Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai da suwaiba ba,don haka da badi'a suka gaisa kawai,ta diba kayan wankanta ta shige bandakin tayi wanka,sannan ta fito ta dauki kayan da zata saka ta wuce dakin hajja donta shirya,saboda ta fuskanci kamar suwaiba ta sanyawa duk wani motsinta ido,batason ta fusata harta buda baki ta gaya mata magana,shi yasa tabar musu dakin da niyyar kwana dakin hajja.


Saman abun sallah ta tadda hajjan,da alama idarwarta kenan,ta dubi xahran,saidai batace komai ba,har zuwa sanda ta gama addu'o'inta,ita kuma zahran ta gama shirinta,tayi tsalle ta haye gadon hajjan,sai a sannan ta magantu
"Ke zahra'u....tashi kije ki amshi abinci wajen gaje ki kaiwa yayanku"
"Habba hajja,don Allah ki qyaleni mana na huta,ni wallahi bacci nakeji" ta fada tana tura baki,dakewa hajjan tayi
"Tashi ki fita ki bani waje....billahillazi idan na fito na ganki a sassan nan....ke bama sassana ba ko ina nema sai ranki ya baci,ki amshi abinci ki kai masa ya kirani yace a kawo masa,kuma babu uban da zaije kaiwa mijinki abinci...." Tana tura baki tana komai haka ta sauko ta daga saman gadon,har takai bakin qofa ta sake kiranta
"Ba abinci kawai nace ki kai masa ba,karki dawomin sai gobe,idan kinqi ji kuma ba kyaqi gani ba" ko waiwayawa ta dubi hajjan batayi ba tsabar takaici ta qara gaba,itakam gaskiya hajja tana son wuce mata gona da iri,idan batayi wasa ba ta tattara ta koma makaranta zasu jima kafin su ganta,kowa ma a gidan ta shafeshi.
23/10/2021, 08:48 - ๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป: 36
*KIJI TSORON ALLAHโ˜๐Ÿพโ˜๐Ÿพโ˜๐ŸพKADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*




Tana tafe a hanya riqe da kwandon kayan abincin kamar ta sakesu ta sanya kuka saboda takaici,ji take gaba daya hajja ta gama takura rayuwarta tako ina,tana wannan qunci har takai qofar dakin nashi.


Turawa tayi hadi dayin sallama qasa qasa,alamun ranta na a bace ne,a lokacin yana zaune saman kujera,ya miqe qafafunsa lan center table dan qarami dake gabansa,system ce saman cinyarsa yana typing da mugun sauri,da alama wani muhimmin magana yakeyi,dakin a dan hargitse yake da kaya.


Sau daya ya daga kai ya kalleta ya amsa sallamar ya maida kansa ga system dinsa,saita qaraso a hankali ta aje kwandon gefanshi,tsaye tayi ta rasa meye abunda zatayi,tana tunanin ta koma idan yaso hajjan tayi kwadonta ta cinye,idan kuma ta zauna din kamar ta zubda kanta ne,zaiga ita ta kawo kanta ma kenan,kamar tadda yayi mata sharri a abuja.


Sake daga kai yayi ya dubeta,idanunta nacan wani sashen daban,don ta jima bata iya hada idanu dashi,tun lokacin da wancan abun ya faru,duk yadda yakai ga qwaqwqwafi da qwaqwar su hada idanun bata yarda
"Have a sit please.....bana son tsaiwa" ta jishin,saita samu waje tana zama din,cikin ranta tana mitar har a gayawa soja tsaiwa zaice wani baison tsaiwa,takaicinsa ya sake cikata,ta rasa me zata masa ta fanshe haushin da hajjan ke cusa mata a kanshi,don haka ta tsiri zuba mishi abinci,kowanne plate saita cikashi ta tura gabanshi,shi sam baisan ma me ake ba,harta gama zubawar,saita miqe ta nufi dan qaramin fridge dinsa dake dakin ta bude.


Jere yake da hadaddun zobo,wanda da alama jin zuwansa yasa umminta tayi masa,tunda dama itake masa,saboda din mutum ne da idan ba dole ba bai fiya son lemon kwali roba kona kwalba ba,yafi gabe gagajiya,zobo ginger ko kunun aya,su yafi sha indai yana gida.


Murmushin mugunta ta saki,babu abinda zai dace da tsarin ta irin zobon,ta ciroshi cikin wata kwalba me kyau da ummin ke aikawa can wani store ana siyo mata ita,tana yanayi da jug amma ba jug bane,dan tsukakken bakine da ita,sata hada da cup din data gani saman fridge din ta taka a hankali ta koma wajensa.


Sai data iso dab dashi ta soma tsiyaya zobon,taf ta cika kofi,sai kawai ta saki cup din ya sullube daga hannunta,ya kuwa fada saman cinyarsa,take ya masa wanka a fararen kayan dake jikinsa,ya kuma fantsame har screen na system din da yaketa faman latsawa.


Cikin ba zatar zubar abu mai sanyi daya ji a jikinsa ya daga kai yana dubanta,tana tsaye a kansa,saidai tayi narai narai da idanu alamun rashin gaskiya,baice mata komai ba sai qoqarin kashe system din da yake saboda karya shiga ciki.


Sai data fara shutting down sannan ta tsinci muryarsa
"Kin saba ai" tayi mamaki da taji iya abinda ya fada kenan,saboda ita da gaske fusatashi takeson yi,saidai batasan lamfo yayi mata ba,sai daya gama kashe system din,ya janye dukka takaddun da yaga zasu baci sannan ya miqe.


Idanu ta zura masa qirjinta na bugun uku uku sanda taga ya nufota,hannusa guda daya cikin aljihun wandonsa fari daya baci face face da zobo,wani taku yake slowly,saidai ya aza qwayar idanunsa cikin nata sosai,wanda hakan taji ya mata nauyi matuqa,ya kuma qara mata fargaba,duk da haka ta kasa dauke qafarta ta ษ—ara daga inda take tsayen harya cimmata.


Wata iriyar tsaiwa gab da juna sosai,har yatsun qafarsa na dungurin nata,har yanzu kallon qwayar idanunta yake data kasa janyewa daga cikin tasa,hannayensa ya daga sama gaba daya,kamar wanda yayi laifi aka kamashi yayi surrender
"Farashin da zaki biya wannan gangancin da kika yimin shine,ki cire kayan jikina ki daurayemin jikina da kika batamin haka kawai ina zaman zamana.....na yafe miki wankin kayan.....don yanzu dana saki ma waccar tsohuwar zata isheni da kwarorota da terere" kamar ya dauko guduma ya kwada mata haka taji,tsoro da firgici suka cikata,saboda daga yanayin yadda yake maganar ya tabbatar mata cewa da gaske yake bada wasa ba,ta kalli hagu da damarta,ko ina ya tare babu wajen kubuta,amma zata gwada,don kome zai mata ba zata iya abinda yace din ba,gwara ya mata duka da bulalarshi yafi mata sauqi.


"Am so sorry" ta samu kanta da furtawa cikin rawar murya,sake hade rai yayi tamau
"A soron gidanku nake kwana?" Yayi maganar yana dage mata dukka girarshi,saita kada kai
"Kayi haquri....banfa sani ba" kanshi ya kautar yana sake hade rai
"Sanda aka raba haquri bacci nakeyi" saita ware idanunta duka,wai dama ya haidar din ya iya magana haka,harda su baqar magana duka?
"To ka cire kayan....ka bani Allah xan wanke"
"Banaso,nima ina da hannu,and bakisan ni qazami bane....daqyar nake iya yin wanka?,kinga shine xaifi bani wahala ba wanki ba" sake zare ido tayi,tasan dai zaginta kawai yake,mutumin da idan heater din sassansa ta samu matsala kowa a gidan ya banu da dafa ruwan wanka.


Ta gama fahimtar bazai haqura ba dai din,don haka ta faki idanunsa,tayi wuff da niyyar guduwa,saidai taku uku kacal tayi taji an danqi hannunta
"Baki isa ba,ki batan jiki,ki batan kaya ki batamin guri kuma sannan ki gudu?,selfish girl".


Qafa ta soma bubbugawa tana tara qwalla ko zai tausaya mata,yadda dai takeqa hajja ta karya mata zuciya,saidai abinda bata sani ba,hakan da takeyi tsokano 'yan maza takeyi,saboda ko ina na jikinta dake rawa,idanunsa ya lumshe ya dora yatsansa saman labbansa bayan ya bude idon yace
"Shshshsh......ni banyi kuka ba saike?,zan baki another option.....koki wankemin jiki,ko na wanke da kaina,amma fa yadda kika jiqani kema saikin jiqe" da sauri ta gyada kanta,a tunaninta wannan shine zaifi mata sauqi,saboda tayi zato zaya dauko zobon ne ya kwara mata shikenan an wuce wajen,saidai ina,kafin takai ga wani tunanin sai ji tayi kawai ya dauketa gaba daya yayi bandaki da ita.


Cikin kwamin wankan daya cikashi da ruwan dumi ya jefata,wanda a niyyarsa dama idan ya gama cin abinci yayi wanka ya samu ya kwanta,tuni idanunta suka raina fata sanda ya salube hijabin jikinta,tuni rigarta ta lafe sosai a jikinta,ta bayyana duk wata halitta ta jikinta,gashin kanta da yasha ruwa shima yabi wuyanta ya kwanta,tuni ta dunqule waje daya,saboda ta fuskanci babu wata mafaka ko matsera.


Shi kuwa baya ya juya mata,haka kawai murmushin yadda tayin ya subuce masa,yakai geji,yana jin ya kamata ko yaya shima ya dana.


Batayi aune ba saijin mutum tayi tsulum cikin ruwan,da sauri ta daga kai don yin qorafi,amma suna hada idanu ta maida kanta qasa,qirjinta na wani irin bugawa,zuciyarta kamar xata fito,bata raina kanta ba sai daya dauketa gaba daya yayi mata masauki a qirjinsa,cikin hanzari ya ware hannayensa ya soma yawo dasu ko wane sashe na jikinsa,duk wani waje da yasan yana tsole masa idanu.


Cikin lokaci qanqani ta gigice,tana tuna abinda ya faru kwanaki uku ko hudu baya kada ya sake maimaita kansa,shikam ko a jikinsa,sai da yaga dama a qashin kansa sannan ya saurara.


Wankansa yayi har a sannan bata iya kallonshi ba,sai daya gama ya daura babban towel a qugunsa,saiya bude rariyar ruwan ya fita ya tara mata wani
"Zaki iya wanka" daga haka ya taka ya fice.


Tana qananun qwalla tana wankan,a haka harta kammala,sai kuma ta rasa me zata sanya ta fito?,idan ma ta fito din wanne kayan zata sanya tunda wanda tazo dasu sun jiqe?,towel ta hanga don haka dole shi ta daura,Allah yasa ya cire mata hijabin bai jiqe ba,saita saka shi ta fito daga toilet din a hankali kamar wadda ta yiwa sarki qarya kanta a qasa.


Waje daya ta samu ta zauna sanda ta fito din,yayin da yake gaban mudubi yana shafa mai,wani wasai yakejin ranshi da gangar jikinsa,wani shauqi da baisan daga ina ya taso ba yana ratsashi,itadai batasan me ake ciki ba sai taji sautin muryarsa yana cewa
"Hello hajja.....a samu yaro ya kawo mata kayan sawarta" shuru ya danyi da alama silleshi hajjan take,don murmusawa yayi kadan sannan yace
"Gani nan....zanzo na dauka da kaina" da haka ya kife wayar,ya qarasa shiryawa a gurguje ya fice,saita bishi da kallo tana dora hannu saman ka,shikenan ya janyo mata,ta shiga uku wajen hajja,tasan wallahi watan yi mata tijara ne ya kama,yanzu duk wanda yaga yaje dauka mata kaya saiya dauka wani abunne ya faru,kawai sai taji hawaye yana sauko mata.


Ya kusa minti goma sannan ya dawo,ya zube mata kayan wajen kala uku,abun kunyar ma data daga harda undies dinta da bra,ji tayi kaman qasa ta tsage mata ta shige,sauqinta daya ma daya dan fita ya bata waje ta shirya,bayan ya dawo yana daga zaune yasa tayi serving nasa,saita samu waje ta zauna bayan ta gama,lokaci lokaci yana satar kallonta,murmushi na subuce masa,can qasan ransa ya furta
"Silly girl,zanyi maganin wannan tsiwar taki" yana kallonta tayi kwanciyarta saman kujera,baice da ita komai ba,saida baccinta yayi nisa kawai ta tsinci kanta saman gadonshi,ta motsa yace da ita
"Kina tashi akwai punishment,just sleep" saita maida kanta ta kwantar tana irga qarfin hali da iya qarfa qarfa na ya haidar din,ita gaba daya kwance mata kai yakeyi,dukka halayen da take gani yanzu tattare dashi mugun baqin halaye ne da babu wanda ya zaceshi dasu
(Ni kuwa nace matar mutum ai ba wasa ba,duk wanda ke cika baki akan mace ba'a biyo ta kansa bane),ta qasan ido take hango duk motsinsa,saboda bayan yaci abincin aikinsa yaci gaba dayi,saidai wannan karon rubuce rubuce ne yaketa yi wanda batasan na meye ba.


A hankali qamshinsa daya kama zanin gadon da abun rufarsa ke ratsa qafofin hancinta,wani tattausan qamshi data kasa banbance na meye da meye,tun da can kusan lambarsa kenan,dashi ake gane yana waje,har zuwa yanzu kuwa duk wanda ya sanshi ya sanshi da qamshi,sannu sannu take shaqar iska zuwa hunhunta har wani bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba da ita.


*_WASHEGARI_*


Tun bayan sallar asuba bacci ya sake daukarta me nauyi,ita da tayi niyyar zata gudu tunda duku duku,don ba zata iya hada idanu da jama'ar gidan ba,sai gashi bacci ya kwafsa mata,ba ita ta farka ba sai goma saura.


A rude ta sauka daga gadon,saita hau juye juye,babu kowa cikin dakin sai ita,don haka ta nufi qofa da hanzarinta tana addu'ar kar ya shigo har sai ta fice,don babu abinda taqi jini irin su hadu a yanzun,idan ta tuna abinda ya faru jiya ji take kamar qasa ta tsage mata ta shige.


Saidai ta makara,addu'arta bata ci ba,tana murda handle din shima yana murdawa,sai sukayi kacibus bakin qofa,yadda ya sako kai gaba daya yana tsareta da idanu ya sanyata ja baya ta bashi hanya ya shigo.


"Ina kwana" ta gaidashi tana kauda idanu,ya amsa mata da
"Kin tashi lafiya?" Saita kasa maida masa amsa,bai damu ba yace
"Muje....ciki nima zan shiga" da sauri tayi gaba,kamar wadda ake tsunkuli
"Easy mana" ya fada yana taddota,suka jera kafada shi da ita
"Ko sau daya mana,yau kawai hajja ta yaba mana" da xata iya juyawa zatayi ta maka masa harara,wanne yabon hajja ita takeso,bayan ta kaita ta barota,babu wani abu a jikinta a yanzu da baisan wajen zamansa da size dinsa ba,itakam ai sun gama da ita shida hajjan,bai sake cewa komai ba itama haka,haka suka ci gaba da takawa har zuwa cikin gidan.


Duk wanda suka gamu dashi sai taji kunya ta kamata kamar ta shige qarqashin qasa,musamman da sukaci karo da abba babba,cikin farinciki yake dubansu sanda suke gaidashi,harda yi musu addu'a sannan suka wuce.


"Muje ki fara gaida ummi" yace da ita yana tareta daga yin sassan hajja,saita bishi suka wuce sassan ummin tata.


Tana cikin yin breakfast suka shiga,saita ture kwanon,fuskarta itama cikeda jin dadin daya kasa boyuwa take amsa gaisuwarsu,haka taci gaba da binsu da kallo har suka fito daga sassan
"Kinsan girman ladan sanya farinciki a zuciyar iyaye?,muje ki gaida mama itama" ya fadi yana nuna mata hanya,bata ce masa uffan ba ta bishi suka isa sassan maman,ita dinma kamar sauran,farincikinta bai boyu ba,hatta da momy da suka gaisar,sai jikinta yayi sanyi,dukka wannan farincikin na meye?,na ganinsu ne tare da Aliyyun kawai?,da wannan tunanin suka wuce sassan mai gayya mai aiki hajja.


Dukkansu suna falo harda me jego,suwaiba da badi'a,saisu anty aliya da suka zo suyar nama,idanun da sukayo kansu gaba daya sai taji kamar zata zube a qasa,kunya kamar ta kasheta,saita dinga mammazewa,ta qarasa cikinsu ta gaidasu,hajja ce dai sai data tura mata qeya sannan ta amsa.


Bayan sun gaisa haidar din yadan zauna a cikinsu anty aliyan,abinda yakan jima baiyi ba kenan,ba kasafai suke samun damar zamansa cikinsu ayi hira sosai ba,sai lokaci lokaci,hakan ya sanya zahra barin falon ta shige dakin hajja,don nata dakin su suwaiba su shige ciki.


Tana nan kwance hajja ta shigo dakin yakai sau uku,a fakaice take mata habaici a waqe anaso ana kaiwa kasuwa,irin salon waqoqin mutan da din nan,dadai ta gaji da habaicin hajja saita miqe ta fice tabar mata dakin.


Har yanzu yana falon shida anty aliya da anty nusaiba,zata wuce kitchen ta samu abinda zataci taji suna masa godiya,da alama ya musu irin alkhairin daya saba ne.


Inna gaje ce kawai a kitchen din,sai tayi zamanta kawai a ciki,ta hada mata abincin ta soma ci suna hira,ita dinma zancan haidar din take mata
"Ai gaskiya uwar masu gida kin dace,kinyi dace da mijin qwarai mai hannun alkhairi,inda ace shidin wani hamshaqin attajiri ne Allah ne yasan mutum nawa me zasuyi kudi ta sanadinsa,ko a yanzun ma ya zama inuwa ga mutane da yawa,saidai addu'ar Allah ya qara arziqi" murmushi ta yiwa inna gajen kawai,ta can qasan ranta sai taji zuciyarta na amsawa da amin............
23/10/2021, 08:48 - ๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป: 37

*KIJI TSORON ALLAH,โ˜๐Ÿพโ˜๐Ÿพโ˜๐ŸพKADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*



Washegari kuwa qaryar ciwo ta yiwa hajja bayan ta gama hada kayan da xata koma makaranta dasu a washegari,tayi kwanciyarta da wuri,duk da baccin bai dauketa ba amma tasha chart dinta,har daga bisani baccin gaske yayi gaba da ita.


Tunda ilham ta kawo masa abincin yace ta ajiye a nan,tsahon wani lokaci yana zaune,shi baici abincin ba,bai kuma ce a fita dashi ba,haka kawai duk yaji baya cikin sukuni,abincin ma baya sha'awa ci,xuwa wani lokaci sai gashi ya miqe,ya saka hannu ya bude dakin,ya leqa farfajiyar waje kamar me neman wani abu,daga baya kuma ya rufe qofan ya dawo ciki yana jan tsaki.


Gaban kwanukan abincin ya dawo ya soma saving kanshi,abinda ya jima rabon da yayi,tsakula kawai yayi yaji cikinsa ya cushe,saiya tura abincin gefe ya miqe ya nufi bakin fridge don dauko abin sha.

******** ***** ********


Tsaye take dakin hajjan rataye da qaramar jakarta,tana tsayen amma sai faman duba agogo take,tana so ta isa akan lokaci ne,akwai lecturer din dake nemansu,kuma tasan halinsa sarai,mtuqar ta wuce lokacin tofa ba shakka ko dawa take yawo ba zai bari ta shiga ba.


"Don Allah hajja ki sauri....zan makara fa" ta fada a shagwabe,saita rufe akwatin data bude din,ta miqa mata baqar leda
"Gashinan,ki tabbtar komai dake ciki kin shanyeshi kafin dawowarki gidan nan,Allah ya tsare....ina shi haidar din?"
"Munyi sallama fa,bacci yake,mustapha zai kaini" idanu hajjan ta tsareta dashi,bata yarda da zancanta ba,don tun jiya taga tana aiken yara suna siyo mata abubuwan da bata dashi a kantin layinsu da ษ—ai da ษ—ai,ta mata shuru ne kawai tayi kamar bata gani ba
"Motarsa kam dama ai wajen mustapha ta kwana,don ya aikeshi gidan innarku da safe zaije yakai mata saqo" qafa ta bubbuga
"Wai hajja yarda ne bakiyi dani ba"
"Na yarda dake,Allah ya kiyaye hanya" ta fada tana tattare kayanta data fito dasu,sanadin daukowa zahran abinda ta batan,ta san sarai indai baisan da tafiyarta ba bazai qyale ba,don baya daukan irin wadan nan abubuwan.


Sai data shiga ta yiwa duk mutanen gidan sallama,bata tarda mama ba ta fita tun sassafe dubiya,umminta dubu biyu ta bata,sai taqi karba,duk da ta yiwa account dinta tas saboda siyayyar data yiwa kanta da kanta,don kada ta tambayi haidar din,wanda tunda take bata taba yiwa kan nata siyayya ba sai wannan karon.


Gaban motar ta shige sanda mustapha ke kunna motar,ya tasheta suka fice daga gidan.


Tun basuyi nisa ba suka soma hirarsu yadda suka saba,cikin raha da zolaya,gab da zasu shiga farawa wayar mustaphan tayi tsuwwa,sai zahran ta xolayeshi
"Tun daxu ake faman kiranka,hala wata mai rabon wahalarce" ta fada tana sheqe masa da dariya
"Allah kinga makwancina da yawa.....ki zuba ido,sai nafi mijinki kudi,kibar ganin aikinmu har yanzu baizo hannu ba,hausawa suka ce gayawa wanda ya tara ya kiyayi me nema.....kai shine ma ke kira" ya fada yana zaro ido,sai zahran ta qyalqyale da dariya
"Qaryar kawai,ashema cika bakin naka bai kai ba,tunda gashi daga ganin sunansa kawai ya saka fargaba" hannunsa daya ya daga
"Na yarda wallahi....ke....kinsan soja kuwa....hmmmm" daga haka ya daga wayar,ya sanyata a handsfree.


Husky voice dinsa ce ta cika wayar,kamar bai jima da tashi a barci ba
"Kai kana ina?" Ya tambayeshi a dake,cikin girmamawa yace
"Gamu a hanya zan maida inna wuro makaranta"
"Waye ya baka izini?" Ya jefa masa tambayar data saka mustapha ware idanu yana duban zahra,wadda itama shi take kallo,dukkansu gabansu na faduwa,bai iya amsa mishi ba ya tsintoshi yana cewa
"Duk inda kuke ku dawo yanzu yanzun nan" daga haka ษ—if ya katse wayar,saiya soma neman wajen tsayawa,ya gangara gefan titi zaiyi reverse.


Kallonsa zahran tayi
"Wai komawa zakayi?" Girarsa ya dage duka yana kallonta sannan yace
"Eh mana....au so kike nace masa a'ah,tab....wallahi bazan iya ba,ke da kike matarsa ma bakice komai ba saini"
"To gaskiya malam tsaya na fita,na tari wata ta kaini,saboda indai banyi attending class ba daganan zuwa lokacin da lecturer din yace ba da wuya bai zame min matsala ba" lock yayi sauri ya sanyawa qofofin sannan ya fara reverse yana cewa
"Kinsan Allah ba xaki jawomin ba,ai kiyi haquri kawai na miqa masa ke da motar sa".


Kafin su isa gida kuwa mita da qorafi mustapha ya shata,kamar ma shine haidar din,shidai dariya yake sheqa mata
"Sai dana tambayeki ya san zan kaiki kika ce eh,to ashe ma ko sallama bakiyi masa ba,bayan kinsan halin guy din nan,ba'a canza masa ko take masa doka,nidai na kaiki lafiya shine kawai mafitata a wajensa" .


Suna shiga harabar gidan ya sake kiransa
"Ok" kawai taji yace,ya kashe wayar sanda xahra ke tambayarsa
"Me yace?"
"Yace nakai masa key din" haushi takaici da baqinciki ya cika,wato ita bata ga tsuntsu bata ga tarko,saita balle murfin motar ta shige sassan hajja.


A falo ta sameta zaune tana karyawa,ta dinga kumbure kumburenta da qunquni amma hajjan bata ce mata ci kanki ba,a haka har kusan awa daya,wanda tuni ta fara qwalla,sai ga husna ta shigo,tace wai ta fito inji ya haidar,jakarta ta figa tafita kamar jakarce tayi mata laifi,ko magana bata yiwa hajjan ba,ita kuwa hajja sam bata damu ba,murmushi kawai ta saka,saboda hango tarin nasarori daga wajen haidar,wanda ta tabbatar nasarar da zata samu akan haidar,ita zata kai har kan zahran.


Yana zaune gaban motar ya kamo sashen labari na bbc hausa yana sauraron labaransu na ranar,yayi masifar kyau cika da kwarjini cikin qananun kaya,idanunsa saye cikin wani sunglasses mai azabar kyau qirar wannan shekarar,wanda glass din ya qara masa kwarjini qwarai,jikinsa ba abinda yake fitarwa sai qamshi mai sanyi,wanda yacakuda da qamshin freshner na motar da sanyin ac dai wadda baya rabo da ita.


Tana shiga motar sanyin daya cikawa motar ya sanyata yin gulmarsa a ranta,taja murfin motar ta rufe,sannan ta waiwaya kadan tana gaisheshi,ko kallonta baiyi ba ya tada motar,ya jata da gudu suka fice daga gidan,saita lafe jikin murfin motar kawai,tana jin bugun zuciyarta yana sauyawa.


Shuru ne ya ratsa motar sanda yake tsala gudu dasu saman hanya,duk da suna cikin gari basu fita wajen gari ba,ta karanci shima gwanin gudu ne sosai a mota.


"Kin rainani ko?" Ta tsinci muryarsa yana fada a taqaice,dan waiwaya tayi ta dubeshi kafin ta dauke kai,kansa da idanunsa suka suna kallon titi ne,kasa amsawa tayi,sai tayi shuru tana murxa yatsunta kamar yadda shima yayi shurun,kamar bazaice komai ba kuma saiya bude bakinsa gently yace mata
"Ko auren uwaka ubaka mukayi dake auren tasha nidin mijinki ne,kinda da haqqi wuyana kamar yadda nima nake da haqqi wuyanki,bare ma aurenmu yafi gaban nan,koda bakiso bani so,koda babu shaquwa a tsakaninmu,tunda iyayenmu mutane mafi daraja a rayuwarmu su suka daurashi,fita babu izinin miji haramunne kuma ba dai dai bane....sannan komai niya kamata na zama a sahun gaba wajen sani kafin kowa.....so please.....please kada ki sake,idan ba haka ba saina daure qafafunki a inda ake daure qafafun marasa ji irinki" maganganunsa sunsa jikinta yayi sanyi,saita tsinci kanta da furta
"Kayi haquri" softly,wanda hakan ya bashi mamaki,sai kuma yaji dadi har cikin ransa,kamar yadda itama mamaki ya kamata,tayi tunanin zai balbaleta da fada ne har yayi ma kamar zaya daketa,kamar yadda yake musu acan baya idan sukayi laifi,ko kuma zai gaggaya mata magana,ko yace ta tafi a motar haya,a haya suke hangen halinsa,mutum mai kushin hali fushi da fada,kafiya da taurin kai,amma sai taga duka baiyi ko daya ba,ya gaya mata magana ce ta hankali,wanda duk me hankali ta isheshi ya fahimta cikin ruwan sanyi,basai an qara masa da wani abun daban ba.


Bata yanke daga wannan tunanin ba

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment