Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

0903 234 5899
*_Mamuhgee 24_*
Saida safe dukkaninsu sukasan farhat batada lafiya Koda suka Isa dakinta tana zaune jikin dad dinsu Yana zaune bakin gadonta sanye da black jallabiya ta maza me tsananin taushi sai kyallin maiqo takeyi alamar ta masu abun duniya ce.

Itace agaba ashigowa kafin Afia Amma tana ganinsa tayi slow afia ta wuceta tana qarasa dayan gefen ta farhat din ta zauna tana cewa"

Gud morning dad,
Farhat bakida lafiya bamusaniba mum Sarah ke fada Mana yanzu da safen Nan.

Dago fuskarsa yayi dake fayau dinta sai wani daukan ido take ya kalleta da idanuwansa Wanda itama daidai shi ta sata kallo suka hada ido tayi saurin sauke idonta muryarta da wani irin salon sanyi dabata saniba tace"

Barka da safiya.

Har lokacin kallonta yakeyi
Tasake dagowa ta saci kallonsa suka sake hada ido sai kawai tunanin ganin dayayi Mata jiya da daddare kusan Babu komai a jikinta take wata matsananciyar kunya ta mamayeta batasan lokacinda ta rufe idoba ta fita da gudu Kamar karamar yarinya.

Da mamaki afia ta dago ta kalli kofar kafin ta juyo ta saci kallon dad dinta da bataga alamar ma yasan da NURU tashigo bare tace kofar yake kallo ta maida kallonta kan farhat tana cewa"

Sorry baby aunt NURU taje Sanyo kayane sbd batasan dad na Nanba ta taho da sleeping dress ajikinta shine Takoma ta sauyo nasan kin matsu tazo gurinki ko baby?

Gyada Kai farhat din tayi tana kwantawa jikin afia din tace"

Afia I saw mum yesterday a school dinmu she was there before I fainted......

Da sauri AFIA ta dago ta kalli farhat din tareda kallon dad dinsu da sauri shima saidai ko Gama juyowa batayiba ya miqe ya fice kamarma baiji me farhat taceba afia tabi bayansa da kallo kafin tadawo da kallonta kan farhat cikin mamaki tace"

Baby dagaske Kinga mum?

Gyada Kai tayi tana kallon afia din tace"

Eh naganta tazo kafin ta iso gurina I fainted daganan shikenan saidai Naga dad kawai.

Wani yawu afia ta hadiye kafin ta ta danne mamakinta da farin cikinta tana miqewa tace"

Ok baby Bari naje naturo Miki NURU tazo tayi Miki wanka da brush saita Baki abinci akwai abinda zanyi yanzu na gaggawa ok baby.

Wucewa tayi ta fice da sauri ta nufi dakinsu ta janyo doguwar riga tasanya akan kayan baccin jikinta ta dauki wayarta da sauri ta fice ta nufa library dinsu Dan Yin waya.

Doguwar kimono NURU ta doro akan kayan jikinta na bacci kafin ta wuce ta nufa kicin ta hadawa farhat Dan guntun breakfast sharp sharp ta dauko a qaramin faranti ta nufa dakin tana adduar Allah yasa ya fice.

Ganin baya dakin yasata qarasowa da wuri ta ajiye tray din tana cewa"

Sweetie kiyi hkr bamu San bakida lfy ba,jiya ma anan nayi wanka Amma banluraba sbd hankalina yatafi wani gurin dabam na......kasa qarasawa tayi tana sake tunano abinda yafarun sai kawai ta sauya zancen da sakin qaramin murmushi tana cewa"

Ok sweetie muje ayi brush kizo ga breakfast sai asha magani.

Tayar da ita tayi suka nufi toilet din suka shige.
Harsuka gama komai har wanka da Shirin farhat din kafin suka fito zuwa nasu dakin itama NURU tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga suka fito Palo ta kunna Mata cartoon takoma ciki tayi Shirin makaranta tazo ta fice har lokacin afia Bata shigowaba tanacan.

Tsaye take cikin libry din idanuwanta sunyi jajir sbd tsananin baqin cikin dake mamaye da zuciyarta ayanxun datake waya da mum dinta cikin tsananin sanyin murya da sarewa tace"

Haryanxu Babu 'yayanki acikin ranki kenan?sbd wani burinki na duniya mum kike fadar haka? Tayaya kike tunanin dad zai iya rayuwa ahaka for how long kikeso yayita jiranki?mum please ki......

Cikin iko da muryarta me taushi ta katse afia da cewa"

Zandawo wa MALEEK Amma ba yanxuba haryanxu akwai abubuwan dake gabana,afia kinada naci akan zance daya koyaushe bayan nace Miki zandawo Amma ba yanzu ba idan akwai abinda yafi cancanta yanzu dakiyi shine ki raba maleek da yarinyar daya aura Kuma tabar gidan gabaki daya sbd matuqar tananan koya saketa bazan iya dawowaba infact inason sauyin gida tunda harta zauna a wannan gidan koba komai idan haryanzu kunason aikinta zaku iya zama da ita acan Amma dai Ni Kam a sauyamin gida musamman farhat da lalurorinta sunyi yawa yau ciwo gobe lafiya....

Cikin mamaki,takaici da baqin ciki daya Gama kashe afia tabude Baki tace"

Mum shin akan abindake gabanki kika watsar da 'yayanki musamman Yar qanqanuwa Kamar farhat harkina cewa lalurarta yayi yawa?
Ciwone fa atareda ita Wanda Allah ne ya Dora Mata ba ita tadorawa kantaba, badan NURU ba da yanzu dukkanin mu munshiga wani hali and now kina cewa akoreta?a koreta kokuma mubita can mu zauna kenan kin yafemu?
Mum inasonku keda dad duka saidai I'm sorry to say this to you yau nafi son dad ayanzu fiyedake da duk wani tunaninki Dan kuwa koba komai shi yasan haqqinmu 'yayansa akanshi Yana bamu Dan haka mum tunda haryanxu Bakida mijinki da yayanki aranki inaga zaifi idan na karbi hakan na runguma nakuma amince Dan kuwa na tabbatarda dana amince da hakan tuntuni da bazan cutatu hakaba,
Na lalata rayuwar mutum uku sbd hope din Zaki dawo saidai Ashe mafarkinane kawai....hawayen baqin ciki me tsanani ne suka gangaro Mata ta kashe wayar da qarfi tareda wurgi da ita sbd Jin mum din na cewa"

Afia ke yarinyace haryanxu bazaki ganeba Dan haka please don't call again idan Baki shirya daukan abubuwan dazan fada mikiba.

Kuka me qarfi ta sake tareda daukar wayar taqara kwadawa da qasa tana qoqarin sulalewa qasa cikin kuka taji hannuwan dad dinta duka biyu ya riqota Yana kallon kyakkyawar fuskarta ya girgiza Mata Kai ahankali ya bude Baki cikin muryarsa me nutsuwa da dadin sauti yace"

AFIA MALEEK karki manta ke 'yar maleek ce jikar kaleeb our beautiful and brave lioness and you know wat thats means right princess??

Da jajayen idanuwanta ta dago ta kallesa zatayi mgn yace"

Ya Isa haka banason Jin komai all I want from you shine ki maida hankali akan karatunki ki Gina career dinki da kanki.

Sakinta yayi tareda juyawa zai fice saikuma ya dakata batareda ya juyoba ya bude Baki wannan karon cikin cikakken iko da bada umarni cikin sautinsa me daidaita nutsuwarta yace"

Wannan shine Karo na karshe daza'a Kuma maganarta acikin gidan Nan.
Karo na karshe.

Gyada Kai tayi tana sawa ranta batada uwa araye daga yau itama sbd dukkanin inda take tunanin mum dinta yau ta kai limit Dan Bata taba daukar uwa zata iya yafe har yayanta ba datake ikirarin Bata buqatar farhat sbd tacika ciwo, wannan kalmar ta rusa duk wata sauran hope datake dashi akan mahaifiyarsu.

Fitowa tayi tana shigowa Palo ta tararda farhat zaune apalon tana kallon cartoon cikin walwala abinta tana ganin afia din tasake murmushin farin cikin ganinta tana cewa"

Afia bakije makaranta ba kina inane tun dazu?
Aunt NURU ta tafi ta dauka kintafine.

Kasa magana afia tayi tausayin qanwarta me tsanani na shigarta har batasan sanda hawaye suka ciko Mata idoba suna gangarowa ta qaraso ta zauna gefen farhat din tareda rungumeta jikinta tanajin tsananin so da kaunar yarinyar tareda tausayinta,tayaya uwa zatace Bata buqatar 'danta sbd wani ciwo na harbawa da Allah ya sako Masa,
Ta Yaya mum dinsu zatace Bata buqatar farhat?
Kamar farhat din tasani saita lafe jikin afian batace komaiba hawayen afian Bata sauka kan jikinta sun Jima ahaka kafin Afia ta zame tareda Miqewa yayi daki ta rufe kanta tana wani irin kuka me ciwo da baqin cikin rayuwa,
Babu abinda Allah be basuba najin dadin duniya sai rashin uwa tagari da soyayyar uwa da Basu samuba kwata kwata,
Suna cikin ni'imar dukiya me yawa,
Mulki na sarauta me girma,uba nagari da soyayyarsa,ilimi na Boko Dana addini,kyawun jiki Dana fuska taredana zuciya daidai gwargwado Amma uwa Basu samu komai daga garetaba bayan dawainiyar daukan ciki da haihuwa duk cikinsu Babu Wanda yayi shekara yanashan nononta take zaresu tabarwa masu aikisu sune komai nasu tayaya zasu qarar da soyayyar uwa.

Sai yamma NURU tadawo tun apalo ta sake tabbatarda farhat ta warware Dan da gudu ta tarbeta suka fada kan kujera cikin murna take bawa NURU labarin yau dad yafita da ita Amma Basu dadeba suka dawo.

Miqewa NURU tayi tana cewa"

Iyye yau Daddy ya kyauta Mana sweetie taje yawon datake so.

Duk da haka fa aunt NURU alqawarin mu Yananan fa dakikace Zaki kaini yawo har wani qasa daban.

Hanyar daki suka nufa tana cewa"
Eh banmantaba saina gama karatu idan zanje Vegas attaching papers Dina na Gina career Dina dake zanje Inshallah sweetie.

Tsalle tasaki tana cewa"

Yes yes my Lewa

Suna shiga daki afia na zaune tayi wanka sanyeda gajeran wando da shimi tana aiki da laptop tana ganinsu ta sake fuska tana cewa NURU"

Welcome baby.

Thank you princess"NURU tace tana zare kayan jikinta tana fadawa Afia zancen dasuke da farhat suna dariya.

Wanka tayi tazo yayi sallah ta Sanya qananun kayan Shan iska itama tasha coke daya ta Dan kwanta sbd ta Dan gaji Kuma batajin yunwa Dan taji snacks a wani coffee shop.

Tana bacci wayarta tadauki ringing afia dake zaune ta kalli wayar saitaga sunan padima.
Murmushi tasaki sbd tasan padima abakin NURU Amma Basu taba gaisawaba Dan haka ta dauka Kai tsaye tareda cewa"

Assalm alaikm padima ānichī gini inidēti neshi? (ya kike ya gida/hw are you doing and family).

Tsit padima data Kira da Dan qungun kukanta tayi Jin muryar afia wadda takeda tabbacin itace 'yar maleek da ake fada Dan haka saita Dan saita murya cikin girmamawa da kulawa da sautin muryarta daya tabbatarda tayi kuka tace"

Lafiya kalau alhmdlh li'iliti.
Ya karatu da hidima?

Murmushi me sauti afia tayi tace"

Ba hidima saidai karatu shima munatayi inshallah munkusa gamawa, NURU na bacci yanzu saidai ko Zaki sake Kira anjima kokuma idan ta tashi saina fada Mata ok?

Dan kame kame padiman tafara tana cewa"

Eh baza'a tada ita bane yanzu da magana zamuyi me mahimmanci ne?

Kai tsaye afia tace"

Aa baza'a tashetaba yanzu dai lokacinda ta tashi dakanta kokin manta Matar maleek ce?
Koma yayane bazan tashetaba saita tashi da kanta matuqar ba lokacin sallah bane kawai ya isa yasa na tasheta sai idan dad ne dakansa yake nemanta which kuma is not possible for now dai.

Wani Abu padima taji yataso Mata kamar zata ashararo ashar ta danne tana cewa" Sabala ibilis cikin ranta.
Wato NURU har matsayin nata yafara kaiwa haka tun wuri.
Jin shiru yasa afia cewa"

Ko da akwai matsale ne a gida?
Kifadamun zanyi maganan da ita idan ta tashi.

Shiyafi komai sauki 'yar maleek padima tafada cikin ranta tareda sauke wani wahalallen numfashi tana karye murya zuwa rawa rawar son kuka tace"

Dama nafada Mata maganar rashin lafiyan danake fama dashine abin yafara tsanani anyi magani anan gida baiyiba shine tace zata kaini Inga likita anan ko za'a dace.

Da mamaki a bayyane afia tace"

Anan Kuma?
Tun yaushe ne ciwon?

Tsawon shekara"padima tafada tana hawaye.

Gyara zama afia tayi tana cewa"

Shekara daya ciwo ajiki shine NURU Bata taba fadaba.?
Menene matsalar?

Ciwon zuciyane yanzu nakai Ina amai da tarin jini wani lokacin.

Innalillahi padima meyasa bakuje ko English hospital na can ba.

Shiru padima tayi tana hawaye da shehekar data sake bawa afia tsoro tafara Mata tambayoyin akan yanda takeji da kalar jinin datake gani tana nazartawa da 'dan nata ilimin na likita da Bata qarasa zamaba.

Girgiza Kai tayi cikin jimami da tausayawa tareda tsoro tace"

Padima this is serious yakamata kiga likita cikin gaggawa gaskia.

Kuka padiman tasake fashewa dashi tana cewa"

Bansan Yaya zanga likitaba Dan Allah li'iliti ki taimakeni NURU takasa taimakona banason na mutu yanzu.
Ki taimakeni ki kawoni gurinki ki kaini gurin likita Dan Allah.

Shiru afia tayi ciki rasa sanin abinyi Nan take Sadai koma menene batada ikon kawo padima Nan take Dole saidai NURUn ce zatace akawota tukuna akawota din sbd kawo mutum Kai tsaye gidan MALEEK wani aikine Dan kuwa sai ankaita gizah an tantance kafin akawota gidan MALEEK Wanda yanzu Kam NURU ce kawai takeda ikon kira gizah tafada tanason akawo Mata padiman.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda nutsuwa cikin son fahimtarda padiman tace"

Kiyi hkr padima Inshallah Zaki samu lafiya Amma yanzu dai Ni inshallah zan nema appointment na babban likitan da Zaki gani anan Amma maganar zuwanki zanyiwa NURU magana idan ta tashi saita Kira inda za'a kawo ki anan din.

Nagode sosai Allah yaqara girma ina gaida NURUn idan ta tashi.

Katse wayarta tayi tareda wurgi da ita tana jerowa daga afia din har NURU zagi sbd Sam sunqi hawa yanda takeson suhau su rikice da tausayinta yazama basa tunanin komai saina tausayinta tasamu Isa qasar.
##MAMUH#





_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

0903 234 5899
*_Mamuhgee 23_*

Abdul-rahman (sudais) is a young boy who's so passionate about putting the Holy Qur'an into memory. Please help this little boy grow his YouTube channel *ABDUL-RAHMAAN* you got nothing to lose in sha Allah thank you and Jazakumullah khair🙏🏻

https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0

Do subscribe please



****************
Kodata fito kasa zuwa dakin farhat tayi sbd gabaki daya kafafunta sunyi sanyi toilet dinma tana fitowa ta zube kan gado a kife tana sauke ajiyar zuciya a jejjere Dan Kamar har lokacin tanajin dumi da softness na hannunsa akan mararta.
Bude kofar da akaine yasata Dan juyowa ahankali taga afia ce ta tashi zaune da sauri tana cewa"

Princess tadawo.

Dariya afia tayi tana qarasowa ta aje shopping bags din dake hannunta tace"

Harkinji sauki kenan?

Waskewa NURU tayi da cewa"

Eh" tajawo kayan tana budewa Dan mantar da kanta tunanin abinda yafaru din.

Duk abinda take buqata afian tasiyo Mata ta tashi ta tattara kayan tasa musu su a inda suke aje kowanne tayi sallah tazo ta zauna suna duba wani sabon Francie's program na likitoci da lawyers tareda engineers a laptop.
Sai la'asar lis tayi wanka ta sauya cikin White three quarter da farar top me laushi ta fita tayi dakin farhat afia tabi bayanta da kallo sbd kusan kome NURU tasaka kyau yake Mata inama ace Imran dinta tafara aura dashine zata more rayuwa sbd yanda yake Sonta Amma dad dinta bazata taba samun so agaresaba har abada sbd mum ce kawai a zuciyarsa.

NURU na shiga dakin farhat ta taddata itama sanye da fararen qananun Kaya tana jiranta har ta fidda kayan drwing din Nan suka baje suka fara.
Sai bayan magriba suka gama
Farhat ta dauka da gudu taje nunawa dadynta ya duba Masu idan sunyi daidai Amma bayanan kusan so uku tana komawa bayanan ta karba wayar NURU ta saka numbernsa dake cikin kanta ta Kira Bai dagaba tukuna ta hakura anan dakin sukai sallarsu suka kunna cartoon suka baje abinsu adakin suna kallo Saida lokacin cin abincinsu na dare yayi suka fito zuwa dining suka zazzauna sukaci suka koshi suka shige anan dakin farhat NURU tayi barci Bata koma nasu ba Dan dama hakan takeyi wani lokacin.

Qarfe goma Sha biyu da mintuna ya nufo dakin farhat din wadda kusan kullum idan haryana gida saiyazo ya dubata da daddare sbd qarancin shekarunta musamman yau dayasan saitayi nemansa sbd zanenta yaduba Mata Dan haka ya nufa dakin Kai tsaye ya bude yashigo tareda rufe kofar har zai kunna wuta gudun kada ya tadata yasa Bai kunna dinbaya qaraso bakin gadonta tareda zaunawa bakin gadon ya Kai hannu yakunna bedside lamp kadan haske ya 'dan bayyana yana waiwayowa yaganta itace kwance abakin gadon farhat na quryar gadon ya sauke sahirtaccen numfashi Yana kallon kayan baccin jikinsu itadai farhat komai iri daya riga da guntun wando royal blue bacci suke duk su duka hankali kwance.

Dan qara rage hasken wutar yayi sbd kaman hasken zai damesu yajanyo musu bargo ya lullubesu ko Gama janye hannunsa baiyiba NURU tasa kada ta yaye lullubin Dan dama Bata cikason rufaba cikin bacci.

Fuskarta yayiwa kallon minti biyu ya dauke Kai tareda Miqewa ya nufi hanyar ficewa harya taba kofa zai fita saiya tsaya tareda Dan rufe ido ya bude tunanin Dole wani daga cikin masu aiki zasu tadasu da asuba yasashi dawowa yasake Jan bargon ya rufa Mata saidai Yana dauke hannu takai hannu cikin baccin zata yaye yakai hannu zai danne hannuwansu suka sauka atareda nashi akan nata Wanda Kai tsaye yasata bude manyan idanuwanta dake cikeda bacci ta dagosu.

Kasa yadda tayi da abinda tagani tasan mafarkine kawai take Dan haka saita juya hannunta tasanya tafin hannunta tana sake tattaba hannunsa Dan Jin tsananin taushinsu ta lumshe ido baccinta na fizgarta har lokacin tafin hannuwansu na hade.
Dan sarquwa yayi da yawu kadan yasaki Dan qaramin tari Mara dogon sauti Wanda yasata bude idanuwanta duka da qarfi tareda zaburowa daidai motsawar farhat sai yayi saurin dafeta Takoma kwance sbd kada ta tada farhat ga farhat din da surutu zata iya jeho wani zance akan hakan.

Kallonsa takeyi face to face akaro na farko a rayuwarta zuciyarta na harbawa a tsorace yayi Mata kallo daya da idanuwansa da yau suka shiga daidai cikin nata take taji jikinta ya sake gabaki daya sai kawai ta sake a jikinsa ya hadiye wani mugun yawu a maqogaransa Wanda yasata kallon moqoshinsa sbd yanda Adams apple dinsa yayi sama yayi qasa ta maqoshin nasa.

Miqewa yayi tsaye yaraba jikinsu sbd asthma dinsa dayakejin kaman zata tashi ya juya ya fice adakin yabarta kwance Bata iya ko daga hannunta sbd mutuwar jiki saidai ido databisa dashi cikin wani irin yanayi na kunyane ko na menene ta Bata saniba illa dai Abu daya data tabbatar ayau shine kyawun da Allah yabasa Wanda ko rabinsa 'yayansa Basu daukoba cikin yama manyanta kenan...daganan baccinta ya watse har kusan asuba Bata samu baccinba gashi gobe tanada zuwa makaranta Dole ta rintse idanuwanta Dan tayi baccin Kona Dole ne.

Qarfe shida ta farka ta sauko gado tashiga toilet tayo alwala ta tada farhat sukai sallah ta fice.
Tana shiga dakinsu ta tada afia sallah kafin ta fito ita ta fice zuwa kitchen aikin breakfast.

Tana gamawa ta jere a dining takoma daki tayi wanka tashirya cikin black riga da wando ta doro doguwar kimono fara akai ta daura black scarf me kauri tafito sukayi breakfast itadasu afia da farhat suna gamawa kowa yaje ya dauko jakarsa suka fito.

Da Mr Omar suka fara cin Karo tsaye jikin motar dazasu tafi da ita makaranta tareda sabon driver cikin girmamawa yana Dan taudasa harshe cikin sakin fuska yace"

Gud morning Mrs MALEEK.
Gud morning princess.

Kallonsa AFIA tayi Jin abinda yace itadai NURU sidadawa tayi ta wuce Jin kalmar tamata girma ta shige mota tana kunna wayarta da Imran yahanata sakat da kira saigashi tana kunnawar kiransa na shigowa ta dannata silent tana Dan kallon gefen Mr Omar dake tsaye idanuwansa kuwa quru akan wayarta tana juyowa ya dauke Kai Yana cewa"

Adawo lafiya.

Suna barin gidan ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar data kusa katsewa cikin sanyi da rawar murya na rasa abin cewa da damuwa tace"

Hello im ka......da wata gigitacciyar ajiyar zuciya ya katseta yana cewa"

NURU labarin aurenki Bai kasheniba duka ya kashe rayuwata gabaki daya amma rashin daukan wayarki zai kashenine sbd.....

Da siririyar murya tayi saurin katse zancen da cewa"

Kariga kasan komai Im tayaya zan iya daukan wayanka yanzu inajin tsoron hakan.

Kasa danne abinda yakeji yayi cikin wata wahalalliyar murya idanuwansa na cikowa da hawayen zafi da ciwon da zuciyarsa kemasa ya bude Baki dakyar yace"

NURU shin da gaske kin auri MALEEK sbd wlh nakasa ji nakasa yarda da komai inason ji daga bakinki Dan kuwa nasan nikadaine a zuciyarki nakasa yadda da hakan NURU na.....

I'm sorry im bansan mezan iya cewaba Amma dai koma menene gskiyan shine aure dai andaura Wanda Koda bada son Rainaba Dole zan kiyaye dokan aure Dan Allah im kayi hakuri komai yafaru ne kaman daga sama,nasani kana tsananin Sona haka Nima Ina......shiru tayi Idanuwanta na cikowa da wasu irin hawayen karyewan zuciya sbd Jin sautin kukansa dake fita ahankali cikin karyewa da zuciyarsa keyi taji zuciyarta ta karye itama hawayenta na gangarowa takasa karasa mganar ta kashe wayar sbd kukansa reras dake ji cikin qaramin sauti.

Kasa cewa komai afia tayi tanajinsu sbd tausayinsu datakeji musamman im Wanda tafi kowa shaida irin so me girma dayakewa NURUn.

Farhat kuwa riqo hannun NURUn tayi tana kallon hawayen daya gangaro Mata tace"

Aunt NURU meya samu uncle Imran din Naga kina kuka.

Dauke kanta tayi tana goge hawayenta da tissue ta Dan qaqalo murmushin yaqe tace"

Ba komai kafiyansa kalau he's just missing you princess farhat.

Murmushi tayi tace"

kema Yana missing naki ko??

Shiru sukayi Babu Wanda yasamu damar cewa kalaba har suka Isa aka ajeta suka wuce Dan su sunada Dan nisa.

Suna isa makarantar Kai tsaye ladies washroom ta nufa ta nutsar da kanta tareda bude kanta kwakwalwarta tasamu damar haddace abinda take nanatawa kanta na cewa tanada haqqin auren wani akanta yanzu dokar Allah na kanta.

A dauki mintuna aciki kafin ta samu 'yar nutsuwa ta gyara fusakrta ta fito tana duba wayarta dake ringing ga mamakinta saitaga numbern ta Ethiopia ce Kiran daga gidane kenan da hanzari ta dauka tana tafiya cikin sa'a kuwa padima ce cikin tsananin farin ciki tace"

Hey padima hw are you??

Dif padima tayi sbd batasan abinda NURUn tafada meyake nufiba tana danne baqin cikinta tayi kasa da murya cikin tsananin damuwa tace"

Nuru kina lafiya kuwa?
Ya gida?
Yasu farhat?

Lafiya kalau kowama Yana lafiya,yayasu abal da meryam Ina ammi?

Sake qasa da murya tayi tace"

Lafiyansu kalau nuru.

Kefa padima kina lafiya dai ina?Kuma Yaya jikinki?

Antabo Mata inda take jira sai kawai takasa riqe kukan 'dacin ran datakeji tsawon kwanaki cikin qaramar sheshekar kuka tace"

NURU wlh bansamu saukiba Ni kilama ciwon ajaline abun yamin tsanani Kuma Babu wani magani dasu abal ke bani hasalima haryanxu fushi sukeyi Dani tun kan maganar cikin Nan da Babu nidai Dan Allah NURU kitaimekeni inason gyara rayuwata sbd Nima na faranta ran iyayenmu.

Sanyi jikin NURU yayi ta danyi shiru na seconds kafin ta sauke numfashi me zafi asanyaye tace"

Padima kidaina kuka Inshallah Zaki samu lafiya bazan Bari wani Abu yasamekiba da yardan Allah,
Yanzu Ina makaranta idan nakoma gida zanyi shawaran zuwanki na tambayi AFIA muji idan da hali sai jekadi takawoki Nan anemamiki lafiya.

Da qaramar muryar kuka tace"
Ngd sosai NURU Dan Allah kadaki manta ayi magana da wuri kada abin yayi qarfi fiyeda da.

Tana kashe wayar tafara tunanin Yaya zatayi yanzu da wannan sabuwar damuwar Kuma,da haka ta shiga class.

Qarfe biyar saura suka dawo amatuqar gajiye Dan ko zama batayiba ta aje Jakarta ta tareda zare kimono dinta ta nufi dakin farhat dan wanka take tsananin buqata da fitsari dayake neman matsarta gashi AFIA tarigata shiga toilet bazata iya jiraba.

Tana Shiga dakin farhat bata ciki Kai tsaye ta tube tareda janyo qaramin towel din farhat ta daura tafada toilet.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacinda ruwa masu dumi suka sauka jikinta sbd yau Bata zauna sosaiba sbd zuwanta biyu kotu yau ga damuwar padima data Imran Amma yanzu taji sauki komai datayi wankan Nan.

Farhat yau da zazzabi tadawo daga school sbd bayan drwing din da jiya aka bawa kowa yayo yau games sukayi ita tana cikin masu football Wanda yadata haki da yawa Amma sbd ba qura asthmanta be tashiba saidai ta kwaso zazzabi me qarfi Wanda tun a school tayi collapsing aka Kira MALEEK Koda suka Isa ta farfado Amma Kam tanajin jin zazzabi sosai siadai yanzu zazzabin ya sauka gabaki daya saitasamu bacci ya dauketa Dan hakane yasa Koda suka dawo gida da ita ganin su afia basanan yasa yatafi da ita samanshi yanzu ta balcony daya hango dawowarshi saiya daukota ya dawo da ita dakinta danta samu kulawa gurinsu afian sosai.

Fitowa tayi tana gyara zaman towel din farhat dayayi Mata kadan tana sauke ajiyar zuciyar nustuwar data samu tana qarasowa tsakiyar dakin taganshi tsaye bakin gadon da farhat ke bacci wata mummunar razana tayi ta damqi towel din da qarfi Jin zai sabule Mata ta sake dagowa da sauri ta kallesa cikin tsananin tsoro.

Tsabar rudewa rigarta dake gefen gadon ta nufo da sauri zata dauka kafin ta iso yabar gurin batareda yabari ta qaraso gurinba ya fice dakin gaba daya Dan towel din ko Gama rufeta baiyiba sbd qanqantarsa.

Zamewa tayi bakin gadon farhat tana kallon kanta tareda dafe goshinta tanajin wani irin yanayi na damuwa.
Zarar kayanta tayi ta fice da sauri ta fada dakinsu ta Sanya kaya tayi sallah ta zauna gefen afia batareda tace komaiba ta zurfafa tunanin wani Abu dayakasa fita cikin ranta afia

Please Login or Register in order to submit comment