Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Azeema ta kalli Barira da Safiya tace “ku bamu guri.”

Nan suka juya suka fita.

Jakadiya na zube a kasa, Azeema ta kalleta sannan tace “Jakadiya! Ya zaman gun Hajiya inna?”

Jakadiya ta dago tace “lafiya kalau sai abinda ba’a rasa ba, ya sabuwar Jakadiyar?”

Azeema ta kafeta da ido wanda yasa Jakadiya sauke idanunta kasa tare da shan jinin jikinta.

Wani kasaitacen murmushi ta saki sannan tace “Me kike boyemin?”

Kallanta Jakadiya tak tace “ni?”

Idanta na kanta batace komai ba, Jakadiya tace “me zan boye miki ni kuwa Gimbiya? Girma ya kamani me zai sa nai abinda zai sani cikin tashin hankali?”

Azeema ta murmusa sannan tace “ya akai ni kuma nakeji a jikina kina boyen wani abin?”

Jakadiya ta kalleta tace “Wallahi Gimbiya ba abinda nake boye miki”
Azeema tace “na yarda wasa nake miki.”

Jakadiya tai ajiyar zuciya, Azeema ta sake kallanta tace “lokacin Marigayi akwai wani abu daya faru wanda har ya canza yanayinsa?”

Jakadiya tai murmushi tace “Gimbiya dama ai dole akwai ranar da zakaji baka jin dadi ko a batama rai, balleshi Sarki?”

“Ba irin wannam nake nufi ba, yanayin da harku kuka san akwai matsala?”

Jakadiya tai shiru tana nazari kafin ta kalleta tace “na kasa tuno komai Gimbiya, a gafarceni.”

Azeema tace “shikenan, sai dai duk sanda kika tuno ki sanar dani.”

Jakadiya ta mike, harzata fita ta juyo da sauri tace “Gimbiya!”

Azeema ta kalleta, Jakadiya ta sake zubewa tace “akwai wani lokaci guda daya, wanda ko abinci dakyar yakecin kadan, fita inba fadaba baya zuwa ko ina? In baki manta ba ko ku matansa inkum nemi ganinsa cewa yake ku koma.”

Azeema ta kalleta da sauri tace “na tuna, amma lokacin ya yanayinsa yake?”

Tace “ba wanda ya sani, saboda shi kadai yake zama.”

Azeema tai shiru kafin tace “nagode, zan aiko da sako.”

Jakadiya tai godiya sannan ta rufa babban mayafin nan, tana fita Barira dama na kofa tai dakinsu da ita.

Jakadiya ta bude kanta sannan ta kalli Binta wacce haryanzu ita kadaice a dakin.”

Tace “ina Yariman?”

Binta tace “yana bangarensa.”

Jakadiya ta kalleta tace “inhar kinasan kasancewa dashi sai kin cire tsoron dake ranki, nan masarautace in kika cigaba da haka rayuwarki ma bazaki tsira da ita ba.”

Tana kaiwa nan ta fita, Binta tai shiru tana maimaita kalaman nata, itakam Junaid take san gani duk abin duniya ya dameta.

Tunani tai ko ta fita ta kofar itama ta nemeshi? Ko kallansa tai ta dawo?

Wannan shawarar tasata ta fita.

*************

Yana zaune yayi shiru, wata hadadiyar alkyabba dakakiya mai matukar tsada da kyau Azeema ta aiko mai da ita, kallo daya kayima Alkyabar nan sai ka sake kallanta saboda tsananin daukan idon da take dashi, ga wani hadaden takalmi na sarauta a gefe.

Fuskarsa kawai inka kalla zaka san duk wannan abin baya gabansa. Azi ne ya shigo ya kalleshi yace “Yarima ya baka shirya ba?”

Junaid ya kalleshi yace “an dubo Bintan?”

Azi yace “anje itama wanka takeyi.”

Junaid ya kalli kayan yace “jiranta nake tazo ga gani kafin nasa.”

Azi ya kalleshi yace “inka saka zaku hadu acan gun taron, kaga sai taci gani dakyau.”

Junaid ya kalleshi sannan yace “rikemin wannan nata ne.”

Azi ya kalli ledar ya bude ciki, dariya yasa yace “yanzu Yarima duk abinda kaci sai ka tafi mata dashi?”

Yace “kaima kasan Binta, ba lalai ta iya cin abinci acan ba, shiyasa zanyi magana mu dawo nan da ita.”

Hari dake shirin shigowa ta tsaya jikinta a sanyaye, sai dai tasan bazai taba yiwuwa ba.

Azi ma kallansa kawai yake, dan yasan rayuwar dayai acan shida Binta basu isa ko rabi suyi anan ba.”

Junaid ya dau kayan ya shiga daki ya shirya, murmushi yai yace “harna hango idanki.”

Aikowa akai akan ya fito, hakan yasa ya karasa shiryawa ya sa turare sannan ya fito.

Hari na hangoshi ta hau guda tana cewa “Yarima Allah ya kara lafiya ya kawo zuri’a ta gari.”


************

Cikin fada Hajjo ta kalli Fure tace “bata gama ba?”

Fure ta kara lekawa dakin sannan tace “yanzu take karasawa, Hajjo ta kalli Zubair ta mai alama daya mata magana sannan ta hade fuska tana cewa “ko uban me takewa kwalliya?”

Fitowa tai tare da hade fuska tana cewa “dan Allah Hajjo ki bari na kara gyara fuska ba.”

Kallan mamaki Hajjo ta mata tundaga sama har kasa, bugagiyar hamshakiyar alkyabbar da akai rabin shekara ana yinta saboda taron sallah shi ta sa?

Zeenatu ta kalleta tace “nayi kyau?”

A hankali Hajjo ta kalli fuskarta, sannan ta maida idanunta kan kafarta, takalmin da Mai Martaba ya kawo mata wanda ko sashi batai ba shi ta sa?

Zeenatu tace “Hajjo!”

Bakin ciki tsabar ya cikawa Hajjo rai kasa magana tai, gaba kawai tai Zubair yabi bayanta, sannan itama ta bisu.

Duk inda suka wuce kallan Zeenatu ake saboda tsabar haduwar datai, wanda koni sai dana sake waigawa.

*******
Katan filin da aka gyara shi dan yin wannan taran suka nufa, masu hawan doki suna gefe suna jiran a fara dan suyi wasa.

Masu wasan takobi ma na gefe, masu kidan kalangu ma suna ciki, busar sarewa kawai ke tashi.

Yarima wanda ya taho akan doki ne ya nufi bangaren Azeema dan su tafi tare kamar yanda ta aika a sanar mai.

Yana shiga yaga bangarenta makil da mutane, mamaki ne ya kamashi ganin jiya fa aka aika, ya akai mutane dayawa suka samu halarta haka?

Nan ya fara gaisawa da mutane, kowa sai fara’a yake ana mai lale lale da dawowa, duk yanda yaso ya hango Binta abin yaci tura saboda yawan mutanen dake ta matsowa gunsa.

Safiya ce tazo ta nemi da kowa ya tafi gun taro suma gasunan tahowa, nan kowa ya sa takalminsa ya fita.

Safiya tsayawa tai tana kallan Junaid hawaye suna gangaro mata.

Jiki a sanyaye ya kalli Azi, da sauri Azi ya matso ya radamai cewa yayarsa ce.

Junaid ya matsa kusa da ita, murmushin farin ciki ta hau yi tana goge hawayenta.

Nuna mata yai da yatsarsa akan ta goge nan.

Nan ta goge tana dariya, tace Junaid Barka Barka

Murmushi yai, fitowar Azeema ce ta sa suka maida hankali kanta.

Fadar uban gayun da Azeema tai ma bata lokaci ne, dan ta kashe lokaci ganin ta fito a yanda takeso.

Junaid ya matsa ya gaisheta.

Fuskarta dauke da fara’a tace “Yarima muje mutane na jira, dan wasu komawa zasuyi a yau.”

Kallan cikin gidan yai sannan yace “Binta fa?”

Tace “muje yanzu zasu taho da bata karasa shiryawa bane, kasan mu mata akwai wuyar shiri.”

Nan suka tafi yana sake waigawa, barira tai daki da sauri dan su fito suma.

Sai dai me? Ba Binta ba alamun ta, idanu ta zaro a tsorace tai kofar baya dan nemanta.


A waje kuwa Binta tana tafe tana neman gidan Junaid, tun abin na mata dadi hartazo ta gaji, sai neman gun take gashi duk wanda ta nema dan ta tambayeshi daga yaga yanayinta zaiyi gaba.

Tana tafe tana share hawayenta dan itakam batama san inda take ba.

Daidai nan ne lokacin dasu Zeenatu da Hajjo suka taho ta kan layin, Binta na share hawayenta sam bata gansu ba, sai jitai an bigeta ta baya.

Da sauri ta nemi juyawa wanda hakan ya bugi hannunta.

Da sauri ta ja baya sannan ta kallesu.

Zeenatu ranta yakai kololuwar matuka gun baci, tana huci ta daga hannu ta sharara mata mari, wanda ya gigita Binta.

Tace dago.

Binta ta sake dagowa ta kara kifa mata wani marin wanda sai dayasa ta tafadi.

Ta daga wani zata kara mata, Zubair ya riketa yace “ya isa muje.”

Hajjo ta makama Binta harara sukai gaba.

Wani irin kuka tasa tana kiran Junaid, dan tabbas raban da a mareta haka harta manta.

Kuka take sosai, ta kasa ko mikewa.


A can gun tro kuwa duk wannan abin da ake hankalin Junaid baya gun, ganin Binta taki zuwa yasa ya mike ya kalli Azi yace “muje naga taki zuwa.”

Azeema dake zaune kusa dashi ta kalleshi tace “ina zaka?”
Yace “naga haryanzu Binta batazo ba?”

Haushi ya kamata amma ta murmusa tace “yanzu zata zo ko kuma Azi yaje ya dubo ko basu gama ba, hakan yayi?”

Junaid ya kalli Azi yamai alama dayaje, nan Azi ya juya.



************
Ayusher
***********


*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Shida


Azi na fita su Hajjo na shigowa gun, duk inda Zeenatu ta gifta zakiji ana gimbiya kinyi kyau, kanta ne ya kara fasuwa ta tabbatar abinda ke kwance a kasan ranta zai karbu.

Azeema tana ganinsu ta mike dan tarbar Hajjo wacce kowa keta gaishewa.
Azeema na karasowa Zeena ta matso ta wani riko hannunta, duk da suna shiri da Zeenatu amma yau ce rana ta farko data taba riketa haka.

Zeenatu cikin farincikin tace "Umma karama barka barka."

Azeema tai murmushi duk da daurewa kawai tai saboda mutanen dake gun, sannan ta zare hannunta suka gaisa da Hajjo, tare da nuna mata gurin zamanta.

Hajjo ta kalli Zubair tace "muje ka gaisa da kanin naka."

Ta fadi haka ne dan ta batawa Azeema rai.
"Oh hakane fa ashe Yarima Zubair baiga kaninsa ba."

A tare suka jera inda Junaid ke zaune mutane duk wanda yazo sai ya gaisheshi sannan yake komawa ya zauna.

Suna karasowa Azeema ta kalleshi tace "ka gaida Uwar gidan Sarki."

Junaid ya gaishe ta fuskar sa a daure, murmushi ta sake tana cewa lale lale Junaid.

Kallan Zubair tai tace "babban dan sarki."
Junaid ya mika mai hannu, suka gaisa.
Ta bude baki zata gabatar da Zeena tai saurin cewa "ni ai ka sanni."

Junaid sai yanzu ya kula da ita, kallo daya ya mata ya juya.

Wannan abu ya bata mamaki, dan har kasa boyewa tai tace "Ya Junaid!"

Kallanta ya sakeyi tace "baka ganeni bane? Duk da nasan na bata maka amma a karshe ai nice........"

Hajjo ce ta tabata alamar tai shiru, fuskar ta ce ta canza dan da a nishadance tazo gun amma abinda ya mata yasa taji ranta ya baci.

Azeema ce ta nuna ma Azeema gefen Junaid ta zauna, Zubair ya zauna a gefenta, ita kuma ta zauna a dayan bangaren Junaid, Zeenatu na gefenta.

Zeena sai cika take, me mutumin nan yake nufi da kallan da ya mata? Kamar irin yaga shara? Ai ko me tamai bada saninta bane balle ya tuhumeta.

Haushin kayan data saka da bata lokacin datai gun kintsawa ne ya kara kular da ita, meyasa to takesan ta birge Junaid? Tambayar data zo mata kenan.

Da sauri ta kalleshi ya zubawa shirin dawakan da ake ido sai dai inka kula dakyau zakaga idansa ba a gun yake ba.

A hankali ta bi inda yake kallo, hanyar shigowa taga yana kallo, a fili tace "wani yake jira?"

Azeema ta kalleta tace "wa?"

Zeenatu tai murmushi tace "naga kamar kofa yake kallo."

Azeema ta kalli Junaid sannan ta kalleta tace "wasa yake kallo"
Zeena ta kara kallansa tace hala ni naga daban.
Ta fada itama tare da kallan masu wasan.

Gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa sam abinda ake ma bai sani ba.

Busa da taken isowar mai martaba ce yasa Azeema cikin wani farinciki.
Kallansa tai tacemai "mai martaba ya iso."

Hajjo ta kalli Zubair tace "me yake anan shi kuma?"

Zubair yace "Hajjo karki nuna wani abin."

Kallan Azeema tai wacce ke murmushin jin dadi.

Shigowar mai martaba ya dau hankalin mutane,dan ba wanda yai tunanin zuwansa.

Kusa da Junaid fadawan suka je, Azeema ta mike tana godiya, Sarki ya kalli Junaid yai gyaran murya wanda yasa kowa yin shiru.

Kallan Junaid yai yace sai kuma ya dan murmusa yace "ganin bansan me kake so ba yasa nai tunanin abu daya."

Ya kalleshi yace "nama alkawari a wannan guri na baka izini ka zabi duk wani abu guda daya da kakeso, ko menene shi ni kuma na ma alkawarin yimakashi indai inada hali."

Junaid ya mike yai godiya nan aka hau tafa musu ana taya Junaid murna, Hajjo kam ta cika harta gama batsewa, yanzu kam ran Zubair ma ya baci dan hannunta ya dunkule da karfi.

Kowa ya gama sanin mezai faru domin abu ne mai sauki, Junaid zai nemi abashi mulki kuma dole ne Sarki ya bashi tunda alkawari yai, wannan al'amari ya batawa magoya bayan Hajjo da danta rai, Azeema kam wani dadi ne ya kamata ta sake yima Sarki godiya.

Sarki ya juya ya bar gun, Zeenatu tai shiru itama tana tunanin abinda ya faru a lokacin, me mahaifinta ke nufi.

Sarki na juyawa Junaid ya kalli Azeema yace "bari ma duba Azi da alama wani abin ya samu Binta."

Bai ko jira tayi magana ba ya juya da sauri, bayin dake kula dashi sukabi bayansa.

Kallan Junaid mutanen dake gun sukai, ina zaije bayan wannan taran anshiryashi ne saboda shi?

Safiya dake gefe ta mike da sauri dan ta tareshi, sai dai kafin ta karasa yabar gun, ganin kar mutane su ankara da halin da ake ciki yasa ta wayance da zuwa gun Azeema wacce ta cika fal a kasan ranta, Zeenatu ce ta mike da sauri tana kokarin fita daga gun, da alama binshi take san yi taga ina zashi haka, muryar Hajjo taji tace “ina zaki?”

Kallan Hajjo tai sannan tace “kaina ke dan......”

Gun zamanta ta nuna mata da kanta, hakan yasa ta koma ta zauna fuska a hade.

Azeema ce ta mike, cikin nuna jin dadinta da wadanda suka hallari taran sannan ta sanar dasu wasani kala kala da za’a gabatar nan gaba tare da basu hakuri akan Junaid yadanje ganin wanine amma yanzu zai dawo.

Azeema ta kallo Safiya tace “Barira har yanzu bata zo ba ita ma?”

Tace “eh bari na dubota”
Kiyi masa kafin a ganshi da yarinyar.”

Yarinya? Safiya ta tambaya, Azeema ta mata alama dataje kawai, juyawa tai ta fita, Zeena da kunnenta ke makale agun taji kalmar yarinya da aka ambata amma bata fahimci me ake nufi ba.

Yarinya? Abinda ke yawo akanta kenan......

Junaid kam yana fita bangaren Azeema yaje, sai dai ba kowa a bangaren, hakan yasa ya nufi nashi bangaren, yana zuwa a bakin kofar shiga ma yaga Hari yace “Hari tana ciki ne?”

Hari hankali a tashe tace “Yarima an rasa inda take.”

Idanunsa ne suka fito alamar tsantsan mamaki, hankalinshi a tashe yace “ba’a ganta ba kamar ya?” Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa ya gama tashi.

Harira tace “ina zaune Azi ya shigo shida Barira tagun Gimbiya wai suna neman Binta, ganin bata nan shine suka rabu zuwa nemanta ni kuma na tsaya anan ko zata zo.”

Bai kara tofa komai ba ya juya hankali a tashe, Hari na kiransa amma inaa baibi ta kanta ba, bayinsa ne suka bishi a baya.

Yama rasa ta ina zai fara neman nata ganin yanayi guri ba kadan ba, tunda gashi ko Azi bai gani ba bare Bari.

Haka sukai ta bi suna nemanta, itama Safiya ta fito da tata tawagar suna neman Junaid su kuma.

Gaba daya jikinsa ya gamayin sanyi gani yake ma ta bar masarautar ne, yana tafe yana dana sanim dawowarsa nan, danshi bai ga amfani dawowarsa cikin daula ba ita kuma ta koma ita kadai.


Wata bishiya ya gani, ya tsaya tare da kura mata ido yana tunanin yanda suke zama a bayan gari, yana saman bishiya ita kuma tana kasa suna hira.

Baisan sanda murmushi ya bayyana a fuskarsa ba dan gani yake kamar a wannan lokacin akeyi.

Harya juya yaji alamun ana cilla dutse karami.
Da sauri ya leka bayan bishiyar, tana zaune rike da kananan duwatsu tana cillawa daga inda take.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki tare da jingina da jikin bishiyar.
Binta jin yanda yaja ajiyar zuciya ne yasa ta juyo ta kalleshi.

Idanu suka kurama juna yana daga jikin bishiyar ita kuma tana zaune.
Kuka?
Me akamin da zanyi kuka?
To ya naga idanki haka?
Tace “kawai na gaji ne.”

Me kike anan?
Tunani?
A tare suka saki murmushi wanda ya bayyanar da begen juna da sukey.
Matsowa yai kusa da ita ya zauna yace “bata kikai?”

Ta dan harareshi tace “eh mana garin neman wani.”

Dariya yai yace “Ahhh yazanyi da Bintar nan banaji zata ita yini bata ganni ba”

Dariya tai itama tace “Ahhhh ya zanyi da Ya Junaid banaji inyaga bai ganni ba zai samu nutsuwa.”

Yanzun ma a tare sukai dariya kafin tace “Allah yaya wannan gidan naku yai girma.”

Yace “bakya sanshi mu koma?”

Kallansa tai a ranta tace ta ina zan sake rabaka da iyayenka?
A fili tace “in nace mu koma zaka yarda?”

“Kina musu? Kin dai sanni ko?”

Da sauri tace “wasa nake Yarima, ban isa ba.”

“Kin tsorata kenan?”

Tana dariya tace “tuni ma.”

Mikewa yai yace “muje.”

Mikewa tai suka fara takawa a tare, suna tafe suna hirarsu yana bata labarin abinda akai batanan duk da shima bakomai ya fahimta ba.

Suna shawo kwana Safiya ta hangoshi, da sauri ta karasa, tace “Junaid kazo ka koma, mutane na nemanka, karsuyi zargin wani abin.”

Kallanta yai yace “Ba’a gama ba?”

Tace “eh karkasa mutanen da sukazo dominka suji ba dadi.”

Ta karasa tare da kallan Binta.
Yarinyar dazu?
Junaid ne ya kalli Binta yace “muje?”

Kayan jikinta ta kalla, sai a lokacin ta kula da irin shigar dayai da kuma irin shigar da Safiya tai, jitai tasha jinin jikinta, ta kalleshi tai murmushi tace “a’a kaje ni zan jiraka a inda ka ganni yanzu.”

Kai ya girgiza alamar a’a sannan yace “sai dai in mu tafi tare ko ki zauna gun Hari.”

Safiya ta kalli yarinyar itama cikin rashin jin dadin wannan abu, wacece? Ina ya samota? Da alama soyayya ce mai tsananin karfi tsakaninsu wanda ita kanta ganinsu na farko tare yasa ta fahimci haka, tab lalai da matsala......

Muryar Binta ce ta katseta tace “zan jira gun Harira.”
Nan suka karasa bangarenshi sai dayaga ita da Harira sun rike hannu sun shiga sannan ya juya.

Harira na rufe kofa ta jawo Binta ta rungume, wanda jin haka yasa Binta sakin kuka, tabbas yanzu kam jikinta ya fara bata Junaid ya mata nisa, yafi karfinta.........




*Ayusher.....*


*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Goma Sha Bakwai*


Azeema ce ta zauna a bakin ta wuce ciki bayan ta gama sallamar da jama’ar ta, tana shiga ta zauna a gefen gado cikin bacin rai.

Safiya ce ta turo kofar a hankali ta shigo, kallanta Azeema tai tace “ya wuce?”
Safiya tace “nayi nayi ya taho nan yace ya gaji ne amma ni nasan saboda yarinyar nan yake san komawa.”
Safiya ta karaso tace “wacece wai?”
Azeema tace “ina ma na santa? A can inda suka taso ya hadu da ita.”
“Yanzu haka zamu bar yarinya mara asali tana juya Junaid? Taya zamu dawo da abinda muka rasa hannunmu yana haka?”

Azeema ta kalleta a hankali ta saki wani lalausan murmushi wanda Safiya tace “Umma me kike tunani?”

Kallanta tai tace “ke a naki tunanin Junaid nada wayau a wannan lokacin?”
Tace “bangane ba.”
Azeema ta murmusa sannan ta mike tsaye tace “baisan komai ba, banda ita a wannan lokacin, me kike tunanin zai faru in aka kamata da gagarumin laifi?”
Safiya tace “bangane ba, hankalinsa ne zai tashi?”
Azeema ta kalleta sannan tai ajiyar zuciya tace “basu kwana biyu zan dau mataki a na ukun, kwana biyun zan barshi ne yai bankwana da ita.”

Safiya ta kalleta dan sau da dama in Azeema na magana ba komai take ganewa ba.
Jin kamar ta sauke nauyin dake kanta ne yasa ta mike ta shiga toilet.
Safiya ta bita da kallo.

********

Binta ce zaune Hari na taje mata kai, Hari tace “hanzu kin ware da kikai wanka?”
Kai ta daga tana murmushi tace “Bansan ya akai naji kuka yaki daina zuwa min ba dazu.”
Hari tai murmushi tace “Binta!”
Naam
Hari tadanyi shiru kafin tace “sai kinyi hakuri dan rayuwar masarauta ba daya take da rayuwar da kika sani ba, sannan dole sai kinyi hakurin janye jikinki daga gun Junaid inba haka ba daga ke har shi kuma bazaku tsira ba.”
Kallanta Binta ta juyo tai tace “bangane ba Hari.”
Hari ta daure mata kanta tace “bazaki gane ba duk bayanin da zan miki sai dai inaso ki kula da mutanen masarautar nan, karki yarda da kowa inba Junaid.”
Binta ta daga kai alamar fahimta sannan tace “Mahaifiyarsa fa?”
Hari ta kalleta tace “itace mace ta farko da zaki kula da ita, dan kowa ansan cikinsa amma ita ba wanda yake sanin nata, sannan ba sarauniyar dazatai murna da danta ya kwaso mata mace wacce ba yar mulki ba irinki”

Binta cikin rashin fahimta tace “ni ai tare muka taso.”
Hari ta mike tace “da alama an gama taran naji masu busa sun daina.”

Binta na kokarin fitowa Junaid na shigowa bangaren.
Daga nesa ya kalleta cikin jin dadi, gashi tai wanka ta sa kaya duk da kayan ta ne nacan amma tayi kyau.
Fuskarsa dauke da murmushi yake kallanta harta karaso inda yake.

Tace “wai harkun gama?”
Fuskarsa ya canza yace “ko na koma?” Yai maganar yana neman juyawa, da sauri tace “wasa nakeyi.”
Kallanta yai yace “Muje?”
Kai ta daga suka nufi cikin kilisarsa yana nuna mata.
Sannan yace “dazu na tafin miki da abu amma Azi ya manta inda ya ajiye saboda nemanki da akai tayi.”

Tace “ina binka bashi.”
Dariya sukai a tare.....

**********

Ran Hajjo yakai matuka gun baci dan abinda akai a tarancan ba karamin bata mata rai yai ba.
Kallan Zubair tai tace “kaga abinda nake ce maka ko? Idan har bamuyi da gaske ba yan kallo za’a barmu a gidan nan.”

Zubair ya kalleta shikanshi abinda ya faru ya bata masa rai, yace “Amma Hajjo abinda mai martaba yai dazu ya kyauta?”
Ramlatu wace ta biyesu ce ta kalli Hajjo tace “sai fa mun dage inba haka ba komai zai lalace ne ba tare da mun shirya ba.”

Hajjo ta kalleta sannan tace “Zubair jeka zan nemeka.”

Nan Zubair ya mike ya fita, Hajjo ce ta maida dubanta kan Ramlatu tace “kin samo yanda za’ai?”

Ramlatu ta kalleta tace “karki damu ina tunanin ido zamu zuba komai zai wakana ne in muka sa hannu kadan.”
Hajjo tace “me kike nufi?”
Murmushi ti sannan ta kara matsowa tace “kinsan ya taho da yarinya daga can inda ya taso?”

Cikin mamaki Hajjo tace “yarinya kuma?”
“Eh dazu bakiga ya fita ba ana taro, haka kawai jikina yaban akwai wani abu shine na tura abi bayansa.”

Hajjo cikin kaguwa tace “sai akai ya?”

Ashe yarinya yake nema
Hajjo mamaki karara ya bayyana a fuskarta tace “meye tsakaninsu?”

Ramlatu tai dariya tace “meye tsakanin mace da namiji ai ko daga yanda ya mike yabar gun alamace ta tanada babban matsayi a gunshi.”
Wata irin dariya Hajjo ta saka wanda ki kaina ban taba jin tayi dariya haka ba, har kwallace ta taru a idanta sannan tace “zanso ganin halin da Azeema ke ciki.”

Ramlatu tai dariya itama tace “shiyasa zamu taimaka kadan muja baya muyi kallo.”

Hajjo tace “kisa a sanar da cewar Junaid ya taho da mata daga can tana zaune a bangarensa.”

Ramlatu tace “angama Hajjo.”
Dariya suka sakeyi, Hajjo tace “ashe fadan ba namu bane, tsakanin uwa sa d’a za’ai.”
Ramlatu tace “sosai mu namu ido, har na kosa naga abinda zai faru.”

Hajjo tai murmushin jin dadi tace “nima.”

Zeenatu dake tsaye a kofa zata shigo ne taji suna zancen ta juya ranta a bace tana cijen lebe, yarinya? Itace kenan wacce Azeema ke magana dazu?
Tana shiga bangarenta ta wuce daki ta rufe kofa cikin takaici da jin haushi, shiyasa Junaid ko kallan mutumci bai mata ba dazu kenan?

Tabbas sai ta dawo da hankalinsa kanta, shiru tai kafin tace meye nawa nasan kaida hankalinsa kaina?
Shiru tai tana tunanin sa tun daga sanda yazo a matsayin bawa har zuwa wannan lokacin data ganshi.
Idanu ta lumshe kafin ta kifa kanta kan gado, tabbas sam Junaid take kuma ta riga tayi alkawari duk sanda ta samu namijin da takeso ko za’a mutu sai ta sameshi.

****************

Yau wani irin nishadi ya tashi dashi, fitowa falansa yai dan yaji motsin Binta, kallanta yai cikin jin dadi yace “kin tashi?”

Ta kalleshi tace “ ya akai kasan nice?”
Murmushi yai sannan ya zauna yace “me kikeyi?”
Gyara
Alama ya mata datazo ta zauna, nan ta matso ta zauna tare da kallansa

Please Login or Register in order to submit comment