Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ne?"

Cikin kuka tace "Yagudu da wayata, naduba ko'ina baya Nan, wallahi gidan Nan zan Bari" tana fadar haka ta kwasa da gudu tayi cikin gida

Anan Ummah ta fahimci komai, Kai tsaye tabi Bayan Waheeda har d'akinsu, tana zuwa ta rufeta da duka, daqyar yanbiyu suka ceceta, Ummah taja kofar Dakin ta kulle Waheeda aciki, Dan tayi alqawari wannan Karon Waheeda tadena fita bare taja mata wata masifar


Har dare Waheeda tana d'akinsu akulle, Ummah tahana kowa yabudeta, Daddy ne ya dawo daga wajan aiki Sai masifa yake, ta inda yake shiga batanan yake fita ba
Duk sunyi shiru babu Wanda ya tanka masa, ita kanta Ummah ba tasan me zatace ba

Kallan 'yanbiyu yayi yace "kuje ku budeta tazo Nan Ina nemanta"

Inti taje ta bude Waheeda, akan gadon su taganta har lokacin kuka take, ta kifa kanta akan cinyoyin ta,dogon gashin kanta yazubo gadon Bayan ta, wani Kuma yarufe mata fuska kamar de mace me aljannu, kanta har ciwo yake saboda kuka, yanzu shikkenan wayarta tatafi, wayar ko wata daya Babban Yaya baiyi da siya mata itaba, ta Ina zata Iya Kallan idonsa tace takawo saurayi gida shikuma ya sace mata wayar? Intisar tace "kije Daddy yana kiranki"

Ahankali tataso, suna zuwa falon kowa yabita da kallo, su Sa'ad jisuke kamar Su make ta, Daddy ya kalleta yace "Dan wanne gidane Yaron? A wacce unguwa yake?"

Cikin kuka tace "Dadday bansan gidansu ba, ni bansan shi ba, yau nata6a ganinsa, Dan girman Allah Daddy karka fadawa Babban Yaya, Allah kasheni zaiyi"

Cikin fishi Daddy yace "yau kika fara ganinsa har kika d'auki waya kika bashi saboda ga yayanku me kudin banza yasiya miki waya ko?"

Ihsan tace "Daddy kayi hakuri, insha Allah bazata sake ba"

Sa'eed yakalli Ummah yace "Ummah kikira Babban Yaya kifada masa Dan Allah, sonake ya dawo ya kakkarya yarinyar Nan, Danni idan nakamaki saina miki Dukan mutuwa, inyaso nakawo gawarki, tunda haka kike so Dama"

Waheeda de tayi shiru, takasa cewa komai, Sai Jan zuciya take, fuskar Nan tayi jajir saboda kuka

Ummah tace "bazan kirashi ba Sa'eed, kullum Waheeda cikin janyo mana masifa take, kullum ninake kiransa nafada masa, yanzu Kam, bazan kirashi ba, idan kullum zan dinga kiransa Ina fada masa matsala ai Kuma idan yaga kirana gabansa faduwa zai dinga yi,sannan Kuma bance kufada masa ba, kubarshi yayi aikinsa, Daddynku zai dauki mataki akan haka"


Haka suka zauna a falon kowa yayi jugum, anrasa takamaimai Wanda zai kira Babban Yaya yafada masa abinda yake faruwa ๐Ÿ˜‚

Washe gari Waheeda bataje school ba, haka ta zauna tayi shiru adaki kamar marar lafiya, ko sunan Babban Yaya taji an ambata gabanta faduwa yake,yanda ta nutsu awaje daya, Sai gidan yayi shiru, idan ka kalli Waheeda saita baka sha'awa yanda tazama wata kamila, saide kowa taciki na ciki


Tsawon kwana biyu kenan da 6atan wayar Waheeda, har yanzu babu Wanda ya fad'awa Babban Yaya, sannan daddy bai d'auki wani qwaqwaqwaran mataki ba, asalima fishi yake da'ita, Kuma a kwana biyun Nan Waheeda bataje makaranta ba, tana zaune agida abun duniya yataru yayi mata yawa, yau da yamma suna zaune, Anty Maryam tashigo gidan cikin tashi Hankali, tana zuwa ta nufi Ummah tace "Ummah yajikin Waheeda? Ashe batada lafiya Amma Ummah kukasa fadamin? Awanne asbitin aka kwantar da'ita?"

Kafin Ummah tasake magana, Maya tayi sallama cikin falon nasu tana sharar hawaye, ta qarasa wajan Ummah tace "Ummah ashe Waheeda batada lafiya? Shiyasa Bata shiga makaranta kwana biyu? Na tambayi 'yanbiyu sunce min lafiyarta kalau ashe 6oyemin sukayi"

Kan Ummah ya d'aure, ta kalli Maryam dinta dakuma Maya tace "Wai wacce Waheeda kuke magana a kaine?"

Wayar Ummah ce tayi qara, ta d'auka tare fadin "sa'ad ya akayi?"

Yace" Ummah, wannan gayen daya sace wayar Waheeda fa inaga Dan damfara ne, ba'iya wayar yakeso ba, harda damfara a tsarin nasa, yanzu Ina zaune yaturo min saqo Wai me wannan wayar batada lafiya, tana kwance agadon Asbiti, Ana buqatar tallafin kudi, Sai kuma account number aqasan saqon"

Ummah tace "innalillah.... Sa'ad shiyasa na kulleta Adaki fa, saboda muna Zaman zamanmu wata Rana zatasa azo har gida a sacemu"

Sa'eed ne yake Kiran wayar, Ummah tace "Sa'ad kashe, ga dan'uwanka Nan Shima yana kira"

Tana daukar wayar Sa'eed din, Shima abinda yafada mata kenan, Ummah ta kashe wayar ta kalli su Maryam "wallahi lafiyar Waheeda kalau......" anan Ummah ta basu labarin abinda yake faruwa, Maya tace "Kai Amma wannan anyi tsinanne, yazo har gida yasace mata waya sannan ya dinga turawa mutane cewa batada lafiya aturo Masa kudi?, Ummah Ina Waheedan?"

Ummah ta nunawa Maya d'akinsu Waheeda, tatashi ta nufi Dakin, anan taga Waheeda ta zauna tayi shiru tana tunani

Maya ta dafata tace" Alhamdulillah, har hankali na ya kwanta wallahi qawata, text fa akamin bakida lafiya, kina gadon Asbiti a kwance, Wai Ana buqatar tallafin kudi ta wani account Number dayake Qasan saqon "

Waheeda tayi shiru takasa Bawa Maya amsa, Maya tace" Waheeda kalau kike kuwa? Inata magana kinyi shiru? Yanzu Waheeda shawarar Dana baki ashe baki d'auka ba saida kika kula saurayi?"

Waheeda tacire hannunta daga tagumin da tayi tace"Maya Babban Yaya"๐Ÿ˜‚


*** ** ***


Motsa jiki yake cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali, wayarsa dake ajiye acan Gefe yaji tana ringing, kafin ya dauka harta katse, dakatawa yayi da abinda yake ya d'auki ruwa yasha, sannan ya d'auki wayar, number datake kiransa ma baisan taba, saikuma saqo guda daya, daga Waheeda, yayi mamakin ganin saqon ta, saboda yasan bata masa text message, Kiran ma ba sosai take neman saba, shiyasa saqon ya d'auki Hankalinsa, wajan zama ya nema, sannan ya bud'e saqon Nata, abinda yagani ne yasashi yatsina fuskar sa, kamarya yatura kudi ta wannan account din? Waheeda ce batada lafiya Amma akasa fada masa har wani account number ake turowa atura tallafin kudi tanan? Account number waye wannan din?
"mashirmaciya" yafadi hakan a fili
Sannan yayi Dialing number Tata, har ta kusa katsewa sannan aka d'auka, memakon yaji muryar Waheeda, Sai yaji muryar wani, lokaci d'aya yanayin fuskar sa ta sauya,wani irin baqin kishi yataso masa, cikin 6acin rai,yace "waye?"

Daga d'ayan bangaren Sas soja yace "yayan me wayar ne, dama batada lafiya ne, tana kwance agadon Asbiti, muna neman tallafin kudi ne Wanda za'a mata aiki dashi, shine mukabi list din contact dinta muka tura musu"

Sumar Kansa ya hargitsa, cikin ransa yace Waheeda zata kasheni, Amma a fili saiyace "za'a turo" daga Nan yakashe wayar

Yana kashewa wani Kiran yasake shigo wa, number da'aka kirashi da'ita d'azu ne, ya d'auka tareda sallama, daga d'ayan bangaren akace "dawa muke magana?"

Kai tsaye yace "Naufal Umar Arabo,a.k.a Big Brother"

"Ok ikon Allah, ashe Big Brother ne, wato yalla6ai abinda yake faruwa shine, akwai wata yarinya da akai kidnapping dinta, kidnappers din sun nemi atura musu kudi, Kuma iyayen yarinyar sun tura musu kudin, daga qarshe Sai suka aikowa iyayen yarinyar da gawar 'yarsu, to Wanda aka turawa kud'in mun bibiyi Sim card din dayake amfani dashi mungano yana waya da iyayen yarinyar ne ta wata number waya, munyi bincike akan number, mungano number wata yarinya ce sunanta Waheeda Umar Arabo, kamar yanda mukagani a rigister Sim card din, saboda haka munyi tracking number Waheeda Umar Arabo mun dauki wasu daga numbers din dayake kira, aciki muka Gani harda taka number,yanzu haka ma kunyi waya, shine mukeso ka temaka mana, kafada mana inda yarinyar take, zamuje da'ita office dinmu, domin ta amsa mana wasu tambayoyi dangane da wannan Mai laifin ko Allah zaisa mu kamashi "

Babban Yaya yayi shiruuuu yadafe goshinsa da hannunsa ๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™‚๏ธ?,Yama Rasa abinda zaice, har sukaji yayi shiru sukace"yalla6ai lafiya dai ko?ko bakasan yarinyar ba?"


Ajiyar zuciya yayi yace"nasanta, she's my Sister, kuyi hakuri kubani awa hudu, zanzo qasar, saina Baku ita"

Godia sukayi masa dangane da had'in kan daya basu,sannan suka kashe wayar


Yajima a zaune a wajan, Yama Rasa wazai nema domin qarin bayani? Menene yahad'a ta da wani har zata d'auki waya ta bashi? Tashi yayi yaje ya shirya, yayi mutuqar kyau cikin qananun Kaya, saida ya toshe kunnansa da Bluetooth sannan ya d'auki wayarsa ya futo daga gidan

Karfe hudu na yamma ne yakawo shi gida, yana zuwa yakirasu, yafad'a musu yazo,su qara so sutafi da yarinyar, tun karfe uku yakamata ace yazo, but saida yagama da jama'arsa sannan yaqara so cikin gidan, kowa ganinsa yayi afalo kamar anjefo shi, gaba d'ayansu suna Nan 'Yan gidan, zama yayi akan kujera, cikin mamakin ganinsa Ummah tace "Son, lafiya naganka agida?"

Kansa a qasa yace "aina Dena zuwa ko'ina Ummah, haqura zanyi da aikina, saboda idan natafi ma, Waheeda Virus zata dawo Dani"โ˜น๏ธ๐Ÿ™Š๐Ÿ˜‚


Ummah tayi shiru kamar andoka mata sanda, cikin ranta tace yaji komai kenan, su Ihsan ne suka tafi da gudu d'aki suka fad'awa Waheeda Babban Yaya yazo



Gabantane yafadi, ahankali tatashi tad'auko hijab d'inta ta6oye shi abayanta, tare suka futo falo, Waheeda tafara bin bango zata gudu, a lokacin Yan sanda sukai sallama cikin falon

Babban Yaya yad'ago Kansa ya Kalle su, idanunsa sunyi jajir saboda tsantsar 6acin rai, ba taredaya Kalle taba yace "ke Zonan"

Hawayene suka fara sintiri akan kyakykyawar fuskar ta, agaban sa ta tsugunna tafara sheshshekar kuka,but takasa magana,kwata kwata taqi d'agowa ta kalli qwayar idonsa, cikin 6acin rai yace "ni Baban kine?"

Cikin kuka ta girgiza masa Kai hawaye wani nabin wani

Yace "to tunda ban haifeki ba, bazai iyu ki kasheni da raina ba"

qafarsa takama tariqe, cikin kuka , tace "Babban Yaya, Allah natuba, bazan sake ba, Babban Yaya kayi hakuri karka sa sutafi Dani, wallahi Allah bazan sake ba"


Kuka ne yakama 'yanbiyu, su kansu Waheeda tabasu tausayi, sukuwa 'yanbiyu maza Sa'ad da Sa'eed, wayarsu suka d'auka suke dannawa, Ummah ma tayi shiru tana Kallan su

Gaba d'aya falon ya kaure da kukan Waheeda dakuma na 'yanbiyu, Babban Yaya ya kalli 'Yan sandan dasuke tsaye a bakin qofa yace "Yalla6ai gatanan kutafi da'ita"

Volume din kukansu ne yaqaru, wata daga cikin police din mace, tazo takama hannun Waheeda tana janta, cikin kuka Waheeda take fadin "wayyo Allah na zasu tafi Dani, Babban Yaya! Babban Yaya!! Babban Yaya!!"
Har suka jata, suka tafi da'ita, bata daina kiransa ba.





Amnah
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandama๐Ÿ˜‡: BABBAN YAYA


Writing By Amnah El Yaqoub


Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/


13&14


'Yanbiyu ne sukai d'akinsu da gudu suna kuka, Ihsan ta d'auki wayarta cikin kuka ta fad'awa Anty Maryam halin da ake ciki.


Kwantar da Kansa yayi ajikin kujera ya Lumshe idonsa, yanda take qwala masa kira har yanzu muryarta takasa barin kunnansa, Ummah ta Kalle shi tace "kaje Kaci abinci kahuta"

Ajiyar zuciya yayi, sannan ya bud'e idonsa yatashi yanufi qofa
Ummah tace "Ina zakaje Kuma?"

Cikin damuwa yace "Zanje ayi bincike akan Yaron ne"

Sa'eed dake danne danne awaya yad'aga Kansa yace "Babban Yaya Dan Allah ka rabu da yarinyar Nan, kaje ka huta"

Wani irin kallo yayiwa Sa'eed ba tareda yace komai ba yafice daga falon, Ummah tayi ajiyar zuciya tareda miqewa, tana mamakin irin wannan shaquwa ta Naufal da Waheeda, tasan bazai iya barinta acan ba,haqiqa yana kula da qannansa yanda ya kamata, Albarka tashiga saka masa acikin zuciyarta, tasan cewa tayi sa'ar samun sa acikin a matsayin Babba, koda babu ransu, zai iya riqe qannansa sa.


Yana zuwa compound driver ya d'auke shi suka fita, saboda yagaji


Kai tsaye mtn office suka nufa, yasa aka rufe layin Nata, sannan sukaje police station sukai report,sannan yayiwa d.p.o magana akan abinda yake faruwa,d.p.o ya basu wani 'Dan sanda suka nufi banki dashi, acan banki ma Kai tsaye yanemi ganin manajan bankin, yayi sa'ah kuwa yana Nan, saide yana shirin fita ne, kasancewar sa sananne Sai kowa yake Kallan sa acikin bankin, suna qarasa wa office din manaja, yafad'a masa abinda yakawo shi, manaja yanemi account din da gayen yake turawa, sukayi bincike akan account din, anan aka Gano asalin sunansa, da sunan iyayensa dakuma sauran bayanai, Babban Yaya yayi masa godia sannan yasa driver yakai shi inda aka Kai Waheeda, suna zuwa aka basu wajan zama, d'aya daga cikin ma'aikatan yace "yalla6ai yarinyar Nan fa tunda mukazo take kuka, daqyar da lallashi muka samu tabamu amsar abinda mukeso"

Babban Yaya yace "Baku daketa bane, inda taji duka zata muku bayani ai"

Murmushi yayi yace "ai hakan ma mungode sosai wallahi, ta fad'a mana itama damfarar ta yayi, yanzu zaku iya tafiya,mukuma zamuci gaba da bincike, idan wani abun yataso, insha Allah zamuyi Maka waya"

Babban Yaya yabashi wata takarda yace "ga wannan, abinda na bincika ne Nima, nasan insha Allah Shima zai taimaka muku"

Cikin farinciki yad'ago kansa yana Kallan Babban Yaya Bayan yagama ganin bayanan dasuke jikin takardar yace "taimako kuwa, sosai da sosai, godia muke yalla6ai"

Kawai d'aga masa kai yayi batare da yace komai ba, Dan muguwar gajiya yakeji, bacci kawai yake buqata,gashi magrib har tayi

Wata matace dake Sanye da uniform din kaki, tazo tareda Waheeda, ta rissina ta gaida Babban Yaya Sannan tajuya, Babban Yaya bai kalli inda Waheeda take ba yayi wucewar sa gaba, driver ya Mara masa baya ๐Ÿคฃ

Gashi de shine Babban yayansu, Amma muddin tafiya ta had'ashi da'ita shine yake bude mata mota, tarasa dalili, Amma baya barinta tabude mota da kanta, yau kuwa yana zuwa yashiga baya ya zauna, yasa hannu yarufe motar, Waheeda ta tsaya tayi shiru tana ganin ikon Allah, wato in taga Dama ta6ude kofar ta da kanta kenan, yau ba mutunci, batayi gigin bude gefen dayake ba, tayi sauri ta zagaya daya gefen tabude tashiga, tana shiga wani Sanyi da qamshin turaren sa ya bugeta, tasa hannu tarufe motar, driver yaja suka tafi
Lumshe idonsa yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya, lokaci d'aya wata irin nutsuwa take shigarsa wadda baisan dalilin taba, Waheeda ta Kalle shi da jajayen idanuwanta, cikin sanyin murya wadda take nuna tayi laushi, ta zubar da makaman yaqinta tace "Sorry Babban Yaya...."

Yana jinta yayi shiru, hannunta dake rawa saboda tsoro ta 'Dora akan tsintsiyar hannun sa wadda take cike da gashi, cikin fishi yasa hannu yabige hannun ta yajuya mata baya yana Kallan window, lokaci d'aya ta rushe da wani irin Kuka
Driver ya d'aga murya yace "kiyi hakuri Waheeda, ba gashi kin futo ba, gaki ga yayanku, ai kuka yaqare"๐Ÿ˜ƒ

Waheeda tayi shiru tana goge hawaye, Amma kamar ruwa tana gogewa wanine yake sake sakkowa, har cikin ransa kukan ta yana ta6a ransa, Amma dole ne ya nuna mata kuskuren ta


Suna zuwa gida ma kafin a dedeta parking yafice daga motar yayi ciki,itama tafuto tana goge idonta tabi bayansa jiki a sanyaye, gaba d'ayansu family din na Arabo suna falon, daga kan iyayen har 'ya'yan, yana shiga qannansa suka fara yimasa sannu da zuwa daga mazan har matan, fuskar sa a d'aure yake amsa musu, yanemi waje ya zauna yana gaida su Hajiya Anty da Uncle Usman, saikuma Daddynsa, Waheeda tana shigo wa 'yanbiyu da Anty Maryam sukayi kanta suka rungume ta, cikin farin ciki suke fadin "Thank you Babban Yaya"

Saida suka saketa, sannan ta kalli kowa na falon, bata nufi kowa ba Sai hajiya Anty, tana zuwa ta fad'a jikinta tasaki wani irin kuka, Hajiya Anty ta rungume ta aqirjinta, tanajin soyaiyar yarinyar har cikin ranta, kasa bata hakuri tayi, Sai Bayan ta datake bubbugawa, Ummah ta Kalle shi tace "sannunku, ai jinake acan zata kwana"๐Ÿ˜…

Daddy yace "Nima abinda naso kenan, tunda bata jin magana"

Uncle Usman yayi murmushi baice komai ba, Ummah tajuya ta kalli Waheeda datake kuka a jikin Hajiya Anty tace "kitashi kije kisaka muku abinci keda yayanku"

Har zuwa lokacin fuskar sa a daure take, cikin sauri yace "A a Ummah tabarshi kawai"

Waheeda tanajin irin amsar daya bayar tasake riqe hajiya Anty tana fashewa da sabon kuka, Hajiya Anty tayi qasa da muryarta tace "sorry Baby na menene Kuma na kukan? Ba gashi kin dawo ba?"

Cikin kuka tace "To ai Babban Yayan yaqi ya huce"

Anty tayi murmushi tace "rabu dashi, anjima kije d'akinsa kibashi hakuri"

'Daga mata Kai tayi, sannan tatashi daga jikinta ta wuce d'akinsu domin watsa ruwa.

Sai a lokacin 'Yan falon suke fara'ah, kana Gani kasan akwai had'in Kai dakuma jituwa a tsakanin su, anan sukaci gaba da zama Bayan mazan sun iyo sallah sun dawo,'yanbiyu ne suka had'a abinci, suka kawo falon aka baje anacin abinci, uncle Usman ya kalli Sa'ad yace "Kai jeka kiramin yayanku a d'akinsa"


Sa'ad yaje yakira shi, yana Sanye da jallabiya fara qal, daga Gani kasan Sai mutum Ma'abocin tsafta ne zai saka ta, tsugunna wa yayi agaban iyayen nasa, uncle Usman yace "munyi waya da Yaya Habu, yanata tambayar ku, to tun kafin yafara korafi, yakamata ka shiryawa qannanka tafiya,suje suyi masa kwana biyu"

Wani irin farinciki ne yakama Babban Yaya, yaji dadi da Uncle Usman yace ya shirya wa qannansa tafiya,hakan yana nufin banda shi kenan, dama damuwar Waheeda duk ta isheshi, Gara su tattara sutafi subar masa gidan dagashi da ummah ๐Ÿ˜‡

Kafin yabada amsa
Daddy yace "Usman yakake cireshi daga ciki? Yashirya su tafi gaba d'aya kawai, Sai suyi sati d'aya,su huta saisu dawo"


Uncle Usman yace "ba aiki yake ba Yaya? Yaje qauye ya zauna har sati d'aya?"

Daddy yace "wanne irin aiki? Ai yayi retired, d'azu dayazo yace bazai sake komawa ba, saboda idan yakoma ma matsalar Waheeda zata dawo dashi, to idan ya zauna anan ma babu abinda zaiyi, Gara suje qauyen"

Uncle Usman yayi Daria yace "a a, suyi kwana biyar de, idan sukaga dangi saisu dawo"

Yana jin yanda suke tattaunawa yaji ransa ya6aci, baya son zuwa wajan baba Habu, saboda idan yaje ya dinga masa maganar aure kenan, shikuma ba auren yake soba, lallausar sumar Kansa ya shafa yace "zamuyi kwana biyu uncle, ya'isa, saboda aiki na" ๐Ÿ˜‚

Daddy yace "zaka koma aikin kenan"

Babban Yaya duk ransa babu dadi a taqaice yace "eh"

Ya tashi zai nufi d'akinsa, Ummah tace "bazakaci abincin ba? Kowa yana zaune shine zaka koma d'aki ka zauna kamar sabuwar amarya?"

Yace "Ummah na qoshi"

"kamarya ka qoshi? Ban fahimta ba? Kadawo daga wannan doguwar tafiyar kace bazakaci abinci ba? Yi hakuri Dawo ka zauna nabaka"

Yanbiyu suka had'a ido sukai murmushi, Daddy yace "a a, Usman kaji fa, ni banta6a ganin uwar da bata 6oye son d'anta nafarko ba sai Hajiya, qarara take nunawa Yaron Nan soyaiya"

Uncle Usman yayi murmushi yace "ya qwace wa Waheeda kujerar tane, ga auta,me za'ayi da tsohon tuzuru"

Babban Yaya yayi murmushi yace "Ummah Nasha madara, saida safenku"

Ummah Tajuya ta kalli hajiya Anty tace "kinga fishi yake, tun dazu nake masa maganar abinci yaqi ci"

Hajiya Anty takalli Waheeda,tuni Waheeda ta d'auki haske, tatashi tafara zuba abincin tace "Bari nakai masa Ummah"

Ummah tace "jeki Kai masa, idan yaqi ci kirabu dashi, shiyasan meyake damunsa Kuma"

Waheeda tadauki abincin ta nufi d'akinsa dashi

Gaba d'ayansu 'Yan falon Saida furucin Ummah ya basu dariya, Wai shiyasan meyake damunsa

Anty Maryam ta shirya zata tafi, Sa'eed ya d'auketa shida Sa'ad, zasu rakata gidanta


Waheeda na zuwa kofar d'akin nasa batama nemi izni ba tatura 'Dakin nasa tashiga, yana zaune agefen gadonsa abun duniya yataru yamasa yawa, ga zancen tafiyar su qauye gakuma 6acin ran Waheeda

Yanayin data ganshi aciki ne yasa tayi sauri tayi qasa da idonta, daga shi zai gajeran wando da alama bacci zaiyi, inde yayi wannan shigar Dama tasan bacci zaiyi, agaban sa ya ajiye abincin kanta aqasa tace "gashi Wai inji Ummah"

Tafad'i haka Sannan ta takure awaje d'aya kamar wata baquwa

Yace "ki d'auka kimaida mata, ai nace Nasha madara"

Muryarta ce tafara rawa tace "Dan Allah Kaci"

"kindamu dacin abinci nane? Inda bakya son damuwata ai bazaki dinga batamin rai ba, idan aure kike so saiki futo fili kifadamin aure kike so Sai Amiki"


Cikin sauri tace "Allah Bahaka bane, ni banason aure, Dan Allah kayi hakuri Kaci abincin"

"nafada miki bazanci ba, Ummah ce ta aikoki kikawo min, Kuma nariga nafada mata banajin yunwa"

Kanta aqasa tace "qarya fa nake, nice nakawo ma"

"to saiki koma dashi, bazanci ba"

Kukane yazo mata, ahankali hawaye ya silalo daga idanunta, cikin kuka tace "Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri kadena fishi Dani, wallahi bazan sake ba, kakawo paper da biro muyi dakai arubuce bazan sake 6atama raiba"

"ko gaban alqali mukaje bazaki daina halinki ba, kitashi kije kawai, rayuwa ce, ta'ishi kowa"

Tanajin wannan furucin nasa tasake fashewa da Kuka, da sauri ta nufeshi tad'ora kanta akan cinyarsa tana bashi hakuri cikin kuka

๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณZaro idonsa yayi, cikin sauri yahad'e qafafunsa waje d'aya, sannan ya janye kanta daga wajan,gudun karta sake aikata abinda tayi yanzun, ta6aro masa aiki, yasa cikin sauri yace "naji... Naji, Nina haqura, shikkenan komai ya wuce, Bani abincin"

Cikin sauri ta bashi abincin, sannan tace "kona baka Babban Yaya?"

Yace "a a, tashi kije, zanci da kaina"

Tashi tayi tsaye sannan tace "thank you" tafuto daga Dakin, shikuma yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya

Bata dad'e da futowa daga falon ba su hajiya Anty suka tafi, suna fita Maya tazo gidan, Bayan sun gaisa dasu Ummah, Waheeda tajata sukayi cikin d'aki, zama sukai akan gado Maya ta qarewa Waheeda kallo, tace "lalle Waheeda kinga rayuwa, 'yanbiyu suka cemin 'Yan sanda sun tafi dake bakiji yanda gabana yafadi ba"

Waheeda tayi ajiyar zuciya tace "Maya ai rayuwa Kam Ina kan ganinta, Babban Yaya nefa yace sutafi Dani" ๐Ÿฅบ

"ai Dama saida nace Miki ki dinga jin maganar sa" cewar Maya

Waheeda tace "to Maya mutum saiya zauna babu saurayi? Candy fa muke shirin yi, idan ya hanani kula samari shine zai aure ni?"

Maya tace "kika Sani"


Cikin masifa ta hayaiyaqowa Maya tace "kamarya nasani,? Me kike nufi? Koji kike agarin maguzawa muke?"

Maya ta dafata tace "maida wuqar qawata, ke kinsan da hakan meyasa zakice min idan bakiyi samari ba shizai aure ki?"

Tashi tayi tsaye ta nuna wa Maya qofa da hannunta, tace "tashi kifice daga 'Dakin Nan kafin namiki rashin mutuncin Dana saba Maya, nasan irin Zaman da zanyi dake wallahi"

'Yanbiyu ne suka shigo 'Dakin suka tarar da drama, Ihsan tace "kema de Maya da naci kike, Ana wulaqantaki kina liqewa, ai shikkenan"
Tana fad'ar haka tatada kabbarar sallah duk da ba tasan menene dalilin fad'an nasu ba

Intisar tace "Maya muje na rakaki hanya, mungode, Dakin Sani ma bakizo ba, Dan waheeda ba'a mata gwaninta, gobe ma qauye zamu tafi muyi kwana biyu"

Maya ta kalli Waheeda tayi murmushi tace "a dawo lafiya qawata" daga Nan suka futo daga 'Dakin, Waheeda kuwa ko uffan ba tace musu ba, tayaya ma Maya zata dinga had'ata da Babban Yaya? Yayanta uwa d'aya uba d'aya saikace wasu kafirai ba musulmai ba? Tsaki tasaki Bayan fitarsu tashige toilet domin d'auro alwala


Washe gari haka suka had'a kayansu, kowa ya shirya Amma banda Babban Yaya, yana d'akinsa yaqi futowa, kwata kwata baya son zuwa, Amma babu yanda ya'iya, haka yafuto suka had'u afalo, sukayi wa Ummah sallama

Suna zuwa compound yaja ya tsaya, jiyake kamar yafashe da Kuka, Sa'ad ya Kalle shi yace "Babban Yaya ya za'ayi ne?, Naga kamar mota d'aya tayi mana kadan"


Waheeda tayi zuruf tace "eh wallahi, aqaro mana wata, kowa yabaje son ransa" ๐Ÿ˜ƒ

Babban Yaya ya kalleta, sannan ya kalli Sa'ad yace "bawata mota daza'a qara, mushiga Prado din can kawai muje, babu driver acikin mu ai bare muyi kayan motoci"

Waheeda tayi qasa da kanta, cikin ranta tace wannan Dani yake, sukuwa yanbiyu dariya suka saka, ta Kalle su ta share su


Sa'ad ne zaiyi driving, Babban Yaya yana gefansa, Bayan motar Kuma Sa'eed da Yanbiyu da Waheeda suka shiga, kasancewar glass din motar baqi ne Sai sukai tafiyar su cikin salama babu Wanda yake ganin Babban Yaya bare masoyansa su tsayar dasu

Tafiya tayi tafiya yanmatan duk sunyi shiru kowa yana danna wayarsa banda Waheeda, โ˜น๏ธ
Saisu Babban Yaya dasuke fira shida yanbiyu maza, Waheeda taga kowa harkar sa yake ba'a Tata, ta kalli Babban Yaya tace "Bร bban Yaya yunwa nakeji"

Sa'eed yace "Ina abincin dakuka Dauko?"


Waheeda tace "wanne abinci? Ai bamu Dauko komai ba"

Babban Yaya yajuya ya Kalle su gaba daya yace "waiku wanne irin mashirmata ne? Ku baku iya komai na mata ba komai Sai ance kuyi? Babu irin shirin Nan da mata suke yi kamar su snaks? Saide kici babu kuwa" ya qarasa maganar yana hararar Waheeda

Cikin sauri tayi qasa da kanta, saida suka yi gaba sannan yaga wani yaro yana saida qwai, suka dakata yasauke glass din qasa kadan ya cewa Yaron "basu su juye subaka bucket din"

Waheeda ta leqo kanta tace "Bร bban Yaya nikam guda uku ma ya isheni, bazan iyacin sama da uku ba"


Cikin mamaki ya kalleta yace "Toda nawa zakici ya isheki inba ukun ba?"

Bakinta ta turo gaba tayi shiru, kowa saida ya Debi qwan yanda yakeso, sannan yabawa Yaron kudin da yafi karfin qwan gaba daya harna bucket din, sukaci gaba da tafiya, Waheeda ta 6are guda daya tad'an tashi kadan daga
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment