Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta alfarmar gaske, wanda kudin da aka kashe gun shirya ta ma ba kadan bane.

Tana zaune akan wata had’ad’iyar kujerar mulki, tayi kyau iya haduwa.
Dauke kansa yai daga kanta sannan ya duba inda zsi hango Binta.

Bai ganta ba hakan yasa ya fara sa kafa cikin gun yana dan amsa gaisuwar da ake mai.

Me zai gani? Daga kasan Zeena ya hango binta zaune kan tabarma, Safiya na tsaye itama ranta da alama ya sosu.
Hajjo wacce ta shirya wannan wulakancin ce takalleshi tace “barka da zuwa Ango.”

Kallanta yai sannan yai murmushi yace “barka dai Hajjo.”

Kusa da Zeena ta nuna mai ya zauna, ya kalleta sannan ya kalli Zeena yace “Ayya Hajjo bayana ciwo yake banajin zama akan kujera, kasa nakeso.”

Kasa? Cikin mamaki ta tambayeshi a hankali.
Yace “eh.”
Kallan manyan mutanem data gayyata tai sannan tace “Junaid ka daure ka zauna akan kujera saboda mutane.”
Mutane? Ya za’ayi? Yanzu kuma naji ma zaman kasan bazan iya ba, komawa nake san yi.”

Ido Hajjo t zaro tace “komawa?”
Yace”eh Hajjo ni na kawo kaina kuma inada ikon komawa.”

Zeena wacce ta zuba musu ido tana san sanin me suke tattauna wa haka.

Hajjo tace “ni matsayin mahaifiyarka nake kuma na umarceka daka wuce ka zauna.”
Yace “to Hajjo zan zauna.”

Yana fadin haka ya fara takawa, murmushi Zeena ta saki cikin jin dadi, kallansa tai cikin so tana jin wani dadh na ratsata.

Har yakai jikin kujerar ta kawai ya karasa kan tabarmar da Binta ke kai ya zauna.

Ido aka zubamai, kowa ya saki baki, balle da akaga kayansu iri daya.

Zeena gaba daya jitai kanta ya kulle, Hajjo kam kasa ko motsi tai.

A hankali Binta tace “yaya me kake anan?”

Kusa da kunnenta ya matso cikin rada yace “na jure ganin ana wulakantaki ne dan ba yanda zanyi, yanzu kuwa ke matata ce bazan iya jure ganin ana taba min ke ba, ko wanene kuwa.”

Murmushi ta saki wanda gaba daya idan mutane na kansu, Safiya kam tama rasa me zatai, lalai wato Azeema tasan akwai abinda zai faru shiyasa batazo ba.


Tab🙊🚶🏻♀️



*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{33}

Gaba daya Hajjo kallan mutanen gun ta shiga yi wanda suke gulma da zunden abinda ke faruwa, Zeena kam hawaye ne taji ya zubo mata ta zubawa Junaid ido wanda ko kallanta baiyi ba.

Hajjo ta kalli Zeena wacce kana ganinta kasan tana cikin tsananin kunci.
Safiya ta daure ta kalli Junaid tace “ya isa haka nan, bari zan maida Binta ka zauna ku rabu lfy, ka gama wulakantasu wannan ma ya isa.”

Binta ta kalleshi tace “ni zan koma yaya, kayi hakuri.”
Mikewa tai Junaid yabita da kallo suka bar gun, Ramlatu ce tasa dariya tace “masha Allah, dama mun shirya haka ne dan kowa ya gane wacece Amaryar, yanzu tunda kun ganta shiyasa ta tafi, taran dama na Yarima Junaid ne da Gimbiya Zeena.”

Junaid ya mike ya zaune kuda da Zeena fuskarsa a hade tam kai bakace shine dazu yake rada ba.

Zeena kam gaba daya komai ya fita a kanta, duk kwanakin data dauka tanw gyaran jikinta dan ta farantamai, a haka ta kare?

Junaid baiyo minti goma a zaune ba ya kalli Hajjo yace “in ba laifi zan koma.”
Kallansa tai cikin kufula tace “banda wulakancin da ka mana wani kake neman sakewa?”
Zeena ya kalla yace “baso kike mu tashi ba?”

Kallan Hajjo tai tace “Hajjo zamuyi magna ne, ku karasa.”
Hajjo zata sake magana Zeena ta mike, Junaid ya mike suka bar gun a tare.

Suna fita daga gun ta kalleshi idanunta a raunane tace “nagode da toxartani dakai a cikin mutane.”
Cikin kasaita ya kalleta kamar zaiyi magana kawai ya fara tafiya, da kallo ta bishi idanunta suka ciciko.
Fure ce ta matso da sauri tace “Gimbiya karki bata kwalliyarki.....”

Waska mata mari tai cikin sauke jin haushi ta tace “kwalliyar uban me?”

Ta juya ta fara tafiya, dakinta ta shiga tana shiga ta rufe kofa cikin tsananin kunar rai.

Junaid kam bangaren Azeema ya wuce daga gun da yake, tana zaune cikin tsirarin mutanen da basu je ba, ana yi mai iso suka fara guda da kiranshi Ango kasha kamshi, kamshin ma har guda biyu.

Junaid ya gaishesu ya wuce ciki, Azeema ta mike ta bi bayansa.

Yana zaune a kasa a dakinta ta shiga, zama tai akan kujerar dake gabansa tace “harkun dawo?”
Ido ya zuba mata bai ce komai ba, tace “menene?”
Shiru yai wanda ya da hankalinta yadan tashi sai gani tai ya saki murmushi yace “kawai ina mamakin meya hana Ummana zuwa gun taron nan ne.”

Kallansa tai tana nazarinsa, sannan tace “banadan jin dadi ne shi yasa.”
Kai ya jinjina a hankali cikin alamar gamsuwa yace “ayya! Na tabbatar Ummana bazataki zuwa gun ba haka kawai bayan tasan za’a wulakanta mata surukar ta wanda danta ke so ba.”

Gaban Azeema ne ya fadi, ta kalleshi sannan ta kakaro murmushi tai sai dai bata tofa komai ba.
Mikewa yai ya mata sallama ya fita, idanunta ta runtse.

Junaid na fita yai kofar baya inda ta sadashi da inda Binta take zaune.
Tana kwance a daki, ya shiga falan, ganin bakowa ya bude kofar dakin a hankali, tana kwance idanunta na zubar da kwalla.
Tuno sanda suka isa gun tai, Ramlatu ta nuna mata tabarma akan ta zauna anan bayan ko bakin gun kowa a kan kujera yake.

Junaid ne ya tako a hankali, jin motsi yasa tai saurin goge hawayenta ta dago dan ganin waye.

Junaid ne ya tsaya a inda yake kusa da gadan, ya sakar mata wani lallausan murmushi.
Itama murmushin ta maidamai idanunta na kara neman ciko kwalla.

Karasowa yai a hankali jikin gadan ya zauna, kallansa tai tace “yaushe kazo?”
Hannu yasa a hankali kan fuskarta yana dan murza hannun a hankali, sannan ya jawota jikinsa ya rungume.

Shiru suka danyi a hankali yace “kiyi hakuri Binta, na kawoki inda ba’asan darajar ki ba, sai dai daga yanzu bazan sake bari wani yacimin zarafinki ba.”

A hankali tace “bakomai Yaya, barina da akai na cigaba da zama kusa dakai ya isheni.”

A hankali ya dagota yace “nagode Binta, a koda yaushe ina alfahari da kasancewarki tare dani.”

Tace “nice da godiya yaya, ka ceci rayuwata dana mahaifiyata ka kuma kula dani kamar yar gata.”

Murmushi ya sake mata cikin tausayinta ya sake rungumeta, kafin ya saketa yace “inaso ki san kome zai faru daga yanzu Junaid na dauke da Binta a cikin ransa, sannan kome Junaid yakeyi bazai taba mantawa da ita ba.”

Kai ta daga alamar fahimta sannan tace “to Ya Junaid.”
Ni ynzu mijinki ne haka za’a cigaba da cemin Yaya?

Kasa dakai tai tana murmushin kunya, yace “ba’a san nazo nan ba zan wuce.”
Kai t daga alamar to sannan tace “Nagode Ya Junaid.”
Sai kin iso.
Kai tai da kanta cikin kunya
Mikewa yai ya fita, haryakai kofa ya sake juyowa ya kalleta sannan ya fita.

Ta baya ya fita.

*****


Hajjo cikin takaici ta nufi dakin Zeena ranta a bace matuka.
Tana shiga tace “A haka kike sansa har kika nemi auransa bada amincewa ta ba?”

Zeena dake kwance ta mike zaune tace “Hajjo dan Allah ki barni da abinda ke damuna, duk ba ke kikaja ba, da baki gayyaceta ba hakan zai faru ne? Ko da baki sata a kasa ba hakan zai faru?”

“Wato laifin nawa ne kenan? Sanda na fada miki abinda zanyi ba dadi kikaji ba?”

Zeena cikin masifa tace “to yanzu waye ya wulakanta?”

Kin rufemin baki ko sai na fasashi? Waye yace kice kina san wanda baya sanki? Ai mace in tanada tunani gwara ta auri wanda bataso yake san akan ta auri wanda takeso baya santa.”

Zeena ta turo baki ta kwanta, kin tashi kin shirya ko sai ranki ya baci?

Zeena tana jinta batace komai ba dan bakin ciki.

Hajjo cikin bacin rai ta fita.

Dakinta ta shiga ta kalli Zubair dake jiranta tace “kai kuma ya akai?”
Yace “Hajjo gaskiya kima Abba magana ya bani wani mulkin, sam bazan iya zama banda komai ba.

Ka tashi ka bar nan ko sai ranka ya baci, ni wai meyasa gaba daya kuke nema ku kasheni da bakin ciki saboda waccen yaran? Kanwarka ta aureshi kai kuma ka bari ya kwace abinda yake naka, sannan yanzu kazo kana min wani zance daban?

Zubair ya mike ya fita rai a bace.

Yana fita Hajjo ta da hannu akanta dake sarawa.

********

Azeema da kanta ta shirya Binta dan tabbas taji kunyar abinda ta aikata, sannan ta fahimci Junaid yasan da saninta.

Safiya da Barira suka taimaka mata aka shiryata.

Sanye take cikin atamfa tayi kyau sosai, dan Azeema duk kayan lefen da sukai dinka mata su tai saboda rashin kayan sawar ta.
Lefe ma haka aka kaima Zeena ukun na Binta, sai dai Junaid bai tanka ba.

Binta tayi kyau sosai, Azeema ta mika mata kofi cike da madara tace ta shanye.
Binta ta shanye sannan Azeema ta kalleta tace “Binta!”

Binta a hankali tace “Naam”
Azeem tace “kiyi hakuri abubuwan dana aikata miki, sannan inaso kisan zaman masarauta bazai taba yiwuwa da hali irin naki ba.”

Kallanta Binta tai cikin rashin fahimta, Azeema tacigaba “dolene ki san kanki, ki kuma zama mai san kanki.”

Bata gane me take nufi ba, Azeema tace “Duk sanda kikaga bazaki dauki abinda ake miki ba ki tuno kalaman nan lokacin zaki fahimta, sannan a kods yaushe ki zama mai amfani da damarki.”

A hankali Binta tace “Nagode Gimbiya, nasan dalilinki na rashin sona wanda ko wanene bazai so wacce ba’a san iyayenta bama, sai dai a koda yaushe ina miki godiya a raina nakin korata da kikai, balle harkika barni na auri Yaya, nagode sosai.”

Jikin Azeema ne ya kara sanyi, ta kalli su Safiya tace “in lokaci yayi ankai Zeena sai ku kaita.”

Tace “to.”

********
“Kin zama matar Junaid daga wannan rana, dan haka a koda yaushe ki zama mai kama kai da kuma kula da mijinki, sannan duk sanda kika ga mijinki yayi abinda bai dace ba ki zama mai kokarin nuna masa.” Sarki ya kalleta bayan yazo nan a ransa yace “Allah yasa sadaukarwa da auranku danai ya biya mun bukatata.”

Zeena tai godiya sannan tai sallama suka fito.

Hajjo zamu wuce, abinda Zeena ke fada kenan a jikin kofar dakin Hajjo.
Hajjo na jinta sai dai haushin abinda ya faru dazu ya hanata fitowa.

Kanwar Hajjo tace “Zeena muje lokaci na wucewa kece Uwar gida ke za’a fara kaiwa.”

Zeena ta gyara alkyabarta ta sauketa ta rufe fuskarta sannan suka riketa suka hau guda suka fito.

Mutane sun cika a gun ‘yan kai Amarya, sai busa ake ana guda tare da kirari.

Haka suka nufi bangaren Junaid.

Bangarenta wanda yasha gyara ta ko ina.

Suka ajiyeta sannan sai datakai wajen awa daya aka kawo Binta nata bangaren dake gefe.

Junaid na zaune kan salaya yana tilawa, sai daya gama sannan ya rufe qur’anin yahau addu’oi tare da fatan Allah ya bashi damar yin abinda ya dace a koda yaushe.
Yan kai amarya kowa ya watse.

Zeena ta kalli Fure tace “mikon madubi naga fuskata.”

Da sauri Fure ta miko mata, Zeena ta kalli fuskarta ta kara dan gyagyarawa sannan ta maids fuskarta ta rufe.

Binta kam sanin Safiya tace mata yau kwanan Zeena ne tunda itace Uwar gida yasa ta sauke alkyabar ta ta dauro alwala tai salla.

Junaid ne ya kalli Azi wanda ke durkushe yana jiran Junaid ya nufi bangaren Gimbiya.

Junaid ya tashi ganin wannan ne tuni na kusan biyar da Azi ke mai.

Junaid ya na mikewa Azi yace “Yauwa Yarima, an gaisheka.”

Junaid bai tankashi ba suka fito, bangaren Binta ya kalla, harya juya sai kuma Azi yaga ya nufi can.

Hankali a tashe Azi yace “Yarima yau kaine xakaje gun Gimbiya Zeena itace uwar gida.”

Junaid ya kalleshi yace “na sani.”
Azi yai kasa dakai, bakin kofarta yaje kamar zai shiga sai kuma ya juga suka nufi sashen Zeena.

Fure haryanzu bai iso ba?
Fure tace “haryanzu Gimbiya.”

Zeena haushi ya kamata tace “badai gun yarinyar can zaije ba ko?”

Da sauri Fure tace inaaaa ai bazai yiwu ba.

Isowar Junaid aka sanar wanda yasa Zeena jin dadi.

Junaid na shigowa suka fita suka bar dakin dukansu.

Kallanta yai sannan ya karasa cikin dakin, zama yai akan kujera sannan ya gyara kafafunsa ya kishingida

Zeena dake zaune taji shiru hakan yasa tadan bude kanta.

Tsananin mamaki ne yasa ta bude baki tana kallansa.........

🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{34}

Cikin rashin fahimta Zeena ta kalleshi tace "Ya Junaid?"

Idanunsa na rufe bai bude ba yace "Hmm."
"Mekenan?"
Ta fada fuska dauke da mamaki, juya baya yai ya fuskanci gefen kujera yace "inkinyi sallah ki kwanta, ni bacci zanyi."

Idanu ta zaro cikin mamaki, sai dai a matsayinta na maje me aji batasan me zata sake cemai ba.
Gaba daya ta kasa ko mikewa daga inda take, tafi awa daya a haka kafin ta mike cikin takaici tai alwala tai sallah, kusa dashi taje ta zuba mai ido, shikam baccin sa yake sosai zuciya daya, bakinta ne ya shiga rawa cikin takaici ta juya ta kwanta.

Jin sanyin gari yasa taja bargo, kallansa tai hanayensa a hade, da alama shima sanyin yake ji harararsa tai tace kai taji din.
Ta juya baya, sai dai sam ta kasa bacci, haka ta mike ta dau bargon ta rufamai ta luluba da zanin gadan.

Da safe bayan yai sallah ya zauna ya kasa yana nazari, tare da kallan Zeena wacce ke bacci.


Zeena kam baccinta ta shara dan sai da rana ta fito.

Idanu ta bude cikin bacci, mamaki tai da idanunta suka sauka akan Junaid.
Yana zaune yana kallanta hannayensa a harde, da sauri ta mike zaune tace “Ya Junaid!”

Idanunsa na kanta yace “ada bayan Jakadiya dake bangaren Marigayi, a cikin bayinshi akwai wanda ya bar masarautar nan bayan rasuwarsa?”

Kallansa tai cikin mamaki sannan tace “yaya ya daga tashi dai tambayar da ni kaina bansan ta ba?”

Ki tuno, kin tabaji anyi maganar wani wanda yabar masarautar nan bayan rasuwarsa.

Kallansa tai kafin tace “ni dai mutum biyu na tabaji, daya Allah yamai rasuwa.”
Dayan fa?
Tai dan shiru kafin tace “ban sani ba gaskiya, wasu sunce ya rasu wasu sunce yanada rai.”

Su waye sukace ya rasu su waye sukace yana da rai?

Kallansa tai cikin dan shakka, sannan tai shiru, mikewa yai a hankali yazo inda take kan gado, ya zauna, yace “wanene?”
Kallansa tai a hankali sannan tace “nadaiji rannan Hajjo na umartan a nemo mata shi, sunanshi Sabisu, shine mai kula da sarki.”

Shiru yai kafin yace “Hajjo ta sameshi?”

Kallansa Zeena tai tace “menene Ya Junaid?”

Yace “kawai ina san sanin wadanda suka taimaki mahaifina ne.”

Sam bata yadda da wannan zancen ba, yanda ta dago ne yasa yace “menene?”

Shiru tai a ranta tana neman saita kwakwalwarta sannan tace “Bata sameshi ba a iya sanina kenan.”

Mikewa yai sannan yace “nagode.”

Har ya juya zai fita tace “idan na samoma shi me zan samu?”

Juyowa yai ya kalleta, itama kallansa takeyi tace “na tabbatar hanya ta sai tafi taka saboda baka dade anan ba, idan na samoma shi ni kuma me zan samu daga gareka?”

Wani rainanen murmushi ya saki yace “me kikeso?”

Shiru tai tare da dan motsa baki, yace “me? Kwana dani?”

Kallansa tai zuciyar ta tayi matukar kuntata, idanunta ne suka ciciko tace “in naso haka laifi ne? Meyasa yaya kake yabamin magana san ranka?”

Kallanta yai sai dai baice komai ba ya juya zai fita.

Daurewa tai tace “karka manta zamu gaida Umma karama.”
Bai amsa mata ba yai fitarsa.

Cikin takaici ta sa hannu ta cilar da filo din dake bayanta.

Junaid kam yana fita ya kalli Azi yace “Azi ka nemomin wani sanisu a bangaren Marigayi yake.”

Gaban Azi ne ya fadi ya kalleshi yace “Sabisu?”

Junaid ya tsaya tare da kallan idansa yace kasanshi ne?

Dasauri Azi yace “a’a”
Junaid yace “ka nemomin shi sannan inka san inda yake karka fadawa kowa ko shi kansa, ka sanar dani gun.”

Azi yace to.

Bangaren Binta ya nufa.

Tana ta gyara gadan data tashi daga bacci ya shiga.
Jin motsin bude kofar dakin da take ne yasa ta juyo.
Tsayawa yai a jikin kofar cikin wani irin farin ciki yace “Hajiya Binta me kikeyi?”

Ya Junaid!

A hankali ya fara takowa yana zuwa yasa hannu ya rikota, kan gado ya zaunar da ita sannan ya kwanta akan cinyarta tare da rufe idanunsa.

Shiru tai tare da saukar da kanta kasa, sai dai hakan ya kai fuskarta saitin nashi fuskar.
Shiru tai tana kallan fuskarsa, wani sansanyan murmushi ta saki tana kallan fuskarsa.

Bai bude idanunsa ba sai jitai yace “irin wannan kure kallo? Ko so kike ki gano munina?”

Hannu tasa da sauri ta rufe fuskarta, kansa ya juyar saitin cikinta, yasa hannunsa yasa ya zagayo dashi zuwa bayansa.
A hankali taja wani dan numfashi, ya.....”
Katseta yai da cewa “jina nake kamar a mafarki.”

Wani murmushi ta saki, tare da yin shiru, a hankali dan karamin bacci ya daukeshi, saboda farkawar dayai da daddare yana kokarin gano abinda bashida masaniya a kanshi.

Hannu tasa a kansa tana shafa a hankali, can tace “nice nake ganin komai kamar a mafarki? Ban taba kawo wannan rana ba a tsayin rayuwata, ina mamaki abinda ke faruwa, a da na dauka a matsayin yaya na daukeka, sai dai tun daga sanda kabi bayan Gimbiya nasan zuciyata da biyu ta daukeka.
Kaine dai bansan ko haryanzu a matsayin kanwa nake na a gareka.”

Bata taba zata ba sai gani tai ya juyo ya kalleta, hannu yasa ya turata kan gadan tai baya ta kwanta, matsowa yai kusa da ita ta samanta yasa hannu a kan fuskarta yace “kinasan sani?”

Hannu tasa ta rufe fuskarta, hannu yasa ya zare hannunta yace “shine abinda yake damunki?”

Shiru tai sai dai tadan daga kai kadan, a hankali ya turo fuskarsa saitin tata, ya sumbaci goshints, ya sumbashi idanunta wanda ta lumshe su saboda wani shauki daya zo mata.

Kan hancinta ya sake sumbata sannan ya saukar da bakinsa kan nata, dan karamin sumba ya fara mata sannan ya kalleta tare da kara kai bakinshi cikin nata.

Me takeji?
Gaba daya jitai komai na jikinta ya kule, sai da ya gama sumbatarta sosai, sannan ya dago ya sa hannu ya dan kishingida ta gefenta ya kalleta yace “Ni tun sanda nasan kaina nasan ina sanki.”
A hankali ta bude idanunta da gaba daya suka shanye, ta kalleshi, yace “gani ke ba da wannan kika dauken ba yasa bantaba nuna miki ba.

Idanunta ne suke ciciko, tace “Ya Junaid nagode da kakesan wannan wacce batada gatan.”

Yatsansa ya saka akan lebanta sannan ya hade fuska sosai da sosai yace “meye hakan?”

Kallansa tai taga yanda ransa ya baci, mikewa yai ya zauna fuskarsa a hade.

Tanadaga kwance tasa hannu ta kamo rigarshi, dan jan rigar tai hakan ya sashi yai baya, tace “na daina.”

Kallanta yai yace “karki sake”

Da sauri tace “to.”

Jawota yai jikinsa ya rungume.

Baisan bacci ya daukeshi ba, ganin yanda yake bacci yasa ta zare jikinta a hankali ta fito ta rufe kofar.

Harira ta gani a waje, ta bude mata, Harira ta kalli kuyangun tace “ku shiga da abincin.”

Nan suka fara shiga da abincin, Binta ta kalleta, Harira tace “Azi yace yarima yana nan ko?”

Binta ta daga kai alamar eh.

Nan suka ajiye suka fita.

*********


Ta gama kwalliya duk da fuskarta kana kallo kasan ba ta farinciki duk kuwa da kasancewar ta Amarya.

Kallan Fure tai wacce ke gyara mata kanta tace “Ki aika a cema Yarima na shirya.”

Fure ta ajiye comb din ta fita.

Sai dai ba kowa a bangarensa sai bayinsa, nan suka sanar mata yana bangaren Binta.

Mamaki ya kama Fure cikin jin haushi ta nufi bangaren Zeena ta sanar da ita.

Zeena cikin mamaki tace “mene?”

Fure tace “ancema wai bacci yake.”

Bacin raine karara ya bayyana a fuskar Zeena ta mike a fusace tace kiramin Bintan.

Binta tasa kaya kenan bayan tayi wanka tana jiran Junaid ya tashi suci abinci dan dama tun can ma tare suke ci.

Harira ce ta shigo da sauri ta kalli Binta.

Binta tace “Harira ashe kina nan.”

Ana magana a waje.”

Binta ta fito, ganin Fure yasa tace “ya akai?”

Fure tace kizo.
Ta juya.

Zeena na zaune a falanta Binta ta shiga.

Kallanta tai cikin tsananin kishi, sannan ta daure bacin ranta tace “dama tambaya zanyi Ya Junaid ya farka?”

Binta tai kalleta, Zeena tai murmushi tace “dazu yace zaije gunki ganin ke kadai kika kwana, sannan yace bacci yakeji nasan kila yadan kwanta ne.”

Binta tai shiru ta kasa magana, Zeena ta mike da kyar tace “zauna mana, kefa yanzu matar yarima ce, kiyi hakuri nima ba dadi nakeji ba.”
Tadanyi kasa da murya tace kinsan maza da ranar daren farko, sai ana komawa baccin safe.”


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{35}

Binta dake kasa tace "bakomai nan ma ya isa."
Yanda tai maganar Gimbiya ta fahimci taji haushi, a ranta tace kiji yanda naji kema, sannan nasan bazai taba cemiki bai kwana dani ba shima.
Wata zuciyarce tace inya fada fa?

Binta ce ta katseta da cewa "zan sanar masa."

Sannan ta nemi izinin tafiya.
Tana fita Zeena ta kumburo fuska cikin tsananin kishi, maganar daya yaba mata jiya ta tuno, wato daga cemai me zata samu shine zai fada mata haka?

*****
Binta kam tana fita ta nufi bangarenta sam ta rasa me yasa take jinta duk ba dadi, a iya saninta dai Zeena matarsa ce yana kuma da hakkin yin duk abinda yaga dama da ita, to menene nata najin haushi?

Turo kofar bangarenta tai, mamaki ne ya kamata dataga Junaid a zaune akan kujera.
Kallanta hai yace “Daga ina?”

Tace “naje gun Harira ne.”

Hannunsa ya miko mata, a hankali ta karaso ta rike hannunsa, jiti ya jawota ta zauna akan cinyarsa, yace “Binta!”

Naam!
Ya zuba mata idoyace “yanzu da da fa ba daya bane, kada ki kuskura ki bar wani ya rainaki, ke matar Junaid ce, ko gunsu Harira karki sake zuwa in kina nemanta ki aika tazo.”

Tace to, yace “ni dai a iya sanina Binta da ko Junaid bai isa takata ya wuce ba amma tunda kikazo nan kin bari kowa ya rainaki, karki kuskura ki cigaba da bari ana rainaki, in ba haka ba nan gaba baki isa ki gyara ba.”

Dariya tadanyi tace “ko kaine?”
Yace “eh ko nine kimin masifa yanda kika saba da in aka bata miki rai.”
Dariya ta sakeyi sannan tace “Abinci.”

Kallan Abincin yai yace “a bangaren Umma karama zamu karya.”

Jikinta ne yai sanyi ta daga kai alamar to sannan ta mike daga kan cinyarsa tace “ana jiranka.”

Mikewa yai yace “bari na shirya”

Ya fita, da kallo ta bishi sannan ta zauna abakin kujerar daya tashi cikin sanyin jiki.

*********

Junaid na fita ya wuce ya shirya, sanye yake cikin dakakiyar shadda kalar gajinare hula ya saka sannan ya saka takalmi yayi kyau kwarai da gaske.
Yana fitowa ya kalli Azi yace “ki kira Binta.”

Azi ya kalleshi sai dai ganin yanda ya hade fuska yace “To Rankanya dade.”

Nan ya kalli dayan bawan nasa yace “yima Zeenatu magana.”
Nan shima ya jiya da sauri.

Junaid ya karasa sa takalminsa sannan ya fito ragowar hadiman na biye dashi.
Binta dake zaune inda aka barta Azi ya sanar da ita sakon Junaid, cikin jin dadin hakan yasa ta mike da sauri ta shiga daki itama ta zura alkyabarta, kasancewar karta tsaya kwalliya ta bata ran Junaid yasa ta fito.

Zeena ce tsaye kusa dashi da alama magana sukeyi, kallan Zeena tai taga tasha uban kwalliya.
Dan murmushi ta kakaro sannan ta nufo su.
Agun Zeena da Junaid kuwa kallansa tai tace “bangane Binta muke jira ba?”

Wani kallo ya mata yace “batada hakkin zuwa ne?”
“Ba haka bane amma ai......”
Yace “badai haryanzu a matsayin wacce batada matsayi a gidan nan kike kallanta ba?”

Ranta ne ya baci ta kalleshi, yace “karki manta kishiyarki ce matar Junaid, a ynzu in aka wulakanta matata kamar ni aka wulakanta, kuma ke ma kamar ke aka wulakanta.”

Shiru tai saboda tama rasa me zatace ta ina dan an wulakanta Binta aka wulakantata?
Isowar Binta ne yasa t mata wani banzan kallo.

Junaid wanda haryanzu fuskarsa a hade take yace “muje.”

Haka suka taho

Please Login or Register in order to submit comment