Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karonma da kallo ya hajjan ta bita,cikin ranta ta amsa addu'ar data yiwa mijinta kuma masoyinta,tana jin yarinyar cikin ranta sosai fiyr da sauran jikokinta,su biyu kacal suka samu irin wannan babban matsayin,duk da qoqarin boyewa da take da kuma nuna duka dai dai suke.


Tana yawan godiya ga Allah daya sanya qauna da zumunci mai qarfi tsakanin ahalinta,tun daga kan yaranta zuwa jikokinta,tsabar son su zamaTsintsiya madaurinki daya ya sanya tun mijinta na raye suka yanke zaman dukka yaransu maza tattare a waje daya,matanne basu da wannan ikon ko qarfin a kansu,hakan kuma yayi tasiri wajen sake maida zuri'ar tata tsintsiya madaurinki daya,duk da ance zaman tare zo mu zauna zo mu saba,hakanan baka rasa banbancin halaye da ra'ayi wanda kan kawo sabani lokaci zuwa lokaci,saidai a nata ahalin akwai qarancin hakan sosai,don bazai yiwu ace babu ba,kusan halayya ce tadan adam,kuma sunna ce ta zaman tare.


Duk da wannan babban abinda ke bata mamaki da daure mata kai shine rashin jituwar dake tsakanin zahran da yayanta,kusan abune daya dauko dogon tarihi ya kuma samo asali da tushe tun da dadewa,tun abun bai zama wani abun damuwa kallo ko dubayya ba har takai a yanzun yana damunta lokaci zuwa lokaci,saidai tana saka ran watarana komai zai zama tarihi,kamar akwai sauran quruciya ne jikin xahran.


Sashen yayan mahaifinta da suke kira da abba babba ta fara shiga,sashe ne mai kyau kamar yadda ainihin ginin gidan ya nuna,babban falo wanda ya cinye set din kujeru har guda biyu,dakuna a qasa kitchen da bandaki,sai dakunan matan gidan dake sama,duk da kowacce tana da guda daya a qasa.


Mommy ta tadda a falon ,wanda ke mazaunin amaryar abba babba tana cirewa yara da dawowarsu gidan kenan unifoarm,wanda dukkansu yaran gidan suna makaranta guda ne,akan daukosu tare a kuma kaisu tare,bisa jagorancin drivern gidan a wadatacciyar motar da aka ware musu don wannan hidimar.


Kanta ta daga tana amsa sallamarta sanda take cirewa yaronta safarshi,fuskarta fadade da fara'a tace
"Maraba da 'yan boarding" qarasowa tayi tana murmushi,ta zauna hannun kujerar tana amsawa gami da yiwa mus'ab da ake cirewa safa tsiya
"Wai kai bakasan ka girma bane,saura kadan kayi shekara goma fa,amma har yanzu safa ake cire ma"
"Murmushi mommy ta saki
"Kema kya fada inna wuro,kullum sai an cire masa kamar yaron goye..." Dariya ta sakeyi tana kuma dan tsokanarsa kafin daga bisani ta juya tana gaida mommyn,fuska a sake take amsata,ta tambayi abba babba
"Abbanku ai kinsan ba zama,tun sassafe ya fita kasuwa"
"Mama fa?" (Uwar gidan mommy)
"Yau suna hidima ne,ita dinma tun dazu ta fice" jin haka yasa ta miqe tana zura hannu a aljihun rigarta,ta soma zaro alawa masu dan girma tana rabawa wadanda ta taras a falon,duk data girmesu amma ba wani girma ne me yawa can ba,shekarun data basun bazai gaza biyu zuwa uku ba,idan yayi yawa hudu
"Baki gajiya,keda kika dawo daga makaranta harda wata tsaraba" murmushi kawai ta yiwa mummyn tana ficewa.


Sashe na biyu ta shiga,sassan abba yusuf,wanda keda matan aure biyu shima da yara tara,amarya nada uku,uwargidan nada shida,shima dai kamar shigen ginin waccan sashen,komai cikin tsari,da alama kusan dabi'ar jama'ar gidan ce wato tsafta,su dinma faran faran suka gaisa ta wuce sashen abba abu wanda cikakken sunanshi shine abubakar,matarshi daya da yara bakwai,sai abban tsakiya shima matarshi daya,daga nan sai sashen mahaifinta.


Sashe ne dake da girma da qima a idanunta,yake kuma da dimbin tarihi cikin rayuwarta,sashen da a shekarun naya suka rayu kamar sauran sassa dake gidan,cikin walwala farinciki da qaunar juna,qarqashin inuwar adalin uba kuma mahaifi a wajenta,saidai ta farat daya mai rabawa ta raba mai raba soyayyar iyaye da 'ya yansu wato mutuwa,a lokacin da suke tsaka da gudanar da rayuwarsu.


Mahaifinta uba ne da ya zama daya tamkar da dubu,wanda bashi yiwuwa ta manta soyayyarshi garesu,musamman ita din da take 'yar fari a wajensa,ta kuma ci sunan mahaifiyarsa,saiya zamana soyayya da kulawar da yake bata ta dabance,har kullum mutuwarshi sabuwa ce a ranta,rana da lokacin basu taba bace mata ba daga idanunta.


A hankali tayi sallama cikin falon,qannenta dake xaune suna cin abincin rana suka amsa,cikin farinciki qauna irin ta 'yan uwantaka suka miqe suna mata oyoyo,fuskarta washe da fara'a take amsa musu,wanda hayaniyarsu ta fito da mahaifiyarta dake kitchen.


Kyakkyawar mace mai kyan zubi da haiba,ma'abociyar tsafta nutsuwa da kyakkyawar dabi'a,wanda kyawun dabi'arta ya sanya koda bayan rasuwar mai gidanta dangin mijinta suka kasa rabuwa da ita,suka roqi alfarma taci gaba da xama dasu har zuwa sanda xata buqaci aure,su kuma zasu tsaya mata tamkar nata dangin.


Duk da cewa bata rasa wani gata ko kulawa daga nata dangin ba,amma hakan bai hanata amsar tayinsu ba,saboda tsantsar dattako irin na uwar mijinta,da yadda ta nuna mata qauna da kulawa tun haduwarsu har xuwa yau din,bugu da qari kuma,bata jin xata iya sake aure a sauran rayuwarta data rage,tunda ta rasa miji daya tamkar da dubu irin sa'id uban 'ya'yanta.


A nutse ta qarasa daura da inda mahaifiyar tata ke zaune
"Ina wuni ummi"
"Lafiya qalau,ya makaranta ya kuka barosu"
"Lafiya lau ummi,wannan karon duka babu dadi,ni kadai aka bari a makaranta,yasira ta rigani dawowa" tana zare carbin hannunta ta amsa
"Eh ai jikin nata alhmdlh da sauqi,jiya na shiga na dubata" ajiyar zuciya tadan saki
"Tana raina ummi,gobe in sha Allahu nima zanje na dubata"
"Ya kamata kuwa,don dazu yaayan ma ya kirani yace an daukoki ko?"
"Eh su ya musty ne ma suka je a motar wancan mutumin" sosai ummin nata ta tsareta da idanu tana kallonta,sai a sannan ga gane tabargazar data tafka,saita dauke nata idanun tana son wayancewa
"Inna wuro?,waye wancan mutumin?,yayan naku?,ashe qara lalacewa kike?,duk fadan da nake miki bakiji kenan?" Marairaice mata tayi,don idan da sabo ta saba da fada daga wajen ummin indai a kanshi ne,abu na qarshe kuma data fi tsana kenan a rayuwarta
"Kiyi haquri ummi,mantawa nayi,bazan sake ba" kanta ta dauke kawai daga gareta,tasan ta fada ne kawai,amma wannan halayyar ta jima dason rabata da ita amma ta kasa,ta zame mata jiki,rabuwa da ita sai a hankali,bata tashi daga wajen ba sai data ji tace
"Allah ya kyauta,Allah ya rabaki da wannan halin".


Dakinta dake sashen wanda ba kasafai ta fiya kwana a ciki ba ta wuce,tsaf yake kamar ko yaushe,duk da bata kwana ciki amma kullum saita gyarashi,'yar madaidaiciyat cupboard dinta ta bude,ta zabi kayan sawa adadin wanda takeso,ta debi kayan kwalliya mayafanta da sauran muhimman abubuwa don maidasu sassan hajja,saboda muddin ta dawo hutu tafi xama a can,bama ita kadai ba duka 'yammatan gidan dakin dake sashen hajjan suke tarewa har sai ta koma.


Ita dinma tafison zaman can din,saboda tafi sakewa sosai fiye da sassansu,hajjan na barinta tayi yadda takeso koma bayan ummin nata dake da tsauri da kuma dokoki iri iri.


Kai tsaye ta koma sassan hajjan,duka sun fice da alama kowacce akwai abinda zatayi,hakan ya mata itama saboda wanka takesonyi ta kuma rama bashin baccin da batayi ba daren jiya a makaranta,don su kwana waqe waqe na murnar tafiya gida hutu,gabanin asuba koma kowa ya shiga sabgarsa taci gaba da hada kayansa da kuma bin layin wanka.


Sai data fara zuwa gun wayarta dake chargy,hopefully ta taba screen din ya kawo haske cikin zumudi,don ta tabbatar zata iske texs ko miscal na nuraddeen kamar yadda ya saba mata a kullum idan ta dawo hutu.


Saidai kuma ga tarin mamakinta babu kiran hakanan babu saqon nashi,sosai abun ya daure mata kai,amma saita bashi uzuri,ta shiga ta duba balance dinta.


Naira hamsin ce tayi ragowa a layin nata,ta tuna zahra takwararta ce ta mata transfer kyauta ana ya gobe xasu koma hutu,tunda tace ga wanda ya tura mata kudin ta raba musu 50/50 a ciki sai taji credit din bai burgeta ba,amma yanzun zai mata amfani,don haka kai tsaye ta shiga rubuto lambobin nuraddeen daka wanda ta jima da haddacesu ta danna kira,take sunan my happiness ya bayyana saman screen dinta,ta kalli sunan ta saki murmushi tana kuma sauraron yadda wayar ke ringing.


Dab da zata katse aka daga,sallama ya fara yi mata,saita sauke a jiyat zuciya cikin shagwaba tace
"Nayi fushi"
"Afuwa,kaina bisa wuyana,kina raina inata son na karki,damac ce ban samu ba". Duk da uzuri ya nema amma sai taji banbarakwai,don wannan shine karon farko daya soma neman uzuri irin haka a wajenta,amma saita saki murmushi
"Nayi maka,amma fa lasam nayi kewarka da yawa"
"Nima haka princess,an dawo lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh"
"Ya makarantar,ya mutan gidan?"
"Kowa lafiya lau" zai soma magana taji ana mata warning cewa kudinta sun kusa qarewa,daga bisani ta tambayeshi me yace
"Nace ne ina hajja da ummi"
"Duk lafiya na samesu....." Ta kasa kunne taji yace xai shigo a yau din,saidai tuni kamfanin waya suka katse kiran saboda qarewar kudin wayar tata,saita aje wayar gefanta tana dan dubanta,tasan cewa babu jimawa xai biyo sawun kiran nata,don haka ta zauna daura da wayar tana dan gyaran kayanta tana dakon kiran.


Harta gama gyaran bataji shigowar kira ba,sai data miqe tana shirin shiga bandaki ta watsa ruwa taji sautin shigowar saqo,ta miqa hannu da hanzari tana dubawa,saqon daga nuradden dinne
"Zan kiraki" abinda ya qunsa kenan,saita maida wayar ta ajjiye ranta tana cewa
"Lallai yau wanne irin busy happiness ya shiga haka" ta wuce bandakin bayan ta daura towel din wanka.


Aqalla minti goma sha biyar ta shafe a bandakin sannan ta fito tana mita
"Haba,babu inda yakai gida dadi,me za'ayi da makarantar kwana,babu abinda yakai gida dadi wallahi,inda a school ne ina ka isa ka dade haka,da tuni an matsanta miki daki fito,mtseww...wallahi badan yaaya da kuma ummi da bazan koma ba" da wannan qananun mitocin mata ta qarasa gefan qatuwar kafitar dake dakin ta zauna,wanda daura da ita 'yar drower ce dake jere da kayan shafe shafenta,zahra ba daga baya bace wajen son ado da kwalliya,hakanan idan ta fannin yawan sutura da kayan qyale qyalen rayuwa ne tana sahun gaba cikin 'yammatan gidan,saboda ta kowanne fanni yi mata ake dalilin maraicinta,qannen mahaifiyarta mata da yayan mahaifiyar nata dake matuqar qaunarta,wanda dukkan abinda xaiwa yaransa to lallai fa saiya yiwa zahran,hakanan 'yan uwan mahaifinta dake gidan,duk sanda wani xaima iyalinsa saiya hada da ita,ga hajja a gefe itama da ba'a barta a baya ba.


Sa'annan uwa uba wani irin farinjini da Allah ya yiwa zahran tun tana mitsitsiyarta,don mahaifanta ma sam basa yarda a karbi abun hannun kowa akan yarinyar,haka halittarta take,tun abun na baiwa mamanta mamaki harya koma bata tsoro,hakan ya sanya tun kan ta mallaki hankalinta ta tsaya kai da fata wajen mata addu'ar samun kariya da samun miji na gari,don ita kanta tasan Allah ya yiwa diyartata baiwar wani asirtaccen boyayyen kyau,tana tsoro n kada hakan ya zama wata sila da za'a shiga rayuwar diyartata a cutata mata babu dalili,ta sani cewa sautari baiwar kyau jarrabawa ce,qalilan ne kuma cikin mutane ke iya cinyeta,musamman mata.

A nutse ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar atamfa cotton mai budadden dinki,ta gyara kanta da ribbom wanda da wahala kaga kitso a kanta,duk wanda ya santa yasan bata qaunar kitso tun yarinta har zuwa yanzu data girma,duk sanda xa'a mata kitso saita tarawa mai kitson jama'a saboda tsabagen kuka,daya daga cikin abinda ya sake sawa basa jituwa da yayanta kenan,yana ganin kamar an bata ta ne an sangarta ta.


Tana tsaka da fesa turarenta mai sanyin qamshi wanda ta saba ta soma jiyo sautinsa.


Sassanyar murya mai zaqi,amma cike da kaushi da kuma fada yake magana,da alama wani abun ya faru ne,baki ta tabe tana aje turaren nata,maimakon ta fito yadda tayi niyya da farko sai kawai ta fasa,ta koma gefan katifar ta zauna tana sauraren fadan nashi,duk da cewa bata iya fuskantar me yake fada.


Baki ta sake tabewa karo na biyu
"Ayi mutum sai shegen kaushin hali da fushi,Allah ya kyauta" ta fada tana jawo filo bayan tayi rub da ciki saman katifar,sannan ta janyo wayarta tana sake duba kira ko saqon nuraddeen,saidai har yanzun babu ko daya,saita maida ta aje tana ayyanawa wala'alla bai gama uzurinsa bane.


Shigowar hafsat dakin kamar wadda aka tunkudo ya sanyata miqewa ta xauna,fuskarta a hade da alamun kamar ma hawaye ta gama yi
"Yaya?" Zahra ta jefa mata tambayar tana gyara zamanta idanunta kan hafsan
"Yaa haidar mana......shikenan da zarar ya dawo mutum bashi da sauran sakewa,kome kayi baka masa dai dai ba,haba?" Koda bata tambaya ba tasan kwanan zancen,don halayyarshi ba baquwar halayya bace a wajensu,don haka baki ta tabe
"Hmmmm,ai ni shi yasa nake godewa Allah dasu abba basu dauko aqidar sai munyi karatu ba kafin aure,inda haka ne Allah kafin mubar gidan nan saiya sa mana hawan jini" dubanta hafsa tayi
"Ni kuma kinsan hakan baimun ba,nafison naci gaba da karatu kafin ayimin aure,inda xasu sauya shawara wallahi hakan yafimin,amma ya haidar kusan yafi kowa na'am da wannan tsarin tun xamanin su ya khairiyya" hararara zahra ta jefeta dashi tana cewa
"Bakinki ya sari danyan kashi,ni da kike gani na nan ba'a da candy qalilan ce inji 'yan arabiyya,babu wani karatu da xan tsaya wahal da kaina inayi,me yafi aure dadi?,kaida masoyinka?,ka samu 'yanci babu me takuraka?,tabdijan,ke ai saikita zama kici takarda da biron" ta fada tana komawa zuwa kwanciyarta ta daxun.


Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don duk cikinsu kowa ya san ra'ayin mahaifansu ya dace da ra'ayin zahran,kuma ita hakan yayi mata dai dai
"Allah ya shiryeki zahra"
"Amin....ai dan sunna bayaqi sunna ba ko"
"Wannan haka yake malamarmu"
"Kyaji dashi" ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna hira,tana kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani abun kafin ta dawo ta kwanta tadan matse gajiya.
23/10/2021, 08:36 - 👍🏻👍🏻: *KIJI TSORON ALLAH☝🏾,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*


03


Kusan minti talatin kafin ta daina jin duriyarsa,zuwa sannan bacci ya soma fisgar hafsat,saita aje wayarta ta miqe a hankali tana gyara daurin dankwalin kanta,ta isa bakin qofar dakinta ta zura takalmanta sannan ta wuce kai tsaye zuwa falon.


Kyakkyawan matashin saurayin da a qalla bazai wuce shekara talatin bane zaune cikin falon,saman lallausan center carfet din dake shimfide tsakiyar kujerun,ya miqe dogayen qafafunsa ya kuma hardesu waje daya yana kadasu a hankali,kallon farko da zakayi masa zaka fahimci wani irin kwarjini shimfide saman fuskarsa,wanda ke cakude da rashin fara'a da kuma daurewar fuska,wanda ko a yanzun da yake zaune shi kadai cikin falon wayarshi qirar iphone 12 na tsakiyar tafukan hannayenshi dake saman cinyoyinsa yana amfani da ita fuskarshi a hade take,da alama gwanin iya tsare gida ne qwarai,gefansa kwanukan abinci ne a jere,bata sani ba ci zaiyi ko kuma baida niyyar ci ya ajesu ne kuma baxai magantu yace azo a dauke ba.


Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa ba sai sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da saisayen irin sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana sheqi,da alama ana bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da kwarjini takeyi ba,ta kuma dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane waje daya,saboda aikine na hidimtawa qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al'umma da rayukansu.


Saɗaf saɗaf take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi ya daga kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida kanshi ga wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa qudurinta na wuceshi da tayi niyya,ta dawo da baya
"Ina yini yaa haidar" kamar bai jita ba,hakan ya bala'in ɓata ranta,ta tsani wannam halayyar tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba damuwarta bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.


Ganin bai amsa ba ya sanyata miqewa donta wuce abinta,sai a sannan ya magantu
"Lafiya.....zoki zubamin" ya fada ba tare da ɗago daga duban wayarshi ba yana mata nuni da fulasan gefansa.


Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza yana jiran wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira har sai mai zuba masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don tana fara zuba abincin ta tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.


Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya koma cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan masauki saman farar shirt din dake jikinsa.


Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya maida idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki da niyyar yi masa bayani saidai ya rigata magantuwa
"U r very stupid....baki da hankali ne?...."
"Ashsha.....inna wuro garin ƙaƙa?" Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta amma sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso
"Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi" tsaki ya saki kawai yana miqewa,ba tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita
"Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu mutanen,sakamakon sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)"
"No,barshi kawai"
"Abincin fa?" Ta fada sanda yake gab da ficewa
"Ku amfaneshi"ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.


Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida murguɗe murguɗen rawa
"Ja'irah,hala kina sane ko?" Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke fidda qamshin turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa
"Inda ina sane ai da sai abun yafi haka.....arashi aka samu,kuma hakan yamin dai dai"
"Zahra....zahra....kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba"
"To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka kawai sai nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma yana nan,da nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya damemu" daga haka ta jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon ikon Allah"


"Allah ya shirya" hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata ba taci gaba da zurin abincinta.


Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa dinkin A shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta me keyboard itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me waya torching,ita dinma sai da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga kwata kwata haidar ya barta da wayar,a hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace sam ba za'a watsa masa qasa a idanu ba,tunda wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa uba an hanata walwala an dauketa an kaita makarantar kwana aiko ba'a hanata riqe waya ba a duk sanda tazo hutu,tunda hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe wayar yafi riqeta yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.


"Lalalaaaa......lallai zahra.....wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin hadawa yaa haidar abinci bane?" Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta dubeta
"Sune mana....kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki" kamar wadda ta danawa wuta a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido
"Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka"
"Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari" cewar hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki
"Ko iya haka ma alhmdlh" dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta
"Daɗina dake hajja baki iya samun magana daya ba.....muje sister ki bani labarin daxu"
"Zakici ƙaniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki" ta fuskanci sarai me take nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin ƙarshe sai tafi kowa mita da jin ciwon hukuncin da za'a matan.


Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan
"Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci" ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane salma
"Ki saurara min 'yar baqincikin baccin mutum" daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
"Wai kinsan meke faruwa kuwa?"
"A'ah saikin fada" inji zahra
"Sabon kamu fa nayi" sosai zahra ta maida kallonta ga salma
"Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?" Farr tayi da idanunta
"Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman" idanu dukka zahra ta fiddo waje
"Keee salma.....kiji tsoron Allah,sulaiman din?" Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta
"Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?" Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami
"Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba".


Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban zahra
"Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata.....idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba'a samun wanda hakan bane.....amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha'inta ne,basu da *ALƘIBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba.....na shafa rana guda naji wayam" ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.


Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma 'yar tamore
"Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba" zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
"Eh....kekam taki zuciyar na daɗe da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan" kusan hirar da suka dinga yi kenan a

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment