Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

delah gizah??

Yana miqewa yace"

Eh Anneti tasamu attack na zuciya yau da safe.

Yana fadar hakan ya wuce gabaki daya.

Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na bugawa tana nanata zancen tafiyar.

Kasa yadda da tafiyar dad dinta zuciyarta tayi dari bisa dari sbd zuwansa zai iya kawo komai na lalacewan faranta da adduar datai shekaru tanayi na ganin dawowar iyayenta tare,
Shin Tata dad zaije delah gizah yanzu bayan zuwansa batareda matarsaba zai bayyanawa duniya cewan sun rabu Wanda hakan daidai yakeda rasa qimarsa da darajarsa hakama Kuma hakan zai jawo kokuma bada damar shigowar wata cikin rayuwar mahaifinsu ko Mata ko negestati.

Dafe kanta dake neman tarwatsewa sbd tsananin tarin damuwa data sawa kanta akan wani irin zazzafan kishi datake jiwa mahaifiyarta Dan haka bazata iya Bari dad yayi tafiyar Nan gizah ba sbd sanin tsananin qarfin iko da dokoki tareda al'adun mulkin irin na delah gizah.

NURU dake cikin Tata damuwar me nauyi tana zaune gefen AFIA din taji yanda takeda sauke ajiyar zuciya alaman Bata cikin kwanciyar hankali ko daya ta bude Baki ahankali cikin kulawa tace"

AFIA kinada damuwan wani abune?kimata sauke ajiyan zuciya.

Kasa waiwayowa tayi takalli NURUn sbd idanuwanta dasukai zuru zuru sbd masifar data sakawa ranta ta kishin mahaifinta ga wata mace
Batareda ta juyoba tace"

Bakomai kawai kaina na ciwo ne shima inaga sbd rashin bacci ne da bansamu nayiba jiyan.

Kafin NURU tayi magana ta miqe ta nufi toilet tashige ta rufo qofa.
Hawaye takeson Yi Amma ta daure tana kallon fuskarta cikin mirror ta rintse ido tana Jin shin mum dinta ta cancanci wannan fadan datake tare Mata kuwa?
Shin idan ta dage ta Hana dad dinta rayuwa da wata mace akan Taya mum dinta kishi tayi adalci a tsakaninsu kuwa bayan mum din itace ta lalata komai tayi watsi dasu ta tafi neman duniya wadda idan ba Allah yasoba har abada bazata samu duniya irinta dad dinsu ba.

Share hawayenta tayi tareda wanke fuskarta ta dauro alwalar azahar datai ta fito tana qoqarin sakewa Dan kawarda tambayoyin NURU akanta.

NURU dake binta da ido ganin babu damuwar komai a kan fuskan AFIA din sai tabar tamabayarta tana sauke numfashi Dan harta fara shiga tunanin kodai maganartane da Imran tazama matsala tunda tasanma kila zuwa yanzu yagama fadawa MALEEK komai.

Farhat ce tashigo daukeda littafi a hannunta tayo gurin NURU ta zauna kan cinyarta tana cewa"

Lewa nakasa gama wannan dubamin kigani.

Sallah Afia ta tayar tana dauke tunaninta daga kansu sbd Sam Babu Wanda zai gane abinda takeji.

Tana idar da sallar tadawo cikinsu suka cigaba da abinda sukeyi da ita Dan tasamu ta fitarda tunani da damuwardake azalzalar ranta.

Har dare tana sintirin yawo tsakanin Palo da 'dakinsu akai akai sbd tanason ganin dad dinta akan ko tafiyarsa delah gizah na Nan.

Har suka kwanta Bata samu ganin dad dinba sbd bai dawoba koya dawo ya wuce sama ya shige Bata saniba gashi tana Kiran Mr Omar Amma wayan Bata shiga haka ta hakura ta kwanta badan taso ba.

Washe gari da safe daga NURU har Farhat sun wuce makaranta ita kadaice Bata tafiba sbd ta sakawa ranta zata zauna harsai tasamu yin magana da dad dinta.

Guraren 11 na safe kuwa saigashi ya sauko qamshinsa na gauraya palon ahankali ahankali sai kyakkyawar fuskarsa dake kame kamar koyaushe
Tai Masa kallon qaunarsa amatsayinsa na mahaifinta datake tsananin kauna da alfahari dashi ta miqe tsaye tana aje laptop din dake kan cinyarta tana amfani da ita ta saki wani siririn murmushi tana qarasawa gurinsa tace"

Good morning dad,barka da fitowa.

Kallon kyakkyawar fuskarta dake yanayi da tasa yayi Yana alfahari da ita sbd juriyarta da iliminta tareda hakurinta ya bude Baki da muryarsa me amon iko yace"

Morning li'iliti(princess)

Murmushi tasake saki tana kallon dining din dayake qoqarin zama tace"

Dad can I join you?

Batareda ya dagoba yace"

Sure princess.

Janyo kujeran dining din tayi ta zauna tana cewa" thank you abal.

Tsit gurin ya dauka suna cin abinci Babu me mgnar sai ita dake cin abincin ahankali sbd son fara kawo zancen tagaji da wasi wasin yin zancen ko kartayi kawai saita kasa dannewan ta aje spoon din hannunta a natse ta kallesa da taushin murya tace"

Dad Yaya jikin Anneti(sarauniyar mahaifiya/mahaifiyarsa)
Zaka tafi tafi gizah kenan dad?

Dan kallonta yayi tareda sassauta fuskarsa ya gyada Mata Kai.

Sake gyara zama tayi cikin tausasa harshenta da bayyanarda damuwar data Dade da dannewa cikin ranta da biyayyarta ga dad din nata tace"

Dad maganarku da mum zai fito fili idan kaje....shiru ta Dan Yi tana kallon kamewar fuskarsa ta daure taci gaba da cewa"
Idan zancen ya bayyana cewan mum ta tafiyarta tabar...... kallo daya yayi Mata da fararen idanuwansa takasa qarasa sauran zancen ta marairaice fuska tace"

Dad please ko zaka duba kagani kodan sunan mum da naka dazai iya baci.

Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa tsaye ya kalleta yace"

Take care princess"ya wuce.

Kasa motsawa tayi kanta na toshewa sbd hakan na nufi zancenta be karbu ba agurin dad dinta sbd hakan da yayi shine rashin amintarsa ga zance idan ankawo Masa.
Miqewa itama tayi tabar gurin Takoma daki ta zauna ta jawo waya ta Nemo numbern mum dinta tafara tunanin takira ko karta Kira,
Fasa Kira tayi tai wurgi da wayar tareda Miqewa tsaye ta sauya Kaya ta fito tashiga mota ta fice daga gidan Dan zuwa dauko NURU datasan yanzu ta Isa gamawa tunda ita yau Bata samu zuwaba.

Tunda suka dawo taketa qoqarin cire damuwarta sbd kada NURU tagane saidai NURUn tana lure da ita saidai batason takura Mata da tambaya sbd batasaniba ko matsalar ta sirrice.

Kwana sukayi ahaka suka Kuma yini ahakan har akai kwana biyu
cikin kwana biyun duk ta Hana kanta sukuni da tunanin al'amarin Wanda take ganin rushewa familynta zaiyi idan wata tashigo cikinsu amatsayin matar dad dinsu ko negestati
Itadaima tafi son iyayenta su shirya koma menene hakan yafi shigowar wata cikinsu.

Ganin dai dagaske AFIA na cikin damuwa me qarfi boye kawai take yasa NURU kallonta bayan sun kwanta tace"

Afia koma menene abindake damunki please ki rage idan bazaki iya ciresaba ko hakura dashiba sbd wannan damuwan naki bamajin dadin ganinki ahaka ko farhat dake qaraman yarinya tafara cewa menene akaiwa AFIA.
Please AFIA kicire koma menene kibarwa Allah a rayuwa dama akwai hakan duk da nasan ke koma menene damuwan ba wani babba bane sbd Babu wani abu najin dadin duniya da Kika rasa Dan Allah ki cire damuwan please baby.

Tunda tafara magana afia ke kallonta sbd wani tunani daya shigota na sha'awar bin dad dinsu gizah Dan koma menene tafison tanacan zatafi samun saukin hanawa kokuma handling maganar rabuwar iyayenta taqi barin ta fita Dan kuwa tasan daga lokacinda maganar ta fita MALEEK na gizah bazai qara awa ashirin da huduba Batareda Matar aure ko negestati ba Dan haka zasu bishi Dan toshe yiyuwar hakan Dan kuwa idan hakan tafaru dad dinta bazai karbi mum dintaba har abada Wanda ita Kuma akan hakan ko kamawa tayi tayi amfani da NURU zatayi Dan Hana wata shigowa rayuwar dad din daidai NURU tayi hkr but she'll have to use her innocence.
Wani numfashi mara karfi ta saki tareda kallon NURUn cikin kauna da kulawa ta riqo hannunta ta rungume tace"
Thank you my NURU" ta rufe idanuwanta ahankali bacci na daukanta.


Washe gari haka ta tashi cikin walwalarta da sakewarta har hakan yasanya NURU da farhat farin ciki sosai har wasan ruwa da basketball sukai yau da yamma a playground Wanda duk abinda sukeyi dad dinsu na gidan dan haka Koda daddare yau taredashi sukai dinner Banda NURU dataqi fitowa tea kawaima Tasha sbd karatun data duqufa dayi Dan gobe tanada zuwa wani court yin wani aikin 4hours dake cikin karatunta.

Acan dining kuwa AFIA ta sanarwa dad dinta sunason binsa Dan Suma su dubo Anneti.

Kallonta yayi kadan tareda maida kallonsa kan farhat dake cewa"

Yes daddy Nima zanje Kuma zamuje da Aunt NURU ma ko AFIA?

Kallon bakin farhat din dako yaushe yake furta sunan NURU ko lewa yayi tareda dauke Kai Yana goge bakinsa yace su zama ready jibi ne tafiyar.

Cikin murna dukkaninsu sukace thank you dad.

Bayan fitarsa NURU tafara wucewa court kafin afia ita Farhat yau Babu zuwa school dinsu.

Sai yamma sosai suka dawo duk su dukansu Koda ta shigo tana waya da Imran da duk yabi ya sukurkurce Mata da cewan amatse yake da MALEEK yabawa su dad dinsa lokacin zuwa.

Murmushi kawai tayi sbd Bata taba tunanin maleek daya Bata ingantacciyar rayuwa tareda 'yayansa zai Bata ingantacciyar rayuwa ta har abada ba ta hanyar bada damar azo neman aurenta Dan tunda haryace idan yadawo zai Basu Daman zuwa ayi magana kenan da yiyuwar barinta tayi aure da rayuwar aure kaman kowaba babban mamakinta data kasa yadda dashi shine yau itace tasamu damar ace MALEEK na Delah gizah guda shine da kansa zai bada aurenta tabbas wannan tunanin idan yafado Mata kanta da tunaninta kasa dauka suke.

Ga tarin dibbin mamakinta tana shigowa Palo Imran suka tarar zaune Yana sako Mata murmushi da wani irin kallon Sonta daya gama yiwa tunaninsa da zuciyarsa mugun kamu saiyakejin kamar bazai iya rayuwa Babu itaba Dan kuwa komai zai iya faruwa dashi idan bai samu NURU ba amatsayin matarsa uwar 'yayan dazai Haifa.

Afia na ganin hakan ta wuce ciki tana Masa dariya da cewa"

Uncle Imran take it easy fa kada ka rasa 6sense dunka akan soyayya mu shiga uku barr IMRAN jalal ya zauce.

Da wata Yar dariyar qarfin hali yabi afia da zancenta idanuwansa suna Jan NURU dake tahowa cikin dogon wando da farar riga sai black scarf daure kanta duk da agajiye take sosai kyawunta ke bayyane tana qarasowa gap dashi ya miqa Mata cup din drink me sanyi da aka kawo Masa Yana cewa"

Have this my love kingaji ko?

Murmushi tasakar Masa takai hannu takarba takai bakinta ta kurba kenan idanuwanta suka sauka cikin na MALEEK dake tsaye da waya a kunnensa yanayi daga Palon ciki take ta qware da qarfi tana sakin tari ta miqawa Imran cup din tarinta na tsananta sosai
Cikin sauri da kulawa ya miqe Yana qoqarin Kai Mata cup din ruwa bakinta Tasha kozata ji sauki sauki sai kawai yaji anriqe cup din ya juyo da sauri sukai ido biyu da Mr Omar dake kallonsa cikin ido Ras ya Dan sake fuskar wata gantalalliyar murmushi tafito Masa yayiwa mum Sarah dayazo da ita kallo daya tayi saurin kallon NURU tana riqota tana Mata sannu tajata sukai ciki
Saida suka shige ya dago ya kalli Imran cikin girmamawar data so kularda Imran yace"

Barr IMRAN idan Babu damuwa zamu iya zuwa palon baqi dake gefen wannan sashen sbd dokokin gidan sun Dan qara tsauri yanzu Babu me sake shigowa sashen MALEEK dagashi sai 'yayansa.
##MAMUH#




_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*
*_Mamuhgee 18_*

Oumahmad collection's
07014488636
Kitchen utensils
Fabrics
Shoes nd bag
Phones
Veils
Children's wears
Furnitures
Dubai,china,India,turkey,Malaysia
Kano hotoro
Fcbk Maryam muhd.



**************
Shiru Imran yayi yana bin Mr Omar da ido baice komaiba sbd Kamar bai gama fahimtar me Mr Omar dinba yace Kuma baiyi abinda yace mishi yayin ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice daga Palon Yana fita harabar gidan ya shiga motarshi ya fice Dan Yana buqatan samun iska me kyau Dan yayi refreshing kwakwalsa dayakejin kaman ta toshe baya gane komai.


Mr Omar mabayanshi yabi da wani irin kallo mai ma'anoni da dama, ciki kuwa harda na tausayawa dan ya hango tsantsar soyayyar Nuru a cikin kwayar idonshi wadda yasan abin kamar da wuya Dan kuwa zancen me girma ne dayafi qarfinsu su 'yan qasa qasa Dan kuwa yana da tabbacin aure tsakanin Nuru da Imran ba abune me yiwa ba duk da dai fadan hakan ba huruminsa bane.
Dan

A bangaren Nuru kuwa karfin hali kawai take har lokacin gashi AFIA ta nace Mata akan tafiyar da zasuyi sai anje da ita Wanda takega kaman ta wuce huruminta Binsu delah gizah ziyartar kakarsu uwa sukutum ta MALEEK,
Amma ganin batada zabi na kanta ko ikon kanta Dole ta shirya 'yan kayanta da basuda wani yawa yawancima dogayen riguna ne Dan Bata dauki me wando ko dayaba da zai nuna tasamu dama da sake da yawa.

Tana zaune jikinta a matukar mace tana qarasa hadawa Farhat kayanta cikin nata pink akwatin me hoton frozen sisters saiga Farhat din ta shigo da gudu ta zauna kan jikinta tana cewa"

My Lewa please kumana pancakes me Honey and chocolate.

Kallon bakinta NURU tayi tareda sake murmushi tana kamo fuskanta tayi kissing goshinta tana cewa"

Kome farhat din aunt NURU takeso za'a Mata.
Muje cikin din yanzu bada dadewaba zakici pancakes sweetie.

Kicin suka nufa tana riqeda hannunta suna shiga ta dorata kan kitchen island ta zauna ita Kuma tafara hadawa farhat din na tayata fira.

Bayan sun gama a kitchen din suka ci nasu saidai na AFIA suka aje Mata a dining.

dakinsu ta nufa ta tararda Afia a kan doguwar kujera rigingine idanuwanta a lumshe ta kifa littafi saman cikinta da alama karatu take bacci ya dauketa batare data sani ba.

Murmushi Nuru tayi ta gyara mata kwanciya ta lullube bargo me taushi kafin tayiwa Farhat wanka ta shiryata cikin kayan bacci marasa nauyi ta kwantar da ita anan dakinsu itama ta nufi toilet din tayo wanka tareda dauro alwala tayi sallar ishai kafin ta Sanya kayan bacci irin na farhat din riga da wando dogo saidai rigar batada hannu sai siriri hakama kayan nada roba ajiki sai suka kwanta jikinta sbd kusan kayan baccinsu su duka ukun duk za'a siyo iri daya ake siyowa saidai banbancin size.

Ta hau gadon zata kwanta farhat ta motsa cikin bacci tace"

Aunt NURU water please.

Kallonta tayi da idanuwanta dasuke Jin bacci tace"

Ruwa farhat??

Yes aunt.

Numfashi ta sauke tareda zuro qafafunta qasa ta saka slippers din dasuke yawo dashi cikin gida ta miqe tsaye tareda daukar qaramar hula ta saka akanta dabai rufe dukaba ta fito.

Al'adarshi ce fitowa cikin dare ya duba inda ya kamata saboda tsaro da fita hakk'in na k'asa dashi, yana kula da ransu da lafiyarsu, dan duk da Maleek ya kasance mutum mai izza da mulki hakan bai sashi ya manta dokokin Allah dake kanshi ba, yana k'ok'arin sosai wajen kaucewa hakk'in mutane, dan haka lokuta da dama yana fitowa cikin dare ya duba lafiyar iyalinshi da sauran mutanen gida.

Ba ruwanshi da lek'awa d'akin kowa dan yasan muhimmancin Privacy sosai iyakacinshi kawai ya duba inda ya kamata.
Ganin haske a cikin yasashi kallon hanyar tareda nufowa cikin nutsuwa saidai bai qarasaba sbd tunda take rayuwarsa nai taba shiga cikinba tun girmansa a iya saninsa Dan haka sai ya tsaya iya dining musamman dayaji kaman motsi a kicin din.

Itakuma daukeda robar ruwa biyu a hannunta ta fito batama lura da komaiba tabi ta gabansa ta wuce saidai taku daya ta qara ta tsaya cak zuciyarta na sauya bugawa sbd idan hancinta yajiyo Mata daidai qamshin MALEEK taji agurin.

Juyowa tayi ahankali Wanda yayi daidai da qarasowarsa zaibar gurin jikinsu ya hadu da sauri tayi baya tana sauke kanta kafafunta na son daukar rawa yayi Mata kallo daya ya wuce yabarta tsaye jikinta na neman yin sanyi sbd Tama rasa halin me tashiga a tsakanin tsoro da firgita.

Daqyar takai kanta daki ta tayarda farhat din zaune tana Bata ruwan abaki tana cikin Sha AFIA ta farka ta tashi zaune tana 'yar guntuwar hamma ta miqe ta nufi toilet.

Farhat data gama Shan ruwan da NURUn ke Bata ta daga Kai ta kalli NURUn tana sake shaqar jikinta tace"

Aunt NURU kina qamshin irin turaren daddy.

Cak Afia dake gaf da shiga toilet ta tsaya batareda ta waiwayo ba ta Kira Jin amsarda NURUn zata fadawa farhat din.

Kasa cewa komai NURU tayi sbd batasan mezata fada ba saidai jin alamar AFIA ta tsaya yasata bude Baki daqyar a Sanyaye tana kamo abinda zata samu cewa tace"

No sweetie hancin kine sbd kila kinyi mafarkin daddy yanzu da kikai bacci.
Kwantar da ita tayi tana cewa"

Koma bacci kinsan gobe akwai zuwa school da wuri gakuma tafiya gizah.

Ajiyar zuciya kusan suka sauke tareda AFIA ta zame ta kwanta gefen farhat din tana rufe idanu ba shiri itama Afian toilet din tashige tana sake sauke numfashi me sanyi.


Washe gari tun 8 ta fice zuwa school bayan tagama breakfast da Shirin farhat data wuce school itama ta wuce sbd Kira da massages dinda Imran keta danno Mata gabaki daya hankalinsa a tashe yake musamman data fada Masa cewan daita za'aje gizah din saiyakejin kaman ya bisu Dan har zuciyarsa tafara bashi shawarar aje contact din Nan daya riqesa Wanda ya Hana rayuwarsa shaqat bare sukuni.

Tana Isa makaranta a can ya tarar dashi harya rigata Isa da kallon mamaki daga ita har afia suke binsa musamman ganin duk yayi wani iri idanuwansa sunyi laushi kaman ma kwana yayi bai rintsa ba.

Cikeda tausayinsa suke kallonsa duk su dukan hardai ita NURUn da idanuwanta sukai rau rau hawaye na neman cikowa cikinsu sonsa na qara shigarta ta tsaya daf dashi tana kallonsa cikin kulawa me tsanani da taushin murya tace"

Im lafiyanka kuwa?
Kana lafiya?
Bakayi bacci ba ko?

Kasa Bata amsa yayi sai kallonta dayakeyi kaman zai hadiyeta afia na ganin hakan ta wuce tabarsu anan tana yar dariyarsu.

Motarsa suka koma suka jingina anan yafara zayyane Mata shawarar dayakeson yankewa ta ajiye aiki sai bayan aurensu tukuna ta girgiza Masa Kai tana cewa"

Karkayi haka im idan muka saka gaggawa a al'amarin zai iya zuwa da tangarda,
Dan Allah kabi komai a hankali.

Murmushi kawai yayi Yana kallonta Yana cewa"

Idan kuka tafi zanyi missing dinki my love.

I will miss you too im Amma fa ka ajiye maganar aje aikin Nan please.

Gyada Mata Kai yayi kaman qaramin yaro sai hakan yabata dariya ta murmusa tana Dan juyar da kanta gefe daganan ya suka fara fira yanata sake langwabe Mata.

Ranar ko wani karatun kirki batasamu yiba sai yamma dasuka dawo Wanda shine dakansa ya dawo da ita tun a gate yana ajeta ya juya ya wuce.

Batajin yunwa Dan taci abinci a makaranta Dan haka wanka tayi tai salloli tana idarwa tasake hada sauran kayansu na tafiya Dan yau da daddaren zasu bi jirgin Daren zuwa gizah.

Kasa zaune tayi takasa tsaye gabaki daya batajin nutsuwar zuciya data gangar jiki daurewa kawai takeyi Amma wlh tana cikin wani hali na tsoro da shakka na zuwanta can din sbd sanin matsayinta Kuma idan taje can Dole tayi bauta kaman sauran bayi matuqar ba maganar zamtowanta negestati zai fito fili ba kuma idan hakan ta fito fili Dole amiqata ga NEGES dinta Wanda duk wannan cigaban rayuwar data samu zai tashi a banza.

Daga ita har afia qarfin haline kawai sukeyi suna sakewa Kamar suna cikin farin cikin tafiyar Wanda kowaccensu cikin ranta a matuqar tsorace take kaman zuciyoyinsu zasuyi tsalle su fada kowa da bikin zuciyarsa.

Qarfe Tara na dare jirginsu zai tashi Dan haka suna sallame sallar ishai suka fito masu aiki na janye da akwatinansu dasuke kaman set Dan duk iri dayane,
Ita doguwar rigace purple ajikinta sai gyale light purple data daura sai handbag da wayarta da sauran Yan abubuwanta qananu dasuke ciki
Qafartama flats Versace ne black a sanye sai face mask data Sanya Dan kaman iska iska takejin yamata yawa.

Mota daya suka shiga su biyu itada afia farhat Kuma motar daddynta tabi.
Har aka Isa airport Babu me doguwar magana acikinsu sai yaqen Dole dasuke zabgawa.

Kai tsaye angama komai nasu suna zuwa ta baya qofar 'yan first class aka bi dasu suka shige duk da hakan maleek nata inda basa ganinsa Amma shi Yana ganinsu da haka jirginsu ya daga massage din Imran na shigowa ko budewa batayiba tasaka wayar flight mode ta saka cikin jaka.


Doguwar tafiya sukayi me nisa ta tsawon awanni masu Dan yawa kafin suka Isa lokacin har qarfe bakwai yayi na safiya.

Airport din cike yake da wasu irin matakan tsaro na musamman da aka baza koina sbd saukowar MALEEK da familynsa.
Motocin daukarsu guda hudune sukazo daukarsu wainda suke na musamman ne Dan kuwa dama Dan maleek aka siyesu zamansa suke duk lokacinda yazo Kuma duk shekara ake sauya Masa su ko ya zo kobai zoba.

Cikin motocin alfarma aka daukesu daga airport din motocin tsaro suna gabansu da bayansu aka nufi babbar masarautar delah gizah dake daukeda babban tarihin arzikinda ko Ina aka sani musamman sbd qarfi da girman mulkinsu.

Duk yanda ake fadar delah ta gizah NURU hankalinta yayi mummunan tashi sbd yau idanuwanta sun gane Mata Dan kuwa duk yanda take tunanin gizah ta wuce Nan,
Tsorone da kamewa suke shigarta dataga tsagwaron dukiyarda idanuwa basa iya gama kalla Dan kuwa ita ayau taga abinda Bata taba ganiba arayuwarta,
Delah dinsu ta can dasuke ganinta aljannar duniya sbd tarin dukiya da zallar mulki Ashe ba komai bace akan Nan asalin delah gizah.

Matakan tsaro ne tako Ina da askarawa da bayi kowanne akan tsari sbd mulkin na wayayyun Kaine mulkine na masu ilimin turai da addini,
Rayuwar masarautar delah gizah tafi tsauri da matakan mulki da zuba zallar ikon sarauta shiyasa duk inda ta kalla saita sauke Kai taji jikinta yayi sanyi musamman dataga yanda ake bawasu afia girma Kamar za'a musu sujjada sbd girmamawa hakama duk Wanda ka kalla ko a kuskurence Babu Wasa ko Sanya ga dukkanin wani Wanda yake qarqashin masarautar Dan kuwa ko doguwar sakin fuska babu tsakanin jinin sarautar 'yan delah gizah din da bayinsu kokuma masu aikinsu basusan komaiba sai rayuwar mulki da iko cikin wadata da arzikinda basusan Yaya zasuyi dashiba.

Babbar masarautace datayi hudu zuwa biyar din delah ta garinsu wadda wannan komai nata ma basai anfadaba kana shigowa zaka kame kanka da kanka sbd Wasa ko laifi kadan saiyayi sanadinka ashafe labarinka.

Komawa tayi ita abiye kawai take dasu afiyan dandai duk tagama Shan jinin jikinta ta kame kanta farhat ce riqeda hannunta Taki saki sbd ita duk Bata wani Saba da kowaba Anan din sai Anneti AFIA ce kawai tasan kowa ta Saba da kowa harma da rayuwar mulkin itama ta iya tsaf Ashe akwai a jininta Dan kuwa take itama ta rikide Takoma li'iliti AFIA UBAYD MALEEK dinta Wanda yasa NURU sake Kama kanta.
Shi maleek ma sunsan ganinsa ayanzu ko su dasuke 'yayansa abune me tsananin wuya agaresu Dan kuwa ayanzu MALEEK yafi komai tsada da wuyar gani a gizah Dan kuwa tsaron dake hanyar zuwa sashensa ko asalin sashen NEGES (sarki) bai samu tsatsauran tsaro ba Kamar nasa sbd shine asalin MALEEK na kujerar kowa yasan shine sarki kawai dai mulkin baya hannunsane Wanda shine yaso Kuma bai tashi karba bane Dan hakane yasa matuqar MALEEK na gizah to kowane irin tsaro da matakai sun ninku.

Babban sashen dake maqale Dana Anneti mahaifiyar MALEEK anan ne masaukinsu dama Wanda yagama Jin gyaran Jin dadin duniya.
Bayine da masu hidimarsu birjik a qaton babban daki guda dake gefen part din Wanda aka zuba musu gadaje irin na Yan makaranta masu hawa bibbiyu su anan suke rayuwa aikinsu kawai shine duk ranarda iyalin maleek sukazo sune masu hidimarsu.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899
*_Mamuhgee 19_*


Assalamu alaikum, ina masu son su iya baking da decoration na birthday cake wanda idan aka kalla sai an kara kalla๐Ÿ˜‡

toh ga dama ta samu er uwa kiyi maza kiyi rigista, sannan zaki koyi ydda ake hada whip cream din da yke daukar awanni ba tare da ya narke ba๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

zaki koyi ydda akeyin vanilla cup cake mai dadin gaske๐Ÿ˜‹ er uwa ba'a iya nan muka tsaya ba zamu koya miki ydda akeyin chocolate bar cookie domin farantawa mai gida da baki๐Ÿฅฐ

kuma duk akan kudi naira 3500 kacal๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
Online class neh full vedios kamar a gabanku akeyi, tare da note da voice note ydda zaku fahimci komai cikin sauki๐Ÿ˜‡


kada kubari wannan dama ta wuceku๐Ÿค—
Domin neman karin bayani ki kira: 07089621678
I.G handle: Umsad cakes nd more๐Ÿ˜



*******************
Zama NURU tayi a makeken royal bed dinda yafi Kama Dana kwanciyar mutum hudu zuwa biyar sbd girmansa ga wani irin ado da komai na dakin yasamu kana shigowa komai na masarautar ma kana gani kasan kana cikin palace.
Sake wani marayan numfashi tayi zazzabin daya kamata Yana sake qarfafa ajikinta Dan

Please Login or Register in order to submit comment