Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin yusra na cewa
"Gaskiya ne,ban sake yarda soja akwaishi da son matarshi ba sai yau....jiba don Allah abun sha'awa,sun sadaukar da farincikinsu ga qasarsu...ma sha Allah,Allah ya dafawa sojojinmu".


Lieutenant jafar wanda a yanzu ya koma captain jafar aka kira,dr nasreen ta damqi hannun zahra cikin farinciki ba tare dama ta sani ba
"Ma sha Allah my happiness....lallai yau ranarmu ce" ta fada tana duban zahra,itama zahra dubanta tayi,tana mamaki cikin ranta wannan wacce irin soyayya ce?wadda bata boyuwa,saita sakarwa dr nasreen murmushi kawai na qarfafa gwiwa,ta gyada kai
"Thanks" ta cewa zahra tana miqewa a nutse ta sauka daga wajen zuwa inda yake tsaye yana jiranta.


Kafin ta qaraso tuni ya miqa mata hannunshi,tana murmushi itama ta isa ta dora hannunta cikin nashi,kamar sun manta da tarin jama'ar dake wajen,ta amsa abun wuyan,tadan rusuna kana ta miqe ta zira masa fuskokinsu dauke da murmushi ta juya tana maqale a kafadarsa aka musu nasu hoton,tana jin salma na fadin
"Wow....matar nan ta hadu wlh"


Sam zahra bata damu ba bata kuma kawo komai ba,don bata tsammaci zuwan sunan Aliyyu ba,sannan tunda daga mama har abba babba na wajen,sun kuma fita cancanta,saidai me?,cikin sakanni sunan aliyyu dabo ya karade abun maganar,wanda kamar qiftawa da bismillah duk sojan daya kasance junior dinsa dake wajen saida suka miqe,sukayi salute nashi sanda yake takowa zuwa inda kowa yake tsaiwa cikin nuna zallar girmamawa,da alama akwai akwai alaqa mai matuqar kyau a tsakaninsu
"Ma sha Allah" 'yan uwa dake kusa taji suna furtawa,lumshe idanunta tayi tana duban wajen yadda suke tsaye,abun ya qayatar da duk wanda yake wajen
"Get up mrs aliyyu dabo" dr nasreen ta soma fadawa zahra cikin fara'a,yayin da dukka su salma suka waiwayo suka sanya mata ido,kai ta kadawa dr nasreen
"Mama tana nan....haka abba ma"
"Tashi kije inna wuro" ta jiyo muryar mama,wanda sam bata zaci taji ba,saita miqe a hankali tana jin wani nauyi na saukar mata,qafafunta sukayi sanyi kamar ba zata iya tafiya ba,wanda wannan ya qarawa tafiyar tata zama slow,hakan saiya qarawa yanayin takun nata ado,da wani salo na daban mai qayatarwa.


Tunda ta taho ya zuba mata idanu da wani salon kallo,wanda ba lallai kowa ya fahimta ba,saif dake tsaye daga gefansa ya soma masa magana qasa qasa
"Smiling please....,just once" banza yayi dashi,saidai idanunsa yana kanta sanda take ci gaba da takowa,taqi kallon koda saitin inda yake,saidai tana sauraren salma dake bayanta tada n tako mata tana mata magiyar karsu bada 'yan uwansu.


Sai data fara amsar abun wuyan sannan ta juya zuwa direction din da yake tsaye,saif ne cikin zaquwa yace
"Please zaki....i beg you mana,kaga fuskarka?,don't behave like......." Qafarsa yasa ya take gefan qafar saif da qarfi,wanda hakan ya sanyashi yin shuru tare da runtse ido
"Mugu" ya fada yana cije lebe,dai dai lokacin da zahran ta qaraso gaban haidar din,sai a sannan idanunsu suka shiga cikin na juna,kowannensu na iya ganin qwayar idanun dan uwansa kai tsaye.....
23/10/2021, 08:45 - 👍🏻👍🏻: 26


Taku biyu ta sakeyi zuwa gabansa,wanda hakan ya qara adadin kusancin dake tsakaninsu,a hankali ta daga hannunta da niyyar zira masa abun,saidai kuma ina,tsahonta bazai taba kaiwa ba,don kanta a dai dai qirjinsa ya tsaya
"Madam kina buqatar qara motsawa kadan,don maigidan naki sadauki ne da gaske tako ina" dukka sai aka sanya dariya,taku daya ta qara ta mannu da jikinsa,qamshin turarukansu suka soma gauraya da juna,gaba daya numfashinta yaso daukewa,sosai bugun zuciyarta ya qaru,ta lumshe idanu tana daga hannunta zuwa saman kansa.


Hucin numfashi taji sosai na sauka saman fuskarta,hakan ya sanya ta bude idanunta,gaba qwayar idanunta ta shige cikin tasa saboda ranqwafowa da yayi da kansa yadda zata samu damar saka masan,saiya lumshe idanunsa gami da budesu lokaci guda still akan fuskarta sanda ta janye nata idanun daga kanshi,karo na farko da yaga abinda mutane suka sha fadi,wanda bai taba gasgatawa ba sai yau,qwayar idanunta irin tasa ce,mai wata irin zaiba da walqiya,har cikin jinin dake zagayawa a jikinsa yake jin yadda tsigar jikinsa na tashi saboda yadda ta mannu sosai da jikinsa sanda take sanya masa abun,saita soma janyewa baya a hankali tana qara tazarar dake tsakaninsu sanda ta gama sanya masa,saidai da baya da baya take takawa tana jin kamar ba zata iya juyawa ba saboda bugun zuciyarta
"Madam....kada dai ki koma,baki gama sakawa sadaukin naki ba,saboda lambobin yabon nashi da saura" taji mc yana fada,tare da qarasowa daura dasu,ta waiwaya tana duban wanda ke miqo mata wani abun shigen irin wancan,saidai bambancin rubutu,hannu biyu tasa ta karba,sannan ta juyo ta dubi haidar dake tsaye,hannunsa saman abunda ta saka masan yanzu,saita sake komawa zuwa inda yaken kamar mai sanda.


Tana isa gabanshi idanuwa suka mata yawa saita fara qoqarin durqushewa a gaban nasa,da hanzari yasa hannu ya dagota,wanda hakan ya sabbaba mata fadawa jikinsa gaba daya,so yake tayi ta gama ta sauka daga wajen,saboda yadda ya fuskanci sunyi calling attention din mutane da yawa,tsintsiyar hannayenta dake riqe da igiyar ya kama,yanajin yadda tsigar jikinsa ta zuba har gefan fuskarsa,saiya ranqwafo kaman dazu,wanda hakan yasa yayiwa fuskarta rumfa fiye da dazun,ya daga hannunta har zuwa wuyansa sannan ya barta ta zura.


Gaba daya jin jikinta take yana rawa,tayi baya kamar daxu zatabar wajen,sai qafafunta suka lanqwashe,ta tafi luu kaman zata fadi,da sauri yakai mata cafka,ya samu nasarar riqo qugunta,ya tsaidata ta tsaya sosai,idanunta a nashi tasa hannunta tadan zame hannunshi daga qugunta da taga kamar baya da niyyar sakinta,sannan ta juya ta soma sauka daga wajen,wanda tuni tafi ya karade wajen,ita kuwa ji take kamar tayi tsuntsuwa ta isa mazauninta,saboda yadda duk inda ta gifta ake binta da idanu,haka duk inda ta gifta sai taji anyi magana akansu qasa qasa
"Beautiful couples"
"Ma sha Allah perfect match"
"Wow ma sha Allah" da dai sauransu,bata iya waiwayawa bare taga wanda ya furta maganar,harta isa mazauninta ta zauna tana fidda ajiyar zuciya me qarfi,tana jin yadda jikinta tacan ciki ya jiqe da gumi
"See love don Allah.....no wonder mata ke macewa murus kan Aliyyu,madam kin musu zarra fa da kikayi wufff dashi,anan wajen naga fuskokin abokan adawa da yawa" caa din dasu salma suka juyo sukayi mata ma yasa bata samu amsa maganar dr nasreen ba,duk da tanajin bata da amsar da zata bata din,sai kawai ta miqe ta soma ratsawa tana fita daga wajen,saboda wani iri da takejin kanta yayi,har yanzu kuma mode dinta bataji ya koma dai dai ba.


Tafiya tayi kadan tabar wajen dake da hayaniyar,gurin akwai qarancin zirga zirga da hayaniyar jama'a sosai,saita samu bayan wata qaramar mota ta hau samanta ta zauna saboda bata da wani tudu sosai motar.


Idanunta ta rufe dukka,ta shaqi iska sosai takai har cikin huhunta sannan ta fesar,a hankali ta soma bita na abinda ya faru yanzu a wajen.
(Ba lallai haka suke gudanar da taron qarin girmansu ba,na tsarashi a hakkane saboda yafi dacewa da abinda zai qayatar dame karatu,ya kuma tafi da salon labarin,ya alaqantu da abinda zaizo a gaba,so pls idan akwai soja ko sojanniya 😂,ko matar soja sai ku karba a hakan🙏🏽)


Sam batasan lokaci yaja haka ba tana zaune a wajen,har aka tashi taron,sai a sannan 'yan gida suka fara neman inda tayi,saidai har suka gaji da neman babu wanda ya ganta,ga kuma wayarta na wajen dr nasreen bare su kirata suji inda tayin,dole wadanda zasu koma a ranar sukayi gaba,su hajja ma daga baya suka bisu,akabar mustapha ya lalubota tunda haidar din ma bai tafi ba


Tare suka jero shida abokin aikin nasa,suna tafe a hankali da alama tattaunawa sukeyi,hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,ya zuwa yanzu babu hula a kanshi,da alama cireta yayi.


A hankali idanunsa ya sauka a kanta,saiya dan zuba mata idanu,yanason tabbatarwa itace,a haka abokin tafiyar tasa ya lura da inda yake kallon,shima sai yabi wajen da kallo
"Lafiya dabo?" Ya tambaya yana dubansa
"Ba komai" ya amsa masa yana dage kafadunsa
"Ina zuwa" ya sake fadi yana nufar inda take din.


Sam batasan da zuwanshi ba,kamar yadda bata tsammaci zuwan nashi ba,kallonta yayi na sakan biyu sannan ya hada yatsunsa ya murza suka bada ɗas ɗas.


Da sauri ta bude idanun nata,sai ta zubesu saman tashi fuskar,take suka hada ido,sai kowa ya janye tashi qwayar idanun,saita kuma ta soma yuqurin saukowa daga saman motar,a lokacin dashi kuma ya juya baya kamar wanda baison ganin saukowar tata ya zaro waya daga aljihunsa
"Kazo maza ina ta baya" ya fada kawai yana kashe wayar,sannan har ta soma takawa zata bar wajen
"Karki dara ko ina....don idan kika batan da gaske babu wanda zaki kuma wahalarwa" iya abinda ya fada kenan,saita waiwayo ta dubeshi ta watsa masa harara,saidai ta makara,don tuni ya sake juyawa ya bada baya,don haka ta dauke kanta ta samu wata motar daban ta jingina,yayin dashi kuma ya koma wajen abokin aikin nasa da suka taho tare,suka jera har zuwa bakin motar haidar din,ya budeta ya shiga ciki duk da qafafunsa na waje,da alama akwai abinda yake daukowa.


Zamansa ba dadewa ta hangi mustapha ya iso wajen,sai haidar din ya fito,ya miqawa drivernsa key,suka shiga shida mustapha,sannan suka taho da motar inda take tsaye.


Cikin salon barkwanci mustaphan yace
"Sojiya yallabiya...yallabai yace a kaiki gida" ko motsa fuskarta batayi ba bare tayi murmushi,ta taka ta isa gaban motar,ta bude murfin baya ta shiga.


Duk yadda mustapha ya qware wajen tuburata da zolayarta wannan karon baici nasara ba,don bata kulashi ba,wani iri takeji cikin jikinta,mutuwar jiki da muguwar kasala,gaba daya bata marmarin komai sai xaman kadaici,kana kuma ta zauna shuru ba tare da magana da kowa ba,a haka suka qarasa gidan.


Hanyar da motar tabi har yanzu idanunsa suna kai,saida major inusa ya taba kafadarshi sannan ya dauke idanunsa ya maida kansa
"U r lucky dabo....komai naka na zuwa cikin nasara da kyawun yanayi,ka godewa Allah,ka samu muqamin da an jima ba'a samu matashi kamarka daya riqeshi ba,ka fito daga babban family masu sonka da qaunarka,masu tarbiyya da kuma hadin kai,lastly ka auri princess charm,she captured all the people's......" Kallon da haidar din ya masa yasa bai qarasa ba,saiya cike zantukan bakinsa da murmushi kawai ya waske zancan,shi kam baima san ya masa kallon ba,kawai abinda ya sani major din ya qware sosai wajen bin mata,abinda yasa sam basa shiri ko jituwa shida haidar din,duk da yadda haidar ke sonshi,saboda mutum ne shi da baya jituwa da duk wani wanda ya kaucewa hanya ko yake ba dai dai ba,matuqar bazai gaya masa gaskiya ya yarda ya dauka ba,idan ka gansu tare da major inusa to sabgar aiki ce,saiya soma takawa yabar major din tsaye a wajen yana bin aliyyun da kallo.
"Shegen yaro......kana ganinsa haka kullum idanunsa a qasa kamar bai kallon kowa,amma yasan takun kowa,the worst part dinma....matan da ake gani bai kallo kuma basa gabansa,yayita yarfasu su kuma da shegen nacin son mai kyau da aji suyita binsa,ashe yana qare musu kallo a fakaice,banda haka ina yaga wannan har yayi wuffff da ita....gaskiya yasha kwana yaron nan" major inusa yake fada shi kadai kamar wani zautacce.


A tsaye ta samesu a falo,tana sallama umminta ta fara gani,sam batasan tazo ba,bata kuma bawa ranta zatazo din ba,saboda batajin dadi ance mata kusan sati guda kenan,duk da ita bata gaya mata ba.


Qarasawa tayi ta gaidata,sannan ta dubi salma dake riqe da jakar hajja,tana ta zuba zance ita dasu yasira wadda itama yau tazo din,duk an fito da jakankunan kayansu maman,wani sanyi ya ratsa zuciyarta,itakam dama ta gaji,so take kawai ayi a gama su wuce ko ta samu sa'ida hajja ta sakar mata mara tayi fitsari.


Data wuwwulga idanunta bata ga jakarta ba,sai tabi bayan salma data koma dauko jakar hannun hajja,ta isketa tana neman jakar a inda hajjan tace mata tana nan
"Don wulaqanci a dauki jakar kowa amma banda tawa,saboda ni bani da gata da galihu?"
"Ai an debi kayan da za'a koma miki dasu,an kawo miki wasu" duban salman tayi sanda take zuge zip din jakar
"Kamar yaya?"girarta ta daga
"Eh to....bari na tsegunta miki,kamar naji hajja tana fadin anan ke za'a barki,zaku taho tare da ya haidar ko?"
"Kambun bala'i!.....ni!,wallahi bazan zauna ba,tabdijan,ai itama hajjan ba haka mukayi da ita ba" ta fada tana jin wani tashin hankali yana ratsata,dafata salma tayi tana boye dariyarta
"Easy mana zuhra."
"Anqi easy din.....naga alama hajja wani abu daban takemin ba so ba,in banda haka ta yaya zata ce na zauna da wannan mutumin a cikin gidansa?,ya kasheni kenan akai musu gawata ko?,dama haka takeso".


"eh haka nakeso don ƙaniyarki....indai wannan shine rashin son to bana qaunarki fadi ki qara fada,ke salma tsaiwar me kikeyi ke kuma daga daukomi jaka?,miqomin driver yazo,ko mu wuce mu barki anan ki tayata zama" wani zillo salma tayi sai gata kusa da hajjan tana cewa
"Rufamin asiri kada ya zaki ya cillani ta window nayi kwanan qofar gida,a jawa yarona da mijina asara" kuka zahra ta saki harda dora hannu aka
"To wallahi nima bazan zauna ba,kowa tsoronsa yake amma haka kawai ni an hadani dashi?,saboda niba mutum bace?,idan ma cinyeni zaiyi ya cinyeni?"
"Eh haka nake nufi don gidanku,ja'irar yarinya" hajja ta sake cewa tana qwalalowa zahra idanu gamida tamke fuskarta kaman bada xahra'un tata take magana ba
"Wuce muje" ta fada tana nunawa salma hanya,tuni salman tayi gaba,tana danne dariyar dake taso mata,ita ta tseguntawa hajja cewa gobe zasuyi liyafar cin abincin dare dukka wadanda aka qarawa girma,kuma kowa da matarsa yake zuwa,idan ma akwai yara harda su,nan take hajjan tace dole haidar dinta shima asan ya zama babban mutum,dama a wajen taga idanun wata qabila yana haka haka akan jikan nata,duk inda yayi tana binsa da wani kallon yaudara na banza da wofi,tota Allah ba tataba,ba qaramin dariya akaci a motar ba da wannan ruɗu da hajjan ta hada ba,tuni itama hajja tabi bayanta,ai kuwa itama zahran saita kwashi jakarta ta rufawa hajjan baya.


Kacibus sukayi da umminta wadda ta sake shigowa ta rage mararta kada fitsari ya dameta a mota,duk sai suka ja baya,ta dubi ummin itama ummin ta dubeta,kallon da tayi mata shi ya sanyayar mata da jiki,saita tsugunna saman jakartata a wajen,ita kuma ummin ta wuce ciki abinta.


Batafi minti biyu ba ta fito,a lokacin zahran ta dawo bakin qofa ta tsuguna kamar me neman gafara ko taimako
"Kiyi duk yadda zakiyi,kiyi duk qoqarin da zakiyi ki nunawa duniya ban baki tarbiyya ba,ki nunawa duniya na sama dake basu isa dake ba,nayi imanin kaf fadin duniya idan na mutu kika laluba daga farko zuwa qarshe baki da masoyiya kamar hajja har abada,hakanan ko yanzu na mutu zan kwanta cikin kabarina hankalina kwance game da aurenki,don nasan ba zaki tozarta a hannun haidar ba,bazai taba wulaqantaki ba,ba hannun gama garin mutum kike ba,shi din na musamman ne wanda yasan da daraja da mutuncin dan adam,wanda ya kulaa ya kuma girmama rayuwar mahaifiyarki,ruwanki kiga girma da mutucinsa saboda haka,ruwanki kisa qafa ki shure.....zakiga kamar ba'a sonki,tako ina an matsa miki.....soyayya ta gaskiya itace ka tsaya tsayin daka wajen ganin naka ya gyaru kafin kowa,sannan matsalar zamantakewa a hausance sunan mace ke fara fitowa kafin na da namiji....baki da hurumin yankewa haidar hukunci sabida tsohon tunaninki na ba *ALƘIBLARKU* daya ba,akwai banbancin ra'ayi tsakaninku ko?,wannan rusashshiyar hujja ce.....a yanzu ina miki magana da harshen uwa zuwa ga diyarta......ki nutsu ki fara dora komai kan muhallinsa da saitinsa.....sai angwada ake sanin na qwarai" daga haka ummin tayi gaba abinta ba tare data waiwayo ba,ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta,ita kadai tasan wanne fata ke gareta,ita kadai tasan adadin sau nawa tana hana idanunta bacci don ingantar rayuwar yaranta.


Da qyar ta tashi daga wajen ba tare data dauke jakarta data janyo wajen ba,a hankali tana jin yadda hayaniya da surutunsu keyin nesa da gidan,da alamu ficewa sukeyi,da qyar takai kanta bakin katifar ta zube,duka zantukan ummin nata sun tsaye mata kamar qusa a qahon zuci,hakanan sun kashe mata duk wani qwari na jikinta.
23/10/2021, 08:46 - 👍🏻👍🏻: 27


Tsahon awa guda gidan ya dauki shuru,duk da lokaci zuwa lokaci tana dan jiyo motsi da maganganu sama sama daga falo zuwa kitchen,wanda ta tabbatar da ma'aikata ne.


Tun azahar take kwance bayan ta gama hawayenta son ranta ta godewa Allah,kota kan abinci bata biba,duk da karin safe ne kawai a cikinta,abu daya ke tada ita shine sallah,sai ruwa kawai data ke sha wanda shima cikin dakin yake jiya da dare suka shigo dashi basu shanye ba,haka ta dinga juyi ita kadai,har zuwa lokacin da duhun magarib ya sako kai,aka fara qwala kiran sallahr magariba,saita miqe tana jin yadda tsakiyar cikinta ya qulle,da alamu ulcer dinta tana son tashi kenan idan batayi wasa ba,hakan ya sanya sai data fara fitowa parlour ta bude fridge ta dauki fresh milk mai sanyi babban gora daya tana duban yadda falon ya koma fes,ko ina ɗas ɗas dashi yana fidda qamshi,kamar ba'a taba yin baqi ba,ba abinda ke fita sai wani samfurin qamshin freshner na musamman,ga abinci a jere a cikin tsari saman dining table,saita dauke kanta ta koma daki,ta zauna ta zuqe madarar tas sannan ta shiga bandaki,tana fitsari taji gefan mararta na qullewa
"Ya salam" ta fada,alamun period na iya zuwa anytime kenan,haka ta daura alwalarta ta dawo dakin ta tayar da sallar.


*Aliyyu Haidar*


Sosai yayi relax a bayan motar bayan ya aje hularsa a gefe yana furzar da iska daga bakinsa,yana jin yadda sanyin ac ke ratsashi tare da qara haifar masa da kasala da kuma tayar masa da gajiyarsa ta zirga zirgar wunin yau.


Zuciyarsa da qwaqwalwarsa tayi nisa wajen tuna abubuwan da suka faru yau wayarsa dake aje tare da hularsa ta dauki tsuwwa,dan qaramin tsaki yaja,ba kasafai ya fiya son kira ba,saidai yau yasha kiran har ya gode Allah,a hakama don yana kashewa ne baya amsa wani.


Ganin sunan me kiran yasa ba shiri yakai hannu ya dauka,labbansa suka motsa cikin ransa ya furta
"Rigimammiyar tsohuwa" saiya kara a kunnensa
"Badai har kunje gida ba?"
"Harma mun huta yanzu haka?"
"Ma sha Allah,sannunku da qoqari,Allah ya qara girma da nisan kwana me amfani"
"Amin ya rabbi...amin Aliyyu,Allah yayiwa rayuwa albarka"
"Amin hajja"
"Yauwa.....dama na kiraka ne na gaya maka,nabar amanar jikata a gidanka" fuska yadan yamutse yana son ya fahimci maganar tata,kamar kuwa tasan tunanin da yakeyi tace
"Matarka zahra....zaku taho tare idan ka gama abinda kake...."
"Amma hajja....bamuyi maganar ba....sannan ma kuma karatunta fa?"
"Kai da ita ku kukasan wani karatu.....,jan kunne na kiraka nayi maka,aronta na baka,bance kuma atabamin ita tun yanzu ba ehe" tun kafin takai ga kashe wayar shiya kashe,saiya jefata gefe yana dafe kansa,hajjan ta soma wuce tunaninsa,tunda harta fara masa manya manyan maganganu irin wannan,banda abinta ma shi da bashi ya nemi a barta ba su suka barta don raɗin kansu har tazo da wannan maganar,shikam wannan sabgar gada dayanta akwai qwara a cikinta.


Da ire iren wannan tunanin daya ci gaba dayi har suka isa gidan,ya fita yabar drivern yana kulle motar,yayi cikin gida,ma'aikatan dake harabar gidan suna masa sannu da dawowa.


A yanayi na gajiya yake nufar dakinsa yana observing na falon,komai fes kamar yadda yakeso,don babu abinda yafi tsana irin qazanta kaf rayuwarshi,shi yasa har yanzu ba abincin kowa yake ci ba,hakanan ba kowa yake bawa wankinsa ba.


Bandaki kawai ya wuce direct ya kunna water heater,saida ruwan ya tafasa ta kashe kanta sannan ya daidaita na zafi dana sanyi yadda zai masa dai dai da wankansa,kana ya shiga qasan ruwan ya soma sauka tun daga kansa yana tafiya da gajiya da kasalar data ma jikinsa qawanya,saiya rufe idanunsa yana tuna irin tarin baiwa da Allah ya masa,musamman a yau din,a hankali can qasan maqoshinsa ya dinga furta
"Alhamdulillah...Alhamdulillah".


Ya kusa minti talatin yana sakarwa jikinsa ruwan dumin sannan ya cuda sabulun wanka ya dauraye ya hada da alwala ya fito.


Sai daya tsane jikinsa da towel sannan ya nemi doguwar riga me gajeran hannu ya sakakkiya ya saka,ya feshe jikinsa da turaruka bayan ya taje kansa,sannan ya koma ya zauna saman kujerar dake dakin ya dauki wayarsa ya soma laluben 'yan gidansu,yanason yi musu ban gajiya,don wayar yakeson ya kashe gaba daya,don idan ya kwanta ya tabbatar salla ce kawai zata tasheshi,saboda yadda yake jin jikinsa.


Abban tsakiya ya fara kira,sannan abba yusuf,abbansa ne daga qarshe sai ya kira ummi,tata number bata shiga ba,don haka ya kira umma sa'annan ya kira mamanshi.


Tana hannun nurain a sannan,da hanzari ya nufi dakin maman yakai mata,don yasan zaiji babu dadi idan yayi gigin daga kiran ya haidar din,tunda yasan bashi yake nema ba.


A ladabce ya gaidata ya mata sannu da hanya,ta amsa masa sannan addu'a ta biyo baya,cikin farincikin dake ratsawa har cikin zuciyarsa yake amsa mata,sai kuma tayi kiran sunanshi
"Don Allah ka kula musu da amanar yarinya da aka bar maka,kada kayi wani abu da xai zamana ka watsamin qasa a ido,ka kuma barar da tarbiyyar da muka baka,a qarshe kuma ka qaryata soyayyar da hajja ke maka"
"In sha Allah mama zan kula....in sha Allah" daga haka sukayi sallama ya aje wayar yana sakin ajiyar zuciya yana shafa kanshi da hannunsa guda.


Tsahon wasu mintuna yana a haka ba tare da yasan me yake tunani ba,saiya miqe ya zura slippers dinsa ya fito falon.


Dining ya isa,ya zauna ya fara zuba black tea ya dumana cikinsa,sannan ya duba abubuwan da aka dafa din,ya zuba iya yadda zai iyaci ya koma saman kujerun falo ya zauna acan ya fara ci yana yi yana duba saqonnin da suka shigo masa waya yana maida amsa tsahon wani lokaci.


Dai dai lokacin da yunwa sosai ta dinga sakadar zahran,ta dinga juyi tana jin yadda ulcer dinta ta fara motsawa harta fara sanya mata ciwo tsakiyar cikinta,saita koma rub da ciki ta kwanta qwalla na sauko mata,ita koma meye ya faru hajja ce sila,ita ta jawo mata komai.


Qarfe hudu na dare ya farka kamar yadda ya saba tashi duk dare,wansa baya komawa daga sannan kuma sai bayan sallar asuba,a nutse ya miqe ya shiga bandaki ya dauro alwala,saiya janyo wayarsa zai duba lokaci,saboda dakin ba'a sanya mishi agogo ba tukunna,don gaba daya cikin kwanaki biyu aka zuba dukka furniture din gidan qarqashin jagorancin wani kamfani,duk da ya kashe kudo sosai shi kansa ya sani,amma yadda suka tsaran gidan da kaya masu kyau da inganci kadai ya isa ya gaya maka sunsan aikinsu.


SMS ya gani wanda da alama tun daren jiya ya shigo,dannawa yayi ya bude saqon,daga ummi ne,saiya zauna saman abun sallar tashi sannan yabude saqon ya fara dubawa.


A hankali ya sauke ajiyar zuciya,a rayuwa bayaga mahaifiyarsa da hajja itace mace ta uku da yake ganin kima da darajarta fiye da kowa,saiya sauke ajiyar zuciya yana tuna cewa akwai jininta cikin gidan,wanda karon farko sun kwana

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment