Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kallo
"Kuma ga amanar matata nan....quda idan ya tabata saina ciki tara"
"Haidar....aliyyu,dani kake maganar" ta fada cikin daga murya sanda yake ficewa daga falon,cikin ransa tana qyaqyacewa da dariyar abinda ya yiwa hajja.


Guri ta samu tana zama tana hade ranta tsaf,duk da cewa zallar farinciki ne qasan ranta me tarin yawa,already sun riga sun gama magana dasu abba babba kan abarsu tunda har sun hada kansu sunma wuce gidansu,shi dama taron biki al'adace kawai,tunda an qulla auren yadda musulunci yace,kuma jama'a sun shaida shikenan
"Gafara kika tsareni da ido mara kunya....ja'ira kamar ba kece nan kamar zaki mutu ba saboda mun aura miki shi,ashe lambu lambu kikayi,qiris kike jira" wannan karon dariyarta kubcewa tayi,sai kuma tayi saurin mazewa
"To tunda nafi qarfina aina haqura na zauna ko?,badai za'a ce banyi biyayya ba" murmushi ne ya qwacewa hajjan itama,tasa hannu tana daga kayan,don ita duk yadda ake kallon lefan bata samu gani ba saboda gajiyar tafiya da take tare da ita,sai yanzu tadan samu ta warware.


Zahra dai bata sanya hannu ba har hajjan ta gama kalla tana daga gefe a zaune,har saida hajjan da kanta tace ta matso ta gani mana,saita girgiza kai alamun a'ah,hakan saiya burge hajjan,duk da cewa an riga da an zama daya,amma har yau akwai abubuwan da zahran ke kunyar yinsu,ba kamar 'yammatan yanzun ba,da wata ma randa za'a kawo lefan tana gidansu,masu kawowa ko qofar gida basa gama kaiwa take tsallen albarka ta fito aci gaba da gani da ita,tana gani tana comment,tana hanawa a tattaba mata wasu abubuwan,Allah ya kyauta.



*_BAYAN KWANAKI BIYU_*


Walima gagaruma haidar din ya shirya a sabon gidan nasu,ranar walimar aka taho mata da akwatunan lefanta,saiya zamana kamar itace a madadin yinin biki,sosai aka ci aka sha,aka gabatar da wa'azi da nasihohi ga mata kan zamantakewar auratayya,wadda ta ratsa zukatan mata da dama,dangi sosai suka halatta,gidan yayi cikar kwari,saidai anyi taro lafiya an kuma watse lafiya.


Rayuwa suka ci gaba da gudanarwa mai cike da tsantsar soyayya da qauna ta kwatance,idanu ko wanxuwar wani a waje baya hanasu nunawa junansu zallar son da sukewa juna,mutane da dama na mamakin haidar din,saboda kowa ya sanshi da miskilancinsa ya sanshi,sai gashi lokaci daya zahra ta sukurkutashi.


Tako wanne fanni yana jin zahran ta cancanci ayi mata kowanne iri so,don dan xamansu da 'yan satittika yasa ya gama fahimtar wacce irin macace ita,ta dauki dukka halayen umminta wajen biyayya wa miji da iya kula dashi,wani irin salo da yake da tabbacin wasunsu ta samosu ne daga wajen hajja,wanda sau tari akwai lokuttan da zai samesu suna hira da ita,tana bata labarin yadda mata ada ke biyayyawa miji ba irin matan yanzu ba.


8:30 pm


A nutse take kai kawo tsakanin kitchen da parlour tana shirya masa abinci,duk inda ta gifta idanunshi yana kanta,shigar da tayin ta dauki hankalinsa matuqa da gaske,duk sanda xata gifta saita bar masa qamshinta,bai taba zaton mata nada son turare haka ba sai da zahran ta kasance matarsa.


Plates ne na qarshe data ajjiye,sai itama ta samu waje tana niyyar xama,hannunsa ya miqa mata yana lumshe ido,ba bata lokaci ta saka hannu nata cikin nasa,hakan ya bashi damar jawota jikinsa,yayi mata mazauni saman cinyarsa,hannayensa ya sanya dukka yana yawo dasu saman jikinta,bata hanashi ba,saboda tasan abinda yafiso kenan,saima ta kwantar da kan nata saman kafadarshi,lungu da saqo na jikinta yake bi yana sansana,tsahon wani lokaci sannan ta kira sunanshe cikin wata lallausar murya
"Hubby na...."
"Makaranta fa....exam ta kusa" shuru ne ya biyo baya,har sai daya kammala abinda ya soma din,saiya dubeta da lumsassun idanunsa da suka jirkice suka qara qanqancewa
"Bana jin xan qyaleki ke kadai xahraty.....zamu tsara komai mu fuskanci komai tare,zamuyi karatun jarrabawa tare,zan kaiki ki dinga zanawa muna dawowa gida tare....nasararki nasara tace,amma da zarar kin kammala,zamu koma abuja,zan koma bakin aikina,yanzun hutun aikin da mukajeyi nake mora,sai kuma yazomin a daidai,Allah ya sanyawa hutun albarka....na mallaki xahrata a cikin sa,ta xama haidar....haidar ya zama zahransa" murmushi tayi,ta juyo gareshi,ta saka hannayenta duka biyun ta saqalo wuyansa,fuskarta dab da tashi
"Na gode sosai da wannan sadaukarwa daka yimin....ina fata ni da kai zamu dawwama a haka,na gode sosai" ta qarasa fada tana hade fuskarsu waje daya,sai kuwa ya sake kai mata cafka,cikin sauri ta zame tana cewa
"Abinci yallabai.....ayimin afuwa a fara cin abinci" ta fada tana saluting nashi kamar yadda sukewa manyansu,idanunsa ya lumshe a kanta sannan ya budesu yana fidda murmushi,yana so tana kuma burgeshi duk sanda ta tsaya gabanshi haka ta qame tayi saluting nashi,bai taba ganin kyau ko burgewa a irin wannan gaisuwar ba sai da zahranshi ta fara yi masa irinta,shima maida mata yayi yana murmushi,har ta zauna bai dauke idanunsa daga kanta ba.


Kamar yadda ya fada din kuwa tare suka tsara komai,kamar yadda yake kama mata aikin gida haka yake tayata karatun jarrabawar,bata taba tunanin haidar din gifted bane,mai matuqar ganewa tarin basira da kuma dabarun koyar da karatu,bata taba marmarin karatu ba,bata taba jin karatun jarrabawa me dadi ba,wanda babu ginsa ko qasawa a ciki ba sai wannan karon,yasan tarin abubuwa game da abinda ta karanta din,idan tace ta gaji yasan yadda zai mata ta samu relief su dora daga inda suka tsaya,su huta suyi bacci su tashi suci gaba,yace so yake ta fita da sakamako mai kyau wanda zata bar tarihin cikin makarantar,kamar yadda shima yabar tarihi cikin tashi makarantar daya gama.


*_BAYAN WASU KWANAKI_*


Yana tsaye daga saman dining yana hada musu tea shi da ita a cup biyu,yanayi yana duba agogo,a shirye yake tsaf cikin wata dakakkiyar shadda sabuwa fil ruwan zuma,wanda saida aka sha daru shida zahran tashi kafin ya yarda ya sanyata,shiri ne na tafiyarsu jarabawa a rana ta farko,ya sake daga kansa yana duban hanya,sai gata ta fito dauke da plate a hannunta,sanye take da wani lafiyayyen lace itama ruwan zuma,dinkin riga da plain zani,sabida yace bai yarda ta saka skert ba.


Duban fuskarta yake sosai,tana tahowa inda yake din tana yatsina fuska
"Yau wani laziness kikeji hubby,kodai exam dince tun kafin a fara take bugunki?,karki fa damu,ina da zato mai qarfi a kanki,kisa a ranki an gamata kawai" ajjiye plate din tayi a gabansa,ta hade hannayenta waje guda 🙏🏽
"Bani da haufi tsoro ko shakka indai sojana yana kusa....mutumin dake iya kula da qasarsa ma bare ni mutum daya?,....na yadda da kaifin basirarsa,hakanan inda malami ne shi xaiyi wuya a sami malami kamarsa kaf qarninsa kuwa,koda bayan mutuwarsa ne da shekara dari" wani kallo ya kafeta dashi,yana jin kamar ya hadiyeta,gwana ce wajen iya tsara kalaman da zasu tafi da hankalin dukkan mai hankali,ya rasa amsar da zai bata illa tukuicin lallausan murmushinsa,wanda ya jima yana shaida mata ya tanadeshi ne kawai saboda ita,ta kuma yarda da hakan dari bisa dari,don takanyi mamakin yadda yake komawa zakin gaske a gaban duk wata mace koma bayanta,hatta da qannensa shakkar nan tasa tana cikin zukatansu
"Kawai dai qwan nan ne,tunda na fara soyashi zuciyata ke tashi...." Ta amsa mishi tambayarsa ta farko sanda take daukar cup din tea din daya miqa mata,idanu ya kuma zura mata yana karantarta sanda take kurbar tea din,har sai data lura,saita dage masa girarta dukka biyun,alamun tambayar lafiya?
"Anya ko hubby....anya ban jefa qwallona a raga ba?" Ido ta fiddo tana aje cup din
"Bana tunanin haka.....haba watanmu nawa sojana....kawai ko a gida banson qarnin qwai,kuma ko xanci ma saina yanka wadatacciyar albasa akai nake ci" kafadunsa ya dage yana bude plate din chips da qwan data aje masa
"Ohkey....amma ko chips din ai kyaci ko?" Fuska ta kyabe cike da shagwaba tana maqale kafada
"Nifa qamshinsu ya gama cikamin ciki.....saidai ka taimaka ka siyamin meatpie a wannan gurinnnnn" dariya taso bashi,tunda ya taba siya mata meatpie din ta maqale masa,saiya maqale kafada shima
"Naqi wayon,saidai idan kin yarda nima....." Qarshen zancan ya furta mata qasa qasa,sarai ta gane abinda yake fada,saita sakar masa kukan shagwaba,ta dauke hand bag dinta dake gabansa ta sauko daga dining din tana diddira qafa,dariya sosai yakeyi shima,ya aje abincin ya biyo bayanta.


Har suka je suka dawo yana tattalinta,suna gama exam din ta zagaya inda ya zauna zaman jiranta ta sameshi,bata yarda kowa ya biyota ba,ya gama ganeta amma tana togewa,kishinsa take hakan ya sanya bata hada kowa dashi.


Da taimakon Allah da kuma agazawar haidar din ta kammala jarrabawar cikin babbar nasara,babu qunci ko takura ko wahala mai yawa,wanda dalibi ke tsintar kansa a duk yayin jarrabawa,wanda tasan cewa sirrin hakan na tattare ne da dafawar haidar din.


Ta yadda da cewa samun masoyin gaskiya babban dace ne a rayuwa,hakanan rashin sa'a a soyayya kada ya sanya mace ta yanke tsammani da samun haske kuma mabudin yayewar dukkan matsalarta,abu daya ake buqata shine,ki sake hankalta a yayin da duk wata qaddara ta sameki ko kika aikata kuskure,kiyi qoqarin zama me kamewa,ki ninki zurfin dora abubuwanki saman sikeli da mizani fiye da ko yaushe,sannan ki zafafa da addu'a,babu ji babu gani,babu daga qafa babu hutu.


Imani da qaddararta da tayi,ta karbeta hannu bibbiyu,ta kuma tsarkake zuciyarta,ta riqe mutuncinta da mutuncin gidansu,ta kuma yi biyayya ga magabatanta shi yasa Allah ya dubeta yayi mata musaya mafi alkhairi,ba shakka yaudara nada zafi da ciwo,tana da qarfin da zatayi barazana ga rayuwar wanda aka yiwa ita,saidai kuma girman ubangiji ya shafe komai,qudirarsa da alkhairinsa kan bayinsa yawa ne dashi,koda yaushe ko godewa ubangiji bisa kowacce irin nau'in qaddarar daya tsagawa rayuwarka,tayi maka dadi ko bata yi maka ba,wannan shike nuni da cikar imanin bawa.


Randa sukayi paper din qarshe ta dinga jin jikinta sama sama,haka dai ta daure akayi sallama da qawaye da abokan karatu,ko cikin mota ma cikin seat ta lafewa haidar din,daya tambaya tace babu komai gajiya ce,bai gasgatata ba amma ya qyaleta,saboda ya lura kaman batason magana ne,zatonsa bai tabbata ba sai da suka bude falo zasu shiga,saita tafi luu zata fadi ya tarota,ya qarasar da ita saman kujera yana mata sannu,gaba daya ya rude cikin qanqanin lokaci,ruwa ya bata mai sanyi tasha,sai numfashinta ya koma normal
"Sannu"
"Lafiyata qalau" tayi qarfin halin fada,saboda zallar damuwar data hanga tattare dashi
"No hubby....baki da lafiya" don kada tayi masa musu kota bata masa lokacima yasa bai tsaya sauraren kalaman bakinta ba ya dauketa cak sai bandaki,ya ajjiyeta sannan ya tara mata ruwan wanka
"Ki wanka na baki minti goma,zan shirya na kaiki kiga likita" saiya fiddo mata towel soson wanka da sabulun wankan ya aje mata,sannan yaja mata qofar ya rufe,saiya wuce daya bandakin shima.


Idanu ya zuba mata sanda ta gama shirin ta fito,saiya riqe hannunta sosai
"Duk yadda kika kai ga boyemin baki da lafiya hubby bazai boyu ba,kin manta ne,ni dake ruhi daya ne yake rayuwa a gangar jiki guda biyu?" Murmushi ta sakar masa,saiya karata da jikinsa suna takawa a hankali yana sake gaya mata wasu kalaman da suka sanyata sakin ajiyar zuciya a jejjere.


A qalla ya kusa minti talatin zaune shida ita cikin motar riqe da hannayenta yana jero mata kalaman nuna zallar qauna da godiya a gareta,tun lokacin da likitan ya shaida masa tana dauke da juna biyu gaba daya yayi wani irin rudewa,ko a yanzun ma hawaye zahran ke futarwa,saboda kalaman da yake amfani dasu a kanta sun girmi kanta,kalamaine da take da cikakken yaqinin ba kowacce mace bace Allah yake mata baiwa da samun mijin da zai furta mata su ba
"Gobe as early as possible zamu wuce abuja...thank god kin gama abinda ya zaunar damu,kinji kuma yace kin da buqatar cikakken hutu,so zan buqaci hajja kawai ta bamu baba gaje mu wuce da ita....but...banda fadar dalili,don i sure tsaf hajja zata hanani tafiya dake" dariya sosai ya bata data tuna da hajjansu,hajiya hajja,ayi tsiya ayi dadi,tana sonsu tana tattalinsu,amma idan tsiyarta ta tashi har su saita dandana musu.


Kamar yadda ya tsara kuwa tun a daren ya gama hada musu abinda yasan suna da buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,tunda komai a kwai a can,ya kira hajja yace baba gaje ta shirya gobe zata rakasu abuja,ta fara masa tambayoyi yace ta bari idan yazo gobe zasuyi magana,ranar kusan kwanan zaune yayi,rabi bacci rabi idanunsa biyu,duk sadda ya farka saiya tuna cewa wai shima ya kusa zama uba?.


Qarfe bakwai a gidan tayi musu
"Wai tafiya abujan na meye haka saikun daukemin gaje kuma?" Zahra ce ta marairaice fuska
"Haba hajja,can dinfa babu dadi wallahi xaman shuru" waiwayawa tayi ta dubeta
"To ba sai ya barki nan ba,ya dinga zuwa?" Baki zahra ta tura
"Habba hajja...a'ah wallahi,ni mijina zanbi"
"Na shiga uku ni fatsima.....yau naga abinda yafi xare tsayi.....innawuro ni kike gayawa haka kanki tsaye." Ilham da husna me zasuyi in banda dariya,baba gaje dake tsaye a gefe tana tayasu,shikam haidar dama bai shigo ba yana wajensu abba babba suna gaisawa,daga can ya tsaya wajen ummi don bincika me dame take da buqata,duk da bata rasa komai,amma bakan baisa ya daina hidima gareta ba,kwata kwacin yadda zaiyima gidansu.


Yana shigowa kuwa tace
"Kama hannun matarka ku ficemin,Allah ya kiyaye hanya,nikam yanzu kunfi qarfina,Allah rabamu qalau" yasan wata tsiyar aka tufka sai baice komai ba banda dariya da yake dannewa,amma ya godewa Allah da hajjan bata harbo jirginsu ba,haka suka fice bayan sunwa kowa sallama.


Shida ita a baya suka zauna,don bazai iya juriyar awanni suna waje daya amma ba ita a gefansa ba,baba gaje da driver suna gidan gaba,hakan ya baiwa zahra damar kwanciya sosai bisa jikinsa,don sam bata jin qwarin jikinta,shi kuma ya tattarota cikin jikin nasa sosai,ya gyara mata yadda zata fi jin dadin kwanciyar.


Tun basuyi nisa ba kiran hajja ya shigo wayarshi
"Anya lafiya zahra'u kuwa take?,ni sai da kuka wuce naga yanayinta baiyimin ba" cikin dakiyar nan tasa yace
"Lafiya take hajja....wani abu ya faru ne?"
"Um um....amma kawai sai nakega kamar me yaron ciki....koma meye ne ka kula da ita da kyau,sannan idan akwai wani abu da baku gane mishi ba kayi hanzarin dawomin da ita gida....kana jina?"
"In sha Allah hajja"
"Allah yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku,ya tsare dukkan abunqi"
"Amin amin,Allah ya qara girma da shekaru masu albarka" ya fada cikin jin dadi,har kullum yana ganin girma da qimar tsohuwar,saboda zallar qauna da take nuna musu shi da soulmate dinsa.


Zuwansu da baba gajen ba qaramin ma'ana yayi ba,domin itama ta hangi abinda hajjan ta hanga,duk da basu gaya mata ba,don haka bata barin zahran tayi komai,komai na gidan ta dauke shi,ita kanta zahran ba qaramin dadin zama da baba gajen takeyi ba,tana debe mata kewa,hakanan duk randa ta tashi jikin babu dadi zata gaya mata wani abu da zatayi wanda zaisa taji sauqi da qwarin jikin nata.


Ta fannin haidar kuwa ta samu dukkan wata kulawa taimako da qwarin gwiwa a matsayinta na mace mai haihuwar fari wadda batasan yadda abun yake ba,shi kansa bai barinta tayi wani abu da zai wahalar da ita,ta kowanne fanni ta zama 'yar lele ta gaske.


Hajja batasan da zaman cikin ba,sai sanda ya samu hutu na sati guda,yace su shirya suje kanon su roqi hajja tabar musu baba gaje,a lokacin cikin nata ya shiga wata na uku,kuma ga duk mutum mai saurin tsinkaye da daukar haske zai fahimci akwai ciki tare da zahran,tayi wani kyau,hakanan ta sake cika,fatarta ta qara haske,sau tari haidar kan sanyata gaba da tsokana,ya hanata sakat,bini bini yana shafa fatarta,idan tayi qorafi sai yace
"Ke dince ki qara wani kyau,fatarki kamar atafa,karfa nan gaba na soma kasa gane hanyar fita daga gida,ko naje nayi shirme gaban manya ki jawomin hukunci" saita tureshi tana tura baki,sabida ita gani take kamar tsokanarta yake,don rannan daya goyata ya zagaya da ita cewa yayi ta sauka,ta fara ninka nauyinta,sai data dinga masa kukan wasa sannan kuma ya lalace wajen lallashi da bata haquri,ire iren yanayin rayuwarsu kenan,idan ka ganshi a cikin gida saika rantse da Allah ba ALIYYU MAS'UD DABO bane,sojan nan daya kasance dodon 'yan ta'adda da marasa gaskiya dake cikin qasar nan,idan ka ganshi a waje sanye da kaki ba zaka ce zaka sameshi a haka cikin gida ba.


*_BAYAN WATA TARA_*



Tsaye suke cikin dakin hajja,taja rungume cikin jikinsa saidai ya rungumeta ne ta bayanta saboda tsinin cikinta wanda ya dora dukka hannayensa biyu akai,yana jin yadda yaron cikinta ke motsawa,kai kace zai fasa cikin ne ya fito,bai dauke hannun ba har sai daya tsagaita da motsin,suka saki ajiyar zuciya shida ita a tare,sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna.


Tausayinya yakeji fiye da kima,koda can shi mutum ne mai tsananin tausayin mace,macen ma ace mai juna biyu,yau saiga abuj cikin gidansa,a jikin mace mafi soyuwa duk duniya a wajensa baya ga iyayensa
"Banda hajja ce hubby duk duniya babu wanda ya isa ya sanyani na wani kawoki wankan gida" murmushi ta saki,ta sanya hannunta tana shafan kwantaccen gashin fuskarsa da ko yaushe yake qara masa kyau da kwarjini
"Kasan dai hajja ta fimu damuwa da kwanunanmu....sannan tun ban dade da shiga third trimester dina ba tace ka dawo dani gida,yanzu idan baka kawoni ba zataga cewa kamar bata isa damu bane,bayan ina da tabbacin cewa tayi hakanne saboda amfanin kanmu" fuskarta ya riqe tsakiyar hannunsa,ya matso da ita dab da tashi,cikin softness yace
"Hubby....inason in zama mutum na farko da zaya dauki 'yarshi" yatsanta ta dora saman lips dinsa tana cewa
"Shshshs.....point of correction.....soja nakeso na haifa,jarumi kamar kai....mai kuma kama dakai" dagowa yayi yana murmushi,ya kama hannayenta duka ya riqe cikin hannunsa
"Little zahra ni kuma nakeso.....kuma inaji a jikina itace"
"Ok....ok,ba anyi yarjejeniya ba akan a bari har sai ranan?,duk wanda yayi wining zai zaba abinda yakeso mutum ya bashi..."
"Yes hubby" ya fada yana lakace hancinta,saita jefa masa harara
"Ka takurawa hancin nan nawa" dariya sosai ya saki yana cewa
"Ya qara kyau ne,kamar na dauke kayana na tafi dashi" tasan cewa girma ya qara fiye dana da,amma ba zai taba fitowa ya gaya mata hakan ba,saidai kullum idan ya dameshi da cewa hancinta yayi qato ko yayi muni sai yace mata suyi musanye da nata,ko ta bashi kayanshi yana so shi a haka.


Rigima ta soma yi masa kan ta gane dariya yake mata saboda tayi muni,lallashin duniya taqi shuru saboda bai daina dariyar badai,har sai da hajja tazo ta tankada qeyarsa sannan aka samu salama.


Tana zama saqonsa yana shigowa wayar tata

_zan qara kwana daya ko Allah zaisa ina da rabon ganin baby na,but please kada ki sanarwa kowa_


Idanu ta zaro cike da mamakinsa,muhimmin taro suke dashi da mr president a jibi amma yace bazai tafi ba,saita koma daki ta kirashi tana son tayi convincing dinsa kan ya tafi saboda muhimmancin taron amma fur yaqi,dole ta rabu dashi,ya daddogara ta dawo falo saboda ciwon mara da baya da yaketa tsunkulinta.


A falon tayi kwanciyarta suna hira da hajja,jifa jifa tana cije lebe idan aka mintsineta,saita dinga mamaki,don bata taba ciwon mara haka mai naci ba kamar nayau,ana mintsinarta amma da tayi daya biyu uku a rana shikenan sai washegari,amma nayau din yaqi barinta batasan dalili ba.


Ciwon bayan da taji yana yawa saita koma daki da niyyar kwanciya ko zai ragu,saidai tana shiga kamar an dado ciwon ne,tayi tayi ta zauna ta kasa qafarta ta riqe gam,dole ta dinga qwalawa hajja kira,sai gata bagatatan ba shiri.


Tuni ta fahimci haihuwa ce,ta aika umaima ta kira mata mamarta matar abban tsakiya,ta sanya ilham kuma ta shiga tsohon dakin zahran ta dauko kayan da aka ware don tafiya asibiti.


Kafin ilham ta dauko kayan maman umaima ta qaraso ciwon ya ta'azzaran mata,ta kasa tafiya bare akai ga batun zuwa asibiti,don haka hajja tace adan dakata ko zai lafa mata sai a tafin,saidai ina,gaba kawai ciwon yakeyi,wanda harta kasa jure masa tana neman taimako,baba gaje da kuma hajjan su suka riqeta lokacin da suka fahimci haihuwar tazo gadan gadan,cikin ikon Allah da taimakon addu'a cikin mintunan da basu wuce uku ba kukan jariri ya karade sassan hajjan gaba daya.


Kusan tare suka saki ajiyar zuciya ita da hajjan,farinciki mara misaltuwa ya sauka a zukatansu gaba daya,hajjan ce da kanta,duk da tsufa ta dauke yaron daketa watsal watsal cikin qazantar da suka fito tare yana canyara kuka,ta kasa daurewa saidata rungumeshi cikin jikinta qwalla na gangarowa daga idanunta
"Alhamdulillah....alhamdulillah" shine kawai abinda yake fita daga bakinta,sannan ta qarasa dab da zahran ta dora mata yaron saman cikinta tana shafa sumar kanta
"Sannu takwarata,sannu da qoqari,barka da arziqi" saita lumshe idanunta cikin matuqar jin kunya,gefe guda na zuciyarta farinciki na mamayeta,idanunta kan fuskar yaron,fuskar da ko ba'a wanketa ba ta bayyana kamar ya Aliyyunta daya dauko,sak shi,kamar kaki yayi ya aje,take wata qauna irin wadda ubangiji S W T yake dasawa a zukatan bayinsa tsakanin uwa da ɗa ta fara kwaranya a zuciyarta.


Kafin kace meye wannan labarin haihuwar ya zaga gidan,tuni aka soma gyaran zahran da jaririnta,cikin qasa da awa guda tayi wankanta da ruwan dumi,an goge yaron da kyau,an gyara mata dakin hajjan yadda zai dace da yanayin jaririn,hajjan tasa an dora mata kunu bayan ta soma da bata tea mai uban kauri da bournvita saboda ruwan nono.


Sau wajen biyar yana attempting bude gidan nasa ya shiga sai yaja tsaki ya fasa,yayi imanin koda ya shiga baqiqqirin gidan zai masa,bazai ma iya zama ba,saboda babu fitilar gidan,daga qarshe kamar wanda ake umarta,yaji kawai zuciyarsa ta yanke masa ya koma gidan hajjan ya wuni da zahran,idan yaso idan dare yayi ma ya bude tsohon dakinsa na gidan yayi kwanciyarsa,duk da babu komai yanzun a dakin sai katifa,ya tabbatar sai yafi samun relief akan ya kasance tana nesa dashi.


Tunda ya doso gidan yaji gabansa yana faduwa,sanda shamsu ya bude masa qofar gidan ya ga kamar yanason magana dashi,amma bai tsaya ba sai daya isa inda suke aje motocinsu,yana kashe motar kuma yayi sassan hajjan.


Sanda ya shigo yayi dai dai da lokacin da jaririn ke kukan neman nono,baba gaje na kan zahran tana gwada mata yadda ake feeding yaro,tana ta dariyar rashin sabo irin na zahra
"Saiko kin dage,don na fuskanci me gidan nawa acici ne".


Tuntube ya kusa ci da filallukan falon hajjan saboda yadda zuciyarsa ta bashi amsar zahransa ce ta haihu yana qaryatata,banda ingarma ne kuma tsayayye da faduwa zaiyi qasa warwas,ko takan hajjan dake masa magana baibi ba yayi inda yaji kukan na fitowa wato dakin gadon hajjan.


Kyakkyawan gani kuwa idanunsa suka masa,zahransa rungume da kyakkyawan baby cikin jikinta tana shayar dashi,idanunta a runtse da alama ta jin zafin yadda yake tsotso ne,tashi guda tayi wani mugun kyau,fatarta kamar an qara mata sinadaran kyau,baisan ya isa garesu ba saida yaji muryar baba gaje dake fita tana cewa
"A barshi yasha sosai kafin a cireshi,ruwan maman sai yafi saurin zuwa,idan kin gama saiki magana zaku asibiti su sake tabbatar da lafiyarki"



Qamshinsa ne kawai ya sanar mata da zuwansa,saita

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

1 year ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment