Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai tace “Junaid.....”
Sai kuma tai shiru tace “ka huta inka tashi sai a kirata.”

Kai ya jinjina sannan yace “ina bandaki?”

Nuna mai tai da sauri sannan tace “nasa a kawo ma kaya.”

Kaya? Ya tambaya cikin mamaki, tace “eh na tura gun masu dinkin mu na masarauta, nasan baza’a rasa wanda suka ma Zubair ba.”

Baice komai ba dan baisan ma me zaice ba, juyawa tai ta fita, zama yai a bakin gado yai shiru yana tunanin wannan lamari, wai meya faru ne daga sanda aka kulleshi?

Azeema ce ta turo kofa dauke da kaya, mika mai tana cewa “me kake tunani?”

Shiru yai yana kallanta, murmushi ta saki tace “inada abubuwa dayawa danake san tambayarka sai dai ganin yanayin da kake ciki yasa nake jurewa.”

Yanzu kam shima murmushin yai, tace “Junaid!”

Kallanta yai tace “Nagode daka jure abinda ya faru,nagode wa Allah daya barmin kai da rai.”

Tausayinta ne ya kamashi, juyawa tai da sauri tabar dakin.

Junaid ya dafa kansa, lalai bai kyauta ba da yake jin zafin mahaifiyarsa bayan abar tausayi ce.

Mikewa yai jikinshi duk ba karfi, wanka yai tare da alwala sannan ya fito, kayan ya saka sannan ya tada sallah.

Bari ce ta kwankwasa jin shiru yasa ta koma, kara dawowa tai ta kwankwasa Junaid ya bata izinin shigowa.

Abinci ta shiga jerawa a kan karamin carpet din dake dakin, haka tai ta shigowa dashi tana jerawa, data ajiye na karshen ne ta zube a kasa tace “yarina barka da dawowa.”

Kallanta yai yace “ina Binta?”

Tana dakinmu, taci abinci ne?

Cikin mamaki ta kalleshi, tace an kai mata.

Ki duba nasan bata fara ci ba kice mata ta dawo nan.

Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, shima kallanta yai yace “da wani abin ne?”

Da sauri tace “a’a”

Mikewa tai ta fito kilisar Gimbiya Azeema wacce ke bada sako akan a sanar wa Safiyah halin da ake ciki.

Gaba daya Azeema ta kasa zama sai ake take gun yan uwanta na kusa dana nesa.

Bari ce ta matso kusa da ita ta sanar da ita abinda Yarima yace “ shiru tai cikin rashin jin dadin zancen tace “ kice taje”
Da sauri Barira ta kalleta tace “Gimbiya.”

Azeema ta juyo ta kalleta tace “ki bar Junaid yai duk abinda yake so, ni zan san abin yi.”

Barira ta jinjina kai sannan tai dakinsu.


Kamar kuwa ya sani tana zaune sai jujuya abincin take taki ci, Barira ta sanar da ita sakon Yarima da sauri ta mike ta dau kwanan tai dakin.

Barira ta bita da kallo, cikin takaici.

**********

Hajjo kam sai matse hannayenta takeyi daga zaune, tabbas gaggarumin matsala na neman afkowa a tare da ita.

Zeenatu wacce ke zaune itama tayi shiru tana tunanin abinda ke faruwa.

Zubair ne ya daure yace “wai da gaske yaran nan ne Junaid?”

Hajjo tace “da gaske wlh, yanzu ya zamuyi? Dan wlh akwai gagarumin matsala.”

Zeenatu ta kalla wacce tai shiru kafin wani murmushi ya bayyana a fuskarta, Hajjo cikin mamaki tace “ke kuma fa?”

Zeenatu ta kalli Hajjo da sauri tace “ya akai bamu gane ba Hajjo? Yaran nan wlh sam baiyi kama da bawa ba, ko daga yanayin maganarsa zakasan jininmu ne, ya akai idanunmu ya rufe?”

Ran Hajjo ya baci tace “to ke yanzu ana zancen abinda zai biyo nan gaba wato ke abinda ya faru a baya kike maimaitawa?”

Zeenatu ta sake murmusawa tace “abin ne abin birg.......”

Uban hararar da Hajjo ta maka mata ne yasa ta kalli Zubair tace “yaya wai meye na damuwa? Milkin nan fa kowa yasan naka ne meye na wani tada hankali?”

Zubair ya kalleta yace “kinba Sulaiman din hakuri?”

Tace “kai yaya ana cikin wannan yanayi wake zancen wani Sulaiman?”

Hajjo tai dan tsaki tace “aiki Fure ta kiramin Ramlatu.”

Nan Zeenatu ta mike, Hajjo ta kalli Zubair tace “Zubairu karka kuskura adan tsakankanin nan kai laifi, kabi kowa a sannu, kai luf kamar baka nan kafin na samo mafita, dan wallahi barin yaran nan daidai yake da ajiye matsayinka.”

Zubair ya kalleta yace “Hajjo kisan yanda za’ai.”

Tace “karka damu, in ta gama rama abinda aka ma danta sai musan abinda zamuyi.”

Yace “kina nufin sai ta rama?”

Hajjo tai wata dariya tace “bakasan Azeema bane, ita a tarihinta bata barin ta kwana ko a mutu ko ai rai amma sai ta fanshe.”

Zubair yai shiru yana tunani.

*****

Suna cin abinci yana tambayeta abubuwan da suka faru tana fadamai, ko mai ya bude sai ya turo gabanta yace “binta ga kaza kin taba ci kuwa?

Dariya tai tace “Ya Junaid nifa bamu shirya bama wlh, ka taho ka barni.”

Ahhhh ya rike ciki wai ciwo,
Hankalinta a tashe ta kalleshi tace “ Ya Junaid?”

Ganin yanda ta rikice yasa ya saki dariya yana cewa “yanzu mun shirya?”

Hade rai tai tace “Ya Junaid.”

Tai maganar cikin shagwaba.

Azeema dake jikin kofa rike da kofar ta kalli Wanzamin dake gefe kansa a kasa tace “ko zaka bari sai anjima?”

Yace to ya juya tare da mata sallama, shiru tai tana tunanin wannan yarinyar, itafa danta bazai zauna yana biyewa yarinyar nan cikin masarautar nan ba, wanda tasan yanzu idan kowa kansa zai koma.


*Ayusher*

Dan Allah ku daina min sharing din littafi, ina iya bakin kokarina na ganin an zauna lafiya da kowa, dan Allah wannan littafin na kudi ne ku daina yadamin shi.

Nagode



*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Uku.


Haka sukai ta hirar su kamar ba wata matsala a gabansu, wanda hakan ba karamin batama Azeema rai ba, zama tai a kilisarta tai shiru tare da zubawa kofar ido.

Barira ta sunkuyo tace “Gimbiya haka zamu barsu?”

Kallanta tai tace “kinsa a gyara bangaren Yarima?”

Tace “eh na tabbatar ma sun gama, badai tare zaki bar.........”

Wani banzan kallo data mata ne yasa ta yin gum da bakinta.

Azeema ta mike ta shiga dakin.

Suna dariya suna ganin ta sukai shiru, Junaid ya kalleta, Binta kam saurin mekewa tai tsaye ta ja baya.

Azeema ta kalleta tace “Gashi ganinki yasa Junaid ya ware, angode.”

Binta tai kasa dakai tana kallansa.

Murmushi ya sakar mata.

Azeema ta zauna a bakin gado tace “Junaid!”

Yanda ta kira sunan nashi ne ya sa shi kallanta bayan ya amsa, tace “an gyara maka ban garenka, zamuje yanzu ma kaika, dan gobe za’ai taron murnar dawowarka.

Ta danyi ajiyar zuciya sannan ga cigaba “Sai dai inaso kai da Binta ku rage nuna mu’amalar ku cikin jama’a.”
Kallan Binta tai sannan ta kalli Junaid, Binta!
Junaid ya kirata, nan bamu guri ya fada yana kallan Azeema.

Binta ta mike tai waje.

Azeema ta kalleshi tace “Junaid kai yarima garin nan ne, idan kowa akanka yake, me kake tunanin za’ace in aka ganka da mace budurwa?”

Junaid yace “menene damuwata akan abinda zasuce? Binta kanwa tace wacce na taso tare da ita a lokacin da banda kowa, ban fahimci dalilin da zaisa na ja baya da ita ba dan yanzu na zama wani abin.”

Azeema tai murmushi tace “ba haka nake nufi ba, in kana cikin mutane ne sannan Junaid ko ba dan kai ba ko dan ita ya kamata saboda inba haka ba mutane zasu takura mata.”

Shiru yai bai ce komai ba, tace “ka barta anan sai su dinga kwana da su Barira in yaso da safe sai ta dinga zuwa.”

Junaid ya kalleta da sauri tace badai tunani kake ku zauna tare ba?

Yace “me zai haka? Bayan haka muka taso?”

Tai shiru kafin tace “ Junaid kayi hakuri ka barta anan.”

Kamar zai sake magana sai kuma yaga kamar bai dace haduwarsa ta farko da mahaifiyarsa ba ya dinga bijire mata haka ba.
Shikenan.

Azeema tace “Nagode Junaid Nagode.”

“Ga amanar Binta nan.”

Tace “ni na taho maka da ita karka damu zan kula da ita, sannan Azi da Hari da ragowar bayin da mukace su taho sun iso su suka gyara ma bangarenka.”

Cikin jin dadi ya kalleta, tace “Junaid!”

Naam

“Kai jinin mai Martaba ne karka yadda wani ya kawo ma raini, sannan duk wanda ya nemi yima zancen banza.........”
Sai kuma tai shiru ganin kamar bayasan maganar duba da yanayin da fuskarsa tai.


Murmushi tai tace “Junaid yaushe zaka ban labarin rayuwar dakai.”

“Ba wani labari, mun daiyi rayuwar mu tundaga yarinta har kawo yanzu.”

Kai ta jinjina tace “Alhamdulila.”

Shiru suka danyi saboda rashin sabon dake tsakaninsu, kafin yace “meye dalilin sarki na kaini can?”

Kallansa tai da sauri saboda batai tunanin tambayar ba, tace “ bansani ba wlh, sai dai nasan yayi hakane dan hankalin ka ya kwanta.”

“Bawai ina inajin haushi bane, sai dai haryanzu ina ganin akwai dalili bayan waccan.”

Shiru Azeema tai jin kalamansa yasa itama ta fara tunanin tabbas dan kawai Junaid yai rayuwa hankali a kwance bazai zama dalilin da zaisa ya dauke danta bada saninta ba ya boyeshi, tabbas akwai wani abin kenan? To menene?


Junaid ne ya kalleta yace “karki damu nayi maganarne ba tare da nazari ba.”

Murmushi tai cikin jin dadi a kalla yana da dogon nazarin da akesan mai mulki ya kasance dashi.


Mikewa yai yace “Su Harin suna ina?”

Tace “bari nazo muje.”

Dakin huta, ta mikr tana cewa muje na fara nunama hanya.

Nan suka fito, Binta bata gun hakan yasa yace “Binta fa? Barira tace “ta shiga bandaki.”

Yace “bari na jira ta fito.”

Azeema ta kalleshi tace “muje Junaid in ta fito sai Barira ta kawota.”

Ya kalli Barira wacce tai saurin cewa zan fada mata inta fito.

Nan suka nufi waje, a hanya sai kallan Junaid ake ana gaisheshi, Suna kokarin yin kwanar dazata sadasu da bangaren Junaid ne sukaji ance “Barka da Yamma.”

Juyowa Azeema tai, ta hade fuska tsam tare da binta da kallo, Zeena ta karaso fuska a sake, Junaid kam ganin ba dashi ake ba bai ko juyo ba.

Zeena tace “Nazo bada hakuri naga zaku fita.”

Azeema tace “hakuri? Laifin me kikai?”

Tace “Tuba nake na yi abinda na bata miki rai.”

Azeema ta juya batace komai ba, dan bataji zata hakura tabbas sai ta fanshe.

Zeena ta bi bayanta tana kallan Junaid tace “Yarima kayi hakuri bansan kai wanene ba lokacin.”

Juyowa yai ya kalleta, tsayawa tai tare da kura mai ido, maida kansa yai hanya baice mata komai ba.

Shiru tai bata kara daga kafarta ba wanda hakan yasa du Azeema sukai gaba.

Fure ce tace “Gimbiya menene?”

Zeena ta kalleta da sauri sannan ta kalli gun da su Junaid suke, haushi ya kamata tace “uban me kike da har suka wuce mu?”

Fure tace “tuba nake Gimbiya.”

Takaici ya kamata tace “meye ma amfanin fitowar? Ko so kike na bisu kamar jela?”

Fure tace “tuba nake Gimbiya.”

Cikin takaici ta juya ta koma bangaren Hajjo.

Azeema kam wani irin dadi ne ya kamara dataga kallan da Junaid ya mata wanda ta san hakan ne ya tsorata ta tabbas jinin sarautar na nan na yawo a jikinsa.

Yana shiga ya hango Azi na gyra harabar waje.

Azi na ganshi ya matso cikin tsananin jin dadi, kasa yai da kansa yace “Yarima.”

Junaid ya kalleshi cikin jin dadi yace “Azi kunzo lafiya?”

Azi yai saurin zubewa a kasa yace “tuba nake yarima na barka cikin wani hali.”

Junaid yai murmushi yace “nina umarceka ka barni ai, ina su Hari?”

Suna ciki hala dan da suna nan.

Kai ya jinjina sannan suka shiga ciki, yanda aka gyara gun me gashi kato sosai ya birgeshi.

Azeema tace “Junaid nan asali da bangaren Mai Martaba ne, anan mahaifinka ya zauna, sai dai shekaru biyar da suka wuce aka kara fadada masarautar wanda aka sakema Takawa wani ginin shine ya tashi, dazu ya turo akan abude maka.”

Junaid ya kalleta yace “amma hakan ba matsala?

Tace “ba wani matsala tunda umarnin Sarki ne.”

Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa yana kara kallan gun, Azeema ta shiga nununamai yanda gun yake.
***
Zeena hartaje zata shiga bangaren Hajjo ta kalli Fure tace “Fure ni me zasuje yi bangaren Takawa na da?”

Fure tai shiru, Zeena tace “kin fadamin ko kuwa?

Fure tai kasa dakai tace “Sarki ya bar ma Junaid.”

Ido ta zaro tace “mene?”

Kallan Fure ta karayi tace “Hajjo ta sani?”

Fure ta girgiza kai alamar a’a.

Zeenatu tace mu koma bangarena baza’a huce a kaina ba.

*******

Da sauri Binta ta shigo, sannan ta kalli Kuyangar data jata wai akan an aiketa, Barira ta kalleta tace “kun dawo?”

Binta tace eh tana kallan bangaren Junaid.

Barira tace “kije ki huta shima ya tafi bangarensa saboda ya gaji wai yana san hutawa.”

Binta tai shiru cikin rashin jin dadin ya tafi ya barta ta shiga ciki.


*******

Azeema ta dade acan kafin ta fito ita da kuyanginta.

Junaid ya kalli Hari yace “Hari haryanzu Binta bata karaso ba?”

Tace “Yarima!”

Itakam Hari girma duk ya fara zuwa mata ta kuma san zamansa da Binta bazai yiwu yanda yake tunani na, sai dai batasan me xatace mai ba.

Junaid ya kalleta yace “Hari ki tura a dubo, dan tazo taga nan.”

Hari tace to Yarima ta fito.

Shiru tai tare da kallan Azi wanda shima kallanta yake, su sun san yanzu Junaid zai san me ake nufi da sarauta, ilolinta, matsaloli da kums kalubalen dazai fuskanta.....


*********




*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Hudu

Har bayan sallar isha’i Junaid baiga Binta tazo ba, ga abincin dare an jera mai amma baibi takansu ba, hankalinsa ne ya tashi, fitowa yai ya kalli Kuyangun dake tsaye bakin kofa ya kalli ta farkon yace “Ina Hari?”

Tace tana daki, yace “kinsan bangaren Umma?”

Tace “Gimbiya Azeema?”

Yace “eh, kije kice ma Binta tazo.”

Tace “to Yarima sannan ta juya.”

********

Binta zaune a gaban Azeema, Azeema cikin sakin fuska tace “Binta nasan kin damu da Junaid sannan kin shaku dashi ta yanda bama zato a lokacin da bashida kowa sai ke, sai dai ina neman alfarma daya daga gurin ki.

Binta ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa, Azeema tace “dan Allah ki dan janye daga Junaid.”

Gaban Binta ne ya fadi, hankali a tashe ta kalleta, Azeema ganin yanda abin ya shigeta yasa ta murmusa tace “ba cewa nai ki janye daga gareshi gaba daya ba alfarma nake nema ki dan bari wannan uwar data rabu da danta shekara da shekaru ta dan samu damar shakuwa dashi na wasu yan lokuta.”

Idanun Binta ne suka ciciko. Azeema tace “nasan zaki fahimceni, kimin wannan alfarma kinji Binta?”

Binta ta daga kai alamar to hawaye suka gangaro mata, Azeema ta rike hannunta tace “nagode kwarai da yanda kika taimaki dan nan nawa, ma tabbatar samunki kusa dashi ne yasa ya iye jure rashin mu.”

Wasu hawayen ne suka cigaba da zubo mata, Azeema ta kalli Barira tace “kuje da ita gobe a hado mata abubuwan bukata.”

Barira tace “to Gimbiya.”

Nan Binta ya mike tai bangaren su Barira, tana shiga ta tsugunna tana hawaye, duk da ta fahimci Gimbiya sai dai tana ganin ba’a mata adalci ba ana neman rabata da Junaid wanda bataji ko yini zata iyayi bashi, a yanzu haka ma ji take kamar ta ruga inda yake.

Binta na shiga daki Barira ta kalli Gimbiya cikin jin dadi tace “Gimbiya kinyi maganinta.”

Azeema ta girgiza kai alamar a’a tace “matsalar ba ita bace Junaid ne, me kike tunanin zai faru in mutane sukasan ya dawo da mace sannan ba matarsa ba? Macen ma mara asali?”

Barira tace “ya zamuyi gobe?”

Da safe ki kiramin jakadiya.

Jakadiya? Barira ta tambaya, Azeema ta mike ba tare da ta amsa mata ba, taje shiga daki baiwar da Junaid ya aiko ta shigo ta sanar da Barira sakon Junaid.

Barira tace “wayyo tayi bacci, tun dazu dama take cewa bacci takeji kanta na ciwo.”

Kuyangar nan da jin haka ta juya, Azeema ta shiga ciki.

Zama tai a bakin gadon ta kalaman Junaid ne ke mata yawo, tabbas akwai wani dalilin dayasa Sarki ya daukeshi, to menene dalili? Baiso danta yai mulki? Kai ta girgiza da sauri dan tasan ba shi bane, tabbas gobe zata bigi cikin Jakadiya taji ko ta san wani abin, dan da dukkan alamu Abdulsalam ma baisan komai ba.

Ta dade tana juye akan gado kafin ta samu bacci ya dauketa.

***********

Jin Binta tayi bacci yasa ran Junaid yadan sosu, sai dai baiyi zargin komai ba, yana nan a zaune yana tunanin cin abinci Azi ya kwankwasa mai.

Bayan ya shigo ne ya sanarwa Junaid akan Sarki AbdulSalam na san ganinsa.

Tare suka fito da Azi dan dama bai sanshi ba bai taba ganinsa ba.

Sun isa fadar mai martaba, yana zaune an jera mai abinci a gabansa, Ji Zagi na sanarda isowar Junaid ne yasa ya kalli bakin kofa, har Junaid ya shigo ya zauna daga can gefe idanunsa na kansa, wani sansanyan murmushi ya saka ya nuna masa kusa dashi yace “dawo nan.”

Junaid ya karasa sannan ya gaisheshi, Abdulsalam ya amsa cikin tsananin kulawa sannan yace “Junaid!”

Kallansa yai sai gani yai yayi murmushi wanda yasa Junaid din dan murmusawa kadan shima.

Wai kaine ka zama saurayi haka? Wasa wasa in yaro ba agabam mutum ya taso ba saurin girman sa zaka gani.

Junaid baice komai ba sai dai yanda yake maganar yasa ya dan saki jikinsa.

Abdulsalam yace “bismillah.”

Ya fada yana mikamai spoon, Junaid ya amsa sannan suka fara cin abinci tare, sai turomai gabansa yakeyi wanda yasa Junaid din aake murmusawa, Sarki ya kalleshi bayan sun gama yace “Junaid!”

Junaid ya kalleshi tare da maida hankalinsa kansa, ka yafemin nasan duk da umarni ne na mahaifinka ban kyauta ba na barinka danai, da alama san kai nane yamin yawa?

Junaid cikin mamaki tace “san kai?”

Abdulsalam ya jinjina kai alamar eh, yace “kamar yanda kasani mahaifinka ne sarki, ban taba tunanin amsar mulki daga gunsa ba aka sari maban taba kawowa zan mulki kasarnan tamu ba, sai dai daga sanda Yaya ya furta min naji sha’awar hakan, sai dai nasan in har kana nan dole wasu sai sunyi tunanin yin amfani dakai gun karya ni.”

Yadanyi shiru kafin ya kalleshi yace “san kai ko?”

Junaid ya daga kai alamaf eh yace “san kai ne.”

Sarki ya kalleshi, Junaid ya murmusa yace “amma san kan mai amfani, akalla bakai kayi tunanin fotar dani ba, sannan baka taba tunanin sauke mahaifina ka hau ba, sannan sai daya furta sannan kaji kanaso.”

Ido Sarki ya kuramai cikin tsananin jin dadin kalamansa, kafin yace “nayi mamaki.”

Junaid yace “kayi hakuri in na bata maka, sau da dama nakanyi magana ne akan abinda raina ya bani.”

Sarki yace “hakan akeso ai, ya zama ko za’aji haushi ka aji amma a kalla ka fadi abinda ka sani.”

Junaid ya kalleshi suka murmusa a tare, Sarki yace “gobe za’ai taron dawowar ka zakaga mutane da dama da baka sani ba, yan uwanka da duk baka san dasu ba.”

Yace “haka Um......”

Sai yai shiru, sunan nama wahalar fada?

Ya kalleshi tare da dan shafar wuyansa, Abdulsalam yace “gashi nima so nake ka dinga kirana da Abba ba yanda kakecemin Kawu ba sanda kana karami.”

Junaid ya kalleshi da sauri, dariya sosai AbdulSalam yai wanda har fadawa sukai mamakin wannan lamari, yace “wasa nake ma, wato har ka fara hangowa ko?”

Junaid yace “ya nuna?”

Sarki yace “sosai, sai kayi kokarin gun nuna abinda ke ranka, dan nan masarautace za’ai amfani da abinda kake so a cutar dakai.”

Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa, me yasa yaji ya sake da mutumin nan daga haduwa daya? Lalai y cancanci a kirashi sarki yasan yanda zaiyi yaja mutum jikinsa.

Sunyi sallama Junaid ya fito fuskarsa a sake, Azi yace “da alama Yarima kaji dadin zuwan nan.”

Junaid ya kalleshi yace “ya nuna?”

Azi yace “gashinan a fuskarka.”

Da sauri Junaid ya hade fuska yace “Azi, a duk lokacin dakaga ina kokarin bayyana abu a fuskata kamin alama yanda zan gane, kafin na saba.”

Azi yi dariya yace “koyarwar da akai yau kenan?”

Junaid ya ce “eh.”

Haka suka wuce bangarensa ya zubawa abincin nan ido kafin yasa a kwashe sannan ya shiga ya kwanta, kan binta sosai yake mata ciwo? Yaso biyawa daga gun Sarki saidai yana tsoron karya tashesu daga bacci.

***********

Hajjo ranta yayi mugun baci mikewa zaune tai a kan gadonta cikin tsananin takaici, yanzu bangaren da take so ya barma Zubair har fadamai tayi shine ya ba wa wani Junaid? Fuskar tabta hade ranta yayi mugun baci, dan dama dazu da Ramlatu tazo haushi ya kamata da taga itama Ramlatun yanzu tsoron Azeemar take, yanzu kuma sai taji wannan zance?

Tayi tsaki yafi cikin kwano kafin bacci ya dauketa.
Da safe tana tashi aka kawo mata labarin cin abinci da hirar da Junaid sukai da Sarki jiya wanda har ana jin dariyarsa har waje.
Cikin takaici ta cilar da kofin dake hannunta, wanda ya kusa bige Zeena datake kokarin shigowa yanzu, tana ganin haka ta fara kokarin juyawa.

Cikin tsawa tace “ina zaki?”

Zeena ta juyo ta dawo ta zauna, Hajjo ta kalleta tace “kinba Sulaiman din hakuri? Kindai san gobe zai koma ko? Da yau dai tafi ma Takawa yace ya bari ayi taro dashi.”

Kallan Hajjo tai tace “ni wlh ba hakurin dazan bashi, koma naje kara batamai rai zanyi dan wlh ba sanshi na......”

Hajjo ta buga mata kallo tace “kema nema kike ki batamin rai? Dama tun shigowar yaran nan masarautar nan raina yake baci kema so kike ki karamin da wani?”

Zeena tace “Hajjo kinga Junaid din ne? Baki ganshi ba da ya sa kaya har........”

“Kin rufemin baki ko sai na sa an kulleki a daki?”

Zeena ta kalleta a tsorace, Hajjo tace “me kike tunani zamuyi a cikin wannan yanayi, dan in muka bari abu yai gaba daga ni har ku ba wanda zai tsira...”

Zeena tai shiru dan tasan gaskiya Hajjo ta fada, dole su san mafita kafin abu yai tsamari.......



*************




*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Biyar.


Bangren Azeema tun safe ake ta baki, sai hidima aketayi, Safiya kam itace shugabar taro, sai karban baki takeyi, suk ala ala take itama ta samu ganin kanin nata.

Jakadiya ce ta shigo ta baya, inda ta shiga dakinsu Barira, Binta na gyara dakin ta shigo, kallan Binta tai tace wacce ke gaisheta tace "daga ina? Dan ban sanki anan ba?"

Binta tai kasa dakai dan batasan me zatace ba, Jakadiya tai dariya tace kin dade anan ne?
Binta tace "a'a jiya nazo."

Jiya? A ranta ta maimaita sannan cikin dabara tace "oh ko kece kikazo tare da Yarima Junaid?"

Binta ta daga kai alamar eh, Jakadiya tace da mace ya dawo kenan? Boyeta ake anan?
Jakadiya tace "amma kamar ke ba baiwa bace bako?"

Binta tace eh, Jakadiya tai wani murmushin gamsuwa da abinda take tunani, fuskarta a sake tace "ina Barira kice na shigo."

Binta ta leko, ganin yanda mutane sukai yawa yasa ta koma ciki, Jakadiya ta leka sannan tace "daure ki fita."

Binta ta kalleta tace "ban hango Bariran ba.”

Jakadiya ta leko da kanta, daga can gefe ta hango Safiya na hidima tace “jeki gun waccen kice tazo Jakadiya na nan.”

Binta ta fito tana bin gefe gefe, ba wanda yabi ta kanta saboda sunata hirarsu, kusa da Safiya taje, ta kasa mata magana saboda tanata magana da wasu, Jakadiya dake leke tana kallanta ta girgiza kai tace “tab harna tausayawa rayuwarki.”

Safiya ganin taki tafiya yasa ta kalleta tace “lafiya?”

Binta tace “Jakadiya ce wai tana dakin can.”

Safiya ta mike da sauri tai ciki gun Azeema.

Azeema na zaune, Barira tana gyara mata kai, ga kujerar da take kai daga kasa turaren sura ne aka sakashi yake turarata, kayan da zata sa na gefe.

Safiya ta shigo ta sanar da ita zuwan Jakadiyar, Azeema wacce idanta ke lumshe ta bude su ta kalli Safiya tace “ki shigo da ita nan a boye.”

Nan Safiya ta juya ta nufi dakinsu Barira, Binta na tsugunr a gefe ta shigo nan tace “muje.”

Babban mayafi ta rufa mata suka wuce cikin dakin da sauri.

Suna shiga

Please Login or Register in order to submit comment