Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka nufi bangaren Azeema.

Kallan Zeena yai bayan sun dan yi tafiya mai dan tsayi jefi jefi suna daga hannu in an gaishesu, yace “ni Shamaki yaushe ya samu mukaminsa?”

Kara matsowa tai kusa dashi hakan yasa Binta tadan ware kadan da su, tace “sanda Abba ya hau mulki.”
Shamakin da fa?
Tace yayansa ne saukeshi akai, Junaid yace “Galadima fa?”
Tace tunda shine haryanzu kum........”

Baya tai tana neman faduwa, da sauri yasa hannu yariko hannunta.
Binta ta kalla wacce gaba daya takeji kamar an wareta, wacce ganin Zeena da Junaid a haka ya kara sa taji gaba daya komai ya tsaya mata.
Wani murmushin wulakanci ta watsama Binta, sannan ta dago.
Junaid yace “Kina Gimbiya bakya ganin hanya.” Ya fada yana saketa.

Gyara tsayuwarta tai tana ‘yar dariya kadan, tace “tafiyarce bakaga yau wahala takemin ba?”

Cikin rashin fahimtar me take nufi ya maida kanshi kan Binta wacce ita ta fahimci me take san cewa.

Junaid ne ya matsa kusa da ita yace “Binta!”

Kallansa tai sannan tai murmushin yake tace “Naam.”

Muje, naga ne kin tsaya, kai ta daga alamar to.
Haka suka isa bangaren Gimbiya Azeema wacce take ta jiransu.
Da hanzari Barira ta karaso tace “sun iso Gimbiya.”

Nan ta kara gyara zamanta tasa aka musu iso.

Junaid ne ya fara shiga sai Zeena sannan Binta.

Gaisheta suka fara yi ta amsa.

Kallan Zeena tai wacce take ta wani iyayi wai ta kasa zama daidai, sannan ta kalli Binta wacce tai shiru, ta kalli Junaid wanda kamar kullum yanzu fuskarsa daf take.

Nan ta kalli abincin da aka jera sosai a gun tace “kuci abinci zan shiga ciki.”

Nan ta mike tai ciki, Zeena ta kalli Fure tace “Fure zubamin.”
Fure ta taho da sauri, Junaid ya kalleta yace “ku bamu guri.”

Nan kowa ya fita, cikin mamaki Zeena ta kalleshi, kallanta yai yace “ki zuba da kanki.”
In zuba?
Ta fada tana nuna kanta.
Dauke kai yai daga kanta yace “Binta bismillah.”

Yanzu kam bazata kara bari a maidata ‘yar kallo ba.

Da sauri ta jawo plate ta zuba mai abinci, sannan ta zuba nata.
Spoon ya mika mata shima ya dauka, dariya yai yace “naki wayan shine aka cikamin?”
Itama dariya tai tace “ya kamata kai kaci dayawa dan Allah nasan yunwa kake ji.”

“Ahhhh na manta ashe kina gane in cikina ya rarake, lalai zanyi dabara yanda bazaki dinga ganewa ba”

Dan Kallan Zeena tai ta gefen ido wacce ta cika ta batse ko abincin ma ta kasa sawa.

Kallan Junaid kawai take dama yana dariya haka?
Binta ce ta kalleta tace “Gimbiya na zuba miki?”

Zeena tai shiru tana nazari kafin tace “basai kin zubamin ba, tunda ya Junaid yace nashi yamai yawa bari muci tare.”

Cikin mamaki Junaid ya kalleta, Binta ta zuba mata ido itama.

Junaid ya kalli Binta sannan ya nuna mata plate da idanunsa alamar t zuba nata ya dauke kai.

Cikin kufula ta jawo plate ta zuba.

Safiya wacce sanda sukazo tana hada kayanta taga Azeema ta shigo.

Kallanta tai tace “Umma ya kika shigo kika barsu, bayan kinsan mata biyu lokaci daya akwai hidima?”

Azeema ta zauna tare da cewa “hakan ne yasa na taso.”

Safiya tace “ni Binta nakeji, itada bata magana sosai, Zeena nasan haka zataita kunsa mata haushi.”

Azeena ta gyara zamanta tace “intaga ana neman kwace mata miji ta kwaci kanta, zama ka fadawa mutum karya bari amai kaza da kaza bata lokaci ne, in taga mijinta na neman yin nisa da ita ta mike.”

Safiya tai dariya tace “Umma kenan komai naki sai kin hasaso kike aikata shi.”

A falo kuwa haka kowa yai shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa.

Zeena na jin haushin abinda Junaid ke mata, Binta na kishin yanda Zeena da Junaid ke maida ita yar kallo, Junaid kam tunanin Shamaki da Galadima yakeyi, kallan Zeena yai sannan yace “Waziri fa?”

Fuska ta hade tace “shima tun lokacin Marigayi.”

Junaid yai shiru yana tunani.

Binta ce ta zuba ruwa ta ajiye kusa dashi, kallanta yai sannan ya sakar mata murmushi yace “Nagode!”

Itama murmushin ta maidamai tare da nunamai wata kwanon agun.

Kallan robar yai sannan yace “a’a”

Tace “kai Ya Junaid!”

Yace “Allah karkici kin manta abinda ya saki?”
Da sauri tace “na hakura ba sai ka fadaba.”

Zeena ta kalli kwanon dake cike da gwaza, sannan ta haraeta tare da tabe baki.


***********

Sarki ne ya kalli Shamaki yace “ka gano inda Sabisun yake?”

Shamaki ya girgiza kai yace “haryanzu ranka ya dade, amma wai me yasa kake nemanshi yanzu?”

Sarki yace “haka kawai nakejin hankalina ya kasa kwanciya, ni gaba daya yaran can gani nake kamar kallan mu yake yana nazari akan mu.”

Dariya Shamaki yai yace “karka damu Ranka ya dade na tabbatar yanzu da yke danka kuma sirikinka bazai kawo wannan a ransa bama.”

Sarki ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “haka nake fata.”

******
Ayusher🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{36}


A bangaren Azeema ya barsu, fitowa yai ya nufi bangaren Hajiya Inna.

Daga baranda ya tsaya yana amsa gaisuwar Jakadiya.

Junaid ya kalli Jakadiyar yace “Jakadiya ina san magana dake.”

A tsorace ta kalleshi tace “To Yarima.”

Fitowa tai tabi bayansa har bayan ginin Hajiya Inna.
Su biyu ne agun, ya kalleta yace “Jakadiya shekararki nawa kina aiki anan gidan?”

Dan murmushi tai tace “tun ina Yarinya nake anan.”

Junaid ya kalleta yace “meyasa Hajiya Inna batasan Umma?”

Da sauri Jakadiya ta kalleshi, Junaid cikin yanayin maganarsa ta kasaita ya kalleta yace “tambayarki nake, dalilin zuwa na da kaina dan karma kiyi tunanin boyemin wani abu ne, zan iya shiga na tambayi Hajiya Innan da kaina.”

Hankalin Jakadiya ne ya tashi, ta zube a kasa tace “Yarima!”

Junaid yace “menene dalili? Na tabbatar ba akan ta sake aure bane.”

Shiru tai sai da Junaid yai gyaran murya alamar bacin rai.

Da sauri tace “Yarima ka gafarceni amma Hajiya In
tace tun Marigayi nada rai Gimbiya da Sarki suna san juna, tace san mulki ne yasa Gimbiya taki auran Sarkin yanzu ta zabi Sarki Zubair.”


Junaid ya kalleta yace “dan tana sanshi ta auri yayansa menene na tsanar?”

Jakadiya gabanta ya sake faduwa, hankali a tashe ta kalli Junaid tace “wannan Hajiya Inna ce kawai tasan dalilinta.”

Ido Junaid ya zuba mata sannan a hankali yabar gun ba tare da yace komai ba.

Gaba daya kansa ne ya kulle, dan har bibiyu yake gani.

Dakewa yai harya isa bangarensa, a daki ya zauna yana tunani, in tana sansa kenan Hajiya Inna tana zarginsu da kebencewa bayan anyi aure ko me? In haka take zargi kenan shima haihuwarsa akwai ayar tambaya? Wani murmushin takaici yai yace “ta yaya? Ai da ba wanda zai kawo maganar aure na da Zeena a cikinsu, to menene?”

Sai can bayan Magrib Azi ya shigo yace “Yarima lokacin zuwa bangaren Binta yayi.”

Junaid ya kalleshi sannan ya mike jiki a sanyaye, Azi cikin mamaki ya kalleshi, ya dauka zumudi zai hana Junaid mantawa, meke faruwa?


*******


Zagaye take tayi a cikin dakinta, gaba daya hankalinta nakan bangaren Binta dan ta tabbatar Junaid nacan tunda kwananta ne, zama tai a bakin gado ta harari kujerar daya kwanta daren jiya, mikewa tai zumbur ta sa mayafi ta fito falo.

Fure da sauri ta taso tace “Gimbiya lafiya?”

Zeena ta kalleta tace “Bangaren Maman Rabi zani.”

Ramlatu? Abinda ya fado ran Fure kenan, tace “Gimbiya me zakiyi acan?”

Wani banzan kallo ta mata tace “mu biyu zamu koma banasan kowa yasan inda muke.”
Da sauri Fure tace to.
Fitowa tai ta aiki kuyangin dake waje suka wuf suka fice.

Ramlatu na zaune suna hira Fure ta shigo.
Zubewa tai ta gaisheta sannan ta mata alama data sallami mutanen dake gun, nan Ramlatu ta sallamesh.

Kallan Fure tai tace “lafiya?”
Gani tai an bude labile kallan mai shigowa tai, mamaki ne ya kamata ganin Zeena.

Da sauri ta mike tsaye tace “Gimbiya?”

Zeena ta karaso ta zauna sannan ta kalleta, sallamar Fure tai sannan ta maida hankalinta kan Ramlatu tace “Ramlatu kun samo inda Sabisu yake?”

Mamaki karara ne ya bayyana a fuskar Ramlatu tace “Sabisu?”

Zeena ta hade fuska tace “kunsamo inda yake?”

Cikin mamaki tace “ai bangane bane, me zaki mai?”

Zeena tace “Zaki fadamin ko sai na fita na nufi bangaren Umma karama na fada mata kin amso magani?”

Hankalin Ramlatu ne ya tashi a tsorace ta kalle Zeena tace “bamu sameshi ba amma munji labarin yana wani kauye wai Bukul.”

Bukul?
Zeena ta tambaya.
Ramlatu tace “eh amma da alama Hajjo ta hakura dan bata sake sawa a nemeshi ba.”

Zeena ta kalleta tace “kar wani mai numfashi yasan nazo gunki balle yasan maganar da mukai.”
Ta mike ta fito.

Suna isa bangarenta ta kalli Fure tace “da gari yadanyi haske kadan kije bangaren Binta kice Yarima ina bangarensa ina jiransa.”

Kallan mamaki Fure ta mata sai dai batace komai ba sai to.

A can bangaren Junaid kuwa, bayan sunyi sallah tare ne akan sallaya ta kalleshi cikin kulawa ganin yanda yai shiru yana dan nazari.
Hannu tasa a hankali ta kamo hannunsa, kallanta yai sannan yai murmushi.

“Meke damunka Ya Junaid?”

Wani sansanyan murmushi ya sakar mata yace “zuciyata ke sanar dani wani abin wanda kuma bansan kwakwalwata ta amince dashi.”
Hannunsa tadan murza kadan tace “in har bakasan amincewa dashi ko tsoron tabbatar da abinda kake zargi, ka hakura dashi mana.”

Kai ya girgiza mata alamar a’a yace “abu ne da dole sai nayi.”

Kai ta daga alamar ta fahimta.

Kallanta yai yace “shiyasa nake neman alfarma.”
Alfarma?
Ta tambayeshi, yace “zaki iya jirana?”

Kallan mamaki tamai na rashin fahimta, yace “zuciyata gaba daya bata nan gun, sannan ina tsoron abinda zan binciko wanda kila ya shafi tsatsona da rayuwata, zaki jira na gama abinda nake? Banasan na shiga hakkin daya daga cikinkin ku.”

Gaba daya jikinta ne yai sanyi duk da batasan me yake nufi ba amma tasan tabbas abinda yake tsoro yanada waya a ransa wanda har yasa yake tunani haka.
Kai ta daga alamar to hannu yasa ya jawota jikinsa ya rungume, tsoron abinda zuciyarsa take rayamai yakeyi.

Kwanciya ya fara yi ya jawota jikinsa ya rungume tsam, in har mahaifiyarsa nada wani tabo baisan ya zaiyi rayuwarsa ba.

Yanda ya matse binta ne yasa a hankali tace “Yaya!”

Kallanta yai sannan ya sassauta rikon yace Yahkuri Binta.”

Murmushi tai ta dago kanta ta kalleshi, ganin yanayinsa ne yasa ta kwanta a kafadarsa cikin tausayamai.

A hankali bacci ya dauketa.
Junaid kam kasa bacci yai sai can wajen dayan dare ya samu bacci ya daukeshi.

Yana sallar asuba ya kalli Azi bayan sun fito daga masallaci zai mai magana kenan Hadimin sarki wanda ke jikinsa ya iso gun da suke.

Junaid ya kalla bayan ya gaisheshi yace “Yarima Mai Martaba yace da rana ka shigo fada.”

Junais yace to.
Yana tafiya ya kalli Azi yace “Azi inaso ka tafi neman Sabisu, karka bari kowa ya san abinda kakeyi.”

Da sauri Azi yace “to Yarima.” Daga nan ya fita.

Junaid ya shiga bangaren Binta tana zaune kan sallaya tana wa Junaid addu’a da fatan dacewa.

Zama yai a bayanta a hankali yasa kansa akan bayanta.

Murmushi tai bayan ta kammala addu’arta a tare suka shafa sannan ta gaisheshi.
Kallanta yai yace “Binta kin tashi lfy?”
Cikin jin dadi tace “lafiya kalau Ya Junaid.”

Murmushi yai yace “Da alama Bintata ta fara dawuwa.”
Dariya tai tace “Da ina naje?”
Yace “kin bari masarauta ta cinye rabinki.”

Dariya ta sakeyi shima yana dariya yace “ba haka bane?”

Zatai magana sukaji ana magana.

Cikin mamaki ya kalleta ganin yanzu gari ya waye.
Binta ta fito ta bude kofa.

Fure ta gani cikin mamaki tace “lafiya?”

Fure tace “Gimbiya ce tace acema Yarima tanada magana tana bangarensa.”

Tsayawa Binta tai cikin tsananin mamaki, Fure ta juya.

Binta jiki a sanyaye ta nufi ciki, kallan Junaid tai wanda yace “waye? Wai ya akai bakida hadimai ne sai wata guda daya da na gani jiya?”

Binta ta kalleshi tace “Gimbiya ce ke jiranka a bangarenka.”

Cikin mamaki ya kalleta, Gimbiya?
Tace eh.
Yanda tai maganar kana gani kasan taji haushi.

Shiru yai yana tunani, ta samo wani abin ne? Kamar bazai tashi ba har Binta taji dadi sai taga zumbur ya mike.

Kallansa tai da sauri tace “ina zaka yaya?”
Yace “bari naje zan dawo.”
Mamaki ne ya kamata dako magana bai sake mata ba ya fita.

Kasa motsi tai a inda take, shiru tai tana tunani, yace bazai kwanta da ita ba bayan jiya ya kwana da Zeena, yanzu kuma ya tafi ya barta? Anya Ya Junaid dinta ne?

Junaid ne ya nufi bangarensa.

Zeena na zaune a falo ya shiga.

Zama yai daga kujerar dake kallan tata yace “ya akai?”

Kallansa tai sannan ta dan lumshe ido tace “magana nakeso muyi.”

Kallanta yake baice komai ba.
Tace “na samo inda Sabisu yake.”

Kallanta yai da sauri sai kuma yace “taya zaki san inda yake a yini daya?”

Tace “Shikenan tunda baka yarda ba.”
Ta mike zata fita.
Hannu yasa da sauri ya riko hannunta.
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba yace “Yana ina?”

A hankali ta juyo ta kalleshi tace “Yana Bukul.”

Mikewa yai da sauri, yace “inane Bukul?”
Tace “bansani ba nima haka kawai akacemin, sai dai yanda nasamoma inda yake nima sai ka amince da abinda nake so.”

Kallanta yai baice komai ba, tacigaba “Kamin alkawarin bani dama nima.”

Dama?
Ta cigaba “Zuciyara zata hakura da rashin san da kakemin kafin aure amma bazata iya daukar kiyayyarka ba bayan aure.


Kallanga yai baice komai ba.
Shiru suka danyi.
Cikin jin haushin aikar Azi dayai, ya shiga tunanin abinyi.

Kusa da shi ta kara matsowa tace “Meyasa kake nemanshi wai? Kai Da Hajjo bansan me kuke nema dashi ba.”

Junaid ya kalleta yace “Inaji dole na fita da kaina.”

*******
Ayusher🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{37}


Kallansa tai hankali a tashe tace "ina zaka?" Ta fada tare da riko hannunsa.
Kallanta yai ya kura mata ido yana nazari.

Gani tai ya saki wani dan siririn murmushi wanda ya bata tsoro, tace "ya akai?"

"Ba sai naje da kaina ba, tunda bansan ya yake ba balle inda zan sameshi takamaimai." Gaba daya batasan me yake nufi ba shi yasa ta kasa cewa komai, hannunsa ya zare cikin nata sannan ya fita.
Kasa tsaidashi tai saboda tana tunanin abinda yake nufi a kanta.

Junaid na fita hadimansa suka biyo bayanshi, bangaren Azeema ya nufa.

Tana daga kwance ana dan matsa mata kafarta.

Barirace ta shigo ta sanar da ita isowar Yarima, kallan Barira tai tace "Junaid?"

"Eh Gimbiya."
Mikewa zaune tai ta sallamesu, Junaid ne ya shigo ya zauna a kasa.

Sai daya gaisheta ta amsa tare da tambayan kwanan matansa.
Suna lafiya ya fada yana kallanta.

Kallansa tai tace "da wani abin ne?"

Junaid yace "matsalarku da Hajiya Inna, bakya tunanin ya kamata ki bata hakuri? Halin rayuwa shi ake dubawa."

Kallansa tai tace "Junaid ko na bata bazata taba hakura ba, ta riga tasa abinda takeso a ranta."

Abinda takeso? Ya tambayeta.
Dan zamanta ta gyara tace "a'a kasan in mutum baya san wani kiris yake jira."

"Amma da tana sanki ai."
Dan murmushi tai cikin waskewa tace "hmm...." gani batasan cigaba da zancen yasa yace "ko kinsan Sabisu?"

"Sabisu? Waye hakan?"
"Awwwww nagane shi bawan Mahaifinka, ya akai ka sanshi?"

Dan kallanta yai yana nazari akanta kafin yace " naji su Hajjo na nemanshi ne."

Hajjo? Tai tambayar cikin mamaki, idanu ta zaro da sauri, sannan ta sauke idanta kasa saboda karya gane, yace "eh bandai san dalilinsu ba."

Yake tai tace "Allah sarki."
Har ya mike yace "naji yana wani kauye wai Bukul."

Mikewa yai ya mata sallama ya fita, yana fitowa Falo ya bi bayan kofar da kallo, yace "Umma dan dan Allah ko menene karya zama akwai ki a ciki."

Tunda ya fito ta kasa ko motsi, meke faruwa?

Fitowa yai ya koma bangarensa, bangaren Zeena ya fara shiga sai dai batanan, hakan yasa ya wuce bangaren Binta yana nazari.

Binta na zaune a bakin gado duk abin duniya ya isheta, jin motsin yasa ta fito da sauri.

Tana ganin Junaid ne taji wani dadi ya zo mata wanda har taji idanunta na neman kawo ruwa.

Mamaki ne ya kamashi, a hankali ya tako inda take, yana karasowa ta rungumeshi.

"Ya akai?"

Tace "bakomai."

Dagota yai a hankali ya zubawa fuskarta ido, a hankali ya sumbaceta, sannan yace "kinji haushi ne?"

Cikin sanyin murya tace "naji amma kadan"

Murmushi yai yace "wannan karan nayi laifi dafatan baza'a hukuntani ba."

Dariya ta dan yi tana neman dan matsawa daga jikinsa ya kara kankameta, tana kallansa tace "bari naga wannan karan wani hukuncin za'ama."

Murmushi yai yace "kenan laifin biyu nai tunda jiya nan na taho da safe kenan kowa namai laifi?"

Fuska tadan hade, yace "zan tafi Binta inada abinda zanyi, nazo ne na fada miki."

Jiki a sanyaye ta kalleshi tare da yin murmushin yake tace "Uhm hmm."

A hankalinya zare ta daga jikinsa yace "kici abinci, sannan zan nemi Harira ta kawo miki hadimai, dan ita ta girma ne amma da ita ta dace dake."

Kai Binta ta daga alamar gamsuwa sannan tace "to Ya Junaid."

Sake sumbatar kuncinta yai sannan ya juya ya fita, da kallo ta bishi.

Yana shiga bangarensa yaga Zeena acan.

Tsayawa yai yana kallanta cikin mamaki.
Tana ganinya shigo ta mike da sauri tace "Ya Junaid me kake nufi? Wai me kake san ji gun Sabisu?"

Kallanta yai yace "kije ki sanar da Hajjo inda Sabisu yake, da alama itace take nemansa ba ni ba."

Kallan mamaki ta masa tace "bangane ba."

Shiru yai yana san mata karin bayani sai dai inya tuna yar Hajjo ce sai yaji bazai iya ba, dan ya tabbatar daga tayi subutar baki komai ya wargaje kenan.

Zeena ce ta kamo hannunsa tace "menene?"

Kallanta yai sannan yai murmushi yace "bakomai kawai ina ganin ita take nemanshi bani ba."

Shiru tai tana kallansa ta tabbatar akwai dalilinsa nayin haka.

Shikenan zan fada mata, kallanta yai a hankali yace "nagode."

Dayake bata taba kawo jin hakan daga gareshi ba shiyasa kalmar ta shigeta dakyau, hannunsa ta saki gaba daya jikinta yai sanyi.

Murmushi ya mata yace "zaki iya sanar da ita yanzu?"
Kai ta daga alamar eh, sannan tace "nagode Ya Junaid."

Dame?
Kai ta girgiza alamar ba komai sannan ta fita.

Tana fita ta tsaya a waje, wani sanshi ne yake kara shigarta da darajashi.

Tana kokarin wucewa sashinta taga Harira a bakin kofar Binta da alama abincin safe suka kawo mata.
Binta ce ta bude mata hakan yasa suka hada idanu, su Hari ne suka zube suna gaisheta.
Binta ce ta gaisheta, tana mamakin meyasa batabi ta can baya ba inda zata shiga bangarenta, amma sai data zagayo ta nan?

Zeena ce ta amsa cikin isa sannan ta wuce, Fure ce ta matso da sauri tace "Gimbiya kina birgeni wato ki nuna mata daga can kike kenan."

Wani kallo tama Fure batace komai ba har suka shiga bangarenta.

Junaid kam zama yai a kan kujera tare da hade hannayensa yana fatan samun nasara akan abinda ya shirya.

Shiru yai yana nazari........


******

Harira na shiga ta kalli Binta, tace "Ranki ya dadw inasan magana dake inba damuwa."

Binta cikin dariya tace "lalai Hari muje ciki."

Da sauri tace "a'a nan ma yayi."

Hadiman sun ajiye abincin sun fita sannan Hari ta kalleta.

Tace "Kiyi hakuri da tambayar da zan miki."

Binta tace "Hari ni ki daina min magana haka kimin magana kanki tsaye yanda muka saba."

Hari ta kalleta tace "ba abinda ya faru daren jiya?"

Kasancewar ta gane abinda take nufi yasa Binta tace "eh."
Harira tace "Gimbiya fa?"

Binta tace "bansani ba amma ta kirani tana sanar dani abu ya faru."

Harira ta kalleta tace "Dama tun kafin aure naso na sanar dake amma bansamu dama ba kasancewar kuna bangaren Gimbiya sai dai yau naga ya kamata ki sani.
Kada ki kuskura ki cigaba da sanyin nan da kike neman daurawa kanki, da can kinada sanyi amma abin bai kai haka ba, yanzu ba ke kadai bace agun Yarima, idan har kika cigaba da abinda kikeyi kina zaune wlh Junaid ganinsa ma sai ya gagareki."

Cikin mamaki ta kalleta tace "bangane nida mijina ya gagaren gani ba."

"Gidan sarauta kike bayan nan ku biyu ne sannan bayanan matarshi yar sarauta ce jinin mulki, kina tunanin shakuwa da san da yake miki zai dawwama ne?"

Binta tace "Harira Ya Junaid ne fa?"

Cikin dan zafi Harira tace "ba namiji bane? Maza duk inda suke irinsu daya, idan har kika cigaba da wannan halin naki kina zaune sai kin rokama zai ganki, me kike mai anan? Banda ki zauna kullum kina kiransa? Kinsan matsalarsa? Kinsan burinsa? Kinsan abinda ke kasan ransa? Kinsan me yake tunani?"

"Taya zansan abinda bai fadamin ba?"

Dole a matsayinki na matarsa wacce kuka taso tare sai kin mike kinji menene matsalarsa, na tabbatar shima yanasan sanar dake bayasan saki a damuwa ne."

Gaba daya jikin Binta ne yai sanyi, Harira tace "anjima zan kawo miki hadiman da zasu kula dake."
Tana kaiwa nan ta mata sallama ta mike.

Shiru Binta tai tana nazarin kallamanta tabbas gaskiya Harira ta sanar da ita.

********

"Me kike anan? Haryaushe akai auren da zaki fara yawo?"

Hajjo ta tambayi Zeena dake zaune.

Zeena ta kalleta tace "kefa Hajjo dadina dake rashin hakuri, sai kiji ai dame nazo miki ko?"

Hajjo ta hade fuska tace “menene?”

“Sabisu!”

Da sauri Hajjo ta kalleta tace “ya ya? Ke a ina ma kika sanshi?”

Ranar ina nan kuke labari da Ramlatu, na samo inda yake.”

Da sauri Hajjo ta matso tace “a ina yake?”

“Bukul wani kauye ne.”

Kallan mamaki Hajjo ta mata tace “ya akai kika sani?”

Shiru Hajjo tai tana kallanta, Zeena tace “menene?”

“Junaid kikaji yana nemanshi?”

Zeena tai shiru badai Junaid abinda yakeso kenan ba? So yake ai zargin yana nemanshi? Kai ta girgiza sauri ganin abin bai bada ma’ana ba.

Kallan Hajjo tai tace “koma menene ni ki fadamin meyasa kike nemanshi?”

Hajjo ta kalleta ta matso tace “Bincike nake san yi, so nake in samo abinda mahaifinki bai isa ya hana Zubair mulki ba.”

Baki ta tabe tace “wai ke haryanzu Hajjo batun ba Zubair mulki yana nan?”

Wata muguwar harara Hajjo ta bata tace “tashi ki tafi gun mijinki da alama nan gaba komai naki ma gun mijinki zai koma.”

Zeena ta mike ba musu ta masa sallama ta fita.

Wani irin haushi ne ya kama Hajjo kafin tai maza tasa a kira mata Zubair dan yazo ya sa a nemo mata Sabisu.


**********

Junaid ne ya shigo cikin fadar Zagi na mai kiran Lafiya.

Junaid ya shigo sannan ya gaida mai martaba.

Sarki cikin nuna jin dadinsa yace “Matawalle an shigo?”

Junaid yace “Eh Ranka ya dade.”

Nan su Shamaki da su Waziri da sauransu suka fara gaisheshi.

Junaid ya amsa cikin isa da kasaita irin ta ‘ya’yan sarki.

Sarki yai dan gyaran murya yace “Dama nasa kazo ne saboda a sanar dakai abubuwan da zaka dingayi a matsayinka ma matawalle.”

Junaid yai dan kasa dakai cikin girmamawa yace “to Ranka ya dade.”

Galadima ne ya kalli sarki yace “Ranka ya dade naga bai dade da aure ba da nauka za’a barshi ya dan huta zuwa sati biyu.”

Junaid kam a ranshi yace ina za’a banni na huta ba’a san nasamu lokacin bincike?


Haka sukai tattauna sannan suka taso.


*********

Azeema tayi shiru tanata zagaye a dakinta tana jiran Barira, can Barira ta shigo da sauri, ta yaye mayafinta tace “Gimbiya na sanar ma Gimbiya Safiya, tace ta sanar ma Mijinta yanzu zai wuce.”

Azeema ta jinjina kai cikin gamsuwa.

******
Hajjo ce ta kalli Zubair tace “ka tura kanin nawa?”

Yace “eh Hajjo sai danaga tafiyarsa na shigo.

*******

Junaid na kishingide a bangarensa idanunsa a lumshe a hankali naga ya sake yin wani sansanyan murmushi wanda nace hmmm

🤔🚶🏻♀️

******Ayusher🏌🏻♀️******


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{38}


Yau kwana biyu kenan da tafiyar Azi, gaba daya Mai Martaba yasa Junaid ya shiga hidima ta ko ina.
Yar yanzu ba wacce ya kwana da ita tsakanin Zeena da Binta.
Yau ya kasance ranar Zeena ne, yana zaune a bangarensa bayan ya kammala abubuwan daya kamata yai, shiru yai yana duba wasu takardu tare da fatan dawowar Azi a wannan rana.
Tun safe yake jiran isowarsa amma haryanzu shiru.
Kamar da wasa yaji Azi yace "Yarima nine!"

Zamansa ya gyara yamai iso, Azi ya shigo ya zube a gabansa ya fara gaisheshi.
Junaid ya amsa sannan yace "ya ya?"

Azi ya kalleshi ya danyi shiru.
Junaid yai dan murmushi yace

Please Login or Register in order to submit comment