Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rana ta kwalle kuma taga babu
jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da
take kwance sai ta mike zaune zumbur a lokacin
da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai
ta sauko daga kan gadon da sauri ta leka bandaki
don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma
sai ta iske bandakin wayam babu kowa a cikinsa
a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan
ta kimtsa
gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata
kofa saiga wata kuyanga ta shigo, kuyangar ta zube
kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata
sarauniya ta turoni nayi miki jagora zuwa can
turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki
shadila ta dubi yadda rana ta kwalle ta cikin tagar
dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har
yanzu sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake
risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki
tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama
kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun dade da
tafiya kallon GASAR JARUMTAKA, koda jin wannan
batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi
kuma ta ji babu abinda take so sama da ta ganta a
filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da
kuyangar yi maza ki kaini wajan sarauniya
ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar
ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin shardila na
biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin
dake falonta ita kadai tana jiran sai ga kuyanga tare
da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike
tsaye da sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta
ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare
da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin
har suka kusan gama cin abincin dayansu baice kala ba
a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai
ta dubi luzaira tace yake kawata ki gafarceni na bata
miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi
kalaci ba domin barcina ne yayi nauyi, kafin shardila
ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai kallonta cikin murmushi
tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa
akan hakan domin danki ya gaya mini cewar yana
zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata
lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata matsala
dake damunki
koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu
abinda yake damuna kuma bani da wata matsala
haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da
daddare wata kila bakunta ce ta janyo hakan
koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya
ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda domin
ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace
ko dai kewar sarki shardas ce ta hanaki barci
kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin
na san cewa yanzu tuni an dade da fara wasa
babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta
tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike
tsaye saboda dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka
gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka tanadar
musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun
da zasuyi musu rakiya tun daga nesa shardila ta
hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani
bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake
gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta ba face
a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi
ta kallonta,
abinda bata sani ba shine tsananin kyawun fuskarta da kyan
surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata
nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja
aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin
GASAR JARUMTAKA.
.
NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga
Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya kaimu Gobe
zamu ci gaba
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
nake cewa Ku zama
lafiya
TSATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da
azababben yaki tsakanin sadauki darkus da jaruma
siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu
SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama juriya da
bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar
jikin daya ba
Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan
da yawa daga cikin yan kallo dai sun firgice ne da
al amarin siyama
kai harni Al amin da nake wannan typing din na
rikice da lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa
siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda
za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal
a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin
damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri
acikin lamarin
Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka
ne a nono kuma tun tana da shekaru hudu kacal a
duniya mahaifinta ya far bata horon yaki
Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin tashin
tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya
Luzuraina nan ta iso, take farinciki ya kama sarki
hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace
abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar
bakuwarmu
koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin
ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma sai ya kasa
sakamakon ganin wani irin mugun naushi da
darkus ya yiwa siyama a fuska cikin tsananin shammace,
saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga
cikin hancinta kuma ya yi feshi daga cikin bakinta
ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da
tsananin juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa
da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama
ta doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama
tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta
duro kasa
ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon
jini har shima yaji wani jiri ya kwashe shi ya tafi
luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya
tokare jikinsa da hannu guda ya taso sama kamar
sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki
kamar ma lokacinne suka fara yakin, A dai dai
wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila
suka shigo cikin filin gasar suka durfafo inda su
sarki ke zaune dakaru na take musu baya , tun daga
nesa Abul siyama ya hango shardila sai yaji
zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji
ba a rayuwarsa
koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata
rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya
kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa
domin a sannan ne ya tabbatar da abin da yake zargi duk
da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle
Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta
kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don komai
ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari
domin ta gusar da wasu wasin dake cikin zuciyarta
bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata
ga mutum mai hannu daya da nakasashshiyar
kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta tabbatar
da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take
zata shaidashi,
amma har suka iso inda su sarki hulbasu ke zaune
amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan
hankalinta bai kawo kan Abul Siyama ba shine
ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu
ya zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma
wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma fuskar
Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da
wanibabban mayafi na alfarma, luzuraina da shardila
suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga hagunsa
shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa
tun da suka zauna abul siyama bai yarda ya kalli
inda suke ba
shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma
yana kan gumurzun da ake yi a tsakiyar filin
gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko
tunanin gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan
su Luzuraina
Al amin Ahmed Misau, Guyson Ko kuma A square nake
yayin da shardila ta kyalla ido ta hango siyama a
tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki
tayi arba da fuskarta sai taji zuciyarta ta buga
da karfi
ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama
tana matukar kama da mahaifinta, nan take shardila ta
gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta
ce wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru
bakwai baya
lallai hakan ya tabbatar mata da cewar kenan Hailur
na nan a raye kuma a cikin wannan gari
koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba
da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko zataga Hailur
shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin
da take ciki sai ya noke yana mai sunkuyar da
kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya
tabbatar da cewa suna hada idanu zata shaidashi
duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani
idan kuwa ta shaidashi a gaban kowa zata fashe da kuka
ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa
zai tonu su sadauki Murzanu su shaidashi
idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan
domin sai labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar
hakan ta faru kuwa hatta sarki hulbasu ya shiga
cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki
shardas
Cewa zaiyi ya boye babban makiyinsa a birninsa
don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya
mallake kasar ma gaba daya, nan take idanun Hailur
suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye
domin shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade
da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga
ta alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki
Murzanu na take mata baya sai ya kamu da tsananin
bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai
a yanzu ta zama matar sarki shardas, aikuwa
bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima
hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila
ya rungumeta
nan take zuciyar hailur ta sake bugawa da karfin
gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin
zuciyarsa yace ' shin wannan yaro dana ne ko kuwa
dan sarki shardas ne
tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama don
haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas
shardila na dauke da cikin dana, wai shin kana zaton
cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife
danka a cikin gidan sarautarsa, kai hailur ! Idan ma
mafarki kake yi toka farka ''
wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa
nan fa yaji cewar babu abinda yake bukata sama
da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta
bashi amsar wadannan tambayoyi dake yi masa yawo
a cikin zuciya
lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga
fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun
kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku uku
ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas
siyama tana tsananin kama da tsohon mijinta hailur
babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta
shine ganin irin yanayin yadda take yin yakinta
Al amin ahmed nake Guyson, iri daya ne sak dana
tsohon mijinta Hailur
kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai
zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle kalle da
waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta
hailur amma shiru kamar maye yaci shirwa
ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da
ita duk da cewar fuskarsa a rufe take cikin rawani
kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana
tare da luzuraina abarin hagun sarkin,
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai
ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa wanda zai
iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin
damtse irin na darkus sai gashi naci da juriyar
siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen
mahaifinta yasa ta iya kwatar kanta awajensa
tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban
hannayansu har sai da suka gaji ainun makaman nasu
suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar
juna da hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa
siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa irinsa
kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar
masifar yaki sai da takai ga sun durkushe kasa a tare
kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu
a hakan
kowannansu ya kama layi kamar wanda ya sha giya
suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin
wannan hali
daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya
luuu ! Suka baje a kasa tare suna numfarfashi kamar
ransu zai fita...........
.
A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe
Marubucin Littafin yace....
.
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN
SADAUKI DARKUS DA JARUMA SIYAMA ???
.
WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR
JARUMTAKA A TSAKANINSU ?
.
MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE
MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA HAILUR DA SUKA RABU
TSAWON LOKACI ?
.
SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI
YA KAI KUNNEN BABBAN MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN
YA AURI MASOYIYARSA KUMA MATARSA?
.
MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a littafi na 5 donjin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari
Daga mai debe muku kewa a ko yaushe
Ni Al amin Ahmed Misau Wanda keda inkiyar Guyson
ko A square nake cewa Mu zama Lafiya.
Amma Ku meye kuka hango a haduwar Hailur da
shardila wata irin Dambarwa za a yi ne kam
sai naji daga gare ku...
TSATSUBA
Abdulaziz s madakin gini
Hausaebooks
Made:- by shuraih Usman
Domin samun wasu kayatattun littatafan hausa amatsayin hausa ebooks sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan wannan adireshin http://shuraih.waphall.com


TSATSUBA
Littafi Na Biyar (5)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
suka bingire kasa suna fitar da numfarfashi kamar
ransu zai fita a dai dai wannan lokaci ne aka buga
gangar tsayar da yaki sannan alkalin gasa ya
rugo izuwa cikin tsakiyar fili ya fuskanci jama a
yace yaku jama a kuyi sani cewa wannan gumurzu
tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama babu
zakara a tsakaninsu wato sunyi MUTUWAR KASKO
don haka zasu sake haduwa a zagayen karshe
na wannan wasa wanda za ayi rana i ta yau
don haka yanzu zamu kirawo jarumai na gaba
domin aci gaba da wannan gasa, gama fadin hakan
keda wuya sai aka dauke sadauki Darkus da jaruma siyama
daga cikin filin aka kaisu can gefe daya maimakon
a shigar dasu cikin wannan asibiti wanda aka tanada
domin yiwa jaruman gasar magani, dalilin da yasa
kuwa ba a shigar da su cikin wannan asibiti
ba shine babu mai wani babban rauni a cikinsu
akan hancinsu da bakunansu ne kadai jini ke diga
lokacin da jaruma siyama ta dawo cikin haiyacinta
sai ta dubi inda su sarki hulbasu ke zaune tana
mai mamakin dalilin da ya hana mahaifinta zuwa
inda take a lokacin da hankalinta ya gushe bayan an
tsayar da wasansu, bisa mamaki sai siyama taga
babu mahaifinta a inda yake zaune amma kuma
sai taga shardila ta kura mata idanu ko kiftawa
batayi duk da cewa kuwa ta rufe fuskarta da bakin kyalle idanunta kadai
ake gani
nan fa hankalin siyama ya dugunzuma ainun
in ba don ma ta hango mahaifiyarta ba ta taso daga inda take zaune
ta taho wajenta ba da mikewa zata yi ta bazama
mahaifin nata Hailur, da isowar zalima wato mahaifiyar
siyama sai ta rungumete cikin murna tana
mai yi mata jinjina bisa bajintar da ta nuna a wannan
wasa da tayi
A dai dai wannan lokaci ne wani likita yazo garesu
da nufin zai duba tafiyar siyama amma sai zalina ta tsaidashi tace babu wani
likita da zai duba lafiyar yata face ni don haka mun
gode bama bukatar taimakonka, koda gama fadin
hakan sai zalina ta bude wani kullin tsumma dake
hannunta ta dauko wani ruwan magani a cikin
wata yar doguwar kwalba ta mikawa siyama
siyama ta karba ta bude murfin kwalbar ta sa abakinta
tasha mukurwa biyu kacal sannan ta rufe kwalbar ta
mai dawa zalina
Faruwar hakan keda wuya sai jinin dake yoyo a
hannun siyama da bakinta ya tsaya cak kamar bai
taba diga ba kuma nan take taji duk gajiyar dake
jikinta ta dauke fuskarta ce kawai da idanunta a
dan kumbure sakamakon naushin da darkus ya yi mata
a can gefe daya kuma likita ne ke duba sadauki darkus
ana sa masa magani a kan hancinsa don tsaida
jinin dake yoyo koda darkus ya dawo cikin
hayyacinsa ya waiga bayansa yayi arba da jaruma siyama
sai ya daka mata harara yaji ya tsaneta fiye da
komai a rayuwarsa, nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone bisa ganin cewa yarinya karama ta
gagareshi a filin gasa, nan fa ya fara tunanin cewa ta kowanne hali sai ya kaita kas a zagaye
na biyu da zasu hadu wato
a wasan karshe da za ayi na gasar idan rana ta
zagayo kuma babu abinda zai yi ya dawo da kimarsa
da mutuncinsa a birnin face ya kashe wannan
karamar yarinya siyama ya zamana cewa ta mutu murus har lahira
a cikin filin gasa kuwa mai gabatarwa yazo
tsakiyar fili yaci gaba da jawabi sannan ya kirawo
sunayan jarumai na gaba wadanda zasuyi
fafata a wannan gasa
A dai dai wannan lokaci ne sarki hulbasu ya dubi
Hailur yace yakai abokina hakika ka baiwa yar
ka horon yaki na ban al ajabi domin ta bani mamaki
matuka
kuma akwai alamun cewa zata iya lashe wannan gasa
amma ka sani cewa lashe wannan gasa ba abune
mai sauki ba saboda babu irin abinda jaruman
gasar nan basayi don ganin sukai gaci, suna yin
tsafi tuggu da makirci iri iri don ganin sun sami
nasara ta kowacce hanya don haka dole ne kasa ido
akan yarka domin daga yanzu rayuwarta
na cikin hadari kada ka tafi izuwa gida kai tsaye
daganan ina son ku biyoni izuwa cikin gidan
sarautata domin ku dauke hankalin makiya
dolene ku sauya gidan zama kuma nima zan baku shawarwari da taimako
wai shin ma kasan kuwa irin ladan da yarka zata samu
idan ta lashe wannan gasa ta jarumtaka ? Koda
jin wannan tambaya sai hailur ya sunkui da kansa
kas saboda yaga shardila ta kalleshi don kada taga
kwayar idanunsa ta shaidashi sai yaki yarda ya dago
kansa
sa ar ma da yayi ko kadan bata jin abin da suke
tattaunawa shi da sarki kasancewar suna magana ne cikin kus kus
yadda babu mai iya jin abinda suke tattaunawa
hailur ya risina cikin girmamawa yace yakai
abokina wane irin lada za a baiwa yata idan ta lashe
wannan gasa
sarki hulbasu yayi murmushi sannan yace
da farko dai za a bata babbar gona guda daya
daga cikin manyan gonakan garin nan gami da
dinare dubu dari bakwai sannan kuma zan bata
mukamin shugabar dakarun dake tsaron lafiyata
muddin zata iya rantsuwa bisa rike amanata da
kuma siyar da rayuwarta don kare tawa idan har ta
sami wannan mukami zata rinka samun albashi
mafi tsoka a kan duk albashin da ake biyan dakaruna
daga wannan matsayi kuma zata iya zama sarkin
yakin birnin nan gaba daya bayan ta fuskanci wadansu
jarrabobi da matakai
Al amin Ahmed Misau, Guyson
.
Duk mutumin da ya sami wannan dama wacce yarka
ta samu dole ne ya fuskanci makiya da yawa
daga cikin manyan fadawana domin sun san cewa
zaizone yafi su matsayi da arziki, lokacin da sarki
hulbasu yazo nan a zancensa sai hankalin hailur ya
dugunzuma ainun take yaji yayi nadamar sanya
siyama a cikin wannan gasa saboda dalilai guda biyu
dalili na farko shine yanzu ya sanya rayuwar
siyama a cikin hadari domin zata tara abokan gaba
wadanda za su rinka farautar rayuwarta kamar
yadda mai jin kishirwa ke neman ruwan sha, abu na
biyu kuma idan ta tsallake kowanne hadari
da dukkan matakai da zata nisanta dashi
inma bai yi sa a ba ya rasata gaba daya kamar yadda ya
rasa matarsa shardila wacce ya tabbatar da cewar
tana dauke da juna biyu a lokacin da suka rabu
A yanzu da hailur yaga yarima hulkas sai ya fara
tunanin ko dansa ne wannan yaro ko kuma dan sarki
shardas ne
tabbas babu mai bashi amsar wannan tambaya
face shardila da kanta kuma yana shakkar ya sadu da ita
domin idan wani daga cikin dakarunta ya
gansu komai ya dagule kenan domin sai sarki
shardas ya samu labarin cewa yana raye to ba mashi ba matarsa zalima da yarsa
siyama ma rayuwarsu ta shiga hadarin da shiba
zai iya kare suba
hailur ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace ta
yaya zan iya saduwa da shardila a sirrance ba tare
da kowa ya ganni ba ko yaji babu wanda zai iya
taimaka mini na iya ganawa da shadila asirrance
face sarki hulbasu, hailur baya son sarki hulbasu ya san
cewa shine ainihin abokin gabar sarki shardas wanda tuni aka
dauka cewa ya mutu tun shekaru bakwai baya, hailu na cikin wannan tunani ne
yaji an ruguntsume da wani masifaffen azababben
yaki a tsakiyar filin gasa koda ya daga kansa yayi
arba da jaruman biyu dake fafatawa a filin
gasar sai ya cika da mamaki, ba komai ne ya sashi
wannan mamaki ba face ganin cewar dayansu amintaccen
yaronsa ne sadauki Ruhaisu jarumin da ya aminta
dashi dari bisa dari a cikin dukkanin yaransa lokacin a yake kan matsayin
shugaban kabilarsu
koda hailur yayi arba da ruhaisu sai farin ciki ya lullubeshi
domin indai ruhaisu na tare dashi zai iya nemo
masa ire iren sauran jama arsu da sukayi saura a raye
domin su sake tayar da kabilarsu kuma su taimaka
masa wajan bashi kariya dashi da iyalansa
jarumin da yake karawa da ruhaisu kuwa wani
narkeken katone wanda ya ninkashi girma
da tsayi sau uku
kuma a zahiri ma yafi shi surar sdaukantakada
jarumtaka ana kiransa da suna Jamar, amma suna
fara artabu sai jamar ya raina kansa domin ruhaisu yafishi zafin nama da
iya yaki
nan da nan ya rikitashi kuma ya kuntatashi sai
gashi Jamar yana ta ja da baya kuma yana ta
kokarin kare kansa baya ma iya kai hari koda
ruhaisu ya tabbatar da cewar yafi jamar iya yaki
da fadan hannu sai kafa sai ya shammaceshi ya
daka tsalle sama ya doki habarsa da guiwarsa ta dama
saboda karfin dukan sai da jamar yayi sama a
lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa yana saman kafin ya fado kasa sai
ruhaisu ya kara dukan kirjinsa da karfin gaske
kawai saiji akayi jamar ya fado kasa tim kamar
giwa ta fadi kuma ya baje kas a sume ko kyakkyawan
motsi ba yayi
koda ganin haka sai filin gasar ya rude da shewa aka
kama yiwa ruhaisu tafi da jinjina ba don komai ba
sai don saboda shine jarumi na farko da ya fara
lashe wasansa na farko a cikin kankanin lokaci
da fara gasa tunda ko rabin sa a ba ayi ana gumurzun
ba ya sami wannan nasara
ana cikin wannan
yanayine hAilur ya dubi
sarki hulbasu yace hakika wannan jarumi ya burgeni
matuka zan so na gana dashi, koda jin haka sai
sarki hulbasu ya yi murmushi yace ai wannan mai
saukine zan shirya duk yadda zaka gana dashi nan
ba da dadewa ba
yanzu ina so kaje ka ruko yarka da matarka ka shigo
cikin tawagata domin mu shiga cikin gidan sarautata
tare
koda jin haka sai hailur ya dubi sarki hulbasu cikin
alamun damuwa yace bana son na shiga cikin
filin nan ranka ya dade ka taimaka min ka aika wani daga
cikin hadimanka ya taho da siyama da zalina
koda jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi
murmushi yace shikenan an gama, nan take sarki ya
kira wani hadiminsa ya turashi yaje ya taho da jaruma
siyama da mahaifiyarta suka shigo cikin tawagar sarki
hulbasu
koda hailu ya yunkura zai mike tsaye daga kan
kujerar da yake zaune sai santsi ya kwashe shi ya
zame zai fadi kasa
a lokacinne rawanin da hailur ya rufe fuskarsa dashi
ya zame kafin ya mayar da rawanin kan fuskarsa
shadila ta yi arba dashi domin ya hada idanu da ita
cikin kaduwa yai sauri ya mayar da rawanin
ita kuwa shadila sai ta kame a inda take tsaye saboda
tsananin mamaki da kaduwa da murna bata san
sa adda hawaye ya fara zubo mata ba....
Nima dai saboda tsananin farin ciki da murna
bansan lokacin da na ajiye typing dinnan ba nake
cewa
A huta lafiya
kafinann
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
daga Zauran Labarai
nake magana
SATSUBA
Littafi Na Biyar (5)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Duk da cewa itama ta rufe idanunta da bakin kyalle sai
da sarki hulbasu ya lura da halin da take ciki amma
sai ya basar yayi kamar bai fahimci komai ba
ita kuwa luzuraina sam bata lura da duk abinda ke
faruwa ba yarima hulkas ne ya lura da irin satar
kallon da mahaifiyarsa ke yiwa abul siyama
kuma yaga sa adda hawaye ya zubo mata, nan take
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa dalilin faruwar
wannan lamari don haka sai zuciyarsa
ta kama zargi da wasu wasi amma ya kasa
gane abin ma da yake zargi da wasi wasin a kansa
haka dai sarki da mukarrabansa suka mimmike tsaye a cikin filin gasar aka kawo
musu dawakansu suka hau sannan suka
fice daga cikin filin gasar dakaru na zagaye dasu gaba
da baya da kuma tsakiyarsu
Ashe Tun sa adda aka gama fafatawa tsakanin
sadauki darkus da jaruma siyama tuni sadauki darkus ya
kebe da wadansu zakwakuran yaransa ya basu
umarni akan cewa da zarar sun ga jaruma siyama da
iyayanta sun fito daga cikin filin gasar a kashe su a
sirrance ba tare da kowa ya gane abinda ya kashe sun ba
baya ga wannan mugun abu da sadauki darkus ya shirya
ashe shima sarkin yakin sarki hulbasu ma ya
tura wadansu yaran nasa ma a sirrance sun je
can hanyar bayan gari sun labe rike da da kwari da baka sun dana kawai jira
suke suga giftawar jaruma siyama da iyayenta
akan hanyarsu ta komawa gida su sakar musu
harbi su kashesu
lokacin da shi sarkin yaki wanda ake

Please Login or Register in order to submit comment