Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamar to, suka wuce.

Shiru Junaid yai harsai da suka rufe kofa sannan ya juya ya shiga ciki.

Zama yai akan kujera tare da hada hannayensa, tabbas Hajjo ko Zeenatu ne suka aikata hakan, sannan dolene ya canza takunsa tunkafin Binta ta rasa ranta a dalilinsa.

Shiru yai yana tunani, ke din? Kalaman Sarki ne suka fadomai, kai ya girgiza da sauri yace “ba ita bace, wadancan biyu dai a cikinsu ne.”

Inhar yanaso ya kare Binta to lalai dole ya fahimci masarautar nan ya kuma san abinda ya dace yai.

Azi? Kiransa yai, wanda ke waje.

Shigowa yai ga zube a gabansa, Junaid ya kalleshi yace “Azi fadamin me ka sani a game da masarautar nan?”

Azi yai shiru kafin yace “bansan abubuwa ba saidai nasan kana tsakiyan makiyanka.”

Junai ya kalleshi yace “nasan wannan amma me kake tunani a tattare da ita?”

Azi yai shiru can yace “karka yadda da kowa.”

Junaid yai murmushi yace “tashi kaje na yafe tambayar.”

Azi ya mike yai waje, Junaid ya kalleshi sannan ya mike ya shiga dakinsa........


Binta kam na shiga ta ci abinci ta sha ruwa dakyar tai sallah ta hau bacci.

Harira ta zuba mata ido tana kallanta, tana tausayinta sai dai ta tabbatar Azeema tanada hujjarta na kin yadda da ita, sai dai aganinta abin baikai haka ba, gwara tace ta tafi data nemi halaka ta.


******

*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin da Daya.*

Duk yanda Junaid yaso yai bacci ya kasa, wannan lamarin ya tsaya mai a rai, ance ya taho da mata, ance tanada ciki, sannan an kulleta.

Kenan nan gaba baisan abinda za’a iya yima Binta ba? Kawai a dalilinsa.

Acan bangaren Binta itama sam ta tunda ta farka cikin dare ta kasa bacci, juyi kawai take tana tunani metama mahaifiyar Junaid da zata sa a kulleta? Anya zamanta anan alkairi ne? Karfa ace ta zama wacce a dalilinta Junaid ya shiga wani hali.

Jitai kamar ana magana a waje mikewa tai a hankali ta leka windown dakin, Harira ce tsaye ga Azi a gefe, Azi yace “kiyi hakuri nasa kin taso.”
Tace “ban mayi bacci ba dama, abinda ke damuna nasan shine ya hanaka bacci.”

Azi ya kalleta yace “waye ya kulleta?”
Shiru tai kafin tace “Barira ce.”
Sam baiyi mamaki ba sai dai yace “zance har gun Sarki inaga yaje akan Junaid ya taho da mace a cewar wasu ma tanada ciki.”
Jikin Binta ne ya fara rawa, muryar Harira taji tace “yanzu lokaci ne na Junaid ya cire yarinta da rashin damuwar dake ransa, inba haka ba haka zai zama wanda bashida ra’ayin kansa, dan a hankali sai Gimbiya ta juyamai ra’ayinsa.”

Zubewa tai ta zauna, a hankali wasu zafaffan hawaye suka shiga zubo mata.


******

Me kake tunani? Ke mana Gimbiya ta
A hankali ta juyo da fuskarsa zata sumbaceshi, idanunta ta bude sannan ta kara maidasu ta rufe, hara budesu tai sannan a hankali ta mirgina akan gadan, saura kiris ta afka kasa ta danna kanta da pillow tare da yin ajiyar zuciya, meke damuna?

A hankali ta mike zaune sannan ta kalli kofa cikin gadara tace “Fure.”
Jin shiru yasa ta sauko daga kan makeken gadan naga sannan ta bude kofa.

Fure ce keta kokarin nuna musu inda zasu ajiye abinci, jin bude kofa yasa ta juyo, ganin Zeena yasa ta taho da sauri.

Zeena tace “Fure zo.”
Fure ta bita suka shiga ciki, zama tai a kan gadonta mika mata kafarta da sauri ta fara matsa mata su, Zeena ta kalleta tace “Fure me kike tunani tsakanina da Yarima?”

Ba tare da wani dogon tunani ba tace “makiya?”
Kafa tasa ta hanbareta, Fure ta fadi, da sauri ta mike ta cigaba da tausar, Zeena ta hade fuska, Fure tace “Gimbiya badai kina tunanin wani abin bane bako?”

Kamar me?

Fure tace “bakomai dama a shirmenane nake tunani ko kina sanshi.”
Kara bigeta tai da kafa tace “ni nake sanshi? Bama shi ba? Tashi ki ban gun banamasan tausar.”

Da sauri Fure ta zube a kasa tace “tuba nake Gimbiya sai dai ina ganin in kinassn Junaid ai komai mai sauki ne indai yana sanki, inkuwa bayayi ki fadawa Takawa.”

A kufule tace “kina tunanin zan auri wanda bai sona? Kuma uban wa yace miki ina sanshi? Tashi ki fita.

Ta zube tana bata hakuri, Zeena a zuciya tasa hannu ta finciketa tai waje da ita ta rufe kofarta, zama tai dabas akan gado cikin kuluwa ta zauna agaban madubi, kanta ta kalla cikin takaici ta mike tai bandaki.

********

Kasancewar kasa bacci dayai hakan yasashi yin bacci sosai, dan sai da rana ta fito ma ya farka, a zabure ya mike yai sallah sannan ya kara kwanciya, bacci ne ya sake daukarsa sai dai bai dade ba yaji motsin bayi na gyare gyare hakan ya sashi farkawa.

Fitowa yai ya shiga yai wanka sannan ya shirya ya fito, bangarensu Harira ya nufa, Azi na ganin ya fito ya ajiye ban ruwan da yakeyi ya nufoshi, duk da bayin dake binsa a baya.
Junaid ya kalli Azi yace “zanga jikin Binta ne.”
Yace “ko a kirata?”
Bari naje.
“to Yarima, dama dazu aka aiko kaje bangaren Gimbiya kuyi karin kumallo.”
To kawai yace yai ciki.

Harira najin an sanar da isowar Yarima gun yasa ta kalli Binta dake kwance tace “Binta, yarima yazo.”

Kallanta tai tace “Hari kice ina bacci dan Allah.”
Cikin mamaki Hari tace “meyasa? Junaid ne fa?”

Murmushi tai wanda hawaye suka taru a idanta tace “dan Allah.”
Harira ta kalleta sannan ta mike tai waje, gaida Junaid tai sannan tace mai tana bacci tare da cewa “in ta tashi tazo.”
Junaid ya kurawa dakin ido sannan ya juya, Binta ce ta share kwallarta Hari ta shigo tace “Binta?”
Binta ta kalleta tace “taya yana Yarima zaizo nan? Ba gwara yace inzo ba? Hari bansan ya zanyi ba...........”

Kuka ne ya kunce mata, tausayinta ne ya kama Harira ta matso ta rungumeta, Binta tana kuka tace “bankai matsayin da zan wargaza mai rayuwar daya dace da ita ba......”
Harira tai shiru tasan tabbas hakane, amma ya za’ayi? Junaid da Binta sun taso tun basusan kansu ba, taya zasu amshi wannan saban yanayin?????


*********
Junaid kam yasan idan Binta biyu dan tun asali ko rashin lafiya takeyi bata taba kaiwa wannan lokacin tana bacci? Sai dai baisan dalilin sa shima nakin tilastawa sai ya ganta ba, yana fitowa waje yai suka nufi nangaren Azeema.

Azeema tana zaune akan kujerar ta tasha ado sosai kamar yadda ta saba tana zaune tana dan kada dan yatsanta, Allah ne kadai yasan me take tunani a wannan lokacin, barira ce ta matso tace “Gimbiya sun dauketa jiyan.”

Ba tare da ta bude ido ba tace “iyanzu nasan ya fahimci nisanci da itane kadai kwanciyar hankalinta, inba haka ba wayasan mezai sameta gaba.”

Barira tai murmushi tace “banaji tace nice na kulleta.”
Azeema tace “in ta fada kina tunanin shi zai yadda? Bayan yasan kina wajen wanzami lokacin? Kinga in ta fada alamace ta tana neman shiga tsakanina dashi, wanda har gwara tai shiru.”

Sanarwar isowar Gimbiya Zeena ne yasa Azeema ta bude idanunta a hankali, Zeena kuma?

