Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole ta yiwa zahran wannan tambayar,saboda uwa bai kamata a muhallin irin wannan da kike bincike da qwaqwwafi ba ki dinga boye wasu maganganun,wai don kawai kunya da nauyinsu,kan zahran a qasa tana fitar da qwalla tace
"Allah ya tsareni ummi,ubangiji ya tsare miki ni,kuma har abada bana fatan ya bani ikon ko damar da zata sanya nayi fatali da tarbiyyar da kuka gine ni a kanta,wallahi wallahi koda tunanin aikata hakan bai taba zuwa kaina ba bare na aikata ummi,ki yarda da 'yarki" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke
"Na yarda dake.....ba kuma wai ina zarginki bane,amma ya zama dole nayi aikina na uwa na bincika da kyau,na tabbatar addu'ar da kullum ba dare ba rana da nake miki keda 'yar uwarki dama sauran dukkan yaran dake gidan nan ba zata fadi qasa banza ba,na yarda jarabtace kamar yadda take rubuce a rayuwar kowanne musulmi.....kici gaba da addu'a,kada dimuwa ko zafin jarrabawa yasa ki kasa cin ribar haqurinki....karbi wannan" ta fada taba miqa mata wata doguwar takarda,addu'o'ine a rubuce a cikinta,addu'o'i ingantattu masu ma'ana,wanda suke dauke da kalmomi masu girma da tsarki gami da kambama ubangiji,wadanda su kadai sun isa sanya nutsuwa a zuciyar bawa da samun biyan buqata daga wajen ubangijin talikai.


Godiya ta yiwa ummin sannan ta baro sashen,tun a ranar sata soma addu'o'in ta dinga jin sukuni da nutsuwa yana ratsata,ta sake jin zuciyarta wasai kuma fes,haqiqa ubangiji yayi gaskiya da yace ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata suke samun nutsuwa,lallai babu abinda yakai ambaton ubangiji sanya nutsuwa a zuciyar mai damuwa.


Cikin satin ta hada kayanta ta koma bakin karatunta,tunda komai ya daidaita an koma makaranta,ta kuma fuskanci karatunta da kyau,ta watsar da duk wani damuwa da hayaniyar soyayya,babu wani da namiji da take tsaiwa ta kalla sau biyu ma bare ta saurari kalaman bakinsa,duk ta musu kudin goro gaba dayansu.


*_BAYAN WANI LOKACI_*


Zaune take cikin dakin kwanan dalibai wanda ya zama mallakinsu ita da hindatu batula da jannah,yayin da nadiya da farida suke daki daya daura da nasu suda wasu mutum biyun,to amma idan baka sani ba zaka zaci dukkansu daki guda suke,saboda kusan komai a nan dakinsu zahran sukeyi,hatta da abinci daya sukeyi,duk da basi fiya ma girma abinci ba,saidai suyo takeaway,idan kaga girkakken abinci to aikin zahra ne,sau tari sukan mata qorafin tana walahar da kanta da wani girki,ta bari kawai suyo takeaway suci,takan ce
"Ni ban saba bafa,abincin da zaka girka da kanka yafi albarka,sannan kayan anincin da nazo dasu daga gida saina jibgesu su lalace?,ko kuma na maidasu gida idan an tambayeni nace qawaye suna siya min ina ci?" To su dinma idan ta dafa kowa dafifi yake wajen ci,saboda ita din ba baya bace wajen iya girki.


Kamar yau dinma dakin nasu cike yake da hayaniyar 'yammata,kasancewar suna cikin ranakun qarshen mako ne,kuma wannan karon kusan dukkaninsu basuje gida weekend ba,ita zahra saboda CA da zasu fara,kuma a satin zasuyi kusan gudan hudu,shi yasa taga gwara ta zauna waje guda tayi karatu sosai.



Yau dinma ita ta dafa musu abincin,kowa yaci ya qoshi,da suka kammala saita taja takardunta da system dinta saman gadonta ta barsu nan tsakar dakin kan carfet din da suka malale dakin dashi
"Yar allazi boko" taji su suna tsokanarta,bata kulasu ba sai murmushi kawai datayi taci gaba da karatunta,batason ta tsaya tankasu su dauke mata hankalinta,suma sukanyi karatun,amma saidai baiko kai nata ba,sukance sun gaji basu iyawa,da sun taba iya yadda zasu iya suke ajewa su shiga sabgarsu.


Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
"Ferry....zoki gani....maza maza zo kiga" da sauri farida ta aje tata wayar ta matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
"What.....muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic dinta,kan bala'i" saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status dinta
"Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa" dariya wata rabi'ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
"Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da basu amanna dari bisa dari.....everybody listen to me" ta fada tana gyara zamanta sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi'ah din ta soma fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na kanta
"Luggar mazan yanzu.....zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp....kuma zasu iya dora hotonta a status...amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki kuma qara amanna dasu...so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu ta haka,kada ku saurara kunji....kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na dauka ku dauka ku watsar dasu" ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.


Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.


Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba sune suka sake dawowa ba,basu din bane yanzun jannah ce,sanye da straight gown da hill shoes,sai qaramar hand bag da qaramin mayafi data nade wuyanta dashi,kusan shigarta kenan wanda kusan kullum sai sunyi rigima da zahra akan haka.


Yau din fuskarta sam babu alamun walwala,gefan gadonta ta samu ta zube tana zare mayafin kanta cikin masifa take magana
"Ni hisham zaiwa haka?,ni zaiwa wannan akuyancin?" Hindatu dake kwance bacci ya fara dibarta ta daga kai tana dubanta
"Ke kuma meya hadaki da hisham din naki yau?" Iska ta furzar daga bakinta sannan ta zame 'yar hular dake kanta ta sabule takalminta ta zauna sosai saman gadon tana harde hannayenta
"Yau ni hisham zai fito qarara yacemin nayi haquri da maganar aurenmu....shi matarsa ta gida ta isheshi" sosai hindatun ta tashi ta zauna
"Hisham din da kansa da bakinsa?" Kai ta jinjina cikin tsananin jin zafi
"Shi din fa....shi yasa ya kasa zuwa ya gaida dad,ko mami ma danace yaje cewa yayi wasu shirye shirye yakeson ya kammala tukunna...."dauke kanta hindatu tayi zuwa sashen da zahra ke zaune
"Kinji fa zahra?" Saita ture littafinta gefe
"Naji" ta fada tana saukowa daga saman gadonta,ta daura dankwali sannan ta fita zuwa toilet,mintina kadan ta dawo ta samesu suna tattaunawa,ta koma bakin gadonta ta zauna sannan ta dubi jannah.


"A inda kullum muke fada dake kenan fadan gaskiya....ita kuma gaskiya daci gareta,hakanan fure take bata 'ya'ya,ita kuma rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka girba,ba zaka taba shuka qaya ba kace inibi kakeson cira,jannah.....na dade ina miki nuni da waye hisham,illa da dafin dake tattare dashi,hisham yayi amfani da son da kike masa yayi fooling naki,ya kuma yi amfani da damarsa a kanki,a yanzu ya gaji dake ne shi yasa ya fito miki ta wannan hanyar kai tsaye,don ya ajjiyeki ya kuma lalubi wata mai tsautsayin me qaramin tunanin....kiyi haquri da harsh word da nake amfani dasu a kanki,kawai ni duk inda gaskiya irin wannan tazo gittawa ta gabana saina fadeta,abinda yasa na kira dame qaramin tunani shine....babu ta yadda wanda yakeson ya aureki ki zame masa uwar yaransa kuma mace ta gari abar alfahari ya daukeki cikin motarsa yana yawo dake,ya daukeki ba cikin gidanku ba,ba gaban iyayenki ba,ku hadu a wani waje ya saki gaban mota kuna yawo,yaje ya killace 'yarsa,yaje ya killace matarsa,yaje ya killace mamarsa....amma kefa?,saboda baki da wani daraja,baki da wani matsayi da za'a baki,shi yasa bai dauki hakan a bakin komai ba,daga sanda wanda yace miki yana son aurenki yazo miki da magana kan matarsa qazama ce,matarsa bata iya soyayya ba,matarsa yar qauye ce,kece kika iya komai,matarsa ta gaza ta kowanne fanni,amma kuma ko yaushe yana nanuqe dake,yana fasa miki kai,ta wani sashen kuma a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri"sosai taga yadda jikinta yayi masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita kadai ba har hindatu dake kwance.

********** ******** ********

*_ƘADDARA....ta riga fata_*



Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi hotel don su huta a can a cewarsu.


Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.


Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
"Amini....ko sau daya baki taba karar binmu bafa" kallonta tayi
"Ko sha'awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen kamar ba'a bakin komai ba zuwanshi" dariya sosai hindatu tayi
"Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa'ida wajene da iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga hayaniyar gida data jama'a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak" kai zahran ta girgiza
"Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo" ranta ta bata da alamun bataji dadi ba
"Shikenan....tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake....na gode,dama sunatamin dariyar cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan" saita sauka daga gefan gadon ta koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.


Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa zata fita zahran ta kira sunanta
"Haushi kikaji kenan?" Kafada ta daga
"Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya ba" kaita kada tana murmushi
"Zanje....shikenan ko?" Cikin murna ta dawo
"Na gode sosai....ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da kanki zaki ce muje" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
23/10/2021, 08:41 - 👍🏻👍🏻: 17

*KIJI TSORON ALLAH ☝🏾☝🏾☝🏾,karki taba kayan da ba naki ba ba kuma mallakinki bane*



Ƙarfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu hindatun suka tafi.


Ɗaya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta ankara da haka
"Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya isa ya shigo" murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.


Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
"Zahra....ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa" kaita kada tana hamma
"Kai a'ah,sai an idar da sallah" daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya debeta.


Sanda ta farka hindatu ce kawai tayi saura a dakin,tana niyyar saukowa daga gadon tana duba agogo,qarfe bakwai da ashirin na dare,inda Allah ya taimaketa tana hutun sallah
"Duka ina suka shiga?" Ta jefawa hindatun tambayar wadda ke tsaye gaban madubi tana gyara sumarta da mayukan gyaran kai
"Duk sun fice,amma sun kusa dawowa"
"Fita kuma?,nan duka bai ishesu yawo ba?" Ta sake tambayar hindatun
"Nan kusa da inda muke nefa,aka bude wani sabon wajen cin abinci daxun,to na wani abokin farida ne,shine ya gayyacesu" baki kawai ta tabe,ba shakka duk inda wayewa tayi yawa matsala ce,su a wajensun wannan normal ne,ba wani abu bane,amma a asalin tarbiyyar malam bahaushe wannan din mummunar illa ce,saita miqe ta shiga toilet ta canza pad ta kuma daura alwala ta dawo ta zauna bakin gadon tana karanto azkar dinta na maraice da bata samu damar karantowa ba,tana yi tana duban hindatu daketa shiri da alama fita zatayi,batace mata komai ba har sai data ga ta daga waya tayi magana na 'yan mintuna ta aje,ta dauki mayafinta tana yafawa
"Ina kuma zaki kema?" Waiwaya tayi tana duban zahran
"Waya zamuje siya nida mudassir a glass show,minti talatin ta isa munje mun dawo" sosai zahran ta hade fuska
"Yanzu kina ganin kamata ce ki fita da saurayi takwas saura na dare siyan waya?,cikin motarsa daga ke saishi?"
"Babu komai qawata kada ki damu,ko a gida dana sanarwa mommy muke tafiya" maganar ta ratsata,batasan illar boko xallah ba sai yanxu,gaba daya duk wani abu daya kamata a kalleshi amatsayin abun qyama suba hakan bane a wajensu saboda rashin tasirin ilimin addini,saita miqe ta isa inda hindatun ke tsaye.


"Hindatu,a koda yaushe inason ki dinga tuna cewa kina rayuwa ne a qasar hausa,ina son ki dinga tuna cewa qa'ida da kwaikwayo kan tafarkin addini shine gaba da komai,na miki uzurin rashin tashi kan irin nawa bigiren,wala'alla har a zuciyarki ba komai bane hakan,amma idan baki sani ba bari na gaya miki illar.....akwai babbar illa a wajen 'ya mace ko ince ganganci wajen shiga motar wani da namiji,nasha maimaita miki wannan maganar....abinda yasa na nace mata shine,shiga motar da namiji ki yadda ya tuqaki shine mafarin komai,shine sila da dalili na faruwar komai,komai zai iya faruwa,idan nace komai ciki harda rasa budurcinki gaba daya....." Idanu hindatun ta qwalalo
"Ki yarda dani qawa.....wallahi ban taba zina ba,ban taba bada kaina ba" murmushi zahra tayi ta dafa kafadarta
"Haba hindatu....ta yaya zan miki wannan mummunan qazafin,amma idan kin kubuta daga zargina sauran mutane fa,kin isa ki wanke kanki?,akwai abubuwan da zaka dinga aikatawa da zasu iya ja maka mummunan zargi da zato daga mutane,zargi mai wuyar wanke kai,irin wannan rayuwar,ku kunsan bakwa wani mummunan aikin,amma shaidar da mutane zasu muku itace ku bana gari bane,idan kin shiga motarsa komai bai faru ba zaki iya kubuta daga riqe miki hannu da zaiyi?,zaki iya kare kanki daga yunqurin miki kiss ko runguma?,idan yaso cutar dake kin isa ki bawa kanki kariya?,sannan kome ya miki baki da hujja,laifinki ne,ke kika kai kanki hindatu" sosai jikinta yayi sanyi,ta daga kai tana duban zahran
"Gaskiya kika gayamin qawata,na kuma fahimta maganarki,sannan na gode miki qwarai da gaske,ban dauki hakan a wata babbar tawaya ba sai da kika nusashsheni,in sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba" ta qarashe maganar tana cire mayafinta,sannan ta dauki wayarta ta tura masa tex ta koma ta zauna.


Daya daga cikin halayen hindatun da suke burge zahra kenan,sauqin kai da kuma saurin daukan shawara.


Tana zama saiga sauran suna shigowa,kafin kace me sun sake hautsina dakin
"Kai....kai jama'a,ku bakwa gajiya dan Allah da hayaniya?" Inji zahra da suka hana kunnuwanta sakat,dariya suka saka gaba daya jannah tace
"Kamar yadda baki gajiya da karatu ba" saita saki murmushi kawai tana gyada kai,tasan me hali dai bazai fasa halinsa ba.


***** ***** ****** *****


Washegari a daki dukka suka yini a tare,saidai da yammaci lis suka shirya dukkansu domin zuwa siyayyan kayayyakin amfani da kuma kallon wani sabon hausa film da za'a haska a film house cinema dake ado bayero mall.


Fir tace ba zata bisu ba,hakanan idan suka jima basu dawo ba saidai suzo suga ta tafi,basu ji dadi ba,saboda sunce ba jimawa zasuyi ba,hakanan bai kyautu su barta ita kadai ba,amma tace sam itadai sai sun dawo,hasalima akwai sauran karatunta da bata qarashe ba,haka suka shirya suke fice a motar jannah.


Karatunta taci gaba dayi,lokaci lokaci tana kallon tv dake aiki,saidai ba'a jima ba taji zaman ya gundireta,shuru hakanan babu kowa ba motsin kowa,don haka ta aje littafin tana duba agogo,dab ake da kiran sallar magariba,koda ta fita bata da matsala,tunda tana fashin sallah,don haka ta dauki mayafin doguwar rigarta ta yane kanta,sannan ta zira plate din takalminta daya dace da kayan jikinta,ta buda dakin ta fito.


A sama suke,saidai akwai qawatacciya kuma doguwar baranda ta bayan dakunan wadda zaka iya hangen farfajiyar hotel din idan ka tsaya ta jikinta,hakanan wanda yake qasa shima zai iya ganinka idan kaso,anan din ta tsaya,tana kallon yadda mutane ke kai kawo cikin hotel din kowa na sabgar gabansa,wanda yawanci duk wanda zai shigo ko ya fita cikin mota yake,da kadan da kadan take kallon wajen tana kuma karantar wasu abubuwa masu tarin yawa.


A qalla ta shafe kusan minti ashirin tsaye a haka har duhu yadan fara yi sannan taji tsaiwar ta soma isarta,saita janye idanunta da niyyar juyawa tabar wajen,saidai caraf idanun nata suka fada kansa.


Matashin saurayine fari sol,ma'abocin tsaho hakanan baida jiki,mai yalwar baqar sumar kai da kuma qasumba,sanyw da qananun kaya yana kuma tsaye jikin motarsa idanunsa fes bisa kanta,tsaki taja mai qarfi data lura da irin kallon qurilla da yake mata,ranta yana quna,tana fadi a ranta,wama yasan adadin lokacin da ya shafe yana kallonta bata sani ba.


Koda ta koma daki bandaki ta shiga ta sauya audugar jikinta,sannan ta dawo ta fesawa hannuwanta da jikinta turare ta koma kan karatunta,tanayi tana duba lokaci,saidai har yanzu babu su hindatun babu alamarsu,ranta ya soma baci,ta soma jin haushin kanta kan me yasa ta biyosu?,bayan gaba daya tsarin rayuwarsu ma ba daya bane?,yanzu meye amfanin zamanta a nan?,saita dauki wayarta ta soma kira.


Saidai duk wadda ta kira din tana shiga tana kuma ringing amma ba'a dagawa,babu kuma amsa,haka ta qaraci kiransu gaba dayansu babu wanda ya daga,zuwa sannan tara da rabi na dare agogo ke nuna mata,ga yunwa tana ji,duk da sun gaya mata taje tayi order din abinci a reception idan tana da buqata kowanne iri ne,to batason fita shi yasa bata karbo ba,ga wayar dakinsun daxu ta samu matsala bare ta kira daga daki a kawo mata,zuwa yanzu kuma yunwa takeji bata wasa ba,hakan yasa ya zame mata tilas ta fita ta karbo din kenan,saita sake tashi ta gyara yafenta ta kuma fito daga dakin.


Cikin tuqi mai cike da nutsuwa ya sako kai farfajiyar hotel din,hannunsa daya yana tuqin dashi,yayin da daya hannun yake amsa wayar cikin nuna girmamawa ga ubangidansa da gazo gani cikin hotel din,wanda ganawa ce ta sirri da zasuyi dashi gabanin taron qasa sa za'a gabatar na dukka ma'aikatan tsaro na qasa,kama daga sojojin sama dana qasa dana ruwa gaba daya,yanzun yana amsar direction ne na daki da inda zai ganshi,har ya qaraso wurin ajiyar motoci sannan ya ida wayar yana mai cewa
"Yes sir!" Sannan ya sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta gaba daya,ya janyo aljihun motar ya zurata,sannan ya zauna na wasu mintuna yana karantar yanayin wajen a matsayinsa na qwararren jami'in tsaro,sai daya tabbatar komai na wajen yayi masa sannan ya bude murfin motar ya fito.


Duk wanda ya kalleshi saiya kuma,duk da cewa babu wata alama da zata nuna maka yanayin aikinsa,amma shigar da yayi da wasu shegun qananun kaya masu kyau da aji sun amsheshi,takawa yake zuwa reception cikin wata tafiya me cike da kuzari mazantaka da kuma karsashi,hannunsa daya riqe da key din motarsa,daya hannun kuma wata 'yar mitsitsiyar waya ce da yake iya rumtseta a tafin hannunsa guda daya.


Yana magana da daya daga cikin receptionist din sanda ta qarasa saukowa,a nutse itama ta tsaya saitin daya ma'aikacin wajen tana gaya masa abinda ya sauko da ita.


Cak ya tsaya da maganar da yakeyi,a hankali ya juya kanshi zuwa sashen da yakejin muryar na fitowa,daidai sanda itama qamshin turaren da take tsammanin ta sanshi,a kuma cikin gidansu ya soma shiga hancinta,har kuma yaja hankalinta zuwa ga kallon gefanta.


Ido hudu sukayi,cikin matuqar tsoro da razani taja baya tana kallon cikin idanunsa,yayin da shima ya kafeta da idanun yana mata wani kallo daya sanya taji kamar an maida qafafunta sama ne kanta kuma a qasa,tashin hankali da gigita suka bayyana tun daga zuciyarta zuwa saman fuskarta.


*_kuyi manage don Allah,yau nayi busy_*
23/10/2021, 08:41 - 👍🏻👍🏻: 18
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
_______________________________



Da wani irin zafi ya soma takawa inda take tsayen,tamkar ma ya manta da cewa gap din dake tsakaninsu ba wani me yawa bane,itama sai tayi yunqurin ja da baya,wanda hakan yasa yakai mata cafka da zafinsa,ya samu nasarar riqe singalalin hannunta,abinda ya sake rudata kenan ta sake daburcewa,tsoro ya kuma cikata,yayin daya bude baki cikin wata tsawa
"Me ya kawoki nan!" Ya

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment