Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

wajan zamanta, tamiqawa Babban Yaya saitin bakinsa tace "Babban Yaya haaa"


Dafe Kansa yayi da hannunsa yayi shiru πŸ€¦πŸ»β€β™‚οΈ?

Cikin fada Sa'eed yace "ke Dalla malama kimana shiru, haba, duk kin damemu, yarasa qwan dazaici saina bakin titi saikace ke?"

Babban Yaya yayi murmushi, yasaka hannun sa ya riqe hannun Waheeda data miqo masa qwan, sannan ya karyi Dan kadan, yasaki hannun Nata, Waheeda Takoma wajan zamanta ta zauna, tanacin sauran Wanda Babban Yaya ya karya, har suka kusa Garin, bata sake magana ba, daga qarshe ma bacci ne ya dauketa, saida suka qarasa Garin sannan suka tasheta


Sosai Baba Habu da yayansa sukai murna da zuwansu, Sai Nan Nan ake dasu, matarsa mama Haajara ta shimfida musu tabarma a tsakar gida kowa ya zauna, Ana sake sabuwar gaisuwa


Shayinsu na buzaye tatashi tadora musu,suna fira tana ajiyewa kowa agabansa,ta miqe tace "Bari adora muku abinci, ga miya Nan nagama ta tun safe, Waheeda tatashi tacire hijabin jikinta tace"zauna mama, zan Dora"

Tafadi haka tana nufar inda aka ajiye tukwanen gidan, Babban Yaya ya daga Kai ya kalleta, cikin ransa yace kamar me Hankali

Baba Habu ya dauki wayarsa yafara magana "gasu sun qara so mekuke jirane Baku zoba?"

Daga daya bangaren akayi magana, saiya sake cewa "wanne irin zabbi? Ga kaji Nan tun jiya Haajara take aikin su, zasuci, kutaho kuga yan'uwanku, banason rashin zumunci ni" 🀣

Kallan mama Haajara yayi yace "su Yahya ne, Suda yakamata ace suna gidan Nan dasu zamu karbi baqi Amma ke kiji Wai sun tafi neman zabbi zasu kawo asoya musu"

Murmushi sukayi dukansu, yajuya ya kalli mazan yace "to ku aiba zama zakuyi ba, tashi zakuyi mutafi ku gaisa da yan'unguwa, daga Nan muje na nuna muku gonakin mu, nida iyayenku"

Babban Yaya ya sunkuyar da Kansa baice komai ba, Dan tsoro yake yasan halin tijarar baba Habu karya jaji6o masa wata yarinyar awannan qauyen

Sa'eed yace "Baba yanzu fa kagama cewa baqi,inamu Ina Gona? tokuje dasu Babban Yaya ni zan d'anyi wani abu"

Baba Habu yace "kaji wani sakarci, tokai kana namiji Ina kaga ta zama? Sa'adun ne ko Sa'eedu? Namiji baya zama, kutashi muje"

Sa'ad yayi dariya yace "Sa'eed ne baba, ka ganeshi dakyau"

Haka suka fita badan ransu yasoba, mama Haajara ta kalli tukunyar da Waheeda ta 'Dora, tace "Waheeda wannan tukunyar a6ule take" Waheeda hankalin ta yana kan girki batajiba

Ihsan tace "Waheeda tukunyar da kika Dora a6ule take fa"

Juyowa tayi ta Kalle su, dama aciki take dasu, suna ganin ta tana aiki Amma babu Wanda ya taso acikinsu,sun Barta tana Fama da hayaqi, dankwalinta ta turo gaba, tulun dogon gashinta yafuto ta qeyarta, tace "kibarta taita zuba, Ina wuta tana ruwa, Sai muga wa Allah zai Bawa sa'ah"

Mama Haajara tayi dariya tace "a a Waheeda, ba za'ayi hakaba" tatashi ta nufi wajan girkin, suma yanbiyu suka taso, saita basu salat da tumatir su yanka



Majalissa Majalissa Baba Habu yake yawo dasu Babban Yaya yana nunawa abokai da yan'uwan Arziqi su, kan kace me, matasa sun taru a wajan Babban Yaya, wasu suyi photo wasu Kuma videos, wasu Kuma kawai binsa suke sunata zance, ayawon zaga Garin dasuke suka hadu dasu Yahya, sune suka janye Babban Yaya kasancewar su sa'anni,sannan suka nufi gonar dashi, daga baya baba Habu ya qaraso tareda su Sa'ad, gonakin yafara nuna musu yace "wannan Babbar gonar ta Usman ce, gata Umaru can agaba, duk ni nake kula musu dashi, dazaku iya da munje wasu gonakin daku duk kun Gani"

Babban Yaya yace "Baba gobe Sai muje ai, Sai muga gari ma"

Baba Habu yayi fara'ah yace "eto Kuma kaima kace wani abu, yanzu to riqe wannan fartanyar, gyara min Nan wajan kacire ciyawar nan data futo" πŸ˜‚

Sa'ad yace "baba muda mukazo ganin gona Kuma saimu fara aiki?"πŸ€”

"aiku ba mazaje bane, kubar namiji yayi aiki"

Babban Yaya yarasa abinda yake masa dadi, haka ya karba yafara cire ciyawar dasuka futo, abokan baba Habu ne sukazo wuce wa ya daga murya yace "malam idi, ku qaraso ku gaisa da yarana Yan birni"

Su malam idi suna zuwa sukace "masha Allah, Wai duka Nan yaran Usman da Umaru ne?"

Baba Habu yace "a a, duka yaran Umaru ne, shi Usman ai babu yaro awajansa"

Ya nuna musu Babban Yaya da Kansa yake sunkuye yana Fama da fartanya, yace "ga Babban yayansu Nan nasashi aiki, kuduba kuga qwanjinsa fa, inda zai haqura da wannan tamolar ya dawo Nan mudinga noma Aida yaji dadi, dashi kadai zanbarwa wannan gonar ya nome min ita, haba meza'ai da wata tamola" ☹️ya qarasa maganar yana yatsina fuska

Shide Babban Yaya baice komai ba, Sai abokan baba Habu dinne dasuke dariya dakuma su Sa'ad
Baba Habu yasake Kallan sa yace "kunji yayi shiru kamar salihi, Nan kuwa qungurmin tuzuru ne"

Babban Yaya baice komai ba yanzun ma, Shide fatansa yarabu da wannan tsohon lafiya, abokan nasa ne sukace "ai yanada Hankali, yanzu awannan zamanin ba kowanne Yaya ne zai debo qannan sa yakawo su ganin dangi ba"πŸ˜‚

Baba Habu yace "Eto tanan Kuma yayi qoqari"

Ya kalli Babban Yaya yace "dago haka, muje gida muci abinci kun debo hanya"

Sai a lokacin Babban Yaya yadago, fuskar Nan tasa a daure, babu wasa, haka suka tafi gida, yanbiyu da Waheeda suka zubawa kowa abinci, duk da yaran baba Habu suna zaune aqauye ne hakan baya Hana ganin tsantsar kamar dasuke dasu Babban Yaya, kana ganinsu kaga jini daya.


Baba Habu ya kalli Babban Yaya yace "Ai kamata yayi daga Nan kunufi gida can Niger, can ma kuje kuga yan'uwa"


Sani yayan Yahya yace "qwarai Kam baba, kaga Yan biyu da Waheeda ma Sai suhau a male, nasan basu taba Hawa ba"


Babban Yaya yace "saide wani lokacin baba, saboda makarantar su, idan aka musu hutu, Sai muje"

Uzurin daya basu ne yasa suka amince da maganar tasa, Amma badan makaranta ba, yasan Sai sunje.


Washe gari suka fita ganin gari da safe, Waheeda wani Riga da wando tasaka, kayan sun kamata sosai, amma data saka dogon hijabi babu Wanda yake ganin ta, sunga gari sosai, sune har Rafi ganin ruwa, su Sa'ad suna tareda su Yahya, shikuma Babban Yaya yana bayansu Waheeda yana tafiya yana danna wayarsa.

Fakar Idonsa Waheeda tayi, tacire hijabin Nata,hips dinta yacika wandon taf, sannan ta tattare qafar wandon, tashiga ruwan tafara wasa, suma yanbiyu da sukaga Babban Yaya hankalinsa yana kan waya suma suka shiga, dago Kansa yayi ya gansu suna wasa, bece musu komai ba yanemi waje ya zauna yaci gaba da abunda yake

Cikin tashin Hankali yanbiyu suka fara Kiran sunansa, suna nuna masa Waheeda, yana dago Kansa ya hango Waheeda acan tsakiyar ruwa tana mututuwa idonta Sai juyawa suke ruwa yana gaba da'ita, baisan lokacin da yayi jifa da wayar ba, ya qwala mata kira, sannan yanufe ta da gudu

Yanbiyu suka futo da gudu sukayi wajan su Yahya da Sa'eed zasu fada musu


Batare da tunanin komai ba, Babban Yaya yafad'a cikin ruwan, kafin ma ya qarasa wajan ta hartasha ruwa ta suma, d'aukota yayi tamkar ya dauki jaririya


Cikin tashin Hankali yafara tatta6a jikinta yaji shiru, jikinsa ne yad'auki rawa, fuskarta yakama yariqe yana fadin "ke! ke!! Dan Allah karki tafi"

Jijjigata yake yana fadin haka Amma Waheeda shiru ko motsi takasa, gaba d'aya yanemi nutsuwar sa Yarasa, gabansa yafara fad'uwa kana Kallan faffad'an qirjinsa zaka tabbatar da haka, ta hanyar bugun zuciyar sa, shiru yayi yarasa abin yi, tunani yayi Ana danna cikin Wanda yasha ruwa, yasaka hannunsa akan shafaffan cikinta ya danna Amma ruwa be futo ta bakinta ba, zuciyarsa ce take bashi wata shawara yana yakicewa, daga qarshe Sai ra'ayin zuciyar tasa yabi, saida ya qarewa lallausan pink lips d'inta kallo, sannan ahankali ya sunkuya yahad'e bakinsu waje d'ayaπŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?
Duk yanda zuciyarsa take gargad'insa akan kar yayi komai Bayan iska dazai hura cikin bakin Nata, hakan bai samu ba, laushi da Kuma santsi irin na lips din Waheeda ya d'ebeshi yafara kissing dinta,wannan ne Karon farko daya ta6a kissing din mace a rayuwar sa,wani irin dad'i yaji sosai,saida ya tsotsi lips dinta son ransa, sannan yahura mata iska cikin bakinta da qarfi, sannan ya d'auke lips d'insa daga kan Nata.
wani irin Tari ne yataso mata, a Hankali tafara bud'e idonta, harta bud'esu gaba d'aya, ta d'orasu akan Babban Yaya daya zuba mata ido yana Kallan ta, babu Wanda ya tankawa d'an'uwansa acikinsu, Sai ido dasuka zubawa juna, kowa yana tunani cikin Ransa, tsantsar kyawun dan'uwan Nata take kallo, haqiqa yahad'u harya gaji da had'uwa, shi abin sone ta kowanne fanni,ita kanta tana sarawa yayan nasu wajan iya Gayu dakuma d'aukar wanka.

idanunta Babban Yaya yake kalla a zahiri, Amma abad'ini yayi Nisa cikin tunani, inama zata soshi kamar yanda yake sonta?koda yaushe zuciyarsa tana fad'a masa cewa, bashida mata Sama da'ita, ita din tasa ce shi kad'ai, but tayaya hakan zai kasance?







To Alhamdulillah free page yazo qarshe πŸ₯±

Gashi zan Dena yimuku posting Baku fadamin suwaye iyayen Naufal da Waheeda baπŸ˜‚πŸ˜‚


Dama nafada muku BABBAN YAYA na kudi neko?
Ina Wadanda suke buqatar jin qarshan labarin? Kwamacala tana gaba aradu, yanzu aka fara wasan πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

Da abaka labari gwara ka bayar πŸ‘‡πŸ»


200 posting daya a rana

VIP 400 posting biyu a rana

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaku turo shedar biya ta wannan numberπŸ‘‡πŸ»
08033300034



Ga masu kira, text message, whtsapp, duk ku nemeni ta wannan numberπŸ‘‰πŸ» 08033300034





Next Novel SHAHAB.....

Salonsa daban yake, zaizo muku bada dadewa ba πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
















Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:50 - Ummi TandamaπŸ˜‡: Jikinsa ne yayi Sanyi Bayan tunawa da irin qalubalen dayake gabansa akan hakan, ahankali yakawar da fuskar sa Gefe, sannan ya tashi zaune yakama hannunta yariqe yana kokarin tashinta, jitayi kamar bashida qarfi, taga jikinsa yayi Sanyi, shi kuwa Babban Yaya yanayin daya shiga ciki ne bai gama sakinsa ba, ashe haka akeji? Kokuma de shine yaji dadin sosai saboda wadda yake soce yayiwa kiss din? Tashi tayi zaune, har zuwa lokacin hannunta cikin nasa, tana 'Dan qaramin Tari kad'an, a taqaice yace "Sannu"

'Daga masa Kai tayi tace "Babban Yaya da yanzu na mutu, nide mubar Garin Nan, tsoro nakeji"

Fuskarta yariqe yana Kallan qwayar idonta yace "kidena cewa Zaki mutu, banaso"


Murmushi tayi masa, kafin tace wani abu su Yahya suka qaraso,'yanbiyu suka jata zuwa gida,tafiya suke a hanya gaba d'ayansu suna jajantawa juna akan abinda yafaru

Da daddare kasa bacci yayi, haka ya dinga juyi akan gado hannun sa yana kan mararsa datake masa wani irin mugun ciwo, yana tuno laushin lips din Waheeda saiyaji kamar yaje yaqaraπŸ˜³πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?, Sai gab da asuba yasamu bacci ya d'auke shi Bayan ya kwanta rub da ciki, saida ya makara sallar asuba, baida tsarki, saida yayi wanka sannan yayi sallah sakamakon wani irin mafarki da yayi na Waheeda me dadi.


Sai wajan shad'aya
'yanbiyu suka kawo masa abinci, yanaci kuwa yafuto tsakar gida d'aukeda kayansu, koda ace Waheeda batace tanajin tsoron Garin ba, ya zama dole sutafi, bazai juri rashinta atare dashi ba, idan ta mutu a wannan qauyen shi waya kama kenan? πŸ˜‚πŸ€”

Baba Habu yace "a a, ya naganka da Kaya? Ina zakaje"

Kasa yayi da Kansa yace "baba anmin waya ne a wajan aiki, Ana nemana, shiyasa zamu tafi"

"to Amma tafiya babu shiri Naufal? Meyasa bazaku Bari Sai goben ba?"

Murmushi yayi yace "baba zamu sake dawowa"

Haka yahad'a kan qannansa kowa yahad'a kayansa, suna saka kayansu cikin booth din motar wasu samari suka qaraso wajan Babban Yaya suka bashi wata latter, dubawa yayi sannan yayi murmushi, ya Kalle su yace "inde kayan Ball ne, zan turo muku dashi, harda takalma"

Ihu suka Hau yi kowa yana qara yimasa godia, inna Haajara tacika su da kayaiyakin qauye su manshanu da Kuka, dakuma kindirmo, haka suka tafi cikeda kewar 'yan'uwan su su Yahya.


Washe Garin ranar dasuka dawo daga qauye, Daddy da Ummah da Uncle Usman suna zaune afalo suna kallo, Sa'ad da Sa'eed suka shigo falon kansu aqasa, agaban Ummah suka zauna, uncle Usman yace "to 'yanbiyu mekuke sone Naga Kuna sunkuyar da kanku?"

Sa'eed ya Sosa qeyarsa yace "Uncle Dama... Dama uncle..." saikuma yayi shiru yana zungurin Sa'ad

Daddy yayi dariya yace "tunda kaga haka ai zancen bazai wuce na neman kudi ba zasu sauya mota, aikinsu kenan, kuje wajan yayanku yabaku, shine me kudi"

Murmushi sukayi, Sa'eed yace "Daddy Bahaka bane, dama gidansu Hassana ne akace muturo akai kudin gaisuwa"

Uncle Usman ya gyara zama yace "a a, babbar magana, kuce abun yazo" πŸ˜ƒ

Sake sunkuyar da kansu sukai cikin kunya

Daddy yayi murmushi yace "Kundage de Kuma yanbiyu zaku aura kamar ku,kuje ku kiramin yayanku, ai dashi yakamata kufara magana, shikuma saiya fad'a mana"

Tashi sukai suka nufi wani daki kusa da 'Dakin Babban Yaya, babu komai acikin 'Dakin Sai kayan Ball, dagashi Sai qananun Kaya da ball, yana bugawa shi kadai, zama sukai suna Kallan sa, daina abinda yake yayi, ya dawo kusa dasu ya zauna yace "twins ya akayi ne?"

Sa'eed yace "Babban Yaya mun dade bamuyi Ball bafa"

Kallan sa yayi yace "shine matsalar?"

Sa'ad yace "Babban Yaya wallahi ba'ita bace, gidansu Hassana da Hussaina sunyi magana, mu turo akai gaisuwa, Dan Allah Babban Yaya kacewa su Daddy a saka harda ranar ma gaba daya"

Babban Yaya ya saki murmushi yace "um Um... Ashe aure kukeso shine kuka qi magana?"

Dariya sukayi dukansu, yace "to shikkenan, idan nagama zanyi magana dasu Daddy"


Godia sukayi masa sannan suka fice daga Dakin, yana ganin fitarsu yazube a wajan, yafada duniyar tunani, Sai yaushe ne matsalar sa zatazo qarshe ne? πŸ€”

Ko awa d'aya bai qaraba yanufi wajan su daddy Bayan yayi wanka yagama shirya wa, Kansa yana qasa, Bayan yagama yimusu bayanin abinda yakawo shi, uncle Usman yace "yanzu Kai haka kaza6awa rayuwar ka? Maryam qanwar 'yanbiyu tayi aure, abar wannan maganar ma, ita mace ce, toga 'yanbiyun suma sunyi magana, Naufal, yakamata ace ka nemawa kanka mafita, zamanka haka bazai iyu ba, musuka fara fad'awa maganar, muka turo su wajanka, munyi tunanin hakan zaisa kaima ka kawo taka Sai ahad'a ayi gaba d'aya, ashe har yanzu kana Nan kakasa tsaida magana d'aya, maganar gaskiya bazai iyu su Sa'eed su Riga ka aure ba, muna so Kai kafara saboda kaine Babba, tayaya zasu auri Yara sukawo su gidan Nan, Yara su dinga gaisheka a matsayin yayan mijinsu suna ganinka babu aure ba?, saboda haka mun yanke shawara, bazamu hanasu Kai gaisuwa ba, Amma babu maganar sa rana, saka rana Sai Bayan bikinka, kaikuma za'a saka ranar ka yanzu, Kai saka rana, sukuma Kai gaisuwa, Bayan bikinka Sai ayi nasu, akwai yarinya me Hankali sunanta Ummi, kama Santa, Nan maqo tanmu take, Bama saikaje ganintaba bare Asamu matsala, kawai za'a saka ranar, tashi katafi "



Tunda Uncle Usman ya fara masa magana yarasa gane Ina yake zaune? Jiyake kamar a mafarki Wai shi za'a had'a da ummi, yarinyar da kowa ya Santa batada kunya, sude burinsu shine yayi aure Amma babu ruwansu da yarinyar ta dace dashi ko bata dace ba, tasa qaddarar kenan kullum idan yazo Nigeria Sai anyi masa maganar aure, Bai iya cemusu komaiba Sai "to Uncle" daga Nan yatashi yanufi d'akinsa yana tafiya yana had'a hanya, domin kuwa wani irin baqi-baqi yake Gani, yana bude kofar d'akinsa yana kokarin shiga har bige goshinsa yake, Amma baidamu ba, abinda yake ji acikin zuciyar sa yafi bige goshin zafi,kulle Dakin yayi yafad'a kan gadon sa, wani irin hawaye me zafi ya silalo daga idanunsa, lokaci daya yaji duk duniyar tafita a ransa
Bashida wata sauran dabara illa ya kar6i ummi a matsayin matarsa, basu bashi Dama yaje ya ganta Bama bare yayi wata dabarar daya saba yarabu da'ita, tabbas yasan Ummi, yarinyar akwai muni ba laifi, ga rashin kunya, jikinta ne kawai me kyau, tsakanin gidansu da gidansu Babban Yaya gida uku ne a tsakani



***


Abu kamar wasa washe gari aka saka ranar Babban Yaya da Ummi ,wata uku kacal,Amma ba'a saka date din Daurin auren ba, Sai ankai lefe,duk wani hidima da akeyi na al'ada Daddy ne dakansa yayi ta

yau su yanbiyu sukai candy Sai abun yahad'u ya zama kamar wani 'Dan qaramin biki ake, har zuwa lokacin Babban Yaya yana d'a kinsa a kwance, duk abinda yake faruwa hajiya Anty ta fad'a masa ta waya saboda taje 'Dakin nasa taji shi a rufe,saide duk text din data masa babu guda d'aya da yayi mata replay

Acan makaranta kuwa, Waheeda saida ta jira su 'yanbiyu suka gama party a school sannan suka taho, yau driver bai d'auko suba, da kansu zasu taho, suna futowa daga get din makarantar, wani matashi me cikar kamala da kyau, gashi 'Dan Gayu, ya doko musu sallama, Ihsan ce ta amsa masa, yajuya yana Kallan Waheeda yace "qanwata idan babu damuwa Dan Allah inaso kibani number ki"

Waheeda ta tuna karonta da Babban Yaya saita qi bashi amsa tajuya masa baya, murmushi yayi yace "haba qanwata, kamar Wanda zan sace ki?"

Intisar tayi murmushi tace "Gaskiya Yayanmu yahanamu kula samari, Amma zamu baka number sa, idan ya amince shikkenan"

Murmushi yayi yace "gaskiya kun birgeni, daga Gani daga gidan tarbiya kuka futo, insha Allah zan nemeshi, yabani Dama indinga zuwa muna gaisawa da qanwata"
Yaqarasa maganar yana Kallan Waheeda, itade ba tace masa komai ba, saboda idan ta tuna Babban Yaya da police station din dataje, da 6atan wayarta, saitaji duk samarin sun fice mata Arai

Number Babban Yaya Intisar ta bashi, sannan suka tafi, duk inda sukabi Sai an Kalle su, kyawawan yanmata su uku, kana ganinsu kasan ba hausawa bane, napep suka Hau yakaisu har 'kofar gida, suna shiga falo suka tarar da Hajiya Anty taci kwalliya, wuyan ta da kunnanta Sai qyallin gold suke, matar ta'iya daukan wanka na fitar Hankali,yar Gayu ce ta qarshe, raba Goro da alawa take, ga Kuma kudi Nan agaban ta dami dami, zama Waheeda tayi akusa da ita, jikinta yana gogar Nata.

Tad'auko alawar guda d'aya tana sakawa a bakinta, sannan tacire hijabin jikinta, dogon gashinta ya baiyana,kwanciya tayi tareda d'ora kanta a cinyar hajiya Anty,sannan tace "Anty kayan me kike rabawa"

Ummah tace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba waheeda, kin sameta tana aiki memakon ki temaka mata, saide kihau cinyarta"

Bakinta ta turo gaba cikin shagwa6a tace "Ummah Anty cefa"

"eh saboda Anty ce saiki kashe mata cinya"

Hajiya Anty tayi murmushi tace "Goron saka ranar Yayanku ne, yau ansaka masa rana,su Sa'eed Kuma ankai musu gaisuwa"

Da Waheeda da 'Yanbiyu lokaci d'aya suka matso kusa da Hajiya Anty sukace "Babban Yaya?"

Hajiya Anty ta d'aga musu Kai, haba ai da gudu Waheeda tayi d'akinsa, tura kofar tayi tashiga ta ganshi a kwance, ya rungume Fillo a qirjinsa, cikin murna ta fad'a Kansa tana sakin ihun murna, yana jin yanda aka fad'o Kansa yasan ba kowane zaiyi masa hakaba Sai ita, yatsina fuska yayi sannan ya tureta daga jikinsa yace "Yaushe zakiyi Hankali ne?"

Cikin farin ciki tace "Babban Yaya, Dan Allah da pink colour da blue, dakuma green wanne ne yafi kyau?"

Cikin mamaki ya daga Kansa ya kalleta batare daya tashi ba, yace "meyafaru?"

Dantsan hannun sa takama ta riqe, tace "sonake kafadamin wanne ne yafi kyau saimu dakko ankon bikinka"

Wani irin baqin ciki ne yakama shi,cire hannunta daga jikinsa yayi,ya maida Kansa fillo cikin damuwa yace "ni banason auren"

Bata lura da yanda yake rabata da jikinsa ba tasake matsawa jikinsa tace "Meyasa Babban Yaya?"

Juyowa yayi yana Kallan ta, yace "Akwai yarinyar danake so"

Cikin farinciki tace "wayyo Allah, Babban Yaya Dan Allah wacece?"

Kallan ta yayi yakasa magana, zuciyar sa ce take zugashi akan yafad'a mata, to Amma tayaya zata dauki maganar?, qalubalen dayake gabansa dangane da fad'a mata wannan maganar ba qarami bane
Waheeda tace "Babban Yaya nikake kallo, wacece yarinyar?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Sunanku d'aya, kamar ku d'aya"

Wani irin fari tayi da idonta tace "Dan Allah Babban Yaya kakaini wajan ta mugaisa, ka nuna mata ni, kafad'a mata nice qanwarka wadda kafi so"

Lumshe idonsa yayi yabud'e, sannan yace "zan kaiki, Amma karki fad'awa kowa wannan maganar, sirri"

Dariya tayi tace "bazan fad'a ba, Babban Yaya kasan me? Wallahi inaso kayi aure, sonake Naga matarka ta haihu, muga dawa yaran zasuyi kama"

Tashi yayi zaune ya kalleta yace "ke har farinciki kike da bikin ne?"

Tace "sosai ma, wallahi inaso kayi aure"

Cikin wata irin gigitacciyar tsawa, wadda bata ta6ajin yayi mata irinta ba yace "tashi kibarmin dakina, tunda farinciki kike da aure na"

Tace "Babban......"
kafin ta qarasa yatashi tsaye cikin fishi kamar zai rufeta da duka, tana ganin haka tatashi tsaye, jikinta yafara tsuma saboda tsoro, qwalla ce tataru a idonta, tafuto daga Dakin cikin sanyin jiki














Ayi hakuri da wannan ba yawa, muna tayaka murna Babban Yaya πŸ˜‚






Bazanyi zagi ba, Amma duk wacce ta karanta batare data biyaba, nabarta itada mahaliccinta, saboda babu yafiyata aciki






Amnah
1/28/22, 20:50 - Ummi TandamaπŸ˜‡: Tana fita daga d'akin ya zauna akan gadonsa tareda dafe Kansa da hannun saπŸ€¦πŸ»β€β™‚οΈ?
Ita farinciki ma take, meyasa bazata fahimceshi ba? Yace sunansu d'aya, yace suna kama, tayaya zai futo fili yafad'a mata gaskiya? Tayaya zata fahimce shi? Mezai fad'awa iyayensu idan suka ji daga inda maganar tafuto?

Kansa ne ya Sara, yazube akan gadon yana fadin "hasbunallahu wa ni'imal Wakeel"
Bayajin zai iya rayuwa batare da Waheeda ba, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, ya cusa Kansa cikin fillo yana kuka babu me lallashi kamar ba Babban Yaya ba πŸ˜‚


Tana barin 'Dakin nasa, d'akinsu tashige, ta zauna agefen gado tana Kallan p.o.p din 'Dakin,
'yanbiyu ne suka shigo, intisar tace "kekuma lafiya kikayi wani iri kamar marar lafiya?"

Cikin damuwa tace "Babban Yaya ne"


Ihsan da intisar sukasa dariya, Ihsan tace "to me yamiki Kuma?, kema da rawar Kai daga jin ansa masa rana kika d'iba da gudu kikaje"


Kallan su tayi cikin damuw tace "Wai baya son auren ne"

Inti tace "to yanzu ke menene naki aciki? Hanawa zakiyi? Mema za'ai da wannan Ummin, ni wallahi Bana sonta, kullum kaganta tana magana da maza"


Ihsan tace "wallahi kuwa, inajin su Daddy basu Sani bane shiyasa, nifa shiyasa banyi murna ba danaji ance itace, Amma Waheeda uwar rawar Kai harda tafiya wajan sa da gudu, dama yasani yamiki shegen duka"

Waheeda tayi shiru tana tunani, tana so tace musu yafada mata yarinyar dayake so to Amma Kuma data tuna yace mata sirri, Saitayi shiru, tayi ajiyar zuciya tace "nikam Ina sonta, tunda Babban Yaya zata aura, mutumin dayake taimako na aduk halin Dana kasance tayaya zanqi matarsa?"

Ihsan tace "to Allah yabada sa'a Waheeda, ke kikaga Zaki iya"

Daga Nan sukai shiru kowa da abinda yake saqawa Aransa


Ita Waheeda tana tunanin Babban Yaya, duk yanda zaiyi mata fad'a tana shiga damuwa muddin ta ganshi acikin damuwa, saboda Shima baya barinta acikin matsala, ta damu da damuwar sa sosai, batasan meyasa ba, wani lokacin zai mata hukunci akan laifin da tayi, gashi de shine ya6ata mata rai ta hanyar yimata hukunci, Amma Hankalinta baya kwanciya Sai ta bashi hakura taga ya haqura tukunna, gashi yanzu yana wani Hali saboda auran Ummi, batasan ta wanne Hali zata taimaka masa ba,zuciyarta tabata shawara akan tatayashi da addu'ah, haka ta dauki shawarar zuciyarta


Haka Babban Yaya ya wuni ad'aki yaqi futowa, Ummah Kota Kansa batabi ba, saboda tasan fishin nasa akan aure ne, Kuma aure Kam babu fashi


Washe gari yafuto daga d'akin nasa, yana Sanye da kayan ball, suma 'yanbiyu maza shine ajikinsu, zama sukai afalo kowa yana kokarin saka safa, yanmatan ne suka futo daga d'akinsu suma de kayan Ball d'inne ajikinsu, Amma nasu wandon dogo ne, rigar ma me dogon hannu ce, sa6anin na mazan dayake qanana, fita sukai zuwa filinsu na qwallo dayake gidan, shikuma Babban Yaya yana falon yana saka takalmin sa, gaba d'aya iyayen nasu suna compound suna shan shayi, da hajiya Anty da Ummah dakuma Daddy da Uncle Usman, akan idonsu yaran suka futo zasu fara buga Ball din, Amma babu Babban Yaya, a lokacin harya gama saka kambos dinsa, yana zaune ne yana amsa wayar Abokinsa dayake tambayar sa yaushe zai dawo, yana gama waya da abokin nasa wata wayar tashigo, yayi mamaki da'aka kirashi ta wannan number, saboda ba kowane yasan wannan number tashi ba, dauka yayi tareda sallama daga dayan bangaren akace "Yayanmu Ina wuni? Sunana Didat, qanwarka ce tabani number ka,Ina neman alfarma ne awajanka, maganar Gaskiya Ina sonta, idan kabani Dama inaso na nemi aurenta"

Babban Yaya ya Sosa girarsa guda d'aya yace "Sister na kuma?"


Daga d'ayan bangaren Didat yace "eh Yayanmu, na gansu ne abakin get d'in school d'insu, akwai mutum biyu masu kama d'aya, toba suba, d'ayar nake nufi"

Babban Yaya yana jin haka ya Lumshe Idonsa, cikin ransa yace "Waheeda"

Dafarko har yayi niyyar dakatar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment