Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara sunkuyowa tace “Gimbiya Azeema.”

“Uban wayace ina nemanta? Karta kuskura ta shigomin nan dan koda wasa bana nemanta, na dauka na fada mata ko mutuwa naj kartazo nan?”

Jakadiya ta kalleta tace “Hajiya kidan saurara tare take da Junaid kar yaji.”

Junaid?
Ta fada muryarta na rawa, Jakadiya tace “eh.”

Azeema da Junaid da sukai shiru a waje saboda kalaman Hajiya Inna, Junaid ya kalli Azeema wacce itama ta kalleshi tai murmushi tace “karka damu bakomai.”

Jakadiya ce tace su shigo, Junaid ya kalli Azeema sannan suka shiga ciki.

Hajiya Inna ta mika hannunta tana cewa “Junaid!”
Matsawa yai gunta ya rike hannunta, kankame hannun sosai tai muryarta na rawa tace “Junaid! Junaid ashe da gaske sukeyi ka dawo.”
Ido yake kara kuramai? Ta zare hannunta daya tana shafa fuskarsa cikin farin ciki.
Gaisheta yai t amsa tana cewa “ina ka shiga? Kakarka nata addu’ar ganinka kafin ta mutu?”

Azeema ce ta gaisheta, bata tanka mata ba ta cigaba da cewa “lale lale Junaid.”
Azeema cikin sanyin murya takara gaisheta, ran Hajiya Inna a bace tace “tunda na barki kika shigo ai sai kimin shiru ko? Wallahi badan darajar Junaid ba zama a dakin nan bazaki sakeyi ba sai dai bayan raina.”
Azeema tai kasa da kanta, Junaid wanda kalam Hajiya Inna suka mai zafi, balle daya kalli Azeema yaga yanda itma kalaman suka tabata da alama.

Hajiya inna ce tace “Junaid barka barkan mu, yau Allah ya amsa addu’a ta.”
Junaid ya kalleta yai murmushin yake, Azeema ce ta mike tace “kiyi hakuri Hajiya dama Junaid na kawo miki bari na koma.”

“Idan kina magana kamar mutuniyar arziki wannan mata Allah wadan bakin halin ki da tsinanen san kai da san zuciya, yanzu kila in na tambayeki raban dakiyima Zubair addu’a ma kin manta, ki fita zai taho da kafarsa.

Azeema ta kalli Junaid wanda shima kallanta yakey, Murmushi tai mai ta daga mai kai alamar ba komai sannan ta fita.

Hajiya inna ta kalli Jakadiya tace “zubamin gishiri a kofar data fita.”
Wannan kalma ta konama Junaid rai sai dai baice komai ba.


Azeema na fitowa ta kalli Barira wacce idanta ya ciciko tace “meye hakan?”
Barira cikin konar rai tace “ji fa abinda ta miki, in da kara ai bai kamata ta miki hakan a gaban Junaid ba.”

Azeema tai murmushi a ranta tace hakan shine ya kamata da batai ba da banji dadi ba
Amma a fili murmushi kawai tai ta fara tafiya

**********

Hajjo sam ta kasa kwantar da hankalinta, ganin yanda Zeena yau ko shigowa batai ba, kenan da gaske san yaran nan take.

Yamma nayi ta mike ta nufi bangaren mai martaba dan ta san lokacin dawowarsa daga fada ne.”
Takawa ya cire kaya kenan Zagi ya sanar da isowar Hajjo, jalabiya ya zura ya bada izinin ta shigo.

Hajjo ta shigo ta zauna, gaisheshi tai bai amsa ba yace “Hajjo lafiya? Banyi tunanin ganinki ba.”

Kallansa tai tace “me kake nufi da zaka cikama Junaid alkawari akan duk abinda yakeso?”
Kallanta yai yace “akan me zan sanar dake?”

Kallansa tai ranta ya fara baci tace “Naji bakada hujjar sanar dani amma meye matsayin Zubair a masarautar nan?”

Kallanta yai cikin mamaki yace “Mekikesan ji?”

Tace “Ba abinda nake san ji sai dai nazone na tunama, Junaid ba jininka bane, Zubair ne danka wanda ka haifa, duk yanda kake tunanin san mutum baikai san daya kamata kayiwa danka ba.”

Ido ya zuba mata yana kallanta tace “sannan abu na biyu ka aurar da Zeena ga Sulaiman din nan dan hankalina ya kasa kwanciya da yanda ta fara maganar Junaid.”

Duk da yayi mamakin jin kalamanta amma bai tanka ba, tace “kardai ka manta nice matarka wacce nasoka tun bamuda matsayi, duk da ba sona kake ba ka auran amma a kalla inada hakki akanka.”

Tana kaiwa nan ta mike tamai sallama ta fita, shiru yai yana kallanta, harta fita waje yanayin fuskarsa ne ya canza wanda yasani shiga tunanin abinda yake tunani, ban samo amsarba naji yace “waya fada miki?”
Juyawa nai da sauri naga ba kowa agun, da wa yake? Abinda ya fadan kenan, na nuna kaina alamar ni? Lokacin na fahimci wai amsa yaba Hajjo wace ta dade da fita, to me yake nufi da waya fada mata?

Hmmmnmmmm


********


🌞*ZAFIN RANA*🌞
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*




Shiru mai martaba yai kafin yai gyaran murya alamar yanada magana, da sauri bafaden dake jikin kofa ya shigo, kallansa yai yace “A kiran Zeena.”

Da sauri ya juya ya fita, Zeena dake keance akan gadonta ta rasa ina zata sa kanta, fitowa tai a fussce ta zauna, ta kalli Fure dake zaune agun tace “Fure bangaren Yarima nakesan kije ki kiramin Binta.”

Binta? Wacece hakan?
Fure tai tambayar, Zeenatu ta harareta tace “koma wacece meye damuwarki? Kedai ki kiramin ita, sannan ki kirata a boye karki bari Junaid ya ganki.”

Fure tace “Gimbiya taya zani bangarensa na kira wacce bansaniba sannan ba tare da ya ganni ba?”

Ni Fure dan Allah kwakwalwarki tana aiki kuwa? Ke ni meyasa gaba daya bakida irin dabaru da fasaha ne? Wlh na kusa canzaki ki cigaba damin halin kifi.”

Fure ta juya da sauri tai waje, tsaki Azeema tai tace “bari inga yarinyar da har saboda ita yaje gun Hajjo.”

Fure na fita aka shigo neman Zeenatu inji mai martaba.

Mikewa tai jiki a sanyaye dan tasan maganar dai guda daya ce akan aure, shiryawa tai sannan ta fito.

Kallan kuyangarta tai tace “in Fure ta dawo kice su jirani.”
Tace to sannan ta wuce.

Mai Martaba na zaune gabansa katan Littafi na fiqihu ne yana dubawa, Zeenatu tana zuwa bakin kofar ta canza yanayin fuskarta a nutse ta shiga bayan ya bata izinin shiga.

Zama tai daga gefe zama irin na ladabi.
Abdulsalam ne ya kalleta yace “Mahaifiyarki tazo akan na aura miki Sulaiman.”

Da sauri ta kalli Sarki tace “Ranka ya dade tuba nake amma Allah bana san shi.”

Wani murmushi yai yace “ni kike kalla kice bakyasan zabina?”

Kallansa tai ta maida kanta kasa tace “Allah da kaima kanaso bazaka tambayi ra’ayi na ba, zartar da auren kawai zakayi tunda Hajjo tama magana, amma kiran dakamin da tambayar daka min ya nunamin bakaso.”

Shiru yai yana kallanta kafin yai wani kalausan murmushi yace “to naji tunda bakyaso sannan banaso fadamin wa kikeso? Inbaki dashi kuwa na aura miki wanda yamin.”

Kallansa tai da sauri sannan ta maida kanta kasa, yace “baki dashi.”
Tace “akwai amma matsalar ba wanda zai yadda dani.”

Wanene?
Shiru tai gabanta na wani irin faduwa, a hankali tace “Yarima.”

Me kikace?”
A hankali tace “Yarima!”
Ido ya kura mata sannan yace “Kina tunanin Azima da Hajjo zasu yadda?”

Ta kalleshi idanta ya ciciko tace “na sani, shiyasa nake tsoro.”

“Tashi kije.”
Da sauri ta kara kallansa, yace “kin fadi ra’ayinki sannan kinsan bazai yiwu ba, ko kina da wani abin cewa?”
Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a’a.
Mikewa tai ta fito daga fadar.

Tana fita Abdulsalam ya mike ya shiga ciki, shiru yai yana tunani, abubuwa guda biyu suna mai yawo akai, me zai faru idan daga baya asiri ya bayyana?
Sai dai me? Yna tunanin ba abinda Zai faru tunda a lokacin Junaid yana auren Zeenatu in yai sa’a ma harda d’a.

To amma in kuma asiri ya tuno kafin faruwar hakan fa? Ko kuma Junaid ya rufe idansa akan komai fa? In kuma abin ya shafi har Zeenatun fa?
Wadannan dalilai sun sa gaba daya kansa kullewa.

*******
Zeenatu na fitowa ta nufi bangaren Junaid, wanda ita kanta batasan nan ta nufa ba sai data ganta a kofar shiga.
Da sauri tace “Fure me muke anan?”
Da sauri wata kuyanga tace “Fure bata nan ai.”
Zeenatu ta kalli bangaren sannan tai ajiyar zuciya, samun kanta tai da juyawa.

Gimbiya?
Abinda taji an fada kenan, juyawa tai cikin jin kunya, Azi ne Junaid na gefensa.

Kallan Junaid tai a hankali tai dan yake tace “wucewa nazo yi nai.”
Junaid ya kalleta sannan yace “tanan?”
Eh, naje bangaren Mai Martaba ne.”
Oh!
Yace sannan ya nufi hanyar shiga.
Ya Junaid?
Juyowa yai ya kalleta, tai murmushi tace “bamuje gun Hajiya Innan ba.”

Kallanta yai yadanyi wani tunani akasan ransa kadan kafin yace “zaki shigo?”
Shiru tai tana kallansa, yace “inbakyaso ki barshi.”
Tace “tunda kai ka gayyacen ina zan ki zuwa.”

Shiga yai tabi bayansa, zama tai tana kallan bangaren yanda aka gyara shi, murmushi tai tana cewa “dole Hajjo taso aba Ya Zubair nan.”
A hankali tai maganar sai dai Junaid ya jita, kallanta yai bayan ya zauna yace “daga bangaren Hajiya Inna nake.”
Cikin mamaki tace “haba? Kai dawa?”
Yace “Umma ce takaini.”
Ido ta zaro tace “Umma karama? Garin ya?”
Garin ya kuwa? Yai tambayar cikin bugar ciki.
Zeena tai shiru kafin ta kalleshi tace “Hajiya Inna ta haramtawa Umma karama zuwa bangarenta.”

Junaid yace “meyasa? Bayan sirikarta ce?”
Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa.
Can tace “Ya Junaid saboda haka kace nazo?”
Yace “me? In saboda haka ne bazaki shigo ba?”
Tace “bance ba amma a kalla nadanji haushi.”
“Meya hadasu?”
Kai ta girgza alamar rashin sani tace “kawai dai nasan batasanta sannan ta hanata shiga bangarenta, ita da Mai martaba.”

Junaid ya kalleta yace “hardashi?”
Eh shima baya zuwa.
Murmushi Junaid yadanyi kadan fuskarsa kunshe da tunani yace “shikenan, in kin gama gani bangaren sai ki wuce, zan shiga nai magrib.”

Mamaki ne ya kamata kafin ta tattaro abinda zata fada harya rufe kofa.

Labanta ta cizs saboda takaici sannan ta mike ta bar bangaren nasa cikin takaici.

Idanunta ne taji suna kara cicikowa, kenan ita duk inda tai ba dadi, cikin jin haushi ta shiga bangarenta.

Wata yarinya ta gani a tsaye daga gefe kadan inka shiga.

Kallanta tai a wulakance tace “uban me kike anan?”
Binta ta kalleta tace “ance kina nemana ne.”

Ni?
Tai tambayar tana kallanta daga sama har kasa.

Binta tace “haka waccen tace.”
Ta nuna fure wacce ta taho da sauri.

Binta wacce kafafunta harsun gaji da tsayuwa ta dan jingina.
Fure ta karaso tace “Gimbiya itace .”

Da saure Zeenatu ta kara kallan Binta cikin mamaki, kece Binta?”
Eh nice.

Batasan sanda tasa wata dariya ba wacce ni kaina na saki baki ina kallanta.

A hankali ta fara zage Binta wacce ta nemi ta daidaita tsayuwarta.

Binta mamaki ya kamata, Zeenatu sai da tagama kallanta tsaf sannan tace “daga bangaren Ya Junaid nake.”

Binta ta kalleta da sauri, Zeenatu tai murmushi tace “Ashe abinda ya faru dake kenan? Ayya kiyi hakuri kinsan hausawa sunce babban goro sai magogin karfe.”

Binta ta daure ta kalleta tace “me ya sameni?”
Zeenatu ta matso saitin kunnent tace “Ya Junaid ya fadamin komai, tundaga sands ya taimakeki har abinda ya faru kwanan nan.”

Idanun Binta ne suka fara sauyawa, tace “mene?”

Zeenatu ta shagwabe fuska tace “na tausaya miki, shima Ya Junaid yana tausayinki sosai.”

Bakin Binta ne ya fara rawa, kuka na neman kwace mata, daurewa tai ta kalleta sannan ta sunkunya tace “tuba nake Gimbiya amma nasan ba abinda kikaji daga bakin Ya Junaid, sannan ko kinji ma nasan yayi maganar ne bada wani abin ba.”

Zeenatu a zuciya ta kifa mata mari, Binta ta rike gun ta dago tace “menayi kuma?”

Zeenatu tace “tambaya kike? Sai yanzu ma na tuna ashe kece wannan ta rannan.
Sannan yau ya zama rana ta karshe da zaki dinga maida min martani.”
Tana kaiwa nan tai ciki.

Binta ta juya ta fita, tana fita tasa kuka, da gaske Ya Junaid ya fada mata komai? Kuka kawai takeyi ta rasa ma me take tunani.


**********
Junaid bayan yayi sallah ne ya zauna akan sallaya yana tunani, ita da Mai martaba? Meyasa? Shiru yai yana tunani, kafin ya mike.

Waje ya fito yadan tsaya a baranda yana dan kallan kofar da zata sada ka da bangaren bayi, Binta ko tana me?
Shiru yai tare da sakin ajiyar zuciya, ganin ba alamarta ne yasa ya juya kamar zai koma.
Jin an bude kofa ne yasa ya juyo da sauri.

Binta ya gani tana tafe tana share hawaye, tsayawa tai daga bakin kofar itama ta zubamai ido, sun fi minti uku suna kallan juna kowa da abinda ke yawo a ransa kafin Junaid yace “Binta!”
Kallansa tai a hankali ta tako, sai dai bata isa inda yake ba tace “Yarima Barka da dare.”
Ta juya zata wuce.

Shiru yai ya bita da kallo har ta shiga, meya sameta?
Umma ce?
Abinda ya fado mai kenan.




******
Ayusher
24



*ZAFIN RANA*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ*

*Wannan Littafin Na Saidawa ne ga Duk mai Bukatar siya ya tuntubi 07084161619 mungode*


*25*

Binta!
Tana kokarin rufe kofa taji ya kira sunanta, tsayawa tai cak zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, A hankali ta juyo ta kalleshi.

Murmushi ya sakar mata sannan yace " magana nakeso muyi."
A hankali ta fara taka kafafunta zuwa inda yake, idanunta na kansa, tuntube tai saura kiris ta fadi, da sauri ya zabura yace Binta.
Daidaita tsayuwarta tai ta kalleshi har ya sauko daga baranda din da yake.

Kallan juna sukai kawai suka sa dariya, yace "har yanzu dai sai a dinga tafiya ana neman faduwa.
Ta karaso tace "haryanzu dai kafin na fadi an gama razana."

Murmushi suka sakeyi da tuno da yanda sukeyi acan.

Karasowa tai ya zauna a kasa ya zura kafafunsa kasan baranda din, kallansa tai sannan ta zauna daga gefe.
Ya kalleta cikin hasken farin wata yace "daga ina?"
Nadan fitane zagaye."

Zagaye? Ya maimaita tare da yin sansanyan murmushi ganin indai zata fita dashi suke fita.

Kallanshi tai tace "wacce magana?"
"Me kike tunani akan komawa bangaren Umma?"
Kallansa tai da sauri tace "Naam?"
Yace "eh, ko bakyaso?"
Shiru tai tana kallansa, kawar da kansa gefe yai, ganin haka yasa tace "zan koma."

Shiru yai kafin yace "Nagode."
Mikewa tai tace "zan koma gobe in Allah ya kaimu."
Tafiya?
Ya fada ganin ta mike tsaye, juyowa tai ta kalleshi a ranta tace kafi kowa sanin zamana a nan kusa dakai abinda zai haifar.
A fili kam cewa tai na gaji ne.
Ya fahimceta hakan yasa baice komai ba.

Yana nan zaune har ta shiga ciki.

Mikewa yai ya shiga dakinsac zamanta acan shine kwanciyar hankalinsa ya tabbatar intana gunta ba'abinda ta isa ta mata, sannan hakan ne zai bashi damar kwatar mata 'yancinta.


**********

Binta na shiga ta sanar da Harira zata koma gobe bangaren Azeeema, cikin tsananin mamaki Hari tace "Binta hauka kike? Matar da tafi tsanarki kije ki gunta?

Kallan Hari tai ta tuno da kawar da kansa dayai, tace "akwai dalilinsa na yin hakan."

Dalili?
Harira ta tambayeta, Binta ta kwanta tace "eh."
Shiru tai tana tunanin abinda ya faru tsakaninta da Zeena yanzu, me Zeena take nufi? San Junaid take kenan ko me?

Mikewa zaune tai da sauri ta kalli Harira tace "Harira ya ake gane mutum na san wani?"
Harira tace "yanda kike san Junaid."
Ido ta zaro da sauri tace "ni Ya Junaid ai........"
Sai kuma tai shiru, Hari tace "me?"
Kwanciya ta kuma yi da sauri tace "bacci nakeji."

Idanunta ta rufe tana tuno yanda Zeena ke magana, lalai itakam tata ta kare dan ta tabbatar ba abinda Junaid zaiyi da ita yana ganin Zeenah.

A haka har bacci ya dauketa.

Da safe Junaid ya nufi bangaren Azeema, tana zaune a falanta ta lumshe ido tana tunani, ga busar barewa datasa ake mata.

Hannunta daya take dan kadawa wanda duk sands take tunani haka takeyi.

A hankali tace "Barira an kawo rahoton danace?"

Tace "a'a Gimbiya amma nasan Waziri yana hanya."
Sallamar Junaid ne yasa ta bude idanunta dan batai tunanin jinsa ba."

Shigowa yai, tai saurin sallamar kuyangar dakeyin busar, tace "Junaid!"
Gaisheta yai sannan yace "Tuba nake Umma jiya dana dawo bansamu shigowa ba."

Tace "bakomai Junaid nasan kanada dalilinka."

Murmushi yai sannan ya kalleta cikin kulawa yace "Umma wani abu ya hadaku da ita ne? hajiya Inna nake nufi."

Kallansa tai itama sannan ta sallami kowa dake falan ta kalleshi, tace "Karkasa wannan abin a ranka dan nima ban bari ya dameni ba."

Tausayinta ne ya kamashi yace "amma kin mata laifi ne?"
"A'a batasona ne saboda tana jin haushi na auri Abdulsalam wanda ta rika bayan rasuwar Mahaifinka."

Duk da bai gamsu na amma baice komai ba.

Shiru yai kafin ya daidaita zamansa yace "Na umarci Binta ta dawo nan."

Kallansa tai da sauri tace "nan?"

Ta kalleshi cikin tsananin mamaki, dan bata taba tunanin ko ita tace ba zai yadda da hakan.

"Eh, sannan inasan sanin yanda yanayin masarautar take tun lokacin da suka gabata."

Azeema ta kalleshi cikin jin dadi tace "ba matsala, zan sa Mahmud mijin Safiya wanda yake Hakimi ne shi ya sanar dakai komai."

Muje? Ta tambayeshi.
Yace "Eh amma akwai dalilin kiran ne?"

Tace "lokaci lokaci yakan kira mata da yaransa a tattauna."
Junaid ya jinjina kai kawai.

Mikewa tai suka fito, a bakin kofar fita suka ga Binta wacce ke kokarin shigowa rike da ledar kayanta.
Da sauri ta rusuna ta gaisheta, Azeema ta kalleta tace "Binta kin taho?"
Eh.
Shiru tai tana wani tunanin, kafin ta kalli Junaid tace "Junaid me kake tunani in ta bimu?"

Ina?
Murmushi tai tace "Su Barira ma suna zuwa dan taje itama bana ganin akwai matsala."

Junaid yai shiru duk da ya tabbatar akwai wani abin a ranta sai dai rashin sanin menene ya hanashi musawa.
Barira ta kalla sannan tace "Bari a ajiye kayan ku biyomu."
Nan suka shiga ciki.
Kayan kawai suka ajiye suka fito, Binta na tambayar Barira akan ina zasuje.
Barira ga shareta kamar ba da mutum take magana ba, hakan yasata yin shiru.

Bangaren Mai Martaba Sarki Abdulsalam suka nufa.

Fadar sa aka bude musu kofa, Zagi ya sanar da isowarsu.

Jakadiya na tsaye a bakin kofar tana musu barka da zuwa.

Hajjo, Zeena, Zubair da su Ramlatu da ragowar matan sarki da yaransu sun hallara da alama sune sukazo karshe.

Hajjo ta hade fuska, Azeema ta zauna a inda aka ware dominta sannan Jakadiya ta nunawa Junaid inda zai zauna, zama yai su kuma su Binta da ragowa bayi suka koma gefe suka tsafsaya, Binta tana tunanin me take anan?

Azeema kam kallanta tai kadan tace gwara ki fahimci Junaid ya miki nisa hakan ne yasa na kawoki.

Zeena ce ta zubawa Junaid ido cikin jin dadi da mamaki halim da take neman tsintar kanta a ciki.
Gani tai ya dago ya kalli wani gun, idanuntanr suka kai kan Binta, wani irin kululun bakin ciki ne ya kamata.

Sanar wa isowar Mai Martaba da Zagi yai ne yasa kowa ya daidaita.

Abdulsalam ya shigo ya zauna tare da kallan su.

Kowa an ajiye kayan marmari da abinsha a gabanshi.

Bayan an gaida Mai Martaba ne ya kalli Junaid yace "Dafatan Junaid ka fara warewa da zaman nan?"
Junaid yace "Alhamdulila."

Andansyi shiru kafin Sarki yace sannan yace "Bari mu fara gwada tambaya kamar yanda aka saba, dan a tattauna a kara rike sanin juna."

"Idan akace za'a sai Sarki nawa kuke tunanin ya kamata a siye shi?"

Hajjo ce ta kalleshi tace "Rankanya dade wannan tambaya ta ina za'a nemo amsarta?"

Sarki bai kalleta ba yace "wannan tambaya inaso Zubair ya bani amsarta"

Zubair ya kalleshi yaga yanda Sarki ya hada rai yace "ta ina za'a sai sarki? Ai wannan sai dai bayi, idan kuma har akaje ga siyan sarki to lalai sai dai a kwashe duk tattalin arzikin garin a sai shi."

Wani kallo Sarki yamai yace "idan aka kwashe arzikin kasar sai kuma ai rayuwa dame?"
Zubair yai shiru, Ran AbdulSalam ya baci saboda haushin amsar daya bashi, kallan Zeena yai wacce itama taji haushin ansar."

Zeena me kike tunani?

Kallansa tai tace "indai za'a sai sarki to kenan ya zama ba sarki ba"

Yace haka ne indai har aka siye shi ai ya tashi daga matsayinsa, Junaid kai fa me kake tunani?

A siyeshi a silai

Silai?

Azeema ta kalleshi da sauri tace "Junaid!"

Nan kowa ya fara yan kananan maganganu, Zeena ce ta kalleshi itama hankalinta a tashe.

Binta kam idanunta kawai ta runtse dan tasai halin Junaid duk abinda ke ransa fada zai, yanzu me ya kawo zancen silai? Karamin kudi?"

Sarki wanda shi kansa ransa ya baci matuka ya dunkule hannunsa sannan ya dan murmusa yace "me yasa kace haka?"

Junaid yace "A tunanin mutane dayawa Sukai ba wani kudi bane mai daraja sai dai a gun talaka wanda yake neman ci dasha dakyar silay tafi komai daraja a gunsa, kafin a samu wanda baisan darajar sulai daya ba za'a samu talakawan da suka san darajarta ashirin, hakan yasa Silai ta zama kudi mafi daraja a ciki kudi, sannan sai ka hada silai dayawa ne zaka samu kudi mai daraja da kake nema.
Idan har za'a sai sarki to sai a siyeshi a abu mafi daraja wanda talaka da mai kudi sukafi sanin darajarsa."


Yana kaiwa nan yai shiru bai kara tanka komai bs.

Ido Abdulsalam ya zubamai, tabbas koshi bai taba kawo hakan a ransa ba, wannan shi ake kira magana da hikima wanda ake neman Sarki da ita, tabbas dawowar Junaid nan ba karamin matsala zai jawo masa ba nan gaba.

Azeema wacce dadi ya kamata ta kalli Abdulsalam, hannunsa ta kalla dan ta gama saninsa duk wani abu dayake tunani rabi tana ganewa daga kallansa.

Ganin hannunsa a dunkule yasa ta kalli fuskarsa, da sauri ya sake hannunsa sannan ya kalleta cikin nuna tsantssn jin dadinsa yace "Masha Allah! Tabbas wannan shi ake kira magana cikin hikima."


Zeena ce ta kalleshi tace "Mai Martaba ni kaina na tsorata jin Ya Junaid yace silai, sai dai jin bayaninsa yasa na fahimci me yake nufi sannan na fahimci Silai yafi komai daraja kamar yanda Sarki yafi mutanen gari."

Hajjo ce ta sa hannu ta bige Zeena dake gefenta, sannan tace "amsoshi duka sunyi ma'ana kowane da nashi fahimtar."

Azeema ta dau kofin dake gabanta ta kurbi ruwa.

Binta wacce tai shiru tana kallan Junaid wanda ya daure fuska sam ba alamar fara'a a tattare dashi, tabbas Junaid dinta jinin sarauta ne, wanda ita kuma take wacce mahaifinta ma bayaso........

Zeenatu ce ta kalleta ganin yanda take kallan Junsid cikin rauni yasa tace "Binta!"

Kafin ma Binta ta amsa Junaid ya kalli Zeena.

A ranta tace au ashe zaka kalleni, Binta ce ta matso da sauri, Sunkuyowa tai Zeena ta mika mata kofinta tace "dan daurayomin naga kamar kura."

Binta ta kalli Junaid wanda ya dauke kai kamar baisan tana gun ba.
Sai dai gaba daya hankalinsa na kansu, Binta ga amsa tai waje, Azeema ta bita da kallo.

Zubair ne ya kalli Hajjo cikin kunar rai, alams tamai da karya nuna jin haushinsa.

Sarki yai murmushi yace " Junaid kayi tunanin abinda nace ka zaba?"

Junaid yai kasa dakai yace "zan sanar dakai Ranka ya dade."

"Sirri ne kenan?"

Zeena ta tambaya, bai ko kalleta ba sai dai Azeema datace da alama.....




**********
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*



Nanma shiru yay yak'i tankawa, yakumak'i kallon kowa.

Binta ta dawo da kofin da zeena tabata ta d'aurayo, rissinawa tayi ta mik'a mata, d'agowar da zatayi suka had'a ido da Junaid, saurin janyewa tayi, shima ya basar.

Azeema da Idonta ke kallon duk motsinsu taji zuciyarta ta k'untata, amma saita had'iye fushinta tamkar babu komai.

Sarki yacigaba da jeho tambayoyinsa ana bashi amsa, Junaid kam tundaga ta farko bai kuma tankawa ba, sai dai tsaf yake nazari akan amsar kowa da motsin kowa.

Bayan taron ya tashi kowa ya nufi sashensa, Azeema taso Junaid yakoma sashenta dan tanason jin miya tanadi zaba bisa ga k'yautar sarki na abinda yakeso.



*****************

Tunda Junaid yadawo daga sashen mai martaba saiya kasa zama, sai safa da marwa yake a falonsa yana cud'anya wasu abubuwa daya danganci masarautar tasu, a yanzu mafita d'ayace dashi, nutsuwa wajen jin sirri da tushen masarautar tasu, haka kawai jikinshi na bashi ba dalilin dazaisa mahaifinsa ya kaishi can gefen gari ba tare da sanin mahaifiyarsa ba.
Ta wannan hanyarne kawai zai samu amsar tambayarsa akan wanene yasa a fiddashi a masarautar zuwa ke6antaccen waje?.

Ajiyar zuciya ya sauke da addu'ar samun kwarin gwiwa akan samun warwarar cud'ad'd'en al'amari da zuciyarsa ke hangowa gameda abubuwa masu yawan gaske.


*****************

Suna isowa sashenta ta kalli zeena rai 6ace.....

“Hajjo nikam wannan kallon naki tsoro yake ban, nidai nasan banyi wata kato6ara a wannan taronba, banda abin arziki danai.”

Hararta Hajjo tayi tana hura hanci, murya a cinkushe tace, “wani lokacin saina ringaji inama bani Na haifi Zubair ba, kwata-kwata k'wak'walwarsa bata ja yanda ya kamata, dolene na nemo malami ya koyar dashi hikimar zance”.

Dariya Zeena tayi sosai dukda kallon da

Please Login or Register in order to submit comment