Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"bakomai, ko baka sameshi ba akwai masu kawoshi."

Kallansa yai cikin mamaki yace "su wa?"
Junaid yace "inata nemanka ne dan ka samin ido ka dubamin bangaren Gimbiya da bangaren Hajjo, amma yanzu kaje ka huta zuwa dare tukun."

Azi yace "na taho dashi ai."

Ka taho dashi? Ya tambaya gabansa nadan faduwa kadan.
Azi yai kasa dakai yace "Sabisu kanin mahaifina ne shiyasa kana fada nasan inda zan sameshi, yanzun ma dan baiyarda ya taho bane saboda yana tsoron abinda zai faru dashi, sai dana zauna na shawo kansa tukunna tuba nake ranka ya dade.”

Kallansa Junaid yai yace “Kanin mahaifinka?”

Azi yai kasa dakai cikin daukan laifi.
Junaid yace “yana ina yanzu?”

Yana can waje, a boye, bansan meke faruwa ba amma yace “baisan kowa ya ganshi.”
Junaid yace muje na shigo dashi dakaina.”

Fitowa sukai suka je inda Sabisu yake, Sabisu babban mutum ne dan a kalla zai kai shekaru 60, Junaid cikin girmamawa ya gaisheshi.

Kallansa yai cikin jin dadin ganin Junaid yace “Yarima! Ashe zan ganka kafin lokaci na yayi?”

Junaid ya kamo hannunshi yace “kayi hakuri duk da bansan meke faruwa ba amma nasan dalilin abinda ya faru ne ka bar masarautar nan.”

Shiru yai tare da sauke kansa kasa, Junaid ya kalli Azi yace “mu shiga.”
Nan suka shiga Junaid na gaba, su Azi sun ba Sabisu kayan hadimai ya saka, haka suka shigo cikin dari, sunyi sa’s suka wuce bangaren Junaid.

Junaid ne yasa aka kawo mai abinci, sai dayaci sannan ya kalleshi yace “Baba kayi hakuri amma na rasa meyasa nake da tambayoyi dayawa akaina game da masarautar nan.”

Sabisu ya kalleshi yace “Yarima ya akai ka dawo?”
Junaid ya bashi labari a takaici.
Sabisu cikin jinjina kai yace “Alhamdulila da baka dawo ba sai daka mallaki hankalin kanka.”
Junaid ya kalleshi duk da gabansa na faduwa saboda tsoron abinda zai tono amma yace “Sabisu kasan meyasa mahaifina ya kaini can wani gari? Ba da sanin mahaifiyata ba?”

Sabisu yai shiru kafin ya kalleshi yace “Yarima!”
Junaid ya maida jankalinsa kansa yace “ka sanar dani, koma menene zan dauka.”

Ajiyar zuciya yai yace bakomai na sani ba sai dai zan sanar dakai abinda na sani.

Junaid ya tattare hankalinsa kansa cikin danne damuwar dake ransa.
Gimbiya ta dade tana neman haihuwar da namiji sai dai a duk sanda ta haihu cikin rashin sa’a sai ta haifi mace.
Sannan abin ya dameta haka ma mai martaba saboda yasan irin san da Gimbiya kema Abdulsalam amma saboda burin zama matar sarki uwar sarki yasa ta ajiye komai ta aureshi.
Sarki Zubair na tsananin san Gimbiya, haka sukai ta fama amma duk sanda ta haihu sai dai ta haifi mace, daga bayama haihuwar ta tsaya, dan sai datai shekara hudu sannan ta sake samun ciki.
Wannan cikin data samu yazo mata da matsala sabods tasha wahala akansa burin su kawai wannan karan a dace a samu d’a namiji.
Cikin yardar Allah Gimbiya ta haihu ta haifi d’anamiji, sai dai abin mamaki da tsoro yaran yazo ba lafiya, tunda aka haifeka bakai kuka ba sannan bakai bayan gida ba, bayan haka yanayin yanda kake numfashinka ba daidai yake fita ba.
Sai dai wannan rashin lafiya taka Azima ta sa an boyeta, dan inba ni da Mai martaba ba bawanda ya sani a iya sanina kenan.
Sarki yasa an nemo masu magani cikin sirri amma abu yaki yiwuwa.
Duk an fara cire rai dakai, dan har ta fara hakura akan a sanar da mutane dan da alama bazakai rai ba.
Kwatsam wata rana Abdulsalam ya ziyarci Mai Martaba, tun daga sanda ya fito daga bangarensa ......”

Shiru yadanyi tare da dan share kwallarsa, Junaid wanda gaba daya yake jin kalaman Sabisu a kwanyar kansa yace “inajinka.”
Sabisu ya cigaba “Tundaga wannan lokaci Sarki ya fara rashin lafiya, sai dai abin mamaki randa ya kwanta rashin lafiya ranar kai kashi, haka dai ya cigaba da daurewa sai dai mu munsan yanda yake jinya, yana jinya kai kuma kana samun sauki, ranar yana tashi daga bacci ya umarci a fara gini a filinsa dake cam wani kauye, tun daga nan kuma lamari sarki ya canza, kullum zaka sameshi shiru yana tunani.
Ciwon sa baya tashi sai dare, yasha wahala matuka sai dai da safe inka ganshi bazaka gane ba sai dai ramewa dayai.
Sarki ya hana matansa kwana a bangarensa sai dai adanyi hira sannan su koma.
Ka samu lafiya sosai, hankalin kowa ya kwanta banda Sarki dake ta fama.
Akwai wata rana da ya zauna shi da Shamaki nada bana yanzu ba, tun daga wannan rana Sarki ya canza kwarai da gaske, ya fara janye jikinsa daga kan komai, sai ya zauna yai shiru yana tunani.
A lokacin kana shekara 7 ciwonsa ya tsananta, har Allah ya dau ransa.”

Shiru Junaid yai gaba daya ya kara sashi a duhu duk da dai ta wani bangaren ya dan warware masa wasu abun, kenan shi dan Zubair ne da Gimbiya na gaskiya.

Kallansa yai yace “bakasan me suka tattauna ba?”
Sabisu yace “bansani ba Yarima, sannan sai da mai martaba zai rasu ma Abdulsalam ya kira.”

Azi, Junaid ya kirashi, da sauri ya shigo yace “ka kai Baba ya huta a bangarenku, kar ka bari wani yasan wanene shi, sannan inda dama ka zauna dashi.”

Azi yace “angama ranka ya dade.”

Tare suka fita Junaid yai shiru yana nazarin gaba daya a binda yake kwakwalwarsa, indanunsa ya rufe yanna tattara tunaninsa, yafi tsawon awa biyu a haka kafin a hankali naga ya bude idanunsa.

Idansa ne naga yai jaaa sannan ya mike daga inda yake.
Fitowa yai Hadimansa suka taso da sauri.
Azi wanda ya zo gunsa ne ya matso yace “Yarima!”
Junaid ya kalleshi yace “Dawo da shi dakina.”
Dakinka?”
Azi ya tambaya, Junaid yace “eh yanzu.”

Nan Azi ya juya da sauri, fuskar Junaid kadai xaka kalla kasan ba wasa a tattare dashi.
Ba a jima ba sai ga Azi ya dawo da Sabisu, nan suka shiga ciki, Junaid yace “ka zauna anan.”

Nan yace ina na isa zama a bangarenka?
Junaid yace “ina tsoron abinda zai faru kana can ne.”

Sabisu ya jinjina kai, Junaid ne ya kalleshi cikin nazari yace “Akwai maganin da ka sani wanda yake amfani da jinin wani?”

Gaban Sabisu ne ya fadi ya kalli Junaid yace “me kake nufi Yarima?”
Junaid ya kalleshi yace “idan baka sani ba shikenan.”
Ya juya, Sabisu ne yace “sai dai masu sidabaru.”

Junaid ya kalleshi baice komai ba ya fito, bangaren Azeema ya wuce kai tsaye.
Tana zaune cikin bacin rai tana tuno abinda sukai da Mahmud yanzu.
tace “kana nufin Hajjo ta daukeshi kenan?”

Mahmud yace bansani sai dai ina zuwa kauyen ance wani yazo wai Hajjo ce ta aikoshi.”

Azeema ta sauke ajiyar zuciyarta, me Hajjo take sanji?
Barira ce ta sanar da isowar Junaid hakan yasa ta gyara zamanta tare da daidaita tunaninta.
Junaid ne ya shigo cikin dakinta.

Cikin nuna farin ciki tace “Junaid.”
Zama yai sannan ya gaisheta, amsawa tai tace “kwana biyu banjika ba.”

Kallanta yai ya kura mata ido, wanda har tadan sha jinin jikinta tace “Junaid!”

Sanda ina karami banda lafiya ya akai na fara samun sauki lokaci guda? Bayan alokacin an hakura da yin magani?”

Gaba daya jikin Azeema ne ya fara rawa, hannunta ta hade ta matsesu tana kokarin danne fargabar kalamansa wanda bata taba tunanin ji ba.

“Zan fado kamar haka, Wata taga dan data jima tana nema yazo ba lafiya ga wanzamai da duk wasu masu magani sun kasa warkar dashi, hakan yasa ta nemi zuwa gun malaman tsubu, ta nemi wanda ta yarda dashi sukaje gun su biyu, bokan tsubu yace mata in tanaso danya ya warke to lalai sai ta sadaukar da jinin daya daga cikin iyayensa.
Saboda tsoro da fargabar jin abinnan yasa ta dawo tare da hakura da abinda take nema.
Sai dai tasan wanda ta dauka bazai iya jurar ganinta cikin wani hali ba, hakan yasa ya koma ya nemi ai amfani da jinin mahaifin yaran, aiki ya fara ci daga sanda aka fara amfani da mahaifinsa.

Haka rayuwar mahaifinsa ta karkare shikuma dan ya samu sauki.”
Idanunsa ya dago wanda sukai jaaaa sosai kai kace garwashi ne, yace “ Watan nan Umma ce, wanda ta yarda dashi Abdulsalam ne, sannan mahaifin Zubair ne.”

Kafafunwanta ne suka shiga rawa hankalinta yayi kololuwar tashi, gaba daya ta kasa magana saboda gaba daya ta kasa daidaita tunaninta, bata taba tunanin wannan rana zatazo mata a duniyar nan ba.

Junaid ya runtse ido wasu zafaffan kwalla ne suka zubo mai yace “kina tunanin abinda kikai kin cici danki ne saboda kina sansa? Ko kina tunanin abinda kikai Abdulsalam ya aikata ne saboda yana san danki? Ko kina tunanin Zubair be san me kuka aikata ba?”

Hankali a tashe ta sauko kasa, ta fara girgiza kai tace “Junaid Allah bansan komai ba, bani nace Abdulsalam ya koma ba, Allah bansan wannan abun ba.”

Hannunsa ta kamo ya kwace hannunsa yace “baki sani ba? Bayan kinsan Abdulsalam yana sanki? Sannan ke a naki tunanin Abdulsalam sabods ke kadai yai haka? Kina tunanin kece kikai amfani dashi?”

Kallan Junaid tai tana hawaye, kai ya girgizs mata yace “ko daya, kece akai amfani dake, kece Abdulsalam yai amfani dake.”

Me kake nufi Junaid?”

Mikewa yai cikin takaici yace “kiyi tunani dakanki, wannan abinda kika aikata bazan yafe miki ba, kina tunanin kuyi amfani da rayuwar mahaifina sannan kuyi tunanin zanyi rayuwar data dace? Saboda burinki nasan danki ya zama sarki?”

Yanda yai maganar karshe kai kana ji kasan zuciyarsa ta gama raunana da bakinciki.
Hawaye ne suka zubo mai yace “Daga ke har Abdulsalam da duk wani mai hsnnu aciki banaji zan iya yafe muku.”

Kafin ta bude baki tai magana yabar dakin.

Yana fitowa yai bangarensa, duhu duhu ya shiga gani saboda kansa dake juyawa.

Hannu yasa ya rike bango da sauri kansa na wani irin sarawa, gaba daya baya gani sosai......

****
Ayusher🏌🏻♀️
****


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*


{39}

Dakyar ya kai kansa ciki, yana neman faduwa Binta wacce ta fito ganin yanayinsa yasa ta matso da sauri, yana kokarin faduwa ta rikoshi da sauri, kallanta yai bakinsa ne ya shiga rawa, Yaya!

Hannunta ya rike da karfi, ya nuna mata bangarenta.

Rikeshi tai sosai suka shiga ciki.
Tana rufe kofa ya zube ya zauna a kasa.
Mamaki ne ya kamata tace “Ya Junaid!”

Dagowa yai ya kalleta kawai hawaye suka shiga gangaromai, gaba daya ya rasa ta ina ma zai fara.

Ganin yanda yake kuka ne hankalinta ya tashi karara, zama tai kusa dashi a hankali ta sa hannu kan fuskarsa, samun kanta tai da zubar da hawaye.
Hannunsa yasa a kan hannunta cikin rawar baki ya kalleta yace “Binta.......”

Kuka ne ya kwacekai wanda ya kara daga mata hankali sosai.

Kansa ya sa akan kafadarta yana kuka, itama hawaye kawai take tana shafar bayansa dan sam ta kasa magana.

Ya dade a haka dan sunyi kusan awa daya a haka kafin ya share kwallarsa, dagowa yai ya kalleta tana hawaye, a hankali ya kakaro murmushi ya mata.
Hannunsa ya daura kan fuskarta yace “kukan me kike?”

Wasu hawayen ne suka gangaro tace “Nima bansani ba Yaya, zuciya ta na kuna ganin kana kuka, ban taba ganinka cikin irin wannan halin ba.”

Hannu yasa ya share mata hawayen sannan ya jawo kanta ya daura goshinta akan goshinsa, hakan yasa suna jin numfashin juna yace “Binta!”
Hmm tace dan ta kasa amsawa.
Yace “Bazan iya yafe musu ba dukansu.”

Suwa? Ta tambaya cikin sanyin murya, idanunsa ya runtse cikin kunar zuciya yana tuno abinda ke faruwa.

Dago kanta tai ta rungumeshi, kasa magana tai sai kankameshi datai a jikinta.
Idanunsa kawai ya rufe yana kara maimaita bazan yafe musu ba........

Dagota yai kawai ya mike tsaye, kallansa tai tace “Yaya!”

Murmushi yai yace “nagode Binta, samun ki kusa dani ba karamin karfi ya banni ba.”

Kallansa take haryanzu batace komai ba, zan wuce.
Kai ta daga alamar to, ya juya ya wuceta zai fita.

“Bazaka fadamin abinda ke damunka ba?”

“Zan fada miki amma bayanzu ba.”

Ya bude komar ya fita.

Da kallo ta bishi ta kasa tashi a gun, bata taba ganinsa yana kuka ba tunda take dashi, meya sameshi?


*******
Bangarensa yaje, yai Sallah sannan ya ma Sabi’u sai da safe ya fito.
Bangaren Zeena suka nufa wacce tasha wanka cikin ruwan dayasha hadin turare, sannan ta turara jikinta da turaren jiki.

Ba kwalloya tai na sai dai kamshin da take duk wanda ya ji sai ya yaba, ta taje kanta ta daureshi da ribon.

Abincin daren dake ajeye a gefe ta kalla sannan ta kalli Fure tace “Ya Junaid haryanzu?”

jeFure ta sake fita sannan ta dawo tace “inaji yana hanya.”

Kallan Fure tai tace “lekamin bangaren yarinyarcan ko yana can.”

“Ah hb Gimbiya ai yasan kwanankine ya za’ai yaje can?”

Wata harara ta buga mata tace “sau nawa nace ki dai fadamin abinda zanyi? Kinsan Allah kin kosa komawa gun Hajjo na canza ki.”

Da sauri Fure tace “bari naje na dubo.”

Tana fita falo taji ana sanar da isowar Yarima, Junaid ne ya shigo ya wuce ciki.

Zeena wacce dadi ya kamata ta mike tsaye tana jiranshi.

Yana shigowa ya kalleta, kallansa tai itama cikin jin dadi sannan ta kamo hannunsa tace “Yaya ka iso?”

Kallanta yai sannan yadanyi murmushi tare da kokarin zare hannunsa.

Hannun ta sake rikewa sannan ta jashi zuwa inda aka jera abinci.

Zama yai sannan ya kalleta.
Kusa dashi ta zauna cikin salo da jan hankali ta zuba mai abincin sannan ta tura gabansa.

Shiru yai ya kurawa abincin ido yana nazari, spoon din ta dauka ta diba sannan ta nufi bakinshi dashi.

Kallan spoon din dake gabansa yai yana nazarin yaushe ma rabandayaci abinci yau?

Karasa da spoon din tai daf da bakinsa hakan yasa ya kalleta sannan yasa hannu ya amshi spoon din yaci.

Murmushi tai sannan cikin jin dadi tace “Yaya da alama Hajjo bata sameshi ba, dazu Fure dana aikata tace ran Hajjo a bace yake.”

Kallanta yai sannan yace “ko?”

Kai ta daga tace “bansan ya akai ba, kuma Ramlatu ta tabbatar min yana can.”

Kallansa ta sakeyi tace “kana tunanin wani ya daukeshi?”
Kila!
Kawai yaci sannan ya ajiye spoon din ya mike yana kokarin zare hiramin daya yafa a kafarsa.

Mikewa tai a hankali tasa hannu a ta zagayo dashi ta cikinsa, ta kwantar da kanta a bayansa tace “ Ya Junaid.”

Shiru yai baice komai ba, tace “ Ya Junaid!”

Juyowa yai ya kalleta ta sake zagayeshi ta bayansa hannu yasa zai zare hannunta ta sake hade hanayenta da kyau.

Idanu ya kura mata yana tuno abinda akai domin sa? Anyi amfani dashi an salwantar da mahaifinsa.

Gaba daya yanayinsa ne ya canza, idanunsa ya runtse da karfi, sannan yace “kiyi hakuri Zeena amma plz ki bani aran kwana uku.”

Kwana uku? Ta tambaya cikin mamaki.
Hannunta ya zare sannan ya ajiye hiramin ya kwanta akan kujera yace “kwana biyu naki na binta daya kenan, kiyi hakuri.”

Shiru tai tana kallanshi cikin rashin jin dadin abinda ke faruwa.

Daurewa tai ta matso tace “naji amma ka dawo gado mu kwana tare.”
Hannunsa dake kan goshinsa ya sauke ya kalleta.
Tace “bansan meya faru tsakaninka da Binta ba smms na tabbatar baka batta ta kwana ita kadai ba.”

Ta dauka zaice wani abin sai gani tai ya mike ya kwanta akan gado.

Haka zaka kwanta bakaci abincin bs?

Idanunsa a lumshe yace “banajin ci.”

Shiru tai tana kallansa.......

*********

Gaba daya Azeema ta kasa zaune ta kasa tsaye, tama rasa meke damunta, ji take kamar zatai hauka.

Tayi kuka harta gaji, bata taba tunanin akwai wannan ranar da Junaid zai ji wannan kazamin al’amarin data dauka ita kadai tasan sirrinta.
Meyake nufi da Abdulsalam yayi amfani da ita?

Gsba daya kanta ya kasa nutsuwa, Bayan sallar magrib Barira ta shigota sanar da ita zuwan Hajjo.

Gaba daya batajin ganin kowa saboda abinda ke damunta sai dai ta tabbatar in taki ganin Hajjo zatai zargin wani abin.

Haka ta fito gaba daya jiki a sanyeye sai dai tayi kokarin danne wa.

Hajjo na zaune a falo Azeema ta shigo ta zauna.

Hajjo ts zuba mata ido tace “Ina kika boye Sabisu?”

Kallanta Azeema tai tace “mene?”

Hajjo cikin gadara tace “badai sirri kuke boyewa ke da Abdulsalam ba?”

Azeema ta daure tace “ke da kika dauke Sabisu shine kikazo dan ki sanar dani ko me? In kin kama sabisun me kike tunanin boyewa?”

Kallanta Hajjo tai sannan tai dariya tace “mene?”

Azeema ta daure itama tai dariya tace “inkin gams tambayoyin da zakimai kya aikon dashi.

Ta wuce ciki, Hajjo cikin kufula ta dau filo tai cilli dashi.

********

Yana sallar asuba ya nufi bangaren Sarki dan kwana yai yana tunanin abinda zaiyi, yanzu kuwa ya gama tattare nazarinsa.

Sarki mamaki ne ya kamashi jin Junaid na neman iso da duku dukun safiyar nan.

Junaid ne ya shigo ya gaisheshi sannan ya zauna.

Sarki ya zauna yace “Junaid ya akai?”

Kallansa Junaid yai batare da ya dauke idanunsa ba.

Sarki cikin mamaki yace “Junaid!”

“Me Marigayi ya sanar dakai lokacin da zai ce ka daukeni ka kaini kauyen nan?”

Kallansa Sarki yai yace “me ya sanar dani? Ba abinda yacemin ka dauka yabar wasiyya ne?”

Junaid yai murmushi tare da sauke kansa kasa, kafin ya hade fuska tamau yace “ Ka dauka abinda kuka aikata ba wanda zai sani har duniya ta nade?”

Gaban Sarki ne yai wani mugun faduwa kallansa yai ya kasa cewa komai yana nazarin meya sani?

******
Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{40}

Sarki yadan gyara nutsuwarsa yace "Junaid wani shirman ka jiyu? Ina tunanin kai ka girmi aikata irin wadan nan shirmen."

Shirme?

Sarki yace "to nakasa gane me kake san cewa ne gaba daya."

Junaid ya kalleshi sannan yace "ko mu bari anjima mu hadu a fada?"

Abdulsalam cikin faduwar gaba yace "mu hadu a fada ayi me?"

Cikin zazzafan takaici da raunin zuciya ya kalleshi, idanun Junaid gaba daya suncanza sunyi jaa sosai, ya kalleshi bakinsa na rawa na bakin ciki yace "bakaji kunyar kallan Umma dani ba? Baka taba kunyar halakar da mijinta da mahaifina ba sannan ka kallemu kamar ba komai?"

Hankalin Sarki ne ya dugunzuma ya tashi ya daure yace "nifa harayanxu......"

Cikin zafin rai Junaid ya katseshi yace "na hadu da Sabisu, ko haryanzu zaka cigaba da karyatawa?"

Hankalin Sarki yanzu kam kiri kiri ya dugunzuma, yace "Sabisu? Waye hakan?"

Junaid cikin mamakin abinda yace yai dan murmushin takaici yace "ta ina zaka sanshi dama? Kafin in sanar da mutane mugun abinda ka aikata kai gaggawar ajiye mulkin da ka kashe mahaifina duminsa, sannan ka jira hukuncin da ni saban sarki zan maka."


Sarki yanzu ya fahimci inda Junaid yasa gaba, kallansa yai yace "komeya faru na tabbatar baka san mahaifiyarka bace sila? Sannan a dalilin ta cece ka ne akai wannan mumunan abin, shikanshi Zubair din daga baya yasan abinda ya faru."

Cikin tsananin raunin murya Junaid ya kalleshi yace "Abba ya sani?"

Abdulsalam yace "ya san abinda mahaifiyarka ta sa ayi, hakan yasa ya daukeka ya bani na boyeka."

Ha ha ha.....wata irin dariyar bacin rai Junaid yai yace "a naka rashin fahimtar haka ka dauka?"

Abdulsalam ya hade rai yace "me kake san cewa?"

Junaid ya kalleshi cikin zafin rai yace "Ya baka nine yana san ganin iya kacin sanda zakai nadama, sannan ya daukeni daga gunta ne dan ya nuna mata ta nustu ta fahimci halayenka, kana tunanin ya yarda da duk abinda ka fadamai ne?"

Abdulsalam idanunsa ne suka fara canzawa ya turbune fuska yace " ka shiga hankalinka Junaid, duk sanda nakewa Azeema bais yafema danta ba in ya nemi shiga hurimina."

Junaid ya kalleshi yace "ni nawa hurumin daka shiga fa?"

Huruminka?

Junaid cikin zafi yace "mulkin naka ne? Ko kana tunanin badan Hajiya Inna ta rikeka ba har zaka samu damar kai kanka wannan matsayin?"

Yanzu kam hucci kawai yakeyi, Junaid ya kalleshi yace "kai gaggawar sauka daga kan mulkin nan, kwana uku na baka, zanga da wani fuska zaka kalli mutane in sukasan tsubu kukai kuka halaka Sarki Zubair, daga kai har mukarabanka su Shamaki da Waziri da kuka hada baki."

Juyawa yai ya fice.

Ya akai ya san komai yaran nan? Ya tabbatar Sabisu baisan ko rabin abinda ya faru ba, ya akai ya sani? Azeema?


Cikin hanzari ya mike ya nufi bangarenta.

Tana kwance akan gado tsabar damuwa har dan zazzabi ne ya rufeta.

Tana kwance ya shigo, idanunta ta sauke kansa cikin zargi ta zuba mai ido.

Shigowa yai ya zauna kusa da ita, yace "kin fadawa Junaid komai hankalinki ya kwanta?"

Kallansa tai idanunta sun ciciko tace "kenan amfani kai dani ka kashe sarki a matsayin ka ceceni saboda san da kake min?"

Abdulsalam ya kauda kai, mikewa zaune tai cikin takaici tace "yaune rana ta farko dana taba dana sani san da na maka a baya ina mugun dana sanin aurenka da nai, wadan nan sune babban kuskuren dana tafka a rayuwata, wanda bazan taba yafewa kaina ba."

Abdulsalam ya kalleta zuciyarsa na kuna yace "saboda wa na aikata duk abin da na aikata? Ko kina tunanin saboda kaina nai? Duk abinda na aikata nayi ne saboda tsananin sanki da nake, ko kina tunanin zan iya cigaba da ganinki tare da Zubair ne? Sannan saboda wa na aikata abinda na aikata."

Ranta a bace ta sa hannu ta tureshi, tace "karka kuskura kace saboda nine, a haukata da haka na dauka amma yanzu nasan babu ni a cikin tunaninka, kayi amfani da halin da nake ciki ne ka biya burin dake ranka."


Sarki ya kalleta yace "koma menene yanzu bashida amfani, abinda ya faru ya faru, ki fadawa Junaid ya manta komai, yazo yana min kashedin na ajiye mulki nan da kwana uku, ke kinsan ba abu mai yiwuwa bane kinsan halina kinsan abinda zanyi da wanss bazan ba."

Ya juya ya fita, ihu ta kwalla tare da sa kanta cikin cinyarta.
******
Hajjo ce ta kalli Zubair tace "da sassafen nan?"

Zubair yace "da kaina na ganshi Hajjo, bansan me suka tattauna ba amma ransa a bace naga ya fito."

Hajjo tace aika a tambayo Zeena muji ko ta sani, kallanta yai yace "wannan yanda take san Junaid zata fadi wani abu ne?"

Hajjo cikin kuluwa tace "aka mugani ko za'a dace "


Junaid yana fitowa ya kalli bangaren Binta, ya kalli na Zeena, sannan ya kalli nashi sanda ya boye Sabisu, Binta yake san gani amma yana tsoron sata cikin wani hali, bangaren Zeena ya wuce. Sai yanzu tai sallah, tana kokarin kwanciya taga anbude kofa anshigo.

Cikin mamaki da jin dadinta kalli Junaid, bata taba kawowa zai dawo ba.

Tunawa yai ashefa yar Abdulsalam ce ko?

Juyawa yai da sauri ta sako tace "Ya Junaid."

Kallanta yai ta matso cikin jin dadi tace "nagode daka dawo."


Ya zataji in taji mugun halin babanta?

Zeena ce ta kalleshi tace “Ya Junaid?”

Kallanta yai yasan tabbas batada matsala duk rashin tarbiyya na gari ne ke damunta sai babbar matsalarta isa data mata yawa da rashin hakuri, kallanta yai sannan ya wuce ya kwanta.

Kaina kedan ciwo nake san kwantawa.

Cikin jin dadi ta matsa kusa dashi ta kwanta sannan ta kankameshi.

Kamar zai tureta sai kuma ya fasa hannu yasa ya riketa, ajyar zuciya tai na jin dadi.

Tausayinta yake, yasan itama sai ta shiga wani hali.

Bacci ne ya daukeshi dan dama baiyi bacci ba jiya.


Yana tashi yaga bata nan, ruwa yaji a toilet da alama wanka take, fitowa yai ya bar mangaren.

Hadimans suka bi bayanshi.

Bangaren Binta ya kalla, kamar ya je kamar kar yaje, daurewa yai kawai ya kalli Hadiminsa yamai alama.

Nan suka sanar da zuwanshi.
Binta wacce tai wanka tana zaune tasa abincin safe a gaba tana jujuyawa, jin Junaid yasa ta tashi cikin hanzari ta bude.

Yana shigowa ya kalleta yana dariya yace “ya ganki kinyi wani iri? Kamar mara lafiya?”

Shiru tai kawai tana kallansa, Ahhh tunda ba’a san ganins da alama bari na juya.

Da sauri tace “a’a yaya.”
Juyowa yai yana dariya yace “na sani ai.”

Rungume ta yai yace “ina wannan zatace batasan ganins?”

Tace “in nace fa?”

Yace “hmm duk randa kika fada kinada kyauta.”

Dagowa tai tace “ka tabbatar?”

Yace “sosai.”

Murmushi tai sannan tace “Yaya komai dai lafiya ko?”

Kara rungumeta yai yace “komai zai zama lafiya insha Allah.”

Murmushi tai sannan tace “Allah yasa.”

Kallanta yai yace “inata san na tambayeki, kin tabbatar bakyasan a aikama mahaifinki kinyi aure?”

Kai ta girgiza da sauri tace “in ma

Please Login or Register in order to submit comment