Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Amma jin wannan maganar Tata Sai dariya ta kamashi yace "na haqura da duniya Kuma?"

Fari tayi da idonta tace "Emana, gashinan to babu ruwanka da shiga harkar kowa, rayuwar ka cikin kwanciyar Hankali"

Juyowa yayi yana Kallan ta, har zuwa lokacin dairy din yana rungume a faffadan qirjinsa, yace "tayaya zan haqura da rayuwa Bayan bansamu abinda nake soba?"

Tace "zaka samu Babban Yaya,nasan saboda me kama da nine kace haka, Bari kaji ai dole ma ka sameta ko tana so ko bata so,nikam yanzu banida damuwar komai"

Yace "Serious?"

Wani iri farrrrrr tayi da Zara zaran gashin idonta, sannan ta 'Dora hannunta akan qirjinsa tana so taja littafin daya rungume, shikuma yahana, saima Qasan fillo daya turashi ciki


Bata d'auki hakan a matsayin komai ba, batasan cewa baya son taga dairy din bane, batayi tunanin wani abu na sirrinsa yake rubuta wa aciki ba, shiyasa Bata damu da saita ganiba, saita share, saima hannunta data d'ora akan faffad'an qirjinsa take shafa gashin da yayi kwance akan farar fatarsa, sannan tace "I'm serious Babban Yaya, banda damuwar komai, kana tsaya min akan komai,nasan cewa nafi kowa sa'ar samun Yaya me kula da qanwarsa, shiyasa bayansu Ummah da Daddy banida Wanda yafika"

Kwata kwata Babban Yaya baiji abinda Waheeda take fad'a masa baπŸ˜‚
idanunsa a Lumshe suke, shi Kansa ba zaice ga duniyar dayake ciki ba, wani irin dad'i yakeji yanda take shafa qirjinsa, Waheeda bata lura da yanayin data jefa yayan Nata aciki ba, kawai qirjinsa take shafawa tana wasa da gashin qirjinsa me mutuqar laushi, ahankali tace "Babban Yaya Wai meyasa bakasan aske gashin kirjinka? Yafara yawa fa...."

Babban Yaya baima bud'e Idonsa ba bare yabata amsa, baya so yayi magana ta daina abinda take masa, yafiso taci gaba, Kallan sa tayi taga Idonsa a Lumshe, tayi murmushi tad'auki wayar Ummah data gudo da'ita ta kunna, sannan ta kunna masa tasa wayar, kamar jira ake, tana kunna wayar Babban Yaya kira yashigo da wata number,tsabar nacin da me number take masa ne yasa ya rubuta wa ne number Ummi Nigeria , Waheeda ta janye hannunta daga kan qirjinsa tace "Babban Yaya Ummi Nigeria tana kira, wacece?"

Cikin takaici yabud'e Idonsa, yaji haushin shigo war Kiran wayar, gashinan ta katse masa jin dad'insa, Kansa tsaye yace "Ummi ce"

Cikin murna Waheeda tace "Bari in d'aga mugaisa"

Cikin sauri yatashi zaune yace "kice mata me? Karki d'aga, ni Bana d'aukan wayarta, me kikeso nace mata idan nad'auka?"

Waheeda takama dariya yanda taga ya rikice shi baza'a daga wayar Ummi ba,Sai hakan yasake bata dariya, tace "Toni kabarni in d'auka saimu gaisa"

Ganin zata d'auki wayar yasa yamatso kusa da'ita zai qwace wayarsa,ita Kuma tana ganin haka tahanashi, kokawa suka fara irinta masoya tana d'aga hannunta sama Dan karya qwace wayar shikuma yanaso ya qwace, saura qiris wayar ta katse Waheeda tayi nasarar picking ba tareda ta saniba

Daga d'ayan bangaren ummi tayi gyaran murya tareda lanqwasa harshe tace "Hello Dear"

Taji shiru, tasake cewa "Hello my Dear..." nanma taji shiru Sai alamun ma kokawa dataji anayi tacikin wayar, kasa kunne tayi taji Babban Yaya yana cewa "Kibani wayata nace...."

Waheeda ta hanashi Sai dariya take, tana tsaye akan gadon shikuma yana tsugunne bai tashi tsaye ba, cikin dabara yariqo Hips d'inta da duka hannayensa, cikin dariya tayi baya zata fad'i saiya tareta tafad'o qirjinsa, breast d'inta Wanda ko bra babu, yasauka akan fuskar sa, cikin ransa yace "Ya Salam.......wayyo Allah nah...."

jiyayi gaba d'aya jikinsa ya mutu, yaso ace yanada Dama da saide yasake rungume ta a qirjinsa,zaiso ace yasake cusa Kansa acikin nashanunta, lokaci d'aya yana yinsa yafara sauyawa

Daurewa yayi, yayi ta maza sannan ya qwace wayarsa, yasake ta tafad'a kan gadon tana dariya, wayar ya kalla yaga har anyi minti uku da d'auka.... Ba tareda yayi magana ba yakashe wayar


Daga d'ayan bangaren Ummi tasaki ajiyar zuciya cikin bacin rai tace "Kan ubancan!, da wacce shegiyar yake tare? Ni za'a nunawa bariki?" πŸ€₯😠
1/28/22, 20:50 - Ummi TandamaπŸ˜‡: WN



Sake Kiran wayar Ummi tayi, Amma Naufal yana Gani yayi mursisi yaqi dauka, saima wuta daya kashe, yayi shirin bacci, saboda gaba d'aya yanayinsa ba daidai yake jinsa ba

Waheeda ma fillo taja zata kwanta akan gadon, yana jin alamun kwanciyar ta kamar an tsikare shi yayi sauri yatashi zaune, yace "mezakiyi?"

Kallan sa tayi cikin duhu tace "Bacci mana Babban Yaya"

"ok" abinda yace kenan, sannan ya sauko daga kan gadon ya shimfid'a wani blanket Mai laushi, yaja fillo d'insa ya kwanta, yana d'auke fillon Waheeda taga wannan dairy din, batayi masa magana ba saida taji shiru alamun yayi bacci sannan ta d'auka tafara bud'ewa, 'Dakin yayi duhu bata ganin komai,saita janyo wayar Ummah ta haska tafara karantawa, shafin farko Zanan heart ne ajiki, yayi kyau sosai Zanan,har ya d'auki Hankalinta sosai, shafi na biyu ta bud'e tafara karantawa inda ya rubuta (Rayuwa Mai sauyi,a koda yaushe zata Iya sauya Maka, daga qaddara Mai kyau ko marar kyau,akoda yaushe qaddarar mutum tana iya sauyawa,banajin zan'iya rayuwa ba tareda itaba, Abaya kafin zuwanta komai nawa cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali nake yi, tunda tashigo cikin rayuwa ta, komai ya sauya, Abaya Ina rayuwa ne tareda 'yan'uwana cikin kwanciyar Hankali, haihuwar ta ne...... "

"mekikeyi ne bakiyi bacci ba? "

Waheeda ta tsinci maganar Babban Yaya, cikin sauri tarufe littafin ba tareda ta qarasa karantawa ba
Tasowa yayi ya d'auke Dairy d'insa, sannan yakoma ya kwanta, fatansa d'aya, Allah yasa bataga komai ba

Itama rufe wayar tayi tareda Lumshe idonta, akan me yake magana? Wacece wannan d'in? Yace mata me kama da'ita yakeso, but yanzu akan wa yake magana? Kanta ne ya d'aure gaba d'aya

Shima anasa 6angaren kwata kwata yakasa nutsuwa, yana tsoron ace taga abinda ya rubuta, ahankali yayi maganar qasa qasa yace "Kin karanta?"

Kamar daga sama ta tsinci maganar tasa, girgiza kanta tayi kamar yana ganin ta tace "A a"

Beqara cemata komai ba, itama haka, kasa runtsawa yayi saida yaga tayi bacci sannan yatashi yayi toilet yayi wankan tsarki, sannan ya 6oye dairy din yakoma ya kwanta


Washe gari yariga ta tashi, lokacin data tashi bata ganshi ba, Dakin ta gyara tayi wanka, tasaka wani Riga da wando data Gani acikin kayan daya siyo mata, kayan taketa juyawa tana mamaki Babban Yaya ne da Kansa yasiyo mata wannan kayan?shida baya son su dinga yawo babu hijabi Amma shine da siyo wannan kayan?

(hmm yo bashi za'a sakawa ba🀣)

Wandon crazy ne, Amma yagar jikin batada yawa, Sai Riga marar hannu yar qarama wadda da kadan ta wuce mata cibiya, Bayan rigar kuwa abude yake, Amma gaban rigar wajan breast din a rufe yake, mamaki ne yakamata sosai, haka tayi parking gashin kanta, tadauko bra din data Gani a kayan tasaka, tayi mata cif kamar Wanda ya gwada ta, ko Yaya akai yasan size dinta? πŸ€”
Saida tagama shirya wa tsaf sannan tafita falon, tad'an gyagygyra, daga Nan tayi kitchen tafara hada break fast, tana cikin soya qwai yashigo kitchen din, abakin kofar kitchen din ya tsaya tareda rungume hannun sa yana qare mata kallo tundaga sama har qasa, hips dinta yafi komai daukar hankalin sa, kayan sunyi mata kyau jiyake kamar yaje ya rungume ta, wayarsa ce tayi qara cikin sauri Waheeda ta juya, tana ganinsa tasaki ajiyar zuciya tace "wallahi harna tsorata"

Bece da'ita komai ba Sai falon daya koma ya zauna, ya dauki wayar cikin farinciki, dimple dinsa har lotsawa suke, yace "Anty na takaina"

Hajiya Anty tace "Sai yanzu kaga damar bude wayar kenan, Ina Waheeda?"

Kitchen din ya kalla sannan yace "gatacan tana hada mana breakfast, wallahi anty naji dadin tafiya da yarinyar Nan, kinga da, duk lokacin da zanyi girki da kaina, to Bana fita ball, saide in zauna agida, inyi shara, inyi mopping, inyi wanke wanke, in goge kwanukan, sannan na maida su kitchen, Kai Ina shan wahala fa "

Hajiya Anty tayi shiru tana mamakin yanda Babban Yaya yake cikin farinciki, shida ba gwanin surutu ba, Amma Sai zuba yake kamar kanya, ajiyar zuciya tayi tace" kaide kawai kace sakalci ne yayi Maka yawa, idan kana shan wahalar aiki Aida tuni kayi aure "

Cikin shagwaba yace"wayyo Allah Anty kidena maganar auren Nan Dan Allah, yanzu de yakike? Ina Ummah? "

"Ummanku tana nan lafiya, Nima kira nayi in tabbatar Kuna tareda Waheeda ne ko bakwa tare? "

"muna Tare Anty"


Tace" to shikkenan, kakula da'ita, zan tafi hospital Sai anjima "


Sallama sukayi, adede lokacin Waheeda ta ajiye musu abincin, tana zama taji wayar Ummah tana ringing, tashi tayi tatafi Dakin da gudu saboda kar wayar ta katse, Babban Yaya yabita da kallo yanda Hips dinta suke rawa kamar da niyya take kad'asu, wani irin yawu ya hadiye, sannan ya kunna TV danta dauki Hankalinsa

dubawa tayi taga Didat ne, murmushi tasaki sannan ta zauna abakin gado tareda daukan wayar"Yaya Didat...."


"Ina kika tafi nazo gidan akace bakya Nan?"

"wallahi Bana Nan Ina England tareda Babban Yaya"

Yace "what! mezakiyi acan? Kuma kirasa dawa Zaki tafi Saida namiji?"

Cikin rashin fahimta tace "mekake nufi?"

Kansa yadafe da hannun sa, sannan ya seta Kansa yace "kiyi hakuri Waheeda, inada kishi ne, please Wai yayanku yaushe zaiyi aure ne?"

Tace "menene hadin aurensa da soyaiyar mu?"


Wayancewa yayi yace "haba My dear, Yaya nanefa kamar yanda yake yayanki, laifi ne danna tambaya yaushe zaiyi aure? Ai abun farinciki ne"


Murmushi tasaki taji dadi yanda ya dauki yayanta, tace "yakusa aure, ansaka rana nanda wata uku, Amma ba'a tsaida date ba, Sai ankai lefe"


Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da yaji komai, sannan ne yasa ki ransa suka gaisa sosai, yasake fada mata takula masa da kanta, sannan sukai sallama Takoma falon suka fara break fast itada Babban Yaya


Suna gama cin abinci yafita, baidawo gidan ba har dare, haka ta wuni ita kadai, idan ankira wayar Ummah bata dauka, bataga Kiran yanbiyu ba, tasan cewa sun tafi Saudia, kamar yanda Babban Yaya ya fad'a

Kallo suke cikin kwanciyar Hankali, baya tareda wata aba Wai ita damuwa, asalima yau yabuga Ball wadda bai taba jin dadinta kamar yau ba.

Acan Nigeria kuwa, Su Hajiya Anty da Uncle Usman suna gidan Daddy, babu kowa a gidan duk sun tafi Saudia, Sai iyayen su kadai, Kallan labarai suka gama yi, Uncle Usman ya sauya Tasha, anan yaga Babban Yaya yana buga Ball yanda ransa yakeso kamar ba shine yake qunci saboda ance za'a bashi Ummi ba, Murmushi yayi ya kalli Hajiya Anty yace "kinga d'an wajanki fa"

Murmushi tayi tace "ai qwazon nasa awaje yake, yanzu kwanaki dasukayi da Yara ai kasawa yayi"

Ummah tayi shiru tana tunani, itade bata tanka ba, domin kuwa a cike Takeda Waheeda, Daddy ne ya dauki wayarsa yakira Babban Yaya, tana shiga yace "idan kun gama 6oye 6oyen naku kakawota gida, muna son ganinta, sannan kaima ka tabbatar kataho lefenka yana Nan angama hadawa yakamata kazo kagani, idan kagani komai yayi yanda kakeso Sai akai musu, su tsaida mana ranar auren"


Jikinsa ne yayi Sanyi, cikin ladabi yace "to shikkenan Daddy" daga Nan yakashe wayar ya kalleta yace "kishirya gobe Zaki wuce gida"

Kallan sa tayi tace "Babban Yaya kaifa?"

Shiru yayi yana tunani, shide bayajin zai iya zuwa haka kawai saboda ganin kayan lefen Ummi, to waye ma yace su hada masa wani lefe? Kansa yadafe da hannun sa yace "nikam bazani ba"


Yanda taga yabata amsa ransa duk adagule kawai Saitayi shiru karta sake magana yahuce akan ta


Haka suka wuni ranar babu walwala atare dashi, tana so tace masa yakaita yawo Amma bataga fuska ba, haka tayi shiru tana gudun aikata laifi yahuce akanta, washe gari da safe tare suka tafi club dinsu da'ita,tana Sanye cikin doguwar Riga Abaya, saita yafa mayafin abaryar akanta, idan ka ganta bazaka taba cewa tanajin hausa ba, saita zama kamar wata balarabiya, hannun sa cikin Nata suka futo daga motar da aka kawo su, yana futowa mutane suka yanyameshi yanmata turawa Sai rungumeshi suke, wasu Kuma suna shaking din hannu, yanda yake murmushi dimple dinsa na futowa Sai hakan yabawa Waheeda haushi, suna zaune gida daya kullum yana daure musu fuska Amma Jiba yanda yake sakarwa yanmata jikinsa da fuskarsa, saida yagama photuna dasu sannan sukayi ciki, Waheeda de nemanta ma yayi yarasa, tun tuni wasu daga cikin masoyansa suka janyeta, dressing room dinsu yayi, Bayan Dan wani lokaci suka futo aka fara buga ball, tun tanajin haushinsa tana Kallan yanda yake buga ball din harta dawo ta daina ganin yanda dubban mutane suke murna idan Dan'uwan Nata yajefa qwalla araga

Saida suka gama sannan yayi abinda zaiyi ya dauketa suka wuce airport, a Airport dinma Gani tayi yayi shiru kamar akwai abinda yake damunsa, kasa hakura tayi tace "Babban Yaya meyafaru?"


"banason tafiyar kine"

Baisan lokacin da wannan maganar tafuto daga bakinsa ba kamar Wanda aka qwatota, Kallan sa tayi cikeda farinciki tace "Allah?"

Wayancewa yayi yace "ke wasa nake miki, banason shirme, kawai.... Kawai de... Banji dadin yanda Daddy yamin maganar lefe bane"
Ya qarasa maganar a rarrabe fuskar sa cikeda fishi

"nikuma Babban Yaya banga abun fishi anan ba, zaka iya auren wadda kakeso daga baya"

Cikin 6acin rai yace "Kina tunanin zan hada abinda nakeso dawani abu daban? Kinga banason damuwa, muje kunfara shiga jirgi"

Kanta ta gyada masa batare datace komai ba suka tafi, saida yaga jirginsu yatashi sannan yakoma gida

Jirginsu yana sauka taga driver yana jiranta, mamaki ya kamashi ya kalleta dakyau yace "Waheeda yanaga kin sake kyau? Me yayan naku yake baki?" πŸ€”

Harararsa tayi tace "shafa kaji, ka bude min mota kawai, Kuma gidan Hajiya Anty zaka kaini"

Jinjina Kansa yayi, yasan rashin kunyar Waheeda, zatayi yafi haka, jakar hannunta ya kar6a sannan yace "lalle Waheeda idan kikai shekara a qasar waje bazamu ganeki ba, cikin abunda baifi 'Yan kwanaki ba kikai irin wannan kyau haka?"πŸ€”

Tana jinsa tasaki wani Dan qaramin tsaki, damuwar ta daya yanzu shine Ummah, bata Isa taje wajan Ummah ba, Gara ta gudu gidan Hajiya Anty yafi sauqi

Suna hanya ta turawa Babban Yaya text cewa ta sauka, Saukarsu gidan Hajiya Anty keda wuya taci Karo da wasu akwatuna masu shegen kyau guda ashirin da hudu, dozin daya pink colour, dozin daya blue, akwatunan ne suka dauki hankalin ta, tafara ta6a jikinsu tana qwalawa hajiya Anty kira, futowa tayi daga d'akin ta tayi mutuqar kyau cikin atamfa dinkin Riga da siket, kullum cikin Gayu take bata gajiya

Tana ganin Waheeda tace "Oyoyo daughter" tafadi hakan tareda bude hannayenta, babu musu Waheeda tashige jikinta, Hajiya Anty ta rungume ta tanajin qaunar yarinyar acikin zuciyar ta

Zama sukai akan kujera Waheeda tasake Kallan kayan tace "Anty lefen Babban Yaya ne wannan?"

"lefensa ne, Uncle dinku ne yayi order su daga Dubai, abubuwa kad'an muka qara anan, Amma ba'a saka mata pant da brezia ba, zan Mai magana saiya tambayeta size dinta"

Waheeda tayi ajiyar zuciya "Anty Babban Yaya fa baya son auren Nan, kukuma Naga kun dage"

"zaiso ne Idan akayi, ai kinsan qiyaiya tana komawa soyaiya"

"to Anty, Allah yarufa asiri"


Anty tace "Amin ya Allah, kibude kigani mana"

"a a Anty, basai nagani ba, Allah ya basu Zaman lafiya"

Hajiya Anty tayi murmushi, takasa gane yanayin yarinyar, shin kishi take, kokuma kawai 6acin raine Dan taga yayan Nata ma baya son auren? πŸ€”

A gidan Hajiya Anty tayi Zaman ta har kusan sati daya da dawowar ta, koda wasa bata nufi gidan Ummah ba, sauqin ta daya, suna cikin hutu

Ranar da tayi kwana Tara, ranar su yanbiyu suka dawo daga Saudia, murnar dawowar yan'uwan Nata ne yasa tatafi gidansu, Hajiya Anty tarakata suka tafi tare, lafiya kalau suka gaisa da kowa, anan falon aka baje Ana hira, Ihsan ta kalli Waheeda tace "shikkenan Waheeda kin luser bakije Saudi ba" tafadi hakan cikin sigar tsokana

Waheeda ta yatsina fuska tace "ai zuwa makkah Kiran Allah ne, dama can banda ni yakira, Nan da lokaci kadan kunaji Kuna Gani zamu tafi nid Babban Yaya" tana fadar haka tatashi ta wuce dakinsu

Sa'ad da Sa'eed suka bita da kallo, Sa'eed yace "Sa'ad kasaka yarinyar Nan acikin addu'ah kuwa da mukaje Saudia?"πŸ€”

Kafin Sa'ad yabawa dan'uwan nasa amsa, Ummah tatashi taciro wayar charger tabawa Sa'eed tace "jeka zanemin yarinyar can"


Babu musu kuwa Sa'eed yanufi Dakin nasu, adede lokacin Waheeda tacire Kaya zata shiga wanka, daga ita Sai towel, lokaci daya taji saukar duka ajikinta, ihu tasaki, su Ihsan suka qaraso Dakin suna temakon ta, memakon ya qyaleta, saiya had'a dasu yakama duka, aikuwa babu shiri suka futo kowacce tana Sosa jiki

(duk Wanda ya karanta min littafi be biya ba shida Allah)



Saida yayi mata lilis sannan Yabarta, yana futowa daga d'akin Daddy yashigo, ya zauna a kujera, cikin ladabi hajiya Anty ta gaishe shi sannan tayi musu sallama tatafi, Kallan Ihsan yayi yace "jeki kiramin qanwarku"

Dakinsu tashiga, Waheeda tana kwance aqasan Dakin tana kuka, duk jikinta yayi ja inda wayar tata6a ta,idanunta har sun kumbura gashi sunyi jajir dasu, fada mata saqon Daddy tayi, cikin kuka Waheeda tace "Dan Allah Ihsan d'agani, wallahi bazan iya tashi ba"

Ihsan ta kamata tatashi zaune har towel din yana kokarin cirewa, hijabi tabata tasaka, sannan suka futo falon, zama tayi aqasa tana sheshshekar kuka ahankali, Ummah ta kalleta tace "marar mutunci Ina wayata take?"

Cikin kuka tace "Dan Allah Ummah kiyi hakuri, wayar tana daki, Dan Allah karku fadawa Babban Yaya"

Daddy yace "Waheeda zancen Babban Yaya aiya qare, kifada wa shi wannan Yaron dayake zuwa wajanki yafuto ayi muku aure inda gaske yake, idan Kuma bakya sonsa to akwai huzaifa Yaron Abokina zaizo Shima ki ganshi idan yamiki shikkenan, bazaki gama karatu kamar yan'uwan kiba, aure zan miki "

Waheeda najin haka ta rushe da Kuka tafara Bawa Daddy hakuri, Amma mursisi haka Daddy yatashi yayi daki Yabarta anan, intisar ce ta kamata suka koma daki harda Ihsan ma, suna zuwa Dakin suka fara bata haquri, Amma Inaaa Waheeda Sai kuka take har kanta yazo yafara ciwo, daga qarshe, wani irin zazza6i me zafi yarufe ta


Da asuba daqyar tayi sallah Takoma ta kwanta, ko Yaya ta motsa jikinta saita runtse ido saboda yanda ko'ina na jikinta yake mata ciwo, qarfe goma da rabi Ummah taga abun na Waheeda gaba yake, tun jiya jiki yaqi dadi, Nan da Nan Kuma Hankalinta yatashi, tasa Sa'ad yakaita Asbiti, yanbiyu ne suka shirya ta suka tafi gaba dayansu.

Suna fita wayar Ummah tayi qara, number tagani, ta dauka tareda sallama, daga d'ayan bangaren akace "Mama Huzaifa ne"


Ummah ta fada da fara'art tace "Au Huzaifa, ashe kaine, ya mutanan gida"

"suna Nan kalau Alhamdulillah" daga Nan Kuma Sai yayi shiru baice komai ba

Ummah data fahimci inda yasa gaba, saitace "Huzaifa Waheedan bataji dadi bane, sunje Asbiti yanzu, Amma idan suka dawo, zata kiraka"

Cikin tsantsar damuwa yace "subhanallah.... Ummah meyake damunta? Suna wanne Asbiti, meyake damunta....?"

Ummah ta jijjiga Kai ganin yanda Yaron yarikice lokaci d'aya, tace "suna wani private Hospital Annoor"

Godia yayi mata, sannan yakashe wayar




(idan kinsan bada yardata kika karanta wannan littafin ba, keda Allah, nabarki da Allah, koba yauba karkizo neman yafiya ta ehe)




*** *** **


suna zuwa Asbitin Waheeda ta yanke jiki tafadi,bayan likita ta dubata tace "yarinyar Nan akwai qarancin jini ajikinta, dole zamu qara mata jini leda d'aya zuwa biyu"

Nanfa hankalin 'yan'uwan Nata yatashi, Sa'ad ya kira Ummah yafad'a mata halin da ake ciki, cikin tashin Hankali tace "gatanan zuwa"


Gidan Hajiya Anty tatafi, daga Nan suka nufi asbitin, suna zuwa adede lokacin Shima Huzaifa yazo, had'ad'd'en Gaye ne nabugawa a jarida, wankan tarwada ne, yanada tsayinsa daidai misali, kana ganinsa kasan hutu da jin dadi sun zauna masa, tare suka shiga Dakin da aka kwantar da Waheeda, suna zuwa kuwa numfashin ta yafara yin sama kamar zata suma, hankalin Ummah yatashi, Nan da Nan tafara hawaye, Hajiya Anty tace "Haba Hajiya, idan kina kuka sukuma yaran mezasuyi kenan?"

Kafin Ummah tabata amsa tajuya ta kalli likitar tace "doctor me kuke jirana Baku saka mata jinin ba?"

Likita tace "wallahi hajiya bamuda irin jininta, anje asiyo har yanzu basu dawo ba, group o gareta, jinin yana mana wahalar samu"

Cikin 6acin rai tace "jini yana wahala kenan haka Zaku Barta tamutu mune da asara kenan?"

Likitan tace "Hajiya Bahaka bane kiyi hakur...."

Gyaran murya Huzaifa yayi yace "A a, Anty kiyi hakuri, zanbata, irin jinina ne"
ya kalli doctor yace

"muje lab din ku d'iba"


Tafiya sukai,ya kwanta aka 'Debi jininsa, zasu gwada ko akwai wata cutar, tunani huzaifa yayi hakanma qarin wani 6ata lokacin ne, yafada musu su dauka kawai a saka mata, shi lafiyarsa kalau, haka ya kwanta aka Debi jininsa leda biyu, sannan taje ta daurawa Waheeda tareda allurar bacci, shikuma ya kwanta zuwa wani lokaci sannan yatashi yakoma Dakin da aka kwantar da Waheeda yaharde hannun sa a qirjinsa yana qare mata kallo, Sai yanzu nema yake sake ganin tsantsar kyanta, lokaci daya yaji sonta yana sake qaruwa acikin zuciyar sa, idan bai sameta ba, bayajin zai iya yin aure a rayuwar sa


Sai dare sannan Waheeda taji Dama Dama aka sallameta tareda alqawarin hajiya Anty zataci gaba da dubata agida.

har zuwa wannan lokacin Huzaifa yana Nan bai tafi ba, su 'yanbiyu Sai Kallan sa suke afakaice suna gulma ganin yanda yake komai nasa cikin aji da kamun Kai, saida sukaje gida lokacin karfe Tara nadare, sannan yayi musu sallama yatafi

Washe gari da safe ya dawo dubata, babu laifi jikin Nata akwai sauqi sosai, har falo aka shigo dashi, ta zumbula hijab dinta tafita, kallanta yayi yace "Baby yajikin?"

Wasa take da yatsun hannunta kanta aqasa tace "Alhamdulillah Yaya"

Yatsina fuska yayi yace "Yaya Kuma Waheeda? No.. No... Banason sunan Nan, ki sauya min wani"

Daga Masa Kai tayi, ledar dake hannun sa ya ajiye agabanta, yace "dazan taho ne nashiga super market namiki shopping, nasan bakinki babu dadi tunda rashin lafiya kikayi"

Kanta yana qasa tace "to nagode"

Dan qaramin murmushi yayi yace "Waheeda bazaki Kalle niba?"

Dagowa tayi ta Kalle shi, Saitayi saurin sunkuyar da kanta qasa, sakamakon wani irin abu dataga yana futowa daga Idonsa yana shiga Nata, gabantane yafadi, harta kasa 6oyewa saida tasa hannunta a setin qirjinta, huzaifa yana ganin haka yayi tunanin ko jikin Nata ne yatashi, ahankali yace"sorry na tsaida ke, nasan kin gaji ko? "

Hannunsa yasaka acikin aljihu ya Dauko wani zobe na gold me kyau, yamiqa mata tafin Hannunsa yace" Bani hannunki "

Kallan sa tayi da mamaki, shikuma ya Dan daure fuska yace"bani mana"

Ahankali tad'ora tafin hannunta akan nasa, yatsun hannun ya kalla Zara Zara dasu dogaye, akwai zoben gold a hannunta Wanda Babban Yaya yasiya musu, saiya cire shi yasaka mata nasa yace"wannan yafi kyau, karki cire shi"πŸ™ŠπŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?

Daga masa Kai tayi, ya dauki wayarsa yayi kira, Ana dauka taji yace "Momy ga Waheeda ku gaisa"

Daga bangaren ta tace "to bata wayar"

Waheeda yabawa wayar yace "ga momy na zaku gaisa"

Waheeda ta karba suka gaisa da'ita cikin mutunci, sannan ta bashi wayar, shikuma yayi mata sallama yatafi

Bayan sati daya Waheeda ta warke sosai, Hali ya dawo, tana waya da huzaifa dakuma Didat, saide har yanzu bata fada musu suturo ba, kwata kwata tama manta da maganar





(idan kinsan baki biya littafin nanba kika karanta nabarki keda mahaliccinki)


Daddy ne yasa Ummah tasake yimata maganar, haka ta zauna adaki tayi shiruuu abun duniya yafara yimata yawa,cikin sauri ta turawa huzaifa text, tayi masa maganar, Amma shiru bai turo mata amsa ba,tayi tunanin ko baiga text dinba ta kirashi ya dauka Amma saiya bata haquri cewa zai nemeta,har akai kwana biyu Didat bema kirata ba bare suyi maganar.

Yauma kamar kullum tana daki a zaune tana aikin tunani, Maya ce tazo gidan suka hadu dasu yanbiyu suka shigo Dakin, Sai mita take musu basa son zuwa gidansu

Zama sukai a Dakin Sai hira suke, Amma Waheeda tayi shiru, Maya ce ta kalleta tace "qawata meyafaru ne?"


Waheeda tayi ajiyar zuciya tace "Daddy yasake min maganar auren Nan, na turawa Didat text yaturo iyayensa, Amma har yanzu banji yacemin komai ba"

Wani irin yatsina fuska Maya tayi tace "Didat Kuma? Ke a ganinki wannan sonki yake? Kawai be'iya komai ba Sai kishi, dama Huzaifa kika Bawa Dama"

Ihsan tace "ato fada mata de, danma bakiga yanda yake bane Maya, wallahi yahadu"

Intisar tace "kuka Sani ko Didat din tafuso?"

Waheeda ta murgud'awa intisar baki tace "waye yafada miki Ana mantawa da first lover?"

Inti tace "to karki min rashin kunya, inde Didat ne keda shi, Ina soyaiya abinda kusan sati kikai a kwance babu lafiya Koya leqo qi, gashinan Huzaifa yazo, kije ki qarata da Didat d'in"


Maya tace "Gaskiya Nima Ina ganin Gara Huzaifa, kawai ki share Didat d'innan kiza6o mana Huzy"

Waheeda
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment