Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fadi.

Junaid ne ya shigo cikin isa da takamarsa, ya gaida sarki sannan ya zauna.

Wakilai suka kalli Junaid sannan suka kalli Sarki, wakilin sarkin kano ne yace “wannan sako ne daga mai martaba sarkin Kano, tabbas yana kara jinjina maka yace mu tafin masa da ranar yin nadin shi da kansa zaizo.”

Sarkin Zazzau ma abu daya ya fada, ajiye kayan kyautar da suka kawoma Junaid sukai sannan suka gaisheshi.

Gaba daya Abdulsalam ya kara rikicewa kafafunsa kawai yake matsewa ta cikin kayansa.

Junaid ya amsa tare da yin godiya, sai da suka fita, Turaki yace “ai Sarki wannan lamari kowa yana bashi mamaki, duk da muma ba san murabus dinka muke ba amma in muka tuna namijin kokarin dakai gun yanke wannan hukunci sai musan bakuda bakin magana.”

Nan kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, Abdulsalam ji yake kamar ya saki wani ihu a gun da yake.

Junaid ne ya kalleshi cikin mamaki yace “Takawa ina tafe ina fatan Allah yasa ba abinda kake shirin fada yasa ka taramu ba?”

Abdulsalam ya kalleshi me yake shirin yi?

Zubair ne ya shigo ya zauna, Turaki yace “Mai Martaba badai....?”

Sai yai shiru suna kallan Juna.
Wale yace “Takawa bai kamata ayi abu cikin gaggawa ba.”

Junaid yace “sosai ma kuwa, komai ayishi a hankali, dan Allah ka janye alkawarin nan naka na yau zaka ajiye mulkin nan.”

Bai san sanda ya bude baki ba, Waziri cikin tsoron Junaid ya kalli Sarki anya wannan zai barsu suma kuwa?

Turaki yace “au yau? Indai Alkawari yai ba yanda zamuyi.”

Junaid ya kalli Abdulsalam sannan ya kalli Zubair wanda ya kumbura fam.

Abdulsalam idanunsa ne suka canza kala, ya daure ya kallesu yanzu kam yasan bashida wata mafita, inba so yake komai ya fito ba, an gama daureshi ta ko ina.

Wale ne yace “da alama Sarki sauri yake ya baka mulki a matsayinka na sirikinsa kuma dansa, yafisan yai jika yana gefe.”

Dariya sukai dukansu wanda dariyar ta kasance kamar arsashi ne ya dira a zuciyarsa.

Zubair ya kalla wanda ya gama bata rai, Junaid ya kalla wanda ya kalleshi shima.

Mamaki me ya kamashi dayaji yace “to Mai Martaba.”

Kafin ya fara tunanin me zaiyi kawai yaga ya taso yazo inda yake ya tsuguna, ya dukufo kusa da kunnensa.

Yace “idan har baka sauka ba a wannan lokacin yanzu kuma, duk abinda ya biyo baya a wannan lokacin karkaga laifin kowa sai naka, ga danka ga fadawan ka nan, kowa yaga mumunan halinka da kake boyewa a cikin fara’arka, sannan kar ka manta ina da shaidar laifukanka, kana batamin rai komai xai tarwatse a gun nan.”

Murmushi yai bayan ya dago ya daga kai alamar to sannan ya juya ya zauna.

Waziri dasu Shamaki ba shakka tsananin tsoron Junaid ya gama kamasu.

Sarki ya daure yai gyaran murya, da kyar ya samu ya daidaita muryar sa dake rawa yace “abu dai da kukaji haka yake, ina faran zaku bani hadin kai, nima na samu na huta, dama can asalin mulkin nan na shi ne, na rikemai ne saboda mahaifinsa ne wato yayana ya sani, sai dai yanzu Junaid ya girma yayi aure, na tabbatar ku kanku yanzu kunsan Junaid ya cancanci kujerarsa.”

Zubair kara habaka yai, cikin bacin rai matuka.

Sukam yan fada kowa ya gamsu da maganar Abdulsalam.

Yau zan ajiye mulkin nan, a wannan lokacin ina fatan xaku ba shi hadin kai, na tabbatar xai yi abinda ni da mahaifinsa bamuyi ba.”

Wale yai dan murmushi yace “tabbas Takawa samun irinka a duniya sai an tona.”

Junaid ya rusuna sosai yace “Ina godiya Takawa, na gode daka zabeni sama da jininka, wannan hallarci naka tabbas abin dubawa ne.”

Kallan Shamaki yai yace “a dako sandar mulki a da kamai, inyaso ragowar abin Sarauta sai ranar da za’ai nadin sai a bashi.”


Nan Shamaki ya juya ya fita, Waziri ya kalli Sarki wanda yasan Allah ne kadai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin.


********

Haka Binta ta zauna sai dataga Azeema taci abinci sosai, sannan sukafara hira sama sama duk da rabin hira Binta ce ke bata labarin tasowarsu da abubuwan daya faru a shekarun.

Azeema nata murmushin jin dadi tare da kunyar abinda ta aikata.

*********

Hajjo dake zauna cikin bacin rai ta kalli Ramlatu tace “ya kike ganin zanyi in kamo yarinyarcan?”

Ramlatu tace “ai Gimbiya ce in ta dage a abu ba mai hanata.”

Hajjo a kufule tace “duk ni na barta haka yanzu ga abinda take neman jawomin ai.”

Sanar da isowar Jakadiya da akai ne yasa Hajjo cikin mamaki ta kalli kofa.

Jakadiya cikin haki da alama gudu tai ta shigo ta zube a gabanta tace “Hajjo Hajjo.”

Hajjo ta kalleta rai a bace tace “meye kuma?”

Jakadiya tace “Sarki ya ajiye mulkinsa.”

Mene? Ta tambaya cikin rashin fahimta.

Jakadiya tace “an dako sandar mulki yanzu an shiga da ita fada, bansan meke faruwa ba.”


Hajjo tace “yauwa Abdulsalam gwara kaga Zubair mulkin kafin wacen mara mutuncin ya aikata mana tsiya, ashe shi yasa aka kira Zubair dazu?”

Cikin wata dariyar farin ciki ta tambayi Ramlatu.

Dariya sosai Hajjo take cikin jin dadi tana jin jina kai, Ramlatu sai kara wasa mata kai take.

🙊tab😝

****
Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{47}

Hajjo cikin tsananin murna ta mike ta fito daga sasshenta Ramlatu na bi mata baya cikin tsananin farin ciki.

Daga dan nesa kadan taga kamar Zeena da tata tawagar, baki ta tabe tace “naga bakin ki yanzu mai zaice.”

Hajjo tai gaba ba tare da ta kara ko kallan Zeena ba, Zeena wacce yanzu taji abinda ke faruwa ta taso dan san ganin Hajjo da halin da take ciki ta tsaya daga inda take, fuskarta dauke da mamaki, dan bata taba tunanin ganin Hajjo haka ba.

Kallan Fure tai tace “da alama Hajjo lafiyanta kalau, mu koma tun kafin wani abu ya faru muna waje.”

Nan Fure ta amsa dato, haka suka juya Zeenatu na tafe da tsananin mamakin abubuwa biyu, na farko murabus din da gaba daya bata taba tunani ba, sannan da ganin Hajjo hankali a kwance.

Hajjo tana tsakiyar masarauta inda tafiya kadan ne zai hadasu da Fada sukaji masu kirari da busa sun fara, sam duk yanda masu kirari Ke magana bataji saboda tsabar zumudi.
Ramlatu wacce yanzu kunnanta sukaji Junaid akema kirarin, yasa a tsorace ta matso kusa da Hajjo.

Hajjo ta tsaya ganin yanda tadan tare gefen tafiyarta kadan.

Hajjo tace “ya akai?”

Ramlatu a tsorace tace “Hajjo ina tunanin mu koma daga nan.”

Mu koma ina? Ai dole muje godiya, Ramlatu a tsorace take kallanta sannan tace “tuba nake Hajjo amma dakin danji me masu kirarin nan suke cewa.”

Kallan banza ta mata sannan tace “ina nake da lokacin jin wannan shirman, me suke cewa?”

Ramlatu dai tai shiru kafin tace “mu koma mu kira Yarima Zubair din yazo da kansa.”

Hajjo tai shiru kafin tace “bai kamata muje godiyar ba?”

Ramlatu tace “eh gwara mu jirashi.”

Shiru tai kafin tace “to.”

Juyawa tai suka koma, fuskarnan tata wasai da farinciki, kallan hanya tai tace “waccen yar rainin hankalin ta juya ne?”

Ramlatu da batama jita ba tana tunanin yanda zata zame ta gudu, Hajjo ta kalleta tace “me kike tunani?”

Ramlatu tace “inaji tsabar murna ce tasa kaina ciwo ina tunanin komawa bangarena kafin Yariman ya dawo.”

Hajjo tace “shikenan.”

Nan tai wuf ta gudu da hadimanta, Hajjo tana tafe tana farin ciki, daga sama sama taji kamar sun kira Junaid, sai kuma taji Zubair.

Baki ta tabe tace “wato yayan Junaid? Ni da sunbi ta tawa ko sunanansa basa kiraba.”

Tasa kafa zata shiga bangarenta taga Hadimanta ragowar data bari sun hada kai suna magana, suna ganinta sukai shiru.

Wucewa ciki tai ta zauna.

Batafi minti goma da zama ba sai ka bawan Zubair wanda yafi kusanci dashi ya nemi izini ya shigo.

Hajjo cikin zumudi tace “Aram ya akai? Ina Ranka ya dade din?”

Kallanta yai yace “Hajjo! ki taimaka ki aika a kira Yarima kafin wani abu ya sameshi.”

Me zai sameshi? Ta tambaya cikin mamaki.
Aram yace “Hajjo gaba daya ba wanda yake bi takan Yarima murna kawai suke taya Junaid ba wands ya damu da halin da yake ciki, gashi ba damar ya taso kar a dauka bakin ciki yake.”

Bakin ciki? Ta tambaya hankali a tashe.

Yace “bakiji Sarki ya ba Junaid mulkin na?”


A zabure ta mike tsaye tace “yaba Yarima me?”

Aram yace “yanzu kam ai kowa yasan abinda ke faruwa, tunda gashi anata busa ana kirarin ana sanarwa.”


Gaba daya hankalinta ne ya tashi tace “inji wa? Inki ubanwa yace ya isa ya ba Junaid mulki ba Zubair ba?”

Hajjo gaba daya ta rikice hankalinta a tashe take magana........


*****

Zeena sai sintiri take a sashenta kafin ta kalli Fure tace “hankalina ya kasa kwanciya Fure dubomin Binta.”

Nan Fure tai waje, bata dade ba ta dawo tace “tana bangaren Gimbiya Azeema.”

Zeena tace “tashi muje gun Umman.”

Nan suka fito.

Ramlatu tana gudu ta nufi bangaren Azeema.

Gimbiya na zaune suna hira da Binta, dan Binta yanzu ta sata ta fito falan ta, Barira sai dadi takeji.

Suna cikin hira ne aka fara bushe bushe, Azeema ta kalli Barira tace “Bari duba ki gani meke faruwa? Wannan busar busace ta Sarki.”

Nan Fure ta fita, bata dade ba ta dawo ta sanar da Azeema ai wai sarki me yai murabus yaba Junaid mulki.

Fuskarta dauke da tsananin mamaki tace “AbdulSalam din?”

Barira tace “eh.”

Shiru Azeema tai dan tasan tabbas ba abinda zai sa Abdulsalam yabar mulkim nan da yake so, sai dai ta tabbatar Junaid ne yasashi dole saboda abinda ya aikata.
Muryar Binta ce ta katseta datace “Haba Bari sai kace wasa ta ya za’ai murabus ba wanda ya sani.”

Barira tace “shine abin mamakin, gun a cike yake dam da alama an shirya dama”

Azeema tai shiru idanunta suka ciciko,babban burinta ada bai wuce Junaid ya samu mulki ba amma batasan meyasa yanzu gaba daya zuciyarta a cike take da tsanar kanta.

Shigowar Ramlatu ce yasa ta hade fuska, Ramlatu ta zauna ta gaisheta.

Azeema ta kalleta bayan ta amsa tace “lafiya?”

“Dama nazo wucewa nace bari nazo na gaisheki, na dade banzo na gaidake ba.”

Azeema ta dauke kai ko tanka mata batai ba.

Ramlatu tai dariya tace “Matar Yarima ce?”

Barira tace eh, Binta ce ta gaisheta.

“Ina Gimbiya Zeena? Allah yasa bata wahalar dake kinsam yarinyar nan Hajjo duk ta gama sangartata.”

Binta cikin mamaki ta kalleta, dan ita ko saninta batai ba kafin tace “ba abinda take min.”

Ramlatu tai dariya tace “ko dayake yanzu farko ne na tabbatar.......”

“Ya isa haka nan” abinda Azeema tace mata kenan.

Jiki a sanyaye tai shiru, Azeema tace “inkina gama gaisuwar zaki iya tafiya.”

Ramlatu wacce taji haushin haka ta mike tana dariya tace “ba laifi, bari na wuce.”

Tana kokarin fita ana sanar da isowar Zeena.

Idanu ta zaro kafin ta dan kauda kai.
Azeema ta kalleta sannan tama Barira alamar ta bata izini.

Nan Zeena ta shigo, tsayawa tai cikin mamaki ta kalli Ramlatu wacce yanzun nan fa taganta da Hajjo, Ramlatu tai saurin kallanta kafin tace “nazo wucewa ne shine na shigo mu gaisa, naga mun dade bamu ko gaisa ba.”

Zeena tai wani murmushin takaici tace “ko? Wucewar ce naganki yanzu da Hajjo?”

Ramlatu tai kasa dakai tace “eh zan wuce bangarenane.”

Zeena ta jinjina kai tace “haka akeso ki bar layin da zai sadaki da bangarenki kiyi zagaye, kin kyauta da kika zo gaidata.”

Ramlatu tai kasa dakai, nan tai sum sum ta fice.

Zama Zeena tai ta gaida Azeema, Binta kuma ta gaisheta.

Kallan Azeema tai tace “Umma Karama dan Allah kinsan meke faruwa? Gaba daya na kasa samun nutsuwa, na tabbatar akwai wani abu dake faruwa, duk da Ya Junaid yace kar nai bincike kar na tambaya amma sam hankalina ya kasa nutsuwa.”

Idanun Azeema ne a dan ciciko tace “kibi abinda mijinki yace sannan dake da Binta ku tashi ku koma bangarenku, kar wanda ya sake zuwa nan bangaren har sai Junaid yamin hukunci na.”

Kallanta sukai a tare, Binta tace “hukunci?”

Murmushi Azeema tai tace “duk mai laifi dole ne a hukuntashi, kada wanda yasa baki akan abinda ke faruwa, ku tashi ku koma bangarenku.”

Jiki a sanyaye suka tashi suka fito.

Binta suna fitowa ta kalli Zeena tace “meke faruwa Gimbiya? Ance murabus yanzu Umma tace hukunci.”

Zeena tai shiru kafin ta kalli Binta idanunta sun dan ciciko tace “kenan Umma da Abbana sunma Junaid laifi.”

Laifi?
Binta Shiru tai tana tunanin kalaman Junaid na rannan.

Zeena ta kalleta tace “wani irin laifi kike tunani?”

Binta ta girgiza kai tace “bansani ba.”

Shiru sukai a haka suka koma.



*********

Hajiya inna ta fito daga dakinta dakyar cikin farinciki ta zauna a waje tace “yau ko yanzu na muti Jakadiya hankalina a kwance zan tafi.”

Jakadiya cikin jin dadi tace “Barka Hajiya inna, wannan lamari yayi dadi.”

Junaid! Hajiya Inna ta fada cikin jin dadi......


******
Ayusher🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{48}

Fure ce ta shigo da sauri, ta kallai Zeena wacce ta zuba mata ido itama.

Fure tace “Gimbiya baki daga cikin gida sunzo tayaki murna.”

“Murna? Ai sa bari sai gobe ko?”

Dan tsaki tai sannan ta kalli Fure tace “ke kuma meye?” Dan yanda taga Fure ta zuba mata ido.

Fure ce ta kalleta cikin mamaki tace “Gimbiya yaushe kuka zama kawaye?”

Harara ta maka mata tace “haka kawayen suke? Tashi ki shigo dasu.”

Nan ta fita, matan kanen Abdulsalam ne da kuma yan uwa dake zaune anan.

********

Binta tana fitowa ta kali Hadimarta tace “Rali kira min Harira dan Allah.”

Raliya tai dariya tace “Ranki ya dade in kina san abu ki baku umarni kawai.”

Binta tai murmushi sannan ta shiga ciki itama hankalinta duk a dagule.

Harira ce ta shigo ta gaisheta sannan ta zauna, Binta ta sauko kasa kusa da ita tace “Harira kinji abinda ke faruwa?”

Harira tace “naji sai dai sam na kasa gane meke faruwa.”

Shiru Harira tai tana kallan Binta tace “Karki damu, Yarima yasan me yakeyi duk abinda kikaga ya aikata da dalilinsa.”

Binta tace “na sani sosai sai dai ina tsoron yana cutar da kansa ne.”

Fuskarta dauke da mamaki tace “kamar ya?”

Binta tai shiru dan batasan fadar abinda ke tsakaninta da mijinta duk kankantarsa kuwa.

Harira tai murmushi tace “ki kwantar da hankalinki insha Allah ba komai.”

Kai ta daga a hankali sannan Harira ta mata sallama ta fita.

Tanajin yanda ake magana da guda daga bangaren Zeena ita kuma bako mutum daya a bangarenta, mikewa tai ta shiga ciki tana tunanin hukuncin da Junaid ke dauka.

**********


Sai yamma kowa ya watse Junaid ya tunkari bangaren Sarki.

Abdulsalam najin Zagi na sanar da isowar Junaid yaji gabansa ya fadi, sam shi ko sunansa bayasan yaji an fada.

Junaid ne ya shigo ya zauna sannan ya kalleshi.

Abdulsalam wanda a yan kwanakin nan har ya rame ya canza ne ya kalleshi.

Junaid ya kalleshi sannan ya saki wani irin murmushi yace “kayi kokari sai dai saura abu daya.”

Kallansa Abdulsalam yai zuciyarsa na tafasa, tari ne ya dan kwace mai yana kallan Junaid.

Junaid yace “a randa akai taron nadi a ranar nakeso ka dau matarka Hajjo ka bar masarautarnan.”

Da sauri Abdulsalam yace “muje ina?”

Kafada Junaid ya daga yace “wannan kuma banaji ya dameni.”

Gaba daya Abdulsalam ya rasa me zaice, daurewa yai yasan in ya sake bari yanzu ma galaba Junaid zaici a kansa yace “Ragowar matana da kuma Azeema fa?”

Kallansa Junaid yai yace “baka taba jin kunyar zama da matar yayanka wacce kai ajalinsa ba?”

Abdulsalam yace “ni na kasheshi da hanuna?”

Kaikai ajalinsa.

Ita kuma Azeemar fa?

Tanada laifi babba dan haka yanda na ma hukunci itama haka zan mata.”

Abdulsalam rai a bace yace “na ajiye mulki yanda kakeso amma duk duniya ba mai rabani da Azeema, in har zan bar nan gidan to lalai sai dai na tafi da ita.”

Junaid ya kalleshi, Abdulsalam yace “in komai ya fito ai ba ni kadai zata kwabe wa ba.”

Junaid yai shiru yana nazari akansa kafin ya mai sallama ya fita.

********

Bangarensa ya nufa? Yana tafe ana mai buda yana kan doki, mutane na biye dashi, har ya isa bangarensa.

A bakin kofar shiga daga ciki mata ne a cike suna jiransa, Yana shigowa suka fara tayashi murna, yana amsawa.

Jakadiya tada wanda har da ita a ciki tace “Yarima au Sarki zance barka da sauka Takawa!”

Junaid ya daga kai sannan yai ciki.

Zeena wacce ta gama daukan kwalliyarta, tana jiran su fita taje gun Junaid.

Azi Junaid ya kalla yace “Sabisu na nan ne?”

Azi yace “dazu da kana fada ya fita wai dan kokari zai ga gari.”

Murmushi Junaid yai suka nufi ciki.

*****

Zubair wanda yake tafe Arim na rike dashi, da kyar suka karasa bangaren Hajjo saboda yanda gaba daya bakin ciki da takaici suka gama galabaitashi.

A kasa daram yaga Hajjo ta baje ta zauna a kasa hankalinta a tsananin tashe.

Kallanta yai bayan ya shigo ya zauna a gabanta, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mai yace “anya Hajjo ni dan Abba ne? Ace yana mahaifina amma gaba daya bai damu dani ba baya sona?”

Hajjo wacce tashin hankalinta ya ninka na Zubair ta kalleshi hankalinta a tashe tace “Zubair gaba daya yau ina tunanin kafin dare zan karasa lahira, banaji zan iya rayuwa a haka, ta yaya ma hakan zai faru?”

Ta fada kanta na wani irin sarawa, tana rike shi.

Zubair yace “Goggo ki tashi kije gun Abba dan Allah, wlh ni kam bazan taba yadda ba.”

Ranta a bace ta mike ta shiga dakinta ta kwanta.

Zubair cikin takaici ya mike ya nufi bangarensa.

********

Kallan Harira yai wacce yasa tazo yace “ki sa a hada mana abinci duka a nan, ki sanar dasu suzo nan.”

Harira tace “To Ranka ya dade.”


Bayan sallar isha’i kuwa Zeena da Binta suka nufi bangaren Junaid, yauma Binta ta yi kwalliya sosai, dukansu sai kamshi sukeyi.

Junaid ya sallami kowa a bangarensa dan yanzu saboda komai ya kusa kammala Sabisu ya koma bangarensu Azi.

Binta ce ta fara isowa, Junaid na ganinta ya saki wani murmushin jin dadi, tun dazu yake san ganin fuskar nan.”

Binta ta kalleshi, hannayensa ya bude alamar tazo, murmushi tai a hankali sannan ta zo ta zauna kusa dashi bata rungumenshin ba, kallanta yai ya dan turo baki kadan tare da kauda kansa gefe.

Jiyai ta sumbaceshi a kuncinsa, juyowa yai ya kalleta yace “wannan cin hanci ne?”

Murmushi tai ta dan matso saitin kunnensa tace “in na rungumeka uwar gida ta shigo ince me?”

Hannu yasa kamar mai nazari sannan yace “itama in tazo sai ta rungumeni.”

Wata harara ta galla mai tace “da cewa nai bazata rungume kan ba?”

Yace “ba haka kila ce ba?”

Haushi ya kamata tace “Allah zan rama.”

Ta fada tare da hade rai.

Sanar da isowar Zeena ne yasa ya kalli kofa, shigowa tai cikin shiga ta isa da matsayi.

Tayi kyau sosai, gefen damanshi ta zauna sannan ta gaisheshi.

Amsawa yai fuskarsa a sake.

Shiru suka danyi kafin ya kalli Zeena wacce gaba daya hankalinta da tunaninta rabi makan tasan abinda ke faruwa.

Hannunta ya kamo ya rike, da sauri ta kalleshi cikin sanyin murya yace “Zeena!”

Jikinta ne gaba daya yai sanyi sai idanu data zuba mai, Junaid yace “Ga Binta nan, inaso ki kula da ita, kece uwar gida sannan matsayinki a masarautarnan mai karfi ne, yanzu komai na rayuwa zai canza, bakoda yaushe zan samu damar kula daku ba dan haka ina rokonki da ki ajiye duk wani halaye naki da kikasan basu da kyau, ke yanzu uwa ce ga mutane dayawa dolene ki zama abin koyi ga mutane, bazan yadda da sakarci da cin zarafi ba kamar yadda kika saba a baya.”

Hawaye ne suka zubo mata ta daga kai alamar to.

Junaid ya saketa sannan ya kalli Binta wacce gaba daya jikinta yai sanyi, yace “Binta!” Kallansa tai ya rike hannunta yace “kece karama, banasan wani abu daya danganci rashin kunya ko wani batanci daga gareki, duk da nasan halayenki sai dai inaso ki kiyayi kanki daga biyewa mutanen da zasu kawo miki gulma da kuma hadaku da mutane.”

A hankali Binta ta daga kai alamar fahimta.

Murmushi Junaid yai sannan yace “muci abinci?”

Zeena ce ta kalleshi tace “Abba yama laifi ko?”

Yanda tai tambayar ne yasa ya kalleta, saboda tambaya ce da aka yishi cikin shakkar amsar da zataji.”

Yanda take kallansa yasa yasan a tsorace take yace “karkisa irin wadan nan abin a ranki, Abdulsalam mahaifinki ne ki daukeshi a fuskar da kika sanshi, nima zan daukeshi a fuskar dana sanshi.”

Kallanta yai sannan ya kalli Binta yace “Bismillah!”

***
Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{49}

Kasancewar ranan kwanan Zeena ne bayan sun gama cin abinci Binta ta musu sallama ta nufi sashenta.

Zeena tasa su Fure suka kwashe kwanuka, kallan Junaid tai wanda yasashi kallanta yace “me kike san cewa?”

Tambaya nake sanyi kuma bansan ta yanda zanyi ba? Kasan haka na taso magana ina fadarta ne daga raina, sai dai yanzu nasan dole ne na dinga sanin abinda zan fada kafin ya fito daga bakina.”

Cikin jin dadin kalamanta yace “menene?”

Idanunsa ta kalla wanda ke mata kwarjini ga so da take masa har cikin jikinta tace “ Hajjo......” ta kasa kuma karasawa sai kasa da idanunta datai, jitai kwalla tana neman zubo mata, haka kawai jikinta ke bata laifin Abba mai karfi ne tunda har ya iya ajiye mulkinsa saboda shi.

Idanunta a runtse tana kokarin maida kwallarta ne taji hannunsa akan fuskarta gaba daya jikinta ne ya amsa, a hankali ya dagota ta kalleshi, da kyar ta kakaro murmushi ta mai wanda suka kara bayyana kwallarta dake neman zubowa, yanda ya zuba mata ido ne yasa kwallar suka gangaro a kan hannunsa.

Idanunsa ya lumshe sannan ya sake kallanta, murmushi ta sake yi na dauriya tace “Yaya na sani ni mai laifi ce, ma taso ba ruwana da halin da wani zai shiga a dalilina, wannan banzan halin nawa ya ja mutane dayawa sun shiga wani hali ciki hadda kai, banda bakin da zan nemi ka saukaka ma mahaifiyata da mahaifina.......”

Wasu kwalla ne suka sake gangarowa akan hannunsa, wannan lokacin shine karo na farko dayaji Zeena har ransa, ya aureta ne saboda burinsa ma auran Binta, san Binta a jininsa yake tun baisan kanta ba take da babban matsayi mai karfi a ransa, sai dai a wannan lokacin ya fahimci Zeena ta samu guri a ransa, dan tabbas tausayinta yakeji sosai, ya sani yanzu shi kadai ne da ita, dole ko dan haka ya boye abinda mahaifinta ya aikata in ba haka ba mutane ma kinta itama zasuyi.

Hannu ta dago tana neman share hawayenta, hannunta ya rike da daya hannunsa, jitai zuciyarta na kara raunana, kallansa tai tana san sake magana kuka ya kwace mata.

Jawota jikinsa yai ya rungumeta, sai datai kuka sosai sannan ta daina, ba tare da yace mata komai ba, sai data gama sannan yace mata “Karki damu komai zaizo da sauki insha Allah, sannan in har kika canza halayenki komai naki zai canza, kada ki manta na fadamiki kece ido na nacikin gida, dole ne ki dinga sanin abinda zaki dinga yi daga wannan lokacin.”

Kai ta daga tana kwance a jikinsa tace “insha Allah bazan taba baka kunya ba.”

Murmushi yai, dagowa tai a hankali ta kalleshi sannan itama tai murmushi tace “nagode da ka bani dama.”

Mikewa yai sannan ya mika mata hannunsa, wani irin dadi ne ya kamata ta mika masa nata hannun cikin wani irin jin dadi da ita kadai tasan yanda takeji.

Hannunta ya kama suka shiga daki, a bakin gadan ta zauna cikin kunya, tana cewa “yau na fara shigowa dakinka.”

A hankalinya taka zuwa inda take ya zauna a gefenta, hannunsa dataji ta ratsin cikinta ne yasa ta dan rike numfashinta tare da saukeshi a hankali.

Kansa ya sako ta kafadarta yace “garin ya ya?”

Gaba daya ta kasa magana saboda wani irin yanayi data tsinci kanta a ciki, dan juyowa tai ta kalleshi, hannu yasa yai baya da ita a hankali ta kwanta akan gadon, idanunta na lumshe sai gabanta dake wani irin faduwa.

Bakinsa ya sa a cikin nata................

**********


Washegari!

Cikin tsananin kunya ta tashi, bakowa a dakin hakan yasa ta dinga tuno abinda ya faru jiya tana dariya tare da rufe fuskarta, da alama

Please Login or Register in order to submit comment