Zeena ce ta shigo tasha kwalliya kai kace wani taro zata, alkyabar dake jikinta kalar sararin samaniya, Azeema ta zuba mata ido harta zo ta zauna, Fure ce ta ajiye kwanuka guda biyu.

Zeena ta gaishe da Azeema sannan tace “Umma karama jiya nazo gaisheki akace bakida lafiya shiyasa nasa a miki farfesu na kawo miki, nayi sa’a bakiyi karin kumallo ba.”

Azeema ta kura mata ido, wanda haryasata yin kasa dakai? Murmushi tai sannan tace “nagode sosai, Allah ya saka da alkairi.”

Zeena tace ameen, sannan ta mike tace bari naje.
Azeema bata tanka mata ba sai dai idanunta na kanta, yanda Zeena ke tafiya a hankali ne yasa ta fahimci batasan tafiya, har sai da Zeena taje bakin kofa sannan Azeema tace “ko zakici abinci damu? Duk da nasan ba lalai........”
Kafin ta karasa Zeena ta juyo ta kalleta tace “Ba wani abin?”
Azeema tai dariya a kasan ranta tace me kike shirin yi?
Azeema tace “ba wani abin, dama Junaid ne zaizo in ba wani abin ki zauna.”

Zeena ta zauna suka danyi shiru, sannan ta kalli Azeema tace “Umma karama naji ana zancen Ya Junaid ko yazo da yarinya ko mata?”

Azeema ta kalleta kamar bazata amsa ba sai tai murmushi kuma tace “wace mata ana zaune kalau? Yarinyace da ya taimaka daga can.”

A hankali tai dan ajiyar zuciya sannan ta kalli Azeema tana murmushi, Azeema cikin zargi tace “Hajjo tasan kina nan?”
Zeena tace “a’a amma in na koma zan fada mata, dama dubaki nazoyi......”

Sanarwar isowar Junaid akai, wanda yasa gaban Zeena faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba.
Junaid ne ya shigo, kallan Zeena yai cikin mamaki, Azeema tai murmushi tace “karaso mana.”

Junaid ya karasa ya zauna a dayan gefen, gaida Azeema yai sannan Zeena ce gaisheshi.

Kallanta yai sannan ya amsa, Azeema ce tace “ina Binta? Na dauka tare zaku taho?”

Yace “batadan jin dadi ne.”

Azeema ta kalli Zeena tace “ashe jiya Zeenatu tazo.”

“Eh kina bacci.”

Murmushi tai sannan ta mike tace “fara cin abinci bari nazo.”
Ta mike ta shiga dakinta, tayi haka ne dan tanasan fahimtar meke kan Zeenatu.

Zeenatu tana fita ta kalli Junaid tace “yaya na zubama?”
Kallanta yai bai tanka mata ba,tai shiru kafin tace “ zamuje yau din?”
Ina?
Ta kalleshi .
“ka manta? Nace zan kaika gun Hajiya Inna?”

Baice komai ba hakan yasa tace “ anjima da yamma sai muje?”

Kallanta yai yana tunanin itace? Itace ta kulle Binta?
Yanda ya kalleta ne yasa cikin salo tace “ya Junaid.”

“Kinsan Binta?”
“Binta? Wacece?”
Ido ya zuba mata ganin yanda fuskarta karara ta nuna alamar tambaya take yasa yace “shikenan.”

Ta bude baki zatai magana Azeema ta fito, kallansa tai bata ce komai ba.

Azeema ce ta kalleta tace “ya naga baku zuba komai ba?”

Nan Zeena tadan ja plate ta mikawa Junaid.


************

Mene? Zeena tana ina?

Zubair yace “yanzu naganta ta nufi bangaren Azeema.
Cikin zafi Hajjo tace “jiya mafa ance taje wai uban me ke kan yarinyar nan?”

Zubair cikin hasala shima yace “anya Zeena ba akwai abinda ke ranta ba?”

Hajjo ta tuno kalamanta datai rannan, shiru tai tare da dunkule hannunta.”

Zubair yace “akwai ko?”

Hajjo ta kalleshi tace “haukarta ce.”


*******

*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin da Biyu*


Azeema ta zauna sannan ta kalli Zeena wacce tai shiru ta kasa ko zuba abincin, Binta? Tunowa tai da yanzu Azeema ta tambayeshi ina Binta? Itace? Itace yarinyar daya taho da ita?

