Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan dukkanin shedu sun bayyanarda yayi kisan da gangan ne ba bisaga qaddara ko dalilin Kare Kai ba ko dalilin ceton Rai to tabbas kisa ce ta Kai tsaye zata hau kansa....
Saurin dafa afian tayi ganin tana neman fita hayyacinta cikin sauri tace"

Dukkanin wannan kadaki yanke ko daya sbd bakisan akan me kisar ta afkuba kika tayine Dan kariyar Kai ko bisaga kaddara kadaki cire Rai daga sauqin ubangiji kiyi kokari kiriqe jarumtar fuskantar komai Inshallah ba hakan bane Ina Mata fata.

Miqewa NURUn tayi Jin tahowar farhat dake kiranta tun daga cikin bedroom ta juya ta kalli kofar dakin kafin ta dawo da kallonta kan Afia a natse tace"

Ina zuwa Bari nadubo ta.

Wucewa tayi zuwa dakin dake gefen nata Wanda aka tsarashi da komai na yara domin farhat din tana shiga ta qaqalo murmushi tana kallon kallon farhat din data shirya cikin riga da wandon asalin yadin qasar na sarauta me kyau ta qaraso gurinta tana cewa"

Heyy sweetie you look more pretty.

Cikin Jin Dadi ta qaraso gurin NURUn tana fadawa jikinta suka juyo zuwa palo tana cewa"

Aunt jiya Ina Kika kwana Kika barni Ni kadai?

Siririn Murmushi NURU tayi tana kawar da zancen tareda Dan dagowa ta kalli inda afia data bari Palon tana fatar Bata jiyo zancen da farhat din tafada ba ta kamo hannun farhat din suka nufi gefen da dining yake ta miqawa Akira hannunta tana cewa"

Kije da ita taci abinci Ina zuwa.

Komawa bedroom dinta tayi tayi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar royal gown ash ta fito Akira dake jiran fitowarta ta gyara tsayuwa suka nufi sashen Anneti Dan sai yanzu tunanin zuwa Kai Mata gaisuwa ya shigeta musamman tasan tanacan cikin damuwar al'amarin itama tabar afia zaune agurin tana saqa da warwarar yanda zata tarbi al'amarin wa mahaifiyarta sbd ko kowa ya yadda da ita ta aikata hakan bazata taba yadda da mum dinta zata aikata hakan ba.

Koda aka sanarwa Anneti qarasowar NURU gurinta sai farin ciki ya shigeta taji ta Dan samu nutsuwa da saukin abindayake cin ranta ta fito daidai shigowan NURUn data qaraso har gabanta ta durqusa har qasa ta gaisheta cikin girmamawa
Da farin ciki Anneti ta dagota tareda nuna Mata gurin zama tana amsawa cikin kulawa tace"

NURU ya kike?
Kina lafiya dai ko?

Alhmdlh"tafada cikin nutsuwa tana Dan dagowa bayan sun gama gausawar tace"

Ashe abin daya faru kenan¿Allah ya kawo mafitar wannan al'amari tareda tsare gaba.

Ajiyar zuciya Anneti tasake tana gyara zama ahankali cikin bayyanarda 'yar damuwarta tace"

Allah ne kawai masanin wannan al'amarin Amma dai koma Yaya yake
Allah ya fitar da kowa yakawo mafita
Musamman shi maleek da abin yafaru a qarqashinsa Wanda yasa Yan jaridu keta fidda labarai marasa Dadi akai
bana fatan hakan yazamo matsala agaresa, ki kula dashi sosai kibashi kulawa Dan Yana cikin tsananin damuwa na tabbata.

Shiru NURU tayi dukkanin jikinta nayin sanyi da wannan sabon bayanin data samu.
Boyayyan numfashi ta sauke tanajin tsananin buqatar son ganinsa Dan Bata lurada cewa halinda yake ciki ba kenan tun jiyan da bazata baro gurinsa ba gashi yanzu batada ikon maida kanta batareda ya nemi ganintaba.

Miqewa tayi jiki Sanyaye ta fito Takoma tanajin danuwarsa na lullubeta tana shiga Kai tsaye daki ta wuce tafara tubewa ta saka Kaya marasa nauyi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta kwanta tareda lafewa kan gadon tanajin kaman zazzabi na neman shigarta.

Baccine yafara fizgarta cikin tunanin datai nisa daga sama sama taji Ana Kiran sunanta ta bude idanuwanta ahankali dasukai nauyi sbd kanta daya fara ciwo tuni, ta dishi dishi taga kaman jekadi take gani gabanta ta bude idanuwanta gabaki daya tana waresu akanta.
Jekadi data fahimci NURUn Bata gasgata ita bace saita Dan murmushi ahankali tana cewa"

Allah qarawa MUSHRAn maleek kyau da lafiyar bacci.

Da sauri ta tashi zaune har batasan lokacinda tafada jikin jekadin ba ta rungumeta da qarfi idanuwanta na cikowa da hawayen farin cikin ganinta da tausayinta tace"

Alhmdlh Masha Allah jekadi kindawo kindowo.

Farin cikine yakama jekadi ta zame tana kallon NURUn wadda Allah ne ya hada kauna tsakaninsu tun farko ta kalli idanuwanta dasuka ciko da hawaye tace"

Karkiyi kuka Allah zakiyiwa godia Allah yaqaro haske a rayuwarki kinji,share hawayen ki gyara fuskanki maleek ke buqatan ganinki tareda afia.

Sai alokacin ta tunoda lailah ta kalli jekadi cikin sanyi da tausayin afia dayake sake kameta tace"

Mum din afia fa??

Ajiyar zuciya jekadi tayi tareda dagowa a natse tace"

Tana hannun hukuma haryanzu sbd anyi bincike an tabbatar itace saidai haryanxu takasa tsayawa ta nutsu tayi bayaninda zai taimaketa.

Shiru sukayi dukkaninsu NURU na jajanta abin cikin ranta da yanda Afia zata dauki abin.

Ficewa jekadi tayi tana cewa tana jiranta a Palo itakuma ta nufi toilet ta wanko fuskarta ta fito ta Dan gyara ta sauya Kaya zuwa doguwar jallabiya maroon ta fito tana qamshin turaren _bosslady_ dayake fita ajikinta ahankali Bata saka sosaiba sbd kada taqarawa afia damuwa akan tata hakama Bata shafawa fuskarta komaiba duk sbd afia Dan batason saka Mata damuwar wani tunanin daban.

Data fito kallo daya jekadi Tai Mata tana karanto Mata adduoin tsari daga sharrin ido Dana Baki sbd ko Yaya NURUn tafito ita din kyanta me sanyi ne.
Afia kuwa Batada wani kwanciyar hankalinda zaisa tayiwa NURUn kallon tsaf itama dai tayi kokari ta shirya kanta suka fito jekadi na gaba suna baya sai su Akira dake take nasu bayan har zuwa bakin sashenshi kowa ya dakata daganan daga jekadi saisu suka qarasa ciki a palo na biyu suka taddashi zaune Yana sauraren bayaninda mr Omar keyi Masa hankali kwance Yana sanye cikin wani coffee brown kaftan dasuka fiddo da qyallin da fatarsa keyi kwarjininsa yana sake bayyana tareda cika idon me kallonsa
Yana Jin shigowarsu Bai waiwayoba saima takardun daya bude Yana karantawa na sakin jekadi da akai a yau din
Mr Omar kuwa sauya bayanin dayakeyi yayi da kallon gefensu NURU da cewa"

Barka da shigowa.

Da Kai NURU ta amsa Masa ahankali tana satar kallon gefen maleek din kadan Wanda Bai nuna ya San da shigowar tasu ba
Afia kuwa Batada karfin amsa Masa
Zama sukayi kafin ya dago ahankali ya zubawa NURU idanuwansa dasuka sata saurin cafko numfashinta daya tashi barin jikinta sbd kallon tajisa ajikinta sosai, ta dago fuska ahankali ta kallesa ya juyarda kallonsa kan Afia tausayin 'yar tasa na kaunarta na sake shigarsa sbd yanason 'yayansa fiyeda yanda ake gani
Ya bude Baki Kai tsaye cikin kulawa da kamewa yace"

Afia maleek yaya?kina lafiya dai ko?

Shiru tayi Idanuwanta nason cikowa da hawaye ta dago ta kallesa tana hango kulawa da kaunarta gurin dad din nata sai hawayenta suka gangaro ta girgiza Masa Kai ahankali tana cewa"

Bana cikin nutsuwa dad.

Dan gyara zama yayi Yana ajiye takardun hannunsa ya sake kame muryarsa yace"

Mum dinki itace damuwarki right?

Gyada Kai tayi tana sauke Kai kalar tausayi.

Afia idan kinmin alqawarin Zaki kwantarda hankalinki ki nutsu kodan karatunki da bawa Taki rayuwar mahimmanci ki daina biyewa tunani irin na mum dinki then namiki alqawarin Babu abinda zai samu mum dinki zata fita cikin case dinnan lafiya Amma Zaki Bata shawaran ta tafi ta inganta rayuwarta ta wani hanyar kin saurari abinda nake fada right??

Dagowa tayi ta kallesa da hawayen dake gudu akan fuskarta ta gyada Kai tana cewa"

Yes Dad namaka alqawari Inshallah dagani har ita zamu cika wannan alqawarin.

Daukan takardun gabansa yayi ya bude tareda karban biro a hannun Mr Omar yasaka hannu cikin takardun tareda rufewa ya miqawa Mr Omar yace"

Ka sameta tabaka sunan lawyernta shine zai qarasa aikin yakai takardun can zasu saketa kada abari 'yan media su sani ko kadan infact dagacan a haura da ita tabar qasar gabaki daya.

Da sauri afia ta qaraso gabansa tana Masa godiya cikin tsananin farin ciki tace"

Imran ne lawyern mum zankirasa zaizo ayau Inshallah dad.

Sunan Imran data ambata yasa NURU kallon afian ta sauke kanta.

Fita afia NURUn ma ta miqe zatabi bayanta jekadi zata dakatar da ita maleek yayi Mata kallon ta barta ta wuce.

Bayan fitarsu ya kalli Mr Omar yace"

Ayi Mata takardun ganin likitan tabin hankali kada a taba barin afia tasan mum din Tata tasamu tabin hankali sbd shock din wannan al'amarin
a fitar da ita abar Mata gidan Vegas tazauna can taringa ganin likita akai akai har Allah ya yaye Mata
Afia Kuma iyakacinta da ita airport.

Allah yaqarawa maleek tausayi da adalci.

Sai maganar Dan jaridar daya fara wallafa cewan 'yar uwar.....'dan shiru yayi Wanda yasa Mr Omar da jekadi kallon juna suna Dan murmushin dasu kadai sukasan ma'anarsa
Mr Omar ya karbi zancen da cewa'

Za'a shigarda bayyananniyar qarar shariar sama akan Wanda yafara wallafa labarin ankashe 'yar uwar mushrah sbd haryanxu bayan mu da hukumar dake hannunka babu Wanda yaga asalin gawar ta Yaya yasan wacece aka kashe hadda alaqarta da mushrah,
Dan Haka inda bayanin yafara fitowa zai fada.

Ahankali maleek ya gyada Masa Kai Yana cewa"

Daga gobe kada abarsu fitowa kowa ta zauna a sashenta a tsananta tsaro a hanyoyin bangaroransu sbd komai zai iya faruwa idan aka fallasa zancen qarar Dan jaridar sbd kada asan inda yasamu zancen.

Juyawa sukai suka fice suka bar sashen nasa sbd wayar dazai fara da kaleeb.

Sbd tsaro Koda afia Takoma sashenta doka aka bayar kadata sake fitowa sai gobe Dan Haka ita Bata damuba take tasaka aka kawo Mata sabuwar waya dayake tana tareda layinta na qasar saita Sanya ta nemi numbern Imran.

Cikin tsananin damuwar halinda suka samu labarin abindaya faru cikin tsananin damuwa yake tambayar afian Yaya case din ke tafiya sbd case ne na masarauta babu me halin Shiga danma sunyi mamakin da hukuma tashiga zancen Dan masarauta irin delah gizah sune suke hukuncin komai daya shafesu da kansu Amma Kuma ace MALEEK dakansa ya bawa hukuma damar shigowa ciki duk da hukumarma tasace sai abinda yace suke amfani dashi.

Cikin nutsuwa afia tace"

Ni yanxu duk wannan bana tunaninsa yanxu sbd ya amince zai sa asaki mum a sirrance tabar qasar Dan Haka kana buqatan isowa cikin gaggawa gobe ka isarda takardun abaka ita ku tafi
Dan Allah kamun alqawarin zaka kularmin da ita sbd nasan yanzu tana cikin tsananin hali na tashin hankali.

Dan shiru yayi Yana cewa"

Bazai yiyi nazo gobe ba sbd Kar takardun nikadai lawyer bazan iya zuwaba Dole sai munje tareda wani lawyern Wanda zai duba takardun dazanje dasu agurin dama wannan Dole 2 lawyers ne suke zuwa Dan Haka Ina buqatan time Zan nemo wani lawyer din Wanda zai bamu time dinsa yazo taredani.

Shiru afia tayi cikin tsoro da tashin hankali tace"

Baza'a iya jiraba damace dad yabawa mum Dan Allah kazo kawai an zamu samu wani lawyer din.....

Shiru tayi cikeda nazarin abin data tuno na cewan NURU ma lawyernce
Wani sanyi ya lullubeta ta maida wayar kunnenta tana cewa"

Kazo NURU is here nasan zataje tareda Kai Inshallah zanyi mgn da ita.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 44_*

_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_

_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_

_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*

_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*

_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*

_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*

_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_*

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*

_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*

_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_*

****************
Shiru Imran yayi Jin sunan NURU data ambata Yana nazarin abin cikin ransa sbd baya fatan samun wani kebantaccen lokaci dagashi se NURU Dan bazai iya riqe zuciyarsa ba,bazai iya danne kansa daga Mata tambyarda yaketa son Jim amsarta daga gareta Dan Dan kuwa zuciyarsa takasa amincewa ta yarda ba auren tilas neba akaiwa NURU Dan batada gata,
Yanason ji daga bakinta cewar ta aminnce da auren kokuwa haryanzu tana sonsa Dan a shirye yake daya qararda duk abinda shida mahaifinsa suka mallaka Dan ya kwatar Mata yancinta a warware aure abarta da Wanda ta zaba Dan Haka wannan alqawarinane duk suka hadu harsuka samu damar magana yanada burin sanin raayinta akansa da aurenta Duk da Haka baiso haduwarsu tazo ta wannan hanyarba Dan shi me kishine bazaizo NURUn taje irin wurin Nan ba duk da aikintane Amma baida niyar barinta Koda shine ya aureta ta ringa shiga irin wainann cases din.

Numfashi ya sauke tareda boyayyar ajiyar zuciya ahankali kafin ya bude Baki yace"

Ba damuwa zan bincika tafiyar inshallah zanyi kokari ko cikin Daren nan ne na taso ko gobe tunda safe kifada Mata.

Aje wayar yayi Yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare Yana rufe idanuwansa da Basu Gama dawowa daidaiba tun ciwon dayayi ya warke
Ya miqe tsaye Yana jefar da wayarsa kan kujera sbd wasu feelings dinsa da afia ke Shirin tado Masa kokuma Tama tado Masa shi akan soyayyar NURU data fara koyawa kansa dangana.

Afia kuwa tana aje wayar taji hankalinta ya Dan kwanta sbd tanada tabbacin mum dinta zata samu damar fara wata kyakkyawar rayuwar koba a gidan dad dinta ba tana Mata fatan samun rayuwa kwanciyar hankali da nutsuwa tareda sauyawa Dan kuwa wannan al'amarin daya faru babban darasine gareta.

Tana buqatan mgnar da NURU gashi ba waya hannun NURUn sai kawai ta fito da kanta zata nufi gurin NURUn tasamu tsaro a bakin sashinta tareda umarnin ba fita koina sai gobe.

Da mamaki ta kalli Wanda yake shugaban tsaron tace"

Daga Ina umarnin yafito?

Sauke Kai yayi cikin nutsuwa yace"

Daga gurin MALEEK.

Siririn numfashi ta sauke tareda hakura ta juya Takoma batareda tace komaiba sbd daga yanxu umarnin dad dinta abune me girma a rayuwarta da bazata iya tsallakewaba badan alfarwar da yayiwa mum dinta kawai ba hadda tabbatarwa datai shine komai nata samun mahaifi kamarsa sai antona.

Dawowa tayi ta nufi bedroom dinta Kai tsaye ta tube sai alokacin tasamu damar qwarin watsawa jikinta ruwa tanajin al'amarin ya warware Mata Inshallah.

Acikin Daren ranar Mr Omar yayi qwalailar bincikensa tareda yonasi wani jami'in tsaron maleek suka gano jaridar data fara wallafa labarin
Suka zurfafa binciken daya nuna Kai tsaye jaridar ta fitarda labarin ne tun qarfe shida na safiyar ranar alhalin ba'a Kuma maganar kisan Bata bayyanaba sai qarfe takwas na safe ma su maleek suka Isa gurin Kuma Basu Kira hukuma ba sai qarfe Tara hakan ke nuni da labarin yasamu masu jaridar ne kamar ma tun cikin Daren da abin yafaru kenan kafin afkuwar abin ma.

Da wannan aka Isa gidan jaridar Kai tsaye aka kama shugaban companyn zuwa headquarters Kai tsaye Maleek yabada umarnin rashin sassauci ga binciken mutumin Wanda dam jira suke su Kuma jamian tsaron suka hau gana Masa azabar data sakashi saurin bada bayani Nan take cewar wani ne acikin Daren yakawo Masa information din saidai baiga fuskarsa sosaiba.

Kallonsa commissioner din yayi Yana jinjina Kai yace"

Me kagani Wanda zaka iya tunawa game dashi Wanda zai taimaka Mana nemosa da kanmu?

Wahalallen numfashi ya sauke Yana hadiye yawunsa dasuka gama gauraya da jinin dukan da akai Masa yace"

Idanuwansa zuwa saman hancinsa sbd Yana sanyeda baqin nose mask.

Ajiyar zuciya commissioner ya sauke tareda Mr Omar Wanda dama Allah Allah yake su samu bayani me kyau dazai bada hujja me ma'ana ya kalli commissioner Yana cewa"

Zansaka aturo Mana Wanda zai Mana sketch yanzun Nan kafin safe nakeson agama inshallah.

Juyawa yayi ya fice commissioner yasa aka maida managern aka rufe Kafin a me sketch din yazo.

Daganan Kai tsaye Maleek Mr Omar yakira ya sanar Masa komai
Shiru MALEEK yayi na 'yan mintuna kafin ya Dan motsa tareda bude Baki yace"

Kaje da kanka gurin tareda wani me sketch din gurinta itama ayo na idanuwan Wanda yakai Mata meriz sai ahada agani Dan nasan mutum dayane sbd tabbatarwa.

Bayan Mr Omar ya tabbatarda anfara zana fuskar Wanda managern gidan jaridar yagani tukuna cikin tsakiyar Daren ya wuce delah Ana fitowa sallar asuba Yana sauka ya wuce Dan aiwatarda dayan aikin.

Qarfe takwas na safe afia ta Isa sashen NURU Kai tsaye bedroom dinta ta nufa har lokacin NURUn na bacci ta tashi ba saidai kasa hakurinda afia tayi yasa ta tada ita ahankali tana Kiran sunanta.

Bude ido NURUn tayi ahankali tana kallon afia dake tsaye tana kallonta cikin kulawa tace"

Sorry na tasheki
Ina tsananin buqatan taimakonki ne Dan Allah.

Da mamaki NURUn ta tashi zaune tana tattare gashinta ta dauki band gefen gadon ta daure gashin tana yaye bargonta tace"

Lafiya dai Ina ko??

Ajiyar zuciya afia ta sauke tareda juyawa ta nufi sofa ta zauna tana kallon NURUn tace"

Ki kimtsa tukuna sai muyi mgnar.

Zuro qafafunta qasa tayi tareda miqewa tsaye sanye cikin kayan bacci riga da wando masu santsi farare tas sun lafe jikinta ta nufi toilet tashige tana waiwayen afia akan tunanin ko wani abun yakuma faruwane.

Brush kawai tayi takasa wanka sbd hankalinta yafara tashi akan tunani da wasi wasin lafiya.

Tana fitowa Palo ta fito inda afia din Takoma ta zauna tana Dan kallon tv sama sama Amma hankalinta nakan yanda NURU zata karbi zancen saidai tasan yanada wuya takasa Mata wannan alfarman tunda aikintane.

Zama NURU tayi kusada afia din tana kallonta dukkanin hankalinta akanta tace"

Gani menene??

Numfashi afia tasake sauke akaro na biyu tana kallon NURUn cikin nutsuwa da nuna damuwarta da mahimmancin da maganar take dashi agurinta tace"

Maganar mum dinace yau nazo neman alfarma dama taimako agurinki,
Kinsan yanda nakeson mahaifiyata dakuma yanda nasamu wannan sassaucin yazo gareta, Dan Allah ko Zaki min alfarmar cika sauran formalities na karbota a matsayinki na lawyer duk da nasan Baki Gama zama cikakkiyar lawyer din ba Amma dai kinada damar zuwa.
Akaro na farko yau Ina roqonki wata alfarma Ina fatan Kuma Zakiyi sbd Ni Dan nasan abinda mum tayi Miki Bata cancanci ki taimaka din ba Amma Kuma Ina roqonki kiyi sbd Ni da farhat.

Tsit NURU tayi tana dauke wuta sbd Bata taba tunanin wannan maganar ba bama ta taba kawo tunanin shiga cikin wannan al'amarin ba gaba daya
Musamman na mum din afian Wanda shigarta kamarba bazai yiyuba sbd ba ita ke ikon kanta ba hakama ita tayaya zata iya zuwa Kai tsaye wannan aikin?¿
Kasa cewa komai tayi ta dago ta kalli afia batamasan me zata ce Mata ba Dan neman alfarma agurinta da afia tayi kamar abune da bazata iya cewa aa ba hakama Kuma tanajin shakkar amincewar sbd batamasan ta Yaya zata sanar da Wanda yake ikonta zancen.

Ganin Shirun NURUn yasa afia shiga damuwa takira sunan NURUn tana cewa"

Bazaki iyaba right???

Zubawa afian ido NURU tayi tana sake shiga tunanin rasa abin cewa ta girgiza Kai ahankali ta bude Baki tace"

Afia Babu alfarmar dazaki roqa gurina nakasa Miki matuqar Bata sabawa ubangiji bace saidai ta Yaya za'a sanarwa dadynki Kuma Kinga.....

Katseta afia tayi da cewa"

Dad dakansa jiya gabanki yabada damar komai gameda case din mum din wannan maganar ta sirrice yanzu idan nace zamu dauko lawyer daga waje then komai zai iya sauyawa
So please NURU ki amince dan Allah dad Bai taba dakatar damuba ko hanamu harkan data shafi karatu bare yanzu aiki Dan Allah ki yarda Ina roqonki.

Dagowa NURU tayi takalli afian tareda Dan sauke ajiyar zuciya tace"

Na amince Amma sai dad dinki ya amince Zan nema izininsa.

Shiru afia tayi tana kallon NURUn tana nazarin abin data fada din saidai tunda ta amince batada zabin daya wuce itama amincewa da bayanin tace"

Thank you.

Miqewa tayi zata fice ta dakata da cewa"
Anjima Imran zai iso inshallah saikuyi mgna.

Ficewa tayi tabar NURUn zaune mamaki na kasheta Jin da Imran zasu tafi kenan.
Faduwa gabanta yayi sbd tunani biyu dasuka shigeta take,
Na farko ta Yaya zata fadawa MALEEK maganar zuwan harda qarin Imran ne abokin aikin,
Ma biyu tayaya zata iya fita daga ita sai Imran bazata iyaba sbd tasan Imran din sai yayi kokarin tado Mata da maganarsu data wuce wadda hakan baya cikin abindata shirya dawowa dashi.
Bangare daya afia nason daureta da jijiyoyin jikinta.

Daqyar ta iya tashi daga Inda afian ta barta ta nufi bedroom tafada toilet jekadi dake jinsu batace komaiba ta juya ta fice daga sashen Kai tsaye ta nemi numbern Mr Omar ta fada Masa komai yace idan yadawo zai sanarda maleek.

Qarfe goma Sha biyu na ranar Mr Omar ya sauka a airport na gizah na dawowarsa Dan yagamo abinda yaje Yi Kuma adaidai lokacin Imran jalal ya sauka a airport din cikin sa'a suka hadu dukkaninsu motar masarauta tazo daukansu shi Mr Omar drivern maleek yazo daukansu shikuma Imran drivern Anneti afia tasaka yazo daukansa.

Kallon kallone yashiga tsakaninsu Mr Omar ya saki wani murmushi Yana miqawa Imran din hannu yana kallonsa yace"

Barka da zuwa Barr Imran jalal and all the best.

Miqa Masa hannu Imran yayi Yana cewa"

Thank you Mr Omar.

Murmushi Mr Omar yasake sakewa Yana Dan kallon gefen Imran din yace"

Kai kadai kazo??
I mean nasan kasan kana buqatan wani lawyern ga aikin.¿

Sai alokacin Imran yasaki murmushi Yana kallon Mr Omar din yace"

Aikina ne Kuma nasan da hakan shiyasa lawyern da nake buqatan muyi aikin tare tana Nan Dama
Fata dai kawai idan zaka iya jimirin ganin hakan.

Wani irin Murmushi me Fadi Mr Omar yasake Yana sake cewa"

Good luck with that too."ya juya ya wuce Yana sake sakin murmushi yashige mota aka jashi sukabar Imran din a tsaye Yana bin motar da kallo kafin ya sauke numfashi me zafi yashiga tasa motar da akazo daukansa suka wuce Suma Yana Jin tamkar zuciyarsa nason karbuwa da qiyayyar Mr Omar sbd koyaushe shine yake shiga hancinsa da kudundune Amma sbd qiyayya bata cikin abindayake Bari Yana shigarsa yasa yake yaqar hakan Yana dannewa sbd ya dauki qiyayya wani aikin wahala da kake dorawa kanka yazo Kuma ya ringa wahalar dakai ka rasa focus da sukunin rayuwa karshe ka wargaza kanka agurin qiyayyar wani.

Kai tsaye dukkaninsu masarauta suka nufo cikin sa'a kusan atare motocinsu suka iso Mr Omar ya wuce Kai tsaye sashen maleek daukeda sketch din dayazo dashi daga delah shikuma Imran afia ce da kanta ta bada umarnin kaisa sashen baqi na musamman kafin ya huta suyi mgn.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 45_*



*_Mamuhgee 44_*

_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_

_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_

_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*

_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*

_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*

_*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*

_*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_*

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*

_*from lavender Catering

Please Login or Register in order to submit comment