Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da girmansa,babban gadone lafiyayye guda daya,sai kujera one sitter da two sitter da tv plasma daga gabansu kadan zaune saman wata tv stand ta zamani me tsari da yawan lockers,wanda ta tabbatar anan ya boye tarin takardunsa masu muhimmanci,bayan dan qaramin study room dinsa dake manne da dakin.


Haidar dake zaune saman daya daga cikin kujerun ya daga kanshi ya amsa sallamar,suka hada idanu saiya maida kan nasa qasa yana ci gaba da duba takardun daya barbaje a gabansa.


Yau daya sai taji ya mata wani irin kwarjini daya ratsa har cikin qasusuwanta,duk da cewa ba yaune karon farko data saba ganinsa ya hade girarsa haka ba,a'ah....dama dabi'arsa ce hakan.


A nutse ta qaraso gabansa ta aje kwandon,so tayi ta tafi amma suna hada ido sanda take shirin tashi saita koma ta zauna,kaf gidan sunsan tsarinsa baya sarving abinci da kansa,tuntuni sun saba al'adarsa haka,yana da wata izza da jin sarauta a jininsa.


Tana kammale kwanukan taji ya magantu cikin qasaitar nan tasa,takarda da biro ne ya aje gabanta
"Ki rubuta duk wani da kike buqata na komawa school",daga haka ya dauki bowl din dake daukw da farfesun danyan kifi ya saka spoon ya fara shan romon a nutse bayan ya harde qafarsa cikij ta juna,yayin daya maida kallonsa ga tv dake aiki kan qaramin sauti da bazai damu mutum ba.


Ta gefan idanu ta kalli takardar sannan taja tsaki cikin ranta
"An gaya masa na damu ne da wani kayan hannunsa,koda can shi yakemin" tana kaiwa nan ta miqe abunta ta soma takawa zata bar dakin.


Taku biyu rak tayi ta tsinci dakakkiyar muryarsa yana cewa
"In kika sake kika fita saina biyoki har gaban hajjan na kakkarya wadan nan sili silin qafafun" yadda yayi maganar ya tabbatar mata bada wasa yake ba,duk da taji haushin ba'ar da yayi mata haka ta shanye,ta juyo tana zumbure zumbure,ta dawo ta samu can gefe ta zauna bayan ta dauko takardar.


Abu uku kawai ta rubuta taje gabansa ta ajjiye,da idanu ya kalli rubutun,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanun nasa ba tare da yace komai ba,hakan ya bata damar ficewa tana gunguni cikin zuciyarta.


Koda ta koma da kallo hajja ta bita,saboda bata tsammaci dawowarta da wurwuri haka ba,amma saita shanye,bata ce da ita komai ba.


Washegari tana kwance hajjan ta shigo
"Tashi kije ki gyara dakin mijinki" batasan sanda ta dawo rigingine daga kwanciyar rub da cikin da take ba fuskarta a hade tana duban hajja
"Waye kuma mijina?" Daquwa ta watsa mata
"Ungo nan....nace ungo nan,zaki tashi ko sai na radeki?" Ta fada tana kai mata dundu,tuni ta hantsilo daga gadon tana sosa bayan kamar ma ta sameta tana kuma duban hajjan
"Abun har yakai haka hajja?" Ta tambayeta kamar zata saki kuka
"Yama fi haka,indai zaki dinga min musu da shegen taurin kai....kuma indai kika ci gaba da yimin haka naga wanda ya isa ya karba miki takardar taki duk duniya" da haka ta juya ta fice daga dakin.


Tsoron furucin da tayi ne ya sanyata zarar mayafin doguwar rigar jikinta ta yafa tana ta mita a haka ta fice.


Har zata wuce hajjan ta kirata ta miqa mata key din,wanda dama can hajjan nada shi,daya a wajensa daya a wajenta,daya kuma a wajen mamarshi,ta amsa ta wuce tana fadi qasa qasa
"Kya ci gaba da share masa idan na komawata makaranta"
"Idan na barkin kin koma ba" hajjan ta bata amsa,sai tayi turus ta dakata da tafiyar da take tana dubanta kamar zata saki kuka
"Haba hajja,bafa haka mukayi dake ba"
"Zaki wuce ko saina iskeki?" Kamar zata dora hannu aka haka ta juya ta fice.


Kamar waccar ranar dakin ba wani dauda yayi ba,sai squeezing da beadsheet din yayi alamun an kwanta akai ne,mayafin ta daura saman kanta sannan ta fara kauda kayayyakin da suke ba'a muhallinsu ba.


Ta isa gefan gadon bayan ta gama gyara qasan,tasa hannu tana janye zanin gadon wasu frames masu kyau suka fado,cikin fargaba ta zagaya inda suka fadin,tana addu ar Allah yasa basu fashe ba,ta tsugunna ta soma daukesu.


Hotunan yaa zahra ne dukka guda ukun,kowanne sanye da hijabi take,fuskarta dauke da murmushi,kamar idan ka kirata zata amsa maka
"Margayiya" ta fada cikin zuciyarta,dan tsurawa hoton idanu tayi,sai kuma ta miqe tana jan tsaki data tuna daga inda hoton ya fado
"Aikin banza....har wani kwana da hoto yake waishi baban soyayya,aisai ka bita can shine ka burge,inda wani ne da yaji magana a wajenka" ta fada tana tuna yadda ya dinga treating din issue dinta dasu nuraddeen,locker din gefan gadon ta jawo ta watsa frames din,duk da tana iya hangen wasu pics din wanda da alama na yaa zahran ne,saita koma gadon taci gaba da gyarawa,kafin ta gama ta shiga toilet dinsa don wankewa.


Sai data kalli bandakin ta tabbatar komai ya fita fes sannan ta murda qofar ta fito.


Bata tsammaci ganinsa ko dawowarsa ba a sannan,bayanshi kawai ta hanga yana tsaye gaban gadonsa ya baje wasu takardu yana zaba,da alama daukarsu ne ya dawo dashi.


Jin taku ya sanyashi juyawa a hankali,sai suka hada ido na sakanni kafin ya dauke idanunsa ya maida ga abinda yakeyi ba tare daya ce komai ba,sai tabi ta bayansa itama ta fice daga dakin.


Batafi minti biyu da fita ba ya shiga wajen hajjan yana hadiye zuciya riqe da envalope a hannunsa
"Hajja....me yarinyar can kemin cikin daki bayan bana nan?"
"Sata ubana" ta amsa masa itama tana tsareshi da idanu,saiya lumshe idanunsa,tsohuwar tana bashi ciwon kai yadda ya kamata,ita kadai duk duniya ta isa tayi masa karen tsayen da take masa,saiya juya kawai ba tare daya sake cewa komai ba ya fice daga sashen
"Zanyi maganinku" ta fada a ranta,tana dauke idanunta saiga zahra
"Wai hajja ma tuhumata yake da shigar masa daki?,nidai wallahi hajja kina jamin ina zaman zamana" ta fada kamar zata saki kuka
"Yanzu ma na fara jaza miki" tuni ta tara qwalla a idanunta
"Bazan sake masa shara ba Allah,ayiwa mutum aiki sannan ya rasa me zai sakamin dashi?,to dakin nasa dakin wa yafi cikin gidan nan?"
"Idan bakije kinyi ba nida kaina kuwa zan dauki tsintsiya naje na share masa,idan kuma banje ba zansa daya daga cikin iyayenki yayi"saroro zahra tayi kafin ta juya zuwa cikin dakinta da sauri.


Mita take ita daya kamar zataci kanta,tana qissima sauran kwanakin daya rage tayi tafiyarta makaranta,ita gobe ma gidan salma ko hafsat zata,sai kuma ta tuna idan tace zata din sai hajjan nan tace saita tambaya,ita kuwa data tambaya gwara haqura da zuwan.


*BAYAN KWANA BIYU*


Ana ya gobe zata koma makarantarta,tana falo tana sake goge wasu kayan da zata tafi dasu atamfofinta,musaddiq jikan gidan yayi sallama shi da nurain,hannunsu dauke da leda suka zubw gaban hajja
"Gashi inji yaa zaki,na yaya zahra ne"
"Shi yana ina?" Hajja ta tambaya
"Yana waje yana sallamar wasu baqi ne" inji nurain yana hayewa saman kujera
"Jeka kace min idan ya gama yazo ina son magana dashi".


Jin haka ya sanya zahra a gurguje ta gama goge kayan nata ta miqe zata shige daki
"Ke....dawo ki kwashe wadan nan kayan daga gabana" tana zumbura baki tana fushinta haka ta dawo ta kwashe ledojin ta jasu har cikin daki,ta musu waje ta jibge ta shiga sabgarta.


A gurguje ya leqo saboda kiran da hajjan tace tana masa,bayan sun gama gaisawa tace dashi
"Qarfe nawa zaka miqata makarantar a gobe?,don inason na qarasa hada mata abinda yayi shaura" kansa ya daga ya kalli hajjan
"Oh....ai dama bani ke kaita ba ko?"
"A sanda take babu igiyar kowa a kanta kuma ba matar wani bace ba ba...banason dogon magana,ka shirya gobe da wuri ka maidata makaranta" yasani cewa koda ya fada wani abun ma babu abinda zai janyo masa sai bala'en hajjan,wanda ya lura da cewa yanzun wani bala'i ta koya,motsi kadan zata ce anemo mata tsoho da tsohuwarshi.


******* *WASHEGARI********



K'arfe takwas da wasu mintuna ta gama shirinta tsaf,ta shiga tayi sallama da umminta sannan ta shiga sashen abba babba shima tayi masa sallama,sannan ta wuce dakin mama,maman haidar ta mata sallama
"Allah ya kiyaye hanya,ya bada ilimi me amfani" ta miqa mata wata baqar leda da batasan meye a ciki ba,hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya sannan ta fito.


Tana takowa zuwa bakin motar tana kallon yadda ake sanya mata kayanta bayan motar tashi,shi yana zaune daga ciki ba tare da ya ko motsa ba,tana tsaye har aka gama sanyawa sannan ta matsa ta bude gaban motar ta shiga a hankali.


"Ina kwana" ta furta domin bin umarnin umminta,bata ji ya amsa ba duk da taji alamun motsin fitar sauti,dama kuma ba damuwarta bace ya amsa din ko kada ya amsa,illa iyaka tasan cewa ta fita haqqi,ta kuma cikasa nasiha.


A hankali ya tada motar kana ya saitata ya fice daga gidan,kafin subar layin ya sanya hannunshi gaban motar ya dauko wayarsa yayi kira ya sata handsfree ya aje,bugu biyu aka daga
"Ka sameni a nasarawa sardauna cresent" daga haka ya katse kiran ba tare daya jira amsar da za'a bashi ba.


Tafiyar kurame da takura daga wajen zahra ta mintuna ba dasu gaza ashirin ba ya tsaya qofar wani gini wanda ake gab da kammalashi,kashe motar yayi ya zare key din ya fita daga cikinta y kulle sannan ya jingina da murfin,ita dai batace komai ba tana kalloshi ta cikin glass din har zuwa sanda ta hangi shigowar ya musty a napep na haya,bataji me suka tattauna ba,saidai taga ya miqa masa.key din,kana ya matsa daga jikin motar zuwa ginin gidan dake gabansu,shi kuma mustapha ya bude motar ya shigo.


Sai daya rufe sannan yace da ita cikin tsokana
"Sai matar babban yaya....Allah dai ya biya,matar soja marmari daga nesa" harara ta watsa masa
"Kaga ya musty bama haka dakai,dadai ya shamsu ne nasan zaiyi abinda yafi haka,don Allah ja muje,ni hakan ma yafimin dai dai" ta fada tana yatsina,yayin da mustapha ya qyalqyale da dariya.


Ko kadan hakan bai bata haushi ba,saboda tasan cewa inda shine zai kaita babu komai cikin tafiyar face zallar takura har su isa,wala'alla ma sai yayi ko ya gaya mata abinda ranta zai baci a banza.


Sanda ta shiga dakinsu kamar hadin baki duka roommate din nata suna nan,har da sauran ma,ihu suka saka suna kiran ga amarya ga amarya,bata tanka su ba saima harara data watsa musu
"Duk ku iya bakinku wallahi" don har ga Allah har cikin zuciyarta tana jin sune sila,su suka jaza mata komai,saidai ko kadan basuji gargadin nata ba,saima ci gaba da zolayarta da suke,hindu tace
"Erhmmm....erhmmm...ashe ashe dai....yayan dai da aketa nunamin sam baida kirki.....ashe dai kece zaki wufffff da abinki akemin hannunka me sanda" kicin kicin zahra tayi da ranta sanda take aje jakankunanta saman katifarta
"Kinga hindatu....idan baso kike aji kanmu ba ki aje wannan maganar....am seriouse bana sonta" saida suka gama kidansu da rawarsu sannan suka qyaleta.


Zuwa washegari ta gama gyara komai nata,batayi qasa a gwiwa ba ta koma lactures cike da hazaqa karsashi da qwarin gwiwa,saidai haka nan ta samu kanta da takatsantsan da mu'amalarta da mazan ajinsu,duk da cewa dama can duk wanda ya sa ta yasan tana da wannan zarrar,amma a yanzun takatsantsan da kamewan ya qaru,tunda ada issue din karatu yakan hadasu,amma a yanzun mawuyacine idan ba ya zama dolen dole ba.
23/10/2021, 08:45 - 👍🏻👍🏻: 24
*_Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗_*
*_Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm_*
*_Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉_*
*_Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅_*
*_Mg's will gv you the best out of all_*

*_With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃_*
*_We have herbal whitening black soap now nd beauty set available_*
*_Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗_*
*_Just gv it a try now nd see wonders✅_*

Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

*_Nd guess wht🦻_*

*Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is the time to glow🧖‍♀️*
*Pamper ur skin🦵*
*Shine like a bride 👰*
*be part of the glow* *team karkubari abaku lbr*

Just chat 08062991549 to plc ur orders😘



Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️
______________________________



*_BAYAN SATI BIYU_*



karfe biyu na rana suka fito daga aji,sauri take tana Allah Allah ta isa daki ta cire kayan jikinta ta samu ta watsa ruwa saboda zafi da rana,tuni ruwan sama ya fara samuwa a wasu garuruwan kamar legos abuja da sauransu,ya zuwa sannan kano da kaduna suma suna saka ran samun nasu ruwan saman na farko.


Tana tafe tana qiyastawa a ranta,a qalla wannan satin tanason taje gida weakend,don tunda ta dawo bataje din ba,saboda kuma raguwar karatu da fara shirye shiryen jarabawa tana tunanin zata dauki kwana goma kafin ta dawo,don yanzu sam ba kasafai take jin dadin zama tare dasu hindatu ba,takatsantsan take,batason wata matsalar ta sake kunno kai,saidai duk da haka bata fasa gaya musu gaskiya ba,kuma alhmdlh tana ganin hasken hakan,don da yawa daga dabi'un da basu daukesu a bakin komai ba a baya zuwa yanzu babu mafi yawa daga cikinsu.


Tana gab da shiga dakinsun wayarta da bata jima da kunnata ba ta dauki tsuwwa,saita dauko tana duba me kiran,ya shamsu ne,tadan ja tsaki tana murmushi,tana rayawa a ranta wala'alla ya kirata ne kawai ya tsokaneta ya kuma cakar da ita
"Sai matar yaya" ya fada yana dariya,shida musty kusan sun soma sauya mata suna,tun tana bala'i harta gane ma zugasu takeyi
"Cima zaune....ya akayi?"
"Hajja....ita tasa na kiraki,kuma sai an biyani kudin katin dana qona"
"Karka damu,an gaya maka mu fuqara'u ne irinka?"
"Ni nasan kun girmi wajen....matar aliyyu dabo ce fa.....muma aci gaba da yi mana addu'a....ya haidar ya mana alqawari,upper dinmu tana nan zuwa hannu"
"Kaga...ka gayan saqon hajja ya shamsu koka qona katinka a bati wallahi"
"Naga alama kin soma rainamu nida musty tunda aka daura miki igiyar auren ya zaki....to hajja tace ta kasa samunki,ki shirya nan da minti ashirin ina hanya,zan daukeki nakai mata ke airport"
"Airport kuma?....me hajja keyi a can?"
"Kinga idan kinje kyaji,nidai aikina zanyi"
"Shikenan....saika qaraso" ta fada tana kashe kiran,sannan ta tura qofar dakin nasu ta shiga.


Hindatu ta samu ta zaune gefan gado riqe da plate tana cin abinci,daga ita sai vest da zanin atampha,da alama itama bata jima sa shigowa ba,zafi ya haukatata,sai jannat dake zaune a qasa ita kuma tana shan lemo.


Tana aje jakarta tana musu sannu gami da zare mayafinta,sannan ta soma qoqarin canza kayan jikinta zuwa na wanka,hindatu ta dubeta
"Ga abincinki fa..."
"Ai hindu inajin saina dawo zanci,yanzu ya shamsu yakirani hajja ke nemana wai kuma a airport...ko lafiya" hindun nakai lomar abinci bakinta ta amsa masa
"Lafiya mana,dadai asibiti akace shine zaki tsammaci ba qalau ba"
"Hakane" ta fadi tana sanya hijabinta gami da daukar shower gel dinta ta nufi bandaki.


A gurguje ta shirya cikin atamfa riga da skert da sukayi matuqar yi mata kyau da amsar jikinta,tana fesa turare kiran shamsu ya shigo
"Ki sauri don Allah,hajja nata azalzalata fa"
"Am coming" ta fada tana jefa wayar a jakarta gami da qarasa daura agogon hannunta,ta zura takalminta tana rataya jakarta hindatu tace
"Wannan kwalliyar kyanta zakin maza aka yiwa ita,bakiga yadda kwalliyar ta amsheki ba,sai yaushe kenan?"harara ta jefa mata tana gyara eye glasses dinta wanda ta soma amfani dashi kwanan nan
"To bashi aka yiwa ba sai yaya?,Idan na dade awa uku,shi daya kaini shi zai dawo dani,saboda jibi zan wuce gida,ban kuma gama shirya kayana ba,zanje dasu gida na canza wasu"dariya tayi
"Ai shikenan,Allah ya hadaku a hanya ya dauke abarsa inga ta tsiya,any way.......saikin dawo" inji jannat
"Ki gaida hajja" hindatu ta fada ita kuma tana dariyar maganar jannat wadda zahra keta aikawa saqon harara
"To zataji" ta fada tana fita da dan hanzari,don tasan halin ya shamsun da shegen qorafi.


Suna tafe a mota suna taba hira,duk da yawanci duk tsokana ce yake mata kamar yadda ya saba,kusan haka halinsa yake saidai idan ba'a hadu ba,ba yadda batayi dashi ya gaya mata meke faruwa ba yace shima bai sani ba,yana gida aka bashi wannan umarni,idan taje ta gani,sai tayi shuru kawai tana dan nazari a zuciyarta.


Babu jimawa suka iso filin sauka da tashin jiragen sama dake garin namu na kanon dabo,kai tsaye ya mata jagora tana biye dashi har zuwa inda yace mata hajjan nacan a zaune.


Tun daga nesa ta hangi hajjan,gefanta mama ce da umma matar abba yusuf,daga daya side din kuma abba babba ne da abban tsakiya,gabanta ne yadan fadi kadan,ta ambaci sunan Allah a ranta,sannan ta qarfafawa kanta gwiwa ta isa inda suke.


A ladabce ta gaida kowa idanunta na karantar fuskarsu,babu alamun tashin hankali tattare dasu,saima farinciki data karanto kan fuskar kowannensu,da alamu kuwa tafiya ce ta kamasu,don akwai travelling bag tare dasu,ta kasa tambayar kowa har sai data zauna kusa da hajjan tata
"Hajja....sai ina kuma haka?,ko bana anyi kira?,Allah yayi za'a koma umra?" Ta fada cikin sigar tsokana,baki tadan tabe
"A'ah fa....duk da itama umarar muna saka rai nan ba da dadewa in sha Allahu....amma yanzu dai yayanku ne bikin qarin girmansu ya tashi.....shine ya aiko mana da tikiti zamu sameshi can abujan" ta gane sarai kan wa take magana,saita dan dauke kai cikin sigar bagarar da zancan tace
"Shine takanas kikasa aka dauko miki ni,yanzu hajja ba zamu iya yin sallama ta waya ba?"
"Sallama dawa?,ai dake za'a tafi,kema na siya miki naki tikitin,tafiya kawai ta rage miki" da sauri ta dawo da dubanta ga hajjan
"Tafiya kuma ina?"
"Au....bakiji duka bayanan dana miki ba dazu....to can abuja inda za'ayi bikin".


Wani gumi ne ya yanko mata ta tsakiyar bayanta,wai me yasa hajja keson ta dinga yarfata ne,banda yarfawa tsakani da Allah kawai sai ta jata gayyar sodi haka akeyi?,yanzu tana magana kuma sai cibi ya zama qari,gashi basu kadai bane a wajen,akwai mama,wanda tsakani da Allah tana jin nauyinta,don tsaf hajjan zata iya mata tarere ta barta da kunya,amma saita yanke bari ta gwada tata dabarar
"Banda abun hajja....haka ake tafiya gaba gadi babu shiri babu sanarwa?" Sheqeqe hajjan ta kalleta,da alamu babu nasara a zancan zahran
"Wanne shiri kuma?,duk wani shiri kwa yishi tare da mijinki....idan kuma ta kayan sawa ne gasu nan,takanas na kira ilhama ta hada miki duk abinda tasan ya kamata,sai kuma me?" Shuru zahra tayi tana duban 'yar trolly dinta qaramar wadda takan dauka lokaci zuwa lokaci,cikin ranta tana furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,daga sannan bata sake magana ba,sai kawai taja bakinta ta tsuke,illa wayarta data ciro ta turawa hindu text na cewa ba zata dawo a yau ba,ta kula mata da lamarinta koda wani abun zai taso daga gobe zuwa jibi ta shaida mata,daga haka ma saita kashe wayar gaba daya ta zubawa sarautar Allah idanu,gami da hasashen yadda komai zai wakana,itadai tasan basa hada inuwa daya da haidar,amma ta qarfi da yaji alo tsiya alo danja hajja ta kafe sai sun jiqa kanwa guda dashi,ita sam bata qaunar wannan girman kan nashi da ji da kan nasa kamar wani mace,macen ma saraki.


'Yar kallo kawai zahra ta koma tun daga shigarsu jirgi zuwa saukarsu,tsoron ma da akace akanji a hawa jirgi karon farko ita bai wani dameta ba,saboda inda zatan yafi komai damunta a ranta,ji take kamar ta rufe ido ta bude ta ganta a makaranta.



Suna sauka tun cikin airport din abujan aka taresu,wani matashi sanye da kakin soja ya musu jagora zuwa wata galleliyar sabuwar mota,wanda kallo daya zaka mata kasan cewa sabuwa ce da gaske,shi ya bude musu dukka suka shiga ya shigar da kayansu booth sannan shima ya shiga.


Gaishesu ya soma yi da tattaciyar hausarsa pure bisa dukka alamu dan arewa ne bahaushe,yanayin girmamawarsa garesu ke nuna yasan kosu din su waye a wajen aliyyun,saida suka gama gaisawa sannan ta yada motar suka fice,yayin da kunnuwan zahra ke biye dasu,tana jin yadda suke hirarsu,abba babba na nuna musu wasu guraren da ya sani cikin abujar idan sunzo wucewa ta wajen.



Tafiyar wajen minti talatin da uku ta sadasu da unguwar da suka nufa,unguwa ce dake cike da tsari da gine gine masu ban sha'awa,a hankali driver din yace
"Oga ya bada umarnin a saukeku a sabon gidansa,akwai duk abunda kuke da buqata,wani uzuri ya riqeshi amma nan bada jimawa ba zai iso ya riskeku a gidan"
"To ba matsala,ya kirani bayan mun sauka ai,munyi magana dashi" cewar abban tsakiya,kai matashin ke gyadawa sanda yake yunqurin tura motar tasu cikin wani madaidaicin gida dake dauke da matsakaicin qawataccen gate bayan mai tsaron gate din shima dake sanye da kaki ya bude musu gate din.


Wata madaidaiciyar rumfar adana motoci ya shiga ya faka motar kusa da wata mota dake a rufe ruf,da alama ita dinma sabuwace,zaka gane hakan kota iya tayoyinta.


"Ma sha Allah....ma sha Allah" kawai kowa ke fada,saboda yadda gidan ya tsaru ya kuma qawatu,duk da cewa ba wani qaton gida bane,saidai yana da yalwa dai dai misali,akwai haraba madaidaiciya wadda ke dauke da wata rumfa ta bunu da wasu irin kujeru qasanta da teburi saboda dora kofuna da lemuka,akwai balcony mai kyau da wasunirin kujeru guda hudu da wani irin qarfe da aka zube a cikinsa bayabga furanni wanda ta cikinsa balcony din zaka isa falon gidan,wanda ya dauki set din kujeru biyu sai dining area,daga daya bangaren akwai gajeran corridor wanda ke dauke da dakunan bacci guda biyu da bandaki a tsakiyarsu,duk da kowanne daki yana da bandaki,uwa uba kuma akwai wani spare dakin cikin falon.


Akwai ma'aikata maza guda biyu da suka tadda cikin gidan,daya shine kukun sa,daya kuma me gyara falon gidan da bandakuna,banda bedrooms dinsa.


Dakin dake cikin balcony din nan aka budewa su hajja,yayin dasu abba babba kuma aka bude musu na ainihin falon.


"Ma sha Allah....gaskiya ne,wannan gida saidai fatan alheri,Allah yasa an shiga a sa'a" umma ta fada tana kallon kowanne bango na dakin da aka qawata da wasu fitilu da fenti mai kyau,ga kuma qyallin sabunta na haska dakin ya qara masa wani haske me kyau.


Tunda ta samu gefan qatuwar katifar dake yashe a dakin bata ce uffan ba,duk hirar da suke tayi a tsakaninsu nata idanu,abu

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment