Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

shekara d'aya πŸ‘ŒπŸ»

Yau duk suna zaune afalo gaba d'ayansu,yana jin yanda intisar take cewa "akai musu wannan uban kayan Amma abada tukwicin dubu ashirin?"πŸ€”

Ihsan tace "ai sai kiyi tayi, kanki akeji, tunda sude bazasu qara komai ba, ni dazu danahau Instagram ma kayan nagani anata turawa, mutane Sai cewa suke anyi almubazzaranci dayawa, Kuma nasan Yan gidan sune suka saka kayan a internet"

Babban Yaya Ko Kallan su baiyi ba,bare ya tanka, yasan suna magana ne akan 'Yan gidansu ummi, wayarsa ce ahannunsa yana Kallan pictures din Waheeda, wasu tun tana zama, wani Kuma ahannunsa take yana bata fida tana Sha, wani Kuma tana cikin baho yana mata wanka, wani Kuma yad'agata sama yana kissing Kumatunta, a lokacin tafuto daga d'akinsu wayar Ummah tana hannunta, Kai tsaye wajan sa ta nufa ta zauna, yana ganin ta yayi saurin rufe wayarsa kartaga abinda yake Gani, wayar Ummah ce tasake qara, cikin 6acin rai ta dauka tace "Wai Dan Allah Didat mekake so nama? Nafad'ama gaskiya kadena kirana anriga ankawo kayan aure na"

Daga d'ayan bangaren Didat yace "wallahi Waheeda idan kika kuskura kika auri wani baniba wallahi saikin kashe auren kin futo kin aure ni...."

Cikin 6acin rai tace "au haka kace?"

"eh haka nace, Dan renin hankali kince min Inturo iyayena baki tsaya kinji abinda zan fad'a miki ba kawai saiki cemin yanzu ankawo miki kayan aure.... A a, sadaki aka kawo miki ba Kaya ba, wallahi idan kika yarda aka miki aure da wanina dagani harke Sai ran kowa ya6abaci "
Dif... Yakashe wayarsa


Waheeda tasaki tsaki ba tareda tace komai ba, tajuya ta kalli Babban Yaya har zata masa magana saitaga ya daure fuska, dolenta taja bakinta tayi shiru 😬


Da daddare abokinsa mashkur yazo,zaune suke akan had'ad'd'iyar motar Mashkur din, wadda yayi parking dinta a compound din gidan, mashkur 'Dan Gayu ne na gaske, akwai d'aukar wanka tamkar Babban Yaya, Ihsan ce ta kawo musu lemuka ta ajiye akan 'Dan qaramin wani dinning table dake gabansu,ta gaida mashkur sannan tajuya, har tayi Nisa Idonsa yana kanta, bata dad'e da tafiya ba intisar takawo musu cups, cikin mamaki ya kalleta yace "kaiii, Wai daga shigar ki har kika sauya Kaya kika futo?"πŸ€”

Murmushi tayi tace "a a, Bani bace, Ihsan ce dazun"

Murmushi yayi tareda shafa qeyarsa,intisar tajuya tatafi, mashkur ya dubi Babban Yaya yace "tsakani da Allah kunada wannan kyawawan yanmatan Amma kabarni Ina shan wahalar neman matar Aure? Gaskiya Allah yamuku kyau Abokina, Wannan kyanta ace zan'iya had'asu duk su biyun, da lokaci d'aya zanyi wuf dasu"

Babban Yaya ya Kalle shi yace "banason is'kanci mashkur...."

Mashkur ya d'auki lemo guda d'aya ya tsiyaya acikin cup sannan yace "to na tambaye ka meyakamata mu tsara na bikin kaqi cewa komai, to bagara inyi abinda ya shafeni ba, Kai kasamu matar ne shiyasa kake mana is'kanci, nikuwa Sai yanzu nagani, Dan Allah Bro wannan ta farkon datazo, Ina ciki...."

Babban Yaya yayi ajiyar zuciya, cikin ransa yafara godewa Allah daba Waheeda ce takawo musu lemon ba 🀣
Yatsani yaji wani namijin yana cewa yana sonta

Ya kalli mashkur yace"ni bazaka Jamin raini awajansu ba, kamusu magana da kanka, sannan babu abinda zamu tsara, ayi bikin haka, mashkur inaji araina matsawar narasa yarinyar danake so, to wallahi mutuwa zanyi...."

Mashkur dayakai cup din lemo bakinsa cikin sauri yafasa Sha ya ajiye, sannan ya Kalle shi da mamaki yace"kasan mekake fad'a kuwa Naufal?"

"yes, bazan iya daina sonta ba"

Mashkur yace "wacce me sa'ar ce wannan? Why not kafad'a mata? Mekake jira?"

Babban Yaya yace "lokaci yaqure min mashkur, bazan iya fad'a mata ba, Amma wani bangaren inaji ajikina ita d'in tawa ce"



Cikin sanyin jiki mashkur ya bubbuga kafad'arsa, yace "kayi hakuri Abokina, yanzu meka yanke akan hakan? Wanne irin mataki ka d'auka?"

Cikin damuwa yace "band'auki kowanne mataki ba, kawai Ina addu'ah de..."

"no, hakan ai yayi kad'an Friend, saura sati hud'u bikinka fa, kamata yayi mushirya muje Saudia, Nima zan tayaka da addu'ah Allah yabaka za6inka, idan har zai kasance alkhairi agareka, idan Kuma ba alkhairi bane Allah yabaka haquri da juriya akan rashinta "


Ransa duk adagule ya kalli mashkur yace "mashkur lokaci yariga yaquremin.... Itama aure zatayi, tayaya za'a fasa dawani ayi Dani? Tayaya zan rabu da wannan nacacciyar yarinyar ummi? Wallahi haushin ta nakeji, idan ta kuskura ta aure ni ko.... Wallahi saina mata filla-filla aranar da aka kawota kuma da niyya"


Mashkur ya kwashe da wata irin dariya sannan yace "Abokina bakada Dama wallahi, kadena wannan tunanin, kasa aranka zaka yarda da qaddara mekyau ko marar kyau, sannan karka manta komai yayi zafi maganin sa Allah, a lokacin daka shiga cikin matsala kadinga tunawa cewa akwai Allah.... Saboda haka yanzu ma shi zamu kaiwa kukan mu, me muke yanzu a qasar? Mushirya gobe mutafi Saudia, daga Nan kawai muwuce England.... "


Sai a lokacin Babban Yaya yasaki wata irin ajiyar zuciya, yace
" nagode Friend"

cikin farinciki suka rungume juna




Washe gari karfe goma a compound tayiwa Babban Yaya, sunyi waya da mashkur zasu had'u a Airport, Waheeda da Yanbiyu ne suka rakoshi har wajan motar dazai shiga, wayar Ummah tana hannun Waheeda, Huzaifa ne ya kirata cikin murna ta d'auka tafara masa magana Sai wani kashe murya take.... Babban Yaya yabude motar zai shiga ya kalleta yace "mahaukaciya..." 🀣


Yanbiyu sunji abinda yace, sunsan cewa akusa yake, danhaka sukai murmushi suka juya ciki

Waheeda ta katse wayar sannan ta Kalle shi tace "Babban Yaya mekace?"

Cikin 6acin rai yace "bansani ba"

Jikinta ne yayi Sanyi, ta qarasa wajan sa tace "nayi laifi ne Babban Yaya? Kayi hakuri...."

Fasa shiga motar yayi, yafuto tareda d'ora hannun sa akan murfin motar, cikin masifa yace "au tambaya tama kike me kikayi? Kullum kina liqewa mutum saikace kaska, kwata kwata baki iya Jan aji ba, to Bari kiji, namiji tsanar mace me naci yake, marar aikin yi kawai..."

Kukane yakama Waheeda, ita tarasa meta masa tun ranar da aka kawo lefen ta yake daure mata fuska,komai tayi saiya dinga Jin haushinta, bata iya haqura ba saida ta rushe da Kuka Sannan tayi cikin gidan da gudu

Tsaki yasaki yanajin haushin zuciyar sa Kuma, Dan me zaisa Waheeda kuka? 🀣Yanzu haka kukan ma ya haddasa mata ciwon Kai, wani tsakin yasake saki, yarufe motar zaibi Bayan ta, domin yabata haquri

"Salamu Alaikum"

Juyawa yayi yaga meyi masa sallama, budurwa ce Babba, wankan tarwad'a, tanada tsayi had'eda jiki, saide babu alamun kyau atare da'ita, hannunta d'aukeda wani flask d'in abinci,Kallan rashin Sani yayi mata, beyi mata magana ba yajuya zaiyi cikin gida

Cikin sauri Tariqo rigarsa tace "Husband baka ganni bane?"

Cak! Yaja ya tsaya a'inda yake, sannan ya Juyo cikin nutsuwa yacire hannunta data riqe masa Riga, ya kalli idonta yace "Dama kece?"

Ummi tayi farrrr da idonta, cikin yanga tace "nice, meyafaru ne Naga kamar kana cikin 6acin rai? To kayi hakuri ga girkina nakawo ma da hannu na nayishi, idan Kaci zakaji dadi"


Cikin tsananin 6acin rai yanunata da hannu yace "Ummi!!!, kidena damuna, kidena shiga cikin rayuwa ta, waike Ana so dole ne? Sau nawa zan fad'a miki Bana ra'ayin ki? Ba girki ba, ko kanki Zaki Bani bazanyi ra'ayin ki ba"


Cikin rashin kunya tace "qarya kake wallahi, Kai d'in wa? Dazaka dinga fadamin baqar magana, cemaka akai ni dinma sonka nake? Inaso na aure ka ne saboda duniya tasan cewa eh Nima na auri mashahurin mutum, Naga alama bakasan darajar mace ba, Amma duk lokacin daka aureni saina koyama yanda ake...... "


Cikin 6acin rai yakai hannu zai wanketa da Mari tareda wata irin tsawa yace"Ummi!!!"


Tsananin tsoro ummi ta tsorata da yana yinsa,jikinta ya d'auki rawa batasan lokacin da flask din hannunta yafad'i qasa ba, jallop rice din ciki ta zubeπŸ˜‚


Idanunsa harsun sauya Kala sun koma ja saboda 6acin rai, cikin sauri Hajiya Anty taqaraso wajan su tariqe hannunsa, shigowarta kenan gidan, ta tarar da wannan drama, cikin 6acin rai ta Kalle shi tace "Duka Kuma Naufal....?"

Yanda yaji tafad'i kalmar duka d'in kamar zatayi kuka duk Sai jikinsa yayi Sanyi, Amma sai huci yake, tunda yake ba'a ta6a yimasa rashin kunya kamar yanda ummi tamasa ba yau, Hajiya Anty ta maida Kallan ta wajan Ummi tace "kiyi hakuri, d'auki flask d'inki kitafi"

Ummi ta tsugunna ta d'auka, sannan ta d'ago ta kalli Hajiya Anty sannan tasakar mata tsaki, ta wuce tabar gidan

Babban Yaya yana ganin abinda Ummi tayiwa Hajiya Anty yabi Bayan ta zai damqo ta, Hajiya Anty ganin yabi Bayan ummi tasan tsaf zai lakad'a mata duka, Dan haka cikin sauri ta ruqoshi, tace "karabu da'ita nace"

"Amma Anty... Kina.... Kina ganin abinda tamiki fa..."
Yafad'i maganar a rarrabe cikeda qunan rai


Murmushi tayi tace "naji, karabu da'ita"

Jijjiga Kansa yayi, sannan yashiga motar sa yamata key yabar gidan,wajan Waheedan ma fasa zuwa yayi πŸ€—




πŸ˜‡πŸ˜‡πŸ˜‡
1/28/22, 20:51 - Ummi TandamaπŸ˜‡: QN




Kwanan su uku a Saudia suna gudanar da addu'ah shida mashkur, gaba d'aya kashe wayoyinsu sukayi, ibada kawai suka sa agaba,Sai akwana na hudun ne sannan suka koma England.

Kwanansu hud'u da komawa England yakira wayar Hajiya Anty, Bayan sun gaisa yace "Anty kiyi hakuri akan abinda yarinyar Nan tamiki, na lura kwata kwata batada kunya...... Sannan duk laifin ku ne dakuka liqa min ita"

Murmushi tayi "son rigima, to kayi hakuri mana watarana zata dena, karka damu babu komai, baka fita wajan aiki bane Naga kiranka da wannan safiyar?"

"Ina gida Anty, yau babu inda zanje, zan zauna agida inyi shara, inyi mopping, inyi wanke wanke, Anty Allah nagaji...." ya qarasa maganar cikin shagwa6a

Murmushi tayi tace "yau Kuma shagwa6ar ce tatashi?, ko Inturo ma Waheeda?" tafad'i hakan tana so Tasha cikinsa ko zataji wata maganar

Murmushi yayi, yasan Sarai da biyu tayi masa wannan maganar, yaganota, cikin dakiya yace "tazo tamin me? Anty wannan yarinyar ai damuwa ce... Nayafe tayi zamanta"

Murmushi tayi tace "to shikkenan, yaushe zaka dawo?"

Yatsina fuska yayi sannan yace "ai kinsan zuwan nawa yana hannun Waheeda.... Idan tayi wani abun to zaku ganni, but nide ara'ayina bazan dawo ba Sai biki"

Dariya tayi tace "Haka Waheedan tazama? Karka yimata sharri" πŸ˜ƒ

Sun dad'e suna zance, daga baya sukai sallama.


** *** **


Cikin hawaye yake yiwa Baban nasa bayanin komai, Alhaji Attahir ya Jinjina Kansa cike da 6acin rai, duk abinda d'ansa yakeso Tofa Shima yanaso, wacce irin yarinya ce wannan da zata rusa farincikin d'ansa? Kallan sa yayi yace "ita yarinyar bazata iya hakuri harna dawo daga tafiya ba, insamu iyayenta muyi magana dasu? Yar gidan wacece ne?"

Cikin kuka Didat yace "yarinyar Alhaji Umar Arabo ce"

Alhaji Attahir yace "Nasan Alhaji Umar, ka kwantar hankalinka, zamuje dakai ayi magana, dole a warware wannan maganar auren datace anyi dawani, dakai za'ayi wannan auren, ka kwantar da hankalinka kaji?"

Kakar Didat dake zaune agefe tayi murmushi, ganin mahaifin nasa zai samo masa abinda yake so, haqiqa tana tsananin son Didat, bata son abinda zai shiga tsakanin sa da farincikin sa, tun Bayan rasuwar mahaifiyar sa, itace taci gaba da Kula dashi, shiyasa take jinsa har cikin zuciyar ta


** *** **

Tafiya suke ahankali agefen titi suna hirarsu ta qawaye, Maya ta kalli qawar tata, "gaskiya qawata na gode da ziyara, naji dad'in zuwanki gidanmu"

Waheeda tace "Dama rashin dama ne yasa Bana zuwa ai"

Maya ta kalleta tace "yanaga yanayin ki kamar kina cikin damuwa?"

Ajiyar zuciya tayi "wallahi Maya, Babban Yaya ne, fishi yake Dani, narasa yanda zan masa, ya cika rigima wallahi"πŸ˜”

Maya tayi wani murmushi Mai d'auke da ma'anoni tace "inyee saikace wani Babynki Babban yayan kike cewa yacika rigima? Meya miki to?"

"tunda akai maganar auren Nan, narasa gane Kansa, kwata kwata baya sakarmin fuska kamar baya, sannan Bahaka yakewa 'yanbiyu ba"

Maya ta riqe hannunta tace "qawata ki kirashi kibashi hakuri, nasan yana jin maganar ki, sannan ki marairaice masa kamar Zaki masa kuka, aikin gane dai, shagwa6a Zaki masa duk ki haukata shi"


Zare hannunta tayi daga cikin na Maya tace "me kike nufi? Waike Dan Allah meyake damunki ne? Saurayina ne dazan dinga masa wannan abun? Maya Babban Yaya fa nace Miki ba Huzaifa ba"

Maya ta yatsina fuska ganin plan d'in Nata bai samu kar6uwa ba tace "toki rabu dashi kawai, ai zai huce ne, yaushe Zaki fara gyaran jiki ne? Biki Sai matsowa yake, Gara fa tun yanzu kifara shan abubuwa Wanda zasu sa kifara tsiyaya, sonake kisa Huzaifa kuka a Daren farkon ku"

Ajiyar zuciya tayi tace "Anty tace gobe zan fara zuwa, kitaho da safe ki sameni a gidan Hajiya Antyn, saina yiwa Huzaifa magana yazo yakaimu gidan, namanta ma ban fada miki ba, Su Daddy sunce muje Asbiti ayi mana text, na jini, kinsan yanzu yanayin rayuwar ya sauya komai Sai ahankali "

Maya ta Jinjina kanta, tafara wani tunani, ta kalli Waheeda tace"hakane Kam, saikaje ka auri me sikila ma baka Sani ba, Gara kuje din Kam, wanne Asbiti zakuje? "

Zuciya d'aya Waheeda tace"na fad'awa Huzaifan de, yacemin tunda gobe zamuje wajan gyaran jiki,jibi Sai muje asbitin, akwai asbitin da ake duba 'Yan gidansu, (Al'islah Hospital) private ne, can nake tunanin zamuje"

Maya tace "to shikkenan, Allah yakaimu goben, saina shigo"

Daga Nan sukai sallama, kowa yatafi gida


** *** **


Washe gari da safe Maya a gidan Hajiya Anty tasamu Waheeda, anan sukayi breakfast sannan Waheeda takira Huzaifa yazo yad'aukesu suka tafi

Maya tana gidan baya, Waheeda da huzaifa suna gaba, Sai kashe mata murya yake suna soyaiya, hankalin Maya yana kan wayarta tana daddannawa, a gidan da Hajiya Anty ta fad'a musu yasauke su, sannan yatafi, gidan suka shiga aka fara yimata gyaran jikin yanda ya kamata, tsawon lokaci suka d'auka ana mata abu d'aya,Bayan angama gyaran jiki matar tabata wasu magungunan na mata, ta zaunar da'ita a gabanta, saida taga ta Shanye sannan,wani irin qyalli Waheeda tafara, gyaran yau ma kenan, ita kanta Maya Kallan ta take tana mamakin yanda tayi kyau, to rana d'aya ma kenan idan kuma aka gama gyaran gaba d'aya Yaya Waheeda zata kasance? πŸ€”

basu gama da wuri ba Sai wajan yamma, sukayi mata sallama saikuma gobe idan sun dawo

Allah ne kawai yakawo su gida lafiya, domin kuwa Huzaifa yana ganin irin gyaran da akayi Waheeda saiya susuce bashida aiki saide yajuya ya kalleta, yana driving yana Kallan ta, Maya ta godewa Allah data ganta a kofar gidansu sunzo lafiya, tana futowa daga motar ta leqasu ta window tace "to wallahi ango kakula da qawata sosai, nide na godewa Allah tunda ankawoni gida lafiya"

Dariya huzaifa yayi ya shafa sumar Kansa, yasan Sarai taga halin daya shiga ne shiyasa tayi masa wannan maganar, Waheeda ma tayi mata murmushi tace "to Sai munyi waya qawata, gobe karki shirya da wuri, saida yamma zamuje, saboda da safe, Asbiti zamuje"

Maya tace "to shikkenan qawata, Allah yakaimu, kikula mana da angon namu"
Ta qarasa maganar cikin tsokana

Huzaifa yaja motar suka tafi, har zuwa lokacin Maya tana tsaye a'inda suka sauketa, saida taga sunbar layin gaba daya,memakon tashiga gidansu sai ta tare adedeta tashiga,tayi masa kwatance sukad'au wata hanyar


** *** **


Tafiya suke cikeda nishadi, kana ganinsu kasan suna cikin tsantsar farinciki, qamshin turaren sa yahad'u da Nata ga Kuma sanyin esi Sai abun yaqara bada armashi
Kallan sa tayi "Bae kadinga sauri muje mana, kana driving kamar baka so"

Kallan ta yayi "so kike nayi sauri Dan muje asbitin mugama da wuri kitafi kibarni ko?"

Murmushi tayi batare da tace komai ba, yasake Kallan ta yace "inason murmushinki Waheeda, yana birgeni, musanman idan Naga wannan dimple din...."

Kallan sa tayi "da gaske? Aikuwa koda yaushe zan dinga yima ka shi, saboda inci gaba da birgeka a koda yaushe, Dan banasan wata Rana kaga wata yarinyar itama ta birgeka"

Kafad'a ya d'aga yace "ai Bana tunanin akwai yarinyar dazata birgeni Bayan ke Waheeda, nifa banga amfanin zuwa wannan text din namu ba, saboda nasan kede lafiyarki kalau, Kuma Nima haka,idan kinada wata cuta ma ai saide in nine nasaka miki, tunda nine nabaki jini batare da angwada jinin nawa ba "

Cikin rashin damuwa tace"dansu Daddy sun matsa ne ai, Amma yanda nake jin ka acikin zuciyata ko wacce irin cuta ce dakai, zan iya zama dakai Bae"

Murmushi yayi ba tareda yace mata komai ba, suna qarasa wa asbitin sukayi wa nurse bayani,dayake tasan Huzaifa tun tuni, Nan asbitin suke zuwa duka family d'insu, cikin qanqanin lokaci aka d'auki jininsu aka basu wajan zama

Basuyi awa d'aya ba, doctor yakirasu zuwa office d'insa, zama sukai ya Kalle su yayi murmushi yace "Huzaifa kace ankusa angoncewa"

Murmushi Huzaifa yayi, "Eh wallahi Doctor, ga madam Nan"

Yace "To Allah yasanya alkhairi, Allah yabaku zuri'ah Dayyiba"

Ahankali Waheeda dake wasa da yatsun hannunta tace "Amin"

Takarda ya miqawa Huzaifa yace "toga result d'inka, Congratulations, baka d'aukeda kowacce irin cuta...."πŸ˜ƒ

Huzaifa ya kar6a yana fadin "to Alhamdulillah"


Kallan ta Doctor yayi yace "Waheeda"

'Dagowa tayi ta Kalle shi sannan tace "Na'am"

Yayi ajiyar zuciya yace "Waheeda duk abinda kikaga yasamu Bawa, to anaso ya yarda da qaddarar sa, ita cuta ba mutuwa bace, sannan idan kin yarda da shawarwarin dazan baki Zaki zauna lafiya, sannan Zaki rayu kamar kowa idan nad'oraki akan magani,kuma....."

"dan Allah dakata Doctor Mahmud, mekakeso kace ne?"

Cewar huzaifa daya dakatar da doctor

Doctor ya kalli idon Waheeda da yayi tsilli-tsilli tana Kallan su duka su biyun, sannan yace "Waheeda kiyi hakuri, Amma abunda bincikenmu ya nuna shine kina d'aukeda qwayar cuta me karya garkuwar jiki"

Lokaci d'aya, Waheeda da Huzaifa suka miqe tsaye

Huzaifa yace "What...? HIV fa doctor, tayaya?"

Gaban Waheeda yayanke yafad'i, tasaka hannu tadafe qirjinta, kanta take girgizawa kwata kwata takasa magana, lokaci d'aya jiri yad'ebeta tazube qasa sumanmiya "

Cikin sauri Huzaifa yabita, jijjigata yafara yi, yana fad'in" Waheeda!! Waheeda kitashi Dan Allah!! "

Office d'in aka turo, wata matashiyar budurwa tashigo, taci Gayu iya Gayu, tana ganin Huzaifa tace"Yaya Huzaifa lafiya Kuma? Meyasame ta?"

Huzaifa ya kalleta baice mata komai ba yasaka hannu ya d'auki Waheeda cancak, yafice daga office d'in

Yana fita matashiyar budurwar ta kalli doctor tace"meyake faruwa ne doctor?"

Kai tsaye yace "ta tsorata ne sakamakon gwajin da muka mata, muka Gano tana d'aukeda cutar qanjamau,but ni banga abun suma ba, kowanne Bawa da irin qaddararsa,Kuma ba lalle saika yi iskanci ne zaka sameta ba, akwai hanyo yi dayawa, wasu a wajan mahaifiyar su suke dauka, wasu ta hanyar hada jini Dame irin cutar, kokuma ayima allura da sirinjin Wanda yake d'aukeda cutar, kokuma sex, ko amfani da wani qarfe kamar su kibiya, to gashi ita tun kafin ma nafada mata magungunan daya kamata ta dinga Sha harta sume"

Cikin razani budurwar tace "mene? Wallahi saina fad'awa Hajiya, Kuma akan me qanjamau din yake wannan rawar jikin?Huzaifa d'an'uwana ne, cousin d'inane, bazamu Bari ya auri me wannan cutar ba, ta shafa masa masifa, ita tasan inda tasamu cutar ta"

Tana fad'ar haka, tafice daga office d'in, Doctor yayi murmushi sannan yabud'e wani file yaci gaba da rubuce-rubuce


Motar ya bud'e yasaka ta aciki,har zuwa lokacin Waheeda bata farfad'o ba, Shima yashiga, dube dube yafara anan yaga wayarta cikin hand bag dinta , Kai tsaye contact d'in wayar ya duba, mutum d'aya ne yafad'o masa, dayake wayar Ummah ce yana ganin Ansa Naufal Son,yakira wayar, Babban Yaya yana gida yana motsa jiki, yaga Kiran Ummah, dayake ringing d'inta daban ne, saiya daina abinda yake ya d'auki wayar

Cikin damuwa Huzaifa ya zayyane masa komai, Babban Yaya yadafe Kansa da hannun saπŸ€¦πŸ»β€β™‚οΈyakasa cewa komai,banda innalillah wa inna ilaihirraji'un babu abinda yake maimaita wa a ransa, lokaci d'aya yarasa a'ina yake, a zaune yake ko a tsaye, gabansa banda Dukan uku uku babu abinda yake,Hiv Kuma? Hasbunallah..... yana jin Yanda Huzaifa yake fad'in "hallo hello, baka jinane?"

'Dif yakashe wayar, cikin tashin Hankali yazura kayansa yanufi Airport, ko wanka bai tsaya yiba


** *** **



Suna zuwa gida yad'aukota a hannun sa yafuto da'ita daga cikin motar, yanbiyu dasuke daukan photo a compound sukaga Huzaifa ya 'Dauko Waheeda, cikin sauri suka nufesu, Adede lokacin Didat da kakarsa da babansa suka shigo gidan, ta window din motar ya hango Wani ya dauki Waheeda a hannun sa, tun kafin babansa ya qarasa tsayawa da motar, yabud'e yafuto ya nufesu, yana zuwa ya cakumi wuyan Huzaifa "ubanwa yace ka d'auki wannan yarinyar...?"

Huzaifa ya kalli gaban rigarsa, yaga yanda Didat ya riqeshi cikin 6acin rai yasaki Waheeda tayi qasa, 'yanbiyu suna ganin haka sukai kan yar qanwar su suka cacimeta Sai jijjiga ta suke, Ihsan tayi gudu cikin gida ta fad'awa Ummah abinda yake faruwa, intisar Kuma tayi wajan fomfon da'ake bayin fulawa ta 'Debo ruwa ta watsa mata, lokaci d'aya ta farka tareda sakin wani irin kuka

Huzaifa yakama Didat, suka fara dambe πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?
Baban Didat ya kamashi yace "wuce mutafi gida, banason tashin Hankali son"

Ummah ta qaraso wajan itada Ihsan cikin tashin Hankali take tambaya ''menene yafaru?"Didat dayake ta haki da kumfan baki yace "Ummah saboda me wannan banzan zai dinga d'aukar Waheeda? saboda me Ina son yarinya wani qato zai dinga riqeta"

Cikin 6acin rai Huzaifa yace "nafi karfin a kirani qato, tunda nine Nan zan aure ta"

Didat yanuna shi da hannu yace "Dan zaka aure ta shine hakan yabaka damar ta6a jikinta? Aibaka aure taba"

Hajiya Anty tashigo gidan ta shirya tsaf zata wuce Asbiti, tabiyo wa Ummah zasu gaisa,kamar yanda tasaba, tana zuwa batabi takan kowa ba tanufi Waheeda, datake kuka kamar ranta zai fita, tambayar ta take "meyake faruwa?"

Amma Waheeda tayi shiru tama kasa magana.

kakar Didat ce ta matso ta kama hannun sa tace "muje" ta sake Kallan Ummah tace "Hajiya zamu dawo daga baya"tana fad'ar haka tajuya tashiga motar su, shikuma Didat babansa yakama hannun sa, yayinda Huzaifa yake sake gyara gaban rigar sa da Didat ya cukwikwiye masa, mutuqar tashin Hankali Hajiya Anty tashiga, jikinta Sai rawa yake tana kallon Waheeda, bata taba ganinta tana irin wannan kukan ba, gashi taqi yimata magana, Cikin 6acin rai ta make Waheeda da duka,tace"Dan ubanki bazaki fadamin abinda yake faruwa ba? "

Cikin kuka tace" Wai... Waii.... Ninn nice nake da qanjamau... "ta qarasa maganar tana rushewa da Kuka

Yanbiyu suka zaro ido😳 suna fad'in"qanjamau Kuma?"

Didat da babansa suka juyo da sauri, kowa Idonsa akan Waheeda sunaso suji ta amsa abinda yanbiyu suke tambaya, ahankali ta daga musu kanta alamun hakane

Didat ya kalli Waheeda ya jijjiga Kansa, sannan yayi gaba, babansa ma yabi bayansa suka tafi

Yanbiyu ne suka ja Waheeda sukayi ciki da'ita, gaban hijab dinta duk ya jiqe da hawaye, hannunta ta dora aka, tana rusa uban kuka, Hajiya Anty tabiyo bayansu cikin wani irin yanayi, kwata kwata bata sanin inda take jefa kafarta, kawai tafiya take, Ummah kuwa jitayi kamar tana tafiya akan is'ka, kalmar qanjamau d'innan Sai yawo take acikin zuciyar ta,Huzaifa yashiga motarsa yaja yabar gidan

ihun da Waheeda take ne yafuto da Daddy daga cikin daki cikin sauri, Nan yafara tambayar ba'asi, Amma kowa yakasa bashi amsa, da Yanbiyu da Waheeda kowa Sai kuka yake, su Sa'ad da Sa'eed ma suka futo daga daki kowa yana tambayar ba'asi

Hajiya Anty tadauko wayarta ajaka takira Uncle Usman tace "Alhaji gidannan fa babu lafiya, katashi daga baccin Nan kazo" tana fada masa haka muryarta na rawa alamun kuka zata fara, daga Nan ta kashe wayar ta

Ko minti biyar ba'ayi ba saiga uncle Usman yashigo dagashi Sai jallabiya, Daddy yace "Hajiya, mu duk munzo Nan mun zauna, muna tambayar ku meyake faruwa kunyi mana shiru, Yara suna kuka kunbarsu babu Wanda yake lallashin su"

Ummah ta Kalle shi "Alhaji Wai Waheeda ce me qanjamau..." tana fad'a masa haka hawaye yazubo daga idonta

Daddy da Uncle Usman suka nemi waje suka zauna suna fadin "innalillahi wa inna ilaihirraji'un...."

Hajiya Anty tadafe kanta daya ke ciwo kamar zai fado,Waheeda tanajin furucin Ummah tafara girgiza kanta,cikin kuka tace "wallahi ni banida komai, Allah sharri akamin" yanda take kukan abin tausayi shine yasake karya zuciyar yan'uwan Nata ma, Nan da Nan falon nasu ya kaure da koke-koke,
Ahankali Hajiya Anty tatashi ta janyo ta jikinta ta rungume ta, idanun Waheeda yayi jajir, fuskarta ma haka, Sai ajiyar zuciya take, Hajiya Anty ta kwantar da kanta a qirjinta tana bubbuga Bayan ta, Amma kwata kwata takasa cemata komai, ita kadai tasan metake ji acikin zuciyar ta

Maya ce takira wayar yanbiyu, cikin kuka intisar ta d'auka, Maya tace "Inti nakira wayar Ummah zanyi magana da Waheeda to ba'a d'auka ba, Dan Allah ki had'ani da'ita"

Cikin kuka intisar tace "Maya Waheeda babu lafiya"
Maya tace "innalillahi.... Kinga Bari kawai Gani Nan zuwa, tunda naji kina
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment