Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dariya ta kamashi cikin sauri yakashe wayar kar Ummah ta d'auka taga waya a kunne

Hajiya Anty tace"mun shiga uku Yaya, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, to ai yanzu saitaje ta wanke ta yayansu" πŸ˜‚


Ummah tace "shiyasa na dage akan ayi mata auren, Hankali na zaifi kwanciya"


Babban Yaya yadinga dariya ad'aki shi kad'ai,yana mamaki Waheeda ce tafad'i irin wannan maganar? πŸ€”Shiyasa daya tambayeta laifin me tayiwa Ummah tayi shiru taqi fad'a masa?


Ummah bata Bawa yanbiyu abincin sun kawo ba, Sa'eed tabawa yakai musu,Bayan tafiyarsa Babban Yaya yaje yayi nocking d'akin tanajinsa taqi bud'e masa haka ya haqura yajuya

Abu kamar wasa kwata kwata Waheeda taqi bud'e d'akin, inde taji alamun yana gida saita rufe d'akin ta, babu abinda take a gidan, tanajin yafita, saita futo tayi harkokinta Takoma d'aki, abinda tasa aranta shine itade bazata iya wannan rashin kunyar da Babban Yaya ba, domin kuwa rayuwar aure daban, rayuwarsu kafin aure daban, Gara suci gaba da tafiya Ahaka


Babban Yaya tun yanabi takanta harya dawo ya share ta, yau tanajin qaran TV afalo tafuto daga d'akin, lemo ne a gabansa dakuma computer yana typing, d'agowa yayi ya kalleta sau d'aya yamaida Kansa ga rubutun dayake

Zama tayi aqasan kujerar dayake zaune, ta sunkuyar da kanta qasa, batare daya kalleta ba yatashi daga wajan zai wuce d'akinsa, cikin sauri tatashi tabi bayansa, d'akinsa yashiga zai rufe kofar saigata kamar an jefota, d'aure fuska yayi yace "menene Kuma? Inace gudu na kike?"

Wasa tafara da yatsun hannunta, idonta yaciko da qwalla tace "Dan Allah Babban Yaya ka temaka ka sakeni...."

Cikin sauri ya kalleta, Kansa ya Sara kamar an doka masa guduma, cikin sauri yace "meyasa?"

Hawaye ne yazubo mata, tace "haka Nan..."

Yace "hakanan? To kiyi hakuri, bazan iyaba, because.... I luv you, sannan karki kuskura kisake min wannan maganar"
Yafad'i hakan tareda juyawa zai shige d'akinsa, kuka tafashe dashi tace "Dan Allah Babban....." kafin ta qarasa maganar Tata yajuyo yahad'e bakinsu waje d'aya

Lumshe idonta tayi, hawaye masu zafi suka silalo daga idanuwanta, tanajin yanda yake tsotsar lips d'inta kamar yasamu sweet, daga baya yakama harshen ta yana musu wata irin tsotsa kamar ba Babban Yaya ba, bud'e Idonsa yayi yaga yanda take hawaye kamar anbud'e famfo, ahankali yasaka Hannunsa yakama kanta yariqe,ya Lumshe idonsa yacigaba da kissing d'inta, abunda yadad'e yana mafarkin samu Sai gashi yau yayi mata shi, tana cikin hayyacinta Kuma a matsayin matarsa

saida yasha bakinta sosai sannan yasake ta, yana sakinta Tajuya d'akin ta da gudu tana kuka, Shima jingina yayi da jikin kofar d'akin yana sauke numfashi, ga wata irin sha'awa datake taso masa, jiyake kamar yaje wajan Waheeda


Mararsa ce ta murd'a yasaka hannu yadafe, ahankali ya qarasa kan gadon, tareda d'aukan wayarsa, yarasa wazai kira Ummah kokuma Hajiya Anty? Wazai fad'wa matsalar sa? Ummah de da'ita yasaba, yasaba fad'a mata komai, Dan haka yanzun ma ita zai nema, Ahankali yayi Dialing number ta, tana d'auka ya Lumshe Idonsa yace "Ummah, Waheeda taqi hakura har yanzu, Ummah me zanyi mata tasoni?, Ina sonta Ummah, yanzu cemin tayi insaketa fa Ummah... "ya qarasa maganar cikin rawar murya

Ummah tayi murmushi tace "kashirya katafi England, zanyi maganin komai son"

Kai tsaye yace "to Ummah" sannan yakashe wayar



Waheeda ma anata 6angaren cikin kuka takira Hajiya Anty, saboda tasan Kota kira Ummah ba goyon baya zata samu ba πŸ˜ƒ

Anty tace "Daughter lafiya?"

"Anty Allah nagaji...." abinda tace kenan, tafad'i maganar cikin kuka

Anty tace "subhanallah, meyafaru ne? Kimin bayani Waheeda duk Hankali na yatashi"

Hawayen tashare tace "Anty ni bazan iya zama dashi ba, haka kawai saiya dinga min wasu irin abubuwa, aishi Yaya nane, meyasa zaimin haka"

Anty ta dafe kantaπŸ€¦πŸ»β€β™€οΈtareda murmushi tace "to kiyi hakuri yadena, zanyi masa magana karya sake 6ata miki rai, kinji Daughter"

'Daga kanta tayi kamar ba waya take ba, sannan tace "to" tareda kashe wayar



Kamar yanda Ummah ta bashi shawara rabuwa yayi da Waheeda, washe gari da safe ya shirya zai koma bakin aikinsa

Driver ne yad'aukeshi, Kai tsaye yace "muje gidansu Maya"

Suna zuwa driver yafuto da sari yabud'e masa motar, yaro yatura Akira masa Maya, babu 6ata lokaci kuwa Sai gata tafuto, tana ganinsa ta qarasa wajansa tace "Babban Yaya Ina kwana"

Idanu yazuba mata yace "Lafiya Maya, zuwa nayi inyi miki godia"

Murmushi tayi tace "babu komai wallahi, Allah yabada Zaman lafiya"

Envelope yamiqa mata cikeda kud'i yace "ga wannan ki kaiwa mamanku, sannan ki shirya Bayan qawarki tagama fishi zaku tafi Saudia tare insha Allah"

Cikin murna Maya tace "Babban Yaya mungode, Allah yasaka da alkhairi"

Yace "Amin, idan kinsamu lokaci kije gidan ki lallasheta, kibata shawara" yafad'i hakan yana Sosa girarsa d'aya πŸ˜ƒ

Tace "to insha Allah zanje"

Murmushi yayi yashiga motar, yana fatan ace ta fahimci shawarar dayake nufi abawa Waheeda, fatansa d'aya Allah yasa tabata shawara irin wadda Ummah taji suna fad'a awaya πŸ™ŠπŸ™ˆπŸ™ŠπŸ™Š


Kafin su qarasa Airport yaga text yashigo wayarsa daga Ummi naban haquri, shareta yayi baiyi mata replay ba, ya goge number ta daga wayarsa, ya tabbatar taji labari ne cewa Waheeda lafiyarta kalau, shiyasa takeso ta lalla6o tadawo πŸ˜‚



** *** **



Sai wajan azahar Maya takira wayar yanbiyu suka kwatanta mata gidan da Waheeda take, sannan ta shirya tatafi, tana zuwa megadi yatareta yana mata tambayoyi tayi masa bayani sannan Yabarta tashiga

A falon ta dinga doka sallama Waheeda tana kwance ad'aki tana jinta taqi futowa, Maya dataji shiru saita fara bud'e qofofin tana dubawa sannan tayi nasarar bud'e na Waheeda

Mamaki ya kamata ganin Waheeda idonta biyu, qarasawa tayi ta zauna akusa da'ita tace "qawata kiyi haquri, nayi tunanin kin huce shiyasa nazo, ashe har yanzu Ina Nan acikin ranki"

Ba tareda ta kalleta ba tace "aina fad'a miki NI DAKE har abada Maya"

Maya tace "subhanallah, Waheeda me yayi zafi haka?nad'auka namiki gata ne akan aurenki da Babban Yaya, ashe Bahaka bane Wai Waheeda harni kika shaqe duk qawancen mu"

Tashi tayi zaune, cikin masifa tace "eh na shaqe kin, kiyi abinda zakiyi, ai wallahi Maya Kin bani mamaki, banta6a tunanin dake za'a had'a baki a auramin Babban Yaya ba, kin cuceni kuma kin gama Dani"

Cikin sanyin jiki Maya tace "ban cuceki ba Waheeda, temakon d'an'uwanki nayi, Duk Wanda ya zauna daku zaisan cewa Babban Yaya yana sonki, Kuma nasan cewa bazaki ta6a samun masoyi kamar saba, Babban Yaya yana qaunarki Waheeda, Kuma kun dace da juna sosai"

"yanzu ke Maya idan kece akace ki auri yayanki Safwan zakiji dad'i?"

Maya tace "to menene aciki? Abu d'ayane zai dameni yanda zan sake inyi masa abubuwan soyaiya na aure, Kuma Shima lokaci ne ahankali zan saba, kema kuma idan wannan ce damuwar ki toki daina,Babban Yaya zaisa ki manta da cewa shi yayanki ne, sannan karki manta da qaddara, kowa da irin tasa,Kuma munyi alqawari zamu yarda da'ita me kyau ko marar kyau"

Waheeda tana jijjiga qafa cikin damuwa tace "shikkenan ya wuce, Amma karki sake min irin haka, ni banaso, Shima Kuma bazan iya zama dashi ba, saboda tsabar abun kunya rannan har kiss yamin, Ina zan Kai wannan rashin kunyar?"

Maya tasaki dariya tace "yakaiki rashin kunya ne? Keda kowa yasan halinki ne haka bakida kunya? To menene ma danya miki kiss? Haka zakiyi haquri ki yarda, kema kiyi masa, wannan shawarar dakika Bani de akan za'amin aure itace zata dawo kanki, haka Zaki kama abun mijinki ki wanke"

"Dan girman Allah Maya kidena min wannan maganar, kodan kinga na kulaki? Ni banason jin wannan abun kunyar,inrasa wazanyi wa hakan Sai Babban Yaya?"

Maya tace "aikuwa saiki maraba da kishiya"

Cikin rashin damuwa tace "kofa abud'e take, tazo ta zauna ban hanata ba"

Kafin Maya tace wani abu yanbiyu suka shigo d'akin, sunci kwalliya iri d'aya ko ganesu bakayi, abinci suka ajiye mata Ihsan tace "ke ga abincin ki Nan inji Ummah"

Kallan abincin tayi tace "wannan ai yayi mana kad'an, ko Babban Yaya zai iya cinyewa, yanda yake cin abinci idan yasamu waje to wallahi shi kad'ai ma zai cinye wannan"


Intisar tace "wanne Babban Yaya Kuma shida yatafi England? Ni jinake ma dake zai tafi, ashe shi kad'ai yatafi, ke yanzu Waheeda ba abun kunya bane wannan? Sabon aure Amma kibar ango yatafi shi kad'ai? Kyaje yakula wasu matan acan wallahi, tunda yanzu ya d'and'ana yaji dad'in mace "πŸ™ŠπŸ˜‚

Cikin 6acin rai Waheeda tace" uwar me ya d'and'ana? Inti banason rashin mutunci wallahi, ba England ba, yatafi kafi England ma,dayau yafara huld'a da mata? Da idona na ganshi mata suna yanyameshi Sai yage musu baki yake, da idona nagani "


Ihsan tace" to babu so menene Kuma yakawo kishi? Keda kike cewa bakya sonsa miye dankinga mata suna yanyameshi? d'an ball nefa, ba mata ba mazama yanyameshi zasuyi, malama kinaso kina yiwa mutane ihu ke bakya so "

Tace" eh banaso, ba Kuma zan so ba, da yau yafara kula matan dazaku zo Kuna cewa nabarshi yatafi, inda ace nasan baya gidan ma da tuni Nima na kama gabana, Zaman me zanyi yanzun Ina masa gadin gida? Saikace wacce batada galihu, Nina tafi gida idan kun gama kwa taho "tafadi haka tana Jan hijabin ta tafice daga d'akin πŸ˜‚πŸ˜‚



Babu yanda suka iya haka suka futo suka biyo bayanta, saida sukazo gida sannan Maya tamusu sallama tatafi gida, sukuma suka shige cikin gida, megadi Sai tsokanar Waheeda yake yana fad'in"Amarya kinsha qamshi"


Yau kwananta hud'u agida, Amma kamar bata gidan, Dafarko tayi tunanin zasu kulata, shiyasa take wuni ad'aki, dataga babu Wanda yake shiga harkar ta, saita fara futowa tana abin gabanta, daga Ummah har Daddy idan ta gaishe su daga sun amsa basa qara cemata komai, haka yanbiyu ma tun lokacin dasuka mata fad'a tamusu rashin kunya suka tattara ta suka watsar, Hajiya Anty tahad'o mata magungunan mata masu kyau, ta zaunar da'ita ta mata bayanin yanda zata dinga amfani dasu, sannan tabata haquri akan Takoma gidan mijinta, Amma Waheeda tayi mursisi taqi komawa, magungunan ma ta ajiye su taqi shan kod'aya aciki.


Yau satinta uku agida, Kuma har zuwa wannan lokacin bata kira Babban Yaya ba, Shima bai kirata ba, Kuma babu Wanda yace tattara kayan ki kikoma, kowa yazuba mata ido kawai.

Yau suna break fast afalo gaba d'ayansu, banda Daddy, Sa'eed ya kalli Waheeda sannan ya kalli Ummah yace "Wai wannan yarinyar Zaman me take a gidannan Ummah?"

Ummah ta Kalle shi tace "gatanan ka tambayeta"

Kallan Waheeda yayi yace "keme kikeyi har yanzu baki koma ba?"

Idonta ne yayi qwalqwal yakawo ruwa, tana juya spoon acikin cup d'in tea d'in dake gabanta tace "ni Bana sonshi...."

Sa'ad yayi sauri yace "to cemiki akai shid'in sonki yake? Banda qaddara ma me Babban Yaya zaiyi dake? Ga yanmata Nan had'ad'd'u suna bibiyarsa zai tsaya anan Ana Rena masa Hankali"

Sa'eed ma yace "okay bakya sonsa ko? To Alhamdulillah, Ummah kawai idan yazo kibashi shawara yasake ta kawai"

Ummah ta ajiye bread d'in hannunta tace "na fad'a masa tun shekaran jiya da mukai waya, idan yasamu lokaci Yazo ya rubuta mata takardar, saisu koma makaranta itadasu Ihsan"

Sa'eed yace "Hakan ma yafi, Dan wannan yarinyar Dama ba ajin auren sa bace, kawai de Dan Allah ya rubuta Sai anyi ne, ni Gara ma dayake shirya abinda yafi masa, abinda Yayanke d'in yayi daidai, yanzu ne yasan zaiyi aure"

Gaban Waheeda yayanke yafad'i, ahankali ta zaro idonta 😳batare datace komai ba

Shima Sa'ad yace "eh gaskiya Kam ya kyauta"

Hajiya Anty ce tashigo falon zata yiwa Ummah sallama kamar yanda tasaba idan zata tafi wajan aiki, tajisu suna fad'in eh ya kyauta Kam tace "waye ya kyauta?"

Ummah tayi murmushi tace "Wai suna magana ne akan auren yayansu, kinsan jiya Daddynsu yamasa waya yace idan zai taho yahad'o wasu kayan lefen Sai akai gidansu ummin, tunda tabada haquri Kuma Shima Naufal d'in yace ya haqura zai aure ta" πŸ˜‚

Waheeda taji numfashinta yana yin sama kamar zai d'auke, gabanta Sai fad'uwa yake, takasa d'agowa ta Kalle su, sukwa yanbiyu Sai lodar abinci suke ko bakinsu ba'aji

Hajiya Anty ta kalli Waheeda tace "yanzu Yaya ba zakuyi haquri da maganar Ummin nanba? Ayita yin abu de? Duka duka yaushe yayi aure dazaku sake da'aura masa wani auren?"


Ummah tace "to Antynsu Yaya zanyi dashi? Jiyafa kirana yayi kamar zaiyi kuka shide ayi ayi a aura masa Ummi,yanaso yazo gobe ko jibi ayi agama magana, so yake yazo yatafi da'ita England, ita Kuma Waheeda tunda tana zaune agida, saitaci gaba da Kula da gidan, idan sukazo hutu kinga har saga gida tsaf dashi 'yar aiki ta gyara musu "

Waheeda tacika tacika tazo wuya, batasan lokacin data Fashe da Kuka ba, cikin gudu tayi d'akinsu tad'auki wayar inti takira Maya, bugu biyu Maya ta d'auka tace"inti ya akayi Ina qawata? "

Waheeda tasaka mata kuka tace" Maya yanzu kowa baya sona, Shima Babban Yaya yadena sona, Wai ummi zai aura, Kuma Daddy yace yazo yakawo kayan lefe idan anyi auren yatafi da ummi, Nina shiga uku na Maya ya zanyi? "

taqara sa maganar cikin kuka

Maya tace" kema Waheeda kinada laifi, bakya bashi kulawa dole hankalin sa yakoma kan wata"

"to ya yakeso namasa Maya? Rannan fa kuka yakemin saikace qaramin yaro, ni wallahi yafi qarfina bazan Iyawa shagwa6ar saba"

"babu Wanda yazo da iyawa Waheeda, kowa dakika Gani Koya yayi, kikasan me Ummin ta qulla masa? Tayaya za'ai ki zauna kinada kamar Babban Yaya?"

Cikin hawaye tace "to tashi zanyi?"

Dariya takama Maya, ganin duk tsiwa irinta qawar Tata yanzu Babban Yaya kad'ai yana nema ya rikita ta, tace "ni bance ki tashi ba, ba zama ba kiyi kwanciyar ki ma, lokacin dakika ce yana kuka kamata yayi kijashi ajikinki, ki rungume abinki ki lallashe shi, na tabbatar bakiyi hakan ba, Waheeda dole saikin ajiye wannan yayan agefe ki d'aukeshi as mijinki, inba hakaba wallahi tunda kikaji maganar Ummi tashigo to tsaf zai aure ta, Dan maza idan sukai niyyar qara aure ba'a hanasu,kikama hanya kitafi gidanki, kikirashi awaya kibashi haquri kiyi masa shagwa6a,tunda kince Ummah tace zaizo to idan yazo kicire kunya kinuna masa soyaiya tsantsa, sonake yanda yace zai auri ummi ya dawo da Kansa yace yafasa "

Waheeda tayi ajiyar zuciya tace"zan iya kuwa Maya? "

"Mezai Hana? Wai Waheeda Ina wayonki yake ne? Naga kece me Bani irin wannan shawarar, kitashi kiyi abinda nace kawai, wannan gidan naki ne ke kad'ai insha Allah qawata, babu wadda zata shigo "

Ahankali tayi ajiyar zuciya tace"to Maya"

sannan ta kashe wayar

Kai tsaye truly d'inta tad'auko, magungunan da Hajiya Anty tabata shita fara d'auka tasaka a jakar πŸ˜‚
Sannan tadauko duk kayanta, tasaka aciki, ta janyo jakar tafuto falo

Suna zaune Sai ganin Waheeda sukai tafuto da jaka
Mamaki ya kamasu, basuyi tunanin wannan plan d'in dasuka had'a zaiyi tasiri akanta ba, ko sallama bata musu ba tafice daga falon cikin fishi


Tana fita suka kwashe da dariya, Hajiya Anty ta kalli Ummah tace "lalle Yaya kin kawo point" πŸ˜‚



✍�
1/28/22, 20:51 - Ummi TandamaπŸ˜‡: AL


Driver tasa yakaita gidan, suna zuwa kuwa megadi ya kar6i kayan hannunta yakai mata shi har ciki, sannan yajuya yakoma gate.


A falon tabar kayan Nata ko d'aki bata shiga dashi ba, tacire hijabin ta tafara gyara gidan, bata gama ba Sai wajan azahar, takai kayan d'aki sannan tayi wanka tasaka Riga yar qarama, iyakarta gwiwarta, tadafa indomie ta zauna tanaci tana kallo a TV, d'aki tashiga tad'auki magungunan ta Tasha, sannan ta kwanta tahuta, Sai wajan qarfe uku tadafa musu fried rice, ta kaiwa megadi sannan ta kulle falon tayi kwanciyar ta, kullum haka takeyi, idan tadafa abinci zata kaiwa megadi nasa, sannan tarufe falon saikuma washe gari, magungunan ta kuwa bata wasa dasu kullum Sha take, ita kanta tanaji ajikinta, yanda maganin yake mata aiki

Saboda magungunan sunada kyau sosai, satinta d'aya da komawa da sukaga bata dawo ba, Sai hankalin su ya kwanta, ganin haka yasa Hajiya Anty tatura mata Dame gyaran jiki take zuwa har gida takeyi mata, kullum Maya zatazo tatayata aikin gida, ita Kuma ta zauna ayi mata gyaran jiki, wataran yanbiyu suzo suhad'u su hud'u a gidan sutayata hira, kasancewar gyaran jikin yanzu a zaune take agida babu inda take zuwa Sai yafi kyau fiyeda na wancen Karon, jikinta yayi wani fresh, ko'ina yasake cika saboda yanda Hajiya Anty tahad'ata da magungunan ingantattu masu kyau, tsawon sati uku suka d'auka anayi mata gyaran jiki da turere Kala Kala na jiki dakuma na tsugunno, yau matar tagama aikinta danhaka bata zoba, suma su Ihsan basu zo ba, gyaran gidan tayi, ko'ina yad'auki qamshi, tayi abinci daidai cikinta, ta zauna taci Sannan ta wuce d'aki, bacci ne ya d'auketa, bata tashi ba Sai wajan shad'aya, futowa falon tayi zata je kitchen ta d'ora abinci, d'azu bata Bawa megadi ba, 'yar qaramar Riga ce ajikinta, iyakarta gwiwarta, bata saka brezia ba, kana ganin yanda boobs d'inta suke a tsaye ta cikin rigar, kanta babu kitso duk gashin ya bazu a fuskarta, fatarta Sai qyalli take tana d'aukan ido kamar ka latsata jini yafuto

Tana bud'e kofar d'akin tana futowa falo ta tsaya tayi wata irin miqa tareda hamma, kwata kwata bata lura da mutum a falon ba, Babban Yaya dayake zaune yad'ora kafa d'aya kan d'aya yana waya da mashkur, lokaci d'aya yanemi nutsuwarsa yarasa, soyake ya d'auke Idonsa akanta Amma yakasa, yanda ta turo qirjinta gaba yafi komai Jan hankalinsa, daqyar ya sunkuyar da Kansa yana Sosa girarsa d'aya sannan yace "inaji"

Daga d'ayan bangaren mashkur yace "Dan Allah Abokina katemaka kabani number yarinyar Nan, yanzu tun dad'ewa Ina bin kanka akan yarinyar Nan Amma ka hanani number ta?"


Tun lokacin daya ce inaji, Waheeda taqame a falon tana kallon sa, yaushe yazo? Duk saita rikice tarasa me zata masa, inda ace dane da gudu zataje ta fad'a jikinsa, Amma yanzu meyasa ta kasa? Anya zata Iya amfani da shawarar Maya kuwa? Kalli yanda ya shareta Shima kamar be ganta ba, ahankali ta juya zata nufi kitchen

Babban Yaya ya kalleta qasa-qasa, yaga yanda hips d'inta suke juyawa, wani irin yawu ya had'iye sannan ya sauya wayar dayake da mashkur, yayi kamar da Mace yake waya, memakon yabawa mashkur amsa saiyace "na fad'a miki ko awa d'aya bazan iya a gidannan batare Dana ganki ba, tun jiya nake mafarkin had'uwa dake, ko minti talatin banyi da zuwa Bama, yanzu zanzo naganki, kibani abinda kika tanadar min"


Waheeda ta tsaya cak, gabanta yana fad'uwa, sake Kallan ta yayi, yayi tunanin zata taho da gudu ta fad'o Kansa kamar yanda tasaba, yaga ta tsaya ko juyowa batayi ba, mashkur yace "man ni zakayi wa wulaqanci ko? Zamu had'une, inama magana kanamin wani irin zance"

cikin sauri Babban Yaya yasake cewa "a a, karki damu wallahi, qanwata tana zaune agidan, dama itace me kula da gidan, shara, wanke wanke, da duk ayyukan gida, zata kula da wannan, Gani Nan zuwa"
Qitt yakashe wayar sannan yatashi yafice da sauri, gidan Ummah ya nufa, Dama yayi tunanin zai samu kar6uwa ne a wajan Waheeda, da babu abinda zaisa Ummah ta ganshi yau ☹️
Amma tunda bai samu hakan ba, Gara yanemi Ummansa Kota d'ebe masa kewa da hira


Tana ganin fitarsa ta tsugunna a wajan tafashe da Kuka,d'aki tashiga da gudu, wayar inti data manta a gidan ita ta d'auka takira layin Ihsan, Ihsan tace "Waheeda yagida"

Fashewa tayi da Kuka tace "Wai Babban Yaya ne zai tafi wajan Ummi, ko magana bemin ba, yatashi yabar gidan, saboda yanzu baya qauna ta"

Ihsan tace "yazo qasar ne? Kiyi hakuri Bari infad'awa Ummah, kiyi shiru"

Kashe wayar Waheeda tayi, gaba daya saitaji komai ma yafice mata Arai, girkin ma fasa dorawa tayi, ta zauna a wajan tana kuka


** *** **


Ihsan tafuto daga d'akinsu, saita tsaya turus ganin Babban Yaya zaune agaban Ummah tana bashi abinci, Sai hirarsu suke cikin nishad'i

Qarasawa tayi tagaidashi, sannan ta kalli Ummah tace "Ummah Waheeda ce take kuka, Wai Babban Yaya yatafi Wajan Ummi, ko magana beyi mata ba"

Ummah tayi murmushi tace "jeki Ihsan"

Ahankali Ihsan ta juya, Saida yaga tatafi sannan ya kalli Ummah yace "Ummah tana kallo nafa, ko sannu da zuwa batamin ba, shine na nuna mata da Ummi nake waya, nikuma da mashkur muke magana akan Ihsan, yadage Wai yana sonta"

Ummah tayi murmushi me ciwo, duk da yafad'a mata abinda zaisa taji dad'i akan maganar mashkur da Ihsan, hakan baiyi tasiri a ranta ba, tafi damuwa da batun Waheeda, taga alama Waheeda bazata sauya ba, Naufal yadad'e baiyi aure ba, yana buqatar kulawar matarsa, inbanda itan ce ta sameshi ta tabbatar idan wata ya aura da tuni yafara kula wasu yanmatan,ajiyar zuciya tayi tace "to Allah ya tabbatar da alkhairi, Son kaje kakaiwa Waheeda takardar ta...."


Cikin sauri ya d'ago ya kalleta yakasa magana, beyi tunanin wannan maganar daga bakin Ummah ba, haushin Kansa yaji, daya Sani be fada mata laifin Waheeda ba, cikin sauri yace "Ummah Dan Allah kiyi haqurrr....."
Hannu ta daga masaβœ‹πŸ? tace "kaje kayi abinda nace kawai"


Beqara ce mata komai ba yafice daga gidan, driving yake Amma baya tareda nutsuwa, tayaya ummah zatace yaje yasaki Waheeda? Ko batasan cewa sakin Waheeda daidai yake da sakin zuciyar sa ba?Anya kwa Ummah tasan irin wahalar dayasha akan Waheeda?

Har yazo gidan yarasa abinda zai aikata takameme, falon yashigo anan ya ganta zaune kan kujera tana share hawaye, wucewa yayi d'akinsa, ya kwanta akan gado tareda fad'awa cikin duniyar tunani, wani tunani ne ya fad'o cikin ransa, cikin sauri yatashi yanemi paper da biro yayi rubutu aciki, ya ninke takardar sannan yafuto daga d'akin, Kai tsaye wajan ta ya nufa, yad'aure fuskarsa yace "idan ban manta ba, last time kince min in temaka in sakeki ko?"

Cikin sauri ta Kalle shi takasa magana, ya kalli qwayar idonta tayi jajir da alama Tasha kuka, cikin kuka tace "Bana baka haquri ba?"

Dariya ce taso kamashi, Amma sai yayi fuska yace "lokaci yaqure Waheeda, akwai wadda zatamin abinda narasa awajanki, har abada bazata iya neman saki awajena ba, saboda tana amfani da ilmin ta, ga takardar ki Nan" ya ajiye mata takardar yajuya zai fita


Ihu tasaka tace "wallahi ban saku ba, babu wadda zaka aura, wallahi bazan bud'e wannan takardar ba garama kazo ka d'auke abarka, Allah ban saku ba...." kuka take sosai tana fad'a masa hakan

Juyowa yayi ya kalleta yace "to idan kin gama kukan ki kulle min gidan,kitafi gidanku, Nima natafi wajan masoya yi ta"

Yana fad'ar haka yafice daga falon yanata dariya, be koma gidan Ummah ba, Kai tsaye gidan Hajiya Anty ya wuce




** *** **



Cikin kuka takira Uncle Usman, yana zaune a office d'in Daddy yayi tunanin Intisar ce saboda number ta yagani, d'auka yayi tareda sallama, saiyaji shiru da alama kuka ake, zamansa ya gyara yace "Intisar meyake faruwa? Lafiya kike kuka?"

Cikin shashshekar kuka tace "Ba inti bace.... Wa... Wahee.... Waheeda ce, Uncle Babban Yaya ne yasakeni, gashinan yabani takarda ta...."

Uncle Usman yatashi tsaye cikin tashin Hankali yace "innalillahi wa inna ilaihirraji'un...., innalillahi wa inna ilaihirraji'un....,kina Ina yanzun?"

"Ina gidansa" cewar Waheeda cikin Jan zuciya

Uncle yace "Kije gidan gamu Nan zuwa"

Daddy ya Kalleshi yace "meyake faruwa?"

Cikin damuwa uncle Usman yace "Wai Naufal ne yasake ta"

Gaban Daddy yafad'i, yace "what?! muje gidan, bari in kirashi, muje muje da sauri"

Cikin hanzari suka fita ko office d'in basu rufeba

Suna hanya Uncle Usman yakira Babban Yaya, yana d'auka ko amsa sallamarsa baiyi ba yafara magana cikin fad'a "ashe bakada Hankali?" πŸ˜‚πŸ™†πŸ»β€β™€οΈ?

Babban Yaya dayake kwance a cinyar Hajiya Anty yace yatashi da sauri yace "Innalillah.... Uncle me nayi?"

Cikin fad'a Uncle Usman yace "nikake tambaya me kayi? To duk abinda kake kabari kazo gidanku ka sameni yanzu yanzun Nan"

Babban Yaya yayi shiru bece komai ba, Uncle Usman yakashe waya, Daddy yace "dabaka kirashi ba Usman, na tabbatar laifi tayi masa shiyasa yakawo qarshan Zaman nasu, shiyasa Nima ban kirashi ba, koma menene muje gidan zamuji komai ai"

Uncle Usman yayi shiru Sai hura hanci yake,tunanin irin yanda zai 6atawa Babban Yaya rai yake, tayaya za'ai yasaki yarinya yamaidata qaramar bazawara?

Babban Yaya yamiqe tsaye yace "Anty zanje gida, uncle yana nemana, da alama nayi masa laifi bansani ba"

Cikin damuwa Anty ta d'auki wayarta tace "A a, me zakayi wa Uncle d'inka? Kaide kayi tunani me kayi masa?, kokuma inkirashi? "

Kwata kwata Babban Yaya ya manta da batun Waheeda, asalima tunani yake irin dad'in da zaiji idan yakoma gidan, saboda yasan idan ta bud'e takardar daya bata taga abinda yake ciki zataji dad'i Kuma yau zasuyi kwanan farinciki, saboda haka baya tunanin wannan Kiran yanada alaqa da Waheeda

Girgiza Kansa yayi yace "karki kirashi, nasan banyi masa komai ba, Bari inje kawai"

Tashi tayi tace "saide mutafi, muje gidan kawai"

Futowa sukai dukansu, suka tafi gidan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment