Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

negestati yatafi da ita inda yake kafin yafara nazari da duban inda zai samo Masa matarda duniya zata shaida UBAYD MALEEK yayi matarda ko indatake akace matarsa lailah data watsa Masa qasa a ido ta kalla tasan tayi babban kuskurenda har abada bazai gyaruba.
A jiya 'daya daga cikin amintaccin bayinsa da tun iayayensu nada rai sukai Masa bauta yai tunanin yonas Wanda cikin wainda aka bawa sauyin 'yanci shikadai ne me 'ya mace wadda zataso amatsayin negestati.....
wani irin numfashi ya sauke ahankali Yana gyara kishingidarsa akan qatuwar shimfidar babbar dardduma me tsananin laushi dayayi sallah bai tashiba Yana adhkar ya numfasa tareda daukar wayarsa dake gefensa ya Kira numbern daza'ayo Masa Kiran tsohuwar jakadiyar marigayiyar matarsa.

Cikin qanqanin lokaci saigata ta iso akai Mata iso tana shigowa ta zube qasa tana kwasar gaisuwa batareda ya dagoba cikin wani irin iko na tsohon sarki yace"

Akwai sabuwar sauyin 'yancin bawai ta negestati 'ya daga wajen bawa yonas 'dan tsohon amintaccen bawana ilyas gasasshiyar tabbarwa nakeso Kuma a sirrance zancen zaizama kije kidubota da kanki ki tabbatarda igancinta idan ta isa ta zamo wadda UBAYD MALEEK zai iya hada shimfida da ita wadda zai iya tafiya da ita can qasar dayake kafin asamo wadda zata maye gurbin igiyoyin aurensa idan yarinyar Bata kaiba atara bayi Mata azabi wadda tafi tsohuwar matarsa komai a killaceta anan cikin delah afara kulawa da ita Ana Bata gyara kafin zuwansa yatafi da ita kokuma kafin na aika Masa da ita.

Angama Kaleeb me delah me gizah.

Juyawa tayi da hanzari Dan zuwa cika umarninsa cikin sauti me amo taji yace"

Babu Wanda zaisan ubayd maleek ya rabu da matarsa hakama babu Wanda zaisan negestatin ta ubayd maleek ce.

Da saurin ta zube qasa cikin girmamawa da tabbarwa tace"

Duk ranarda wannan zancen yafita ta hanyata na bada kaina acire fansar cin amanar danayi.

Jinjina Mata Kai yayi ta miqe tafice tana sake basa gaisuwa.



*************
Zaune suke jigum jigum fuskokinsu cikeda damuwa da baqin ciki Babu me iya mgn se sautin kukan padima dake fita ahankali ahankali tana roqon abal da ummi dasu yafe Mata tsautsayi ne.

Cikin nauyin zuciya abal ya dago ya kalleta da idanuwansa dasukai jajir kafin ya kalli ummin da ita shita kalla da idanuwanta dake cikowa da hawaye tana maidawa sbd batason zubarwada padima hawaye kada Allah ya kamata da laifin sakasu zubda hawaye abin yamata yawa,
Fahimtar abinda abal ke nufi da kallon dayai Mata yasa ta bude Baki daqyar cikin nauyin nurya data toshe da baqin ciki tace"

Padima mune iyayenki da bazamu taba zabar Miki abinda zai cutatar dake Dan haka kiji tsoron Allah kifada gskiar abinda yake faruwa,
Nice na haifeku duk ku duka Kuma nasan halin kowannenku fiyeda ku kanku tun ranarda akai maganar badake delah zuciyarki Bata amintaba Kuma shine dalilin dayasa Kika Hana kanki sukuni koba haka ba???

Tsit tayi tana Dan share hawayenta cikin jin tsoron anfara ganota takasa dago Kai ta kalli kowa cikin tsananin fushi da baqin ciki abal yace"

Hakane koba haka ba?

A kidime cikin tsoro tace"

Eh Hakane.

Dukkaninsu wani sabon baqin cikine ya turniqesu musamman NURU da hawayenta suka fara gangarowa.

A qyamace ummi tasake jefa Mata kallon baqin ciki tace"

Sbd baqyason abadake delah shiyasa jika bawa wani kanki yayi Miki ciki sbd ki nuna bamu isa dakeba duniyar dakikeso ita Kika saka gaba....

Da sauri ta girgiza Kai tana fashewa da kuka tace"

Ummi kuyi hakuri wlh banda ciki Amma..Amma...Amma tsoron hukuncin kasheku danima idan naje delah aka....aka..aka gano...yasa nace inada ciki sbd NURU ta yarda taje ta yanda Babu abinda zaisamu kowa wlh ummi sharrin shedan ne Kuma....

Wani wawan gigitaccen Mari abal ya sauke Mata guda biyu Wanda yasata zubewa kwance tana hadiye sauran maganar cikin tsananin tashin hankali sbd yaune karo na farko da aka taba lafiyar jikinta.

Kasa mgn ummi tayi sai hawaye sbd sunkasa riquwa yanxu Kam,
Cikin baqin ciki abal yace"

Sbd son ranki Kika siyarda mutuncinki,
Kika ringa wasa da amfani da qaunarda 'yar uwarki ke Miki harkina qarya da zance me girma na cewar kinada ciki Dan kawai bakyaso.
Kinyiwa kanki padima,
Kinyiwa rayuwarki,
Ban Miki bakiba Amma wannan abinda kikai shine babban kuskure mafi girma dazakiyi danasani akansa Amma tunda ke Kika zaba hakan 'yar uwarki zataje delah kekuma idan kingama tsare tsaren burikan naki amed din yafito zanmuku aure dashi Allah yabawa kowa alkhairinda yake fata.

Miqewa yayi Rai bace ya fice yabar gidan ummi ma qala batace Mata ba ta miqewarta meryam na riqeda hannunta.
Ba kunya padima ta tashi zaune tana share hawaye duk fushinda za'ayi tasan kowa zai sauko itadai tunda buqata tabiya angama me wahalar.
Kallon NURU tayi zatai mgn NURUn ta miqe batareda ta kalletaba zuciyarta na Mata zafi da radadin abinda padima tai Mata baqin ciki goma da ashirin ga tafiya delah ga abinda padima tayi ita rayuwartama ta ruguje gabaki dayanta sbd shikenan ta tabbata batada rabon zama acikin igiyoyin aure idan taje delah tariga tazama negestati idan ba Allah ne yayi Mata raboba tasamu damar shiga inuwar aure.

Gabaki daya gidan rikicewa yayi Babu me farin ciki bare walwala tundaga ranar sai padima data bushe ido tasakewarta da walwalarta da komai tunda buqatarta tabiya kowama yayita baqin cikinsa duk zasu dawo daidai idan komai yasake wucewa.

NURU ta sauya sosai gabaki daya yanxu batada walwala kullum cikin damuwa da tunani take idanuwanta harsum bushe da kukan tayi tayi tagaji harta daina saidai ido.

Ranarda jekadiyar Kaleb tazo duba NURUn tayi Mata kallo harna qurulla take tagama tabbatarda NURUn itace mafi cancantuwa Nan take takaiwa Kaleb rahoto yabada umarnin afara gyaranta tun agidansu kafin kwanakin daukota su cika.

Al'amari yadawo sabo sbd irin zarya da matakan tsaro da bayin da aka kawo aka zuba a gidan yasa al'amarin yafara bawa kowa tsoro da mamaki itadai padima ko ajikinta matsuwartama ayi ayi agama NURUn ta tafi sbd tsoron karma wani abu ya gitta aqara dawoda abun kanta.

Hankalin iyayensu yafara tashine sbd tunanin wannan tsananta tsaron da matakan dasukai yawa da wuya idanba gizah za'a Kai NURU ba sbd sai 'da mafi kusanci da sarauta akewa irin wannan taka tsantsan din Amma dai Babu iko ko hurumin tambaya.

Cikin kwana goma sha daya dukkanin Wanda yayiwa NURU kallo daya baya sakewa a qaidance idan ba hakaba hukunci zai hau kansa sbd wani irin sauyi me yawa datayi,
Fatarta ta sauya fiyeda tsammani,
Haskenta ya ninku komai nata santsi yake musamman gashinta dako dankwali baya zama sbd tsantsi ga sutura ta alfarma da aka kawo daga Kaleb Kai tsaye a sirrance.

Ayau tun safiyar jiya take kuka har idanuwanta basa iya gani sosai sbd yaune ranar tarewarta/ma'ana tafiyarta,
Ammi da abal kwana sukai Bata nasihu da rarrashinta ita ammin ma Kamar yanda NURUn ke kuka hake takeyi Daren farko lafiyayyun motaci biyar sukazo daukeda dukiya da abinci tareda sitiru na alfarma wa iyayen negestatin kafin aka dauketa a sirrance tareda mahaifinta yakarata yakaita har gaban Kaleb Wanda yasake narkawa abal din dukiyar tukaici rakiya aka nufi wani kebantattcen sashe na musamman daya gama hada jin dadin duniya da NURUn tareda sabbin masu kula da ita su shida cif cif ha'di da jekadiyar Kaleb Wanda ke sake yaba zabinsu na NURUn.
##MAMUH#

*Last free page*

_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899
*_Mamuhgee 6_*
Gyara kwanciya tayi ahankali cikin sanyin jiki da rashin kuzarin daya mamayeta na kukan datun jiya da aka kawota ta kwana tanayinsa.
Juyar dakai tayi daga kallon makeken dakin baccin ma'ana bedroom dinda take Wanda ita kaf rayuwarta da tunaninta dama irin labare labaren da padima ke fada Mata akan akwai daula da jin dadin rayuwa tareda qyale qyalin rayuwa Bata taba ayyano tunanin ganinsu Kamar hakaba abin ya shallake tunaninta musamman da tun jiyan sanyin AC ke shigarta a hankali Saida 'dayar me aikinta data shigo dubata cikin dare taga yanda ta qudundune ta bude Mata qaton duvet me tsananin laushi da Sanya nutsuwa ta lulluba Mata batamasan lokacinda tasake shigewa cikinsaba tana gyara kwanciya sbd sanyin yayi Mata yawa ga tsoron baqunta na kwanciya daki ita daya.

Jin akaro na biyu ansake kwankwasa Mata qofa Ana sake sanar da ita anagama shirya Mata abinci yasa ta tashi zaune tareda miqewa ta nufi qofar qafafunta na rawa murya na rawa cikin sanyi tace"

Ganinan zuwa.

Bayi Takoma akaro na babu adadi tana sake kakkala ko Ina batasan Yaya zatai tayi wanka ba gabaki daya a firgice take ita yanzu ta daina kallon wasu abubuwan na masu daula amatsayin Jin dadin rayuwa sai abun tsoro.

Jin shiru da yawa yasa jekadiyar Kaleb shigowa bedroom din Kai tsaye ta duba makeken gadon Wanda yake zagaye da wani irin transparent labule fari tas taga Bata hango daga ciki kan gadon saita juya tana kallon qofar toilet ta qaraso ahankali takira sunanta.

Jin jekadi ce yasata fitowa a sanyaye tana kallon qasa ta tsaya daga bakin qofar bayin.
Kai tsaye jekadiyar ta fahimci komai dama Kuma daga yau ne za'a fara kokkoyawa NURUn komai hatta kwanciya sai ankoya Mata.

Shiga bayin tayi tana cewa"
Biyoni kigani.

Shiga sukayi bayin tafara nunnuna Mata komai daya bayan daya tareda fidda sabbin setin brush masu tsadar gaske da toothpaste Suma kala kala sai towels da aka jere Suma kusan sunfi guda biyar bangaren kayan wanka kuwa su sabulu da turaren wanka ba'ama magana Nan dai ta tayata komai har kusan wankanma ita tayi Mata Saida suka gama tafito NURUn tasake dauraye jikinta tafito daureda towel dinda yafi kowanne girma shima kusan daqyar ta daurosa kallo daya jekadi tai Mata ta dauke Kai tana sake yabawa da jinjinawa tunanin kaleeb na karbanwa UBAYD MALEEK yarinya 'danya sharaf sa'ar 'yarsa Kamar wannan tabbas za'aga 'yaya masu manyan idanuwa da hanci Dan kuwa NURUn tubarkallah uwa uba UBAYD din da shikam idan shima 'yayan zasu dauko angama magana.

Da kanta ta tsaya tana sake nunnunawa NURUn wasu abubuwan na dangane da shafa da qamshi da sauransu hardai ta shiryata cikin doguwar Bahrain gown blue wadda tasake haskota ta nada Mata gyalen take tayi fes kamar ba NURUn abal ba suka fito tana biyeda jekadi Kamar jela suka fito babban matsakaicin palonta suka nufa inda aka jere Mata abincin sai alokacin hanjinta sukai wani qugin yunwa Dan rabonta da abinci dama tun jiya da a gida ammi tai Mata dole ya Dan ci sbd cushewar ciki da damuwa.

Zama tayi Nan daya daga cikin bayinta tazo ta zuzzuba Mata komai nanma Saida jekadi ta nuna Mata amfanin kowane cokali duk da Bata iyaci dacokali ba tanada nutsuwar cin abinci tun agida kowa yasanta a natse take gudanarda komai na rayuwarta Wanda zaisa Kai tsaye bazaka gane batasan komaiba na wayayyi ko wayayyiyar rayuwa.
Ba laifi taci abincin sosai sbd tana jin matauqar yunwa gashi Kuma bazatace ta taba cin abinci irin wannan ba.
Bayan tagama cin abincin janta jekadi tayi aka sake kimtsata suka nufi gurin Kaleb Dan Kai gaisuwar safe dakuma Kai godiya da zaben dayayiwa NURUn Wanda jekadi a hanya take fada Mata yanda zatayi da yanda zatace.

Suna Isa Saida sukai tsayuwar kusan mintuna talatin kafin akai musu iso suka shiga bangaren tun daga qofar farko NURU ke kallon aljannar duniya danma ba halin bude ido sosai tayi sbd dokace babu Wanda ake Bari yakalli fuskar negestati batareda NEGES dinta yafara ganinta ba bare ita datake ta MALEEK guda shiyasa kusan fiyeda Rabin fuskarta rufe yake cikin burka(hular doguwar rigar dake jikinta)

Duk tarin qofofin Palo palon dasuka wuce akwai masu tsaronsu harsuka Kai wadda tafi kowacce zama babba da tsaro
Nanma Saida akai musu iso tukuna aka bude musu suka shiga aka rufo.

Zubewa jekadi tayi tana kwasar gaisuwa cikin tsananin girmamawa da ladabi.
A natse itama NURUn ta durqusa qasa kanta na qasa ta yaye fuskarta cikin sanyin da nutsuwarta ta gaidashi batareda tayi Masa kirarin dataji jekadi nata jerowaba sbd Bata iyaba.

Kallo 'daya yayiwa NURUn ya tabbatarda nutsuwarta ya dauke Kai Yana amsa gaisuwarsu tareda Basu izinin miqewa.

Basu wani jimaba suka fito zuwa sashe sashe na cikin delah din Wanda wani sashen a mota suka jejje sbd nisa da girman DELAH din,
Ayau ta tabbatarda arziki ma Ashe na wani sunane Dan kuwa taga inda arziki yake magana,
Tabbas delah wani Depot ne na arziki Dan idanuwanta da tunaninta sunkasa daukar wasu abubuwan data gani ahakanma akecewa gizah ta dame delah tabbas idan mutum beyi da gaskeba a irin Nan tsaf imaninsa zai barsa sbd kwadayin dawwama acikin irin wannan daula ta mulki.

Sai magriba suka samu damar dawowa sashenta duk da haka bawai koina suka samu zuwaba Kai gaisuwa saidai duk inda sukaje babu Wanda yaga fuskarta andai tabbarmusu da sabuwar negestati ce.
Tarin tukuicin dukiyar data samu ayau din Bata bayyanuwa danma asalin tukuicin na tafe ne ranarda za'a tabbatarda budurcinta delah ta sheda.

Kallon uban dukiyar zinarai da situru tayi tana rintse idanuwanta cikin tsananin azabar gajiya Dan qafafuwanta har wani numfashin azaba sukeyi daqyar ta miqe ta daddafa tashiga toilet tayi wanka ta gasa qafafuwanta tana tsiyayar hawayen tausayin kanta da kewar iyayenta itafa shikenan yanxu haka zataita rayuwa daga ita sai bayi sai idan neges dinda take tasa ya buqaci ganinta a turakarsa.

Tunanin hakan yasa kukanta tsananta tafara kuka sosai cikin bayin tana cusa kana cikin qafafunta Dan zaune take cikin bathtub.
Da kanta ta rarrashi kanta tasake dauraye jikinta tayi alwala tafito tazo daqyar ta tsaya akan qafafunta tayi sallolin da duk basuyiba yau din tana idarwa da kanta ta sidado ta fito cin abinci da yunwama Kamar ta kusa kasheta.
Tana zama dakanta ta zuba abincin sbd duk basanan suna gurin sallah Suma Dan Suma Kam sun gaji hannu tasaka Bata tsaya saka wani cokaliba kadanma taci sbd cikinta daya qulle tasha lemun sabuwar abarba ta miqe ta nufi daki tana shiga ta kwanta kife take baccin wahala yayi gaba da ita.


Washe gari ma yini tayi daki kwance abinci kawai ke fiddo da ita Palo har dare bataga jekadi ba sai washe gari da yamma tazo bayan ta tabbatarda NURUn ta huta daga wahalar shekaran jiyan kafin suka fara gudanarda aikin dake gabansu.

Sannu ahankali jekadi take koyarda ita komai na al'amuran rayuwar gidan sarautarsu ta delah,
Duk wani abu dayakamata NURUn ta sani Kuma ta iya Ana kan koya matashi Kuma tana 'dan ganewa duk da hankalinta tashi yake idan Ana fada Mata wasu abubuwan ko koya Mata sbd batasan ta Yaya zata gudanar da rayuwarta ahakan ba,

Ta bangaren iyayenta kuwa tuni ta aika musu da dukkanin tarin dukiyar tukuicin data samu.
Ga kaleeb ta bangare daya kullum saita je takai Masa gaisuwa Wanda jekadi ce ta 'dorata akan hakan bawai Dan al'ada bace kawai tanason Gina qauna me qarfi ne tsakanin NURUn da kaleeb sbd sanin irin tsananin qauna dake tsakanin Kaleb da UBAYD MALEEK.

Sannu ahankali tafara sabawa da rayuwar delah ga jekadi ma data Dan shaqu da ita sbd tana Mata kallon uwa kokuma tacema Kaka musamman sbd itama jekadin tsakani da Allah taji tana qaunar NURUn sbd nutsuwa da biyayyarta ga rashin son hayaniya sai hakan kesake saka Mata nutsuwa da shigar NURUn rayuwar UBAYD koba komai UBAYD Kamar 'dane agareta sbd agabanta aka haifesa yagirma.

Tsawon watanta biyu a delah Amma haryanxu ko a zance bataji maganar waye aka bada ita gurinsaba,yaushe za'a kaita,Ina yake haryanxu shiru duk bataji komaiba Abu daya tasani shine jekadi ta fada Mata wata me kamawa za'a kaita wani guri.
Da farko hankalinta ya tashi Jin tafiya wani guri Amma sai jekadi tafara kwantar mata da hankali da cewar zasu dawo bawai zaman dindin bane itadai Sam hankalinta yakasa kwanciya ko bacci yanzu kasawa takeyi saitajin Kamar rabuwa zatai da gida har abada.

Ganin kwana biyu har wata rama ta sakota gaba da tunani da damuwa yasa jekadi takwai Kaleb zancen sai tunani ya shegesa yace anfasa Kiran zuwan UBAYD sbd idan yazoma kowa zai San shi keda negestatin Kuma Kamar yanda akasan MALEEK da ikonsa bazai taba karban negestati ba matuqar ba baya tareda matarsaba hakan zaisa afara tunanin sun rabu Wanda za'a iya amfani da wannan gurin muguwar manaqisar mulki akawo suka ga karban mulkinsa Wanda keleb bazai taba Bari hakan tafaru ba yafison koda za'a San ubayd da matarsa sun rabu zuwa lokacin sun samu wata Matar aure kawai za'a daura idanba hakaba da matsala babba Dan haka yasa aka matso da tafiyar NURUn tareda Bata damar izinin zuwa ganin iyayenta da daddaren yau.


Qatuwar baqar Mercedes Benz beymach ta ajiyeta gefen gidansu da qarfe goma sha biyu na dare Wanda shine lokacin barinsu fita delah tana kallon qofar gidansu jikinta yayi mugun sanyi taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta ziro qafarta waje ahankali tareda fitowa.
Kai tsaye itace agaba jekadi na gefenta tana cewa"

Karkiyi kuka gaban iyayenki Zaki daga musu hankali Kuma laifine babba yin kuka was umarnin masarauta Dan haka ki kula.

Batace komaiba itadai burinta ta Isa cikin gidan taga ahalinta cikin sa'a kuwa har lokacin abal dinta da ammi na zaune tsakar gidan kan shimfida suna Shan iska sbd tsananin zafin da akeyi yau din meryam ma na kwance gefen ammi tayi bacci ammin na Mata fitar sauro.

Da budaddiyar murya jekadi ta rangado sallamar da har maqota anaji sbd asan da zuwan NEGESTATI ne.

Da ammin da abal lokaci daya suka miqe suna kallon qofar dasu NURUn ke shigowa wadda qamshinta tuni yafara cika tsakar gidan da hanzari ta qaraso ta fada jikin ammi tana riqo hannun abal duk alokaci daya tana sake hawayen farin cikin ganinsu batareda ta iya cewa komaiba.

Cikin tsananin farin ciki ammi ke Mata yare tana cewa"

Ya Allah NURU munyi kewarki matuqa.

Murmushin farin ciki kawai abal ke saki Yana kallonta ta cikin hasken farin wata Yana sake godewa Allah daya bashi ikon ganin 'yarsa 'daya tasamu gidan zamanta na rayuwa saura daya itama Yana fatan Allah yabasa ikon ganin yayi Mata aure ta tafi nata gidan.

Zama sukai tana tsakiyar iyayenta Meryam ma tuni NURUn ta tayarda ita sbd bazata iya tafiya basui mgn ba tana ganin NURUnta tafada jikinta da qarfi tana ihun murna Wanda ya tado da gimbiyar gidan wato padima ta fito cikin wani irin laushi tana jujjuya ido ta bude da kyau tana kallon mutanen idanuwanta suka sauka kan NURU tasake dubawa dakyau taga NURU ce da sauri ta qaraso tana cewa"

NURU????
Kece yanxu?

Dagowa NURUn tayi fuskarta daukeda murmushin kewar padiman ta taso suka rungume juna tana cewa"

Nayi kewar dukkaninku padima.

Zaman sukayi padiman nabinta da wani kallon kurulla da zallar mamaki tanson yin tunanin fahimatar wani abu kanta Yana toshewa da mamaki dakuma tausayi tausayin NURUn da rayuwarta ta lalace.

Shagala sukai sosai harsaida lokaci yaja jekadi tashigo da cewar zasu tafi Nan jikinsu duka yayi sanyi Amma hakanan suka bawa NURU qwarin gwiwa abal yabita da wasu irin adduoin Sanya albarka masu zafi wainda suka Sanya jikin kowa yin sanyi suna amsawa da Amin.

Har mota suka rakota tashiga padima sai kallon komai take cikin mamaki tana qaryata abinda idanuwanta ke gane Mata sbd tasan ba komai bane duk wannan akan irin rayuwar da ita zatayi a Nan gaba.

NURU kuwa Har suka Isa delah tunaninta bai daina zurfafaba gabaki daya yanzu kanta a toshe yake sai yanda akai da ita yanzu kenan.
Tana Isa sashenta daki ta wuce Kai tsaye ko tubewa bataiba ta kwanta tareda rintse ido.
Washe gari haka akai fita da ita zuwa gurin passport Wanda tun kafin su Isa aka tanadi komai babu Wanda yasamu damar ganin fuskarta sai Wanda ya dauka hotonta dagacan Kai tsaye delah suka dawo washe garima saida aka futa da ita zuwa wani gurin wanda acanma tasake tabbatarda mulki wani abune na daban sbd irin girman da ake Basu ko cikin ansan cewar bama daya daga cikin jinin sarautaceba ita din.

Ranarda ta cika kwana shida da zuwa gidansu ranar aka gama Shirin tafiyarta tsaf a washe gari itada jekadi jirginsu yabar Ethiopia zuwa qasar France.



***********
Breakfast sukeyi zaune su uku akan dining din Wanda suka kwana biyu Basu samu damar cin abinci tareda dad din nasuba sbd rashin zamansa a kwanakin sai yau,
Kallonsa AFIA tayi taga yanda yayi wani irin fresh fatarsa sai wani glowing takeyi tsabar hutu da arzikin dukiya duk da manyancinsa Amma Sam fatarsa taqi bayyana hakan idanma batai kuskure ba saitaga kamar bayan rabuwarsa da mum dinta wani nutsuwa yasamu.

Sake kallonsa tayi wannan karon suka hada ido ya zuba Mata manyan fararen idanuwansa cikin muryarsa me iko yace"

AFIA akwai wani abu ne?

Aje spoon din hannunta tayi ahankali tareda kallonsa gabaki daya cikin taushin murya da 'yar sakuwa tace"

Dad please for how long zamuyita zama haka mum Sarah kwanakin Nan batajin Dadi qafafunta sunfara gazawa Ina tsoron zamu koma rayuwa mu kadai dagani sai farhat sauran maids din babu wani kusanci ko shaquwa tsakaninmu dasu.

Ciki wani irin Isa ya kurba ruwan Black coffee dake cikin farin teacup din hannunsa ya ajiye tareda daukan tissue yakai bakinsa ya goge ahankali ya ajiye tukuna ya dago ya kalleta yaji zancenta ya taba zuciyarsa tabbas suna buqatan abokin zama kada kadaici yayi musu illah gasu yara qananu,
Sam baida sha'awar maidasu zama gizah gurin mahaifiyarsa sbd kada giyar sarauta da mulki ya shigesu Dan kuwa tabbas zai shigesu sbd girma da irin bauta musun daza'aitayi zai gurbata tunaninsu sarauta zatai musu muguwar shiga bazai taba son hakanba Dan haka a yanzu dai baida wani zabi bayan karban negestatin Kaleb Amma bazai taba Bari Susan da hakanba sbd bai karbetaba bakuma zai taba karbantaba zaidai kawo musu itane amatsayin abokiyar debe kewa.

Kallon afian yasake Yi tareda Dan sassauta fuskarsa batareda murmushin yafito dukaba yace"

Akwai abokiyar zama da debe kewa da Kaleb zai Aiko muku da ita ta musamman Dan haka karku damu damuwa ya qare ok??""yafada Yana shafa kan farhat dake kusa dashi tana cin pancakes da Zuma.

Cikin tsananin murna afia tace"

Dad daga delah ne za'a kawo Mana ita?

Gyada Mata Kai yayi cikin Jin dadin ganin farin ciki akan fuskarsu yace"

Yes my angels Dan haka kunada baquwa yanzu Dan haka no worries no sad face no complains.

Yes dady" farhat ta fada tana riqe hannunsa suka miqe tare suna barin dining din Dan yanzu haka yauma tafiya zaiyi zai Kwana biyu acan.

Har mota suka rakasa ya tafi dayake yau weekends ne ba school Yana wucewa suka dawo ciki cikin farin ciki sukaje suna fadawa mum Sarah sunada baquwa tananan zuwa.

Yana barin gida direct airport aka nufa dashi ya Jima Yana tunani kafin ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya lalubo numbern jekadin kakarsa wadda yasan itace maganar negestati take gurinta Kira daya tana ganin me Kira ta daga cikin tsananin girmamawa hadda durqusawa duk da ba agabansa takeba tahau jero gaisuwa Yana sauraronta kafin ya dakatar da ita ta hanyar amsawa a gajerance cikin nauyin murya kai tsaye yace tanason bayani akan negestatin Nan tahau jero Masa asalin NURU da sunanta dakomai akanta cikin gajiya da zancen ya katse Kai tsaye yace"

Kada su afia su taba sanin waccece ita da matsayin datazo dashi.

Angama MALEEK ubayd sarki me kujerar delah gizah.

Yana kashe wayar ya kasheta gabaki daya tareda ajiyewa Yana daukar iPad karanta wani saqo.
Suna Isa airport ba Bata lokaci yashiga jet suka daga.

Sukuma a washe garin aranar jirginsu ya sauka qasar Kai tsaye babbar mota tazo daga gidan daukarsu daga ita sai jekadi ne Dan haka suna isowa makeken gidan na UBAYD MALEEK aptrmt dukkanin masu aiki suka fito suna musu barka da zuwa akai ciki dasu suna shigowa babban palon gidan dayasa NURU Shan jinin jikinta sukai kicibis dasu afia dasuka fito tarbonsu afia na ganin NURU ta tsaya cak tana kallonta cikin yanayi na Jin dadin wannan ai qawace ma aka kawo Mata tasaki fuska sosai tana cewa"

Jekadi wannan ce wadda zata tayamu zaman?

Da sauri cikin girmamawa jekadi tace"

Eh ranki ya dade itace.

Jin haka farhat ta riqo hannun NURU tana cewa"

AFIA tanada kyau sosai kaman Barbie Dina ko???

NURU bayan zare ido Babu abinda takeyi tana kallonsu hankalinta nakan gidan Wanda yasa taji tsoron duniyama gabaki daya na shigarta.

Dakin mum Sarah jekadi tasauka itakuma NURU dakin AFIA afian tajata tana sake tambayar sunanta duk Dadi ya isheta sbd take taji tanason NURUn.
##MAMUH*
HASKE WRITERS.










_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa

Please Login or Register in order to submit comment