Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasoba tashiga ciki ta sauyo dankwalin kanta zuwa veil Mara datayi Rollin sai takalmi data sanyo loafers sabanin Afia datai ado bame yawaba itama kusan irin kayan NURU ne ajikinta suka fito suka wuce afian ce Agaba sai farhat da ita NURUn a baya wadda Sam ko kallon sosai bataiwa Imran ba bare ta lura da Yana Dan kallonta akai akai sbd gabaki daya ita bataso fitanba taso tsayawa tayi karatunta Dan yanzu data fara sanin kanshi da wayar karatun batada babban burin daya wuce samun ilimi me zurfi domin tsayuwa da kanta da iyayenta shiyasa yanzu kwata kwata batada lokacin batawa sbd karatu.

Duk wani yawo da tarin siyayyan da akayo a fitar basa kanta gida tamatsu su koma Dan haka harsuka gama yawon suka dawo bazatace ga takamaimai na kamannin Imran jalal ba Amma shikam yagama karanceta tsaf kaman yanda yake buqata musamman dayayi fira da farhat Sosai yagama fahimtar babban burin NURUn yanzu karatu ne sai hakan yasakashi farin ciki sbd dukkanin wannan na daya daga cikin abinda yake tsananin so ga irin matarda yake ra'ayi.

Ko kafin Monday karatunta tagama fahimatarsa sbd takuran data saka kanta ta saka afia Saida ta tayata bayani harta fahimta dakyau dakyau shiyasa Monday din harsuka je suka dawo cikin annashuwa take musamman data fara da samun yabo gurin Mrs Edward.

Imran jalal kuwa da zuciyarsa takasa hkr da rashin bawa kasa dama agurin NURU yasashi dawo da ziyarar daya Dade da daina kawowa gidan ahankali ahankali tun Bata wani bi takan sha'aninsa dasu afia harta fara sabawa dashin musamman akan karatun dayake dorata akai sosai Dan hakan sai sabo yashiga tsakaninsu duk da baitaba nuna wata alamar so atareda Shiba sbd yasan Basu Isa fara soyayyaba ayanzu tunda karatu ne agabansu sai sunshiga University Koda zasu fara bawa wata soyayya dama.

A bangare makaranta kuwa karatu tuni yadau hanyar nisa Dan kuwa yanzu tana farkon shiga aji uku ita kuwa Afia tana shirye shiryen zuwa _Las Vegas_ karatun shekara daya kafin tadawo tashiga University anan Paris dan haka sai suka Dan shiga damuwa sbd sunrigada sunyi wata irin shaquwa yanzu wadda Sam basa iya ko yini batareda junaba gashi zasuyi rabuwan shekara daya duk da zata ringa zuwa hutu.

Ranar dazata wuce tareda dad dinsu zata tafi Dan haka rakiyar NURU iyakacinta palon ciki Bata fito babban ba har suka wuce cikeda kewar juna.

Bayan tafiyan AFIA sai Kamar wani babban nauyi yahau kan NURU sbd yanzu itace shugabar gidan ita ke bada umarnin komai ta bangare daya ga karatunta ga kula da farhat wadda itama kewar afia ta tabata Amma kasancewar yanzu tamkar ma uwa take ganin NURU sai Bata wani jimaba cikin damuwan tafiyan AFIA din takomawarta Kiriniyarta.

Yau Kam amatuqar gajiye take sbd Suma sunfara shirye shiryen fara midterm exams Dan haka karatu take Babu sauqi ta Dan hakan tana dawowa daga school wanka tayi bayan ta tabbatarda farhat tayi baccin Rana sai itama Takoma daki tayi Mata wankan ta Sanya riga fara mara nauyi da dogon pencil jeans Wanda yakama siraran cinyoyinta tareda bayyana fadin hips dinta ta sanyo hular dabata rufe kanta dukaba ta fito taje kicin tasamu fresh milk me sanyi sosai Tasha tareda lumshe fararen idanuwanta dasuka gama galabaituwa da gajiya ta fito riqeda sauran madaran tazo Palo ta zauna tana daukan wayan afia data kirata suka fara waya tun tana sawa har bacci me Dadi yafara Dan fizgarta Dole sukabar wayar ko motsawa batai daga gurinba bacci me nauyi yayi gaba da ita a palon.

Farhat data tashi nata baccin tana fitowa palon taga NURU tayi bacci kan kujera ta kalla kyakkyawar fuskarta datai fresh sbd samun hutu da gyara saita saki murmushi tareda qarasowa zata gyara Mata kwanciya ganin kaman zata fado tana Dora hannunta akanta taji dirin motocin dad dinta yadawo cikeda farin ciki ta miqe ta nufo qofa da sauri ko ta bude tareda rumgumesa cikin qasa qasa da murya tace"

Welcome dady.

Kallonta yayi cikin kulawa da mamakin meya samu muryanta take magana ahankali
Duk da qarancin shekarunta ta dade da sanin dad dinsu ba komai yake budewa Baki yayi magana ba da kallo ma kawai suna gane maganarsa Dan haka ta fahimci mamakinsa tasakeyin qasa da murya cikin rada tace"

Dady Lewa na Palo and she's sleeping tagaji sosai da yawa koyaushe batada time din hutawa yanzu tasamu tayi bacci please dady kadamu tasheta.

Kallonta yayi suna qarasowa tsakiyar palon dan dama yasan tsawon shekarun Nan farhat Bata mgnar daya biyu saita lewa,my Lewa,my beauty kunnuwansa harsun gaji dajin sunan abakin farhat.

Dan juyi tayi daga kwancen ta sulmoyi zata fado da sauri farhat tayi kanta ta tareta Amma sbd NURUn tafita girma da nauyi saita kasa tareda saima danneta da NURUn tayi batasaniba sbd baccin yayi Mata nauyi sosai Dan tajima Bata baccin kirki Koda daddare.

Da sauri farhat ta kalli inda yake tsaye cak Yana kallon qanqanuwar yarinyar dabatafi AFIA shekaru da girman jiki da komaima.
Cikin wuya farhat tace"

Dady hannuna zai karye aunt NURU nada nauyi sosai.

Cikin wani irin taku da izzar data gama kame jininsa ya iso gurin batareda ya kalli NURUn ba ya Dan ranqwafo yakai dogayen hannuwansa masu siffar qarfi tareda tsananin taushi ya zura qarqashin bayan NURUn farhat tasamu damar janye hannunta tana yarfewa tayi dakinta da gudu tana cewa hannuna zai kumbura Bari nashafa ointment da sauri kada ya kumbura aunt NURU nada nauyi sosai.

Idanuwansa dake raunana kuzarin Wanda duk ya zubawa su ya waiwayo ya zubawa fuskar NURU wadda take wani glowing na zallar asalin kyawun da Allah yayi Mata.
Gangarowa yayi da kallonsa kadan zuwa jikinta a qirjinta ya dakatar da kallon tareda dauke fuska Yana zare hannuwansa daga qarqashinta yabar gurin sai ayau yasan babban shirmen da Kaleb ya tafka da jekadi kenan tsarar 'yar cikinsa suka kawo Masa amatsayin negestati,
Ta Yaya suke tunanin wannan yarinyar tsarar afia zai iya hada shimfida da ita?Tama Yaya zata iya daukan nauyinsa ko ciki baya tunanin kwsmkesonta zai iya dauka bare haihuwa... unbelievable" yafada cikin zuciyarsa a 'dan takaice sbd tunano 'yarsa afia dake tsararta baya tunanin ko Nanda shekara biyar zai aurar da ita Dan ganin kaman tayi mugun qanqanta amma shi ba saurayiba ko 'dan samari akawo Masa wannan.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899
*_MG 11_*
Sai magrib ta farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi sosai tana kallon inda take ta lumshe idanu tana sake tabbatarda tabbas ta gaji matuqa gabaki daya rayuwarta yanzu hutu takeso Dan hakan zata sassautawa kanta tunda dai karatun yanzu yazaunu a kanta.
Tashi tayi zaune tana shafa wuyanta dayayi Mata sakayau sbd yanayin yanda tayi kwanciyar.
A kasale ta miqe tayi ciki tana duba qaton agogon dake bangon palon ta shige palon ciki ta doshi hanyar bedroom dinsu tashige.

Saidayi sallah kafin tayi wanka ta Sanya doguwar riga Mara nauyi black me dogon hannun Kuma har qasa take komaima Bata sanyo akantaba ta fito ta nufi dakin farhat tana Kiran sunanta.

Zaune take tana homework NURUn ta shigo taqaraso kusa da ita ta zauna farhat din ta haye cinyarta tana cewa"

My Lewa dubamin kigani yayi daidai kuwa?

Murmushi NURU tayi tana karba tafara dubawa tana cewa"

Ni danasan farhat Dina nada kokari Babu homework da bazata iyayi daidai ba Amma dai yanzu kinajiye muje kici abinci tukuna daga baya a qarasa lokacin cin abinci yayi.

Kwantawa tayi jikin NURUn tana cewa"

Ni yau banason cin abinci cupcakes and pancakes nakeso cin zakimin ai ko my Lewa?

Kumatunta taja tana sake gyara Mata kwanciya ajikinta cikin tsananin qaunar farhat din tace"

Yes of course sweetie duk abinda kikeso shi zakici.

Ahankali ta sake lafewa jikin NURUn tana cewa"

I love you my Aunt NURU.

I love you too baby.

Tashi sukai NURU na cewa"

Muje cikin yanzu bada dadewaba chief NURU zatayiwa princess pan and cup cakes dinta duka.

Kicin suka nufa cikin murna farhat ke taya NURU aikin da surutu sbd Babu kowa yanxu acikin gidan Dan dama da angama abincin yamma tun 7 na yamma kowanne me aiki na gidan ke barin shashen sukoma sashen masu aiki musamman idan MALEEK na Nan to ita yau batamasan MALEEK din yadawoba Yana gidan.

Saidata gama hada cake din tasaka a oven tafara gasa pancakes din lokacin tuni tacewa farhat taje dining ta zauna gatanan kawowa yanzu.
Cikin farin ciki takeyin aikin daga can cikin kicin din ta Dan dago muryarta me sanyin dadin sauraro tace"

Sweetie kinajin qamshin cake din Nan kuwa daga Nan inda kike sbd I just added your favorite inib yanzu akai inason kina fara cinsa kunnuwanki suyita tsalle Suna gudu sbd Dadi.

Dariya farhat tasaki tana toshe Baki idanuwanta akan fuskan dad dinta daya Dade da samunta a dining din Dan lokacin dinner dinsa yayi.
Ahankali ya dan kallin hanyar qofan dazaikaika kitchen din saikuma ya dauke Kai tareda saka spoon akan lafiyayyan abincin dake gabansa Wanda yanzu Fana tagama serving dinsa ta fice daga sashen gabaki daya.

Kasa kasa da murya farhat tace"

Daddy ai zakaci pancakes dina sbd cakes din aunt NURU are the best
Idan kaci wannan kullum zakaso ka qara kaji Kuma tasaka inib oh oh daddy na matsu akawo.

Dan kallon farhat din yayi da fararen idanuwansa Yana iya ganin farin ciki me tarin yawa da nutsuwar rayuwa gashinan bayyane ko Ina atareda farhat din Wanda hakan yasa yaji wata nutsuwa tashigesa tabbas yaransa deserve the best life,
Yaran MALEEK guda na delah gizah sun cancanci kowane irin farin ciki na duniya dai sbd sune keda matsayinda kusan yafi na kowa a gizah sbd mahaifinsu shine asalin maleek na kujerar sarautar delah gizah Amma rashin dacen uwa Kamar Laila yabarsu da qarewa tamkar marayu gashi shikuma schedules dinsa na rayuwa sun hanashi lokacin zama tareda yaransa.
Amma koma dai menene tunda sunsamu kulawa daga wannan din hakan yamasa Dan kuwa yaransa na cikin walwala da farin ciki Kamar Basu taba shiga damuwan kewan iyayeba musamman AFIA tasamu 'yar uwar dataketa yiwa kanta mafarki da fatan asamu hakama farhat tasamu dukkanin soyayya da kulawan datafi buqata daga iyaye sbd qarancin shekarunta.

Dauke da kyakkyawan tray ta fito kitchen din ta nufo dining room tana
Cewa"

Sweetie are you ready??

Yessss ""farhat tafada da Dan qarfi cikin Jin Dadi da qaguwa.

Ok baby I'm coming ki tabbatarda yau kin rufe qofa da windows dinda kunnuwanki zasu gudu Dan kuwa yau hmmm.

Tana shigowa cikin dining room din tace"

Tadaaa.....cak ta dauke wuta ganin dadynsu farhat din a zaune da 'dan guntun mamakinsu akan fuskanshi sbd su biyun kawai sun cika gidan da hayaniyar datafi ta mutum goma..

Rawa qafafunta suka dauka sbd tsananin tsoro da firgicin data shiga saura kadan tasaki tray din farhat ta karba da sauri tana cewa"

Zaki zubar muyi wahalan banza fa.

Batama San me farhat ke cewa ba gabaki daya ta rude ta tsorota batasan abinyi ba sai kawai ta durqusa cikin rawar murya tace"

Barka da dawowa da fitowa.

Tsit gurin yayi sbd kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kayan dake jikinta da kanta dake bude
Itakuma tunda yau ta ritsu Babu damar wucewa batareda izininsa ba Dan hakan ta sauke Kai durqushe agurin.

Farhat ce ganin shiru shiru dad din nacin abincinsa hankali kwance yasata sauka kan dining din tazo gaban NURU ta kamo hannunta tana janta tashi tace"

Lewa Daddy ya amsa gaisuwanki kitaso muci cakes din kibani abaki na matsu nafara ci.

Dan zare hannunta tayi daga na farhat din tana sake saukar da Kai qasa Dan bada tsananin girmamawa ga zaman maleek dake gurin.

Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa cikin nutsuwa da kamewarsa ya bar gurin sbd yagama cin abincin dakuma hayaniyar dazata iya basa ciwon Kai tasu.

Yana barin gurin ta zube zaune gabaki daya tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana dagowa ahankali ta dan saci kallon bayansa ta sauke Kai da sauri tana dawo da kallonta kan fuskar farhat dake Jan hannunta,
Kyakkyawan hancin farhat ta zubawa ido Wanda yake tsaf tsaf na dadynta ne ta debo ta gangara da idonta kan idanuwan farhat din take kirjinta ya buga da qarfi ta dauke idonta akai tana miqewa Kamar wadda kwai yafashewa aciki.

Kasa zama tayi sbd sanyin qamshin turaren dadyn daya cika gurin Kamar har lokacin kaman Yana gurin Dan haka saitakejin bazatama iya sakewaba Dan Jin take kaman Yana Nan Dan haka a tsaye tabawa farhat din abaki harta qoshi itama biyu kawai taci suka tattare gurin suka nufi daki sukai brush tareda wanka sukai sallar Isha sukai Shirin bacci suka koma dakin farhat din acan suka kwana.

Washe gari datasan Yana Nan batai gigin ko kallon hanyar dining room ba sbd dama acan ne kawai ake haduwa dashi acikin gidan Dan koyaushe Yana samansa Dan ko acan saman Palo biyune dashi kafin akai Master bedroom dinsa.
A kicin tayi breakfast bayan antafi Kai farhat school Dan haka itama tana gamawa driver ya wuce da ita.

Kwana biyu tana kame Bata wani fitowa sai yaunema da farhat ta tashi da zazzabin sanyi me qarfi na asthman datake dashi Wanda kaman agurin dadynta ta dauka Dan shima yanada asthma Amma ba'a taba ganewa sbd kiyayewa.
Kayan sanyi masu kauri ta Sanya Mata da socks da wulan sanyi tareda dumama dakin yadauki dumi takawo Mata tea me zafi tabata ahankali hartashanye tana gama Sha ta koma kicin ta maida kayan tadawo kenan tun daga bakin qofa take jiyo kukan farhat din da sauri taqaraso cikin rufewa ganin amai farhat din keyi sosai take hankalinta yatashi ta dauketa tayi toilet da ita yarinyar tafara galabaita sosai Dan kuwa ko zama Bata iyayi da kanta sbd galabaita.

Wanka tayi Mata tasake Sanya Mata wasu kayan masu nauyi bayan ta shafe Mata jiki da mai me Dan zafi ta sake gyare dakin tsaf ta sauya bedsheet da duvet ta kunna turaren daki dake fita ahankali ahankali Yana gauraye dakin da qamshi sai dakin yayi Dadi sbd ga dumi ga qamshi me Dadi.

Fitowa tayi daga dakin Bata cikin nutsuwarta sbd ciwon na farhat yafara Bata tsoro sbd numfashinta dayake wani daukewa yana dawowa gashi tun safe take Kiran Afia Bata samu gasu mum Sarah ma duk sunyi iya dubarunsu Babu sauqi Dole dadynsu afia din akeson sanarwa sbd anema likita cikin gaggawa Amma shima tun safe bai saukoba hakan yasa hankalinta mummunan tashi tashiga tsoro da firgicin halinda take ganin farhat Dan tana tsananin buqatan ganin likita.

Palo tadawo ta tsaya idanuwanta na cikowa da hawaye tarasa abinyi sai kawai ta zauna kan kujera tareda fashewa da kuka ahankali tana cewa"

Yaya zanyi Ni?

Mum Sarah ce da itama take cikin tashin hankalin tace"

Ki Kira IMRAN kifada Masa saiya Kira MALEEK yafada Masa.

Dago idanuwanta dasukai ja sbd kuka tayi ta kalli mum Sarah cikin sake shiga damuwa me qarfi tace"

Bayan afia Dana kasa samu IMRAN ne na biyun danayita Kira Amma shima wayarsa Bata zuwa.

Ki rubuta Masa text zaigani inshallah.

Hawayen cikin idanuwanta suka gangaro batareda ta damu da shafewaba ta daga wayarta tahau rubuta Masa massage tana turawa ta miqe jiki amatuqar sanyaye ta rurrufe ko Ina Takoma daki gurin farhat din.

Zama tayi bakin gadon tareda zubawa yarinyar idanuwanta dasukai luhu luhu sbd kukan tausayin farhat data zabge cikin yini daya sbd azabar ciwo.
Cikin kuka Mara sauti tace"

Farhat Allah yabaki lafiya
Bazan iya cigaba da ganinki hakaba.

Kuka takeyi sosai kafin daqyar ta iya miqewa ta rage kayan jikinta sbd zafin da dakin ya dauka yayi Mata yawa ita ta Sanya riga da wandon bacci qananu rigar Mara hannu ce sai wandon gajere ne iya cinya ta hau gadon tareda rungumo farhat ajikinta ta lullubesu bayan tayi musu addua har lokacin tsiyayar hawaye takeyi ahaka bacci ya dauketa tana qanqame da farhat din.

IMRAN lokacinda text din NURU yashigo wayarsa ya duba agogo qarfe dayan dare da minti arbain da uku sai hankalinsa yayi mummunan tashi sbd yasan ciwon farhat din zabura yayi ya miqe tsaye Amma Kuma bazai iya zuwa gidanba yanzu Amma Kuma tsoronsa idan har lokacin ciwon bai lafaba kumaba,
Numbern MALEEK ya lalubo a rikice ya Danna Masa Kira
Amma kaman yanda yayi tunani bai dagaba Kuma yasan ba dagawan zaiyiba sai kawai ya rubuta Masa massage cewan farhat na cikin mawuyacin hali tasamu attack na asthman datake dashi Yana turawa yakoma ya zauna Yana dafe kansa cikin rashin nutsuwa Dan yasan NURU ma nacan cikin mawuyacin halin damuwa da firgicin ganin farhat acikin halina ciwo.

Kwance yake idanuwansa ne kawai a rufe ba bacci yakeba sbd yanayin sanyi da ake yau me tsanani dashima yakeson Dan dago Masa da ciwonsa sai qaramin ciwon Kai dake damunsa na rashin bacci shiyasa yau ko fitowa baiyiba ruwan energy drink na powerhorse kawai yakesha sai yaga wayarsa na haske alamar shigowar Kira batareda ya dubaba ya share wayar Dan ba dauka zaiyiba.
Ganin anata Kira yasashi dauka Dan kashe wayar duka saiga text din Imran jalal yashigo bai budeba ta gaban lockscreen din yafara ganin abinda ke rubuce cikin massage din ya tashi zaune ahankali Yana qarasa karantawa ya ajiye wayar tareda Miqewa tsaye cikin nutsuwa ya sauko gadon tareda zura slippers din _Berluti_ masu tsananin tsada da rashin nauyi yafito zuwa qasan sanye cikin sleep wears na _prada_ black colour ya sauko direct bayan wasu shekaru yau ya nufi dakin farhat Kai tsaye.
Murda qofar dakin yayi ya tura wani dumi da qamshin English rosalle oud ya daki fuskansa zuwa cikin hancinsa ya sauke boyayyan numfashi ahankali sbd best mist dinsa kenan na daki ya shigo dakin tareda tura qofa sbd akwai Dan duhu a dakin cikin takunsa na nutsuwa da kamewa ya isa bakin gadon farhat din ya zauna tareda kallon 'yar qaramar fuskarta data fada lokacin daya wani irin tausayin 'yarsa da qaunarta me qarfi na ratsashi yakai hannunsa akan fuskarta ya shafa yanajin kaman yakasa amatsayinsa na mahaifi yakasa Basu rayuwarda suke buqata ta kulawan uwa da uba.

Bedside light ya kunna 'dan haske ya bayyana yasake Kai hannu kan wuyanta zai taba yaji temperature dinta hannunsa ya sauka kan hannun NURU dake rungume da ita kaman zata maidata ciki sai alokacin ya lurada NURUn wadda gabaki daya jikinta ke bayyane farar fatarta dake tas wani irin qyalli takeyi musamman dogayen cinyoyinta dake wani haskawa afili ya dauke kansa Yana Dan yamutsa fuska ya zuwa fuskarta da idanuwanta suka bayyanarda kumburinsu na alaman kukan datasha sai sauke ajiyar zuciyar kukan datai takeyi akai akai cikin baccin ya gangaro da kallonsa kan irin rungumar dataiwa farhat cikeda qauna da alamun dake nuna Jin take kaman ciwon yadawo jikinta.

Ya rintse idanu Yana jinginar dakansa jikin kan gadon hannunsa har lokacin nakan nata batareda yatuna ya daukeba sbd tausayinsu duk su duka wato itada 'yayansa daya shigesa.

Rufe idanuwansa yayi ahakan yanajin numfashin farhat me dumin zafi na sauka ajikinsa itakuma Kuma dumin zafin jikinta na zazzabin wuya daya fara shigarta na shiga ahankali nasa jikin ta hannunsu dasuka hadu.
##MAMUH##




_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899*_Mamuhgee 12_*
Qarfe shida da wasu mintuna ya bude idanuwansa dasukai nauyin baccin daya daukesa daga Nan jinginen kan gadon.
Tashi zaune yayi ahankali yana kallonsu sbd har lokacin bacci sukeyi sosai musamman da alamu ya nuna farhat din ta samu sauki sauki sbd numfashinta daya 'dan daidaita.
Hannunsa dake sarqe cikin na NURU data qanqame ya kalla ahankali tareda dago manyan fararen idanuwansa da bacci ya Dan sauyasu ya zubawa fuskarta datake Kama data 'yan babies kaman farhat dinsa saiya maida kallonsa kan farhat da itama innocent face dinta tayi haske ya saka dayan hannunsa yakama hannunta ya zare hannunsa Yana kallon fararen yatsun hannunta dasuke farare fes kaman Bata aikin komai dasu ya miqe yaja bargo ya rufe musu jikinsu musamman NURUn da cinyoyinta suka gama Shan sanyi duk da Babu wani sanyi ko kadan a dakin shiyasa ma shima baccin yadan daukesa.

Ficewa yayi dakin ya rufo musu qofa yayi samansa Dan yin sallah da yau yayi latti.
Bayan fitarsa ba jimawa NURU ta farka ta tashi jikinta amatuqar mace da Dan nauyin jiki da sauran ciwon kan dabai gama sakinta ba ta zauna tareda kallon farhat tana tabata tareda duddubata ta tabbatarda tasamu sauqin dannewan numfashin saitaji hankalinta yadan kwanta ta sauko gadon ta nufi toilet din dakin tashiga tayi duk abinda zatayi tazo alwala tana Kai ruwa bakinta zatayi shaqar hanci taji wani irin qamshi a tafin hannunta ta Kai hannun hancinta ta sake shaqa taji wani irin qamshi dayaso kashe Mata jiki Amma Kuma takasa tuna na menene tunda tasan last abinda ta taba kafin baccin was kayan baccin data Sanya ta kwanta.
Cigaba tayi da alwalarta tagama tafito Takoma dakinsu acan tayi sallar tana idarwa tadawo ta duba taga farhat Bata farkaba har lokacin bacci takeyi ta gyra Mata lullubinta tareda gyara Mata kanta Takoma daki ta cire kayan baccin ta Sanya dogon wando da rigar sanyi da hula ta nufi kicin Dan hadawa farhat din pancakes da tea din sabuwar Madara datasan farhat na tsananin so ko zata samu taci Dan duk jiyan bata iyacin komaiba sbd tsanani da azabar ciwo.

Tana cikin aikin mum Sarah da itama baccin rabi da rabi tayi sbd damuwar ciwon na farhat tashigo tana Taya NURU aikin bangare daya Kuma ga Fana na aikin hada breakfast na MALEEK.
Sauri tayi tagama sbd kada farhat din tatashi Bata kusa tana gamawa ta aje jere komai a dining ta nufi dakin farhat din tana waya da Afia data Kira a rude sbd Imran yafada Mata saita kwantarwa afian hankali tana cewa farhat din tasamu sauki inshallah.

Turo dakin tayi tashigo Kai tsaye tana ganin farhat din zaune kan gado ta qaraso da sauri cikin farin ciki idanuwanta na cikowa da hawaye cikeda qaunar farhat din me girma tace"

Finally Sweetie kin tashi""rungumeta tayi tana cewa"

I miss you so very much baby
Kinabani tsoro jiya sosai harbansan tunanin me zanyiba......
Idanuwanta ne suka sauka akan MALEEK dake tsaye gefen gadon daga dayan gefen fuskarsa nakan waya dayake dubawa na Kiran dayayiwa Dr Damien.

Wani irin mummunan firgici da tsoro ne yashigeta tayi Saurin gayara hularta data zame tana tashi daga kan gadon tana gyara wuyan rigarta ta sauke Kai qasa tareda zubewa qasa cikin tsananin girmamawa da sanyin murya tace"

Barka da fitowa.

Bai jita bane kokuwa ya akai itadai dataji shiru ta dago sai taga baya gurin saitaji jikinta yasake yin sanyi sbd wani lokacin mantawa takeda matsayinta na baiwa sai irin hakan ta faru take tunowa da ita din bakowa bace face baiwa 'yar bawa jikar bawa gadon bauta,
Allah ne yahada qauna me qarfi da tsafta tsakaninta dasu afia da farhat Wanda ta dauka hakan tamkar wata rahamace ga rayuwarta shiyasa dorewa da dawamammiyar qauna atsakaninta dasu afia yazama cikin adduarta tacikin sujjadarta.

Kamo hannunta taji farhat tayi ta juyo kanta tareda zama kusada ita tana kawar da tunanin damuwa tasaki fuska cikin kulawa tace"

Yaya kikeji yanxu sweetie?

Kwantawa tayi jikin NURUn tana gyada Mata Kai alamar da sauqi.

Shafa kanta NURU tayi tana cewa"

Baby muje ayi brush nahada Miki pancakes dinki kici ko kadan ne zakiji Dadi Dr ma Kuma Yana zuwa hakama uncle Imran na zuwa haddama AFIA nason Jin muryan princess farhat.

Kallonta kawai farhat din keyi sbd Bata iya ko dariya haka ta dauketa takaita toilet tayi Mata wanka da ruwa me zafi tayi Mata brush suka fito ta shafa Mata Mai da duk abinda yakamata ta shiryata cikin Kaya masu kauri sosai tareda hular sanyi da socks ta hannun da qafa suka fito Palo tana daukeda ita suna fitowa babban Palo Ana budewa Imran kofa Yana shigowa cikin kayan sanyi shima sbd yau gari akwai sanyi sosai tana ganinsa taji wani irin sanyi aranta sbd dama Wanda zaiyi magana da dadynsu farhat din take neman mafita.

Qarasowa yayi Yana karban farhat din ya kalleta lokacinda ta lafe ajikinsa cikin kulawa yace"

Sorry farhat baby.

Kallon NURU datai Dan zuru zuru yayi yaji jikinsa na mutuwa da wata sabuwar qaunarta me qarfi ya sassauta kallonsa Yana Mata kallon kulawa yace"

How are you?

Numfashi ta sauke tana kallonsa tareda

Please Login or Register in order to submit comment