Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko kasa na rasa su
koda jin haka sai nayi dariya nace ai kin san cewa komai
sa a ne da rabo
haka dai muka ci gaba da hira har ya rage saura tafiya
kadan mu iso gida
kwatsam muna cikin tafiya sai zalina tayi tuntube ta fadi a lokacin da zuciyarta
ta fara bugawa da karfi, cikin sauri na ajiye mashina
mai cake da barewa na tasheta zaune na dubeta
cikin kaduwa ina mai dudduba jikinta nace lafiya
kuwa menene ya sameki, zalina tayi ajiyar zuciya
ta dubeni cikin alanun firgici kawai sai naga hawaye
ya zubo mata take ta fashe da kuka tana mai cewa
naji a jikina cewa mahaifina yayi kaura, koda jin haka sai
nima hankalina ya tashi na dubeta cikin kwarin guiwa
nace ke haba ! Tashi mu karasa gida mahaifinki na
nan raye
kawai dai zuciyarki ce take raya miki hakan
nan dai na tasheta muka mike tsaye har zuwa wannan
lokacin ina dauke da wannan katon zakin a kafadata
ga kuma barewa a jikin mashina
haka dai muka
cigaba da tafiya harmuka
Iso gida
tun daga nisa muka hango Abul zalina kishingide
a jikin dutsen kogon da muke kwana ya dora
kafarsa daya akan daya yana barci, kuma ga sanda
a hannunsa in ba don dora kafarsa da yayi ba daya bisa
daya da kuma sandar da ya rike a hannunsa da dole ne
ace ya mutu
Al amarin zalina kuwa lokacin da ta hango mahaifinta
a cikin wannan hali tun daga nesa sai jikinta yayi sanyi
Al amin Ahmed Misau Nake Guyson Ko A square
zuciyarta ta karaya kawai sai ta yarda bakan dake
hannunta ta falfala da gudu izuwa gareshi tana
isa gabansa sai ta kura masa idanu koda taga
idanunsa a kafe suke ko kiftawa basa yi kuma babu
inda yake motsi daga cikin gabobin jikinsa sai ta
fada kansa ta rungumeshi tana mai tsandara uban
ihu sannan kuma ta fashe da kuka
koda ganin abin da
ya faru sai nima na rugo da gudu ina dogara sandata
ina isowa na warbar da wannan zaki na kafadata
kuma nayi jifa da sandata da mashin da barewar
ke tsire akai
kawai sai na tsugunna kasa bisa guiwoyina na fara
kuka aka rasa
wanda zai rarrashi wani tsakanina da zalin
nikaina Al amin Na tausaya musu gaskiya
da wannan gagarumin rashin mahaifin ta da sukayi
sai da muka shafe kusan sa a guda muna kuka sannan na
mike tsaye naje na kama kafadar zalina na
tasheta tsaye na shiga rarrashinat, sai da ta dawo cikin
hayyacinta sannan muka fara shirye shiryen
binne gawar mahaifin nata, tun daga wannan rana
muka bar wannan daji ba tare da fatan komawa cikinsa
ba
ko don ziyara ga kabarin mahaifin nata wanda ke cikin
wannan kogon dutse
haka dai mukaci gaba da tafiya a cikin daji mu
kwana nan mu tashi can ba tare da sanin inda muka
dosa ba muna neman inda yake da ni ima mu zauna
muci gaba da rayuwarmu, sai da muka shafe watanni
shida cur muna tafiya sannan muka iso wani daji dake
cikin nan kasarka ta Askandariyya, A nan ne muka zauna
muka ci gaba da rayuwa nida matata zalina inda
muka gina wata yar bukka a gefen wani tsauni
inda muke kwana har ma muka kafa wani garken dabbobin
gida muna kiwo bamu da wata sana a face farauta
kuma mu kan kai fatun dabbobi cikin birnika mu siyar
mu siyo abin da muke bukata da silallan da muka
sayar da fatan dabbobin dajin sannan mu dawo
dajin da muke da zama ba tare da mun taba sha awar
yin rayuwa ba a cikin gari har muka samu rabon
haihuwar Yata SIYAMA
tun siyama tana da shekara biyar a duniya na fara bata
horon yaki har ta cika shekara tara kuma duk irin horon da za a baiwa
babban mutum shi nake bata
hakika siyama tasha bakar wahala sosai a wajen
horon yaki kamar zata rasa ranta kuma sau tari sai
uwarta tayi ta
kuka idan taga tana shan wahalar taji kamar ta
hanani bata horon amma idan ta tuno da irin
kisan gillar da sarki shardas yayiwa kabilarsu da
zuri arsu da tawa sai ta hakura, haka dai siyama taci
gaba da koyon yaki har ya zamana cewa nima
ta fini jarumtaka juriya da naci, a bangaren iya farauta kuwa
ni kaina sai da na cika da mamaki bisa ganin irin
abubuwan al ajabin da take yi a daji da kuma irin
kwarewar da ta samu ta iya harbin kibiya fiye
da mahaifiyarta
bamuyi shawarar sanya siyama a cikin gasar jarumtaka
ba don komai sai saboda mu jarraba karfin
damtsenta da kuma iyakar jarumtakarta kuma
burinmu shine taci gaba da baiwa kanta horo gami da
tanadin daukar fansa akan sarki shardas, ina mai tabbatar
maka da cewa
yanzu haka ko sunan sarki shardas siyama taji
an ambata sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata
kone saboda irin kiyayyar da muka cusa mata
kuma a kullum bata da burin da yafi na mu kyaleta
ta tafi zuwa birnin shardas ita kadai ta shiga har
cikin fadarsa ta kashe shi amma na gaya mata cewa
ba zata taba samun nasara ba a kansa a yanzu face
idan ta mallaki wata Hula da ake kira HULAR LAMSARA
koda Hailur yazo nan a labarinsa sai idanun sarki
hulbasu
suka zazzari ya kamu da tsananin tsoro gami da
mamaki saboda rabonsa da yaji an ambashi sunan
wannan hula ta LAMSARA tun yana yaro karami sai kuma
yanzu da yaji a bakin hailur, tabbas ya sami labarin
hular lamsara a wajan kakansa wato wanda ya haifi ubansa amma bai kara jin
labarinta ba kawo i yanzu
sai da sarki Hulbasu ya baza fatake jarumai da
mayaka izuwa sassan duniya domin su nemo
masa wannan hula ta lamsara amma ba a samu wanda ya jiyo labarin inda
hular take bama
sarki hulbasu yayi gyaran murya sannan ya dubi
hailur a natse yace hakika jikina ya bani cewa lallai
akwai wani babban sirri a tsakanin shardila matar sarki shardas
kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya gano cewa kana nan
a raye kuma anan cikin yankin kasata tobama kai ba
ko iyalinka hatta nida kaina bz an zauna lafiya ba
don zai iya zuwa ya yakeni ya kawai da mulkina
koda jin haka sai hailur ya dubi sarki Hulbasu yace
yakai wannan sarki mai Karamci me yasa ka taimakeni
Alhalin ka san cewa yin hakan hadarine ga rayuwarka
da mulkinka
koda jin haka sai sarki hulbasu yayi gyaran murya
gami da ajiyar zuciya sannan yace A rayuwata
babu abinda na tsana sama da zalunci kuma mahaifina
kafin ya gushe ya bar mini wasiyya akan cewa
idan har ina son nayi nisan kwana akan karagar mulina to
dole ne
Na guji aikata zalunci ga talakawa na dama duk
wadanda suke karkashina ko kasa dani kuma na
kwatanta adalci a tsakaninsu gwargwadon iyawata
ina so ka sani cewa har yanzu sarki shardas bai san
komai ba dangane da wanzuwarka ko baiyanarka a cikin aksata kuma
dolene kaci gaba da boye kanka har izuwa lokacin da
zaka iya fuskantarsa, duk da cewa yanzu kaga matarka
shadila da kuma danka yarima Hulkasa
amma dole ne ka hakura da mallakarsu har sai nan
da zuwa lokacin da ya dace, idan ba haka ba kuwa zaka
rasa su ne gaba daya kuma kai kanka ma zaka rasa kanka
ba zan hanaka ka gana da shadila ba amma kada ku
kuskura ku bari wannan yaro hulkas ya san cewa
kaine mahaifinsa kuma kada ku bari ya san duk abinda
ya faru a baya
hakan ba zai haifar muku da komai ba face rugujewar dukkanin burikanmu
gaba daya da kuma salwantar rayukanmu
yayinda sarki Hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin
hailur ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe har hawaye ya zubo masa kuma
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda
fishi
ya dubi sarki hulbasu yace yanzu kana nufin kace dani
inaji ina gani zan hakura da matata wadda aka
rabani da ita a daren angwancinmu da ita na farko kuma na hakura da
dana wanda tun yana ciki bai san cewa nine ubansa ba
gashi har ya cika shekara bakwai a duniya, ka sani cewa har kwnaan gobe zuciyata bata
bayar da soyayyarta ta gaskiya ba ga kowa face shadila
ina son shadila fiye da yadda nake son kaina
Al amin ahmed Misau Nake Shin tayaya kake tunanin
zan
yarda ta sake kubuce min a karo na biyu al halin ban taba
zaton cewa zamu sake hadu wa ba a cikin wannan
duniya
koda hailur ya zo nana a zancensa sai hawaye ya zubowa
sarki Hulbasu al amarin da yai matukar girgiza
hailur kenan kuma yai matukar bashi mamaki
ya dubeshi yace yakai abokina inda dalikin zubar
wannan hawaye naka mai tsada koda jin wannan
tambaya sai sarki hulbasu yaja dogon numfashi
sannan ya sa hannu ya goge hawayansa ya dubi
hailur cikin alamun karayar zuciya yace yakai abokina
kayi mini tambayar da ta fama min tsohon ciwon dake cikin
zuciyata ne kuma shine asalinsanadin da yaja
mummunar kiyayya tsakanina da sarki shardas inaso
ka sani cewa duk irin kiyayyar dakake yiwa sarki
shardas bata kai koda rabin wacce nake yi masa ba
domin duk ladabin da nake yi masa a yanzu na
dole ne saboda yafi karfina kuma bana son abinda zai
taba kasata da jama'ata, ka sani cewa bakincikin
sarki shardas ne ya kashe mahaifina kuma sarki
shardas ne sanadin dana rasa dana na fari YARIMA
HUZEIN
Cikin alamun tsananin mamaki da kaduwa hailur ya
dubi sarki hulbasu yace tayaya mahaifinka da danka
huzein suka gushe
koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa
sarki hulbasu ya dubi hailur cikin nutsuwa yace
yakai abokina ka saurari labarin da zan baka yanzu
dukkanin amsar tambayar da kayi min yanzu tana
cikinsa......
.
JARUMA SIYAMA DA MAHAIFINTA HAILUR SUNA CIKA
BURINSU NA DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHARDAS ?.
.
MAI ZAI FARU IDAN SARKI HULBASU YA GAMA BAIWA HAILUR
LABARIN MUTUWAR DANSA DA MAHAIFINSA ?
.
A WANNE HALI SHADILA TAKE CIKI BAYAN TAYI ARBA DA TSOHON MIJINTA HAILUR ?
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAN CEWA HAILUR SHINE
MAHAIFINSA NA GASKIYA
.
Marubucin littafin Wato Abdul aziz sani M/ Gini yace
mu hadu a Littafin Tsatsuba na (6) Don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari
mai dumbin darasi fadakarwa da nishadantarwa
Mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe
Al amin Ahmed Misa
Inkiya
Guyson Ko A A Misau nake
TSATSUBA
Littafi na shida 6
Na Abdulaziz Sani M gini
HausaeBook
Made Shuraih Usman

Zaku iya dauko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin eBooks ta hanayar ziyartar shafinmu na
facebook http://shuraih.waphall.com

SATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
LOKACIN DA SARKI HULBASU YA ZO NAN A ZANCENSA SAI HAILUR YA
jinjina kai gami da yin murmushi sannan ya tattara hankalinsa gaba daya kan sarki hulbasu
yace ina saurarenku yakai abokina , koda jin wannan batu
sai shima sarki Hulbasu ya mayar masa da martanin murmushin
da yayi masa sannan ya fara bashi labarin kamar haka....
''KIMANIN SHEKARU GOMA SHA DAYA DA SUKA SHUDE, Sa adda satki shardas ke
nahiyar nan yana cinsu da yaki sai ya zama dodon maza kuma ki gudu sa gudu
domin kuwa duk kasar da ya durfafa sai ya sami nasara akanta, a wannan lokaci mahaifina ne akan
karagar mulki ni kuwa nine sarkin yakinsa, kuma nine kadai dansa a duniya kuma nima
dana guda daya ne tal a duniya wato YARIMA HUZEIN
Lokacin da labari ya riski mahaifina cewar sarki shardas yaci kasashe guda ashirin da
daya da yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi
da farko yayi shiri ya dauki matakin yin yaki da sarki shardas don har ya bami umarni na tara

gaba dayan mayakanmu mu tanadi abinci da kayan yaki da nufin mu yi riga kafi
wato muje mu tari sarki shardas da yaki tun gabanin yazo ya yakemu amma sai wani tunani ya zo
masa ya dakatar da fita
yakin yayi shiri ya tafi izuwa gidan wani mashahurin boka wanda ake kira ZAMARANU IBINI
KALBIYA,, boka zamaranu na zaune a cikin wani
daji ne dake gabam iyakar wannan birni namu kuma masana tarihi da bincike sun tabbatar
da cewar boka zamaranu yafi shekara dari zaune a ciki
wannan daji shi kadai, babu wanda yasan abinda yake yi a cikin dajin ko kuma dalilin
zamansa amma dai an tabbatar da cewar da shi da bukkar
da yake zaune a cikinta kwai rana guda aka gansu sun wanzu
ba a san mafarinsu ba,
mahaifina Ya durfafi dajin DANYUL shi kadai kai tsaye ba tare
da fargabar komai ba alhalin tsawon bayyanar boka zamaranu a dajin babu wani
mahaluki daya sake shigarsa walau MUTUM KO ALJAN ba don komai ba kuwa face sai don
mugayen bakaken aljanun dake cikinsa, AA Misau Sunana, Komai gawurtar ayari na
fatake basa iya ratsa dajin duk tsautsayin da ya sa suka shiga
kuwa shi ke nan sun bata har abada ba za a sake jin
duriyarsu na
a tsawon shekara dari da baiyanar boka zamaranu a cikin dajin
Danyul fatake ko yan fashi ba sa sake shigarsa ba, don haka
nema ake yiwa dajin lakani da BIRNIN FATALWA, AA Misau Sunana
Duk da sanin tsananin hadarin dake cikin wannan dajin
haka mahaifina ya kunna kai cikinsa, kai da ganin yanayin fuskar mahaifina a lokacin
da yake tafiya bisa dokinsa a cikin dajin ka san cewa babu
batun tsoron mutuwa a ransa, in da ma mutuwar zata zo masa to zai marhaban da ita
ai kuwa tunda ya shigo cikin dajin ya rinka yin arba da wadansu irin mugayen bakaken aljanu
masu tsananin muni da ban tsoro, duk sa adda wadannan mugayen aljanu ska tasamma mahaiina da
nufin su dasa masa
wawa sai su ga ko gezau baiyi ba alhalin duk bil adaman da
yayi arba dasu take yake zaucewa ko sumewa hm AA Misau
Sunana, haka dai Aljanin suka yi ta kokarin firgita mahaifina da
razanashi amma ko kadan yaki razana wani lokacin ma sai yayi kamar bai gansu ba ko baijisu ba,
sai da ya shafe kwana tara
yana tafiya kuma baya yarda ya yada zango a ko ina ko
barci zaiyi akan dokinsa yake yi, kuma a tsawon kwana taran
baiyi bawali ba ko bayan gida, kuma baya tsayawa da tafiya face idan dokin nasa ya gaji
ya tsaya don kansa yana hutawa, a ranar kwana na tara ne
ya iso kofar bukkar boka zamaranu wacce ke tsakiyar dokar dajin Danyul.
++ ++
ACAN BIRNIN ASKANDARIYYA KUWA, hankalina dana yan majalisar sarki ya dugunzuma
ainun, domin mun nemi sarki sama da kasa a cikin birnin nan mun rasa babu wanda ya san cewa ya
tafi izuwa dajin Danyul, Ashe cikin tsakiyar dare ya sulale ya fice daga cikin birnin ta hanyar batar
da kamanninsa
++ ++
MAHAIFINA NA isa can kofar bukkar boka zamaranu sai yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak ! Kafin ya sauko daga kan dokin nasa ne yaji an
kyalkyale da dariya kuma sai yaji sautin dariyar yana fitowa
daga kowanne bangare wato gabas da yamma, kudu da
arewa
AA misau Sunana sarki ya leka cikin wannan bukka sai yaga wayam babu kowa a ciki
kawai sai yaji an dafa kafadarsa ta baya, a firgice ya juya da
sauri yayi arba da abinda ya dafa kafadarsa boka zamaranu ne!

Boka zamaranu ya kasance dogon mutum kuma siriri mai
kwala kwalan idanuwa kunnuwansa wasu iri ne kamar ba na mutum ba domin a tsaye suke tamkar
na zomo
yana da tarin gashin girar ido mai kauri da tsawo kuma yana da dogon hanci tamkar alkalami, Gaba
daya gashin kansa gemunsa da sajensa fari ne saboda tsufa
ga masana ilimin karanta shekarun dan adam ta hanyar lura da yanayinsa za su iya bashi
shekaru dari biyu da yaya na haihuwarsa, domin gaba daya fatar jikinsa ma ta yankwane ta bushe
kai kace ma ba mutum
bane
Siffofinsa gaba daya sun juye sun zama abin tsoro koda
sarki yayi arba da boka zamaranu sai yaja da baya a tsorace
a karon farko tunda ya shigo cikin dajin Danyul,
koda ganin haka sai boka zamaranu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yace haba yakai sarki
mai birnin askandariyya
akan wani dalili
Zakaji tsorona alhalin ka wuce abubuwan tsoro sama da guda dubu a baya wadanda suka fini
firgitarwa?
Ka sani cewa kaine kadai mahalukin da ya ratso wannan daji ya iso har nan a raye
tsawon shekara dari da suka gabata kuma kaima din bawai jarumtakarka ko sihirinka bane suka
kwaceka ba face
cire tsoron da kayi a cikin ranka AA Misau Sunana
rashin tsoro a cikin zuciyar mutum shine sirrin shigowa cikin
wannan daji na Danyul har mutum ya cimma burin da yake dashi dashi acikin
dajin ba tare da ya hallaka ba, shin zaka iya gaya mini
dalilin da ya saka siyar da ranka ka shigo wannan daji alhalin
ga mutanenka can sunyi shirin yin yaki da sarki shardas ?
Lokacin da boka zamaranu yazo nan a zancensa sai sarki yayi ajiyar zuciya ya kasa cewa
komai domin a sannan ne yaji bawali ya matse shi kuma wata irin azababbiyar yunwa
da kishirwa sun kamashi, AA Misau Sunana Kenan kuma Nine
Jagoran Wannan typing din Littafin Gaba daya, saboda dama tun a kwana na takwas
da tahowarsa dajin danyul guzurinsa ya kare, da yunwa da kishirwa ya kwana
Kwatsam! Sai sarki yaji boka zamaranu ya sake bushewa da dariya sannan yayi nuni da cikin
bukkar sa yace da sarki
sauko daga kan dokinka ka shiga cikin bukkata ka kawar
da bukatarka
duk abinda kake so zaka samu a ciki koda jin wannan batu sai sarki ya sauko daga kan
dokin nasa da sauri ya ruga izuwa cikin bukkar AA Misau Sunana
Yana shiga sai kansa ya juye ya firgita ainun domin ba a dakin bukka ya tsinci kansa ba, cikin wata
makekiyar fada ya tsinci kansa wacce ta kawatu ainun fice da tasa
take kofar wani makewayi ta bayyana tare da bude kanta
ba tare da wata fargabar komai ba sarki ya ruga
izuwa ciikinta ya kawar da bukatarsa, yana fitowa daga cikin kewayen kuma saiga Abinci
da abin sha iri-iri akan wani dogon tebur na alfarma
sarki ya karasa kan wannan tebur jikinsa na tsuma zuciyarsa cike da tunani da mamaki
domin sa adda ya shigo fadar babu wannan teburi bare
abincin dake kansa
ba tare da fargabar komai ba mahaifina ya zauna yaci gaba da sha sai da yayi gyatsa mai nuni
da alamar Ya koshi
Al amin Ahmed Misau Sunana, faruwar hakan keda wuya
sai boka zamaranu ya baiyyana tsulum a gabansa
yace yauwa tun da yanzu ka sami nutsuwa saika bani amsar
tambayata ?

Mahaifina yayi gyaran murya yace yakai wannan boka mai
daraja kayi sani cewa ba komai ne ya sa na sai da raina na
shigo cikin wannan daji ba alhalin na san cewa duk wanda
ya shigeshi sai ya mutu face sai domin gudun kada nayi
garaje na zuwa yakar sarki shardas saboda masu iya magana sunce mai laya ya kiyaye
mai zamani
A iya sanina ban taba ganin sarkin da ya yaki kasashe ashirin
da daya ba a wannan nahiya tamu har ya sami nasara a kansu
face sarki shardas
duk da na san cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata kasa
mai yawan dakarun yakina, amma duk da hakan sai da
zuciyata ta buga kuma tsoro ya darsu a cikin raina bisa
al amarin sarki shardas, naji daga bakin bokaye da yawa cewa
kaine kadai zaka iya gaya mini wani abu akan sarki
shardas
bisa wannan daliline yasa nazo gareka domin ka sanar dani
shin idan nayi yaki da sarki shardas zan samu nasara a kansa? Baya ga wannan ina so nayi
maka wata tambaya guda daya ? Tambayar kuwa itace
wai shin menene ya zaunar dakai a cikin wannan daji har tsawon shekaru dari ??
Lokacin da boka zamaranu yaji wadannan tambayoyi sai yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa
kamar ba zai ce
komai ba, daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi mahaifina cikin nutuwa yace yakai
wannan sarki kayi sani cewa babu wani jarumi ko matsafi
daga jinsin MUTUM KO ALJAN wanda zai iya kashe sarki shardas a yanzu domin kuwa
yana kan sharafinsa ne kuma zamaninsa ne
wow AA Misau Ke magana Babbar Magana Kenan, ina tabbatar maka
da cewa idan har ka ce zaka yakeshi sai gaba dayan dakarunka sun kare, kuma sai
ya shigo har cikin birninka ya yi maka KISAN GILLA idan kana son ka tsira daga sharrinsa
sai dai ka shirya masa kyauta ta dukiya da bayi mai yawa
ka aika masa kuma ka tambayeshi duk abinda yake bukata daga gareka
domin kai da jama arka ku zauna lafiya, dangane da tambayar
dakayi mini kuwa ta karshe amsar tambayar ka itace
yau shekarata dubu biyu ina jiran zuwan ranar da wata
hula zata bayyana wacce ake kira da suna HULAR LAMSARA
Zamana a cikin wannan daji ba na komai bane face na
binciken gano inda hular lamsara take da kuma yadda zan
iya mallakarta amma har yanzu na kasa gano hakan
sa adda boka zamaranu yazo nan a zancensa sai mamaki ya
kara kama mahaifina yace, yakai wannan boka mai
daraja da abin al ajabi an ce shekaranka dari a cikin wannan daji kuma gashi a yanzu da bakinka ka
gaya mini cewa yanzu shekararka dubu biyu
kana jiran bayyanar hular lamsara to waishin anya kuwa
kai mutum ne ?
AA Misau Sunana koa a zamanin baya sosai na kakannin
kakanninmu mutane basa yin shekaru dubu biyu a doron kasa, sannan kuma ita wannan
hula ta lamsara yaushe ne za ta bayyana kuma me kake so
kayi da ita da har ka shafe shekaru dari a cikin wannan
daji saboda ita?
Koda jin wannan tambayoyi sai boka zamaranu ya bushe da dariya mai karfi har
Dariyar ta kama amsa kuwwa ta cika fadar gaba daya, mahaifina
yaji kamar
kunnuwansa zasu dode ba shiri ya sa hannayansa ya toshe

kunnuwan nasa har sai da ya daina dariyar sannan ya dago ya kalleshi, boka zamaranu
ya mike tsaye yayi tafiyar taku biyar sannan ya juyo ya fuskanci sarki yace ni
mutum ne kamar kai ba aljan ba amma na fito daga cikin
mutanen da suka fi kowanne kabila dadewa a duniya
domin a yanzu haka da kake ganina shekarun haihuwata sun kai dubu biyu da dari hudu da arba'in,
nine kadai mutum
da ya rage a duniya daga cikin jinsinmu kuma nine
kadai na san sirrin kayan yakin MAZAN JIYA guda hudu makaman yakin da babu kamarsu
a duk fadin wannan duniyar gaba daya, idan na mallaki
hular lamsara sai na mallaki duniyar nan gaba dayanta, kuma a sannan ne kadai zan iya
yin aure har na haifi irina wanda a gaba zaiyi shekara dubu takwas yana mulkin duniya
Jikana kuma zai karbi karagar a hannunsa ya ninka shekarunsa
haka dai zuri ata zata ci gaba da mulkin duniya har abada
ba zan taba cika wannan burin nawa ba face na mallaki
hular lamsara
yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wanda zai iya hallaka
sarki shardas face wanda ya fara mallakar wannan hular ta lamsara
A A Misau Sunana Kenan,
da wannan furuci nake yi maka bankwana kuma ina mai shawartarka daka gaggauta barin dajin nan
ka koma izuwa
ga kasarka domin idan ka kara dakika arba in anan zaka
iya rasa rayuwarka
duk amsar da baka ji ba daga tambayoyinka ba zan iya sanar dakai bane
gama fadin hakan keda wuya sai boka zamaranu ya bace
bat
tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, koda ganin haka
sai mahaifina ya mike zumbur ya fice da gudu daga
cikin fadar sai gashi ya bayyana a gaban wannan bukka
a dimauce ya karasa inda dokinsa yake ya daka tsalle ya haye kansa sannan ya
sakar masa linzami ya kama gudu ba sassauci
sai da mahaifina ya sake shafe kwana tara yana tafiya sannan ya dawo gida, yana isowa ya bayar da
umarnin a janye
batun yaki
nan take aka sallami kowa mayakan suka koma izuwa ga gidajensu tare da kwance damarar yakin
da suka daura suna cike da dumbin mamakin
dalilin da ya sa aka fasa zuwa yakin, kashe gari kuwa, da
sassafe sarki ya tashi ayari na dakaru dubu uku dauke da bayi dubu ashirin da kuma dukiya mai
dumbin yawa
ta dinare, lu'u lu'u da murjani cikin akwati dubu suka tafi
izuwa ga birnin sarki shardas da kuma wasika, lokacin
da wannan ayari suka riski sarki shardas yaga dukiyar da
mahaifina ya aiko masa kuma ya karanta wasikarsa wacce ke nuna mubaya a gami da neman
zaman lafiya sai ya bushe da dariyar mugunta sannan yace'
tabbas na cika zaki uban dawa a wannan nahiya kuma dole
ne sarakuna su durkusa a gabana su nemi tsira da jaddada muba ya arsu gareni
nan take sarki shardas ya sa aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da
ita
bayanin dake cikin wasikar shine kamar haka...........
Danjin wani bayani ne sarki shardas ya aiko sai ku tarbeni a Post na gobe ehem Dafatan wannan
labarin yana kayatar daku Idan hakane kawai ku sauke mun comments dinku
gami da likes
kafinnan Nidinne Dai

Al Amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Daga Zauran LabaraiSATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
NAN TAKE SARKI SHARDAS YA SA AKA RUBUTO AMSAR WASIKAR
MAHAIFINA AKA MAIDO MASA DA ITA, BAYANIN DAKE CIKIN WASIKAR SHINE...
Yakai mai birnin askandariyya kayi sani cewa sakonka
na bayi da dukiya ya riskemu, kuma mun gode da wannan karramawa da kayi
mana gami da mubaya'a, amma ka sani cewa ba mu karbi
mubaya'arka ba har saika zo da kanka fadata ka zube
kasa a gabana ka kwashi gaisuwa sannan zamu aminta
da mubaya'arka a garemu, sharadi na biyu kuma shine dole
ne duk shekara ka rinka kawo mini irin wannan kyauta daka
kawo mini ta bayi dubu ashirin da dukiya akwati dubu
sharadi na uku shine dolene ka baiwa wakilina matsayi
da mazauni a kasarka domin su dinga kawo mini rahoto duk abin dake gudana
a cikin birninka da kauyukan kasarka, sako daga sarki mai cikakken iko kuma
sarki dodon maza gallabar sarakuna sarki shardas
** **
Lokacin da wannan wasika ta riski mahaifina aka karanta a
tsakiyar fada sai hankalin kowa ya dugunzuma ni kuwa sai
raina ya baci jikina ya kama tsuma, cikin tsananin fishi na mike tsaye ina

Please Login or Register in order to submit comment