Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jira kawai suke abasu tabbacin zancen gashinan mintuna uku da zancen harsun sake breaking news.


*******
Qarfe shida na yamma daidai lokacinda zancen auren ya fita adaidai lokacin Anneti tayo aike me qarfi na daukar NURU zuwa wani kebantaccen sashe dake cikin sashenta Wanda Babu Wanda yasan inda aka Kai NURUn har afia kuwa Dan Koda aka tafi da ita afian na bacci Dan ko daki ba'a Bari Takoma ba daga Palo Dan haka Koda afia ta tashi da mummunan labari biyu daya Bata mummunan shock taci Karo na farko tun a waya tasamu labarin auren mahaifinta ta fito a rude saikuma tasamu labarin kebe NURU Wanda kowa yace baisan inane aka kebetaba.

Wayar dad dinta ta nema arikice tafara Danna Masa Kira Bata shiga hannuwanta dukkaninsu rawa suke da qafafunta tana sake Danna Kiran dad dinta Kiran Imran sai shigowa wayarta yakeyi na kakkautawa tana kashewa Dan ayanzu batasan ma a Ina kanta yakeba ta zari takalmi tayi sashen Anneti saidai tana shiga bata samu ganinta ba sbd Wai tana hutawa Bata fitowa lokacin dawowa tayi a haukace ta nema numbern kaleeb ta Danna Masa Kira shima Bata samu damar magana dashiba Yana cikin dakin hutawarsa.

Ji take kamar ta Ari hauka sbd so take tasamu bayanin abinda tagani take kumaji idan zancen datayine aka dauka da gaske take ake Shirin auren tun anan.
Palo tadawo ta zaune tana neman rusa kuka sbd idanuwanta dasuka kada sukai jajir ta dafe kanta dake neman tarwatsewa.

Wayartace tayi ringing a zabure ta wawuro wayar tana dubawa sai jikinta yayi wani irin daskarewa sbd tsananin sabon firgici da mamakin data shiga sbd ganin sunan""
MUM" baro baro akan screen dinta sai kawai jikinta ya saki tana kallo wayar na ringing harta tsinke Bata iya dagawa Dan kuwa rabon data ji mum dinsu shekarunma batasaniba tun bayana tafiyarta sai yau Wanda tasan dalilin Kiran baya wuce labarin auren dad dinsu data gani a duniya.

Zubewa tayi kan kujera tareda sake kuka Mara sauti tanajin wani zafin mum dinta da duk itace silar watsewar farin cikinsu" i hate you mum"takeson cewa Amma zuciyarta na hanata saidai wani irin zafin mum din takeji,
Babban baqin cikinta biyu ta rusa rayuwar NURU bayan tasan yanda sukeson juna da Imran hakama Imran ta rusa Masa farin ciki uwa uba me gaba daya bazata iya yadda ta karbi wata ba mum dinsuba amatsayin matar dad dinsu Dan haka Dole zatasan yanda zatayi ta Raba wannan auren ko an hadashi sbd kowa yasamu abinda yakeso.


***
Duk wani gyara da shiri na musamman anfara yiwa NURU shi atake da aka zo da ita Wanda Kuma kala Babu Wanda yake cewa ga duk tambayoyin datake musu sbd ita tsoro da firgici abin yake Bata Dan batasan meyake faruwa duk ta daga hankalinta musamman dataga ire iren gyara na musamman da ake Mata tamkar wata sarauniya Wanda Kuma ta tabbatarda wannan Shirin na aurene kokuma na Shirin kaiwane ga NEGES,to kenen gurin NEGES dinta datake negestatinsa za'a kaita..wasu irin hawayene masu matuqar zafi suka ciko idanuwanta tuno komai ya ruguje kenan daga yanzu a rayuwarta.

DELAH GIZAH ta dauki babban amo na jama'a manyan qasashe da dauloli dabam dabam hadda turawa da larabawa na nesa Dana kusa sun cika gizah damqam shiyasa tsaro da matakai harsunyi yawanda ko matso na Wasa basayi sbd atake zakayi ta bakin ranka sbd matakan tsaron ba dama musamman idan washe gari tayi ranar daurin auren kenan matakan saisunfi tsananta dan kuwa ko yanxu bashiga ba fita a gizah idanba na manyan baqinsuba na daurin aure.

Anneti duk wani farin ciki tana cikinsa musamman datai ido biyu da kyakkyawar fuskar NURU wadda cikin kwana biyu kacal ta sauya sbd tsananin gyara daya maidata tamkar asalin sarauniyar gizah musamman har wani sheqi fatarta keyi tuni tasake bada odar dasa sabon gyaran ciki Wanda zaibadu damar janyo zuciyar MALEEK gareta daga sun kusantu.

Washe gari jekadi na isowa tareda iyayen NURU dasu padima acikin tawaga ta musamman ta kaleeb Wanda Yana shigowa gizah aka rufeta gabaki daya ba shiga ba fita sai bayan daurin aure da qarfe biyun Rana.

Guri na musamman aka sauke iyayen NURU wainda suketa fama da padima da zazzabi me qarfi ya rafketa reras Banda some some Babu abinda takeyi daqyar suka samu tayi bacci kafin sukaci abincin alfarma fiyeda kala goma suka koshi aka kawo kayan Shirin abal dinsu ya shirya masu tafiya dashi suna jira yafito suka nufi can bangarenda za'ayi daurin aure yabar amminsu da sallar nafila tana zuba adduaoin a daura auren Nan lafiya yasa idan akai auren sai mutuwa NURUnta.
Meryam Kuma a zaqe take dataga NURU wadda Babu me ganinta kaf sai mijinta idan tafara fitowa daga maboyarta Wanda wannan al'adarsu ce.

Qarfe biyu aka daura auren UBAYD MALEEK M KALEEB da NURULHUDA ABAL YONAS akan sadakin darhaman zinare Wanda dubban daruruwan hamshaqan duniya suka shaida a masarautar delah gizah dakeda kafaffen tarihin.
Daurin auren yasamu 'yan farin ciki da Yan sabanin hakan da masu burika daban daban akansa Dana alkhairi Dana sharri.
Maganar aurensa ita ta batarda maganar rabuwarsa da matarsa data fara bulla.

Har yamma tayi lis afia Bata cikin cikakkiyar nutsuwarta Dan haka tanajin saqon fitowa da MUSHRAH(bride/sabuwar Matar sarki/amarya)yagama bazuwa a cikin delah gizah ta shirya cikin qarfin hali da danne damuwarta ta shirya tsaf cikin shigar alfarma ta li'ilitinta tafito Dan zuwa miqa gaisuwarta datake al'ada dakuma Dole Dole ga duk wani Wanda ke cikin masarautar delah gizah fitowa Kai gaisuwa ga duk MUSHRAn NEGES wato amaryar sarki.
##MAMUH#


_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899*_Mamuhgee 21_*
Tunda aka fito da ita taga sauyi me matuqar girma da mamaki sbd tsaro da girman da ake Bata kamar za'a bauta Mata yasa taji hankalinta ya ninku gurin tashi da firgici saidai sbd a rufe take Babu me iya ganin hakan gashi takasa Jin komai daga bakin kowa bare ta tabbatarda abinda yake faruwa Abu daya data tabbatar shi shine tabbas yau gurin NEGES dinta za'a miqata Wanda hakan yasa idanuwanta masifar cikowa da hawayen tausayin kanta dana im harma Dana afia da farhat dinta da zasu rabu gashi har abada Bata ikon sauya wannan ikon akanta.

Kai tsaye babban sassan MALEEK UBAYD aka nufa da ita Wanda shine yakeda ikon fara ganinta kafin tafito kowa yaganta Dan haka suna Isa tangamemiyar kofar gurinsa masu tsaro suka bude musu sbd tsananin tsaro da securities din gurin masu Kama da samudawa anan kowa ya tsaya daga ita sai jekadi suka shige aka rufo har lokacin Babu kala jekadi Bata ce ba shiyasa batama San da ita ake tareba bare tasan inda suka shigo.

A kofar palonsa na karshe Wanda dagashi saina hutawarsa sai master bedroom dinsa Dan haka daganan jekadi taja gefe ta tsaya cikin bawa NURUn girma tace"

NURU gaki a kofar shiga gurin uban gidanki Kuma mijinki na halak malak Wanda shine zai budeki kafin kifito al'ummar gizah nason sheda ganinki wato mace me sa'a.

Da haka tayi baya ta fice daganan Takoma can farkon shigowa jiran fitowar NURU din.

Kasa motsi tayi daga inda take tsaye sbd firgicinta daya koma zallar mamaki Dan kaman Bata fahimci me jekadin tagama fadaba ta wuce.
Saitaji kaman tace aure?

Girgiza Kai tayi ahankali tareda sauke Numfashi sbd sanin ba hakan bane itada samun arzikin daukar igiyoyin auren wani sai Allah tunda harta rasa igiyoyin auren im tasan aure gareta sai rabo me qarfi Dan tuni take cikin radadin hakan har lokaci da rayuwar data samu a Paris ya mantar da ita komai yanzu Kuma qaddararta tadawo gareta Dan haka ba gudu bare tsira.

Ahankali ta tura tareda saka Kai cikin qofar da jekadi ta 'dan bude Mata ba dukaba sbd takaitawa NURU aikin bude qofar Wanda badan kofar MALEEK bace itace zata bude Mata ita har qarshe.

Wani irin sanyin AC ne Dana wani qamshi data sani suka fara tarbanta ta maida kofar ta rufe ahankali har lokacin fuskarta arufe take.
Tunda ta iso tsakiyar palon ta tsaya cak batareda ta qara taku ba sbd bugun zuciyarta daya qaru Yana fita da qarfi Dan zuwa yanzu tagama tabbatarda qamshin datake ji musamman data iso tsakiyar palon taji yasake gauraya gurin.

So take ta yaye fuskarta taga inda take sbd firginta daya sake dawowa Amma ba hali sai kawai qafafuwanta suka hau rawa da dukkanin jikinta dama gashi ko abincin kirki tadaina ci kwana biyun sbd tsoro da shakkun datake ciki na abinda yake faruwa
Hannunta dake tsananin rawa ta daga ahankali ta shafo fuskarta dake lullube taji zufan tashin hankalin turaren MALEEK datakeji tako Ina na shiga hancinta take ta lalubo kujera ba shiri sbd jirin dayake Shirin dibarta ta ta zauna akan kejeran cikin rudewan rasa abin,
Dauke wuta tayi atake sbd Jin kusada mutum ta zauna batareda tasaniba rintse ido tayi cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin meyene Wai yake faruwa da ita ta yunqura da sauri zata tashi taji anriqe hannunta ta tsaya cak tareda saurara abinda takeji na qamshin MALEEK zuciyarta na harbawa da qarfi kaman zata faso kirjinta.

Lullubinta taji an yaye ahankali Wanda yasata yin qasa da kanta tareda rufe idanuwanta sbd koma wanene bazata iya kallonsa Kai tsaye ba tunda shugabantane.

Tsit gurin yayi Babu wani motsi Babu wata magana tsawon mintuna shida ahakan kafin ya miqe ahankali har lokacin kayan daurin auren ne ajikinsa dasukai Masa matuqar kyau suka sake boye manyancinsa tareda bayyanarda asalin kyawunsa abun Kamar almara Amma har wani kyalli yakeyi Wanda ake cewa na anganci.

Ciki ya wucewarsa batareda yace komaiba,
Har lokacin Bata dagoba saidataji shigewarsa ta bude fararen idanuwanta ahankali ta dago Amma takasa bin inda yabi Koda kallo ne,
Hannunta daya Kama ta dago ahankali takai hancinta gabanta yasake wani irin faduwa,
Duk Wanda ya yaye fuskarka daga fitowarka wankan boyo shine yakeda Kai da ikonka Kona aure Kona negestati,
MALEEK???
MALEEK???

Toshewa kanta yayi gabaki daya Bata fahimci komaiba ta miqe har lokacin qafafunta na rawa ta fito dama wannan al'adace Kuma ancikata tunda ya yayeta.
Tana fitowa kallo daya jekadi Tai Mata ta hangi tsagwaron rudu da firgicewa atareda ita da hanzari ta qaraso gurinta cikin kulawa da girma tayi qasa da murya tace"

Ki nutsu kada ki daga hankalinki taron mutane ne keson ganin MUSHRAn MALEEK.

Cak ta tsaya tareda waiwayowa ta kalli jekadi da idanuwanta da zuwa lokacin tuni hawaye suka fara gangaro musu kenen dai ta tabbata maleek ne hancinta da wasi wasinta yazama gaskia.

Da sauri jekadi ta Kara gabanta ta boyeta tana cewa"

Allah ya taimaki mushrah wannan ba girmanki bane bayyanarda hawayenki agabanmu Dan Allah ki kwantarda hankalinki
Allah kuma ya huci zuciyarki da salama idan bazaki iya ganin kowaba ayanzu ko zamu rakaki gurin iyayenki dasuka zo kifara mgana dasu wannan sakone daga Kaleeb Kuma Yana Tayaki murnar tareda sanyawa aure albarka.

Ita gabaki daya batasan lokacinda kuka yazo mataba ba shiri jekadi ta nufi sashen Anneti da ita Wanda yafi kusa daga Nan din suna zuwa Anneti tace akaita kuryar dakinta abarta ta huta tukuna dama zataji abin wani iri tunda batada masaniyar komai.

Take aka sanar kowa ya tafi NURU tana hutawa bazata samu damar fitowaba yanzu Wanda hakan yasa kowa yafara mamakin irin sa'a da gata tareda daurewa da NURUn ta samu na take al'ada tun aranar farko.

Afia ma Bata datazo yau da mamaki Takoma sashensu sbd Bata samu damar ganin NURU ba sbd dolen Dole abarta ta huta tasamu nutsuwa Wanda itakuma tasan NURU na buqatarta yanzu sbd tayi Mata bayanin kada ta tayarda hankalinta idan sun bar Nan komai zai koma daidai zata samu Imran dinta.

Kuka tayi sosai batareda tasan Kona meneneba itadai yanzu iyayenta dataji suna kusa takeson gani Dan sune zasu Mata bayanin komai ta fahimta.
Sai dare lis ta fito cikin wasu kayan dabam da aka kawo Mata akasa tayi wanka ta sauya ta fito dukkanin abindake jikinta qyalli yakeyi tundaga kayan dake jikin nata har zuwa wata siririyar diamond necklace dake wuyanta ta daqyar ta iya cin abinci tareda Anneti suna gamawa Ana kawo Mata farhat data rikice musu kwana biyu na rashin ganin NURU din tana ganin NURU ta fallo da gudu itama NURU sai lokacin taji Dan damar abinda takeji ta rungume farhat din cikin samun nutsuwa tace"

I miss you sweetie.

I miss you more my Lewa ohhh Anneti tace ke mamanace yanzu bazaki taba tafiya kibarniba kaman mum ko??

Wani dum NURUn taji takasa dagowa ta kalli Anneti dake jinsu hakama takasa bawa farhat amsa ita Tama rasa kunyace ta kamata kome?

Riqeda hannun farhat din suka fito daga sashen Anneti jekadi da sauran mabiyanta uku na bayansu suka nufi gurin iyayenta farhat nata yaba kyawu da sauyawar datayi itadai gabaki daya tafiyar kawai take hankalinta baya tareda ita abubuwa da yawane suke yawo cikin kanta wainda suka girmi tunaninta.

Suna Isa dukkaninsu jekadi daga waje suka tsaya daga ita sai farhat suka shiga bayan an wangale Mata kofar tana shiga aka rufe abal da amminsu dake zaune a Palo suka kallo qofar atare fuskokinsu na bayyanarda wani yalwataccen farin cikinsu daya kasa boyuwa itama kasa motsawa tayi sbd kasa gasgata mafarki take kokuwa gata ga iyayenta bayan wasu shekaru take idanuwanta suka ciko da hawaye suna Shirin gangarowa meryam data fito daga gurin padima tana ganin kyakkyawar halitta a tsaye cikin palon ta tsaya cak taqare Mata kallo ta tabbatarda NURUntace a guje tayo kanta tana Kiran sunanta NURU ta ware Mata hannu tareda dauketa cak suka qanqame juna tana jero Mata yarensu Wanda farhat ce kawai batasan me take cewa NURUn ba.

Daqyar suka saki juna kowanne farin cikinsa yakasa raguwa ta qaraso gurin amminta ta rungumeta tareda riqo hannun abal dinta cikin yare da muryarta me sanyi tace"

Abal ubana nagari nayi kewarku fiyeda komai da kowa nayi farin cikin ganinku cikin lafiya da wadata.

Murmushin farin ciki me sauti abal yasaki Yana dafa kanta yace"

NURU 'yata tagari munyi farin cikin ganinki cikin koshin lafiya da nustuwar rayuwa,
Bamu taba farin rayuwaba irin Wanda Kika bamu ayanzu na aurenki da muka gani cikin ahali me girma da daraja.

Amminsu kuwa sbd farin ciki takasa cewa komai sai kallon 'yarta takeyi cikin tsananin so da kauna tareda alfahari Wanda yasa NURUn Jin nauyin iyayenta musamman da abal ya dauko maganar auren yana Mata nasihar hakuri da nutsuwa tareda tawakalli daya santa dasu Kuma yake qara Jan hankalinta dasu akan ta rungumi wannan aure da hannu bibbiyu.

Cikin mamaki ta kalli ammi tace"

Ammi Ina padima?

Ajiyar zuciya ammin tasaki tareda Dan satar kallon abal din kafin ta kalli kofar dakin da padiman ke ciki tace"

Tana can akwance batada lafiya sosai gobema inshallah zamu koma gida sbd aje can abal dinku yasamu maganin Bata Wanda zaiyi Mata tunda ciwon na jiri ne.

Subhanallh"NURU tace cikin damuwa da kulawa kafin ta miqe ta nufi hanyar dakin bayan ta kalli farhat dake maqale da ita tacewa ammi ga farhat Nan su gaisa
Ammin tajawota ta Dora kan cinyarta tana tambayarta tana lafiya?

Tana Isa dakin tashiga Kai tsaye padima dataji zuwan NURUn tasake sassake jiki tana maqale murya tareda qaro nishin ciwonda babusa hadda hawayen da tun safe suka kasa tsaya Mata na abinda ya tsaya ya danne zuciyarta.

Da sauri NURU ta qaraso bakin gadon tana kamo padiman tana Kiran sunanta cikin tsananin kulawa Tama dungumota gabaki daya tana cewa"

Padima meya sameki bayan yau Ina cikin tsananin farin cikin ganinku ku duka.

Marairaicewa padima tayi itama tana rungumo NURUn cikin muryar datayi laushi ta ciwo tace"

NURU nayi tsananin kewarki wadda bantaba sanin haka nake kaunarkiba Saida Kika tafi nakasa nutsuwar zuciya,
Wlh NURU nayi kewarki fiyeda zato ga amed ya yaudareni yace yafasa aurena Amma tsoro yahani fadawasu abal Wanda hakan yasa suka tsangwameni"""kuka tasake Mara karfi sosai tana sake shigewa jikin NURUn tace"

Nidai NURU bansan ya zanyiba mutuwa kawai nakeson Yi sbd itace daidaini,
Dan Allah NURU ki yafemun abinda nayi Miki wlh nayi nadama tunda gashinan Naga ishara irin wadda bantaba tsammani ba.

Cikin mamaki NURU ta share Mata hawayenta tana cewa"

Kidaina kuka padima duk wannan yariga ya wuce Kuma shi amed kansa yayiwa sbd Allah zaibaki Wanda yafisa Inshallah idan har kin tsarkake zuciyarki.

Wasu sabbin hawaye tasaki tana satar kallon kofa tace"

NURU bazan taba daina kukaba sbd kuka yaganni.

Da tausayawa NURU tace"

Kidaina fadar hakan padima.

Padiman zatayi mgn saiga amminsu tashigo wadda takasa zama Jin sun Dade aciki tsaf hankalinsu Bai kwanta da kebewar NURU da padima ba Dan haka Bata Bari padima tasake mgn ba ta janye NURU suka fito inda ta zauna tsakiyar iyayenta suna sake zantawa Kamar kadasu tafi goben jintake Kamar tabisu kosu bita musamman Meryam wadda takeda burin dauka duk tayi aure Amma yanzu Kam ko ita Bata gama tantance matsayintaba bare harta dauko wani ya zauna a qarqashinta.

Saida jekadi taga lokacin kaita gurin maleek yayi tashigo ciki ta sanar musu tayi bankwana da iyayenta bayan anshigo da tarin kayan arziki anjere musu daga Kaleeb da Anneti sai babbar kyautar MALEEK wadda ko ciki baa shigo da itaba saidai idan sun Isa gida akai musu.

Dazata fice harda hawayenta padima ta riqo hannunta tana hawaye qasa qasa tace"

NURU ki taimakeni Banda lafiya mutuwa zanyi idan Ba'a nemamin magani ba ciwon zuciya me qarfi nake fama dashi tunda dadewa kullum bana iya bacci ki taimakeni ki tafi Dani ki nemamin magani NURU.

Kallonta NURU tayi a Dan tsorace tace"

Tun yaushe padima shine Baki fadaba idan yayi tsanani wani Abu yasameki fa?

Kallon abal tayi cikin damuwa da kulawa tace"

Abal meyasa ba'a fadamunba ko a wayane da anfadawa jekadi ta fadamun ta waya wannan ciwon ba abun Wasa bane zantambaya afia Inshallah zamu tafi da padima.

Wani mugun kallo ammi tayiwa padiman data bushe idonta ba wani alamar qarya ko yaudara atareda ita abal ya hade fuska tsaf yace"

Kije NURU Allah ya albarkaci rayuwar aurenki ya Hana duk wani Wanda beda fatan alkhairi sa'ar rabarki,
Padima bazata bikiba kowane irin ciwone zamu nema Mata magani Inshallah.

Kallon padima NURU tayi tana Bata hakuri ta ido da cewa tayi hkr Inshallah ta Mata alqawarin dawo da ita hannunta ta nema Mata lafiya idan nasu abal din baiyiba.
Da haka aka wuce da ita tabarsu suna binta da addua suka wuce ciki Babu Wanda yaceda padima dake tsaye idanuwanta sunyi jajir zuciyarta na wani irin zafi da harbawa.

Kai tsaye sashensu datake dasu afia aka maidata sbd saqon maleek daya Isa gurin jekadi ta hanyar Anneti cewar basai ankar NURU gurinsaba yau din gobe zasu koma,
Tana Isa ta tarar da Afia zaune tagama hada musu kayansu tsaf sbd suma dad ya sanar cewa gobe zasu koma dama amatse take dasu bar Nan din sukoma Kota samu kanta tayi tunanin abinda yakamata.

Tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon afia da duk damuwa da sanyin jiki ya bayyana atareda ita taji tausayinsu su duka ya dawo Mata sbd tafi kowa sanin burin afia akan dawo da mahaifiyarta gidan MALEEK gashi yanxu su duka qaddara ta bullo musu ta inda basa zato.

Qamshin NURUn daya cika gurin yasata dagowa sukai ido biyu kowa yakasa motsawa suka tsurawa juna ido kafin Afia ta taso ahankali ta qaraso gaban NURUn ga mamakinta saitaji afia din ta rumgumeta tana cewa"

Thank God you're back NURU nayi kewarki.

Mamaki yasata daskarewa batareda tace komaiba ko motsawa.

Afia kuwa tarigada tasan zaman aure ko rayuwar aure tsakanin NURU da dad dinta bamai yiyuwa bane har abada Dan haka Bata sawa ranta damuwaba Dan duk duniya Babu Wadda dad dinta zaiso idan ba mum dintaba Dan haka tasan shima idan har aka koma Babu wani maganar aure dazaibi hakama NURU tana komawa Imran yadawo bazata yarda ba Imran zataso komawa Dan haka ta daure tacire damuwar komai aranta.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN qNUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899
*_Mamuhgee 22_*
Washe gari tunda safe sakon Anneti na gayyatarsu cin abincin safe tareda ita ya iso musu suka shirya dukkaninsu itadai jekadi dama tunda safe tazo da kayanda NURU zata saka tana Palo takasa ta tsare Dan kuwa komai daya danganci NURU yanxu saiya biyo ta gurinta kafin ya isa gun NURUn.
Da kanta tashirya farhat kafin itama ta shirya cikin doguwar royal gown dinsu me adon golden stones da sequence rigar ta tafine straight shiyasa ta fidda shape din tudun qirjinta zuwa shafaffen cikin har fadin hips dinta saidai adon sequence ne ya 'dan boye bayyanar shape din nata Sosai Sosai Amma duk da hakan yafito sai wuyan rigar dakeda Fadi sosai ta Sanya qaramar siririyar sarkar gold ta doro gyalen rigar akanta ta rufe gashinta dake daure Yana qamshin turaren hayaqin da akai Masa ta fito afia nabinta da kallon yaba kyawun datai Wanda duk be daga Mata hankaliba tunda dai duk abanxane suka fito jekadi na bayan NURU sai sauran masu Binsu suna bayansu kawunansu duk a soke kasa.

Afia ce ke kokarin janta da firar karatunsu da tun shekaran jiya yakamata su koma Amma Basu komaba itama NURUn abin sai lokacin yafado Mata musamman da tafara zuwa Court itama afian tana zuwa asibiti sama sama sbd karatun nasu.
Tun kan su qaraso aka sanarda zuwansu suna isowa suka tararda askarawan maleek kusan guda shida a sassan Anneti din afia na gani tasan dad dinsu na ciki ita Kam NURU batasaniba tunda Babu abinda tasani anan din Dan haka Babu tunanin komai dayazo Mata suna isowa aka wangale musu qofa Ana yiwa NURU gaisuwa ta musamman kafin aka juyo akaiwa AFIA da farhat suka shige.

Suna shiga palon farko duka sauran Yan rakiyarsu suka tsaya anan dagasu se jekadi suka wuce har cikin asalin palon hutawar Anneti suna shiga jekadi ta zube qasa cikin bada girma tace"

Allah yaqara MALEEK kyakkyawar zuciya data fuska,barka da fitowa.

Da hannu kawai ya amsa tareda juyowa Jin muryar AFIA na gaishesa cikin girmamawa itama.
Farhat kuwa kusadashi ta zauna tareda riqe hannunsa tana cewa"

Good morning Daddy.

Da sauri jekadi ta Raba gefen NURU data kusan sanqamewa a tsaye sbd shammatarta da abin yayi Sam ko kadan ko qamshinsa batajiba batama taba saka ran zata ganshi ananba.

Kallon afia yayi da idanuwansa masu haske cikin sautinsa na kamewa ya amsa Mata tareda cewa"

Kuna lafiya?

Gyada Kai tayi tana cewa"

Yes Inshallah.

Ahankali NURU ta tako ta qaraso ciki ta tsaya ta gefen NURU cikin sanyin murya batareda ta kallesa ba kanta na 'dan qasa tace"

Barka da fitowa.

Tsit gurin yayi kafin ya dago ahankali itama ya kalleta Wanda yayi daidai da fitowar Anneti tasaki murmushin ganinsu ta nufi hanyar dining room tana cewa"

Farhat zo ahau table cin abinci Afia zokiyi serving Dina.

Dan kallon NURU afia tayi ta sauke idanuwanta akan budaddiyar gaban rigarta daya bude sosai Dan idan har ba shedan ne yake Mata gixoba tana hango saman nonuwar NURUn kadan ta juya ta wuce tana Dan waiwayowa harta shige dama farhat ita tuni tashige.

Dauke idonsa yayi daga kanta tareda Miqewa baice komaiba ya wuce ciki.

Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd idan har akwai abinda yafi takura da firgici tashiga sbd taji idanuwa akanta saidai Babu tabbacin nasane Kona afia.

Kokarin zama takeyi taji Anneti takira sunanta tafasa ta nufi hanyar dining room din a sukwane tana Dan sauke Kai tana shiga Anneti ta nuna Mata kusada ita ta qaraso ta zauna kirjinta na bugawa sosai sbd duk wannan abin wani iri takejinsa Yana Mata nauyi sbd zuwan komai lokaci daya.

Afia ce tayi serving kowa Nan suka hau cin abincin Babu me mgn musamman itadai gabaki daya bataci abinda ya wuce Loma hudu ba sbd amatuqar takure take.

Maleek ne yafara tashi ya fice kafin Anneti saisu daga baya suna fitowa tuni aka fitarda komai na tafiyarsu suka dunguma zuwa ainihin fadar NEGES inda yayiwa NURU kallon tsaf kafin ya kalli MALEEK Dan kuwa yatabbatarda NURU bazatayima sa'ar afia ba Amma maleek ya aureta.
Yanaga Dole akwai dalilin dayasa MALEEK auren wannan yarinyar wadda akace asalinta ma 'yar bawan kaleeb ne,
Idan har da akwai dalili saiya bincika yaji Dan kuwa wannan karon bazai dagawa MALEEK qafaba Dan Bai shirya sauka mulkiba ya bawa MALEEK kujerarsa Dan haka zai binciki asalin

Please Login or Register in order to submit comment