Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka nan ta hada musu abincin daidai yadda zai ishesu shida abban tsakiya,ta isa falon ta dire musu tayi komawarta daki.


Bata sake fitowa ba sai da taji alamun fitarsu sannan ta fito riqe da mayafinta,sai data shiga kitchen ta hada kayan nata karin sannan ta dawo falon ta zauna kusa da hajja,tana tsaka da cin abincin hajjan tace
"Ina tunanin kafin ku koma makaranta fa iyayenku zasu nemi ganawa da magabatan samarinku,saboda yayanku ya tada maganar aurensa,yanzu haka can suka nufa garinsu yarinyar" duban hajjan tayi tana cin abincinta
"Shi zai kaisu da kanshi kenan?"
"Eh" ta bata amsa tana dauko remote don ta canza tasha,saita tabe baki
"Ey...da yake shi idanunsa da kwalli ai ba laifi bane,inda kaine da ka shiga uku" duka hajjan ta kai mata ta kuma sameta,ta gantsare tana cewa
"Wayyo Allah na.....hajja saikin karyani tukunna?"
"Eh gwara ai na karya ki din....tunda ke baki gajiya da dan banzan qorafi,zancan da ake miki daban wanda kike daban"
"Shikenan tunda haka kika ce,kullum nice me laifi" daga haka ta miqe da farantin a hannunta ta wuce kitchen tana zumbura baki,ta ajjiye sannan ta fito ta yafa mayafinta
"Zan wuce hajja" tayi maganar da alamun jin haushi har yanzu akan fuskarta,kudi hajjan ta miqa mata tana gaya mata kada tayi dare.


Kamar yadda hajjan tace kuwa a ranar akaje dawakin tofa dangin mahaifiyar Aliyyu haidar ko ince zaki aka tambaya masa aurenta hannun iyayenta da suke kawunnai a wajensa,mahaifinta qanine ga mahaifiyarsa,ba tare da wani bata lokaci ba aka basu auren,tunda shima kamar d'a ne a wajensu,suka dawo cike da farinciki da murnar yadda akayi komai cikin girma da karamci.


Washegari abba babba ya bada sanarwar kowacce cikinsu ta yiwa maneminta magana,indai da gaske yake yazo ya gabatar da kanshi tare da magabatansa,don suna so nan da shekara daya su hada su duka a aurar,mata biyar namiji daya.


Ba bata lokaci ta shaidawa sir nasir,wanda ya bayyana murnarsa sosai fiye da zatonta,don har mamaki ta dinga yi yadda yaketa farinciki,kusan ma kamar ya fita so da daukin abun,ya kuma tabbatar mata idan basu zama na farko ko na biyu a zuwa ba.....to ba zasu zama na uku ba.


Saurayin salma shi ya fara zuwa rana daya dana yusra,bayan kwana biyu saurayin yasira da magabatansu sukazo,washegari na hafsat ya bayyana shima,a ranar ne zahra ta karbo wayarta daga gyara,wadda ta matsu qwarai ta gyara din,don tafi kyautata zaton rashin wayar ne ya hana zuwan sir nasir kamar yadda yayi alqawari,tana jonawa a chargy ta lalubo number dinsa ta kira.


Bugu daya ya dauka,sai daya saki ajiyar zuciya sannan yace
"Kin wahalar dani fa"
"Me nayi kuma?"
"Kinsan tafiya ce ta kamani zuwa garinsu mama bagtatan....sai da muka dauki hanya na dinga kiranki ban sameki ba,yanzu haka ina kan hanyar dawowa....dama cewa nayi indai harna sauka ban sameki ba gida kawai zan zarto nan na ganki,idan ba haka ba nasan naci qarya yau na iya barci" murmushi ta saki cikin jin dadin kalamanshi
"To ai gashi na kiraka,nima shurun ya bani mamaki ya kuma daga min hankali"
"An rigani zuwa kenan?,nida naci burin na zama mutum na farko saboda girmamawa a gareki....amma duk da haka bata baci ba" hira suka fara daga haka,a qalla sun kusa kwashe awa daya sannan sukayi sallama,da zummar gobe zai shigo da magabatan nasa,idan yaso ya ganta gaba daya.


Kunya yasa ta rasa yadda zata shaidawa su abban cewa nasir din zaizo,sai da gari ya waye taga indai bata fada din ba zasu fice harkokinsu,dabara ta fado mata ta shaidawa hajja,ita kuma ta gaya musu.


Saidai tana shiga falo da niyyar wucewa dakin hajjan saboda bata kai ga fitowa ba wayarta dake hannunta ta dauki kuwwa,ganin sunan nasir yasa ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana amsa wayar.


Tun daga sallamarsa taji alamun muryarsa ba daidai take ba,kafin takai ga tambayarsa shiya tambayeta
"Kin gayawa su abba zuwan namu ne yau?" Kai ta kada
"A'ah,yanzu dai nake shirin gaya musun" saiya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,cikin alamu na damuwa tace
"Lafiya?"
"Fatima.....wallahi tun jiya nake fama da mama kan maganar....ashe turani garinsu da tayi akwai yarinyar data turawa ni wata na'ima....tunda naje yarinyar take rawar kai a kaina take kuma dawainiya dani,ni ban kawo komai ba sai yanzu dana dawo na kawo wannan maganar mama da abba duka sukace basusan zance ba,sun turani naga na'ima ne don mu hada kanmu".


Kasa magana zahran tayi,tayi shuru kawai tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,gabanta ke faduwa
"Fatima....bana gaya miki wannan maganar bane don ki saka damuwa cikin ranki ba,na gaya miki ne don kada muyi jinkiri wajen zuwa ki zaci wani abu na daban....ba abun damuwa bane,nasan yadda zan shawo kan mama in sha Allah....kuma zanzo na samu abba nayi masa bayanin komai"
"To" abinda ta iya furtawa kenan a sanyaye,sallama tayi masa da kanta,don bata da qwarin gwiwar ci gaba da hira dashi,saita zame ta kwanta kawai cikin wani irin yanayi data kasa tantance wanne iri ne,bata fatan fa rasa nasir sam,saidai kuma tanajin tsoron faruwar hakan can qasan ranta.


Sannu sannu kwanaki suka soma shudewa,nasir yaci gaba da zuwa....ya kuma ci gaba da kiranta a waya kamar yadda suka saba,saidai bai sake tada wancan zancan ba,hakanan maganar ganin abba ma bai kuma tada ita ba,itama bata kuma ce masa komai ba,bata sake tada maganar ba,tana gayawa zuciyarta cewa yana qoqarin sanya mamanshi ne ta amince,tana tsoron ma a tada maganar ya zama silar rasa sir nasir kenan a wajenta.


To daga gida ma ba wanda yayi mata maganar nata manemin,baya ga hajja data yi sau daya,ta kuma yi mata bayanin cewa yana sane zasuzo,ya shaida musu yana jiran su saka rana ne su magabatan nasa.


Ta sani cewa tana da alfarma wajen iyayen nata,sabida tausayawa maraicinta da sukeyi,shi yasa basu matsanta mata kan maganar ba,hakan yasa hankalinta yadan kwanta kadan,a haka har suka koma makaranta,suka kuma shiga ss 3 ajin qarshe na makarantar secondry,wanda abubuwa da dama sun faru,ciki harda bata muqamin shugabar dalibai,bunqasar soyayyarsu da sir nasir,harda kuma kammala abinda ya kawoshi makarantar shida sauran malaman,saboda dawowar malamansu na asali suka miqa musu aikinsu,wanda hakan ya farune saura wata guda su tafi hutun first term.


Randa zai bar makarantar ta shiga damuwa sosai,shi ya ringa lallashinta a inda ha nemi ganinta
"Karki damu mana,saura sati hudu kacal ki taho gida kici gaba da ganina,sannan zanyi qoqari kafin ki koma wannan hutun naga su abba a daidaita maganar aurenmu" da haka ya samu ta rage damuwarta,sannan yayi mata sallama suka rabu cikin kewar juna.


Sati hudun kuwa na zuwa suka fara jarabawa,suna gamawa sukayi gida hutu kamar yadda aka saba sai gida,saidai ko bayan sun koma dinma dai shuru shuru zancan turowar tashi,saidai suna waya kamar yadda suka saba dashi.


*_04:30 pm_*


Kwance take a falon umminta ita daya,babu kowa daga ita sai ilham wadda zahran ta aikata kitchen ta juya mata miyar data dorawa ummin tata,bata nan ummin,ta tafi barka na matar cousin dinta data haihu,ta tafi kuma da duka yaran,don haka ta bar mata girkin,don hajja itama kwana biyu kenan bata nan,ta tafi ainihin garinsu bikin dan qanwarta,yawanci idan zata da zahran take zuwa,hakanan wannan karon taqi binta don haka ta dauki amira da husna daga cikin jikokinta suka rakata.


Wayarta da bata dade da gama waya da nasir ba wadda ke aje saman kanta ta dauki tsuwwa,ta miqa hannu ta daukota tana duba lambar da aka kirata,ba suna alamun bata da ita cikin jerin ma'ajiyar lambobinta,saita daga ta kara a kunneta cikin sallama.


Ana amsa sallamar taji kamar tasan muryar,amma saita tambaya jin ba'a da niyyar yi mata bayani
"Dawa nake magana?"
"Nuraddeen ne....tsohon masoyinki,kuma wanda har a yanzu yake sonki" mamaki ya sanyata tashi ta zauna sosai,kodai da gaske ne shekaran jiya da sukaje gidan anty aliya yusra tace mata taga nuraddeen tsaye hana kallonsu?
"Waye kuma me wannan sunan?" Ta fada cikin gatse da basarwa,murmushi ya saka
"Na tsammaci jin sama da haka ma daga gareki....amma kiyi haquri ki bawa qwaqwalwarki dama ta tuna koni waye...don nazo da qoqon barata ne a karo na biyu a bani dama,damar kuma da zata kaimu har ga aure....." Da sauri ta katseshi
"Kaga dakata.....ka riga daka barar da damarka tuntun tuni,abu daya zan gaya maka shine,daga yau sai yau,kada ka qara tunawa a ranka ka sanni,kada kuma ka sake gigin kirana harka koma va mahaliccinka" daga haka ta datse kiran ta aje wayar ta koma ta kwanta tana jan tsaki.


Kira ya shiga yi a jejjere,da taga zai takura mata saita dauki wayar ta danna masa block ta gyara kwanciyarta,daga qarshe ta sake jan tsaki ta miqe ta nufi kitchen,ta jawo salad din da bata yanka ba ta soma gyarashi tana cewa ilham ta kawo mata ruwa a roba,tana aikin cikin ranta tana mamakin qarfin hali da rainin hankali irin na nuraddeen,gami da zallar rashin kunya da yake tunanin yana da sauran dama,yana kuma da qwarin gwiwar da zai iya fuskantarta ido da ido ya gaya mata wata maganar.


Washegari sha biyu na rana kiran nasir ya shigo mata,tayi mamaki don basu fi awa biyu da gama waya ba,duk da cewa ta sani mayen kiranta ne shi a waya,baya gajiya,amma yadda tazo ta tadda tarin miscal ya bata mamaki,don lokacin bata kusa da wayar,ba bata lokaci tayi masa flashing ko daqiqa uku ba'a rufa ba ya kira.


Cikin zallar mamaki ta samu gefan katifarta ta zauna tana sauraren masifa da bala'in da nasir ke kwararawa cikin waya,wanda ta kasa fahimtar inda zancan ya dosa,ta gane dai akanta yake maganar,kuma duka zallar kishi ne,amma bata gama gane da waye yake ba,har sai daya qara mata haske ta hanyar cewa
"Wallahi saina nuna masa kurensa....ni zai rainawa hankali,harda dora hotonki saman dp?,to idan ma kuna tare ki gaya masa yayi saurin saukewa ya kuma fita daga harkarki tun ba'a ji kanmu ba"
"Wai waye don Allah....kayi haquri kamjn bayani mana"
"Nuraddeen yake ko waye....whatever ma ake kiransa dai ki gaya masa ke ba tashi bace" ita dariya ma zancan ga bata,tana mamakin yadda yake kishinta,ita sam ko wayar jiya ma ta manta sunyi ta dashi bare shi kansa nuraddeen din
"Ka kwantar da hankalinka mana" ta fadi sannan a hankali ta warware masa komai.


Ajiyar zuciya ya saki,cikin sanyin murya yace
"Ok...ok,pls pls fatima,don Allah ki riqemin amana,ki riqemin amanar kanki kinji don Allah,kada ki auri wani saini" idan da sabo ta saba dajin wannan kalmar daga bakinsa,itace kalmarsa ta qarshe duk sansa suka gama hira,idan akwai baquwa aciki itace kada ki auri wani saini
"In sha Allah" ta bashi amsa,saiya saki ajiyar zuciya sannan ya mata sallama yana aje wayar,itama ta aje tata tana jujjuya maganganu da sukayi cikin ranta.


*_ALƘIBLARSU_*🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️



Kwana biyu tsakanin wayarta da nasir din ta shirya zuwa gidan abban gwammaja zata dubashi ciwon qafa ya matsanta masa,ita da yusra suka shirya sai ilham,adaidaita sahu sauka dauka direct har can gwammajan,har qofar gida saboda mota tana iya shiga har qofar gidan.


Mai adaidaitan na saukesu salim na fitowa daga gidan,hannunsa riqe da ledar baqa,cikin raha dake nuna sabon dake tsakaninsu suka gaisa suka dan zolayi juna yadda suka saba sannan tace
"Da alama guduwa zakayi saboda kaga nazo"
"Haba yarinya....ma'aruf ke tsoronki,yanzu zanje na dawo,dinki zankai nan fage"
"Auto,saika dawo,ina jiranka"
"Kamar wani abun arziqi zaki bani baya ga ki karbe na hannun mutum"
"Ai raba arne da makami ibada wallahi" ta fada tana dariya gami da yin cikin gida abinta,shima ya wuce yana cewa yau kam sisi bazai kashe musu ba,basu da aiki saicin banza da wofi.


Ta taras da jikin abban da sauqi,harta zauna suka dan taba hira sannan ta wuce dakin umma suka dasa tasu hirar da hasina,ba jimawa suka shige kitchen suka dorawa umman abincin rana,har suka gama suka zuba suka zauna suka soma ci salim din bai dawo ba,sai da suka gama sun dan miqe suna hira suka jiyo sallamarsa.


Fuskarsa ba kamar dazun ba ya shigo falon,daya daga cikin kujerun falon ya samu ya zauna,daidai lokacin da umman itama ta shigo tana cewa
"A zuba maka abincin ne kafin ka wuce kasuwan?"
"A'ah umma,barshi kawai.....wani labari na samu yanzu mara dadin ji?" Itama guri ta samu ta zauna yayin da dukkaninsu sukayi sak,kowa ya bada hankalinsa kanshi
"Kamar yaya?,wanne irin labari ne haka?" umman ta fada idanunta yana kan salim din,yayin da hasina yusra da zahra suma suka zuba mishi idon suna son jin abinda zai fada...........
23/10/2021, 08:38 - 👍🏻👍🏻: 10
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽

_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_

*kayayyakinmu sune kamar haka*


FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500


*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail

*ko ta number wayarmu kamar haka*

07067943479

*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*

*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾
________________________________


"Yanzu a inda naje kai dinki wajen habibu....yakemin Allah ya sanya alkhairi,yace ashe biki zamuyi babu gayyata?,abun saiya bani mamaki,nace bakin wa?,yace bikin nasir mana!" Sosai maganar ta daki kunnen zahra,wanda ta dinga jin kamar sautin sakin bomb,saidai tayi namijin qoqari wajen tara nutsuwarta ta saurari qarshen zancan
"Ni dai ban iya cewa komai ba,a gabana ya kammala hada babbar rigar nasir din ta daurin aure,har na fito ban iya bashi amsa ba" salati sosai umma ta saka tana tafa hannu,yayin da zahra taji kamar daga zaunen da take ana shirin kada ita,don haka saita jingina da kujerar da take kai,tsahon wasu lokuta kafin umman tace
"Yanzu ta yaya zamu tabbatar da gaskiyar wannan labarin" nazari kadan salim din yayi sannan yace
"Bari na kira habibun,dama yace zai shigo anguwar yanzu wajen wani abokinsa" wayarsa ya ciro ya kirashin,anci sa'a kuwa yana gab da shigowa unguwar,ya roqeshi yanason ganinsa ya basji kwatancen gidan,yace zai iso yanzu in sha Allah.


Mintina ashirin habibu ya shigo har falon umma,a lokacin zahra na jingine kawai ba tare da wani magana ko motsi ba,tana jin yadda suketa tattauna batun a tsakaninsu.


Umma da kanta ta yiwa habibu bayanin komai,shima cikin nuna alhini da rashin jin dadi yace
"Indai ko haka ne tabbas nasiru bai kyauta ba,amma hausawa sunce waqa a bakin mai ita,bari kuji daga gareshi" daga haka ya saka hannunsa a aljihu,ya ciro wayarsa yayi kira sannan ya maidata handsfree.


Ringin uku aka daga,habibune ya soma magana
"Ango ango,ka sha qamshi"
"Chief tailor....yaya akayi?"
"An gama dinkin babbar rigar daurin auren fa"
"Kai amma naji dadi daka cika alqawari,don inason na kaita bugu ne"
"Yaushe to zaka shigo ka karba?"
"Zuwa anjima haka zanje gidansu amaryar,zankai mata invitation lokaci ya qure bata fara rabo da wuri ba,zan qaraso nan wajenka saina amsa din"
"Shikenan,a tahomin da nawa IV din,saura kwana nawa ne?"
"Rana ita yau in sha Allah"
"Ango ango,to Allah ya nuna mana"
"Amin amin,na gode" daga haka ya yanke wayar yana duban salim.


Tuni zahra ta dora hannayenta a fuskarta tana kiran sunan Allah,wai da gaske nasir shima ya yaudareta?,da gaske shima nasir aure zaiyi?,yarinyar da aka bashi zai aura ko wata daban,idan wadda aka bashi ce ai ba garin take ba,to amma yanzun cewa yake zaije gidansu amarya....me hakan ke nufi?,wai meke faruwa da ita ne?"saita miqe kawai ga nufi dakin hasina tana jin jiri yana dibanta,tana shiga ta maida qofar ta rufe don kada ma wani ya biyota,ta samu gefan gadon hasinan ta zauna,saita saki kuka a hankali hade da sheshsheqa.


Kamar wasa sai gashi a ranar kwanan gidan abban gwammaja ya kamasu saboda wani matsanancin ciwon kai daya saukar mata,umma ce ta dinga aikin bata maganganu,da kuma kwatanta mata cewa matar mutum kabarinsa,tayi addu'a idan har ya zalunceta Allah ya fidda mata haqqinta,tana jinsu sanda suke waya da umminta,sai kuma washegari bayan sallar magariba abubukar yayanta yazo da kanshi ya daukesu ya maidosu gida.


Saidai suna shiga bangaren umminta yace ta wuce,ta sameta a falo a zaune,suna hada idanu ta fahimci akwai damuwa qasan ran ummin da take boyewa,saita qarasa a hankali ta zauna gefanta tana gaidata,ta amsa sannan ta dora da cewa
"Ki tsananta addu'a,duk abinda kaso Allah kuma bai baka ba tabbas ba rabonka bane,qila ma ba alkhairi bane a rayuwarka,tashi ki tafi,Allah ya kiyaye"
"Na gode" tafada tana miqewa zuwa sassan hajjan.


Data shiga bata samu hajja ba,saita wuce dakinta,saboda yadda kanta yake sara mata,har yanzu kunnuwanta na jiye mata sanda habibu ya kira nasir din,yake gaya masa saura sati daya daurin aurensa,tana iya jiyo kamar wani sauti mai kama da zumudi zumudi cikin muryarsa,babu alamun bacin rai ko damuwa tattare da sautinsa,saidai bata jima ba hajjan ta shigo cikin jimami,inda ta takura mata sai data tattara ta zuwa dakinta,tace gwara su zauna tare har ta samu sassauci.


Saidai kuma abinda ya bata mamaki shine,a daren ranar saiga nasir ya kirata,kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga,don tunda abun ya faru tsakanin jiya da yau bai kira ba sai yanzun,tana son taji da wacce kalma shi kuma zaiyi amfani?,me zaya fada?,zai kare kanshi ne kamar yadda nuradden ya kare?,ko kuwa zai tabbatarwa da kansa laifinsa?.


A yanayin sallamarsa kawai ta fahimci baisan mai afkuwa ta afku ba,da irin salon daya saba yi mata magana yayi mata,sai daya gama sannan a hankali tace
"Ango" dif yayi na wasu sakanni sannan yace
"Wanne irin wasa ne wannan zahra?,waye kuma angon?" Wani bacin rai ne ya taso mata,wato ita zaya ninke a baibai kenan?ya shirya saidai kawai taji an daura aurensa?,saita miqe ta zauna tana tuna irin kalaman daya jima yana amfani dasu a kanta,tana tuna yadda yake nuna kaffa kaffa da zallar kishi a kanta,tana tuna yadda koda yaushe yana tafe da kyaututuka domin ta,wanda koda taqi amsa zai tilastata ta karba din,zaice tukuicin soyayya kenan kyauta,ashe babban tukuici yana tafe
"Nasir....bude kunnenka da kyau!,idan zaluntata kasoyi to ubangiji yamin kariya da katanga dakai saboda ya bayyana min gaskiyar abinda kake boyewa,ka zalunceni nasir!,kaso ka yadaureni kaje kayi aurenka ba tare da na sani ba?,to na godewa Allah daya bayyanamin shirinka" cikin wata rudewa da dirircewa yake cewa
"Calm down fatima....ki tsaya kiji mana,wallahi Allah ba haka bane,yarinyar nan auren hadi akayi mana da ita.....zabin hajiya da alhaji ce....."
"Watanni nawa?,kwanaki nawa?,amma kullum nuna min kake bata da muhimmanci a wajenka?,hakanan maganar itama bamai muhimmanci bace?,ka gayamin cewa ka gamsar da hajiya ta aminta da naka zabin,amma abun mamaki saiga sauti farinciki daga maqogwaronka kana sanarwa da duniya daurin aurenka,a hakan zakace baka ita akayi?,ahaka kakeso na yarda dakai,bayan an ganemin babu wani damuwa ko kadan tattare dakai?"
"To naji,amma fatima....ina sonki ki yarda dani.....kuma in sha Allah zan aureki a matsayin matata ta biy....."
"Allah ya tsareni da hada hanya da mayaudari....har abada ni dakai nasir na barka kenan,kaje....ina roqon ubangiji yayimin sakayyar abinda kayimin,Allah ya isarmin" daga haka ta kife layin ta sake sakin kuka.


Kuka tayi mai yawan gaske,wanda kafin tayi controlling kanta fa sassauta kukan nasir ya hada mata massages da kiraye kiraye babu adadi har ta kasa irga yawansu,sai kawai ta kashe wayar baki daya ta cusata qasan filo.


A ranar ta balla layin shima kamar yadda ta yiwa nuraddeen,hakanan ta kawar da duk wani abu da tasan zai tuna mata dashi,ta baiwa kanta qwarin gwiwar ci gaba da rayuwa,da kuma fuskantarta,tana mai burin haduwa da kyawawan sakamako a nan gaba


_saidai ina!,kowanne babi na rayuwa tafe yake da qaddararsa,saidai kuma DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUQI!_


Duk da ta cinyewa ranta komai amma hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba,saboda ita damuwa tana da tasirin bayyana gangar jiki koda an danneta a ruhi,hakan yasa ta faɗa sosai kafin komawarta makaranta.


Wannan karon hajja da kanta tayi mata tayin zama a gida ta qara koda sati daya ne ta qara murmurewa kafin sannan amma tace a'ah,saboda jarabawar qarshe ta wa'ec da neco da suka fara jiyo qamshinta,gwra ta tattara hankalinta ta samu sakamako me kyau,don yadda qaddararta ta fara zuwa mata a hagunce ya sanyaya mata jiki.


Da yammacin ranar ana ya gobe zasu tafin haidar ya iso gidan,tana falon hajja tana goge sauran kayanta da zata wuce dasu yayi sallama falon ya shigo.


Kai ta daga ta dubeshi na sakan daya kana ta amsa tana maida kanya ga gugar,har yanzu yana nan da gayunshi kwarjini izza da isa,saima cika da 'yar qiba da kuma murjewa daya sakeyi,hakan ya qara masa kyau sosai,kusan watansa biyu baya nan,sai yau ya dawo.


A sanyaye ta gaidashi,sannan ta tattare gugarta ta wuce ciki tabar falon,duk da haka sai data fara biyawa ta dakin hajja ta gaya mata isowarshi sannan ta fito ta koma dakinta ta barta tana ta murna da zumudin dawowar jikan nata,wanda babu yashi cikin jikokin nata,kasancewarsa jika na farko a wajenta,mai kuma yawan kula da ita da damuwarta,tamkar shita haifa ba mahaifinsa ba.


Wannan karon ma ta fito zata sha ruwa a kitchen taji hajjan na gaya masa abinda ya faru da ita,itakam bataso harga Allah hajjan na gaya masa
"Allah ya sawwaqe" kawai taji yace,qwafa taja a ranta tana cewa maganin hajjan da take gaya masan,aiba matsalar data shafeshi bace dama.


Basu jima da komawa ba lokacin visiting yayi,wanda su shine na qarshe d za'a musu saboda jarrabawa da zasu fara gab da lokacin ziyarar ko kuma bayan lokacin,sun wuni cikin farinciki,kamar yadda aka sani cewa rana ce ta farinciki ga kowanne dan makarantar kwana,wannan karon 'yan gidansu da iyalan abban gwammaja da wuri suka koma,don haka ta dawo hostel abinta.


Gab da zata isa gadonta ta hangi ladifa hamza zaune riqe da takarda cikin hannunta,gefanta kuma maryam mustapha ce riqe da hannun ladifar dake digar hawaye.


Ba laifi suna zaman mutunci sosai dasu,kasancewar zahran mai faran faran da jama'a yasa take da yawan jama'a,banda yanzun da walwalarta taja baya ba kamar da ba,don ko da take shugabar dalibai kusan iya mu'amalarta yasa dalibai ke sonta,musamman juniors da bata yadda a zaluncesu ba don suna qasa dasu,hakanan suma basu isa su raina na sama dasu ba dole su basu girma.




1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment