Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taga ya tsaya qofar wani babban kanti,wanda ya hada komai da komai,kusan komai.na buqatar yau da kullum da amfanin rayuwa suna saidashi
"Wait" kawai yace yana cre set belt din jikinsa ya bude motar ya fita ya nufi shagon,saita bi bayansa da kallo,yana yin yadda yake taku cike da nutsuwa qasaita da ginshira,sai daya shige sannan ta dauke idanunta a hankali tana sauke ajiyar zuciya,yaushe ya haidar ya sauya?,yaushe yayi laushi,to amma ita game da yadda yake mu'amalarsa da yaran gidansu bataga sauyi ba,donko ranar suna sai daya yiwa su salma fata fata kan sunkai dare,kuma mazansu sunzo daukarsu kowacce ta shanya mijinta,har kusan kuka sukayi.


Babu jimawa taji an bude set din baya,shine riqe da babbar leda ya sakata a bayan motar ya rufe,sannan ya dawo set dinsa ya shiga ya sake tada motar.


Basuyi nisa sosai saman titi ba taji ya sanya casset na karatun dr malam umar sani fage,kamar yasan xabinta kenan cikin dukka malamai,babu malamin da take bin karatunsa qafa da qafa kamarsa,take kuma nutsuwa da dukka fatawoyinsa kamar shi,zallar hikima da dora bawa bisa hanya,da doron shari'a hanyar da zaka samu lahira irin malamin,batajin a wannan qarnin akwai malami kamarsa,zaiyi wuya,duk da ba'a rasa bayin Allah,wadanda suke lunguna da saqon qasa da garinmu,kuma Allah baiyi ambatonsu ya bayyana ba a bakunan bayinsa,amma shi yasan da zaman kayansa.


Wannan karatun shiya jagorancesu,ya kuma rakasu har cikin makarantar.


Suna shiga ya rage gudu,ya dinga gangarawa a hankali har yakai iyakar inda motoci ke tsaiwa daga nan babu qari,ya kashe motar sannan yana qoqarin bude murfin motar yace mata
"Dawo set din baya" saiya fita,bude murfin tayi kamar yadda ya umarcetan.


Yana tsaye a wajen motar hannunsa a qirji yace mata
"Ki duba kayan idan sun miki,an siyo su late.....but remember,nidin bamai kudi bane" ya fada carelessly kamar ma bashi yayi maganar ba.


Ledar kawai ta buda ta rufe tace
"An gode,Allah ya saka da alkhairi" saita fito.


Yana tsaye jikin set din data zauna dazun,kuma tabar jakarta a wajen tana da buqatar dauka,murya qasa qasa sanda take tsaye a gabanshi nesa kadan dashi tana facing dinsa tace
"Jakata" saiya dauke idonsa daya tsareta dasu,ya bude motar ya dauko jakar,kudi ya ciro dubu ashirin daga aljihunsa ya bude jakar ya sanya mata yana cewa
"Ki riqe wannan saboda koda wata buqatar zata taso....zanyi tafiya ne,koda zasu yanke miki kafin na dawo,karki tambayi kowa,kiyi gayawa mustapha,zaiyi handling komai" saiya miqa mata jakar,ta sanya hannu zata ansa,sai daya tabbatar ta riqe saiya janye jakar,ta bada amannarta gaba daya,hakanan bata zata ba,don haka ta biyo jakar talau,sai gata taja birki a gabansa,dab dashi,don taqi kadanne tazarar dake tsakaninsu.


Qas tayi da kanta saboda kallon da taga yana mata,ta kuma kasa janyewa,saboda ko yaya ta motsa jikkunansu zasu hadu.


Jakar ya sake miqa mata,ta miqa hannu a sanyaye karo na biyu zata karba,sai yasa daya hannun masa caraf ya damqe tsintsiyar hannunta,a tausashe ya jata ya jinginata da jikin motar,a maimakon dazun da shine ke tsaye jikin motar,sannan a tausashe ya sanya qafarsa tsakanin nata qafafun,ya kuma dafe gwiwar hannunsa saman motar dab da kafadarta,idan daga nesa ka hangesu zakayi tunanin tana rungume cikin jikinsa saboda kusanci,kusancin da jikinta da zuciyarta suka kasa dauka,saboda duk wani fitar numfashinsa tana jin saukarsa saman fuskarta,hakanan qamshin turarensa daya danne nata,uwa uba idanunsa masu kaifi da suka sake yi mata nauyi,sai tayi hanzarin yin gefe da kanta,wanda kafin sakan daya yasa yatsun hannunsa ya kamo habarta,ya maido da fuskartata saitin tashi.


Bai barta ba sai daya lalubo qwayar idanunta ya saka tashi a ciki,cikin wani irin sauti dake fita da qyar,can qasa kamar wanda bacci yaci qarfi ya soma magana
"Zanyi tafiya me nisa.....waje mai hadari,zan iya dawowa,zan iya salwanta a can,duk da bai cikin aikina.....amma zan shiga da kaina saboda na sake sadaukarwa da qasata ruhina,inason in samawa wadanda suke cikin qunci salama da nutsuwar ruhi.....pls forgive me if i hurt you a tarayyarmu"wani irin rauni taji ya mamayeta irin wanda bata taba ji ba,saita daga idanunta da cikin qaramin lokaci suka hada qwalla taf ta dubeshi,bata wani abu mai nauyi na sauka saman zuciyarta cakude da wani yanayi da batasan wanne iri bane,idan kuma ya mutu fa a can kamar yadda yace zai iya salwanta?,wani sashe na zuciyarta ya raya mata,rayawar daya sanya qwallar data tara ta subuce mata,ta gangaro saman kuncinta zuwa habarta
"Oh....no,bafa kuka nace ba,banason kuka ko kadan" yatsunsa ya sanya guda biyu ya dinga dauke mata qwallar,sai daya gogesu tas,maimakon ya daukesu saiya zarto dasu saman qirjinta,tun daga wuyanta zuwa qasa ya fara mata tafiyar tsutsa dasu,ya kuma sanya idanunsa cikin nata,take jikinta ya dauki rawa
"Am gonna miss my......" Shuru yayi bai qarasa ba yana ci gaba da kallonta,cikin qarfin hali ta sanya lallausan hannunta tayi caraf ta riqe hannun nasa tana girgiza masa kai,murmushi ya saka yana sauke hannuwan nasa,sannan yace
"Matsoraciya......" Saiya saka tattausan labbansa a hankali,yayi kissing nata softly da wani irin sanyi saman labban nasa da suka ratsa har kwanyarta ya sakata lumshe ido,tana jin wani feeling na cika zuciyarta,wani yanayi na farinciki yana cikata kamar ana yawo da ita a duniyar gajimare.


A hankali take tafiya,duk da ta bashi baya amma tana jin tsaiwarsa a wajen cikin jikinta,saidai batasan meye ya tsaidashin ba,kafin wani lokaci kafin takai ga bacewa a wajen taji tashin motar tasa a hankali,saita dinga jin wani abu me kama da kewa yanason kamata,inda tayi qarfin hali ta tattara duk wani jarumtata tayi tayi fatali da wannan batun,ta kuma qaryata kanta da kanta.
23/10/2021, 08:48 - 👍🏻👍🏻: 38


Wani mugun shewa taji sanda ta shiga dakin kwanansu,dama tun cikin aji ta fuskanci suna gulmarta da ido,don dai da malami a ajin,babu damar suyi mata magana ne.


Da ido ta bisu ganin yadda suketa mata dariya
"Dalla malamai,banason iskanci,meye abun dariya a jikina?,koni mahaukaciya ce?" Sai sannan hindatu tace
"Mahaukaciya tuburan kuwa......ah,ya haidar din da bashi da mutunci,ya zakin da babu ruwanki dashi,aka hanani neman soyayyar dan bawan Allahn nan,ash kinsan cewa qarshe ne shi a soyayya,ya gama haduwa tako ina,sai gashi ya kasheki da soyayya agun ajiyar motoci,har jama'a suka wuceku ma baki sani ba...nidai gaskiya qawa kinmin yankan baya ba kadan ba" ta fada tana hade fuska,janna tace
"Nifa banga laifinta ba,tsakani da Allah fa,waje zaiga guy irin wannan yana da dama ya bari ya wuceshi,wallahi ko nice sai inda maina ya qaremin,idan kuwa ina zaune yazo ya taya,ai babu wani kwane kwane zanyi wuff da abina".


Babi babi na tsiya suka bude suka dinga yi mata,ita dai ci kanku bata ce musu ba,hakanan ta samu kanta da kasa tanka musu,sai data tafi bandaki sannan suka saurara mata,data dawo kuma aka shiga hirar yaushe gamo,nan ma sai da suka tsokaneta
"Daga yanzu zanje na dawo qawa kuma sai mukaji dif" tsaki taja tana nade abun sallarta
"Wallahi hajja ce,ashe ta timer min" dariya duka suka saka,janna tace
"Allah dai ya biya hajja,wallahi ta kyauta min" harara ta jefa mata,hindatu ta cafke
"Ta taimakeki kuwa,don bakiga kyan da kika qara ba,Allah yasa anyi me gaba daya" ta fada suna tafawa,dadai ta fuskanci iskanci da tsiya suka tanadar mata buhu buhu,saita miqe tabar musu dakin,saidai zancan hindatu ya tuna mata da abinda ya faru a wancan ranar,ranar da yaso yayi mai gaba daya din,sai wani qaramin murmushi ya sube mata,ita kadai taja hijabinta zuwa qasan hancinta tana jin kunyar kanta da kanta.


Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan suka rage musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga qafa ba,ta bada himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci tunaninsa yakan fado mata a rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo kwanciya bacci shine abu na qarshe da zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja sai tayi bitarsa,ranar da zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.


Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.


Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake nesa da ita.


Sannu a hankali ta tabbatarwa da kanta damuwa ce,damuwa ce ta rashin ganinsa ko rashin jin muryarsa na tsahon tagwayen sati,har ana neman shiga sati na uku,hatta a gida hajja ta fara qorafin shuru haidar,bai kira ba,koda an kira ba'a samunsa,to Allah yasa dai lafiya,addu'ar data sanya gaban zahran mugun faduwa,saboda tuna maganar daya gaya mata
_"zanyi tafiya me nisa.....waje me hadari,zan iya dawowa....zan iya salwanta a can.....ki yafemin idan na saba miki a tarayyarmu"_,kawai sai taji kuka ya subuce mata,ta danneshi har sai data kai daki sannan ta sakeshi.


Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da gyararraki ba.


Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad S A W wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai kammala dai daita.


Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu sunata shiri.


Tun sanda ta dawo daga abuja ta lura da wani abu,dabi'un su hindatun su canza gaba daya,abubuwa da yawa sun daina yinsu yanayin shigarsu ya canza sosai,wanda hakan ya bata mamaki,saidai bata taba tambayarsu ba.


Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta zauna gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa
23/10/2021, 08:49 - 👍🏻👍🏻: 39


Da yammacine liqis,tana zaune a falon hajjanta,gidan yau kusan shuru yake saboda dukka yaran gidan suna islamiyya,saura kuma kowa yana wajen sabgarsa ta yau da kullum,kamar sassan nasu yau su biyu ne daga ita sai hajjan.


Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana jin dadin xaman sosai.


Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta dashi a tata wayar
"Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa'a gaya mata" shuru taji anyi,duk da cewa da alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
"Hello....ance hajjan bata kusa,idan ta fito za'a gaya mata" jin still dai an sake yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.


Tana shirin shiga wani grp nasu na 'yan makarantar kachako unity girls,group ne na 'yan set dinsu da suka gama makaranta a shekarar,saiga saqo daga saman watsapp dinta ya shigo da baquwar number,bata fasa shiga grp din ba,sai data shiga ta gama uzurinta ta fito sannan ta duba saqon,saqone da bai wuce layi daya ba,amma saiya tsaya mata a rai,ta dinga nanatashi ita kadai
*_KINYI NESA DA IDANUNA DA RAYUWATA,AMMA KINA KUSA DA RUHI DA ZUCIYATA_*

sake shiga profile din tayi ko zata ga suna,babu suna babu dp,ta bincike contact dinta tsaf babu me irin number,zargin da yazo kanta yasa tayi saurin daukar wayar hajja ta bude,ta loda numbers din ta danna dial ko zataga suna ya fito a number amma babu,tabbacin zarginta ba haka yake ba kenan,ba haidar bane,to waye?.


Jin takun tahowar hajjan yasa ta maida mata wayar ta ajjiye,don ta lura yanzu wani gani gani take mata akan wayarta,saidai ta ganta hajjan
"Me akemin da waya ne?,bana son fa satar lamba ahto....idan mutum naso yayimin magana da kaina na dauka na bashi" shuru zahra ta mata,sai da taga ba zatayi shuru ba sannan tace
"Ni ai duka wayarki hajja babu lambar da xan sata fa,babu,ni kawai ko bandakin zaki shiga ki dinga shiga da abarki ma huta" baki ta tabe
"Oho dai,banda rashin gaskiya daga jin tahowata sai a maida waya da sauri a aje,kinga kuwa ai babu gaskiya ne" ta qarasa maganar tana zama,sai kawai zahran tayi kwanciyarta ba tare data sake amsa mata ba,tana ci gaba da maimaita saqon,jikinta yana bata daga inda saqon ya fito,amma zuciyarta ta gaza gasgata hakan,har sai data gaji da kallon saqon,kamar shi xai bata amsar tambayarta,ta sauka daga watsapp dinma gaba daya,saita dora wayar saman qirjinta ta lumshe idanunta tana tuna wasu abubuwa da suka zame mata farilla kullum sai tayi bitarsu a kwanyarta,haka nan tunasu suke sanyata nishadi suke kuma debe mata kewa.


****** ****** *******

*_BAYAN WASU KWANAKI_*


Yamma ce lis,wanda tun safiyar ranar ake fama da hadowar hadari da kuma washewarsa,saidai zuwa yammacin hadarin ya hadu sosai a sama,yana bada iska mai sanyi hadi da qamshin qasa,wanda hakan ke alamta cewa ruwan sama na tafe kowanne lokaci daga sannan


Ita da umaima da ilham ne a falon hajjan,ilham na mata manyan kitso a kanta saboda wankeshi da tayi,ya kuma isheta hakanan babu kitso,tana mata kitson suna hira jefi jefi,suna kuma kallon tashar arewa 24,gidan yauma babu mutane sosai,duk sun tafi sunan faccalar hafsat data haihu,da yake macace me kirki,kusan kowa ya santa a gidan,sauran yaran kuwa kowa yana makaranta.


Suna daga zaune suka jiyo qarar shigowar mota harabar gidan,ilham ta kalli umaima
"Kai....yau wani cikinsu abba ya dawo gida da wuri,mun shigesu yau munyi fashin makaranta....wallahi mu nema wajen buya" harara zahra ta aike musu tana cewa
"Ko kun buya saina gaya musu,ba yadda banyi daku ba ai kuka qi ji,haka ma hajja,gwara ma ku xauna suxo su ganku yafi muku sauqi" tana rufe baki hancinta ya soma shaqar mata qamshinsa,saita saki ajiyar zuciya,tana mamakin yadda ta damu da lamarinsa haka da yawa,tasan cewa ba shi din bane,kawai kamar ta saka lamarin a ranta ne da yawa shi yasa take jin hakan,don haka tayi shuru tana duban bakin qofar dakin hajja tana kallon yadda iska ke daga labulen falon.


Kamar a mafarki taga tsaiwar mutum bakin qofar falon,gabanta yayi wani faduwa data jima bataji irinta ba,ta daga kanta a hankali daga kan takalman da idanunta ke iya gani zuwa sama fuskar mutumin dake tsaye.


Haidar ne,cikin unifoarm na sojoji da suka bayyana zallar kwarjini da kamalarshi,cikakken unifoarm ne a jikinsa,saidai babu hula a a kanshi,kamar yadda ta lura ba kasafai ya fiya son sanya hular ba.


Idanunsu ne suka sarqe cikin na juna,kowannensu ya shiga kallon dan uwanshi,zuciyoyinsu na wani irin rawa tamkar an kusanta mayen qarfe da qarfe,a hankali ya soma takowa cikin falon,idanunsa cikin nata,wani irin abu mai qarfi yana jansa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,tamkar me sanda haka yaci gaba da takowar har ya iso dab da su
"Ya haidar sannu da xuwa" muryoyin ilham da umaima suka karade kunnuwansu,saiya cira idanuwansa a hankali zuwa kan yaran,sam baigansu ba,bai kula dasu cikin falon ba sai yanzu,saiya gyada kai,muryarsa da wani irin laushi ya amsa da
"Yauwa,sannunku" ya qarashe zancan idanunsa na sauka kan lallausan gashin zahran da ilham takai kitso na qarshe ta kalmashe mata jelar,a hankali cikin wani irin sanyi da laushi zahran ta miqa hannu ta jawo dan kwalinta daya zame tunda aka fara kitson ta lullube kan nata,idanunta har yanzu suna qasa,ta gaza sake hado ido dashi,sai zuciyarta dake wani irin bugu,duk sai suka miqe,ilham ta dauke man kitson da comb suka nufi qofa ita da umaiman.


Kansu gama ficewa hajja ta fito,tayi turus cikin mamaki tana dubansa
"Kai kuma yaushe ka shigo?" Fuskarta na washewa da fara'a
"Yanzun nan,ko minti daya banyi ba" sakin labulen data riqe tayi,ta soma takowa ciki
"Lale marhabin,wannan irin tafiya haka babu sanarwa babu labari?,tun muna ta zuba idanun ganinka har mun haqura mun janye" dan qaramin murmushi ya saki na gefan baki yana gyara tsaiwarsa,har yanzu idanunsa yana kanta,ita ke daukar hankalinsa tunda ya sanya qafafunsa cikin falon,wani irin kyau da haske yaga ta qara masa,sai yake ganin kamar an canza masa ita,bai sani ba,tsabar kewar data addabi ruhinsa zuciyarsa dama gangar jikinsa ce,ko kuma dai hakane da gasken ta sauya,yaci gaba da dubanta ta gefan ido sanda take miqewa daga qasa zuwa kujera,saboda wani irin weak da jikinta yayi cikin qanqanin lokaci
"Barka da dawowa" ta fada kanta na kallon yatsunta data sawa lalle jiya da daddare,saboda ta gaji da yadda sukayi fari,har faratan hannunta.


Ko kadan ba tare da wani jin nauyi ba,kamar ma ya manta da hajja dake wajen ya zuba mata mayun idanunsa
"Barkanki......mun sameku lafiya?" Yadda ya amsa din ya tilastata daga idanuwanta ta kalleshi,taci sa'a kuwa sun hada ido,saiya jefa mata wani kallo data ji ya girma kanta,tayi saurin dauke qwayar idanunta,sai kuma tayi rashin sa'a suka fada kan hajja,ashe su take kallo,hajjan kuwa data gwanance wajen iya fuskewa dauke idanunta tayi kamar ba'ayi hakan ba,saita miqe ma data jiyo ringing din wayarta tana cewa
"Yauwa....ina zuwa,Allah yasa nusaiba ce".


Fitarta sai falon ya zamana daga ita sai shi,gyaran murya yayi kamar wanda ya qware,ta fuskanci so yake ta sake kallon qwayar idanunsa,wanda ta karanci al'amura masu dama a ciki,bata jin xata iya bari cikin lokaci kadan ta fadi qasa warwas,kota bari ya gane lagonta,ita din ba yau ta fara soyayya ba,tuntuni ta gama karantar kanta tsaf,ta kuma karanci inda zuciyarta tasa gaba,saidai karatun ya bata tsoro qwarai,saboda banbance babancen soyayyarshi data mata wani irin kamu ta ruwan sanyi da sauran soyayyar data yiyyi a baya,wanda yawancinsu sun mata kamu ne ta farat daya,bata taba zata ko kawowa cewa soyayyar da zata dinga shiga jikinka tana dafa ka a hankali tafi illa fiye da wadda zata kamaka farat daya ba.


Batasan ya akayi ba,tana tsaka da wannan tunanin ta shaqi qamshinsa sosai,wanda hakan yake gaya mata mamallakin wannan qamshin yana dab da ita fa,saita daga kanta da hanzari,yana tsaye a kanta ya kafeta da ido dai kamar maye,ya ciro hannunsa guda daya amma sai yayi saurin dunquleshi ya kuma janyeshi baya saboda jin motsin fitowa hajja,sannu a hankali shima ya janye jikinsa
"Zan shiga na sanarwa mama dawowata" ya fadi yana juyawa a hankali,saidai fiye da rabin hankalinsa yana kanta,so yake yaji kalaman bakinta,hakanan bai gaji da ganinta ba,yana son yajita cikin jikinsa,yaji dumin lallausan jikinta da yayi kewarsa kamar yayi hauka,baisan haka aikin yake ba,baisan harda kanshi zai nanawa hauka ba,inda ya sani,da bai fara aikin ba bare ya tafi da tabonsa,ya hanashi sukuni,rashin sukunin da saura qiris ya janyo masa damuwa kan aikin da yaje yi din.


Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,ta manta da wanzuwar hajja sam a wajen,sai suka hada idanu da ita,sake fuskewa tayi kamar bata fahimta komai ba,saidai can qarqashin ranta tana jin wani farinciki yana mamayarta,lallai ba shakka Allah shine abun godiya,ta gama karantar komai,tafiyar haidar din aiki ya zame musu kamar wani haske,kuma mataimaki wajen cikar aikinta,ba shakka lokaci yayi,lokaci yayi da za'a kawo qarshen komai kowa ya huta,zatayi qoqari tayi dukkan abinda ya dace,amma zata bashi sati daya kacal taga shin xaiyi wani motsi daya dace shima?.
"Tashi kije ki sama masa wani abun da zaici kafin ya kintsa,tunda yau tazarce kukayi mana saboda tsabar ganda da qyuya,kinsan kuwa shi din ba ci xaiyi ba" karon farko.....lokaci na farko da taji ranta babu damuwa babu takura saboda hajja tace ta sama masa abinci....lokaci na farko da taji tana marmarin shiga kitchen,tun daga qasan ruhinta zuwa zuciyarta,taji a ranta cewa she's ready a dai dai wannan lokacin tayi dukkan girkin daya dace,don haka ba bata lokaci ta yiwa kitchen din tsinke.


Haka kawai ta samu kanta da zurfafa tunaninta kadan ta maidashi can baya,tana tuna kalolin abincin da yafi muradin ci,wanda a wancan lokacin matuqar su sukayi ya dinga gwalewa da kushesa kenan,wataran ma yaqi ci,har sai mama tayi masa fada sannan,ta saki murmushi tana tsaka da aikin,sanda ta tuna wani lokaci da hajja tasa ta diba masa abincin data yiwa abdulyasar,ranar kamar zaiyi me saboda tsabar hade gira,hatta hajjan tasha muzurai,akaci sa'a tayi magana,dama neman mai tankashi yake,yahau fada sosai,har sai dasu hafsat suka dinga kwasarsa suna gulmarsa a boye
"Hmmm...hala yau allurar sojoji ce ta motsa?"
"Allah sarki....duniya labari" ta fada a sarari ita kadai.


Bata dauki wani lokaci mai tsaho ba,kasancewar abincin dai dai cikin daya zuwa mutum biyu tayishi,ta shirya komai bisa wani tsari me birgewa,tana gyara kitchen din hajja ta shigo,ta kalli yadda ta tsara komai saita kyabe baki
"Ashe dai ashe dai,yanzu dukka zakin aka yiwa wannan?" Waiwayowa zahran tayi tana duban kwanukan data shirya da hannunta,sam batasan ma tayi abunda hajjan ta gani din ba sai data magantu,komai a tsare,duk wanda ya kalla saiya burgeshi bare ya bude ciki,flask din hajja ne sababbi,wanda jikoki da 'ya'yanta ke siyo mata da wanda ake bata kyautarsu dake ajiyewa bata amfani dasu suta dauko ta bare ta zuba masa abincin a ciki
"Ya gama ci kuyi lissafin kudin kwanukana,saikun bayani,ko naje har gida na fanshe a kitchen dinki" kunya taji ta kamata sosai,don bata kawo komai a kanta ba sai yanzu,sai ta yiwa hajjan tabarmar kunya,tahau zumbura baki

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment