Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karanta rubutun dake qasan hoton xai gaya maka tabbas ango da amarya ne cikin yanayin hotunan nan da ake kira da free wedding pictures,rubutune a qasa kamar haka

*SAVE THE DATE 22/07 IN SHA ALLAH*


Wani kakkarwa hannayenta suke kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi tana ci gaba da buda hotunan ba tare data iya tsaiwa ta duba rubutun dake qasan kowanne hoto ba,abunda ta iya dubawa shine lokacin da aka dora,6minutes ago,kenan shi ya dora da hannunsa da kansa,tunda sanda ya sauka da sanda ya dora tazarar minti daya ce.


Hafsa ce ta shigo tana dariya abunta riqe da hijabi tana qoqarin sawa,da alama daga waje ta baro abunda ya bata dariyar,sam bata lura da yanayin da innawuro ke ciki ba sai dataji tana kiran sunanta da wata iriyar shaqaqqiyar murya tana yafitota da hannu.


Qarasowa tayi tana dubanta,ba wanda ya iya magana cikinsu sai wayar da zahra ta miqa mata cikin rawar murya tana cewa
"Dubamin don Allah.....dai dai idanuna suke ganemin?" Hannu tasa ta karbi wayar,hoto daya tak ta kalla saita koma saman qafafunta ta zauna itama tana ci gaba da kallon hotonan cikin matuqar mamaki da sanyin jiki,kalamanta a sanyaye qwarai tace
"Nura ne zahra,nuraddeen dinki fa" rasa abu na gaba daya kamata tayi tayi,sai kawai tasa dukka tafin hannunta biyu ta rufe fuskarta dasu kamar wadda bata da muradin ganin duk wani haske dake cikin duniya,tana jin kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,daidai sanda salma ta shigo,da sauri hafsat tace
"Yauwa,zo kigani don Allah,zoki tayani gani" da hanzari salman ta qaraso tana amsar wayar daga hannun hafsat.


Wani ashar salman ta dura,da yake itadin batakai haqurin hafsat ba,ta lalubi waje ta zauna tana cewa
"Meke shurin faruwa kenan zahra?laaa,kinga ana goge hotunan daga status.....sunyi disappearing gaba daya"ta fada tana kallon hafsat tare da nuna mata wayar
"Tabbas gogesu akayi,don ba'afi minti goma da dorasu ba,bajci ace har lokacin saukarsu yayi ba,me nuraddeen ke nufi?" Tambayar da bata da amsarta data cilla mata ita ta sanyata sakin wani irin kuka me ciwo,kukan daya daga hankalinsu gaba daya,lokacinne yasira itama ta sako kai,cikin yanayi na tsoro ta isa wajensu tana tambayarsu abinda ke faruwa,basu kai ga bata amsa ba kira ya shigo wayar zahran,duk da bata duba tasan me kiran,salma cikin fushi tace
"Bari na daga naji dan gidan marasa mutuncin me zaice?"kai hafsa da yasira wadda batasan ma ainihin meke faruwa ba suka daga mata,ta daga wayar ta sakata a handfree tayi shuru ba tare data ce komai ba,muryar nuradden ta bayyana
"Dear.....don Allah karki hukunci da abinda bakisan ainihin menene ba,ki bani dama inyi miki bayani pls"
"Ai karka damu,saqone ka bayar ya kuma iske inda kakeso ya iske,yo meye kuma wani abun damuwa a ciki?,kaci gaba da shagalinka kawai,amma ka sani,indai da haqqin zahra a wuyanka Allah saiya mata sakayya"
"Ki tsaya kiji don Allah,wacece?,hafsat ce ko yusra?"
"Ban sani ba dan gaba da rainin hankali,karka sake kiran wannan number" qit daga haka ta katse wayar,wanda kafin ta kuma cewa komai wani kiran ya sake biyo baya,haka suka sanya wayar gaba kowa ya rasa abun tabukawa,yanata faman kira ba qaqqautawa kamar yadda zahra ke kuka itama babu qaqqautawa,yasira ce ta karbi wayar daga qarshe bayan sun zayyana mata abinda ke faruwa ta kasheta gaba daya,har cikin zuciyarta tana jin wani irin suya da bacin rai,wannan wacce iriyar yaudara ce haka kai tsaye ta rashin mutunci da cin fuska,yana sane ma yayi posting hotunan a status dinsa?,abinda yafi tsaya musu a rai kenan.


Su hudun gaba daya suka hadu suna bata baki,harda nadiya data shigo daga qarshe gami da maimaita zancan cike da mamaki,don dukkansu bama su ba kusan kowa yasan da zaman nuraddeen a matsayin wanda zahra inna wuro ta tsaids zata aura,abun yazo musu matuqa a ba zata.


Ita kadai tasan yanayin data tsinci kanta da zuciyarta a ciki,wani yanayi da tun tasowarta bata taba jin irinsa ba saiyau,jin lamarin take kamar a mafarki,wai ita?,nuradden?,wanne irin abu haka tayi masa dafa cancanci irin wannan yaudarar mai ciwo?,har yana da bakin cewa ta saurareshi?,ta jima cikin wannan rudun,daga qarshe taji babu abinda take da buqata illa kadaicewa tayi kukanta ita kadai ko hakan zai sa ta samu gurbin da zata zuqi numfashi yakai har zuciya da hunhunta,tana jin kamar numfashinta zai katse ne.


Yanayin yadda suka shigarwa hajja zahran na kuka lullube da fuskarta ya sanyata miqewa da sauri cikin firgita tana tambayar
"Kai...meye haka?,lafiya?" Itakam zahra bata iya tsaiwa ba saita wuce kawai zuwa daki,waje ta laluba ta kwanta gami da sake rushewa da sabon kuka.


Bayan minti biyu tajiyo muryar hajja na rafka salati da salallami,da alama sun gama gaya mata komai,sai kawai taja filo ta rufe kanta tana sake fashewa da wani irin kuka,tanajin sanyi na ratsa gabbanta,kafin kace meye wannan zazzabi ya rafketa.


Ba'a rufa awa guda ba hajjan ta shigo dakin
"Takwara.....kukan kike har yanzu?" Ta fadi tana qarasawa inda take kwancen,ta saka hannu ta yaye abun rufar tana kamo hannunta
"La'ilaha ilallahu,ke tashi,kwanciya kikayi xaki kashe kanki,kinji yadda jikinki ya rine da zazzabi?" Cikin daren dukka hankalin hajjan ya tashi,wanda hakan yasa hankalin yaranta su abba babba suma ya tashin,ta matsa lallai lallai saida su shamsu suka dau mota suka kaita asibiti,wanda basu dawo ba sai wajen sha biyu da rabi na dare saboda yadda zazzabin ya mata mugun kamu ya sanya suka dan riqeta sai daya sauka jikinta yadan daidaita.


Washegari duka tana kwance a daki,ko falo baga fito ba bare taga hasken rana,tana kwance tana bitar duka rayuwarsu ita da nuraddeen,bataga ta inda ta gaza ba da xai gujeta,bata ga me ta masa da zai saka mata d a wannan ba.


Duk yadda hajja taso ta fito da ita ta xauna koda a falo ne amma taqi,hankalinta kaf nakan zahran,duk bayan wasu mintuna saita leqo dubata,dukka jama'ar gidan kowa ya shigo ya dubata babba da yaro,amma banda mutum biyu,ummanta dai tasan kara ce da kawaici ya hanata leqoww,don koda hajja ma ta aika mata cewa tayi ace tana gaidata kawai,data sake aikawa sai tace ai tasan tana wajenta babu komai,shi kuwa dayan dama bashi a lissafinta,tama manta dashi cikin jerin jama'ar gidan.


Hajja da kanta ta yiwa abban gwammaja waya sanda yace zaya aiko a maidasu makaranta ita da hasina ta shaida masa bata da lafiya,a barta koda zuwa satin sama ne idan ta sake murmurewa,ya mata sannu da jiki,ya kuma ce zaisa a shaida hukumar makarantar idan ankai hasinan.


Sai da akayi kwanaki biyar da komawa makarantar sannan ta soma jin qwarin jikinta,don ta tattara dukkan wasu lamura na nuraddeen tayi qoqarin yin watsi dasu,a yadda ta lissafa kwanaki uku kenan da daurin aurensa,yana can wala'alla shida amaryarsa cikin farinciki,yama manta da lamarinta,hakan ya sanya washegari da azahar tayi wanka da ruwa mai dumi sosai,tasha dukka magungunanta,ta shirya cikin atamfa riga da zani sannan ta fito falon.


"Yauwa,ko kefa?" Hajja data taras zaune cikin falon ta fada cikin farinciki,tana kallon yadda zahran tadan fada,hancinta da fuskarta suka qara qara tsaho.


Mirmushi tadan yiwa hajja,cikin qarfin hali ta tsokaneta
"Ashe kina tsoro kada na mutu na barki"
"Zaki fara ko?" Hajjan ta fada tana watsa mata daquwa,dai dai sanda inna gaje ta fito daga kitchen zuwa falon
"Aah,ma sha Allah uwar masu gida jiki yayi kyau"
"Eh wallahi inna gaje" ta fada tana dan murmushi
"Alhamdulillahi,mun godewa Allah,Allah ya qara lafiya"
"Amin inna,akwai abinci ne?" Zahran ta tambaya
"Eh yanzu aka gama na rana...bari a zuba miki" inna gaje ta fada tans komawa kitchen din,sai zahran ta bita a baya ta amso abincin ta dawo inda ta tashi ta zauna
"Wannan abincin kamar na wasan yara wuro?" Hajja ta fada tana duban plate din
"Ya isheni hajja" saita qyaleta,tayi bismillah ta fara ci,lokaci lokaci idanunta nakan tv dake aiki.


Sallamar abubakar ce ta karade falon,abubakar shine yaro na farko a sassansu,daga shi sai ita,sai sauran qannenta maza guda biyu,sulaiman da yusuf,sai mace daya ilham,akwai tazarar shekara kusan biyar tsakaninta da abubakar,hakan ya wanzar da girmamawa sosai tsakaninsu,don haka umminsu ta tarbiyyancesu da bawa na gaba dasu girma.


"Maraba da saddiqu.....saukar yaushe?" Hajja ta fada tana dariya
"Ko minti biyu banyi da shigowa gidan ba" ya fada rabin hankalinsa nakan zahra data aje cokalin hannunta tana qoqarin gaidashi
"Lafiya lau...." Ya amsa a taqaice ya dora da
"Me kike a gida,duk 'yan makaranta sun koma makaranta?" Kafin hajja takai ga bada amsa an sake sallama cikin falon,muryarsa ta cika wani irin sauti mai sanyi,saidai tana cike da wani kwarjini mai ratsa kunne.


"Sannu da zuwa yaya" abubakar saddiq ya fada cikin salo na girmamawa,fuskarsa washe da fara'a
"Malam.....kana lafiya?" Ya fada yana miqawa saddiq hannunsa dake daure da wani rantsatsen agogo ruwan zaiba,wanda ya dace da lafiyayyar fatarsa da hutu da kuma kwanciyar hankali ya ratsata.


Da sauri sadiq ya miqa masa nasa hannun sukayi musabaha,saiya soma qoqarin zama hannun kujera yana gaida hajja cikin girmamawa,don shi sam baya wasan jika da kaka da ita,ta amsa cikin kulawa,don shi dinma dan gaban goshinta ne,sakamakon sunan maigidanta da yaci,sannan ta dora da fadin
"Kamar tare kuke da sadiq?" Yana dan latsa wayar hannunsa yace
"Tun dazun na shigo,na shiga ciki ne nadan huta"
"Auto ma sha Allah,ya aikin,da fatan an samu abinda ake bida?"
"Alhmdlh" ya fada hade da ajiyar zuciya yana maida wayarsa aljihun lafiyayyen trouser din jikinsa,wanda kallo daya zaka masa kasan me tsada ne,hakanan mai kayan yasan takan kaya masu aji.


Ido suka hada da xahra,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanunsa duka cikin sakan biyu,ya harde hannayensa a qirji yana duban hajja dakewa sadiq bayanin dalilin xamanta a gidan,cikin sauri tace
"Ina yini" can qasa ya amsa kamar yadda ya saba
"Wallahi yaron ya bani mamaki,a haka kamar na Allah ashe bana arziqi bane,yaudara ce kawai ta kawoshi,yau ne mafa kawai na samu kanta ta fito falo ta zauna" ta qarashe zancan cikin nuna jimamai qwarai kan fuskarta idanunta kuma saman fuskar haidar,wanda ya dauke kansa zuwa yanzu daga kansu kamar ma baisan me ake ba.


Ajiyar zuciya sadiq yayi
"To Allah ya kyauta ya rufa asiri,abinda ya faru ya riga daya faru,sai kiyi qoqarin komawa makaranta.....hajja bari naje mu gaisa da sauran mutanen gidan,ummi ce kawai tasan da shigowata,zuwa anjima zan dawo abani abinda aka ragemin"
"Ka taho dai da abinda ka kawomin" dariya ya saki kana ya juya ya fice daga falon.


"A kawo maka abinci ne?" Hajja ta tambayeshi,kai ya kada alamun a'ah,sannan a nutse ya furta
"Idan akwai fura kawai ta isa" sai ta waiwaya wajen zahra,wadda tana son barin falon,amma kuma tana son kallon programe din da ake yi a wani gidan tv,bata so ya wuceta don yayi mata
"Duba fridge wuro akwai damammiya....kayi sa'a kuwa nonon me kyau ne,wanda aka kawomin ne daga can gida adamawa" yunqurawa tayi ta miqe,ta isa fridge din ta ciro furar,saita miqawa hajjan tasa hannu biyu ta amsa silver da nonon ke ciki,wanda har tsatstsafa yake saboda tsabar sanyi ta miqa masa tana cewa
"Kanaji muna magana kan case din inna wuro baka ce komai ba?" Sai daya amsa furar ya bude yasa ludayin dake kai sannan ya daga shanyayyun idanunsa ya kalli hajjan
"Me zance......i dn't know what to say" duk da bata fahimta qarshen zancensa ba amma saita gyara zamanta
"Na zaci a matsayinka na babba zaka nema yaron kaji komai daga bakinsa....tunda a a zahirin gaskiya suna son junansu" kamar bazai amsa ba,don itakam zahra har tayi nisa da hanyar barin falon,tana ta zumbura baki,sam bataji dadi ba data tuntu eshi da zancan,zata zubda mata aji ne kawai,kuma ma ai yana ji akayi maganar da ya sadiq amma baice komai ba,sai daya dan kurbi furar sannan ya amsata
"Ana aure dole hajja?,kika sani ko batayi masa bane?".


Kamar saukar mashi haka zahra taji maganar a qahon zuciyarta,don sai data kasa jurewa ta waiwayo ta dubesu,shikam shan furarsa yake kamar ma baisan me ya fada ba,cikin bacin rai tayi gaba da sauri ta shige dakinta,batasan dai me hajjan tace masa ba,amma ta jiyo muryarta tana magana,saidai bata iya tantance me take ce masa.
23/10/2021, 08:38 - 👍🏻👍🏻: *KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾,karki taba kayan daba naki bane,ba kuma mallakinki bane*



7


Saman madubi ta samu ta zauna cikin fushi ranta na wani irin suya
"Shifa ya haidar din nan rainin wayonsa yawa ne dashi,ya rainama mutane ajawali,meya daukemu ne?,duk laifin hajja ne,ai tasan bana hada shirgina dashi me yasa zata masa zancan matsalata,aikin banza kawai,don yaga mata na hauka akanshi snine hake raina ajawalin mata,koya dauka kowa baka yake,baisan suna mata suka tara ba,mtsewww......aikin banza kawai" a sarari tayi maganarta,kamar da wani a dakin take magana,taja tsaki tana gyara zamanta saman madubin.


Ji tayi xaman dakin gaba daya baiyi mata bama,gwara ta shiga cikin 'yan uwanta ko zata samu sassauci,saita zaro gogagge cikin hijabanta ta saka ta zira silifas dinta ta fito.


Har yanzu yana zaune falon riqe da babbar abokiyarsa wato waya,ya wani miqe qafafunsa saman center table,gefansa furar da yace a kawo masa ce,ya ajjiyeta ba tare da yayi mata wani shan kirki ba.


Harta giftashi bai daga kai ba,sai data kusa qofar fita taji yace
"Ke!" Tasan da ita yake,dole ta dawo
"Ki tabbata gobe a makaranta kika kwana" abinda ya fada kenan a taqaice,dole ta amsashi da to,duk da kuwa ji take kamar ta rufeshi da duka saboda takaici,haka ta fita tana tura baki gaba,ita sam wallahi babu innamal din komawarta makaranta,so tayi ma ta laƙe da wannan ciwon taqi komawa gaba daya,don itakam gaskiya ta gaji,amma yana son rusa mata plan,to Allah yasa babu kowa a falon sanda ya fada bare a tilastata,shuru kawai zatayi da bakinta,suyita wasan buya harya koma hutunsa,tunda dak ai shima ba dawwama zaiyi ba,da wannan tunanin ta shiga sashensu salma.


A kitchen ta sameta tana kwabin doghnout,sosai taji dadin ganinta
"Gwara da kika fito ai,shi yana can wala'alla yana sha'aninsa keya barki kwance,dama yanzu nake cewa bari na gama kwabin nan naje na fiddoki,na kunna wayarki dazun naga kamar ma ya tura miki saqo" baki zahra ta tabe,tana jan daya robar kwabin ta tattare dogon hannun rigarta ta fara tayata tana cewa
"Can masa....gaba daya ma kamar Allah ya fidda minshi a raina,idan ma ya cuceni yaje shida Allah"
"Kawai yafi" daga haka suka shiga wata hirar,zahran na bata labarin abinda ya faru yanzu a falon hajjan,da kuma cewar da yayi lallai gobe ta koma makaranta
"Kinsan Allah ki rufawa kanki asiri ki tattara goben ki koma,kinfi kowa sanin halin ya haidar ko?" Salma ta fada tana dubanta
"Wallahi wannan karon saidai yaci kansa da kansa yasha baqin ruwa,don ni ko zan koma badai gobe ba ehe,ke saima anyi bikin huda dani" dariya salma ta danyi
"Zahra,zahra kafiya,to Allah ya kauda bacin rana"
"Amin" ta amsa mata,salman ta cire hannunta daga flower data gama kwabawar ta wanke a fanfo,tana goge ruwan a rigar jikinta tace
"Bari na dauko miki wayar" baki ta tabe ba tare data ce komai ba,salma ta juya ta fice.


Kafin ta dawo ta gama kwabin itama ta wanke hannunta,harta samu waje ta zauna,ta dawo ta miqa mata wayar tana cewa
"Ga saqon nan,duba ki gani",still baki ta tabe kana ta sanya hannu ta karba din,ta buda saqon ga fara duba tsahonsa kafin ta koma farko da niyyar karantawa hafsa tayi sallama cikin kitchen din riqe da plate din abinci
"Gawa taqi rami,yanzu hajja tacemin aikin fito" murmushi tayi tana maida idonta kan wayar kana ta amsawa hafsa
"Ke kyaso na mutu tun yanzu?" Kai ta girgiza itama tana neman wajen zama
"A'ah ina fa.....salame zubamin miya don Allah inji umma,haka kawai suka mana tuwo da rana"
"Kya samu wata salamen ta zuba miki kuwa amma bani ba" dariya ta saki,tasan sarai bata son sunan
"Afwa tuba nake"
"Kina da hannu ai sai kizo ki diba" tashi tayi ta isa gaban tukunyar ta bude ta zuba miyar,daidai sanda zahra ta fara karanta saqon a fili


_assalamu alaiki,ina me neman afuwa da gafara daga gareki,nasan cewa na miki ba dai dai ba,amma tuntuni naso na samu lokaci mu tattauna kafin zuwan rana irin wannan amma Allah bai nufa,duk da haka ina mai baki haquri,ki sani matar mutum kabarinsa,kuma Allaj yayi keba matata bace shi yasa ban aureki ba,amma idan da hali kuma zai yiwu ki bani dama ki zamto mata ta biyu a wajena,ina dakon amincewarki_

_nuraddeen_


Wani ashar salma taso zundumawa sai kuma ta katse
"Lallai gayen nan yakai qarshe a rainin wayo"
"Tayani gani don Allah" inji hafsa tana kama haba,yayin da zahra ta saki wani murmushi mai ciwo,da kuma nuni da rainin wayon nuraddeen din ya bata mamaki,don daga haka ta zare sim din wayar kawai ta ballashi biyu ta watsa cikin sink din dake kusa dashi,ta kunna famfo ruwa ya korashi
"Na dauki tarayya ta dashi kamar mafarki,kuma ku saka hakan a ranku,mu shiga next chapter da Allah" ta fada cikin dakiya.


Shigowar yusra kitchen din shi ya tada sabon hira,haka nan suke da wuya kaga mutun daya shi kadai,saidai idan dukka basa gidan
"Na zaci munafuntata kukayi ai kuka zauna kuna wainar fulawa aka rasa me kirana"
"To ba ita akeyi ba kwaɗai...." Dariya ta saki
"Allah qamshin manja na dinga ji,kuma naji kamar daga nan ne,kwanan nan sha'awar wainar fulawa nake wlh,mu kuma cikinmu an rasa me soyawa,kowacce sai tace idan ta soya ba zata iya ci ba,ai shikenan"
"Ni kinma tunamin" hafsa ta fada tana ane farantin data gama cin abinci
"Gidansu zainab ahmad din nan?" Tayi maganar da sigar tambaya tana side hannunta
"Eh" suka amsa a kusan tare
"Wallahi suna wainar fulawa da daddare,harda me qwai dame kifi,ke kinji dadinta kuwa?"
"Wayyo Allah,har kinsa yawuna tsinkewa,yaushe zamuje"
"Yauma idan da kudinki"
"Mu bari sai gobe,yau ya usama yamin alqawarin kyautar dubu daya gobe"
"To kuwa muna aljihunki" inji salma
"Allah ya kaimu" ta amsa musu,daga haka suka sake shiga wata hirar kafin kowa su watse.


Bata koma sassan hajja ba,saita wuce sassansu wajen umminta,tunda ta kwanta ciwon bata ganta ba.


A hankali tayi sallama falon nasu,ita daya ce zaune qasan carfet,gabanta da wata babbar baqar leda tana ta fiddo kayan dake cikinta,wanda suka hada dasu madara bournvita,Klein,corn flaks,sabulai,mayukan shafawa,turaruka,maclien,cream salad,suger na qananun jakankuna da sauran kayan amfanin gida na yau da kullum.


Kayan tabi da kallo sannan ta samu waje ta zauna
"Ummi ina yini?" Kai tadan daga ta kalleta kana ta maida ga abinda takeyi tare da amsa mata
"Lafiya lau,ya jikin naki?"
"Da sauqi alhmdlh"
"To Allah ya qara lafiya"
"Amin amin" ta amsa mata,sai shuru yadan biyo baya,wani lokaci ummin nata kaman tana mata halin fulani na kara da alkunya kamar na diyan fari,duk da cewa ba itace ta farin ba,amma itama abun ya shafeta.


"Haka abu kuma ya faru?,sai ki addu'a Allah yasa hakane yafi alkhairi" ta fada cikin yanayi na rashin bawa abun muhimmanci
"Amin" ta fada tana murxa yatsanta.


Bayan shudewar wasu sakanni ummin ta sake cewa
"Kinga irin hidimar yayanku,shi koda yaushe baya gajiya damu,kowanne lokaci alkhairinsa a tafe yake,ko iya hakan ya isa ya bayyanar da nagartarsa,fatana Allah yasa sauran 'yan uwanshi suyi halinsa"
"Ba amin ba,kura ce da fatar akuya" ta fada a ranta,amma a fili don ta farantawa ummin nata sai tace
"Amin" a taqaice.


Ita ta taimakawa ummin aka raba kayan zuwa ma'ajiyarsu,kowanne abu aka sashi a muhallinsa,tadan jima ranar wajenta,ita kuma a fakaice tana jan hankalinta tare da sake nuna mata girman haidar din,sai da suka gama komai sannan tayi mata sallama gab da za a kira magrib ta baro sashen.


Daga nesa ta hangoshi can inda masu gidan dake da mota ko babur suke ajiyesu,tsaye jikin motarsa,booth din a bude ana fidda kayan ciki zuwa sassa sassa na gidan,baki tadan tabe kana ta nufi sassan hajja.


Canma raba kayan ta tadda hajjan nayi,ita da shafa'atu husna da amira dukka jikokinta ne,sai tayi wucewarta cikin daki,bata tsaya ba ta zarce bandaki,ta daura alwala,saboda gab ake da akira sallah.


Kamar yadda taci alwashi kuwa a washegarin bata gayawa kowa yadda sukayi da yaa zaki ba,sai tayi kwanciyarta luf a daki,wuni guda,hajja tana ta mita da yawo tsakanin falon da dakin kan ta fito,ko kuma jikinne?,saitace lafiya lau take,tana ramuwar baccin da bata samu yi ba,har hajjan dai ta haqura ta qyaleta.


Sai bayan sallar magariba su yusra suka shigo,kowacce sanye da hijabinta
"Zamuje gidansu xainab ahmad,na gayawa yayarta ta soya mana wainar gamu nan zuwa"inji yusra tana isa gaban madubin zahran gana gyara wuyan hijabinta,fuska ta yatsina,don batason fita bare suyi karo dashi,tasan haduwarsu ba zatayi kyauba,tunda ya bata umarni taqi ji
"Kuje kawai kwa tahomin da tawa,banajin fita"
"Ki tashi kawai malama mu wuce,babu mai miki dakon komai" tashi tayi ta zauna sosai tana duban yusran
"Kinsan fa akwai jagwal,ya haidar,banaso mu hadu,so nake har sai ya koma tukunna"
"Dazu naga fitarsa ma....ina jin wajen ya zahra ma ya tafi,kinsan ko ba yanzu zai dawo ba" inji hafsat dake gaban madubi tana shafa powder,jin hakan yasa ta miqe ta zaro hijabinta ta ware ta saka,ta sanya slippers dinta sannan suka fito.


Da kallo hajja ta bisu sanda suke fitowa daga dakin suna 'yar hayaniyarsu,har sunyi gaba hafsat tadan dawo da baya
"Don Allah koda ya haidar zai tambaya ina ina kice kece kika aikemu" baki ta tabe tana dubansu
"Babu ruwan fadimatu zahra'u,ku qarke qalau"
"Hajja mu dake fa bata baci" ta fada tana dariya tayi gaba suka fice.


Kusan awa biyu suka kwashe,har kusan bayan isha'i sannan suka fito,suna tafe suna hirarsu har suka qaraso qofar gidan.


Salma ce a gaba,ita ta fara tura qofar gidan,da sauri ta dawo da baya har tana bige yasira
"Dalla meye haka...kefa kin fiya abun haushi wani lokaci"
"Ya haidar.....wallahi ya dawo,suna baranda shida dasu ya abu sufyan" sak kowaccensu tayi,aka koma kallon kallo tsakaninsu,aka rasa me magana har tsahon wasu sakanni.


Zahra ce ta soma jan tsaki,sannan ta soma yin gaba tana jan hannun hafsat
"Tsoron wai na meye,muje don Allah,fuska kawai xamu masa" qarfafa musu gwiwan da tayi yasa suka soma takawa zuwa ciki.


Zaratan samari ne guda hudu saman wasu fararen kujerun roba,aliyyu na biyar dinsu,dan qaramin teburi ne a gabansu dauke da lemuka da cups,sai dan qayataccen qaramin flask din tea da kofunansa.


Kana dubansu xaka gane akwai abinda suke tattaunawa,saidai aliyyun kacokam hankalinsa nakan wayarsa kamar kullum,lokaci lokaci yana dan sanya bakinsa ba tare daya daga kanshi daga wayar ba,hakan yasa sukaji dadi,sannu a hankali suka fara takawa zasu wuce zuwa sashen da yafi kusa dasu.


Kaman an umarceshi ya daga kansa,idanu biyu sukayi dasu,take kowacce tasha jinin jikinta,yayin da zahra ta fara qoqarin boyewa sosai ta bayansu yadda bazai iya ganinta ba.


Sunan hafsa ya kira,ta amsa kana cikin hanzari ta nufi inda yake,bata wuce sakan biyar ba ta dawo
"Ya haidar

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment