Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa itadai batamasan menene matsayin dazata dauka anan din ba,
Shin me Reno?
Kokuwa baiwa?
Kokuwa negestati?to idan negestatin ne to ta wa?

Dafata AFIA tayi tana zare dankwalin kanta dake nade da dogon gashinta ta zauna tana miqar da hannuwanta a gajiye tace"

NURU Yaya dai?
All okay right???

Dan dagowa tayi jiki ba qwari ta kalli afia din saita sauke kanta tanajin kallon afian ido cikin ido yanzu ba nata bane kila kozasu koma yanda suke sai sun koma gida.

Cikin sanyin harshe tace"

Headache ke damuna Amma inaga na gajiyane zai saki idan na huta.

Cikin kulawa afia tace"

Sorry.

Gyada Kai kawai tayi tana sake dauke kallonta daga kan afia din.

Wanka sukai sauya cikin wasu irin dogayen rigunan alfarma wainda aikene na musamman daga sashen Anneti.

Babban makeken palon suka fito har zuwa dining Wanda yake shaqe taf da kalolin abinci da abin Sha tareda snacks da fruits kowanne sai daukan ido yake yanda aka jeresu kaman mutum goma ne zasuci abincin.

Zama suka farhat na gefen NURU sbd wata irin maqalewa data sameta tun zuwansu sbd farhat din nata rashin son shiga mutane masu yawa irin hakan shiyasa ma ko acan dad dinsu ya Hana bayi ko masu aiki da yawa sbd ko bayan farhat shima bayason guri da mutane da yawa komai girman gurin kuwa.

Cikin nustuwa da kwanciyar hankali sukaci abinci suka koshi suka koma Palo suka zauna aka aika da asanarwa da Anneti zasu zo gurinta kawo gaisuwa Nan da mintuna kadan.

Tunda saqon gasunan zuwa sashenta ya iso Mata farin cikinta ya Dada bayyanuwa sbd a duniya idan abinda tafi so da qauna shine MALEEK dinta da 'yayansa duk da kullum adduarta Allah yaqarowa UBAYD 'yaya masu albarka sbd tanason ganin zuriar UBAYD MALEEK ta yadadu Amma ga dukkan alamu kila hakan bamai yiyuwa bane sbd matarsa kowa ya lura Kuma ya fahimci batason yawan haihuwa.....Dan faduwa gabanta yayi da tunanin wani zancen binciken NEGES yabayar daya fada Mata yana ganin kaman UBAYD MALEEK Bata tareda matarsa.

Saurin rufe fararen idanuwanta da maleek duk su ya sauko tayi cikin wani irin hali na damuwa me tsanani tace"

Ya Allah ya kabar da wannan zancen akan MALEEK dinta Dan kuwa har abada ko amafarki Bata fatan ace hakan yazama gaskia Dan kuwa sbd wannan zancen da NEGES ya fada matane ciwon zuciyarta ya tashi Wanda tasa aka bugawa MALEEK Dan kawai yazo ta tabbatarda abinda hankalinta ya dagu da jinsa.

Saida afia ta tabbatarda zuwa yanzu saqon zuwansu ya isa gurin Anneti kafin suka dungumo zuwa gurin nata.

Tun a hanya NURU ke sake shiga taitayinta tana sake Kama kanta farhat dai na maqale da ita bayi uku na bayansu.

Fadar tsari da kyawun sashen mahaifiyar MALEEK bamai faduwa bane saidai kawai ace Masha Allah da wannan daula.

A babban palonta na kurya suka taddata suna shiga da sallama dauke a bakunansu Banda farhat data saki hannun NURU tayi gurin Anneti da gudu ta fada jikinta cikin tsananin farin ciki.

Farin cikin ganinsu ya Hana Anneti rufe Baki ta budewa afia hannuwanta ta qaraso da sauri ta rumgumeta tana cewa"

Kemiri nafik'akelewi ya Anneti (I miss you so very much Anneti/nayi kewarki sosai Anneti)

Murmushin farin ciki Anneti tasaki itama cikin yare da muryarta me tsananin taushi da dattako tace"

Masha Allah li'iliti takusa zama Mata agurin me gagaruman sa'a
Ya Allah ya albarki rayuwanku ku duka.
Amin sukace dukkaninsu har NURU dake tsaye Dana farko ta kasa qarasowa.

Idanuwa ta zubawa NURU dake tsaye tana kallonsu cikin burgewa suna hada ido tayi saurin sauke kanta tareda zubewa qasa ta durqusa tana cewa"

Barka da hutawa Anneti.

Har lokacin kallonta Anneti keyi sbd kyawun NURU da yanayin kyan fatarta dake haskota yasa take Mata kallon 'yar sarautar delah ce ta bude Baki cikin kulawa ta amsa mata tana maido kallonta kan Afia tace"

Wannan wacece??

Cikin sauri farhat tace"

Aunt NURU ce ta Dade agidanmu taredamu she's family.

Da mamaki tasake kallon NURU tana kallon afia data share zancen Dan batason fadar matsayin NURU na 'yar Taya zama da aka kawo musu ita wadda su tuni suka dauketa 'yar uwa ta jini wadda takewa kallon wani bangare na rayuwarta Dan kuwa qaunace me qarfi a tsakaninsu.

Jawo wani zance afia tayi ta hanyar cewa Nuru ta qaraso ta zauna acikinsu.
A Dan kakkame ta qaraso Amma Bata zaunaba saita zauna a qasa Yana cewa hakanma she's ok.

Ganin NURU da farhat yasa Anneti bataiwa afia maganar mahaifiyarsuba Wanda afia ta lura da hakan hankalinta yatashi sosai matuqa musamman batason ayi tambayar gaban farhat Dan zata fada cewar mum dinsu ta Dade da tafiya tabarsu.

Basu bar sashenba sai dare suna zuwa wanka sukai suka kwanta Banda NURU data fara waya da Imran.

Kasa bacci afia tayi tana saqa da warwara,
Babban abin tsoronta anan shine Dole ita Anneti zata tambaya mum dinsu Dan kuwa MALEEK ko sunyi mgnar da Anneti bazai taba fada Mata komai akaiba ita Kuma duk qaryar dazatayi na kawo wani excuse dazatace ya Hana mum zuwa bazai shigaba Dan kuwa Anneti zata gane komai Daren dadewa Dan haka take buqatan lokaci Wanda zatai amfani dashi ta shirya iyayenta kafin agano.

Da wannan tunanin tayi bacci takuma farka,
Washe gari ma agurin Anneti suka wuni saidai Banda NURU wadda ta Kama kanta ta zauna guri daya sbd yawo ba nata bane acikin masarautar gizah ta yayan masu masarautar ne
Sai washe gari dazasu yawon ziyara cikin masarautar zuwa sashe sashe na 'yayaye da sarauniyoyin gizah shine tabisu saidai tayi danasanin Binsu Dan kuwa sake tabbatarda rashin darajarta tayi shiyasa Bata Kuma gigin binsu ba idan zasu fita acikin gizah din ta Kama kanta ta zauna guri daya sai tunanin gida da iyayenta yadawo Mata Kamar sabo.

Duk yanda Afia ke zamewa Anneti sbd kada tasamu damar yimata maganar mahaifiyarsu yau da kanta taje gurinta Dan tabbatarwa da kaman jita jitan da kaman yakeson fita na rabuwar iyayenta din sbd shekaran jiya da jiya duk sashen dasukaje sai anyi tambayar matar maleek guda ace bataxo duba Anneti ba wane irin uzurine wannan.

Hakan yasa hankalinta tashi matuqa sbd tabbas Kam kowa zaiyi nasa tunanin daban daban ace Annetin delah gizah mahaifiyar MALEEK guda ace matarsa batazo dubata ba tabbas zance yafara bayyana take ta aika sako na musamman ga mahaifinta na cewa akwai karatu me mahimmanci a makaranta sunada buqatan komawa Kuma tana roqonsa daya koma taredasu sbd shine jigonsu bazaso komawaba bataredashiba.

Hakan datayi saiya sake saka Anneti cikin shakka da mamaki sbd sakon MALEEK saiya biyota gurinta yake Isa gurin maleek Dan haka ta aika aje akawo Mata farhat batareda sanin afia din ba.

Agurinta ranar farhat ta kwana da daddare bayan sunyi Shirin kwanciya ta kalli farhat din tana shafa Mata Kai cikin kulawa tace"

Farhat mamanki meyasa bata biyoku ba bayan ga abal dinku dayafita ayyuka yazo dubani??.

Kai tsaye farhat tace"

Mum ta Dade da tafiyanta munata kuka nida afia
Daddy ma da kansa yace idan ta tafi kada tasake dawowa yabata da ita koyaushe.

Wani mummunan bugawa zuciyar Anneti tayi har Saida ta dafe Dan kuwa kiris ne yahana ciwon zuciyarta tashi duk da hakan wani radadin tashin hankali takeji,
Idan dagaske MALEEK yarabu da lailah zancen yafito Babu ta yanda zai karbi mulkinsa Dan kuwa kaf a tarihinsu sarakuna basa sakin matansu wannan wace irin masifa ce.

Cikin tashin hankali tasake sanyaya harshenta tace"

Tun yaushe ne ta tafi?

Tun kafin aunt NURU tazo ne ta tafiyan munata kuka hadda Afia Amma tunda aunt NURU tazo daga delah jekadi takawo Mana ita shikenan muka daina kuka sbd Aunt NURU tana Sona sosai tunda tazo AFIA tadaina damuwa suka zama Best friends tanamun pancakes da komai nakeso Kuma daddy ma tana Masa abinci fa yafi nasu mum Sarah Dadi aunt NURU tafi mum sbd ita Bata barina Ina kuka Kuma tace bazata tafi tabarniba kaman yanda mum tayi idan sunyi aure da uncle Imran ma Dani zata tafi.

Wuta Anneti ta dauke gabaki daya
Numfashinta yafara yankewa tana dannewa,zufa kuwa kaman tana cikin dakin gashin biredi.

Daqyar ta iya daidaita numfashinta ta kalli farhat tana nazartan zantuttukanta daya bayan daya tana fahimtarsu tana kawowa inda farhat tace jekadi takawo musu NURU daga delah sai kawai ta tsaya anan ta shafa kan farhat din tareda kwantar da ita tana Mata addua har tayi bacci.

Palon hutawarta ta Isa ta zauna tareda daukar wayarta ta Nemo numbern jekadi ta Danna Mata Kira.

Cikin girmamawa me girma jekadi ta dauki wayar tareda zubewa qasa tana jerowa Anneti gaisuwa cikin tsananin girma.

Shiru Anneti tayi na mintuna biyu kafin tace"

Jekadi bayanin komai nakeso na NURU yarinyar dake zaune agidan MALEEK.

Tsit jekadi tayi tana juya zancen zufa na karyo Mata cikin tsananin ladabi da girmamawa tayi kasa da Kai kaman agaban Anneti din tace"

Allah ya taimaki Anneti kimun afuwa nafara tambayo izinin fadar wannan magana agurin KALEEB.

KALEEB?" Anneti ta fada ahankali cikin mamaki duk da tasan dama Dole Saida sanin Kaleeb jekadi ke komai.

Katse wayar tayi ta Nemo numbern kaleeb da kanta takirasa.

Kira uku tayi se Ana hudu ya daga cikin muryar girma da mulki take itama tayi qasa da murya tahau gaisuwa cikin tsananin girmamawa tana sake tambayarsa manyanci.

Shiru tayi bayan gaisuwar tarasa ta inda zata faro har Saida yayi gyaran murya a kame yace"

Kiyi maganarki kada ki damu kaleeb zai duba koma menene.

Cikin sanyin murya tace"

Allah ya taimaki kaleeb idan banyi shishigiba inason sanin wacece yarinyar da jekadi takai gidan MALEEK.

Murmushin manya yayi Kai tsaye yace"

Negestatinsa ce sbd ya rabu da matarsa.

Hawaye ne suka ciko Mata ido tace"

Allah ya taimaki kaleeb nagode Allah yaqara girma ina fatan ban dameka ba da Kiran dare danayi.

Bakomai Anneti Allah ya taimakemu duka.
Maganar rabuwar MALEEK da matarsa kuwa kinsan meya dace kiyi qato shiru sbd fitar hakan barazanace ga maleek.

Inshallah kaleeb ngd ahuta lafiya.

Kasa daurewa tayi Saida wasu irin hawaye me zafi suka gangaro Mata sbd wannan masiface agurinta babba.
Ta Yaya zata Hana fitar maganar rabuwar MALEEK da matarsa.

Jekadi takira anan jekadi ta fayyace Mata komai na yanda rabuwar take Wanda yasa ran Anneti baci sai yanzu ne tagano dalilin qin barin ayi maganar da afia keyi sbd Kare mahaifiyarta kada mutuncinta ya zube.
Ko so daya adaren Anneti Bata rintsaba Dan kuwa ki NEGES bazata Bari yaji zancenba tunda zargi kawai yake zata barshi yayita zargin kawai batareda ya tabbatarba.

Washe gari tun qarfe Tara ta aika cewa tana gayyatar su AFIA cin abincin safe a sashenta tareda ita.

Da farko AFIA taji wani Abu na kwanan da farhat tayi acan gurin Anneti Amma da bataji bayani ko ganin sauyi afuskan Anneti ba saita sake abinta Dan ma kada asamu damar yin maganar saita saka NURU shiryawa Dole suka taho tare.

Tunda suka zauna cin abinci Anneti tayiwa NURU kallon sakanni ta dauke kanta ta maida kan Afia dake cin abinci ba damuwar komai aranta.

Suna gamawa NURU ta fice daga sashen gaba daya sbd kallon da Anneti ke Mata yasa hankalinta tashi matuqa tashiga wani irin matsanancin tsoro.

Kai tsaye Anneti ta kalli afia bayan fitar NURUn tace"

Maleek da lailah sun rabu gaskia ne kokuwa???

Wani irin mummunan tarine ya kufcewa afia ta dago da jajayen idanuwanta ta kalli Annetin cikin tsananin firgici da tashin hankali tace"

Aa Basu rabu ba sunanan tare.

Meya hanata zuwa ita?

Sake dagowa tayi dukkanin idanuwanta na qarasa sauyawa cikin dakewa da qarfin hali tace"

Ayyukane sukai Mata yawa tayi tafiya.

Murmushin takaici na manya Anneti ta sake tana kallon zallar kuruciyar afia da yarintarta tace"

Idan har hakane kuna buqatar uwar dazata kula daku da mahaifinku sbd....

Cikin tsananin tashin hankali da firgici afia ta miqe tsaye jikinta har 'yar rawa yakeyi ta zube gaban Anneti cikin rawar murya da Bata girmanta na uwar MALEEK tace"

Anneti Ina roqanki da kadaki kawo Mana kowa bama buqatar wata uwa sbd munada me kula damu wadda take tamkar uwa.

Kallon tsaf Anneti ta Mata saidai tasan zallar kuruciya kecin afia Amma tace"

Wacece ita?

NURU tafada Kai tsaye.

NURU ba mata bace Matar uba ake magana wadda zata zauna daku har abada.

Rintse ido tayi sbd fadar abinda zata cutatar da NURU saidai Dole zatai hakan Dan kawai abar zancen su samu su taciyarsu batareda wani maganar aure aure ba wa dad dinsu.

Bude idanuwanta dasukai jajir tayi ta sauke Kai muryarta na rawa tace"

NURU da dad zasuyi aure idan munkoma.......

Wani razanannan kallo Anneti tai Mata cikin tsananin mamakin mahaikaciyar kuruciya irin tata,
Wace irin zuciyane da afia dazata yiwa mahaifinta qarya Dan Kare mahaifiyarta?.
Ji tayi zuciyarta ta sosu da abinda afian tayi saidai ta danne bacin ranta sbd gudun shedan yashigo cikin lamarin sbd afia ta dauko wata mummunar sabia me qarfi qararda zance irin wanan akan MALEEK guda idan har Bata dauka matsayinsa na mahaifi agaretaba.
Tabbas yau zata nunawa afia yaro man kaza ne,
Ta dauko magana me girma Dan Kare darajar wadda batasan daraja ba Dan haka yau zatasan ba'a Wasa da magana irin wannan.

Kitashi kije zancenki ya karbu.

Ajiyar zuciya boyayya afia ta sauke duk ganin takashe maganar qara auren mahaifinta duk da zuciyarta bata daina bugawaba kamar zata faso ta miqe ta fice tana istigfarin na neman yafiyar ubangiji.

Bayan fitarta waya Anneti ta daga ta Danna Kiran jekadi Kai tsaye cikeda bada umarnin me qarfi tace"

A isarwa kaleeb saqo daga Anneti cewan muna roqon alfarmar auren NURU daga negestati zuwa Mata ga MALEEK na Delah gizah UBAYD MALEEK.

Da qarfi jekadi ta zube qasa tana yiwa Anneti wani irin kirarin tsananin farin ciki da girmamawa.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

0903 234 5899
*_Mamuhgee 20_*

Assalamu alaikum, ina masu son su iya baking da decoration na birthday cake wanda idan aka kalla sai an kara kalla😇

toh ga dama ta samu er uwa kiyi maza kiyi rigista, sannan zaki koyi ydda ake hada whip cream din da yke daukar awanni ba tare da ya narke ba💃🏻

zaki koyi ydda akeyin vanilla cup cake mai dadin gaske😋 er uwa ba'a iya nan muka tsaya ba zamu koya miki ydda akeyin chocolate bar cookie domin farantawa mai gida da baki🥰

kuma duk akan kudi naira 3500 kacal👌🏻
Online class neh full vedios kamar a gabanku akeyi, tare da note da voice note ydda zaku fahimci komai cikin sauki😇

kada kubari wannan dama ta wuceku🤗
Domin neman karin bayani ki kira: 07089621678
I.G handle: Umsad cakes nd more😍

******************
Tana aje wayar miqewa tayi Takoma dakinta tareda dafe kanta da tuni yadauki wani irin ciwo sbd tarin mamakinda afia ta Bata Wanda take sake Dora hakan akan rashin uwane tareda ita tarbiyarta tafara yin qaranci tana sauyawa Dan kuwa ita din Bata saniba Amma abinda tayi laifine me girma da Muni yiwa mahaifinta qarya irin wannan da zata iya zubda mutuncinsa da awani gurin ta fada hakan Dan hakanma ta yanke shawaran Babu Wanda zaisan abinda afia din tayi zata bar zancen akan MALEEK aure kawai zai qara basai kowa yasanda rabuwarsa da matarsaba bare qaryar da afian ta shata Dan Kare mahaifiyarta.


Afia kuwa tana Isa sashensu a palo ta tadda NURU da farhat na zaune Kamar ko yaushe farhat na jikin NURUn suna kallon cartoon din SpongeBob ta tsaya cak tana kallonsu hawaye nason ciko idanuwanta Amma ta danne sbd tanajin zuciyarta na karyewa na abinda tayi din sbd ta Kara NURU Dan biyan buqatarta Wanda idan daga baya bayan sun koma akaji auren NURU da Imran za'a iya daukan hakan amatsayin cin amanar MALEEK datayi tunda yanzu Anneti taji cewar MALEEK zata aura..

Cikin yanayi na sanyi NURU ta dago Jin mutum a tsaye akansu ta kalleta da idanuwanta dasukai laushi sbd ciwon Kai datake ji kadan kadan ta bude baki ahankali tace da sanyin murya tace"

Afia lafiyanki k.....Bata qarasa maganar taba afian ta qaraso hawayen cikin idanuwanta na gangaro ta rungume NURUn tana rintse ido batareda tace komaiba.

Shiru NURUn tayi itama dukkanin jikinta na sake yin sanyi Jin saukan hawayen afia akan bayanta dake bayyane ta cikin doguwar riga Mara hannu.

Sun Jima ahaka kafin NURUn ta dago afia tana kallon idanuwanta dasukai jajir ta saki wani sanyayyan numfashi tace"

Menene yafaru??

Kasa kallonta afia tayi ta juyar da Kai gefe tana hawayen cikin idon suka sake gangarowa kafin ta dago ta zubawa NURU idanuwanta cikin sanyin murya da nadama tace"

NURU idan Baki saniba ayau inason kisani ke din wata babbar bangarene na rayuwata nida farhat,
Ina Jin araina tamkar yanda nakejin farhat sbd na dade da Baki matsayi na 'yar uwar uwa daya uba daya,
NURU wlh kisani duk duniya banajin zanyi Abu Dan kawo cutatarwa gareki Dan haka nake roqonki dakimun uzuri karki zargeni da komai idan har kikaji wata magana ta bullo Miki daga Anneti duk da nasan sirrine da bazata futarba ita kanta saidai koma yayane Ina roqon alfarmarki da kadakice komai duk tsanani kada kifada komai duk abinda akace kice eh sbd hakan shine zai bani lokacin kawo gyara tsakanin dad da mum Dina Wanda kinfi kowa sanin wannan shine burina a duniya and you promise to support me akan hakan right??

Tsit NURU tayi tana kallon afia din kaman wata sokuwa sbd ita anan Bata gane komaiba sbd zancen duk a baibai yake bayan hakan ita menene nata wane matsayi take dashi da afia zatace tashigo cikin zancen komai akace tace eh,to menene zata cewa eh din??

NURU Zaki taimakemu mu dawo da mahaifiyarmu nida farhat??

Cikin tsoro da mamakin shiga huruminda ba nataba ta kalli afian da idanuwanta sukai jajir ta gyada Kai ahankali batareda ta iya bude Baki tayi maganaba sbd Jin abin take yayi Mata nauyi kaman bazata iyaba sbd Jin kamar ba zancenda zata shiga bane.

Zamewa tayi gefen NURUn data shiga tunani haka kawai ta kwanta tareda Dora kanta kan jikin farhat dake jikin NURUn itakuma da hakan duk su duka biyun suka shiga tunani.



****
Tsaf kaleeb yaga sauraron saqo me girma da jekadi tazo dashi idanuwansa nakan makekiyar TVn data kusa cike Rabin bangon palonsa zaka dauka baya sauraronta Amma tsaf yagama Jin komai ya jinjina Kai Yana sake juya zancen cikin ransa da tunaninsa.

Jekadi menene halaye munana da kyawawa na NURULHUDA??
Ya qarfin nutsuwarta da biyayyarta?
Ya qarfi da girman son duniyarta take?

Sake zubewa qasa jekadi tayi cikin girma da tabbacin abinda zata fada Kai tsaye tace"

Allah ya qarawa Kaleeb Nisan kwana da lafiya.
NURU negestati ce wadda zance komai nata da yardar Allah yayi abisaga tsarin da kake son Matar MALEEK ta kasance,
NURU jikace Kuma 'yar asalin amintaccin bayinka da kakanta da mahaifinta,
NURU baiwace me biyayya tareda da'a wadda takaita ga samun ribar zaman rayuwa,
Anneti ce da kanta tayi zabin NURU tazaman Matar aure ga MALEEK wadda zan bada rayuwata akan Anneti Bata yanke komai akan garaje Wanda wannan halin na zurfi da tsaftataccen tunanin daukarsa tayi daga cikin halayen girmanka da adalcinka ya kaleeb.

Jinjina Kai yakuma Yi tareda kallonta wannan karon ya bude Baki cikin gamsuwa da zallar cikar ikonsa yace"

Ahada dukiyar neman auren MALEEK UBAYD zuwaga mahaifinta tareda saqon 'yantawa ga dukkanin zuriarsu tareda tukuicin zuwa gizah ga dukkanin ahalin Dan halartar auren 'yarsu.

Sake zubewa jekadi tayi tana miqa tsagwaron godia da kirari tareda fatan nasara da tarin aduoi ga wannan aure harta fice tanayi cikin tsananin farin take da wannan aure sbd har cikin ranta Allah yasanya Mata kaunar NURU take Kuma fatar cigabanta Wanda tun zuwanta ta yaba takuma Yi tunanin kyawu da halaye na gari irin na NURU matuqar ta zama negestatin MALEEK to ko Bai auretaba wata Rana to tabbas saita zamana negestatinsa datafi matansa daraja a zuciyarsa saigashi abin yazo alokacinda Babu zato ba tsammani Dan haka ko minti biyu Bata qaraba aka fitarda saqon kaleeb take aka fara hada dibbin dukiya da tarin zinarai masu nauyi da daukar ido Wanda yasa take maganar ta fito filin Allah zancen auren ya bazu Kamar wutar daji wasu Basu tabbatarba Saida aka Kai dukiyar gidansu NURU yakasa dauka take aka sauya musu muhalli acikin qanqanin lokaci gari kuwa ya dauka tako Ina zancen akeyi wasu na qaryatawa wasu kuwa mamaki da firgici ya hanasu yadda.

Padima dake zaune bakin kofar dakin da aka jere dukiyar neman auren NURU dakuma Wai MALEEK UBAYD Wanda sunansa kawai sukeji kaf delah din Nan kila idan ba kakansaba sai wasu qalilan ance Babu Wanda ya taba ganinsa koda cikin sa'a ne.,
Sam Bata yardaba da wannan zancen tafi yarda da cewan wani dai acan gizah zai auri NURUn Amma badai MALEEK ba Dan kuwa har abada ko ita datake gaban NURU akomai Bata taba kawosa cikin rantaba bare NURU sokuwa wannna masarautar delah ta boyewa su abal ne amma tasan tsohon da take negestatinsace zai aureta Kuma a iya saninta ba ace musu maleek ba da akazo daukarsu negestati.

Kallonta amminsu tayi lokacinda ta fito dayan dakin riqeda hannun meryam daketa tsalle tsalle da farin ciki me tsanani tun jiya da akace Mata zasuje inda zasuga NURUnta.
Da mamaki ammin tace"

Padima tun jiya kin kasa dogon motsi kin kasa kin tsare kofar dakin Nan bayan kinsan Babu Wanda zai shigo gidan Nan idanma sata kike gudu ki kwantar da hankalinki Mana idanma tambaba kike na waye NURUn zata aura ai zamuje saimu tabbatar sbd muma munkasa yadda da abin al'amarin yazo mana a wani irin girmame saidai koma wane munsan wannan babban cigabe da abin farin ciki ga NURU sbd aure abune me girma dazai tabbatarda darajarta.

Qala padima Bata samu cewaba dan kalma daya acikin zancen ammin Bata fahimta ba babban burinta da damuwarta yanzu shine su tafi gizah din tasamu ganin NURU taji komai daga bakinta shine kawai zai Bata kwanciyar hankali tanaji meryam na fada Mata amed na kiranta waje harso shida tayi kamar batajitaba qarshe korata tayi da wani mugun kallo dayasa meryam din tafiya gurin ammi tana waiwayen padiman sbd ganin yau ko gyaran dogon gashinta batayiba Wanda kullum sai tayi gyaransa Kamar wani sarki.

Daga waje Kuma amed ganin Bata fitoba harya gaji da tsayuwa ya juya ya wuce Yana cewa"

Kome Zakiyi wlh sai anci dukiyar Nan Dani sbd rabona ya koka aciki Dan kuwa nasan yanzu tunda Zaki tafi gurin NURU a gizah dukkanin burinkanki kinsamu damar cikasu wlh maqalewa yanzu nafara Miki mutu ka raba komai Zaki samu taredani zamu cisa.


****
Zaune yake cikin makeken palonsa na quryar sashensa Wanda bayan masu gyarawa Babu Wanda yataba shigarsa ciki Koda kuwa mahaifiyarsace.,
Kyawu da tsarin palon kawai ya isa sanyaka lissafinda bazaka iya kaiwaba musamman sbd komai na sassansa na daban ne Dan zamowarsa MALEEK.
Akaro na biyu ya sake wani boyayyan numfashi Yana sake lumshe fararen idanuwansa dasuka Dan sauya sbd ciwon Kai me qarfi daya damqesa lokaci daya da kaleeb yakirasa ya sanar Masa da aure za'a daura Masa da negestatinsa abisaga umarni dakuma roqon alfarma da neman cika biyayya daga mahaifiyarsa da Bata taba neman wata alfarma daga garesaba ataqaice wannan ne Karo na farko data yanke hukuncin wani Abu akansa tun bayan rasuwar mahaifinsa Yana qarami.
Kaleeb ya sanar dashi an aika komai ankai qarshen komai jibi za'a daura auren Wanda har zancen ya fita shin tayaya zai musa wannan auren da yarinyar datake tamkar 'yar cikinsa Dan kuwa idanma lissafin yaje daidai afia zata girmeta Koda da shekara biyune ko daya.
Ta Yaya aure zai shiga tsakaninsa da wadda yakewa kallo daya da farhat qanqanuwar yarinyar da batafi shekara gomaba.

Wayarsace tayi haske tana vibrating ahankali ya bude idanuwansa ya kalla wayar ahankali yaga sunan Mr Omar akai dauke Kai yayi tareda mayarwa ya rufe tsawon lokaci ahakan kafin ya bude idanuwan daidai Mr Omar nasake Kira sbd sanin MALEEK dakyau da yayi yasa yake iya kwatanta mintunan sake Kira na biyu idan yayi na farko cikin sa'a kuwa ya daga batareda yace komaiba.

Da sauri cikin girmamawa da kaucewa dogon bayani da MALEEK bayaso yace"

Barka da hutawa MALEEK.
Dama 'yan media ne sukeson yada zancen...um..um..maganar auren ko za'a sirrantane?duk Wanda ya fitar Kuma mu dauka mataki akansa.

Kai tsaye yace"

Aure Yana boyune???

Jin haka yasa mr Omar cewa"

Allah ya huci zuciyar MALEEK.

Kashe wayarsa yayi ya ajiye tareda Miqewa yayi ciki Dan kuwa kila Babu me sake ganinsa sai gobe idan kaleeb ya iso daura auren Dan yasan zancen yanzu cikin awanni kadan zai bazu koina musamman NEGES da tun jiya yake son ganinsa Amma baya cikin mode dinda zai iya ganin kowa.

Yana daf da shigewa breaking news din auren THE KING OF DELAH GIZAH MALEEK UBAYD ya sauka acikin cikin qatuwar TVn dake palon ya juyarda idanuwansa ahankali zuwa kan time sai kawai yashige sbd Dama yasan media

Please Login or Register in order to submit comment