Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana cewa
"Wai komai mutum yayi shi bai iya ba,inafa zaman zamana kika ce sai na masa abinci....inda naqi tashi kuma nan ma qilu ta jawo bau,nayin kuma nan ma ban miki gwaninta ba....to inaga kawai a fasa kai abincin"
"Iyeee.....to uwata,ni meye nawa a ciki idan baicin bama,asarata ko taku keda shi?,ki tambaya kiji,mijina bai taba neman abinci ya rasa ba wajena har ya mutu,girki ma daya amsa sunansa ba irin nakun nan ba taba ka lashe....wanda kula da mijinma kamar an muku gori sai ance kuyi,yo ni meye nawa afasa kai masa.....kai....mustapha" tahau qwala kiran gangan da ganganci,don tasan mustapha baya falon,baya ma gidan gaba daya,tun safe abba yusuf ya aikeshi gyaran motarshi,ai kam a sukwane ta saki kwanon hannunta cikin sink ta isa gaban kwanukan
"Saiki bari na bayar da kaina nida nasha aiki,amma kya kira ya musty mai shegen ci da saiya kusa hadawa da flask din duka ya cinye ma?" Dariya sosai ta qwacewa hajja ba tare data shirya ba,sai kuma tadan maze bayan ta gama dariyarta
"Ya suke da mijinki wajen shegen ci,kijimin yarinya" itadai sai raba ido take,kada hajja tayi mata aika aika,bata sake tanka mata ba har ta gama abinda ya kawota kitchen din ta fice abinta ko a jikinta.


Gangar jikinsa ce kawai zaune waje daya da sunan hutu,amma gaba daya zuciyarsa da qwaqwalwarsa sun gaza samun hutun da yake buqata din,ga yunwa da yakeji amma ya kasa katabus,minti daya biyu saiya dubi qofar shigowa sashen nasa,haka kawai jikinsa ke bashi tana nan zuwa gareshi kowanne lokaci,saiya yunqura zai tashi ya aiwatar da abinda zuciyarsa ke gaya masa,sai kuma miskilanci ya maidashinya zaunar,yana sonne ya tabbatarwa kansa cewa aikinsa yayi kyau?,duk da ya fara ganin alamomi da suka sanya ya baiwa kansa mark,tare da shanshano qamshin nasara,mutum ne shi daya tashi kaf rayuwarsa cikin cimma nasara kan abunda yasa gaba,matuqar nasararsa ta kasance......to wannan shine mataki na qarshe da zai kawo qarshen komai.


Miqewa yayi a karo na qarshe,yana jin juriyarsa da haqurinsa sunkai qarshe,bazai iya ci gaba da zaman jira ba,saidai yana isa bakin qofa yaji an murda handle din an turo qofar,dai dai sanda wayarsa ta dauki ringing,saiya dakata daga bayan qofar,ya ciro wayar yana dubawa.


Daya daga cikin jami'ansu ne me suna Deborah,tana qarqashin jagorancinsa,saidai ita din likita ce,wadda sanda suka dawo yabar kulawar sojojin da suka dawo dasu marasa lafiya da masu rauni ana kula dasu a asibitinsu,itace kuma shugabar likitocin ya buqaci zamun duk wani bayani bayan ya tafi kan ci gaban da aka samu kan marasa lafiyan,babbar macace sosai,don tayi shekara a qalla arba'in da takwas,kaf cikin ma'aikatan mata ita kadai yakewa dariya,saboda yana ganin girmanta kamar yadda take ganin nashi.


Mummunar faduwar gaba hadi da bacin raine suka bijiro mata sanda taji ya ambaci sunan mace cikin wayarsa,hakanan yana wayar cikin sakin fuska,abinda ba zata iya tune yaushe ne lokaci na qarshe data jishi yana waya da wani koda namiji bane cikin walwala haka,wani abu ya taso ya tokare mata maqogaro,har yasa kunnuwanta suka toshe,ta daina ji ko gane maganar da yake,maganganun da hasashen da zuciyarta keta kawo mata su take fahimta,don haka tana dire kwandunan hannunta tayi hanyar fita ba tare data ko kalleshi ba.


Duk takunta daya idanunsa na biye da ita,sai hankalinsa ya rabu biyu,rabi naga wayar da yakeyi,rabi kuma na akanta,karon farko daya taba qarewa tafiyarta kallo,kamar wadda ke rangaji haka takunta suke a tsare,saidai yanayin halittarta ne hakan,batasan ma hakan na faruwa ba.


Ganin ta nufo qofar gadan gadan saiya taka a hankali ya qarasa rufe qofar,ya murza muqulli ya rufeta gaba daya,sannan ya jingina jikinsa da qofar,sai ya zaman shida ita suna fuskantar juna.


Zata iya cewa bataji ya yiwa wadda suke wayar sallama ba,yadai zame wayar daga kunnensa ya jefata gefanshi,tsintar kanta kawai tayi cikin jikinsa,ya mata wata kyakkyawar runguma da taso zabge duk wani baci da ranta yayi kan wayar da yayi yanzun.


Tuni jikinta ya soma mutuwa saboda qamshij da jikinsa ke fitarwa,da wani irin dumi dake fita daga jikinsa zuwa nata,amma duk da haka ta aje wannan gefe,ta soma turashi da yunqurin barin jikinsa,da sauri ya sake yi mata qawanya da hannayensa yana sake yi mata kyakkyawan mazauni cikin qirjinsa yana fadin
"Ke......relax mana,kada kiyi kishi....abokiyar aikina ce fa,nothing else" mamaki ne ya kamata sosai,ya akayi ya karanci haka daga idanuwanta kawai?,kamar me aiki da sihiri,ko kuma wanda ya karanci ilimin sanin halayyar dan adam.


Mintuna a qalla kusan biyar suna tsaye a haka,shuru ba tare da ya sake cewa komai ba,ita dinma haka,kowa na sauraren bugun zuciya da fitar numfashin dan uwansa,ita kanta batasan ke ya debeta taci gaba da zama cikin jikinsa ba,sai taga ya kamata tayi koda pretendin ne,kada ta zubda kanta
"Ka sakeni" ta fada tana tura hannayensa,da sauri ya hannunsa ya birkitota ta dawo tana fuskantarsa,a maimakon dazu data bashi baya,hannayensa duka biyun ya sanya ya kama qugunta ya ruqe yana qarewa fuskarta kallo,cikin wata murya mai laushi da sanyi,can qasan maqoshi wanda koda kana kusa dasu sai ka kasa kunnenka sannan zaka iya jin abinda suke fada yace
"Zahra...." Mamaki ya kusan kasheta a tsaye a wajen,dama yasan sunanta ne?,eh dole tace haka,saboda tsahon rayuwarsu cikin gidan bata taba jin ya ambaci sunanta ba ko a wasa,ji tayi duk duniya kamar yafi kowa iya ambaton sunanta,kamar ya fadi sunan nata ne da wani yaren daban ba hausa ba
"Ke kadai ce rayuwata bata da amfani cikin taki rayuwar ko?" Ji tayi tambayar ta mata nauyi sosai,bata kuma gama fahimtar abinda ya fada din
"Yes....kowa yayi kewata amma banda ke....kowa yana nemana amma banda ke,kyautawa kenan?" Lallai yau mamakin da haidar din yake bata ya wuce tunaninta,da zata iya zata so ta daga kanta ta kalli idanunshi da fuskarshi,don ta samu tabbacin daga bakinsa kalaman ke fita
"Kin kyauta....matsamin daga jiki" kamar me jira kuwa ta janye jikinta,haushi ya cikata taf,ita din ya nemeta?,sau nawa yana kiransu hajja tana wajen ba wanda ya taba bi ta kanta,kwanciyarta a asibiti saboda waye tayi?,ko don ba zata iya gaya masa bane.


Caraf aka riqe hannuta,ta waiwayo da sauri don har ta soma yin gaba,fuskarshi a hade kamar bashi ne yayi maganar da yayin dazun ba,saiya sakar mata hannun sanda take zamewa itama daga hannunsa,ta juya zuwa inda ta ajjiye abincin ya bita a baya,ya samu waje ya zauna.


Duk wani motsi da zatayi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wanda hakan ke sake narkar da ita,kamar zata saki kuka haka takejin zuciyarta na rauni,wani abu mai qarfi yana ratsata loko da saqo,daidai sanda ta kammala zuba mishi abincin wayarsa ta dauki tsuwwa,hajja ce saiya daga kanshi tsaye,ya kuma sanya handsfree
"Zaki.....maza ka turomin innawuro....hadari garin" shuru yayi yama kasa amsawa hajjan,shi abun nata ma mamaki yake bashi,haushi ya kuma cikashi sosai,da gaske wannan karon yaji haushi har ransa,don haka yace
"Gata nan,daga yau a dinga turo min mustapha shamsu ko ibrahim su dinga kawomin abincina" saiya katse wayar,tana jinsa bata waiwayo ba,saita qara wuta,dama neman hanyar tafiyarta cikin sauqi take,don ita kadai tasan yadda yake qara wa zuciyarta pressure,tana jin kamar ba zata iya dogon xama dashi ba.


Tana fita ruwa ya tsinke,saita tsaya cak tana kallon yadda ruwan ke sauka daga sama da gudunsa,shahada tayi ta saka qafarta ta fara takawa cikin ruwan,wata walqiya me azabar haske aka saki,take ta haska ko ina kai kace tsakiyar rana ce,cikin sakanni ta dauke,kafin ta gama mutstsika idanunta da walqiyar ta kashe tsawa mai qarfi ta biyo baya,ai batasan sanda ta juya da mugun gudu ba ta koma ciki.


"Subhanallazi yusabbihur ra'adu bi hamdihi,wal mala'ikatu min khifatihi" ya furta addu'ar tsawa sanda yaji tsawar,yana gama rufe bakinsa tana shigowa a rude,ta jiqe sosai sai diga takeyi,sunayin arba kuma saita daburce,ta karanci abinda ya tsoratatan,amma sai yayi kaman bai gane ba.


Qin zama tayi tana ta leqen ruwan,saidai ba alamar zai dauke,ga sanyin ac ya hadu da jiqewar da tayi yana kadata har cikin jikinta,shima ya lura da hakan,amma yana mamakin dakiya da taurin kai irin nata,ya gama karantar komai daga gareta ta cikin qwayar idanunta,amma taba qaryata kanta da kanta da ayyukanta.


A hankali taji sanyin yana raguwa,data lura ashe kashe acn yayi,ya maye gurbinta da room heater,saita dan samu nutsuwa kadan,ta sake saka kanta tana leqen ruwan.


Ta saman kanta taji an yafa mata wani abu me qamshi,ta daga kanta da sauri sai taga ya bude mata lema
"Muje" kawai ya fada,ta tsaya sosai ta fara takawa yana biye da ita riqe da lemar,hannunta riqe da abinda ya yafa matan,wanda ya kasance qaramin bargo ne mai laushi sosai,kuma yana da nauyin da zai kare maka sanyi.


Tayi mamakin yadda yake tafe cikin ruwan,yana riqe da lema yana kare mata ruwan,shi kuma ruwan yana dukansa kamar bai damu bama,hakanan taji ta kasa daurewa,kamar idan tayi shuru bata kyauta ba,cikin sanyin murya tace
"Da ka saka lemar kai a kanka....ni wannan bargon zai qarasa dani ba tare dana jiqe ba"
"Kada ki damu,an koya mana tsaiwa cikin ruwa da rana kona awanni nawan ne ba tare da mun gaji ba....." Kai ta jinjina tana ci gaba da tafiya yana biye da ita.


Suna zuwa bakin sassan hajjan ya zuge lemarsa ya juya abinsa,saita tsinci kanta da cewa
"Na gode" juyowa yayi kawai ya kalleta sannan yayi gaba,sai dataga bacewarsa cikin ruwan dake sauka farfajiyar gidan sannan ta taka ta shige sassan hajjan.


A falo ta tadda tsohuwar tana shan kunun tsamiya,ta rasa qaunarta da kunun tsamiya,saita bita da kallo sanda take sauke bargon daga kanta,can cikin ranta taji tausayin haidar din,daga yadda ya amsata tasan yaji zafi ne,to amma koma meye tafison sai an aiwatar da komai daya kamata sannan,yadda hankalin kowa zaifi kwanciya,ta tar cikin gidansa,an rakata kamar kowacce mace,ko a baya ma data barsu tayi yaqinin ransu babu komai a ciki,babu wannan abun data gani yana yawo yanzu cikin idanuwansu a da din (hmmm to hajja,Allah yasa dai burin naki ya cika na miqa zahra'u dakinta).


Dakinta ta wuce ta canza kaya,ta dawo falo taci abinci,bata jima ba taji bacci na ziyartar idanunta don haka ta wuce dakinta abinta tabar hajja da husna da ilham,wanda suma wani lokaci nan wajenta suke kwana,abba babba ya tsara hakan,saboda yace zahra'un idan ta tafi xa'a bar hajjan ita kadai ne a sassan,kuma ko yanzun ma idan ta tafi makaranta wajen nata babu kowa,shi yasa suka yo qaura suka dawo,dama kuma sunfi son nan din.


*_BAYAN KWANAKI BIYU_*


Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan hajjan,a lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon hajjan,zahra na kitchen tana wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah da za'a fitar cikin kudin hajja da ake juya mata,lokacin fiddawa yayi.


Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari taje din ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu ne,saboda tasan halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan aikinta ya tashi.


A ladace ya cire takalmansa ya qaraso gabansu ya tsugunna,daya bayan daya ya gaidasu,yaji dadin samunsu a tare,tunda yaje bai samesu a sassansu ba dama
"A kawo maka abincinne?" Hajja ta tambayeshi,tunda ta lura kwana biyu wani shareta yake,tun ranar nan,itakam ko a jikinta,tunda tasan koma meye qarshe shi zaifi kowa mora
"A'ah...zanyi magana idan za'a kawomin din....magaa nakeso muyi dama" abbansa ne ya daga kai ya dubeshi yana ninke takardar daya gama rubutu akai,abba yusuf ne ya amsa
"To Allah yasa lafiya" qasaitaccen murmushin nan nashi na gefan baki yayi sannan yace
"Lafiya lau abba.....cikin yarjewar ubangiji inason satin nan da zamu shiga in sha Allah mu wuce umara,nida hajja da abba na.....da kuma mama" Wani farinciki ne ya bayyana sosai saman fuskar hajja,burinta a duniya kenan ta koma qasa mai tsarki,duk da cewa taje har sau biyu,hajji daya umara daya,amma wajene da babu musulmin da bazaiso ya dawwama ma a can ba,lallai ba shakka haidar din wata kyautar Allah ce cikin iyalinta,soyayyar da yake mata mahaifi da mahaifiyarsa kai dama ahalinsa gaba daya abarso a sameta ce cikin zuciyar kowanne daga cikin dangi,don samun dorewar qaunar juna da danqon zumunta.


Kowanne a parlour din son barka yake gami da sanya masa albarka,tare da yaba wannan namijin qoqarin sa yayi
"naso ace na qara da abban tsakiya da abba yusuf,to amma kudin hannuna sun qare,ba zasu isa ayi komai na mutum biyu ba,amma in sha Allah sune a lissafina na gaba" nunawa sukayi babu komai,su da dan uwan nasu duka abu dayane,sannan suna da yaqinin da yardar Allah shi mai kai kowa ne cikin dangi idan da halin yiwuwar hakan.


Sun dan jima anan suna tattaunawa cike da farinciki,kafin daga bisani suyiwa hajja sallama kowa ya nufi wajen neman kudinsa,sai falon ya rage daga hajjan sai haidar din,sai kuma zahra dake kitcehn tana dora abincin rana kawai don idan ta zauna ta huta gaba daya,inna gaje ciwon qafa ya hanata zuwa aiki tun shekaran jiya.


Kira hajjan ta qwalawa zahra tace ta fito da abincin haidar,ta zata kai masa za'ayi,batayi tunanin yana falon ba don haka ta fito gaba gadi haka abunta,wata straight gown ce a jikinta,wadda tayi mata das a jikinta.


Da kallo ya bita bayan ta gaidashi ta aje masa abincin ta koma,suna hada ido da hajja ya hade rai tsam sannan yace
"Yanzun haka take yawo anan?"
"To uban mutane,sai akayi yaya?ni bama wannan ba,tafiyar nan da zahra'u ya dace ayita,don baka je dakin Allah haka ziqau ba,kabar kyautar da yayi maka a gida ba" kallonta yayi ya soma zuba abincin yau da kanshi ba tare daya nema wani ya zuba masa ba
"Yanzu dai babu kudi hannuna,saidai nan gaba idan Allah yayi" hade ranta tayi sosai
"Eh na sani ai ubana.....ni zan biya mata da kaina,saboda haka a sama mata komai da komai,idanma za'a dage tafiyar sai lokacin data samu to a dage din" baice mata komai ba,dama kuma tasan halinta ba zaya tanka ba,don haka taci gaba da sabgarta kawai,tana ta kiran 'yan uwa daya kamata su sani tana gaya musu batun biya mata umarar,abun mamaki kuma don iya qarfa qarfa irin na hajja sai take hadawa da zahra kan harda ita za'a tafin,shidai yana zaune yana cin abinci yana kuma kallon ikon Allah,zahra kuwa na kitchen bata ma san wainar da ake toyawa ba.


Sai da ya gama cin abincinsa sannan ya miqe ya fice,dole zaiyi maganin hajja,zai kawo qarshen wannan mulkin mallakar nata,zata ga nasa qarfin ikon akan aurensa,don haka tun a motarsa driver na jansa ya kira anty alawiyya.


Bayan sun gama gaisawa tayi masa godiya da addu'ar qaruwar aziqi kan umarar da ya biyawa iyayensu saiyayi mata maganar da ita ta sanya ya kiratan
"Kaya nakeso a hadamin,irin wanda ake hadawa amare a akwati" dariya ce taso kubce mata amma ta danne,don kada tayi dariyar ta jama kanta jagwal,duk da cewa ita ke gaba dashi
"Ohkey.....lefe kenan....kaman na nawa?,kuma akwati nawa?"
"Akwati bakwai is okey,nayi hidima da kudaden hannuna....amma banison kaya low quality please,designers kumadd high quality"
"In sha Allah babu matsala"
"Please su zama ready kafin na dawo"
"To shikenan....babu damuwa" saiya yanke wayar ya aje gefa,ya maida idanunsa kan titunan da suke wucewa.
23/10/2021, 08:50 - 👍🏻👍🏻: 40



Wayar ya sake jawowa,wata number ya sake laluba,wanda suke masa aikin ginin filin da ya siya a nan,yadan jima da siyan filin,tun farkon fara aikinsa ya hada albashinsa ya siya,hakanan da kadan da kadan ake aikin gininsa,yadda zaifi masa sauqi bazai wahala ko ya kashe kudi masu yawa ba lokaci guda,zuwa yanzu ginin yayi nisa qwarai,don abinda ya rage ma sauran abubuwan da ba'a rasa bane,da farko yayi niyyar ma ya kammala gidan ya saida,amma da yayi tunani sai yaga,bashi da mazauni kenan duk sanda yazo ganin gida saidai a cikin gidansu,auren da aka daura masa da zahra yasa ya fasa saidashin kwata kwata,saboda koba zahra ba dama dole zaiyi aure,idan kuma yayi auren zai dawwama zuwa gidansu ya zauna?,dole yana buqatar muhalli.


Da kamfanin yayi magana,ya shaida musu abinda yake da buqata cikin gidan,suka gaya masa kudinsa da zaya bayar,yayi musu alqawarin turawa zuwa qarshen wata,a sannan suna can basu dawo ba kenan a yadda ya lissafa,yana saka ran kuma kafin su dawo din an kammala komai,saiya aje wayarsa yana ci gaba da lissafe lissafensa cikin ransa,zuciyarsa fes,yana jin wata nutsuwa da sukuni suna ratsashi.


******** **** ********


Bai sakewa hajja zancan tafiyar zahran ba,kamar yadda bai amshi kudinta ba,tayi tunanin waskewa yakeson yi,saita matsa da mita da qorafi,sai ranar daya sameta zaune ya miqa mata komai da komai na tafiyar zahran da aka kammala bayan an dage tasu tafiyar da sati daya.


Kwalla ce ta qwacewa hajjan,abinda bai taba zaton gani daga idanunta ba,duka shida zahra dake zaune a gefanta suka zuba mata ido,jikinsu duka yayi sanyi
"Allah yayi maka albarka,ubangiji yaci gaba da gin riqo da hannayenka,Allah ya kula maka da rayuwarka,yadda kake taimakon al'ummar annabi kake kula da iyayenka da 'yan uwanka....Allah yayi maka kyakkyawan sakamako,haidar....kaida zahra Allah shine shaida....kaf cikin jikokina babu wadanda suka shiga raina kamar yaku,hakan ya sanya nan duniya tun kuna da qanana bani da burin daya wuce Allah ya hada kanku kuso juna ku zama miji da mata,sai wani al'amari me daure kai ya soma gudana a tsakaninku,amma hikima ta ubangiji da baya maida addu'ar bawansa,sai gashi ya kawo hadin aurenku ta fuskar dani kaina ban tsammata ba.....haidar....ga zahra nan,a yau zan baka amanarta...ka riqe amanar zahra,kai da ita duka nasan halayenku...hakan ya sanya nake da yaqinin dukkanku kun dace da junanku,zaku gasgata abinda nake fada din,zahra,haidar yayanki ne kuma mijinki,ki bishi ki masa biyayya,ki masa biyayya kamar yadda musulunci ya tanada,Allah ya albarkaci rayuwarku" cikin sanyin jiki dukkansu suka amsa da amin,saita miqawa zahra passport din hannunta
"Zaki tafi umara tare damu,mijinki ya biya miki" kamar a mafarki taji fitar furucin daga bakin hajjan,saita daskare a zaune tana jujjuya passport din,yau itace zata qasa me tsarki ta qarqashin ya haidar din?,mutumin da take masa kallon mara qaunarta,wanda bayason yaga suna farinciki da walwala?,mutumin da take kiranshi da mara ALKIBLA?,mai baudadden hali,wanda sam ALKIBLARSU bata zo daya ba,ashe ta sanadinsa zata je taga ma'aiki?sai qwalla ta cika mata idanu,ta sake matsawa kusa dasu muryarta na rawa saboda farinciki
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi,ya qara budi,ubangiji ya biya da jannatulfirdaus" idanunsa ya lumshe yana jin dadin muryarta hade da dadin addu'ar data yi masa ya amsa da
"Amin".


"Wannan kadanne daga alkhairinsa,alkhairin nasa kuma da zaya shiga rayuwarki matuqar kika ci gaba da bin maganar magabatanki,matuqar kika ci gaba da daukar zancansu da muhimmanci,na taba gaya miki,haidar ba irin sauran maza bane gama gari,tun a shekarun quruciya na gama karantar halayyarsa tsaf,tun kafin na haifeki nake sha'awa inama ina da diya da idan ya girma zan bashi ita?,yana da boyayyun nagartattun halaye da dabi'u,yana da sauqin kai da sanyin hali,yana da tausayin mace.....amma dukka ba kowa ke iya karanta da gane hakan ba,saboda matuqar zaka mu'amalanceshi daga nesa,to tabbas zaka masa fassarar mai ra'ayin riqau,mai kakkausan hali,mara tausayi ne,mai zafi da saurin fushi,eh aliyyu yana da ra'ayin riqau akan gaskiya,yana da kafiya kan abinda yasan shine dai dai,yana da fushi idan yasan an sabawa dai dai ko doka,yana da rashin tausayi akan azzalumin mutum mara imani,amma matuqar baka da irin wadan nan siffofin,zakaji dadin zama da haidar fiye da kowane dan adam.....zan baki tips na zama da haidar din,a matsayinki na diyata,ni kuma uwa a gareshi da tasan halayyarsa,ba don ki mallakeshi ba,sai don ki masa biyayya ku samu zaman lafiya da qauna me dorewa" wadan nan sune lafuzzan umminta a sanda take shaida mata batun tafiya da ita bayab ta miqa mata passport dinta ta sanya masa albarka,zama ummin tayi ta dinga zayyana mata abubuwa masu matuqar amfani a rayuwarsu,har zahran ta dinga mamaki da kunyar hakan,saidai ta lura ummin ko a jikinta,saboda ta sani tana gyara rayuwar diyarta ne,tana kuma inganta rayuwar haidar dinta,aikine da takejin ya wajaba a kanta a matsayinta na uwa


*_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO_*


Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don wucewa qasa me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama daya ta abba yusuf ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran biyunne na haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya suka koma gida da sauran yaran gidan da aka taho dasu.


Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana mamayarta,ko hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin magana bane,sau tari wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya wuce duba labarai,ko duba saqonni da suka shafi aikinsu.


Yana ankare da yadda ta kasa sakewa din,nutsuwar data sakeyi ta bashi mamaki,kusan tun tale tale yasan zahra cikin yaran gidan,tayi shuhura wajen aikata laifi da samun kariya daga wajen hajja da a wancan lokacin yake ganin daure mata qarqashi kawai takeyi,abinda ya janyo rashin jituwarsu kenan,yaci alwashin shi bazai bari ta buwayi kowa ba,duk da girma ya sake canzata qwarai,amma a yau din ta sake canzawa,wata kamala ta musamman ke kwaranya tun daga fuskarta zuwa jikinta.


Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba agogon hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a nutse yana daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.


Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna sau nawa ta taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar shadda gezner gray colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin annurin kyau yake fitarwa na musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba suna gani ba yadan ranqwafa ta gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
"Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki" saiya miqe ya barta daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran turarensa tana shaqa wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab dashi
"Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida" hajja ta fada,sai haidar din yace
"Akwai.....muje a duba mata" yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi gaba yabi bayanta.


Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment