Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na rana haqurinta ya qare,ta tsaya qofar dakin nasa tana saisaita kanta,tare da baiwa kanta qwarin gwiwa,a hankali ta dora hannunta saman handle din ta murda qofar ta bude.


Dai dai lokacin yana kwance rub da ciki cikin lallausan bargonsa yana duba saqonni cikin wayarsa,ya lulluba har kusan kansa,wanda duk wanda ya shigo xai dauka ma duka har kan nashi ya rufa,duk da acn dake kadawa cikin dakin amma jikinsa babu riga,sai wani boxer dake a jikinsa.


Duka yau bashi da intention na fita,don ya gama da office gaba daya,sun sanya date ma na tafiyarsu,kowa an bashi damar zuwa ya shirya sosai,yasan kuma yau din ya soke tafiyarsu saboda hajja,don haka ya yanke shawarar yini a gida ya huta sosai.


Tsayawa yayi da replying massages din sanda yaji an turo qofar ba tare daya waiwayo ba,zuciyarta na wani irin bugawa ta dake tayi sallama,saiya juyo rigingine,wanda hakan ya basu damar ganin juna sosai.


Kowanne sai da yaji shock a jikinsa,yanayin data ganshi babu riga ya tsoratar da ita,wanda hakan ya bayyana ingarman qirjinsa,ya kuma bayyanar da tarin gashin daya lullubeshi,mai laushi kamar shima gyara yake masa,inda shi kuma kwalliyarta ta dauki hankalinsa,wanda tsabar zaquwar tazo ta sameshi su wuce yasa ta manta ko dankwali bata daura ba bare aje ga batun mayafi,idanunta ta rintse sannan tace
"Ina kwana....na shirya tun daxun" dan ture bargon yayi,ya kwanta rigingine sosai,saidai ya tallafe kansa da hannayensa guda biyu ta qeyarsa,yadda zai bashi damar kallonta sosai
"Me kika ce?" Ya fada da lallausar muryarsa data soma canzawa saboda wani yanayi daya tsinci kansa,sake maimaitawa tayi harda dan daga murya don yafi jinta sosai.


Ajiyar zuciya ya saki sannan yace
"Na soke tafiyar yau" gaba daya ta bude idanunta gami da wara su a kanshi cikin yanayi na tsoro,wanda hakan ya haifar masa da wani abu cikin jikinsa,saiya lumshe idanu sannan ya bude sanda duka a kanta sanda take fada cikin rudewa
"Amma fa hajja ce tace"
"Hajja ke aurenki?" Ya jefa mata tambayar data sanyata yin shuru,sake maimaita tambayar yayi,a hankali tace
"Amma ita ta....." Sai kuma ta kasa qarasawa,ta canza salon zancan da
"Aro na ta baka,kuma tace ka maidani,bai kamata daga aro ka riqe mata ni ba...." Zancan nata saiya bashi dariya,can qasan ransa ya dara,me yasa suke son maidashi wani sakarai,amma a saman fuskarsa babu alamun dariya,hakanan yaji cikin zuciyarsa yana son nuna mata gaskiyar magana,ya kamata ta fahimci gaskiya ya gayawa kansa,ko yaya ya kamata ta tsorata tasan kuma meye matsayinta,don haka yana daga cikin bargon yace
"Zo ki gani" saita zuba mishi idanu tana dubansa,yayin da shi kuma ya dauke kansa daga kanta,ya maida gefansa kamar mai kallon wani abu.


A hankali ta fara takawa zuwa inda yake kwancen,zuciyarta na gaya mata akwai abinda zai nuna matan,gefansa ta tsaya,tana niyyar cewa gani.....ba zato ba tsammani taji gaba daya an fincikota,kafin ta gane abinda ke faruwa sai gata kane kane saman qirjinsa,ya matseta gam,sautin muryarsa deep inside har ears taji yana fadin
"Daga ke har hajjan bansan a inda kuka gano ana baiwa mutum aron matarsa ba,idan ita ta manta ke bari na baki tambarin da zaki dinga tuna u r my property" kafin ta ankara ya soma aika mata da wasu hot kisses,tun daga cikin kunnenta zuwa wuyanta,saiya fara yamutsata son ranshi da dukka hannayensa biyu,tuni yakai hannunshi muhallin dake tsole masa idanu,abunda ya kusa tafiyar da numfashinsu duka su biyun,zahra tsananin tsoro da firgici,yayin da shi kuma tadda abun fiye da yadda idanu ke iya gani ne,cikin sakanni ya soma fita daga saitinsa.


Mataki bayan mataki ya dinga bi yana wucewa,duk sanda yaje wani mataki sai zuciyarsa da gangar jikinsa ta buqatu zuwa mataki na gaba,ta bangaren zahra gaba daya duniyarta ga gigita,saboda bijirowar abinda bata taba tsammata ko.kawoshi cikin tunaninta ba,koda a cikin mafarki kuwa,hakan ya sake razanata,ta dinga qoqarin tattara dukkan qarfinta daya rage tana yunqurin turashi daga rumfa da kuma babakeren da yayi mata,saidai ina,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,a banza wai man kaza.


Tsoro sosai ya shiga bata ganin yadda ya soma juye mata zakin sosai,ya fara fita daga hayyaci da kamanninsa,ya koma yin komai da zafi zafi kamar mayunwaciyar dabba,mazantakarsa da jarumtarsa kawai yake nunawa ba tare dashi kansa ya sani ba,tsoro sosai ya cikata da fargaba,dana sanin shigowarta dakin ya fara mamayeta.


Bata gane abun da gaske bane sai daya fara neman hanya ɗoɗar,ta tabbatar idan dabararta batayi aiki ba tana ji tana gani kome zai lalace mata,saita saki kuka sosai,wanda dama tun daxun take yinsa,saidai baiyi qarfi ba kamar yanzu da take neman agaji da gaske,kiran sunan hajja da umminta data fara yi shine ya karyashi,ya kuma dawo dashi hayyacinsa,a hankali saiya fara dawowa hayyacinsa,ya kuma soma tuna abinda yake shirin aikatawar,sai duk aka zare masa wata laka ta jikinsa,saiya zame gefe guda,ya kuma hanata tashi sanda take yunqurin tashi cikin kuka,sukaci gaba da kasancewa a haka har tsahon wani lokaci da kukan nata ya tafi gaba daya,sai dan zafi zafi da take ji daga can,duk da ba wani me yawa bane.


Idanunta ta lumshe sanda ya miqe ya sauka daga kan gadon,bandaki ya shiga yana jin wani abu kamar jiri jiri na dibanshi,hakanan yayi sakayau kamae iska zata kwasheshi,ruwa ya tara mata sosai mai dumi,don ya sani daga shi har ita wanka yahau kansu,bai jima ba ya fito
"Ki shiga toilet akwai ruwa a ciki" daga haka ya nufi qofa ya budeta ya fice.


A falo yaci burki,saiya samu daya daga cikin kujerun dining ya zauna akai,yasa gwiwar hannunsa saman cinyarsa yana dafe kansa da dukka tafukan hannayensa,wani iri ciwo kan nashi yaji yana masa,dukka jijiyoyin kansa sun tashi,idanunsa da suka sauya launi har yanzu basu daidata ba,duka kansa ya cushe ya kuma kulle,ya rasa wanne tunani zaiyi,miqewa yayi kawai ya koma dakinta,ya bude nata toilet din ya shiga ya hada nashi ruwan wankan.


A hankali ta sauka daga gadon tana karantar kowanne canji daga jikinta,ta soma takawa zuwa bandakin,yanayinta yadan sauya saidai ba sosai ba,hakan shi ya tabbatar mata bai gama cimma manufarsa ba,don haka data shiga din ma ruwan dumi kadan tayi amfani dashi tajita normal,sai tayi wanka bata jima ba ta maida kayan jikinta ta dawo cikin dakin.


Idanu ta dinga rabawa tana cike da fargabar fita,don batasan ta inda zasu hadu ba idan ta fitan,gaba daya ita wani irin tsoronsa takeji,sanda taji an turo qofar dakin sai taji kamar ta zura da gudu,sai kawai ta sulale ta durqushe a wajen.


_____________________________

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:48 - 👍🏻👍🏻: 35


Cikin wata nutsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan da yayi yake takowa zuwa cikin dakin,hannunsa dauke da babban mayafinta da kuma abun sallah,sai daya fara shimfida abun sallar sannan ya qarasa gareta
"Kinyi alwala?" Ya tambayeta,tana daga duqen tana hawaye ta gyada masa kai
"Ohk....getup,tashi muyi sallah" ya fada yana miqa mata hannusa,a hankali ta daga kai,maimakon ta bashi hannun yadda ya buqata saita fuske masa,ta miqe tsaye a hankali tana jin yadda cinyoyinta suke so su fara tsami,riqe dantsen hannunta yayi,ya tsaidata sosai,sannan ya ware hijabin hannunsa ya sanya mata,saita isa da kanta saman abun sallar ta tsaya,don ta fuskanci jam'i yakeso suyi,saboda guda biyu ya shimfida.


Jallabiya ya ciro ya sanya,sai qaramar hula wadda ke tsayawa iya kewayen tsakiyar ka,ya feshe jikinsa da turarensa na da'iman,sannan ya shiga gaba ya tayar musu da sallar.


Koda suka idar saita miqe da niyyar tafiya dakinta,cikin sassauqar murya ya bata umarnin ta hau gado ta kwanta ta huta,sai tayi kamar bata jishi ba,miqewa yayi yana tattare abun sallarshi,sannan ya cimmata tana dab da fita a dakin.


Cak ya dagata ya rabata da qasa,ya isa da ita saman gadon ya kwantar da ita yana dan nishi
"Ashe dan banzan nauyi ne dake?,ke kika jawo na kusa miki aika aika,sannan zaki fice ki qunshe kanki a daki,salon ciwo ya rufeki ki ja mani magana wajen waccar tsohuwar,tace naci amanarta ban kula da ita ba" rau rau idanunta sukayi suna tara qwalla,lallai ma ya haidar din nan,ya cita wasa da yawa,amma babu komai,saita rama,saiya saka dan yatsantsa saman labbansa yana duban qwayar idanun nata yace
"Shshshsh....keep silence please"lumshe idanunta kawai ta dinga yi a hankali har ta rufesu,don tasan bata da wani sauran abun fada,tana gama rufe idanun nata yaja mata bargo ya lullubeta,sannan ya miqe a hankali ya fice daga dakin.


Da kansa ya dauki mota ya fita nema musu abinci,haka ya dinga tuqi a titin a kasalance,ya sauke dukka glass din side dinsa iskar waje tana shigo masa,wadda ke cakude da sanyin tasowar hadari,don ko rana babu a garin sosai,sai daya gama shawaginsa sannan ya zaba wani gidan abinci ya musu takeaway,ya kuma biya na dare da zasu kawo mishi har gida,don bai saka ran zata iya girki ba,daga dan tabata kadan duk ta wani langabe,saiya saki murmushi shi kadai yana shafa sumarsa zuwa habarsa sanda abinda ya faru ya dawo masa,idanun hajja kawai yake hangowa a lokacin ace taga abinda yaso aikatawar,tabbas da kashinsa ya bushe,tijara kuwa yasan sai wadda bata tuna ba.


Sanda ya koma ma bata tashi ba,saiya zauna yaci nasa abincin shi kadai,ya zauna yana duba labarai daga ingantattun jaridun dake kawo labarai online,saboda ya sake samun information da haske kan aikin dake gabansu.


Ranar gaba daya wasan buya dashi takeyi,gudunsa take hakanan wani tsoronsa take ji,tunda ta samu ta fice daga dakin nashi bata sake bari sun hadu ba,iyaka idan yayi knocking xai gaya mata ga abinci nan ta fito taci,sai ta dai daici ya gama ci sannan zata fito ta diba ta koma daki.


Ta gefe guda gaba daya hankalinta ya karkata zuwa gida,saidai bata ga alamu ba,bata kuma sake jin ya tada maganar ba,gashi a yanzun bata jin zata iya tunkararsa bare tayi masa zancan.


Kwana na uku da faruwan abun,da wani yammaci yana zaune a falo shi kadai,yana dai xaune ne kawai,amma sam bayajin dadin zaman,wanda shi kansa bazaice ga dalili ba,lokaci lokaci yakan dubi sashen qofar dakinta,tun ranar gaba daya hankalinsa da tunaninsa yayi kanta,baisan me yasa ba,amma baya yin wani qwaqwqwaran awanni bai tunata ba,duk data yanke daga hulda dashi,shi kuma bai tsawwala ba,saboda baison ya fiya shiga rayuwarta da yawa ya zamana akwai takura.


Wayarsa ce ta dauki tsuwwa,saiya miqe ya cirota daga chargy yana dubawa,hajja ce dai,murmushi ya saka,yasan darun nata ta kira tayi masa,don haka tun kafin yakai wajen zamanshi ya daga wayar,ya soma gaidata ta dakatar dashi
"Ba gaisawa na kiraka muyi ba,nace maka ka dawomin da yarinya amma kayi kunnen uwar shegu dani ko?,wai shinma ni din sa'arka ce koko yaya aka soma?"murmushi yayi wanda ya tabbatar ta jiyoshi
"Haba tsohuwa....na gaya miki fa matata ce....ya za'ayi ace ni za'a baiwa aro,ai saidai ni na baku....idanma naga dama kenan"
"Qaniyarka,nace qaniyarka.....auren bani na hadashi ba kuna tsalle tsallen banza?...." Saiya datsi numfashinta
"To kuma yanzu tsalle tsallen qauna muke.....basai a barmu ba muyi rawar gaban hantsi ba,koda mun dawo ma dan wankan da nake samu tana min Allah idanu xaki saka mana ki hana ruwa gudu...." Dogon salatin data dauko shiya tsaida zancan da yake,dariya irin wadda ya jima baiyi ba ta taso masa,ya danneta sosai
"Hajja....dama kinyi shuru,kin kuma qyaleni,don kin ganta a kusa dani abinci ma zata bani....ki gaya mata ta rage bani abinci da yawa kada mu dawo ki kasa ganeni"
"Ke zahra'u....kinci qaniyarki....qaniyarki nace" katse wayar yayi yayi dariyarsa son ransa,sai yaji ransa fes,ya samu waje ya zauna yana murmushin tsiyar da ya yiwa hajja,ya tabbatar bashi yaci,ya kuma janyowa zahra jagwal.


Kamar ance ya daga kanshi saiya hangeta bakin qofar dakinta,da alama taji duk yadda sukayi da hajja,kanta ta dauke yayin dashi kuma ya sassauta murmushin fuskarsa,tun daxu take dakon jin fitarsa ta fito taci abincin rana daya ce mata taci amma taji shuru,ganin babu alamun zai tashi,ga yunwa zata hallakata shine kawai tayi shahada ta fito.


Baice mata uffan ba harta diba abincin zata wuce yace
"Zo nan" dan hade rai tayi kafin ta juyo ta maida fuskarta dai dai,saita qaraso,ya dubeta
"Zauna nan kici....daga yau duk sanda kika sake rufe kanki a daki....zan balle qofar na shiga,kuma abinda xai biyo baya bazai miki dadi ba,don banga abinda xaisa ki ringa kulle kanki ba anan" narke fuska tayi,yunwa takeji sosai,kuma bata jin xata iya cin abinci a gabansa,kamar ya karanceta sama taka taji yace
"Eheeennn....idan xaki ci abinci kici,kaman bake muke bawa abincin ba a baki muna share miki majina a hanci" da sauri ta daga kai ta dubeshi,sai suka hada idanu,ta sake kautarwa da sauri saboda yadda ta kafeta da idanunsa dake mata kaifi da yawa,kai ya gyada mata alamun tabbatarwa
"Yesss.....ba zaki iya tunawa ba,saboda a sannan kinyi qanqanta da yawa.....kukan kitso...kukan wanka duk kin iya,da kika girma kuma sai kika zama mai tsiwa da taurin kai....right?" Ya qarashe da tambayarta,sosai maganar ta mata nauyi ta kuma bata kunya,zata iya tuna wani abun,amma wani abun ba zata iya tunawa ba,hakanan taji tana son sake jin wani abu daga bakinsa,mutum ce dakeson labarin quruciyarta,tana son a dinga gaya mata abubuwan da tayi zamanin quruciya wanda ita batasan ta yisu ba,ya karanci hakan akan fuskarta,amma bai sake cewa komai ba,saidai ta sanya cokali ta soma diban abincin a hankali tana taunawa,yayin daya lafe jikin kujera kamar mai kallo a tv,saidai ita yake satar kallo time to time.


Da magariba yayi waya aka sama masa ticket na jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano qarfe biyu na rana,bai shaidawa zahran ba ita kanta sai washegari daya dawo daga sallar asuba,haka nan wannan karon sai taji bata wani daukin tafiyar sosai,haka ta sake abinda yake da buqatar a shirya din,zuwa sanda ya gaya mata xasu fita ta kammala komai,ta yafa mayafinta,ta janyo akwatinta tayo falon.


A tsaye ta sameshi tsakiyar falon yana amsa waya,ya baiwa qofar da zata fito din baya,tun kafin ta qaraso ta gama qare masa kallo,sanye yake da wani trouser da shirt,sai high top takalminsa daya dace da kayan jikinsa,tun bata ga fuskarsa ba amma ta tabbatar da cewa shigar ta amsheshi,ta qara masa kwarjini.


Ta gefansa ta raba zata wuceshi,sai taji an kama hannunta dake riqe da majanyin akwatin matafiyar da take ja,waiwayowa tayi sai suka hada idanu,ya mata alama data saki,don haka ta zame hannunta daga cikin nashi a hankali,ya taka ya biyo bayanta yana ci gaba da yin wayarsa.


Dukkansu a baya suka xauna,driver ne ya jasu,wanda idan ya kaisu airport zai dawo da motar ne gida.


Ko a cikin jirgi ma babu magana tsakaninsu,saidai lokaci zuwa lokaci kowa ya kama dan uwanshi yana satar kallonsa,daga bisani ne haidar ya tanka
"Idan na sake kamaki kina satar kallona saina tsole idanun nan naki" gefe tayi da kanta,ciki ciki tace
"Da wanne idon mutum yasan ina kallonshi" baice komai ba amma taji kamar sautin fitar murmushinsa.


Suna sauka a aminu kano airport driver ya daukesu sai gida,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,tafiyar kusan minti arba'in ita ta kawosu gida,wanda tun daga harabar gidan tasan tabbas taro ake,saboda jama'a da kuma rumfunan da aka kafa,indai lissafinta yayi dai dai yaune sunan yasira kenan,harga Alla ta fidda rai data ji bai sake tada zancan ba,shi yasa ta daina lissafin ma.


Zumudi fal ranta ta saka hannu xata bude murfin motar,sai taji an dafe hannun nata,ta waiwayo da sauri idanunshi na akanta,hakanan tana iya jiyo hucin numfashinsa sosai saman fuskarta saboda yadda yake dab da ita,da wata irin kwantacciyar murya taji yace
"Ki nutsu da kyau,kada ki manta ke din wacece,banason yawo jiki a bude da sunan kina cikin gida....ki kiyayemin mutuncin igiyata" gaba daya ita zancan nauyi ma yayi mata,saita maida kanta daya side din,daga nesa tana hango su salma suna kai kawo,da alama hidima ta dauki zafi
"Soja baya son kawo qorafi ko kawo uzuri,just be obedient to my commands" cikin ranta take mitar ance masa a bariki ake dazai soma lissafa mata wasu qa'idoji,bata gama wannan ba taji ya zame wayarta daga hannunta,yayi wasu danne danne ciki sannan ya miqa mata
"This is my number,just call me idan kina da wata matsala ko buqata,bance ki tambaya kowa komai ba,ummi ko hajja,nayi cancel duka,zaki iya tafiya" da sauri ta buda murfin motar ta fito,wanda fitowar tata yaja idanun mutane da yawa,donma aliyyun zamanshi yayi cikin mota,ya kuma nada umarnin a sake fita dashi daga gidan,batasan inda xaije badai,tadai san koda can baison hayaniya kwata kwata,indai ana wani taro a gidan bai zama,sanda bai kuma wani zama saurayi ba wuni yake cikin dakinsu ya kebe kanshi shi kadai,mama tayita faman fadan me yasa baya son shiga dangi ko ya fito su gaisa,tun tana mita da qorafi harta gaji ta qyale,tunda ta fuskanci halinsa ne hakan,


Nan da nan labarin dawowar tata ya zagaye gidan,aka fara cecekuce da zancan dawowarta,ta fara gaisawa da 'yan uwa data samu harabar gidan,suna amsawa gami da tayata murnar qarin girman da aliyyun ya samu,ta sake fuska sosai tana amsa musu cikin walwala da nuna jin dadi,da yawa suka dinga binta da kallo wanda batasan na meye ba,da haka harta isa sassan abba babba,inda canne yafi cikowar yan suna da yawa,tunda anan mahaifiyar yasiran take wato mommy.


Ihun murna 'yan uwan nata suka saka sanda sukayi arba,kowa yayo kanta,suka cika kunnuwanta da magana,kowa da abinda zaice,salma ce daga can tace
"Allah matar ya haidar ba haka muka taho muka barki ba,anya ya haidar bai cika aiki ba kuwa?" Ta qarashe fada qasa qasa,wani wawan dundu zahra takai mata,akayi sa'a kuwa ta sameta,fa gantsare saboda zafi,sauran suka sheqe da dariya,dai dai sanda mommy ta shigo
"Waiku kam bakusan kun girma ba don Allah,yanzu kalli yadda sahal yake kallonku,kin dirke masa uwa.....daga dawowarki kin biye musu,tashi ki qarasa gaisawa da jama'a ki qyale wadan nan shirmammun,kuna nan a waje ana nemanku kunata baqi"tana kaiwa nan ta fice ta barsu.


Tare suka fito da ita,ta soma lalubar mama don su gaisa,a kitchen na tsintota sunata rabon abinci da taimakon masu aikin gidan,wai yau sai ta tsinci kanta tana kunyar maman,tana kunyar hada idanu da ita,tana shirin tsugunnawa har qasa ta gaidata tace
"A'ah,tashi inna wuro kada ki bata kayanki,bakiga yadda kitchen din yake a kacame ba" saita lalubi kujera ta zauna akai saboda ji take kamar zata fadi ta gaida maman tayi mata barka
"Ki shiga wajen hajja,can ne naga da sauqin mutane" da to ta amsa mata,suka fito tare da hafsa.


Hafsan ce ta dubeta sanda suka fito ta qyalqyale da dariya
"Anya zahraty wannan kunyar nidai ban taba gani kina yiwa mama irinta ba kamar yanzu,lallai yayana ya cika aiki....to ku shirya wallahi kuda hajja,tana nan satin nan gaba daya kullum saita muku dan biki" harara ta watsawa hafsan,bata iya bata amsa ba suka qarasa sassan umminta.


Kusan a tsaitsaye suka gaisa saboda jama'a itama dake cike a sassan nata,sai kawai ta wuce sashen mutuniyar tata hajja.


A dakinta ta sameta ita kadai tana tsaye inna gaje na wanke mata bandaki,da alama wani ya shigar mata ne,haka take,duk sanda wani ya shigar mata bandaki indai baqo ne to sai an wanke mata,har mamakin tsafta irin na tsohuwar zahra keyi,wani lokaci kuma ta tsokaneta
"Waike da kika kusa gangarawa tsaftar nan duk ta meye?" Wanda idan wani ne ya gayawa hajjan haka sai inda qarfin zahran yake,takance
"Kaga tafiya lahira a kanka,hajjanmu ba yanzu ba".


Wani kallo hajjan tabi zahran dashi kafin ta yamutsa fuska sanda take gaidata
"Munafukai....sai yau kuka ga damar tahowa?,aida kun sani kun dawwama a can" ta fada da biyu,sabida ta bigi cikin zahran taji me zata ce,hade rai zahra tayi tadan ja baya
"Zaki fara daga dawowata,ni inacan kamar nayi me saboda kewarki,amma irin marabar da zakimin kenan?"
"Na miki da arziqi ma 'yar nan,ina daya ja'irin?" Baki ta turo ta haye gadon hajjan,wanda tayi kewarsa sosai
"Ki kirashi ki tambayeshi mana" ta fada tana kwanciyarta
"Toooo...da saura kenan" hajjan ta fada a ranta,don tayi tsammanin zata kareshi ne
"Muje zuwa mahaukaci yahau kura" ta kuma fada a ranta
"Duk na isheku riga da wando" ta fada tana shigewa bandaki.


Wunin ranar cikin walwala tayi abinta gaba daya cikin dangi,har zuwa dare sanda aka qare sunan,baqi suka tattafi saura 'yan gidan da yaran gidan aurarru wadanda sukayi aure,suma a cikinsu wasu sun tafi,tawagar su zahra kuwa suna tattare a sassan hajjan sunata kwasar hira,kamar ba za'a rabu ba,don yasiran a nan sassan hajjan take zaune tunda tazo haihuwa.


Tana idar da sallar isha'i zahran ta koma wajen ummin nata,suka sake gaisawa sosai sannan suka taba hira,wanda ta lura kusan fiye da rabin hirar tata kan aurenta da aliyyu ne a fakaice,tana mata jirwaye mai kamar wanka a kansa,ta rasa wanne irin qauna ce a tsakaninsu
"Nasan zakiyi mamaki me yasa na damu da zancan aliyyu a kanki ko inna wuro?....nafi kowa sanin aliyyu mijine na kerewa sa'a,irin mijin da ake cewa mijin marainiya,mijin dana jima ina miki addu'ar samu,kici gaba da gyara mu'amalarku inna wuro,zaki fuskanci abinda nake gaya miki,mazan aure irin haidar a wannan zamanin wahala sukeyi,cikin dari guda daya ne tak,Allah ne ya amshi addu'ar dana jima ina muku ya kawo sanadi da kika zama matarsa" wannan shine magana kusan ta qarshe da sukayi da maman nata,wanda da ita ta dawo zuwa sassan hajja,wanda zuwa yanzu an sake yoyewa,inna gaje ta gyara falon fes,sai fidda qamshi yakeyi.


Dakinta ta shige,saita tadda yasira ta baje abinta ita da jaririnta,sai suwaiba da itama zata kwana,sai wata 'yar uwarsu badi'a,itama ba aure ne da ita ba.


Tunda can dama ba wani shiri suke

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment