Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

take Maka, Amma kayi hakuri, kabar komai yalafa, insha Allah zata fahimce ka, kayi hakuri "

Babban Yaya yakashe wayar, ba tareda yace komai ba, sannan yafuto daga motar yashiga ciki


** *** **


Sa'eed ya kalli Ummah yace "Ummah ku fitar damu daga duhu mana"

Yasake Kallan iyayen nasu maza yace "Daddy, Uncle Dan Allah kuyi mana bayani, me Babban Yaya yake nufi? Tayaya zai iya auren Waheeda Bayan shi Yayanmu ne?"

Daddy yayi ajiyar zuciya yace "Naufal zai iya auren Waheeda"

Yanbiyu da Sa'eed da Sa'ad suka maida Kallan su wajan Daddy

Daddy yaci gaba da fad'in, "koda ace Naufal bai bud'i baki yace zai auri Waheeda ba Toni dakaina zan d'auketa nabashi, saboda banta6a tunanin Yaron Nan Huzaifa zaimin haka ba, ashe bashida tarbiya tunda har zai iya Kallan idonmu, a matsayin mu na iyayensa, ya fad'a mana irin wannan maganganun,abinda yake faruwa Wanda ku Baku saniba shine....


Tun muna Yara nida Usman ne kawai mukai karatun boko, Yaya Habu baiyi ba, shiyasa Lokacin da muka bar nijar muka dawo Nigeria da zama, a lokacin muka zauna da Yaya Habu akan Garin dazamu Yada Zango, a lokacin ya nuna mana shi yana jin dadin Zaman Garin jigawa, saboda haka mubashi wata dukiyar tamu da mukai gado a wajan iyayen mu, ya zauna yaci gaba da juya mana ita acan qauye, mukuma muje birni muyi abinda muka ga yadace

A lokacin babu Wanda ya haihu acikin mu duka mu ukun, Bayan mun dawo Nan da zama a lokacin muka qara karatu, mukasa iyayenku mata a a makaranta, Antynku tana fara karatu Sai Allah yabata ciki, Tasha wahala a lokacin, Yaya Habu yazo ganinta, anan yake sanar damu cewa Shima me d'akinsa tasamu juna biyu, munyi farinciki sosai, Bayan wasu watanni Matar Yaya Habu ta sauka, Aka sakawa yaro suna Yahya, a lokacin muka shirya muka tafi jigawa Wajan suna, tun muna hanya Ummanku take cikin damuwa, saboda tasan zata had'u da danginmu na Niger a gidan Yaya Habu, Kuma sha'anin surutun dangi, tabbas Sai sun fad'a mata magana akan haihuwa, na tambayeta dalilin damuwar ta, ta fad'a min komai bata 6oyemin ba, ashe aloakcin Uncle d'inku dakuma Hajiya Anty, suna jinmu, munje anyi taron suna lafiya angama lafiya, abinda Ummanku take gudu saida yaso yafaru, domin kuwa duk Wanda yaga Anty Da tsohon ciki ita Kuma bata dashi saide su dinga yimata wani Gani-Gani, saida na tsawatar musu

Washe Garin haihuwar Yahya a ranar Antynku ta haifi Naufal, Halaccin da bamu ta6a tunanin zasu mana ba itada Usman shi suka mana, saida suka kira Yaya Habu Dani da umman ku, sannan suka d'auki Naufal suka bamu shi halak Malak, Dafarko naqi yarda nakar6a, saboda suma shi kad'ai suka mallaka, Amma sai Yaya Habu yace mana mukar6a tunda sune suka bamu, tunda ita Antyn tafara haihuwa insha Allah zata sake Haifar wani, Amma yanzu mubarshi ta shayar dashi, saimu kar6eshi, tunda muka dawo gida Ummanku take kula da Naufal, tsakanin sa Da Antynku shine shayarwa dakuma wasa irin na d'a da uwa, har Allah yasa aka yaye Naufal, tazo da kanta ta kawo mana shi,a lokacin yaqi yarda ya zauna damu duk da yasaba da ummanku, dare yanayi zai fara kuka yana Kiran Anty, haka muka haqura saida ya tasa, sannan ummanku ta kar6eshi, a lokacin da hankalin sa Sarai ya dawo gidannan, yasan komai, yasan bamu ne muka haife shi ba, Amma abun mamakin koda wasa baita6a nunawa wani cewa bamune iyayen saba.

Ahankali ahankali soyaiya take sake shiga tsakanin sa da ummanku, har suka saba babu inda zasuje ace shi ba d'anta bane, cikin dangi kowa yasan Yaro na Ummah ne Amma Anty ce ta haifeshi

Bayan wani lokaci tun muna jiran Antynku tasake haihuwa har muka gaji muka barwa Allah, muka d'auki son duniya muka d'ora wa Naufal duka mu hud'un, har tsawon shekara goma

A lokacin kamar wasa ummanku tafara zazza6i muna zuwa Asbiti akace tanada juna biyu, a lokacin Nan gidan Antynku tatare take kula da komai, har Allah yasa ummanku ta sauka ta haifi Yan biyu maza, nida Usman Muka sanya musu Suna Sa'ad dakuma Sa'eed

Daga baya tasake samun wani cikin muka sanya mata sunan mahaifiyar mu, wato Maryam, Bayan shekara biyar tasake haihuwar wasu yanbiyun muka sanya musu suna Intisar dakuma Ihsan, a lokacin munyi tunanin Usman da Antynku zasu kar6e Naufal daga wajanmu, Dan har Ummanku tafara zazza6i tana tsoron arabata dashi saboda yanda yashiga ranta, tasaba dashi fiye da 'ya'yanta na cikinta, Amma koda wasa basu ce mu basu Shiba, Bayan shekara biyu da haihuwar su Ihsan muka sake Haifar Waheeda.


Tunda aka haifi Waheeda Naufal ya liqe mata, tun alokacin muda kanmu mukasan cewa yana qaunar ta sosai, shaquwar su ta daban ce, shine meyi mata wanka, shine goyo, shine siyo mata sweet, gashi ita Kuma batajin magana, Amma haka zai zaneta yamata hukunci yanda ya kamata, Dafarko munyi tunanin soyaiyar dayake mata ta aure ce, to damukaga yanda yake zaneta idan tayi laifi, yake mata hukunci irin Wanda koda ace mune zamu mata hukunci to irinsa zamu mata, Sai muka saduda muka daina tunanin komai akan alaqar su, muka bar komai a matsayin shaquwa,tunda yanbiyu maza kansu yana had'e, suma yanbiyu mata kansu ahad'e yake, Maryam kuwa tana d'akin mijinta, shiyasa bamu damuba Dan shaquwa me qarfi tashiga tsakanin Naufal Waheeda, to yanzu Kuma ga abinda Allah yasa ya kasance, wannan shine labarin. "


Shiru falon yayi, Ummah de tana mamakin Naufal Wai yau shine yake cewa yana son Waheeda, inda tasan cewa haka abubuwa zasu faru, da tuni Waheeda ta dad'e a gidansa, Hajiya Anty kuwa farinciki takeji acikin ranta, Allah yagani tana mutuqar kaunar Waheeda, tanaji da yarinyar sosai, Sai gashi yau Naufal d'inta yafad'i abinda yake ransa, dama ta dad'e tana wannan zargin, to Abaya tana tsoron ace ya nuna yana son Waheeda, saboda su kansu ba Susan tayaya zasu yiwa yaran bayanin abinda yafaru Abaya ba, Amma yanzu da Allah yasa hakan tafaru, ai shikkenan.

Yanbiyu sukai ajiyar zuciya, yanzu ashe Babban Yaya Yaron hajiya Anty ne?

Sukuwa su Sa'eed kasa magana sukai, haqiqa idan hakane sunfi kowanne qanne sa'ar samun Yaya nagari kamar Babban Yaya, Kuma Waheeda da taqi data so, Zaman aure dole πŸ€—

Wayar Daddy tayi qara, ya d'auka tareda fad'in, "minister yaya gida ya iyali?"

"Alhamdulillah Alhaji Umar, ashe Kuma abinda yasamu Waheeda kenan..."

Daddy yace "wallahi"

"kayi hakuri Alhaji Umar, kasan Yaron yanzu ka haifeshi ne baka haifi halinsa ba,Nan uwarsa ta zaunar dashi tagama hure masa kunne, Amma ba laifin Huzaifa bane, kuyi hakuri Alhaji Umar"

Daddy yayi wani murmushi me ciwo yace "Babu damuwa Alhaji, ai har wanima yafuto, Kuma mun bashi"

Cikin sanyin jiki minister yayiwa Daddy sallama, shi Kansa baiso Huzaifa yamasa haka ba, da har yana murna zai samu jikoki kyawawa πŸ₯Ί

'Yanbiyu ne suka tashi sukabi Bayan Waheeda d'aki, suna zuwa suka ganta a kwance akan gadon ta zubawa waje d'aya ido tana kallo tana zubar da hawaye

Zama sukai kusa da'ita, inti tace "Waheeda kiyi hakuri, nasan abinda ciwo mutum kana soyaiya dashi Amma saboda wata cuta ta sameka yagujeka, wallahi Huzaifa yabamu mamaki, Allah yasaka miki, Amma tunda bakida haqqinsa, ai gashinan yanzu kin samu Wanda yafi shi komai da komai, ga kud'i, ga kyau, ga aji, ga kwalliya, ga Kuma farin jini, sannan kinsanshi kinsan halinsa, uwa uba ma d'an uwanki ne "

Ihsan tace" wallahi kuwa, Allah sarki Didat Shima yabani tausayi wallahi, ashe da gaske yake yana son Waheeda, kiduba kiga yanda ya yarda zai aure ta a hakan, Amma yanzu tunda ga Babban Yaya Nan Shikkenan, saikiyi hakuri ki aureshi, Su Daddy sun fad'a mana Hajiya Anty ce ta haifeshi, saboda haka saiki daina cewa zakiyi Zaman Zina dashi... "

"Dan Allah kurabu Dani, waiku idan ku akace zai aure ku zakuji dad'i ne? Tayaya zan iya Zaman aure dashi? Yayana? Tun Ina qarama da wannan fuskar nake Kallan sa"


Ihsan tace "to Sai menene Dan kin Kalle shi a matsayin yayanki? Nawa akayi hakan?"

Waheeda ta goge Hawayen idonta, tatuna lokacin data nuna masa Breast d'inta, da yanda take rufa masa asiri idan ya had'a plan d'in rabuwa da yanmatan da ake had'ashi dasu

tatuna lokacin dayake fad'a mata zata Iya auren me kama dashi meyasa shi bazata aure shi ba?

Tatuna lokacin dayake cemata wadda yakeso suna kama da juna, Kuma sunan su daya , Amma karta fad'awa kowa

tatuna yanda take fad'awa jikinsa any how, ta rungume shi yanda takeso, gaba d'aya yagama jin d'umin qirjinta

tasake tuna yanda take kokarin nuna masa Breast d'inta yana kauda Kai Amma saida ta nuna masa, baqin ciki yakamata, cikin kuka tace "yacuceni,yagama Dani, shikkenan yagama ganin komai...."

Su intisar da basu fahimce ta ba sukace "me kike nufi?"

Cikin rashin kunya tace "bansani ba, Kuma ai bayansa kukebi, bakwa sona Dama can nasani"
Ihasan tasaki dariya tace "inti, dole ne muje muyi anko, muna murna da wannan aure"

Waheeda tace "uwar anko zakuyi ba anko ba"

Intisar tace "to karde kimana rashin kunya yarinya"

Tace "Nayi..., ku kashe ni idan kunso"

Intisar tayi murmushi tace "da ace Dane, zamu kashe ki mukai wa Ummah gawarki, Amma yanzu ba zamu kashe kiba, saide mu barki araye danki auri Babban Yaya"
Daga Nan suka fice suka bar mata d'akin
Suna fita ta kalli hannunta, tacire zoben da Huzaifa yasaka mata tayi jifa dashi, taci gaba da gunjin kuka.


Washe gari Hajiya Anty da qawayenta suka shirya aka maidawa su Huzaifa lefen su, ko tsinke basu d'auka aciki ba.

Har tsawon sati d'aya, Waheeda bata sake da kowa ba a gidan, tun yanbiyu suna bin kanta, har suka daina, Ummah ma tayi Tata nasihar Amma a banza, Waheeda Gani take sun kasa fahimtar tane, tayaya zata Iya Zaman aure da Babban Yaya? Su kwanta gado d'aya,ta tsotsi bakinsa, tamasa romance, abinda take karantawa a littafi Shima tayi masa, ta'ina zata fara hakan? Ina taga fuskar dazata masa duk wad'annan abubuwan?


Kwata kwata falo ma Dena futowa tayi, duk inda tasan zata had'u da Babban Yaya gujewa shiga wajan take, gyaran jikin data fara zuwa ma Shima tadena zuwa,
Daddy daya ga abin Nata Bana qare bane, saiyace surabu da'ita, yasamu Uncle Usman sukai magana, washe gari kuwa Yaya Habu yazo, suka gama abinda yadace, Aranar aka d'aura mata Aure da Babban Yaya akan sadaki naira dubu 'Dari, Babban Yaya yana tareda Mashkur Wanda yazo qasar shekaran jiya, yana jin farinciki a ransa but idan yatuna da Waheeda, jikinsa yana yin Sanyi

Yan gidansu Ummi sunajin labarin 'Daurin auren suka tattaro kayan su na lefe da aka Kai, suka dawo dashi, saboda suma anasu bangaren babu yanda basuyi da Ummi ba, Amma tace ita bata shirya kar6ar qanjamau ba

Da yamma gidan baqi sun zazzo duk da bawani taro zasu yi ba, Amma maqota sun shigo musu,gakuma tawagar Baba Habu, Waheeda tanajin labarin 'Daurin aurenta da Babban Yaya taji wani irin zazza6i yakamata, lokaci d'aya tafara rawar Sanyi, jikinta yayi zafi zau..., Hajiya Anty da taci kwalliya cikin wani leshi me mutuqar tsada, Sai walwali take, tashigo 'Dakin ta dubata, sannan tayi mata allura, ruwan Sanyi ta d'ebo zata koma d'akin ta goge mata jikinta, saiga Babban Yaya yashigo gidan kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, Kallan sa Anty tayi, duk ya fad'a saboda tunani, bashi ruwan tayi tace "wuce kaje ka gogewa matarka jiki,jikinta yayi zafi dayawa, zazza6i takeji"

Kansa ya Jinjina ya kar6i ruwan da towel yace "to Anty"

Kofar d'akin yatura yashiga, tana tareda 'yanbiyu, idonta biyu, Amma tanajin qamshin turaren sa ta Lumshe idonta kamar me bacci, yanbiyu suna ganin shigowar sa suka fice daga d'akin, ajiye Robar hannun sa yayi, yacire Babbar rigar jikinsa, ya ajiye ta agefe, sannan ya zauna agefen gadon setin kanta
Zuba mata ido yayi yana kallanta, d'an qaramin pink lips d'inta ya Kallah yaji ya birgeshi kamar yad'ora nasa akai yayi kissing.
Hannun ta yakama yariqe cikin nasa, yaji zafi sosai, ya sunkuya yayi kissing goshin ta, rigar jikinta yad'age sama, yafara goge mata cinyoyin ta,sannan yafara kokarin cire mata rigar gaba d'aya, Bayan yacire rigar tanajin yanda yake 6alle mata hook d'in brezia d'inta, Amma kwata kwata taqi bud'e idonta ta Kalle shi, wani irin takaici takeji a zuciyar ta, Wai yau Babban Yaya ne yake mata haka, kuka take son yi Amma tahana kanta, saboda bataso ma yasan cewa idonta biyu

Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yayi tozali da cikakkun nashanunta,qare musu kallo yayi ko'ina yacika sosai, Yan qananun nipples d'inta ya Kallah yaji kamar yad'ora bakinsa akai yayi ta tsotsa, hannun sa har rawa yake yad'ora mata towel din a wajan yana gogewa, ahankali yake gogewa baya son yadaina Kuma baya son ya tasheta daga bacci, tun yana gogewa cikin hayyaci harya fara dannawa kad'an kad'an batare daya Sani ba, qaran da wayarsa tafara ne yasa ya dawo hayyacinsa, Bai dauki wayar ba, Sai yayi sauri ya qarasa goge mata jikin, yabude sif d'insu yad'auki wata rigar yasaka mata, sannan yafuto daga d'akin

Tanajin fitarsa wani irin hawaye yazubo mata, tasaka hannu ta share, taja Bargo tashige ciki gaba d'aya, har kanta.


Su Ihsan ne suka dawo 'Dakin, bargon intisar ta janye, suka ganta da wani kayan, cikin murna Ihsan tace "Laaaa kinga ma jikin da sauqi, harta sauya Kaya"

Intisar ta kalleta tace "Waheeda, kukan me kike ne? Waike Dan Allah bakya gajiya da wannan kukan ne? Haba ayitayin abu kusan sati d'aya? Duk kinsa Babban Yaya yarame, saikace wata autar mata, shine ma yake bin kanki wallahi..."

Cikin masifa tatashi zaune tace "eh ai Dan bake yayiwa abinda yamin bane, kinsan me yamin ne dazaki hanani kuka? Kun zo kun dameni, aikin banza..."

Intisar tace "yau Kuma? Keda kike mana iyayi kina cewa yayanki ne in'aka bibiyama yafi sonki akan mu shine Kuma yau Zaki na cewa muka San meya miki? Da yau kuka fara fad'a Kuna shirya wa dazaki mana wannan tambayar?"

Waheeda ta rushe da Kuka, kwata kwata hankalin ta ba'a kwance yake ba, idan tatuna yanda yagama lugwigwita mata qirji yanzu, saitaji inaaa! bazata iya zama dashi ba, tama manta dasu Ihsan take magana, cikin kuka tace "Allah idan yasake min irin abunnan bazan yarda ba saina rama, ba duka ba saide ya kasheni......." ta qarasa maganar cikin tsawa!

Ihsan da intisar suka had'a ido sukayi murmushi tareda barin d'akin, Dan sunga alama an shiga fagen Daba nasu ba πŸ˜‚


Washe gari da safe, Maya tazo gidan itada yayanta Safwan, a lokacin duk family d'in Suna Nan, Daddy da uncle suna duba wasu takardu, Babban Yaya yana Kallan wasa a TV, Sa'ad da Sa'eed sunata dariya ganin yanda wasan yake gudana, Hajiya Anty da Ummah suna gyara kayan lefen Babban Yaya da aka dawo dashi, duk an cire wasu abubuwan, Anty tana rubuta abunda aka d'auke zata sake siyowa Waheeda wasu,
Yanbiyu suna Kallan waya suna dariya, Waheeda ce kawai batanan


Ummah ta Kalle su tace "A a Maya,kune a gidan namu kenan, sannunku da zuwa"

Hajiya Anty cikin tsokana tace "Su Maya amare"πŸ˜ƒ

Murmushi Maya tayi tace "Anty Ina take ne?"

Hajiya Anty tayi murmushi tace "tana d'aki kishiga mana"

Maya ta sunkuyar da kanta qasa tace "A a Anty, ai wajanku nazo gaba d'ayanku"

Babban Yaya yajuya ya kalleta, shide yarinyar tana birge shi, saboda tanada Hankali sosai ga nutsuwa, shiyasa ma ya aminta da qawancen su itada Waheeda, yasan Waheeda zata koyi abubuwa dayawa a wajan yarinyar

Ihsan tace "to Bari nakira miki qawar Taki"

Tana zuwa d'akinsu taga Waheeda a kwance da waya a hannun ta, tace "kizo Maya tazo"

Cikin sauri Waheeda ta miqe, dama tana so taga Maya, tana so ta fad'a mata abinda yake damunta ko zata bata wata shawarar

Cikin sauri kuwa ta iyo gaba Ihsan ta take mata baya, suna zuwa falon ta ganshi a zaune tareda su Sa'eed, gabanta ne yafad'i, cikin sauri tayi qasa da kanta, Shima yana ganin futowarta gaba d'aya saiya Rasa nutsuwar sa, yama manta yana zaune ne da iyayensa da Kuma qannansa a falon, yazuba mata ido yakasa d'auke Idonsa akanta, Hajiya Anty datake gyara Zaman inner wears acikin akwati ta Kalle shi tayi murmushi, dama de tana tunanin da niyya Naufal yasiyo wannan Brezia d'in manya daidai Waheeda, kamar yasan da'ita za'ayi auren.

Sa'ad da Sa'eed suka kalli Babban Yaya suka had'a ido suna Daria qasa-qasa, Sa'ad yayi qasa da murya yanda Babban Yaya bazai ji ba ya cewa Sa'eed "sainaga kamar Dama yana ciki..." πŸ˜‚

Sa'eed yace "nima tunanin danake kenan, Sai yanzu nake ganin alamun hakan"

'Dagowa sukai daga gulmar suka fuske kamar basu ba😎

Har Waheeda ta zauna kusa da Maya Babban Yaya bai daina kallon ta ba, ahankali yad'auke Kansa daga gareta, yana juyowa suka had'a ido da Uncle Usman daya zuba masa ido tun d'azu yake Kallan sa πŸ˜‚
cikin kunya yafara shafa lallausar sumar Kansa tareda sunkuyar da Kansa qasa

Waheeda ta kalli Maya tace "Sai yau kika ga damar zuwa qawa"

Maya ta kalli Waheeda tace "qawa Ina tsoron zuwa wajanki ne, nasan namiki laifi, bansan tayaya zan miki bayani ba..."

Cikin rashin damuwa Waheeda tace "menene yafaru?"

Maya ta kalli kowa na falon tahad'e hannunta biyu waje d'ayaπŸ™πŸ»
cikin rawar murya tace "Daddy, Uncle, Ummah, Anty, Babban Yaya, Qawata, Dan girman Allah ku yafemin, haqiqa nasan na aikata muku laifi, nasaka ku cikin wani Hali, Amma ba komai ne yasa nayi hakan ba Sai saboda taimakon da Babban Yaya yata6a yimin lokacin da muka shiga cikin wani hali nida iyayena, yatemaka mana a lokacin da muke buqatar temakon,.... "

Jin wannan furucin Nata yasa hankalin kowa ya dawo kanta, Sai kowa yazuba mata ido yanaso yaji abinda zatace, Daddy yace"menene yafaru Maryam, fad'amana muji"

Kanta ta sunkuyar tace "Gaskiya Waheeda bata d'aukeda kowacce irin cuta, lafiyarta kalau, tun muna ss2 nafahimci cewa Babban Yaya yana sonta, tundaga lokacin naci d'amarar temaka masa akan Waheeda, Ina bata shawara sosai akansa duk Dan naja ra'ayin ta, to Amma Naga hakan bata samu ba, saboda koda yaushe abinda take fad'a min d'ayane shid'in yayanta ne, Ina tunanin mafita saina ji har ankawo mata kayan lefe, narasa yanda zanyi in rabata da Huzaifa, kawai rannan Sai take fad'amin zasuje Asbiti ayi musu text, da wannan damar nayi amfani nasamu family Doctor d'inku wato Doctor Khamis, na fad'a masa komai, anan Shima yabani goyon baya, ya tambaye ni Dame nakeso ya temaka min, Kai tsaye nafad'a masa tunda shi Babban likita ne nasan yanada alaqa da wasu hospital d'in dayawa, inaso duk asbitin da Waheeda taje a fad'a mata cewa tana d'aukeda cutar qanjamau, ta wannan hanyar ne kawai zan gane wannan Huzaifan datake rawar Kai akansa shin yana mata soyaiyar Gaskiya ne kokuma ta qarya? Idan soyaiyar gaskiya yake mata to zanji dad'i nasan koda qawata ta aure shi zaici gaba da sonta, idan Kuma duk qarya ce, to lokaci zai nuna, Doctor khamis yabani goyon baya sosai, Kuma Alhamdulillah yanzu gashi gaskiya tayi halint...... "

Kafin Maya ta qarasa magana Sai ganin Waheeda sukai tatashi tsaye tashaqe mata wuyaπŸ˜‚πŸ™ŠπŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?

Sosai suka kama dambe, Maya tana kokarin qwatar kanta Waheeda kuwa idonta yarufe takama Maya Sai dukanta take
Su Ummah ne suka tashi da Anty da Kuma yanbiyu suka fara rabiya, Amma Waheeda tayi wa Maya wani irin ruqo kamar ba qawa da qawa ba πŸ˜‚πŸ˜‚

Cikin kuka Waheeda tace "daga yau babu ni babu ke, karki qara zuwa inda nake, dama can kema nasan bakya sona, tun tuni nagane take takenki..."


Wani irin murmushi Babban Yaya yayi,haqiqa dole ya kyautatawa Maya, tayi masa abinda bazai ta6a mantawa ba,dama ta dalilin tane Waheeda bataje Saudia ba saboda Ummah taji suna waya, yanzu kuwa yayi alqawarin had'ata da qawar Tata sutafi Saudia tare, saisuci gaba da damben acan πŸ˜‚


Ummah ta kalleta tace "bazaki saketa ba?"

Cikin kuka Waheeda tace "to Ummah meyasa zatasa a aura min Wanda banaso? Ita uwata ce?"


Uncle Usman ya kalli Babban Yaya yace "Kai tashi kaja matarka kubar gidannan"

Ummah ma tace "eh wallahi, ni nagaji da fitinarki Waheeda, memakon ki godewa Allah bakida cutar komai, saide ki kama dambe? Wuce kibishi kutafi gidanku mun yafe zamanku a gidannan, Allah yabada Zaman lafiya"

Ahankali yatashi yanufeta, har zuwa lokacin hannunta yana jikin hijabin Maya Wanda taqi saki, yana zuwa yasaka hannu yacire mata Nata hannun, sannan yajata zasu bar falon, ihun kuka Waheeda tasa tana fad'in " Ummah dan Allah kuyi hakuri, ni wallahi Bana sonsa, daku zan zauna, Ummah!, Anty!!"

Ummah ta d'aga murya tace "Nayafe Waheeda, kuje can ku qarata"

Haka suka futo daga falon har zuwa wajan motar sa, yana zuwa yabud'e mata tashiga, sannan yarufe Shima yashiga, fita sukai daga gidan suka d'auki hanyar gidansa, tunda tashiga motar takifa kanta acinyar ta tana gunjin kuka, yanajinta bai hanata ba, sunyi Nisa da tafiya yayi tunanin zatayi shiru Amma yaji shiru yarinya Sai kuka take masa, mamaki ya kamashi, Wai shine yau Waheeda take gudu. πŸ˜–


jikinsa ne yayi Sanyi, ahankali yafaka motar agefen titi yakifa Kansa akan sitiyarin motar, Waheeda tana kuka taji sun tsaya, batareda ta d'ago kanta taga dalilin tsaiwar tasu ba taci gaba da Kuka, Ahankali takejin wata shashshekar kukan tana tashi acikin motar, cikin mamaki ta d'ago kanta tazuba masa jajayen idonta, mamaki yasake kamata ganin Babban Yaya yana kuka da Idonsa, abinda bata ta6a ganiba a tarihin rayuwarta, lokaci d'aya ta nemi Nata kukan tarasa, cikin zuciyarta tace "Kuka?"




πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
1/28/22, 20:51 - Ummi TandamaπŸ˜‡: WN



Rikicewa tayi tarasa Yaya zatayi? Babban Yaya da Kuka? Tome aka masa dazai kama yimata kuka? Ita yanzu Yaya yakeso tayi ne? Bata ta6a ganinsa yana kuka ba, Sai hakan yasake d'aga mata hankalin ta tasake fashewa da Kuka,cikin kuka ta kalleshi takasa bashi haquri, cikin taqaici ya d'ago Kansa, Idonsa duk hawaye yace "bazaki min shiru ba saina bige bakinki anan?..."

Itama cikin kuka tace "toba kaine kaqi yin shiru ba..."

Hannunsa duka biyun yasaka yarufe fuskarsa, saida yagama kukansa ma'ishi, sannan yaja motar suka qarasa gidan

Maigadi yazo ya gaishe su cikin ladabi, ganin yanayin uban gidan nasa ba daidai ba yasa yajuya yakoma mazauninsa

Suna shiga falon ya nuna mata d'aki yace "gashinan"

'Dakin tashiga Wanda yaji kayan komai na more rayuwa, fad'awa tayi kan gadon ta Fashe da Kuka, wanne irin aure ne wannan? Babu masu rakiya babu komai ko kayan sakawa Ummah bata bataba, tayaya zata rayu dashi awannan gidan a matsayin ma'aurata? Kuka take sosai saida taji kanta yafara ciwo sannan tayi shiru


Tunda sukazo gidan bai leqo d'akin datake ba, itama bataje inda yake ba, ko kitchen d'inma bata shiga ba bare yasaka ran zata dafa musu wani abun, damuwa tataru tayi masa yawa yarasa ta'ina ma zai fara lallashin ta? Ada yana lallashin tane a matsayin ta na qanwar sa wadda yakeso, yanzu Kuma zai bata kulawa da lallashi ne a matsayin ta na matarsa, to gashi tana cewa bata sonsa, Yaya zaiyi ne?

Da tunani yafara yimasa yawa saiya dauki waya zai kira Ummah ya fad'a mata a aiko musu da abinci, yana kira Ummah ta d'auka tace "Yayansu yagida"

"lafiya Ummah, Am... Ummah idan yaran Nan sungama abinci, sutaho mana dashi"

"to zasu kawo muku, zanzo Nima nasake ja mata kunne nasan Waheeda batajin magana, karka fita ko'ina ka zauna agida ka huta Sai anjima..."

Babban Yaya yariqe wayar yayi shiru, yanaso yace mata Kozai dawo da Waheeda gidane idan tagama hucewa Saisu kawo ta, to Amma yaji kwata kwata Ummah taqi bashi wannan damar ma bare yayi mata doguwar magana, kashe wayar zaiyi, saiyajiyo muryar Anty tana cewa "Amma Yaya da kun Bari yarinyar Nan tad'an sake dashi kafin sutafi, kwata kwata bamu yi mata shirin komai ba, kamar batada gata?"

Ummah tayi tunanin Naufal yakashe waya, shiyasa tana cewa Sai anjima kawai ta ajiye wayar, Babban Yaya kuwa fasa kashe wayar yayi, yayi shiru yana jiran amsar da Ummah zata bayar

Ummah ta kalli Hajiya Anty tace" wanne irin sakewa Kuma Antynsu? Yau tafara zama da Naufal d'in? Tafi kowa sanin halinsa acikinsu, taje tayi ta kukan idan tagaji zata daina, yanzu Hankali na ya kwanta tunda tana d'akin mijinta, kwanaki kamata nayi tana waya da Maya, bansan de kan zancen nasu ba, Amma saina ji ita Waheeda tana hurewa Maya kunne Wai wallahi ta yarda ayi mata auren, inda ace itace yarda zatayi, ai har wanka ma ita zata dinga yiwa mijin, har abar zata kama ta wanke.... "

Babban Yaya yazaro Idonsa 😳,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment