Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sukai sallar asuba tare ta koma bacci lokacin ne ya fita.

Mikewa tai zuciya daya, jin zafin datai ya ratsa ta ne yasa cikin kunya ta koma ta kwanta.

Junaid kam bayan ya gama karatunsa yana ganin gari yayi haske ya mike ya nufi bangaren Azeema.

Gaba daya ba kowa a hanyar dan duku dukun safiya ne, ita kanta Azeemar tayi sallah kenan tadan kishingida a inda ta kwanta din, barira ce ta leko ta sanar da ita isowar Junaid.

Mamaki ne ya kamata matuka, jitai baccin idanta ya ware ta kalleta tace “ya shigo.”

Da sauri ta gyara zamanta, gabanta na faduwa.

Junaid ya shigo ya zauna sannan ya gaisheta, kallansa tai cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa tace “Junaid!”

Kallanta yai bai amsa ba, murmushi tai tace “banyi tsammanin ganinka ba.”

Fuskarsa a hade take babu alamar fara’a a tattare dashi, kallanta yai yace “nazo ne na sanar dake abubuwa guda biyu.”

Jikinta a sanyaye ta kalleshi tace “inaji!”

Nasan kinsan abinda ya faru kin kuma san jiya Sarki ya ajiye mulkinsa, daga yau har zuwa sanda xa’ai nadi bazan sake cewa komai ba, sai dai ina so kisan daga wannan lokacin zan yanke hukunci akan abinda kika aikata a dalilin san zuciyarki.

Azeema ta daga kai cikin dana sani tace “nagode Junaid.”

Bai amsa ba yace “mijinki nace ya bar masarautar nan shida matarsa yace sai dake zai tafi.”

Fuskarta ta hade tace “ni?”

Junaid ya mata kallan eh, haushi ne ya kara rufeta tace “zan dau matakin wannan, ma tabbatar wannan me kadai abinda zan iya na taimakeka, ko da kuwa hakan ya kasance na bi shi ne to lalai zan tafi dashi dan samun sauki da kwanciyar hankali a masarautar nan.”


Kallanta yai yace “Ta yaya kika bari san zuciya ya rufe miki ido? Kinsan yanda nake ji a duk sanda na sa abinci a bakina? Ina tuna ina ci ne a maimakon mahaifina, ko me nakeyi abinda nake tunani kenan, taya a cikin mutanen duk duniya ace ke? Ta ya......”

Idanunsa ya runtse cikin takaici.

Azeema ta share ta kasa cewa komai, idanunsa ya bude yace “ina sauraran yanda zaki sa ya bar masarautar nan.”

Kallansa tai cikin wani yanayi, mikewa yai ya mata sallama ya fita.

Da kallo ta bishi har ya fita, tace “Abban Zubair da ace kana da rai na tabbatar da sai kafi kowa alfahari da yanda danka yake, wannan shine halin cikaken Sarki, karya kuskura ya karaya kar kuma ya ragawa duk wani mai laifi koda kuwa mahaifiyarsa ce.”

Murmushi tai tana mai jin haushin kanta.

******


Dare........
Junaid wanda ya dawo daga fada sunyi karamin zama akan wata shari’a wacce yau ya fara aikinsa.
Daga nan sukai sallah ya taho, kallan bangaren Binta yai sannan yai murmushi yace “Azi bari na dan lekata.”

Azi ya matso yace “Ranka ya dade zatazo anjima ai.”

“Cewa nai bazata zo ba?” Ya tambaya yana san jin me Azi zai sake cewa.

Da sauri Azi yace “gwara mu leka kam kafin tazo.”

Bai amsa mai ba ya nufi bangarenta.

******

Binta na zaune tana gyara jikinta, yau tun safe ita da Hari suke hidimar gyara jikinta, ita har kunya ce ta isheta ganin yanda ake ta hidima.

Harira ta tafi ita kadaice a daki tana tufke gashin kanta, jin bude kofa yasa ba tare da ta juyo ba tace Hari kin dawo mu tafi?

Jin shiru ne yasa ta juyo, Junaid ne ya kalleta tare da harde hannunsa a baya ya fara takowa a hankali yana kallan dakin, yace “baki ganni bane?”

Binta wacce bakinta ke bude ta kalleshi tace “Ya j....au Takawa mai kake anan?”

Hade fuska yai yace “me? Bakya nemana anan?”

Mikewa tai da sauri tazo kusa dashi sannan ta wuceshi zuwa kofa ta tura kofar ta rufe ta dawo gabansa a hankali tace “Yaya ka manta yanzu kai Sarki ne?” Cikin irin radar nan tai maganar shima cikin rada yace “sai akace Sarki karyazo yaga matarsa?”

Tace “ba’a ce ba tunda nima yanzu zanje.”

Murmushi yai cikin rada ya sake cewa “in koma kenan?” Ya fada yana nuna kofa.

Kai ta daga alamar eh, harararta yai ya hade fuska ya juya, dariyarta ta guntse harya fita sannan ta kara shafa humra.

Yana fita Harira na isowa, nan suka fita.

Junaid rai a bace ya koma bangarensa yana zama ya harde hannunsa ya kalli Azi yace “daga yau ko nace zani lekota kacemin na tuna, daga ka fadi haka zan gane.”

Dariya Azi ya dane yace “to Yarima.”

Jin sanar da isowar Binta da akai ne yasa ya mike ya shiga daki, Azi yai dariya ya rasa me yasa Junaid ke komawa yaro inda akai Binta ne.

Binta ce ta shigo ta kalli Azi tace “yana ina?”

Daki Azi ya nuna mata yana murmushi tare da jan kofa ya fita.

Tura kofar tai ta leka, ganin ba kowa yasa ta bude sosai ta shiga tana kallan dakin.

Daga gefe ta ganshi a zaune akan kujera ya harde kafafunsa.

Murmushi tai sannan ta nufi gun tace “Ranka ya dade ashe nan ka boya.”

Hade fuska yai yana kara kallan Littafin daya dauka wanda bude wa kawai yai, zama tai ta kalleshi sannan ta kalli littafin, dariya tai tare da zuwa kusa da kunnensa tace “a juye littafin yake.”

Kallan littafin yai da sauri sannan ya hade fuska yace “a haka nake san karantawa.”

Dariya ta sa tace “Hmmm na manta ashe ana iya yi a haka.”

Harararta yai, hannu tasa ta riko hannunsa tace “Ya Junaid!”

Kamshin da take ne yasa ya dan lumshe ido, kallanta yai tace “nice fa Bintalo!”


Dariya yasa yace “Bintalo?”

Tace “tunda nasan shikadai zai saka dariya ba dole na fada ba.”

Dariya ya sakeyi sannan ya kalleta.

Kallansa tai itama ta sakar mai murmushi, hannu yasa ya jawota jikinsa, kan cinyarsa ta zauna tadan sauke idanunta kasa.

Dagosu tai ta zubamai tace “Yau zanta cewa Ya Junaid saboda yaune rana ta karshe da zan kiraka haka.”

Junaid ya kalleta yace “ban yadda ba, na fisan in muna tare mu biyu ki fadi hakan.”

Kai ta daga cikin amincewa sannan ta sake murmushi.

A hankali ya sa hannu ya matso da fuskarta ya sa bakinsa cikin nata.........

********


Shiri ake sosai na nadin sarauta, sai dai duk wannan shirin Zeena da Binta ke yinshi, Hajjo na kwance ciwon bakin ciki ya kamata, komai nata masifa ne, sau uku Zeena na zuwa tana cewa ta koma batasan ganinta, Zubair kam gaba daya ya zama sauna, shikenan da yawo a gari yana neman abin da zai daukemai kewa ya rage mai bakin ciki.

Azeema kam ita ke aikawa Binta tazo ta nuna mata abinda zatai, duk wani abin masaruta ta koya mata sannan ta nuna mata yanda xata zauna da mutane ba tare da ta bari sun cuce ta ba.

Sosai Binta ta ke daukan darasi take kara sanin yanda al’amura ke tafiya.

Sarki kam gaba daya abin duniya ya isarsa, duk ya rame ya jeme a yan kwanakin nan, haka ya koma daya bangaren aka hau gyarana Junaid bangarensa.

Zeena sau uku shima tana neman iso a gunsa yana maidata wannan abu ya dameta sai dai data fadawa Junaid yace “karta damu zai sa tagansu.”



Azeema yau da kanta ta nufi bangaren Abdulsalam.

Yana zaune a kasa akan dadduma, duk abin duniya ya dameshi yaji isowarta.

Da sauri ya mike ya taho jikin kofa, tana shigowa ya rumgumeta, Azeema!

Abinda ya fada kenan cikin tsananin farin ciki yace “ban taba tunanin zaki zo ganina ba, nagode sosai Azeema nasan kema bazaki iya rayuwa ba ni ba.”

Dan matsar dashi tai daga jikinta sannan ta kalleshi, kallanta yai sannan ya jawota ya zaunar sannan shima ya zauna, Yace “Azeema!”

Kallansa tai sannan tace “yaushe zaka bar masarautar nan?”

Fuskarsa ya canza ya gumtseta yace “bangane ba?”

Tace “sai yaushe zaka daina wannan abin daka daurawa kanka? Har yanzu bakai dana sanin abinda ka aikata bane? Na tabbatar da kayi ba sai na tako na ma magana ba da kanka zaka ce zaka tafi.”

“Zan tafi amma sai dai in har zaki bini.”

Wani murmushin takaici tai tace “in bika in ma me? In bika na ma kallan cutar dani dakai ko na bika na ma kallan makiyi?”

Fuskarsa sosai ya canza yace “ko zan mutu sai dai na mutu dake amma wlh bazan daga kafa na bar nan ba sai dake, inko ba haka ba na mutu a cikin dakin nan.”

Kallansa tai tace mene?”

Yace “nayi rantsuwa kin kuma jini, in har kinaso na bar masarautar nan da Junaid to ki hada kayanki a gobe ma zan barta in dai zaki bini.”

Kallansa kawai take, tari ne ya kwace mata wanda take ta fama dashi, da sauri ya riketa yana cewa “baki da lafiya ne?”

Ture hannunsa tai tana kallansa, yace “Azeema mu tafi tare na rokeki da Allah, bani da lafiya ni kadai nasan jikina na tabbatar bazan dade a duniyan nan ba, ki taimaka ki bini na mutu kusa dake.”

Kallansa kawai takeyi, yace “Azeema ki taimakamin dan Allah.”


*****
Ayusher🏌🏻♀️



*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{50}


Junaid dake durkushe gabanta ta kalla, tamai murmushi jin dadi sannan ta kamo hanunsa ta rike.

Kallanta yai cikin tausayawa yace “Hajiya Inna!”

Cikin maganar tsofafi masu shan wahala ta kalleshi tace “Bazan bar godewa Allah ba dayasa kai dan Zubair ne ba, ina kaico da lokacin da zuciyata ta rayamun Azeema amanar Zubair taci ita da Abdulsalam aka sameka, saboda hankalina ya tashi sanda naje duba d’ana naga halin da yake ciki sannan na taho ina tafe ina tausayinsa kawai na hango Abdulsalam ya nufi ta baya, ina ta binsa saboda ina san naji halin da Zubair yake ciki ne naganshi ya nufi kango, abin mamaki naga Azeema a cikin kangon, wannan lamari yasa na fara kawo shirme a raina sai dai kafin Zubair ya rasu ya fadamin ba haka bane, Duk ‘ya’yan Azeema nashi me, wannan ne yasa na cire hakan a raina sai dai na san tabbas da wani abin a kasa.
Kwatsam sai gashi yana rasuwa ta auri Abdulsalam, tun daga wannan lokaci ne gaba daya na canza musu, nan na kira Abdulsalam ina mai magana akan auran dayai ban sani ba sai cemin yai ai dama can shi da Azeema ke san juna na aurama Zubair saboda d’a nane, sannan ya daukemin kai.”

Kallan Junaid tai saboda wahalar datasha gun magana, tace “tundaga lokacin na yanke tsakanina da Azeema da kuma Abdulsalam!”

Junaid ya kalleta sannan yadan yi murmushi mai tattare da tausayinta yace “kiyi hakuri Hajiya ki yafe musu, sannan Marigayi ne yasa a kaini can ba shi bane.”


Kallansa tai duk da idanunta basa Kai ta daga tace “nayafe musu Junaid banda wani buri a yanzu, balle nasan dakyar ko gobe in zan kai, nagodema Allah dayasa zanga wannan rana.”

Kallanta yai cikin tausayi yace “zaki kai insha Allah.”

Haka ya zauna a gunta kafin ya fito.

********


Bangarensa ya koma saboda shirin yana shiga yaga masu shiryashi sun hallara, gaba daya masarautar cike take taf ta ko ina, shiyasa yai shigar burtu dan zuwa gun Hajiya Inna.

Shiryashi aka farayi.

Daga can cikin gida kuwa Binta da Zeena hidima suke ta ko ina, Azeema ma ta zake sosai tana hidima dan ta gama tsara abinda zata aiwatar a daren yau.

Sarkin kano bai samu zuwa ba sai dai ya turo babban dansa ya wakilceshi, Sarkin Zazzau ma turowa yai, hidima sosai sukeyi, ta ko ina mutane ke hada hadarsu.

Zeena ce ta kalli Fure tace “kin aikama Hajjo kayan?”

Fure ta kalleta jiki a sanyaye tace “tace ma dawo miki dasu.”

Kallan kayan tai da bata kula dasu ba da sannan tai yake tace kawo na kai mata dakaina.

Haka nan suka cigaba da hidima, sosai Binta da Zeena sukai kyau sosai, kayan iri daya ne sai dai kowa kalarsa daban.

Binta da yake ba fara bace sai ta saka sky blue, ita kuma Zeena wace ke fara sosai saboda Abdulsalam tayo ta saka kalar Orange, sunyi kyau sosai.

Safiya uwar hidima ita da mijinta Mahmud ta ko ina hidima sukeyi, an gama shirya Junaid tsaf sannan suka nufi fada danyin nadi.

Haka aka sha shagali wanda ya kwanta a zuciyar wadanda ke farin ciki, wadanda ke bakin ciki kuma ya bar musu babban tabo wanda bazai iya warkewa ba.

Junaid kam yayi kyau har bansan ta yanda zan muku bayani ba, yo abinka da mai taro....lol

Haka akai taro aka gama, a kuma daren ranar ne bayan yayi sallar isha’i a saban sashensa yana mike saboda gajiyar dayai, tunani yake a kira masa Binta tadan taimaka ta bugamai bayansa, gefensa Azi ne wanda ya kira, ya kalleshi yace “Sabisu ya wuce din?”

Azi yace “ya tafi ranka ya dade”

Junaid ya kalleshi yace “Inasan kai tafiya zuwa kauyen nan.”

Kallansa Azi yai yace “wani abin za’ai?”

Junaid ne ya kalleshi yace “Azi girma ya dan fara kamaka kamar ya kamata daga wannan aiken ka kuma yi aure ka zauna da iyalinka.”

Azi cikin kunya yace “ni ka barni a haka Takawa hakan nan kula dakai yafi komai a gareni.”

Junaid yace “a’a in ka dawo zan nemo ma mata da kaina inkai aure sai ka ajiyeta anan cikin masarauta.”

Zubewa Azi yai gaba daya ya rasa ta inda zaiyi magana,ya dago yace “ina godiya Takawa Allah ya karemin kai a koda yaushe.”

Junaid yace “Ameen, ka shirya ka nemomin mahaifin Binta ka taho dashi.”

Azi ya kalleshi yace “nan?”

Junaid ya daga kai, da sauri Azi yace “angama ranka ya dade.”

Zagi ne ya fara sanar da isowar Azeema, nan Azi yai sallama ya fita.

Azeema ce ta shigo bayan an mata iso, Junaid ne ya kalleta har ta shigo, sannan ta zauna, kallanta yai yace “Umma?”

Kallansa tai tana murmushi sannan ta ajiye abinda ke hannunta, kaya ne na sarki wanda kana kallo zakasan kaya ne wanda Sarki kadai ke da damar sashi, kallanta yai sannan ya kara kallan kaya.

Murmushi tai tace “zaka tashi na gwada ma?”

Jiki a sanyaye ya mike, da kanta ta taimaka mai ya saka, ganin yayi mai cif cif ne ya sata yin dariya mai hade da hawaye tace “Alhamdulila, na dauka sai mun sake yi.”

Gaba daya jikinsa ne yai sanyi ya kalleta, kallansa tai tana dariya sannan tace “nagode daka amshi kyautata.”

“Taya zanki amsa?”
Furucin da taji ya fito daga bakinsa kenan, kallansa tai jiki a sanyaye, murmushi ya mata yace “barina kika yanke shawarar yi?”

Idanunta ta zaro ta kalleshi jikinta ya sake yin sanyi a hankali tace “ya akai ka sani?”

Nuna mata yai ta zauna sannan shima ya zauna, kallansa tai yace “taya bazan gane ba? Bayan kina nufin kin kawomin rigar sallama.”

A hankali ta sa hannu a kan fuskarsa tace “Junaid dina ya girma.” Ta fada tana kokarin maida kwallarta.

Sauke hannunta tai tadan ja hancinta tace “Abdulsalam bashi da lafiya.”

Na sani!

Kallansa tai tace “yaushe?”

Murmushi yai yace “jiya, ya kirani.”

Yace me? Ta tambaya cikin sanyin murya.

Shiru yai yana tunowa.

Kallansa tai tana nazarin abinda yake tunani.

Jiya ya kasance kwanan Zeena ne, bai kuma dawo saban bangarensa ba yana kwance a daki hadimin Abdulsalam ya zo da sakon san ganinsa da Abdulsalam yake.

Junaid ya mike zai fita, da sauri Zeena ta rike rigarsa tace “Yaya inzo muje?”

Murmushi ya mata sannan ya dafata yace “yanzu zan dawo.”

Kallansa tai jiki a sanyaye ya fita.

Abdulsalam na zaune a bangarensa Junaid ya shiga.

Zama yai Abdulsalam ya zuba ruwa a kofuna guda biyu dake gabansa sannan ya tura ma Junaid kusa dashi.

Kallansa Junaid yai sannan ya kalli kofunan, Abdulsalam yace “daya ruwa ne kamar yanda kaka na zuba shi, dayan kuma akwai guba a cikin kofin kafin na zuba ruwan.”


Kallansa Junaid yai, Abdulsalam yace “ka dau daya nima na dau daya, idan har ka dau ruwa to tabbas zan mutu a cikin dakin nan, kaga shikenan sai a ce kai ne ka kasheni, idan kuma ka dau gubar kaga shikenan daga wannan gun kowa zai san nine na kasheka nima hukuncina kisa ne zai biyo.”

Junaid wanda ke kallansa ne yai wani murmushi sannan yace “to sai akace kuma dole nasha ruwan?”

Abdulsalam yace “dole ne domin inba haka ba zan shanye duka ruwan kaga duk abinda ya biyo baya kaine.”

Shiru Junaid yai tare da kuramai ido, Abdulsalam ya kalleshi, Junaid yace “baka da lafiya ne?”

Kauda kai Abdulsalam yai, yana juyowa yaga Junaid ya dau ruwan ya juyeshi a daya cup din sannan ya shanye.

Ido Abdulsalam ya zaro yace “bakada hankali ne?”

Junaid ya ajiye cup din sannan ya kalleshi yace “me yasa ka kirani? Nasan ba wai kirana kai dan kawai kai wannan wasan ba?”

Kallansa Yai sannan yai murmushi yace “ya akai kasan bakomai?”

Junaid yace “menene abin wahala a cik? Ta ina zaka samu guba a inda ni nasa a killaceka? Sannan koma ka samu taya zaka sakama mijin yarka? Sannan inka kasheni da wani ido zaka fito? Sannan babban damuwarka shine Umma ta tsaneka.”

Hannu yasa yana murza idanunsa, sannan ya kalleshi yace “na fadi”

Ya akai?

Abdulsalam yaga ya mike ya sanya gwiwowinsa a kasa.

Da sauri Junaid ya kalleshi yace “lafiya?”

Abdulsalam ya kalli Junaid tari ne yadan kwace mai kafin ya tsagaita yace “ Junaid na san laifina bazai musaltu ba? Sai dai bazanji kunyar tambayarka alfarka guda uku ba, ka dubi girman Allah ka yafemin? Nasan abinda nai har abada bazan taba samun sassauci ba, laifi ne babba wanda na aikatawa Allah, sai dai zan karasa rayuwata agun neman yafiya gun Allah, nasan hukuncina a musulunce mai karfi ne, sai dai ina nemi alfarma kasa a kulleni a gidan daka zauna har karshen rayuwata.”

Junaid ne ya kalleshi, Abdulsalam ya kalleshi yace “Sannan abu na biyu ga amanar Zeena da Zubair nan, dan Allah ka kula dasu Junaid, laifina karya shafesu basusan abinda akeyi ba.”

Junaid ne ya hadiya yawon bakinsa, yana kokarin danne raunin da zuciyarsa ke neman yi.

Abdulsalam yace “sai na karshe, ka taimaka ka barni na tafi da Azeema.”

Kallan Junaid yai gaba daya dana sani na damunsa.

Junaid me ya kalleshi yace “na farko dana biyu na yadda dasu sai dai na uku banida hakki akai.”


Kallan Azeema yai ya tuno yanda ya fito ya bashi yana hawaye, Azeema tai murmushi tace “shikenan.”

Ta daure tace “Na fahimci nima zamana anan bazai dada ma komai ba sai bakin ciki. Na tabbatar duk sanda ka tuno abinda ya faro sai ka tsaneni, duk kuma sanda ka ganni sai abin ya dawoma, hakan yasa zan bishi, sai dai ina so kamana hukuncin daya dace damu, duk abinda ka yanke zan zama mai bi.”


Tana kaiwa nan ta mai sallama ta mike.

Kallanta yai yace “Umma!”

Juyowa tai ta kalleshi da raunana idanunta.
Yace “bari a kirashi.”

Kallansa tai sannan ta dawo ta zauna tace “yanzu?”

Azi ya kira yace a kira Sarki.

Hannu yasa a kansa sannan ya rufe idanunsa.


Gaba day jikin Azeema ne yai sanyi zuciyarta na bugawa da karfi da karfi.

Bazata taba yafema Abdulsalam ba sai dai in ta duba ta wani bangaren gani take komai ya faru ne saboda ita, ta tabbatar da badan saboda ita ba da duk hakan bazata faru ba.

*
Ayusher🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{51}



Abdulsalam ne ya shigo gaba daya jikinsa ya kara rarakewa duk ya rame, zama yai Junaid har yanzu bai bude idanunsa ba.

Can sai ga Hajjo wacce yasa itama a kirata daga baya.

Ajiyar zuciya yai sannan ya bude idanunsa a hankali, kallan Abdulsalam yai sannan ya kalli Azeema yace "daga wannan lokacin na haramtawa Azeema da Abdulsalam shigowa cikin gari, zasu koma kauyen dana nemi su zauna, a kuma can zasu cigaba da rayuwa har karshen ransu, sannan dole su zasu nemi abinda zasu ci su sha, hadima daya da hadimi daya na amince su tafi dasu, sannan idan har Hajjo ta nemi ta bisu itama da hadima daya zata tafi, in kuma mijinta ya nemi zamanta anan ko kuma yana neman sauwake mata? zata koma can karshen ginin kewaye, gefen da Hajiya Inna take ta zauna, sannan itama gudun fitina mai tasowa zata bar shiga duk wani sabga data shafi cikin masarauta."

Kallan Hajjo yai sannan yace "sannan Zubair zan nadashi Hakkimi zai bar cikin masarautar nan ya koma Hakimin garin da na bashi."

Maida idanunsa yai yadan lumshe sannan ya sake budesu yace "inaso a cikin gurin nan maganar abinda kuka aikata ta tsaya, wannan ne kadai abinda xan iya muku.

Abdulsalam ya kalla yace "kafin ka tafi gobe kaga nemi ganin 'yarka."

Da sauri yace "to"

Yana kaiwa nan yace "nagama magana."

Abdulsalam ya sake zubewa yana godiya, Azeema kam hawaye ne ya zubo mata saboda harta fara rashin dan nata, ita kuma kaddararta kenan, bata taso da shi ba yanzu kuma shn hadu gashi zasu sake rabuwa.
Kwallarta ta share sannan ta mike ta fita, Abdulsalam yabi bayanta da sauri har yana tuntube.

Hajjo Junaid ya kalla wacce ta sauke kanta kasa ko tofa kalma daya batai ba, kallanta yai, kallansa tai ta daure tace "Zubair laifin me yai?"

Kallanta yai yace ba laifin dayai sai dai zamanshi kusa dake zaisa ki sashi, in ba abinda zakice zan shiga ciki, sannan kema kiga yarki ta damu.

Ya wuce ciki.

Haka tafito gaba daya danta a bace, yanzu kam ba yanda ta iya inba so take a turata kauye ba bayan ba ita ya kar zomon ba, rataya aka bata, bataga abinda zaisa tabishi wani kauye ba.

^****

Abdulsalam ne yabi Azeema da sauri, hannunta ya kamo yace "Azeema nagode sosai......."

Tari ne ya kwace mai, kallansa tai tace "karkai tunanin zan bika ne saboda soyayya ko kiyayya, zan bika ne saboda ma kare mutunci da darajar d'ana."

Kai ya daga da sauri yace "koma menene nidai nagode Azeema ke kadai nake bukata a rayuwata."

Hajjo wacce ta taho tana jin karshen kalamansa ta tabe baki tace "sai ka dauki abinka."

Kallansa tai bayan ta karaso tace "kasan dai ni ina nan ko?"

Yace "nasani."
Ta maka mai harara ta harari Azeema ta wuce, dan inba su ba da duk wannan abin bakin cikin bazai sameta ba, taga samu taga rashi.

*******

Washe gari a fada.

Junaid yai gyaran murya wanda yasa kowa sake nutsuwa, kallansu yai dukansu sannan yace "inada muhimmiyar sanarwa, da farko dai Sarki Abdulsalam da matarsa Gimbiya Azeema zasu bar masarautar nan sakamakon izinin hutawa da sukesan yi, abu na biyu kuma Waziri, Shamaki da Galadima."

Da sauri suka kalleshi gabansu na faduwa, suma ina neman kowa ya kawo sunan dansa wanda zai gajeshi, ya zauna ya huta a gida, lafiyarku itace anin dubawa."

"Sannan abu na uku Zubair!"

Zubair wanda dama yasan menene saboda Hajjo ta fadamai, Junaid yace "na nadaka Hakimin Gabas!"

Da sauri mai kiran lafiya ya fara yima sarki kiraki, su Waziri kuwa yanda kasan an musu duka haka sukaji abin."

Da wannan aka shiga wata hidimar.


Yana fitowa ya hadu da Azi ya dawo, Azi aya kalla yamai alama da ido akan an sameshi?
Azi ya daga kai alamar eh.

Bangarensa suka nufa daga gefen kofa yaga mutumin dake tsaye duk kayan jikinsa a kode, kafarsa wani sidaden silifas ne.

Junaid ya kalleshi da sauri ya zube kasa yana kwasar gaisuwa.

Junaid ya kalleshi sannan ya nemi ya shigo ciki.

Da bakin kofa ya tsuguna gaba daya ya rude, sai da Junaid ya nutsu sannan ya kalleshi yace "kaine Malam Kasim?"

Da sauri yace "eh."

Junaid ya kalleshi cikin takaici yace "ka taba tunanin inda yarka take? Ko a wace irin rayuwa take?"
'Yata?

Ran Junaid ne ya kara baci, da sauri Kasim ya kalli Junaid yace "Binta?"

Junaid ne ya kalleshi, da sauri ya sake zubewa yace "Binta? Tanada rai?"

Junaid yace "ka taba dana sanin abinda ka aikata?"

Kuka Kasim ya saka yace "a koda yaushe cikin dana sani nake, san zuciya yasa na wulakanta yar yarinyar da take marainiya."

Marainiya?

Kasim yana kuka yace "Yarinyar mutumin daya taimakeni na zauna a garin ne, babban mutum ne malami yana zaune da matarsa lokacin da mukazo garin, sai dai yana fama da lalurar ciwon daji, a koda yaushe yana zaune saboda kafafunsa, matarsa nada ciki

Please Login or Register in order to submit comment