saka, Junaid na aiken wata kuyanga akan taje tacewa Binta yana zuwa ta fito, bata kalleshi ba har kuyangar ta tafi sannan suka fito tare.
Bangaren mai martaba suka nufa yana zaune shi kadai suka shigo.

Sai da suka gaisa sannan ya kalli Azeema yace “Azeema meke faruwa?”
Tace “name kenan?”
Maida idansa kan Junaid yai cikin zargi yace “Junaid a ina yarinyar da muka taho tare take kwana?”

Ba tare da wani tunani ba yace “Bangarena.”

Da sauri Sarki ya kalleshi yace “mene?”
Junaid ya kalleshi sannan ya kalli Azeema wacce ya kasa gane halin da take ciki......


*****



*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin*

Mai Martaba yace “wani irin abu nakeji haka? Taya Junaid zai dinga kwana da ita? Bama a bangaren Bayi ba?”

Azeema ce ta kalli Junaid sannan ta kalli Sarki tace “Nasan bai kamata ba sai dai ganin hankalin Junaid ya kasa kwanciya yasa na barshi.”

“Dan hankalin Junaid bai kwanta ba sai ki bari yai abinda zai barmai tabo? Ke din?”
Junaid ne ya daure yace “Tuba nake ranka ya dade amma haryanzu banga aibu akan haka ba, na farko Binta ba a dakina take kwana ba.”

Kallansa Mai martaba yai yace “zan ma tambaya, yanzu daka shigo nan a ina kake?”
“Fadar ka, ranka ya dade.”
To waye ya san kana nan ko kana cikin turakata?”
Junaid yai shiru, yacigaba “yanzu inka shiga cikin dakina ko bandaki na waye ya sani?”
A hankali yace “babu.”
To fadamin Yarinyar a ina take kwana?”
Junaid ya kalleshi yace “a bangarena.”

“Me kake tunani mutane zasu fassara? Abinda basu taba gani ba?”
Junaid yai kasa dakai yace “A gafarceni.”
Sarki ya canza yanayin kallan da yakemai, yace “ka maidata bangaren Azeema ko ta koma bangaren bayi ta zauna, na taho ma da itane jin tare kuka taso, ganinta a kusa dakai zai debe ma kewa, wannan abinda kakeyi bakasan zai iya janyo ta shiga wani hali ba?”

Junaid jiki a sanyaye yace “Tuba nake.”

Sarki yace “shikenan jeka huta.”
Junaid ya mike tare da godiya ya fita.

Idanunsa ya maido kanta ya kura mata ido, fuskarta ta hade itama ta kalleshi, yace “me kike tunani?”
Tace “me kuwa? Na bari ne saboda karyaji ba dadi.”

Wani irin murmushi yai sannan yace “ke din?”
Kallansa tai tace “tundazu kake cewa nidin?me kake nufi.”

Idanunsa na kanta yace “badai kishi kike da yarinyar ba?”

Kallansa tai da sauri tace “kishi?”
Yace “to fadamin menene na barinta ta kwana dashi bayan kinsan za’a yada akan suna kwana tare? Sannan kina ji har gulma ta gama yaduwa ba tare da kin dau mataki ba?”

Ranta ne ya baci ta mike zata fita, mikewa yai ya riko hannunta da sauri, juyowa tai ta kallanshe, hannunta yaja ya shiga da ita dakinsa ya zaunar da ita akan gado yace “haushin me kikaji? Haushin na fadi abinda kika shirya?”

Kallansa tai bakinta tadan motsa sai kuma tai shiru, menene ba haka bane?”

Hannunta ta kwace tace “ya kakeso nayi? Yarona ya dawo amma kamar ya sake barina? Bai damu da mahaifiyar datake jiransa shekara da shekaru ba? Bai damu da yayensa ba? Ba abinda ya dameshi da wace rayuwa nai? Bai damu ya sanar dani rayuwar dayai ba? Komai ka taba zancenshi daya ne Binta, ya kakeso nayi?”

Shiru yai yana kallanta a hankali ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa ya rungumeta yace “hakan da kikai kina tunanin mafitace?”

Tace “bani nai ba, sai dai hakan zaisa ya nesanceta ko dan samun kwanciyar hankalinta, hakan zaisa ya maida hankalinsa kaina.”

Hannayensa ya sa akan kuncinta yace “shiyasa nace kishi kike.”
Dan idanunta ga juya tace “inji wa?”
Yace “gashinan kina abinda kika dade bakiyi ba.”

Murmushi tai tace “ka nemomai mata ya aura dan Allah, na tabbatar in akwai mace a kusa dashi dole ta kama gabanta.”

“Korarta kikesanyi? Kiyi hakurin kwantar da ranki, Junaid naki ne ba wanda zai kwace miki shi.”
Tace “haka da na dauka amma yanzu nasan ba haka bane.”

Murmushi yai sannan adan ja kuncinta yace “wannan mamar akwai neman fada.”

*************

Junaid ransa a bace ya shiga bangarensa, Azi ya bishi da sauri, Junaid ya kalleshi yace “wai kaji abinda ake cewa?
Azi yai kasa dakai yace “Tuba nake Yarima amma zancen nan ba inda baije ba.”

Junaid yai shiru sannan yace “ina Binta?”

Binta? Nan Azi ya mike dan kiranta, Hari na zaune a waje suna hira Azi ya shigo, Hari ta kalleshi yace “Binta fa?”

Binta? Cikin mamaki tace “tabi yarima tun rana.”

“Yarima? Yanzu kuma shiyake nemanta.”

Mikewa tai da sauri suka fito tare, Junaid na zaune suka shigo, kallan Hari yai yace “tana ina?”

Hari tace “ta bika ai.”
Junaid yace “ni? Yaushe?”
Tun rana.
Mikewa yai da sauri tace “bansan waye a gabanta ba amma ba ita kadai ta fita ba.”

Hankalinsa ne ya tashi yace “tun rana?”
Tace “eh wlh tun rana.”

Da sauri Junaid ya fito Azi da Hari ma suka rufa mai baya, nan suka fito waje, Junaid yce “mu nemeta a hankali, kar hankalin wasu ya kawo kanmu.”
Sukace to.

Nan suka fara nemanta sai dai duk inda sukabi babu alamunta ga guri kato, Junaid kam hankalinsa ya tashi ya nufi gun bishiyarnan sai dai ba ta gun, nan jikinsa ya kara sanyi, badai jin abinda ke faruwa wani ya mata wani abun ba?

Kalaman Sarki ne ya fado mai, hankalinsa ne ya kara tashi, Hari dake ta nemanta itama itace ta zo wucewa ta bangaren Raga, kamar zata nufi gun sai ta juya tana tunanin me zai kawota gun, harta juya taji ana dan buga kofar kadan, kasancewar dare ne sai ta kara waigawa cikin dan fargaba, ji tai an kara bugawa kadan, a hankali ta nufi kofar gun, tace “Binta?”

Daga ciki wacce ta gama galabaita ta kasa komai sai kokarin buga kofa da take da kyar, tace “naaam.”

Da sauri Hari ta zari ichen da aka sa aka tare kofar, Binta ta gani a bakin kofa, da sauri ta riketa tace “Binta? Me kike anan?”

Kallanta tai a galabaice tace “bansani ba nima, Hari ruwa ruwa.....”

Hari ta taimaka ta dagata ta ririke hannunta, suka fara takawa a hankali, Hari tace “wani mara imanin ne ya kulleki?”

Binta cikin dauriya tace “Barira ce.”

Da sauri ta kalleta tace “Barira?”

Kai ta daga mata alamar eh, Hari tace “karki fadama Yarima Barira ce.”

Kamar zata tambayeta dalili sai ta kasa saboda karfinta dake tafiya.

Suna shawo kwana Junaid na shawo kwana, da sauri ya karaso inda suke, kallan Binta yai wacce ta kalleshi itama tare da kokarin yin murmushi, ya kalli Hari yace “meya faru?”

Hari tace “watace ta kirata akan tazo injika shine ta kulleta.”

Kallanta yai cikin tausayawa dan ya san shiya ja mata yace “muje ta kwanta.”
Nan suka karasa, suna tafe yana tunani kala kala a kansa har suka isa.
Harira tace “bari na wace da ita can.”
Kai ya daga

Please Login or Register in order to submit comment