Ganin Azeema na kallanta ne yasa tadan zuba abinci kadan a plate juya cokalin kawai takeyi, Fure ce ta shigo tace “Gimbiya ana nemanki.”

Wa? Ta fada tana kallanta, Azeema tace “kije ki gani.”
Mikewa tai ta kalli Junaid wanda ko kallanta bai kuma yi ba, maida kallanta tai kan Azeema tace “Umma karama na wuce.”
Azeema ta daga kai alamar to, Junaid ta kalla tace “Zeena zata wuce “to kawai yace ya cigaba da tunanin da yakeyi, kenan Hajjo ce?

Haushi ne ya turnuketa ta juya ta fita, tana fita Azeema ta kalleshi tace “Junaid!”
Dagowa yai ya kalleta tace “baka huce da abinda ta maka bane?”
Wace?
Murmushi tai tace “shikenan.”

Yana gama cin abincin ya kalleta yace “zanje bangaren Hajjo.”

“Hajjo? Me zakaje yi?”
“Gaisheta zan na fahimci tunda nazo banje ba.”
Azeema kamar zata sake magana sai taga harya mike ma, ganin haka yasa tace “sai ka dawo.”
Juyawa yai ya fita, Azi ya kalla yace muje bangaren Hajjo.”

Zeena tana shiga bangaren Hajjo ta shiga jiki a sanyaye saboda gaba daya jikinta ya gama sanyi.
Hajjo ce ta buga mata wata muguwar harara sannan tace “uban me kikaje yi bangaren Azeema?”

Zama tai fuskarta duk ba dadi tace “Hajjo dan Allah ki kyale ni yanzu ni nanida karfin magana.”

Hajjo ta kalleta a fusace tace “yau zanje na fadawa Mai Martaba ya hadaki aure da Sulaiman ba tare da wani jiranki ba, tunda naga alama in aka barki Allah ne kadai yasan me zaki aikata.”

Kallan Hajjo tai tace “Sulaiman? Wallahi indai kuka auramin shi sai dai ku gai gawata gidan, ni mace ki barni da abinda ke damuna dan Allah........”
Bata karasa ba ta mike tai cikin daki ranta a bace, Hajjo ta bita da kallo cikin takaici sannan tai kwafa, tace wallahi baki isa ba, ki rasa wanda zakiso sai dan da ya ke neman toshewa yayanki gaba?

Tana zaune tana tunanin mafita taji ana sanarda isowar Junaid, tsantsar mamaki ne ya kamata amma ta daure ta nemi ya shigo, Junaid na shigowa ta saki fuska sosai tace “Junaid? Kaine da kanka?”
Junaid ya gaisheta sannan ya ja ya zauna.

Tunani ta shigayi badai shima Zeenatun yake so ba?

Junaid ne ya kalleta yace “a gafarceni tunda nazo bansamu nazo gaisheki ba.”
Murmushi tai tace “ai bakada lokaci ne ni na sani kana ta fama da kokarin daidaita zamanka da mahaifiyarka.”

Kallanta yai sannan yace “Eh da jiya naso zuwa to sai banga Binta ba hakan yasa muka shiga nemanta.”
Yai maganar yana kallan yanayinta, Murmushi tai tace “Binta? Ohhh wace kuka taho tare?”
Yace “eh.” Yadan yi dariya kadan yace “wasu harcewa suke wai na taho da mata.”

Hajjo tai dariya tace “kasan lamarin masarauta akwai gutsiri tsoma, amma ya Gimbiya taji? Suna neman lalatawa danta suna?”

Junaid ya kalleta sannan yai murmushi, baice komai ba.
Tace “irin wannan shi kesa a sa mutum yin abinda bai dace ba in mutum yaga ana neman lalata ma dansa mutuncinsa.”

Junaid ya kalleta sannan yace “Yarima Zubair fa?”

Tace “yana bangarensa,dazu ya barnan, Junaid a kokarta a dinga kula da Gimbiya Azeema dan ta shiga wani hali sanda baka nan.”

Junaid ya kalleta sannan yace “Da a koda yaushe ya kamata yasan me zaiyiwa iyayensa.”

Wannan kalmar taba Hajjo haushi sai dai bata nuna ba tace “hakane, kanasan wani abu a kawoma?”

Yace “a’a zan wuce ma.”

Mikewa yai, jiyai an bude kofa, kallan inda yaji motsin yai, Zeena data fito dan ta wuce bangarenta ne ta zuba mai ido, jitai batasan dauke idanta daga kanshi.

Junaid na ganin itace ya maida idansa kan Hajjo yace “na wuce, A huta lafiya.”

Tace “to a gaishesu.”

Zeenatu tana kallansa har ya fita ko waigowa baiyi ba, jitai idanunta suna neman cikowa kawai ta koma dakin ta rufe.

Junaid na tafe yana tunanin kalamanta, sannan ya hada da kalaman Mai martaba, yana tafe yana auna kalaman can da komai ya daidaita a kansa, yaja ya tsaya.

Azi ya kalleshi yace “Yarima lafiya?”
Junaid ya kalleshi, sannan yace “mu koma bangarena.”
“Ba zaka koma gun Gimbiya ba?”
Yace “anjima.”
Juyawa sukai ya wuce bangarensa, bai nemi Binta ba kawai ya shiga bangarensa ya zauna yana tunani, kenan Umma ce ta kulleta dan ta hukuntata akan abinda mutane ke zarginsa dashi? Kenan batasan Binta kamar yadda take nunawa?

Fitowa yai ya kalli wani bawa dake gefe yace “kiramin Binta.”

Bawan ya amsa da to sannan ya juya.

Tana zaune ta samu tai wanka tana shan kunu da kosai bawan ya sanar da ita Junaid na nemanta.
Kallansa tai tace “to.”
Yana juyawa ta kalli Hari sannan tace “Hari bari naje.”
Ajiye kofin tai sannan ta mike, Hari tace “sai kin dawo.”
Binta tai murmushin yake ta fita.

Junaid na tsaye ya juya bayansa a cikin falan yana kallan window, yana kallanta sanda tazo ta wuce, hannunsa daya ba baya, sallama tai, ya amsa ba tare da ya juyo ba.
Shigowa tai a hankali ta tsaya daga nesa dashi sosai tace “Yarima!”

Junaid bai juyo ba yace “Barira tazo nan jiya?”
Kallansa tai kafin tace “a’a.”
“Ya akai ke da bakida saurin yadda da mutane kikabi mutum ba tare da kin sanshi ba?”
Shiru tai kafin Tace “cewa akai inje injika.”

Yanzu kam juyowa yai gaba dayanshi ya kalleta, tana tsaye tana kallanshi itama, a hankali ya fara takowa zuwa inda take, duk taku daya ji take kamar da bugun zuciyarta yakeyi, yauce rana ta farko a iya tarihinta dashi data taba ganinshi haka ba.

Daf da ita ya matso hartana iya jiyo numfashinsa, gabanta ne ya tsananta faduwa, dagowa tai ta kalleshi.
Yace “waye ya jaki?”
Da kyar ta hadiye yawun bakinta sannan tace “koma wanene ya Junaid baya riga ya wuce ba? Sannan laifi nai shiyasa aka hukuntani, dan Allah kabar maganarnan a inda take.”

Ta fada tare da danyin taku daya zuwa baya, shima taku daya ya kara, ta kalleshi jikinta har rawa yadan fara tace “Ya Junaid!”
Yanda tai maganar kamar mai shirin yin kuka, kansa ya juya sannan ya furzar da wata iska ya kalleta yanayin idanunsa ya canza sosai, wanda ya kara tsoratata, tace “Ya Junaid!”

Bai tanka mata ba yanzun ma sai dai ya kara kallanta, bakinta na rawa muryarta na rawa tace “Ya Junaid dan Allah!”

Taku daya yai baya sannan ya kara wani dayan, kallansa tai tace “idan harba da kwakwaran dalili ba dan Allah kar kazo bangaren su Harira domin ni, sannan na koma can da zama, sannan kuma.....”

Shiru tai tana kallansa, ta daure saboda kukan dake neman kwace mata tace “dan Allah ka rage nemana, in kuma duk hakan ya gagara zan bar gidan nan.”

Tana kaiwa nan ta juya da sauri tai waje, tana fita tai bayan bangarensa da gudu, ta tsuguna ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, wannan shikadai ne abinda zata masa dan ta zauna kusa dashi, dan in har aka cigaba da yanda ake ta tabbatar wata ran ganinsa ma bazata tabayi ba, wanda a rayuwa bata tunanin zata iya kwana ta tashi bata ko sashi a idanta ba.
Kuka take sosai, ta toshe bakinta, gaba daya fuskarta tai jaa, kuka take har iya karfinta wanda duk wani mai tausayi inyaga halin datake ciki zai tausaya mata.

Junaid kam tana fita ya runtse idanunsa shima bai zataba yaji hawaye sun gangaromai, hannu yasa y taba su, sannan ya kalli hannunsa, inhar mahaifiyarsa zata aikata hakan saboda kawai ya damu da Binta to lalai gaba baisan mezata aikata akan hakan ba.

Kansa ne yaji yana sarawa, ya dauka ganinta zaisa hankalinsa dana Binta ya kwanta me ke shirin faruwa?????

Tabbas dolene ya janye Binta daga jikinsa harsai yakai matsayin da zai kwaceta batare da fargaba ko tunanin za’a mata wani abin ba, yau a wannan lokacin ya dau alkawarin tabbas shi Junaid sai ya ba Binta gatan da babu wace mace data taba samunsa, domin tun yana karami burinsa kenan, akoda yaushe yaganta cikin farinciki, yanzu me zai faru da Basu ganta ba jiya? Haka zatai ta zama harta mutu kenan???????



******
Ayusher
*****


🌞*ZAFIN RANA*🌞
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*

*23*


Azeema tana zaune tana jiran Junaid sai dai har dare ba alamarsa, Barira ta kalla bayan tayi sallar isha’i tace “Barira Junaid haryanzu?”
Barira ta sunkuyo tace “ko na je na kirashi?”
Azeema tai saurin cewa “a’a da alama yana can da yarinyar nan.”

Mikewa tai ta wuce dakinta ta kwanta zuciyarta duk ba dadi.
Bata dade da kwanciya ba bacci yai gaba da ita.
Yanda yake nufota ne fuskarshi tana gumi, gudu take hana binta, hannunsa ta kalla taga jariri a rike, gudu take tana keta cikin dajin nan har takai karshe.
Juyowa tai cikin tashin hankali tana hakki, hannayenta ta hade tana neman gafara.
Zubair ka tsaya kaji! Zubair ka........”

A firgice ta farka, da sauri ta jawo bargonta ta gangame jikinta wanda yake rawa, kamar a fili tai gudu nan dan gaba daya jikinta ya jike da gumi, idanunta sun kada sunyi jaa sosai.
Fitilar kwai dake gefenta ta murda da sauri haske ya dan zagaye dakin, shiru tai hankalinta a tashe ta zauna akan gado ta hade kafafunta, tunanin wannan mafarki, ta tabbatar duk duniya ba wanda yasan wannan sirrin to meke faruwa?

Shiru tai tana tunanin kalaman da Jakadiya ta fada mata, da sauri ta girgiza kanta alamar a’a.
Da kyar ta samu bacci ya dauketa a xaunen.

A hankali ta bude idanunta, ganin gari yayi haske ne yasa ta kashe fitilar sannan ta mike ta shiga bandaki.

*********

Fitowa tai bayan ta kimtsa, Barira da ragowar kuyangun ta nata faman gyara bangarensu.
Azeema ta kalli Barira wacce suka zube suna gaisheta suna ganinta.
Azeema tai murmushi tace “Barira kicewa Junaid anjima yazo muje ya gaida Hajiya Inna.”

Cikin mamaki Barira ta kalleta, tace “Gimbiya kinsan matar nan ba sanki take ba karta wulakantaki a gaban Yarima.”

Wani lalausan murmushi ta saka tace “ki sanar dashi.” Ta juya ta shiga ciki.
Barira tai shiru kafin ta aika a sanar da Junaid.

Junaid kam wanda yau ma baisamu baccin kirki ba, yana zaune yana kokarin karatan wasu littafai na tarihi da ya nemi Azi ya amso mai.
Nan Azi ga shigo ya sanar dashi sakon Azeema, yace “to.”

Sai daya gama karatawa zuwa inda zai tsaya sannan ya mike ya shiga daki yai wanka ya shirya, a ido inka ganshi bazaka taba kawo akwai abinda ke damunshi ba saboda babu yanayin komai a tattare dashi.

Karin Kumalo yai sannan suka fito shi da Azi, Azi sai binsa yake da kallo, duk da baisan yanda sukai da Binta ba amma ya hasasu ganin yanda taci koka shima tunda ta tafi bai bar kowa ya shigo bangarensa ba sai shi daya kaima littafai.

Junaid ne ya kalleshi yace “Azi sai yaushe za’a daina kallo na haka?”
Azi yai kasa dakai yana dariya yace “ wai ka gani?”
Junaid yace “ba dole ba? Kana neman sani na fadi kasa.”

A tare suka dan murmusa, can Junaid yace “Waccen gimbiyar tace Hajiya Inna batasan Umma?”

“Gimbiya Zeena?”

Eh
Azi ya danyi shiru kafin yace “bansani ba wallahi Yarima kaga ba’anan na zauna ba nima.”
Junaid ya jinjina kai kawai baice komai ba.

Sun isa bangaren Azeema, ya shiga ciki, zama yai yana jira ta fito.
Barira ce ta fito ta zube tana gaisheshi ido ya zuba mata kamar bazai amsa ba, Barira ta kara gaisheshi gabanta na faduwa jitai ya amsa, a hankali ta saki wani ajiyar zuciya.
Junaid ya kalleta yace “Ki sanar da Umma nazo.”
Mikewa tai da sauri ta nufi dakin Azeema, da ido Junaid ya bita kafin ya dauke idansa daga kanta.

Azeema wacce ta gama shiryawarta tsaf tasha kwalliya yanda ta saba, dan dama Azeema yar kwalliyace sam baka ganinta ba kwalliya sai dai in bacci take.

Tana zaune tayi shiru tana tunani, dan yatsanta kawai take dan dagawa take saukewa tayi nisa cikin tunaninta har batasan sanda Barira ta shigo ba, sai da Barira ta matso kusa da ita tana cewa “Gimbiya Yarima yaxo yana kilisarki.”

Kallanta tai sannan tai murmushi, mikewa tai ta kara daidaita zaman alkyabarta sannan tace “muje.”

Tare suka fito Barira tana binta a baya, gana ganin Junaid ta saki wani lalausan murmushi na farinciki, Junaid.
Ta fada tana kallansa, Kallanta yai da fuskarsa wacce ita kanta ta kasa meke tattare da ita.
Gaisheta yai, amsawa tai tace “jiya inata jiranka.”
Yace “eh dana dawo ne naji banasan fitowa.”
Murmushi tai tace “ka gaji da zirgazirga ne shiyasa, tunda ka dawo kake ta fama.”
Kasa yai da kansa baice komai ba.

Tace “muje?”
Mikewa yai yace “eh.”

Tare suka fito tana nuna mai hanyoyi tare da dan bashi tarihin guraren sama sama, yana biye da ita yana kuma jin tarihin harms tambayarta inda bai fahimta ba yakeyi har suka isa.

Bangaren Hajiya Inna shine daga can karshe karshen ginin, an kewaye mata bangarenta sosai, Azeema suna kokarin shiga ta kalleshi tace “kakatka ce, kayi kokarin sakin jiki da ita.”
Kai ya daga alamar to, sannan tace “Zubair mahaifinka shi kadaine yao tsawan rai a ‘ya’yanta maza, ta haifi maza guda hudu amma duk sun rasu kafin suyi aure shikadai ne har ya hau mulki sannan ya hayayyafa.”
Junaid cikin mamaki da tausayinta yace “ba ita bace mahaifiyar Sarki?”
Tace “AbdulSalam itace ta rikeshi tun yana karami, sai dai ba ita ta haifeshi ba.”

Junaid ya jinjina kai, shiga sukai ciki, Jakadiya wacce ta sauka ta koma bangaren Hajiya Inna tana zaune a waje suna hira da wasu, tana ganin Azeema ta mike da sauri, dukansu suka hau gaishesu, Jakadiya ta kalli Azeema cikin mamaki, dan rabanta da bangaren nan ita kanta bazata iya tunawa ba.

Azeema tai gaba Junaid yabi bayanta, Hajiya inna na zaune tana bare goro Jakadiya ta shigo tana sanar da ita zuwan Azeema.
Hajjiya Inna ta dago dayake bata gani sosai, ta kalli Jakadiya cikin muryar tsofafi tace “wace?”
Jakadiya ta

Please Login or Register in order to submit comment