Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai tace "mene?"

Yace "inkin gama ki je ki kwanta da alama bacci kikeji, sannan wlh zan miki sharadi karki kuskura ko da wasa naji maganar nan a gun mutane, kinsan abinda zanyi da wanda bazan aikata ba."

Gaba daya sakar baki tai tana kallansa, wayaga a dakeka a hanaka kuka, shikam mikewa yai daga gun ya bar mata dakin ya wuce ciki.

Ta fi minti ashirin a zaune agun, tama rasa me zatayi, tazo da zarginta gashi ya tabbata dan tana zargin yana san Azeema ne amma bata tabbatar ba sai a wannan lokacin, lalai akwai tashin hankali, dan bazata taba yarda tai mulki da sannan yanzu tayi ba.

*********

Shikam Abdulsalam suna fita daga takaba ya sanar zai auri Azeema da Salma, wacce itama matar sarki Zubair ce.

Azeema kam damuwar rashin danta ma ta isheta ko bi takan abinda ake batai ba, haka aka daura musu aure aka nemi in tanaso a canza mata fadar ta ko a gyara mata, tace a barta haka.


***********

Junaid kam yasha kuka har ya gaji sai dai a hankali Azi ya dinga daukanshi yana kaishi cikin gari yana kallan yanda mutane ke hada hadar su har shima ya fara sakin jiki, abinka dama da yaro.


A hankali garin ya fara mai dadi, kamar yadda suka saba yau ma sun fita kallan gari su hudu yana ta kallan mutane yana dariya, suna kokarin wucewa aka cillo kaya, da sauri suka kare Junaid, dan sun dauka wani abin cutarwa ne, sai dai kaya ne ya fado, Junaid yadan turesu, ya matso inda kayan suka zubo, wata mata aka hankado waje, saura kadan ta begesu ta fadi kasa, wata yarinya ce ta fito tana kuka ta taho gun matar da alama mahaifiyarta ce, mutumin ya kalleta yace " nace banayi ana aure dolene? Ki tafi gidanku, au ashe fa baki san ma gidan naku bako? Ai dama ance tsintaciyar mage bata mage, munafuka kawai, na sakeki saki uku."

Yana kaiwa nan ya koma ciki tare da rufo kofar da karfi.

Kuka kawai takeyi yarinyar ma tana ta kuka, Junaid tausayinsu ya kamashi, yana neman karasawa gunsh Azi yai saurin rikeshi alamar karyaje.

Junaid ya zare hannunsa yaje kusa dasu kallan yarinyar da bata wuce shekara uku ba tana ta kuka yai.

Kallan matar yai itama yace "Hajiya inaje gidanku?"

Kallansa tai tana kuka tare da girgiza kai alamar bata sani ba.

Kusa da Azi y dawo yace "Azi mu tafi dasu kaga basuda inda zasu zauna."

Da sauri Azi yace "A'a yarima taya zamu dauki mutanen da bamusan su ba? Bamusan halinsu ba? Kana kallo kuma korosu akai."

Junaid yace "kalli fa yarinyar nan kuka take."

Ya fada yana neman yin kuka shima dan yanda take kuka yasa ya tuno da Ummansa.

Da sauri Azi yace "to Yarima amma da sharadin in sukai wani laifin zan korasu."

Yace eh naji.

Da sauri Junaid ya matso ya kalli yarinyar yace "kinasan shan mazarkwaila?"

Kallansa tai sannan ta daga kai, ya kalli maman yace muje gidanmu ku zauna.

Maman ta kalli su Azi, tana tunanin wannan kuma wanene? Su waye?

Ganin ba inda zata zauna yasa ta mike sukabi bayansu, Junaid ya rike hanun yarinyar suna tafiya, har suka isa gidan, suna shiga ya jata ya bata mazarkwaila, tana amsa yace "ya sunanki?"

Tace "Ke."

Kallan mamaki ya mata yace "ke kuma? Sunane?"

Kai ta daga alamar eh, fitowa yai waje inda Azi yake cema Hari ta samar mata makwanci sannan in har zata zauna anan sai ta taimaka da aikin gida, Junaid ya fito ya kalli Mamar yace "ya sunanta? Tace wai ke sunan ta."

Mamar tai kasa dakai cikin kunya, Azi ya kalleshi yace "ai bazata fada ba basa fadan sunan yan fari."

Junaid yace "to ya kenan? Taya za'asan sunanta?"

Azi yace "sai dai a tambayi babanta."

Mamar tai saurin cewa "a'a dan Allah karka tambayeshi zai san inda muke, duk kuma sanda ransa ya baci zai biyomu har nan."

Junaid yace "shikenan sai in bata aran nawa sunan, itama adinga ce mata Junaid."

Dariya suka kwashe dashi duka, Junaid yace "to an rasa sunanta, Azi ya ce to zan dinga kira miki sunayi in anzo kanshi kindaga kai."

Haka suka dinga Junaid nata dariya har sukazo kan Binta, nan ta daga kai.

Junaid ya juyo da sauri yace "Binta."

Nan suka shiga ciki yana gaba tana binshi a baya, Su Hari suka bisu da kallo kafin suyi murmushin jin dadi, ganin ya sake sosai.


*Ayusher Muhd*



*ZAFIN RANA*

Haske Writers Ameen

Pge 4

Bayan shekara goma sha biyu.

Wata irin shakuwa ce mai tsananin karfi tsakanin Junaid da Fatima wato Binta, tare suke komai nasu, mahaifiyar Binta ta rasu shekara hudu da suka wuce a lokacin tana shekara goma sha daya, Binta tayi kuka har ta gaji, a lokacin ta kara sanin mahimmancin Junaid, shikam dama Binta ita ta maye gurbin Umma, kanwarsa, Abbansa da kuma aboki, sun taso komai nasu daya, dan hatta abinci ga nata kwanon ga nashi sukeci, daki kuwa dama a gefen dakinsa take kwana, shima sai sun ci hirarsu sun gaji, lokaci suna yara ma sai dai tai bacci anan Hari ta dauketa, a da Junaid yana kuka sosai na rashin su Umma amma zuwan Binta yasa duk ya daina.

Tun bayan daya kawosu ya umarci kowa na gida karya kara ce masa Yarima a kirashi da sunansa.

Duk da basa so haka nan sukai dole saboda umarni ne wanda kuma sun san dole su bi.

Kamar yanda suka saba yauma sunje can bayan gari suna zaune suna hirarsu.
Yau yana saman bishiya ita kuma tana zaune a kasa tana bare gyada.

Kallanta yai yace "Binta ni sai yaushe zaki ban gyadar ne?"

Kallansa tai tace "ka manta yau baka da ita?"

Da sauri ya mike ya zauna yace "ban gane ba?"

Tace "to wayace ka hau sama ka barni a kasa?"

Yace "wayace mutum har yanzu ya kasa koyon hawa bishiya?"

Baki ta dan turo tace "ba wani yaushe ma ka koyamin? Kullum sai dai kai ka hau ka kyaleni a kasa."

Dariya yai yace "to ke kina mace wai me ke hadaki da hawa bishiya?"

Fuska ta hade tace "kusan duk matan garin nan nasan sun iya hawa sai ni."

Matsa matsa zan sauko.

Bata matsa ba ta kawar da kanta gefe irin fishin nan, saukowa yai ya zauna gefenta ya debi gyadar ya fara ci bai ce mata komai ba, haushi ya kamata ta mike ta dau kwanan gyadar zata bar gun, hartai taku shida bataji yaje komai ba a zuciye ta juyo ta kalleshi, idanunsa na kanta yana cin gyadarsa, tana juyowa ya sakar mata murmushi.

Ta harareshi tace " bazaka ce na dawo ba?"

Kallanta yai sannan yace "to dawo"

Tace "bayan baka ce ba sai dana fada?"

Mirmushi yai sannan ya nuna mata gefe yace "zoki zauna in baki labari."

Baki tadan zumburo ta karaso gun ta zauna, kallanta yai yace "Kinsan me?"

Kallansa tai tare da girgiza kai alamar a'a.

Mikewa yai yana dariya ya wafce kwanon gyadar ya fara gudu.

Mikewa tai ta bishi tana cewa "Allah Ya Junaid ka bani."

Dariya yai tayi yana gudu har sai dayaga ta gaji sannan ya zube a kasa ya kwanta yana kallan sararin samaniya, kwanciya tai kusa dashi tana dariya, cikin haki.

Sun danyi shiru kafin can yace mata "Binta!"

Kallan sa tai cikin nutsuwa saboda yanda ya kira sunanta, yace "Mama? Kina tunaninta?"

Kallansa tai sannan tace "wani sa'in, sannan kasan a makaranta ance mu dingama iyaye addu'a."

Murmushi yai sannan yace " ni bana tuno fuskar Ummana yanzu."

Gaba daya jikinta ne yai sanyi, idanunta suka ciciko, tana neman yin kuka.

Jikinshi ya bashi duk da ba kallanta yake ba, yace "karki soma kukan nan."

Ta ce "Nasan kanasan yin kukan kaima."

Juyowa yai ya kalleta yace "yaushe na ce miki?"

"Nasan saboda kar na damune yasa kake nuna baka damuwa."

Murmushi yai ya mike zaune yace "ko kadan, na girma ne shiyasa kema ya kamata ki daina kuka da wuri kinga kin girma kema."

Itama mikewa tai ta zauna gyada ya mika mata tace "ka baremin."

Murmushi yai sannan ya fara barewa, kallansa tai tace "wai ina Azi yake zuwa a duk bayan kwana 40?"

Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai kuma taji yace " maybe gidan mu."

Cikin mamaki ta kalleshi tace "gidan ku?"

Yace "eh kin manta nace miki Umma nada rai?"

Mamaki ne ya kamata dan da inya fada tana dauka wasa yake mata dan ta kwantar da hankalinta.

Ganin yanda ta bude baki tana kallansa yasashi dariya, yace "menene?"

Cikin mamaki tace "to wai me kake anan? Ka koma gida mana."

Kallanta yai yace "bansan ina bane gidan namu, sannan abinda na sani kawai shine nasan Umma nada rai, shikadai kawai na sani."

Ajiyar zuciya tai cikin rashin jin dadi kafin tace "ko mubi Azi in zai koma?"

Kallanta yai yace "oh ko mu bishi? Amma sai dai a boye dan bazai yadda ya kaimu ba, yau saura kwana....."

Sukai irge a tare sukace bakwai ya je.

Junaid yace "karfa muje da nisa kisha wahala, sannan shi kinga da doki yake zuwa."

Shiru tai cikin rashin jin dadi, yace "to ko na bishi in naga gidan sai nazo mu koma tare?"

Da sauri tace "a'a salan kaki dawowa."

Ta fada tana rike rigarsa.

Dariya yai sannan yace "inki dawowa kamar ya? Ta ina zan barki inyi rayuwa ta daban?"

Itadai bata yadda da wannan shawarar ba hakan yasa ya hakura ma da zancen.


*********

Masarautar Biram

Zaune take akan kilisarta kuyangunta na gefenta, ita kuma tana zaune tana jin kidan da ake mata, murmushi ne ke bayyana a fuskarta najin dadi.

Bude kofar da akai ne yasata ta bude idanunta dake lumshe, kallanta tai har ta zauna.

Masu kida ne zasu ci gaba ta kallesu sannan ta musu alama da su fita.

Hajjo ta bude idanunta ta kalleta, sai da suka fita tace "Menene?"

Budurwar data shigo ta kalleta tace "Umma nikam bazan auri dan Sarki Gobir ba."

Hajjo ta kalleta sannan tace "to wa zaki aura? Wai mi meke damunki? Kowa sai kice bakyaso? Ko ce miki akai zabinki muke nema?"

Kallanta tai tace "ni haushi yake bani, bazan aureshi ba."

Hajjo ranta ya baci, tace "kina kallo babban burin mahaifinki yaga ya aurar dake, amma ke sam bansan menene matsalarki ba."

Shigowar Wani Saurayi ne ya sata kallansa.

Yarima Zubair ne ya shigo, babban dan Abdulsalam wanda ya haifa tun Sarki nada rai, ya samai sunan Zubair wato sunan Yaynsa.

Kallanta yai yace "ke kike biye mata? ku daura mata aure kawai ku kaita, sai muga me zatai."
Ya karasa tare da zama, Zeenat ta kalleshi tace "kash ya akai haka? Gashi kai ba kaine babana ba."

Kallanta yai a zuciye yace "mene?"
Kafada ta daga mai sannan tace "na manta."

Kallan Umma yai yace "Umma yarinyar nan wlh ta gama rainani, kuma ni ba sa'anta bane."

Haushi ya kama Hajjo tace "Ku rufemin baki ko? Ko kunyama bakwaji, gida cike da makiyanku amma ku dinga fada."

Shiru sukai basu sake cewa komai ba.

Hajjo ta kalli kuyangar ta tace "Takawa yana ina?"

Kuyangar tai waje da sauri, bata dade sosai na ta dawo, kallanta Hajjo tai tace yana ina?

Yana bangaren Gimbiya Azeema batada lafiya.

Hajjo tai tabe baki tace "aikin kenan."


*******
*Ayusher Muhd*




*ZAFIN RANA*

*Haske Writers Association* 💡

Pge 5

Bubuga kofa yake iya karfinsa amma ba alamar budewa da take shirin yi, iya karfinsa yake jijigata yana kiran Binta, daga ciki itama kuka take sosai tana kiransa, gaba daya duhu ne agun babu haske ko kadan.

Daga kasan dakin ya hango hayaki yana fitowa, da sauri ya zabura ya mike daga baccin da yakeyi.

Gabansa ne ke dukan uku uku, gashi gaba daya ya jike sharkaf da zufa, kansa ya dafa sannan ya fito daga cikin dakin nasa.

Tsakar gida ya nufa yana tafe yana tunanin abinda ya faru ynzu, ji yai ance "Yari......"
Juyowa yai ya kalleshi saboda garin tar yake da hasken farin wata.

Azi ya matso ya rusuna yace "Junaid lafiya? me kake a daren nan?"

Junaid wanda idanunsa sukai ja jawur ya kalleshi sannan ya cigaba da tafiya, da sauri Azi ya bi bayansa har suka fita daga gidan.
Kara kallansa yai yace "Ina zaka?"

Junaid bai tsaya ba hakan yasa Azi kara binsa, sai da har suka fara shiga cikin gari, duk gidajen mutane a rirufe kowa ya kwanta, ga gari yai sanyi saboda lokacin sanyi ne.

Zama yai akan wani dandali dake gefen wani gida.

Azi ya karasa kusa dashi ya tsaya.
Junaid ya kalleshi yace "zauna."
Azi ya zauna ba tare da yai magana ba, Junaid bai kalleshi ba yace "Saura kwana nawa kaje?"

Da sauri Azi ya kalleshi, Junaid yai murmushi yace "akoda yaushe ina san tambayarka abu sai dai zuciyata na tsoron amsar dazan samu daga gareka."

Azi ya kalleshi cikin tausayawa.
Junaid yai dan shiru kafin yace "ada ina tunanin laifin me na aikata haka da za'a kawoni nan tun ina karami, ba wanda ya taba zuwa yaga a wani hali nake ciki? A yanzu kuwa komai ya fita a kaina gani nake rashin so ne yasa ba wanda ya damu dani."

Azi da sauri yace "ba haka bane Yarima."

Junaid yace "Yarima?" Ya saki wata dariya na takaici.

Azi ya kalleshi yace "Gimbiya batasan an kawo ka nan ba."

Kallansa yai, da sauri Azi ya rufe bakinsa, Junaid cikin mamaki yace "wanene yasa a kawo ni nan kenan? In har Umma bata sani ba?"

Azi ya kalleshi a tsorace, Junaid yai murmushin takaici yace " kasan ba dadan kai ko Hari wani sa'in kuna cewa Yarima ba da tuni na manta ko ni wanene? Fadan sunan da kuke wani sa'in shi kesa nake rike wanene ni, sai dai hakan baisa na dau matsayin da daraja ba, nasan a yanzu ba wanda ma yake tunawa da anyi wani yaro mai suna Junaid."

Shiru yai tare da kallan Wata, yace "in zakaje wannan karan zan bika."

Zanje naga mutanen da suka kulleni wace rayuwa sukeyi."
Gaban Azi ya fadi ya kalleshi yace "Junaid......."

Junaid ya kalleshi yaga duk ya tsorata, dariya yadanyi yace " binka zanyi ba a matsayin Junaid Yarima ba a matsayin yaran daka taho dashi daga can."

Azi haryanzu kallanshi yake yana tsoro, Junaid ya dafa kafadar sa yace "ba abinda zai faru, dan ni dakai kawai zamu ko Binta bazan dauka ba, na tabbatar in kaga na bata anan ai kasan ba abinda zan aikata."

Azi ya jinjina kai yace "to, amma....."
Junaid yace "mu fita da daddare."

Azi yai murmushi dan yana mamakin Junaid yanda wani sa'in kan canki abinda yake neman fada.

Junaid yai gaba, Azi ya mike yabi bayanshi, suna zuwa gida mai makon ya shiga ciki ya samu gu ya zauna, yana tunanin mafarkin dayai mara dadi.


***********

Hannu yasa ya rikota yana neman jawota jikinsa ta dan zare jikinta daga nashi, kallanta yai cikin rashin jin dadi yace "Azeema sai yaushe ne zaki saki jiki dani? Ni fa mijinki ne, shekara nawa kenan?"

Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, mikewa zaune yai ya kalleta yace "ko baki amince dani ba a kalla ki dawo yanda muke dake da ke kanki kinsan dake kadai nake iya shawara."

Kallansa tai sannan tace "Abdulsalam, kace har yanzu ba'a samo Junaid ba?"

Kallanta yai yace "eh."

Ido ta kuramai kafin tace "Taya za'ace kamar kai a garin nan neman yaro ya gagareka? Shekara nawa kenan?"

"Shine dalilin da yasa kika kasa sakar jiki dani?"

Kallansa tai, jawota yai jikinsa ya rungumeta yace "kina tunanin zan cutar miki da danki? Ni?"

Tace "a'a amma baka nemanshi."

Dagota yai yace "ki sa a ranki Junaid na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, bakya tunanin in kikai wannan fatan zakiga hakan ya tabbata?"

Shiru tai tana kallanshi, yace " ba neman mu'alama ta aure nake dake dole ba amma ki saki jiki dani dan Allah, kinfi kowa sanin bazan taba cutar dake ba."

Murmushi ta masa sannan tace "kayi hakuri."

Kara rungumeta yai a ransa yana cewa kiyi hakuri Azeema.

Su biyu ne a cikin dakin Hajjo ta kalleta tace "kinsa an duba?"

Kallanta tai tace "Hajjo danaje gun malam cewa yai akwai mutum daya da zai hana Zubair hawa mulki indai kin halaka shi to lalai ba abinda zai hanashi hawa."

Tsaki tai tace "dayan fa?"
Yace "ki sa masa a abinci indai yaci to lalai zai ji Azeema ta fita a kansa."

Ta karasa tana mika mata dan abu, Hajjo ta sake yin tsaki tace "Ni wai ke Ramlatu haryanzu hankali bai gama shigarki bane?"

Da sauri Ramlatu ta kalli Hajjo, Hajjo tace "Takawa mijin wanene? Ba mijinki bane?"
Tace "miji nane."

Hajjo ta kalleta tace "sai na fada miki abinda zakiyi ki jawo mijinki gunki? Wannan aikin ki ne ki rabashi da Azeema dan ya soki bawai aiki na bane."

Ramlatu ta daga kai da sauri alamar ta fahimta sannan tace "Nagode Hajjo."

Hajjo tai murmushi tare da rike mata hannu tace "duk yanda za'ai ki kwace mijinki daga gun Azeema, tasa kinyi boranci lokacin Marigayi karki bari yanzu ma ki kare a boranci."

Ramlatu ta ce "nagode Hajjo ke kadai ke sona."

Hajjo tace " Zancen Zubair da wani zancen wani zai hanashi hawa mulki da alama yayi kuskure, dan kannen Zubair maza 'ya'ya nane kuma duk cikinsu kowa yasan Zubair ne mai mulki, kar ki damu ke dai kiyi aikinki."

Ramlatu ta daga kai alamar gamsuwa, sannan tai godiya ta fito.

Hajjo ta bita da kallo, matsalar ta daya Zeenatu, indai ta aurar da ita ta gama, Ramlatu zata kula da Azeema.

*********

Cikin dare yaji mostin bude kofa hakan yasashi bude idanunsa, Azi ya gani a jikin kofarsa, mikewa yai daga kan gado, kayan jikinsa ya canza zuwa kalar tausayawa, sannan ya fito ya maida kofar dakin ya rufe, dakin Binta ya kalla jiki a sanyaye, jiya dama sai sakalci takemai, wai batada lafiya.

Ya dade a jikin kofar kafin a hankali yasa hannu ya murda, kallanta yai tanata bacinta hankalinta a kwance, ya zatai in ta tashi taga baya nan? Duk da gobe zai dawo amma ji yake gaba daya ba dadi, yasan gobe sai kuka in bata ganshi ba.

Ko dai ya hakura da zuwa? Da sauri ya maida kofar ya rufe ya kalli Azi dake kallansa, Junaid yai murmushin yake yace muyi sauri muje mu dawo kafin hankali Binta ya tashi.

Azi ya kalleshi tare da daga kai alamar to.

Sun fito suka fara tafiya dan zuwa kauye na gaba inda ake hawa motar ice dan zuwa cikin garin Biram.


Sun isa suka tadda an cika mota hakan yasasu saurin shiga aka dau hanya.


**********
Ayusher pg 5
***********

*ZAFIN RANA*



HASKE WRITERS ASSOCIATION


*Na Ayusher Muhd*


Shafi na shida



Sun isa garin Biram tunda suka shigo Junaid yake bin ko ina da kallo gaba daya yanayin fuskarsa ya canza.

Azi ne ya kalleshi yace “Yar......”
Kallan da Junaid yamai ne yasashi dan murmusawa yace “Wali.”

Tare suka sa dariya dan Junaid yace har su koma da sunan Wali zai dinga kiransa, Junaid bayan sun gama dariyar ya kalleshi yace “Allah ya sa bakin nan karya min tabargaza.”

Azi yai dariya yace “ ni shigar taka ma tafi ban dariya.”

Junaid ya kalli kanshi wasu irin kaya ya saka, wando da riga daban, sannan ya kima wani nadi akansa.

Murmushi yai yace “karka manta da wuri zamu koma dan nasan Binta in taga ban dawo ba kuka zataitayi.”

Azi yace “to, dama kudin kayan abinci zan amso ba dadewa zanyi ba.”

Junaid ya dan tsaya sannan ya kalleshi yace “wake baka?”

Shiru yai yana kallansa, Junaid ya cigaba da tafiya kawai yana cewa “barshi ma dan banasan ji.”

Sun isa masarautar Biram, Azi na isa suka fara gaisawa da dakarun gidan sarki, Junaid na binshi a baya, sun dau hanya zuwa can cikin masarautar, Junaid ya kalleshi yace “mu hadu a tasahar mota kafin rana ta fadi.”

Azi yace to, har Junaid ya fara tafiya yace “Wali.”

Junaid ya kalleshi, Azi ya matso yace “kayi hakuri da duk abinda zaka gani.”
Junaid ya kalleshi ba tare da ya amsa ba kawai yai gaba.

Azi yai shiru yana binsa da kallo, yana tausayinsa sosai, duk da su a tunaninsu gata suka mai amma ta ina zai fahimci hakan? Bayan an rabashi da kowa nashi.


Junaid yana tafe yana kallan cikin masarautar, sam baya tuna abinda ya faru a ciki, duk kuwa yanda yaso ya tuna din.

*********

Yau kamar yanda suka saba akwai rana daya da suke warewa duk matan Sarki na zuwa gun Uwargida sarauniya, a zauna a na cin abinci ana dan hira.

Azeema ce ta kalli Bari suna kan hanyarsu ta zuwa tace “ni wai waye ya kawo wannan bidi’ar??

Bari tai dariya tace “kece ai Gimbiya.”

Azeema ta kalleta tace na sani ai, Bari tai murmushi suka karasa, dukansu kowa ya hallara da alama itace karshen zuwa.

Gaba daya ta kula ma gulmar ta akeyi saboda tana shiga kowa yai shiru.
Wucewa tai ta zauna a gun da aka tanada duminta.

Kallan Hajjo tai tace “Hajjo barka da war haka.”

Hajjo ta kalleta fuska a sake tace “Azeema barka dai.”

Nan kowa ya gaisheta itama, ta amsa fuska a hade dan batasan wargi.

Sun danyi shiru kafin Ramlatu tace “Hajjo ya maganar Gimbiya Azeema ne? An daidaita da Yariman Gobir din?”

Hajjo ta kalleta sannan ta kalli Azeema tace “ai Zubair ya mata magana, kinsan duk inda ‘ya’ya mata suke suna shakkar maganar ‘ya’ya maza, tunda ya mata magana da alama ta shiga hankalinta.”

Azeema ta fahimci magana take neman fada mata, kallanta tai tace “sosai amma yawanci zakiga indai kinsamu yarinya mai jin magana sai kiga kafin ma akai ga haka tafahimta.”

Ran Hajjo ya kai matuka gun baci ta kalleta tace “Hakane sai dai akwai lokacin da maza kan taka rawar gani sosai akan rayuwar kannensu, oh bama wannan ba a rayuwar mu ta bahaushi duk yawan jikokinka indai daga gun ‘ya’ya mata suke to ba naka bane.”

Azeema ta jinjina kai tace “hakane, sai dai akwai yara dawa Hajjo da baki sani ba wanda daka haifesu gwarama babu.”


Fuskar Hajjo ta canza sosai a wannan lokacin dan ranta yakai matuka gun baci, dan har fuskarta sai data nuna.

Dariya ragowar mata suka sa saboda sun fahimci hakan, Ramlatu tace “ hakane sai dai kowa nasan ganin nasa.”

Azeema ta dan yi dariya kadan tace “sosai, ai gani naka akwai dadi.”

Gaba daya hirar ta rage armashi saboda Hajjo tunda ranta ya baci bakomai ma take sa baki.

******

Yana tafe yana waige waige dan ya rasa ta ina zaibi.

Ita kuma wacce ranta ya baci saboda haushin zancen Yariman Gobir din nan da ake mata ta taho cikin bacin rai, tana shawo kwana shi kuma yana juye juye.

Sam bai kula dasu ba yasha gabansu yana waige waige.

Yauce rana ta farko da wani bawa zai tsaya a gabanta.

Cikin tsananin zafin rai ta kalli Bawan dake kula da ita.

Kusa da Junaid ya isa yace “kai dan gidan bafaden, dan gidan asararru, dan gidan wanda basu san kansu ba.”

Cikin mamaki Junaid ya kalleshi dan baisan me ya aikata ba haka ake buga mai zagi haka.

Bafaden nan ya hankade Junaid daga kan hanya wanda hakan yasa shi ya fadi kasa, kallansa yai sannan ya kalli mutanen dake bayan mutumin wanda sai yanzu ma ya kula da zamansu.

Mikewa Junaid yai cikin mamaki yace “Bawan Allah me nai daka hankadeni?”

Bafaden ya juya ya kalli Gimbiya wacce ta kara kuluwa, kallan Bafaden tai tace “biyoni dashi.”

Tana fadan haka ya cafko Junaid wanda ya kara kallansa yana neman kwace kansa yace “kai malam, meye hakan?”

Jansa yai suka cigaba da tafiya, ganin duk maganar da yakeyi Bafaden bashi da niyyar sakarsa ne yasashi yao shiru.


Zeenatu kam tana tafe tana masifa a ranta dan tabbas taji haushin wannan rainin wayan, wato yanzu ko wani ma kazami rainata zai fara yi.

Bangaren Hajjo tai dan dama can zata.

Tana shiga a harabar tsakar gurun ta kalli

Please Login or Register in order to submit comment