Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tana kuka, Sa'ad ne yashigo Dakin yace ta shirya kayanta karfe goma zasu tafi, tanajin abinda yace tasake rushewa da Kuka, harta Bawa yanbiyu tausayi suma suka fara share hawaye ๐Ÿ˜ฅ, sune suka shirya mata kayanta tsaf, sannan Ummah tazo ta lalla6ata taci cake da madara, sannan suka tafi, tabawa kowa tausayi a gidan, Hajiya Anty Kam dataji labari kasa zuwa gidan tayi, zuciyarta bazata dauki hakan ba, gashi babu damar Hana tafiyar Tata tunda Babban Yaya ne ya yanke hukuncin, iyayen nasu sun bashi power sosai babu yanda za'ayi ya yanke hukunci aqetara shi.

Lokacin dasuka kaita,riqesu tayi tanata kuka, saida principal din yasa wata yar ss3 ta riqeta suka tafi hostel tareda kayaiyakinta.

Wunin ranar haka Waheeda take addu'ah cikin ranta Allah yasa karsu Babban Yaya suci match din dayace zasu buga๐Ÿ˜‚

Wannan yar Ss3 din data kaita hostel, Mai suna Rabi'at itace ta dinga bata hakuri ranar, Sai lalla6a Waheeda take tana kwantar da'ita ajikinta, tun Waheeda tana daukar abun na Hankali Sai kuma taga abun yafara wuce Hankali, taga agida ko jinya take yanbiyu basa kwantar da'ita ajikinsu, bare yanzu da lafiyarta kalau, Kuma bawani girman ta tayi ba, Kuma ita a aji biyar din datake anan aka Barta, duka duka tsiran aji dayane a tsakanin su bare ta nuna mata wani abu.
Duk wani abu da tasan ba'a sakawa a makaranta doka ne, tahana Waheeda sakawa, su ribom, zobe, Dan kunne, dasu kwalliya, duk tayiwa Waheeda bayani Kuma ta hanata sakawa.


Washe gari karfe biyar da Minti goma na asuba aka tashe su, Bayan sallar asuba gari yana haske aka sakasu share share, wasu wankin toilet, tun a lokacin Waheeda tafara raina kanta, agida basa irin wannan aikin, Sai yanzu tasake tabbatar wa Babban Yaya yana mata tsana mafi muni, mutumin dazai kawoka wannan muhallin ba qaramin maqiyinka bane,๐Ÿ˜–๐Ÿ˜ƒ
Daqyar tayi sati daya, kafin tafara sakewa da sauran dalibai, acikin sati dayan da tayi harta hada group na qawaye irinta marasa jin magana,Neenah da zuly.


Kansu ahade yake, kudin datazo dashi makarantar shi take sakar musu suke yin komai da komai yanda ransu yakeso, shiyasa tana basu umarni sukebi.

yau data tashi da safe Bayan tagama komai zobunan gold dinta da wannan yar Ss3 din tasata tacire ta6oyesu, suta Dauko tasaka tatafi aji

Malaminsu yana karatu yaga hannunta Sanye da zobe yace "ke ba'a fada miki ba'a zuwa da zobe ko Dan kunne aji ba?"

Tace "Malam hannu nane yayi wani iri sungul babu kyan Gani shiyasa nasaka"

Malamin yace "kwalliya kikazo yi kenan" daga fadar haka ya ajiye littafinsa yafita waje yanemi bulala, yana fita ta daga kanta ta kalli silin din ajin taga wani ya6ule, tatashi tataka kan bancin dasuke zaune tasaka zoben aciki, ta kalli Yan group dinta tace "duk Wanda yafada ku gane min shi, nadena bashi ko sisina"

Malam yana zuwa yace ta bashi zobe tace ita babu wani zobe awajanta, ya tambayi Yan ajin kowa yayi shiru, qarshe baqin ciki ne yasa malamin yahadasu yadakesu gaba daya, ya dauke littafinsa yafice daga ajin๐Ÿ˜Ÿ


Washe gari da abincin ta tafita class bataci a hostel ba saboda ta makara, Kuma an hanasu zuwa da abinci class, tana hango malama tayi sauri tajefa flas din abincin Bayan window, duk wani Salo na6oye abu idan aka zo qwacewa tasan yanda zatayi ta6oye

Saida yagama karatun sa yafita, sannan tasake haurawa ta window tadauko abincin ta taci, tana gama ci senior master dinsu yashigo da wata qawar Rabi'at Wadda Waheeda ta dauketa suka tafi hostel ranar da tazo, agaban allo ya zauna yace "duba minsu daya Bayan daya, principal yace akwai Wanda suke zuwa da waya acikinsu, jiya an tsinci sim card, Kuma zasu iya aikata wa, maza maza duba minsu"

Qawar Rabi'at tazo tafara dubawa, ko'ina saita laluba ajikinsu ko sun 6oye wayar, tana zuwa kan Waheeda taji wani farinciki ya kamata, dama tunda taga Rabi'at tazo da'ita taji tana son yarinyar, ta yiwa Rabi'at magana akan ta Amma taqi bata goyon baya, saboda itama so take takafa Tata gomnatin acikin zuciyar yarinyar, malamin yace "dubamin ita mana, me kike jira ne?"
Cikin sauri ta nufi Waheeda tafara shafa jikinta, hips dinta take shafawa har matsawa take cikin wani irin Salo, malamin yajuya yana amsa waya tafaki idon sauran dalibai tazura hannunta cikin hijabin Waheeda da sunan duba waya tafara matsa mata boobs dinta, Kallan Waheeda tayi takashe mata ido tana sake murza mata nashanunta, Waheeda ta taqarqare tabige mata hannu cikin tsawa tace "Dalla malama Niki Bari, kawai sai wani lalube min jiki kike"

Tsoro ne yakamata, malamin yakashe waya yajuyo ya kalleta cikin fada yace "kunji min marar kunyar yarinya, mezata laluba a jikin ki qwaila dake? Idan kinsaba yiwa sauran malamai rashin kunya to ni duka zakici"

Murmushi tayi tace "malam ai kasan yarinya ce qarama, saida lallama, babu wayar ma ajikinta"

Tsaki yasaki yace mata"muje"
fita sukai daga ajin suka shiga wani




Bayan sun koma hostel sunacin abinci da qawayenta ta Kalle su tace "nifa barin Dakin da Rabi'at dinnan take zanyi, saboda abinda take min yafara isata, saita dinga Jana ajikinta tana wani shafani, haka dazu ma qawarta ta dinga ta6amin Nono, nayi magana malam yayi fada"๐Ÿ˜”

Neenah tace "tabdi kece kika yarda, kitsaya suna lalube miki, qirjinki yazube, sun Riga mijinki ta6awa"

Tsaki tasaki tace "tun yaushe wani tsinanne yata6a? Ai bazan taba yafe wa Aryan ba, inda ace Babban Yaya yaji, nasan kasheni kawai zaiyi"

Zulaihat tace "wani term din kawai kibar Dakin kidawo namu, qaro mana abincin Dan nikam ban qoshi ba, banaso yunwa ta kamani narame"

Waheeda tace "to waye yace miki cin abinci ne takesa mutum qiba? Ai kwanciyar Hankali ne"

Zulaihat tace "to idan bancin ba tayaya Hankali na zai kwanta?"

Haka suka gama firarsu da yamma sukai class

Washe gari suna aji babu malami a ajin, ta hango wata malamar hausa, yar Gayu ce malamar tanata taku daidai, Waheeda ta daga murya tace "Wanka yabi jiki malama"

Cikin sauri malamar tajuyo tace "me kikace?"

Waheeda tace "wanka yabi jiki"

Bulala ce a hannun malamar aikuwa ta Juyo tashiga ajin saida tayiwa Waheeda Bulala shida, Ana gama mata Bulalar takade hannunta tace "aibaki birgeni ba tunda baki kasheni kinkaiwa su Babban Yaya gawata ba"

Malamar ta kalleta tayi qwafa tafice daga ajin

Ita Kuma Waheeda Takoma ta zauna,6acin rai ne yasa malamar tatafi staff room ta fadawa sauran malamai, anan kowanne malami yake fadar irin rashin jin datake masa, malamin Qur'an ne kawai bata masa ba

Shima period dinsa tana shiga, yazo ajin yafara biya musu Qur'an suna karanta wa, Waheeda tafara surutu ahankali yana ganin ta ya shareta, dataga bai dauki mataki akan ta ba kawai saitaci gaba da surutun ta, saboda already tariga ta'iya wajan tun a islamiya, tsayawa yayi da karatun yace "inada wani uzuri yanzu, next week zan dawo muci gaba" yana fadar haka yafita daga ajin, yaga alama yarinyar bataji, idan yayi mata magana Kuma zata Iya masa rashin kunya agaban sauran Yara, Kuma hakan babu dadi, danhaka ya haqura dabiya musu karatun yafita โ˜น๏ธ

Da yamma suna hostel yau labour day ne, kowa share share yake makarantar tayi tsaf

wata yarinya ce yar js1 ta kawo mata wasiqa, tana dubawa taga qawar Rabi'at ce ta aiko mata wasiqa tana sonta, yaga wasiqar tayi a wajan, tayi wani irin tsaki





Haka Nan taji gaba daya makarantar tafita daga ranta, kullum addu'arta daya Allah yasa su Babban Yaya sudena cin qwallo,๐Ÿ˜… Jira take gari ya waye ta kira Ummah a wayar wani malamin ta fada mata abinda yake damunta
Da daddare tana bacci cikin dare taji kamar Ana shafa mata wuya, tayi juyi tasake shigewa cikin Bargo, taci gaba da bacci can taji anriqe mata nipples dinta Ana murzawa, gabantane yafadi tabige hannun tatashi cikin sauri tana dube dube, Dakin duhu qirin babu abinda take Gani, jikinta tafara ta6awa sannan tayi addu'ah Takoma ta kwanta, bacci me dadi yafara daukarta taji an toshe mata hanci da baki andanneta Ana matsa mata qirjinta, kokawa tafara Amma babu riba saboda mutum biyu ne, tanajin yanda aka cire mata Riga Sai murza mata nipples dinta ake kamar za'a cire mata su,kuka tasa tana motsi tana so ta qwace jikinta Amma takasa, Sai hawaye take babu damar numfashi babu damar magana, jitayi kwata kwata bata numfashi kamar zata mutu, ba tasan lokacin da tasa qafarta tahauri wata aciki ba, anan tayi nasarar qwace Boobs dinta daga hannun su, tana jin ansaki bakinta takurma wani uban ihu, aikuwa Yan dakinsu suka tashi, masu a'uziyya nayi masu kunna torch light nayi, daki ya dauki hayaniya, kowa yazo kanta yana tambaya menene, kasa magana tayi Sai zare idonta take tana Kalle Kalle, tahade jikinta waje daya, bata samu damar rera kuka Bama saide hawaye ๐Ÿ˜ฅ

A Daren, kasa komawa tayi ta kwanta, takuma sa a ranta tabar wannan Dakin daga yau, dakinsu Neenah zata koma, da safe kasa saka brezia tayi, saboda gaba daya kan nonon ciwo suke mata, jitake kamar ta ciresu ta jefar, gashi babu Ummah akusa, babu yanbiyu bare ta fada musu ko zataji dadi, haka tafita aji babu brezia Amma tasaka hannunta acikin hijabi babu Wanda zai gane

Period din farko malamin qur'an yashigo ajin, yana ganin Waheeda gabansa yafadi, fatansa daya Allah yasa su wanye lafiya, yana biya musu, Bayan kowa ya karanta saiyace "akaranta mutum d'aid'ai"

Layin farko sun fara biyawa, Waheeda takasa nutsuwa saida tafara yiwa Neenah magana akan abinda aka mata daran yau, tace "Neenah, yau dakinku zan dawo, jiya bakiji yanda akamin ba, aka kama kan Nono na aka riqe kamar za'a cire, har yanzu zafi nakeji yanda kikasan namutu wallahi, Kuma Ina tunanin su Rabi'at ne itada qawarta, saboda jiya da yamma qawartata har wasiqa ta aikomin tana sona, Kuma...."

Kafin ta qarasa magana,ya mu'allim yace "ke..."

Wata daga cikin yaran tajuyo ta kalli su Waheeda tace "Virus Ana magana"

Waheeda tace "au Dani yake? Bansani Bama saboda ba daidai nakeba yau"

Kallan ta yayi yace "ke futo Nan"

Babu musu tafuto, ya dauki dorinar dake gefensa yafara tsula mata ajikinta, gashi jiki babu vest bare taji sauqin saukar bulala๐Ÿคฃ, tun tana mazewa harta dawo tana kuka,haquri tafara bashi Amma ya mu'allim Sai dukanta yake, data gaji da shan azaba kawai saita tashi tayi masa ta Babban Yaya, ta cacimeshi ta rungume shi,๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ?

Aji aka dauki ihu, wasu daga cikin su suna cewa "Virus mu'allim ne"
Sai ihu suke, mu'allim yayi azama yacireta daga jikinsa yatafi staff room ransa abace, yana zuwa yasamu principal cikin fishi yace "ranka yadade daga yau nayi resigned, nabar makarantar Nan, harni da girmana da komai yarinyar Nan zata rungume ni?"

"wacce yarinya?" cewar principal

"yarinyar Nan marar kunya mana Waheeda Virus, gaba daya ta addabi kowa,last week Ina karatu tanamin surutu a aji, ta ganni mun hada ido Amma taci gaba da surutu, to bazan iyaba, saide ku za6a koni ko ita"

Principal yace Akira masa Waheeda, tana zuwa ta tsugunna agaban sa tace "Gani sir"

Yace "Waheeda Yaya akai kika rungume ya mu'allim a aji? Kinada Hankali kuwa?"

Hawayene ya silalo daga idonta tace "sir, dukana yayi, naji zafine sosai bansan na riqeshi ba"

Principal ya kalli ya mu'allim yace "tokaji abinda tace, kaikuma metayi har akai mata irin wannan Dukan dahar yarinya zata kasa sanin ta rungume malami?"

Ya mu'allim yace "surutu take muna karatun alqur'ani"

Principal ya kalli Waheeda yace "meyasa kikai masa surutu yana aji, bakisan girman malamin ki bane?"

Idonta ta goge tace "Sir jiyane da daddare Ina bacci ake ta6amin qirjina, shine nake Bawa Neenah labari a aji, shine ya ganni yace nafuto, Ina futowa Sai ya kama dukana"

Gaba daya malam wajan ne suka hada baki tareda tafa hannu suna fadin "la'ilaha illallah....."

Principal yazaro ido๐Ÿ˜ณyace "aka ta6a miki me? Waheeda har sharrin naki yakai haka? Acikin makaranta ta ake aikata wannan ta'asar? To Bari kiji, saboda ke bazan yarda malami ya ajiye aikinsa ba, hakan bai isheki ba saikin hada kinyiwa dalibaina sharri, malamai sun gama complain akan ki bakya jin magana kwata kwata, saboda haka kitafi gidanku Sai iyayenki sunzo "๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ?

Waheeda tayi shiru tana nazarin maganar sa,gaba dayama satinta uku acikin karantar mezatacewa su Ummah agida idan suka ganta tadawo gida yau? Mezasu fadawa Babban Yaya? Bata gama tunani ba taji principal yace Akira masa mama mairo, matar datake kula dasu a hostel

Mama mairo tana zuwa, yace "ga kudin mota Nan, kidauki wannan yarinyar, da duk kayanta, kikai ta gaban iyayenta kifada musu hukumar makaranta tace akawota gida Sai iyayenta sunzo"

Mama mairo tacika umarnin principal, akaje aka debo kayan Waheeda, suka kama hanyar garinsu

itace ta dinga nuna mata hanya har suka qaraso get din gidan, karfe goma shadaya daidai agida tamusu

Ummah tana kitchen tana kokarin Dora abincin rana saboda yanbiyu suna makaranta, saiji tayi anfado jikinta Ana kuka

Dafarko tsorata Ummah tayi, saboda tasan cewa ita kadai ce a gidan, tana juyowa taga Waheeda duk tayi baqi, cikin tsananin mamaki tace "Waheeda?!!!" ๐Ÿ˜ฑ















Amnah El Yaqoub โœ๐Ÿ?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama๐Ÿ˜‡: BABBAN YAYA


Writing By Amnah El Yaqoub


Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/


7&8


Mama Mairo taqaraso kitchen din itama "Hajiya Ina kwananmu?"

Ummah tasaki Waheeda ta kalli matar, ta manyan ta sosai, aqallah zatayi shekara hamsin dawani abu, tace "Sannu baiwar Allah, mu qarasa falo mana"

Falo suka dawo suka zauna, Ummah ta nufi fridge zata kawo mata ruwa da lemo, mama mairo Sai jinjina Kai take tana qarewa falon nasu kallo, idan banda abu irinna iyayen wannan yarinya mezaisa 'yarsu tana rayuwa acikin wannan daula zasu dauketa su kaita boarding? Gashi Ana nema a lalata yarinya, koda yake kowa da halinsa

Ummah tadawo ta zauna tabud'e lemon ta zubawa mama mairo tana cewa "ga lemo Kisha mama, meyake faruwa ne Naga Autata agida? Wani laifin ta aikata ko?"

Mama mairo ta ajiye cup din hannunta Bayan tagama shan lemon tace "hajiya kinsan sha'anin Yara Sai hakuri,hukumar makaranta ce tace a dawo da'ita gida Sai iyayenta sunje"

Ummah ta dauki waya tana fadin "subhanallah, Bari nakira Yayansu"

Gaban Waheeda yafadi, tasan cewa inde yaji ankorota tabbas zai dawo qasar Nan, Kuma yayi mata gargadi karta yarda ya dawo qasar Nan saboda ita, saboda Dama can matsalar tane yake sakawa ya dawo, shide akaran Kansa yana dadewa kafin yazo gida, saboda yasan indai ya dawo to maganar aure zasu masa, cikin sauri ta riqe hannun Ummah tace "Ummah Dan girman Allah karki kirashi, kibar Yaya Sa'ad da Yaya Sa'eed sumin komai, Dan Allah Ummah kirufamin asiri kar Babban Yaya yaji"

Ummah tazuba mata ido tana Kallan ta, tunda taga haka tasan cewa to Waheeda ta yi wani laifin ne, tace "saina kirashi Waheeda, shine daidai dake tunda ba zakiyi Hankali ba, Anya ma kuwa kina wanka Waheeda? Sati uku da tafiyar ki duk kinyi baqi kamar baki ta6a ganin ruwa ba?" ๐Ÿค”

Mama mairo tayi murmushi tace "Hajiya Bari nawuce kar rana tayi"

Ummah tace "Ina zuwa mama"
tashiga daki takawowa mama Mairo kudi dakuma turamen atamfa guda uku, cikin murna mama mairo takar6a tayi godia tayi musu sallama sannan tatafi Sai yabawa tsarin gidan nasu take

Ummah ta zauna a kujera, tana zama Waheeda tadawo jikinta ta maqalqaleta,jitake kamar za'a sake maidata wannan makarantar, kwata kwata batajin dadi, Kuma batajin zata sake komawa saide tagudu ranar da'aka ce za'a maidata
Ummah tace "Waheeda, kifadamin abinda kikayi aka koroki, rashin kunyar kika sake musu ko?"

Kuka ta Fashe dashi,takasa magana, Ummah tazuba mata ido tace "ikon Allah, bazaki min magana ba kin tsaya kina kuka?"

Cikin kuka tace "Ummah Dan Allah karku maidani, please karki fadawa Babban Yaya"

Ummah tayi shiru batace da'ita komai ba, tasake daukar wayar ta tayi dialing number Naufal, har wayar tagama ringing ta katse bai dauka ba, Sai daga baya yakirata, Ummah ta dauka tace "Yayansu toga Waheeda Nan andawo da'ita gida, sunce Sai iyayenta sunje"

"what?" abinda yace kenan

Ummah tace "to haka de matar data rakota tace, hukumar makaranta sunce akawota gida Sai iyaye sunje"

Shiru yayi yakasa cewa komai, itama Ummah tayi shiru, tayi tunanin ma bazai ce komai ba Sai can taji yace "Bata wayar"

Umma ta miqawa Waheeda waya tace "ga waya inji yayanku"

Cikin kuka tace "Ummah Allah Zagina zaiyi" tatashi tashige dakinsu da gudu cikin kuka

Ummah ta maida wayar kunnanta tace "to taqi kar6a,Kuma Nima taqimin bayanin abinda tayi, matar data kawota Kuma tatafi, itama bata tsaya tamin bayani cikakke ba, Kuma tunda kaga ta 6oye ai kasan laifin Waheeda ne"


"Allah yarufa asiri" abinda yace kenan

Ummah tace "Amin" tareda kashe wayar, tasan dole zaizo, Kuma zai dauki mataki akan haka


Waheeda saita taji Ummah tadena wayar sannan tadawo falon, Ummah ta kalleta tace "saikije kicire kayan ai, kiyi wanka, nasan bakya wanka Waheeda"

dariya ce ta kamata, tayi murmushi ta wuce dakinsu, wanka tayi sosai, sannan ta kwanta bacci, bata tashi ba Sai daya saura, tana futowa falo taga Ummah tana waya da Hajiya Anty, tana fada mata Waheeda tayi Hali andawo da'ita gida ๐Ÿ˜‚

Kitchen ta wuce ta yanka salat, tafuto falo zata hada taci, yanbiyu sukai sallama, suna ganin Waheeda suka saki ihu, suka rungume juna

Ummah ta Kalle su tayi murmushi tace "yauga wasu irin yayu, kunganta agida bazaku tambayi dalili ba kawai saide kuhau ihun murna?"

Babu Wanda yabawa Ummah amsa, duk sun riqe Waheeda suna murna, Ihsan tace "Waheeda kinga yanda kikai baqi? Ko wahala kikesha?infada miki Waheeda tunda kika Dena zuwa makaranta qawarki Maya tazama shiru shiru, abun tausayi kamar anmata mutuwa, saide tazo wajanmu ta zauna"

Waheeda tace "hmm kede Bari kawai Ihsan, Nima nayi missed dinku,boarding babu dadi"

Intisar ta kalli salat din dake gaban Waheeda tace "to aqara yanka wani tumatir din mana"

Waheeda tasake yanka tumatir taja flet din gabanta zata fara Ci, suma suka matso, wani irin kallo tamusu ta kalli Intisar tace "waida harda ku kike nufi?"

Basu kulata ba suka fara ci, ganin haka yasa itama kawai ta sharesu sukaci salat din gaba dayansu

Wunin ranar, haka su Waheeda sukayi shi cikin marmarin juna, babu fada, sun had'e kansu, Sai labarin makaranta take basu kamar basune kullum cikin fada ba.


Kwananta uku agida, Babban Yaya yazo, wannan Karon zuwan dare yayi, shiyasa baisamu cikowar mutane sosai ba, wayar Ummah ce a hannun Waheeda tana yin game, su yanbiyu suna ta Bawa Ummah labarin qawayensu, Sa'ad da Sa'eed suna dinning suna dinner, cikin falon yashigo bakinsa d'aukeda sallama, yana Sanye cikin qananun Kaya dasuka kar6i jikinsa, lokaci daya qamshin turaren sa yacika falon, Waheeda tadago kanta sukai ido biyu dashi, yasaka p-cap yasaka facemask, dakuma wani glass Jan duhu, kwata kwata idan a hanya kuka hadu ba zakace shine ba, ya 6oye kamar sa ne saboda kar mutane su ganeshi suhanashi tafiya, shikuma yagaji sosai hutu yake buqata, ko awanne Hali yake ciki Waheeda zata ganeshi,duk da ya6ata mata rai ya kaita boarding bata jin zata Iya fishi dashi, tanajin sa sosai acikin ranta, ta dauke shi tamkar aboki kokuma wani Amini Nata na daban,yanada mutuqar muhimmanci acikin rayuwar ta

Ahankali ta ajiye wayar Ummah agefenta, cikin dakiya tanufeshi tace "Babban Yaya sannu da zuwa"

Tayi maganar tana qasa da fuskarta, Dan tayi tunanin zataji saukar Mari, Amma ga mamakin ta saiyace "Yauwa"

Yabata wata leda me kyau tareda nuna mata yanbiyu yace "kibasu"

Juyawa tayi cikin ladabi, tabawa yanbiyu ledar tana jira su bude taga menene aciki, suna budewa kuwa sukaga Kayane English wears masu kyau riga da siket, komai iri daya babu banbanci a kayan, murna sukai hauyi kamar qananun Yara, Waheeda tacika tayi fam, Takoma Gefe ta zauna ๐Ÿคฃ

Babban Yaya ya qarasa wajan Ummah yazauna,tareda Dora Kansa akan kafadarta, Ummah ta Kalle shi tace "ya Hanya?"

Kafin yabata amsa su Sa'ad su kazo wajan sa suka zauna, suna masa sannu da zuwa, sumar Kansa ya shafa Bayan ya amsa musu ya kalli Ummah yace "Ummah nagaji wallahi, bacci nakeji"

"to meyasa kataho da daddare? Dakayi zamanka da safe kataho"

Cikin shagwaba yace "Ummah sonake naganki wallahi"

"yau Kuma shagwabar ce tatashi?" cewar Ummah

Dariya yayi, dimples dinsa suka futo, yace "Ummah, yarinyar can ta fada miki abinda yasa suka dawo da'ita gida?"

Ummah ta juya ta kalli Waheeda taga Sai fishi take, tace "gatanan ka tambayeta ko zata fadama, nide ba tacemin komai ba"

Fuskarsa ya daure yace "babu abinda zan tambayeta Ummah, ta shirya kawai gobe zan maidata da kaina, nakira principal din but bai dauki wayata ba"

Ummah ta kalli Waheeda tace "kinji meya ce ai ko? To saiki shirya"

Babu musu Waheeda tace "to Ummah Allah yakaimu" Amma cikin ranta tariga tagama shirya yanda zata gudu tabar gidan, bazata dawo ba Saitaji labarin Babban Yaya yakoma


Tashi yayi zai wuce dakinsa,cikin shagwa6a Waheeda tace "Babban Yaya Toni Ina nawa kayan?"

Juyo wa yayi ya kalleta,yaso Ummah bata Nan dasai yadaki yarinyar Nan, to babu halin duka yanzu, tunda Ummah tamasa fada last time cewa ya dinga jansu ajikinsa, saida ya daure sannan yace "bakiga iri d'ayane kayan ba? Ke yanbiyu ce? Suma nagani ne Kuma su kenan qwaya biyu, shiyasa na Dauko musu"

Tace "to nifa?"

"kiduba irin Wanda kike so" yana fad'a mata haka ya wuce d'akinsa, Ummah ta kalleta tace "tashi ki had'a abinci kikai masa"

Babu musu Waheeda ta nufi kitchen cikin farinciki batare da damuwar komai ba,Dama Babban Yaya takeji, Kuma taga alamun bazai daketa ba


Sosai ta nutsu wajan had'a masa abincin, yanda take had'a komai cikin tsafta zaka iya rantse wa mijinta take hadawa abincin, d'auka tayi ta nufi d'akin nasa, daga bakin kofa ta tsaya tayi masa nocking, saida ta dade a tsaye sannan yazo ya bude mata 'kofar, saura kadan tasaki tiren dake hannunta, sakamakon yanayin data ganshi, dagashi Sai wani Dan gajeran wando, da alama ma wanka zai shiga, gabanta yake faduwa ahankali, cikin nutsuwa ta qarasa gabansa tayi azamar ajiye abincin saboda hannunta rawa yake tsaf zata Iya zubarwa, tarasa meyasa Babban Yaya yake abinda yakeso agaban ta, kwata kwata bayajin kunyar cire Kaya agaban ta, bayajin kunyar su zauna tareda ita dagashi Sai towel din wanka, tasan inda yanbiyu ne cewa zaiyi raina shi zasuyi idan suka ganshi Ahaka, to meyasa ita yake mata haka? Wata zuciyar tace da'ita, may be Dan kun shaqu ne, tunda yana iya hira dake Amma ba yayi da Yanbiyu, ajiyar zuciya ta sauke tafara zuba masa abincin, saida tagama sannan tanemi waje ta zauna, Kallan ta yayi yace "Lafiya?"

"Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri" tafad'i haka hawaye yana silalo wa daga idanunta

"laifin me kika aikata dazaki Bani hakuri?"

"Babban Yaya nasan na takura ma, wallahi Nima ba laifi na bane, yarinyata ce take damuna kawai" ๐Ÿ˜ฅ

Yace "are you serious?, 18 yrs Amma kina cewa yarinta ce take damunki, me kikayi a school din suka koreki?"

Shiru Waheeda tayi, tayaya zata masa bayani? Ce masa zatayi tana yiwa malaman makarantar rashin kunya kokuma dayan maganar zata fada masa? Tayaya zata Iya fada masa magana me nauyi irin haka? Yayanta uwa d'aya uba d'aya shi zata kalla tace wasu suna ta6a mata nonuwa Aida kunya

Hawaye ne suka zubo daga idonta, tasaka hannu ta share tace "kayi Hakuri Babban Yaya"

Kallan ta yayi cikeda mamaki, kawai daga tambaya Sai kuka? Ajiyar zuciya yayi yace "shikkenan, tunda haka kika za6awa rayuwar ki, kina ganin yan'uwanki, banta6a zuwa gida ta dalilin matsalar suba, koda yaushe kece sanadin zuwana, Kuma tunda kika girma kikai wayo babu ranar farinciki dakikamin sanadin zuwanta, kullum matsalar kice takesa nabar aikin danake nazo, kwata kwata bakya tausayi na kamar sauran yan'uwanki,duk zuwan da zanyi Sai iyayena sunmin maganar aure, Bayan kinsan banaso,to saboda me danna Sai musu Kaya zakiyi fishi "

Kanta aqasa tace" kayi hakuri Babban Yaya"

Yace "hmm kamar gaske, Bani abinci na kitashi kitafi"

Abincin tabashi, Amma takasa hada ido dashi, kar6a yayi yafara ci ahankali kamar yaro qarami Wanda baisan abinci, d'agowa tayi ta Kalle shi, ahankali tatashi tahau kan gadon, ta zauna dab dashi, spoon din hannun sa tariqe, ya kalli yanda tariqe masa spoon din yace "miye haka?"

Cikin shagwa6a tace "to Babban Yaya bakacin abincin fa sosai" wani irin abu yaji tundaga Kansa har zuwa tafin qafarsa,kamar bashi ba, Sai gashi ya gagara yimata musu, sakar mata spoon din yayi, tafara bashi abincin yanaci,Kallan ta yake yana mamakin yanda tayi kama dashi sosai, komai nashi ta Dauko, babu wani qarin bayani idan kaganta ka ganshi kasan cewa jini daya ne.

Yace "kishirya da wuri gobe"

Maimakon tabashi amsa Sai tace "Babban Yaya induba rigar danake so a internet saina kawo ma kagani?"

Yace "kiduba"

Mamaki yahanashi kasa yimata wata maganar ta makaranta, tunda yaga alamun akwai abinda take 6oye masa

Saida tagama bashi abincin haryana mamakin yawan abincin dayaci,fita tayi da kwanukan, shikam toilet yashiga yayi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment