Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baro turakar shadila ya aika aje a kirawo
masa babban bokan birnin wanda ake kira da Barwas ibn Mus ab
Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta
masa duk abinda yake faruwa
nan take bokan yake shaida masa abubuwan
matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan
wannan juna biyu data samu ya kasance mai nuna
mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba
ka zamo mai tarairayarta kada ka bari koda kuda ya
taba lafiyarta
kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa adda zata haihu
lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci kun shaku ainun
da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a cikinta
kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar
mallakar hular lamsara ina mai tabbatar maka da cewar
da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne dukanta a tafin hannunka
komai da kowa sai ya
dawo karkashin ikonka kuma babu wani makiyinka da zai
iya samun nasara a kanka
.
Anan zan dakata hakaTSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part F.
.
Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa
sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki
bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai
kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye jikinsa
daga cikin
nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace
tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar hankali
saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo
zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka
sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma
saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin
damuwa yace ya shugabana yaya batun
alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan
tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya yace
ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi
face rashin biyan bukatata, daga wannan rana sarki
shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana
cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu
ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa
Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki
kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga ashe
zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa
da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da kulawa
Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal
sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas
duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu
kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin
zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba a ranta
ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce
nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya kamata
ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci
sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun
rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a cikinta
kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta
watarana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta
bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai a wannan lokaci tana sanye
da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke
nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi
cikinta taga ya dan fara
girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi
ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face
tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda
zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon
soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas
suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar
kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take
ciki
koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da
takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki shardas ya jiyo
a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin
firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu izuwa
cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa a cikin turakar face
shadila ita kadai
a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan
kumatunta
cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan
kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune
ya kama hannayanta biyu ya
rike suka kurawa
juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai
taushi
da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla
wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin
idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar
sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a
duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika
daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na
kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan
na rabaki da duk zuri'arki na kawoki kasata da
karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake
matata ta dole
har abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo
nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare harna
sami gafararki
ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk
da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika daya
ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki
haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake
so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na yiwa
mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har
izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar
fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba zan taba
haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar yadda
na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki
hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai
mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki
alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon shekaru
bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki sani
cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar
nan don tafiya neman hular lamsara
bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan
ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a sannan ne nake
son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa
domin daga wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci
bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da cewar
sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu
gano inda hular
Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san
kamannin danki ba shima bai san nawa ba don haka
ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida
juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan gaba
idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa
duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan hailur kuma nan take zan kasheshi
Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a wajanki
kuma ki tuna cewar
kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki
tun da kinsa na 'yanta matan zuri arku daga matsayin
bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini
wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki
babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya.
A lokacin da Nikuma Zankoma Inda nafi Wayau wato Neman na Aure,,,
..
Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO KARSHE
marubucin Littafin yace.
.
SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A WAJANTA?
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA
.
DAGA KARSHE SHIN AUWZAB ZAN SAMU DAMAR GAMA RUBUTO MUKU WANNAN LITTAFI DUKA ???
.
marubucin yace mu hadu a Littafin TSATSUBA na Uku (3) Don jin cigaban wannan labar
TSATSUBA
Littafi na uku
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
.
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike tsaye
ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi da kallo
kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin
hankali
kamar yadda sarki shardas ya bukata haka al amarin
ya kasance,
wato daga wannan rana suka ci gaba da renon juna biyun nata tare, ya zamana
cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata lokacinsa tare da shadila,
yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na damunta
take zai tura a kirawo likitoci su dubata
sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba
kwana a tashi sai cikin shadila ya tsufa
ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai
dai ayi mata
A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara ne
nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai kawai
akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar
hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara tsawa da
walkiya ; al amarin da ya razana jama'a kenan aka
kama guje guje
A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar
da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta watse
jama'a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu suna
rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin
a sanar da sarki abindake faruwa don ana zaton ko
allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi zasu
hallakar da mutanen kasar
Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka
marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai fuskarsa
a murtuke yana muzurai
koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a gabansa
aka yi tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai
shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka marwas yace ya kai dirkar birnin
Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo
mana?
Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya suke faruwa
a sararin samaniya alhalin babu ko alamar hadari?
Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya bushe
da dariya
Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan
boka barwas ya turbune fsuka yace matar sarkice
zata haihu yu
zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai shahara
a ko ina cikin wannan duniya
daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni namu mai
albarka
za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin
wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da wannan
yaro zaiyi wata tafiya
manufa ya fita daga cikin wannan gari namu
koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda zasuyi
tsakanin murna da bakinciki domin ta leko ne ta koma,
babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane
a cikin bayanin boka barwas sunji cewar da zarar wannan
yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai yaye don haka sai wasu suka
fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da dai
a shiga farinciki da farko a karshe kuma a shiga tasku
Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa
Ana cikin wannan haline aka yi wata irin tsawa mafi
karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har
gidajen birnin gaba daya saida yayi rawa, kasa tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta
dabbobi suka kama guje guje suna shigewa maboya, mutane kuwa suka rude
suka dimauce kamar zasu haukace, A dai dai wannan lokaci ne kukan jaririn
Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa kuwwa
izuwa cikin dazuzzuka
Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan sama
kamar da bakin kwarya wata irin iska mai dadin
sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar
damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya
addabi mutane
faruwar wannan sabon yanayi keda wuya sai
murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa
jama a suka ci gaba da cincirindo a kofar gidan
sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba
da wannan sabon jariri da aka haifa ko ya sami
tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa
wannan jariri dan baiwa ne tunda gashi ni'ima ta sauka a birnin a irin lokacin
da ba ataba samunta ba
shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa
bane daga Allah, ruwane daga shaidanu domin
kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan
nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin hanyar
bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun
a matsayin ababan bautarsu,
bayan kofar fada ta cika makin
da mutane
ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan
mutane sanyin iskar dake kadawa har ya fara addabar
jama'a
amma saboda naci sunki su tarwatse sai
tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan
sarautar dauke da jaririn da shadila akan tafin
hannayensa
jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba
ga sabon yankan cibi a jikinsa ruwan saman nata
dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake kyakyatawa
yana ta wutsil wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya
koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama'a
sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna
take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu
suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka har sau
uku
sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas
jaririn ya karba,
ya fuskanci jama a yace yaku jama ar wannan birni
na
Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi
kukana sun bani da alhalin na shafe shekara
da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina
mai tabbatar muku da cewar wannan da
dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don
haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda
zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas yazo nan
a zancensa sai jama'a suka amsa masa da cewar
sunyi Alkawari zasu so wannan da tamkar dan
cikinsu.
Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi
boka barwas ya mika masa hannu domin ya karbi
jaririn
kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke
babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya sallami jama'a kowa ya watse aka tafi
ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe
bayan jama a sun watse sai sarki shardas da boka barwas
suka juya suka nufi cikin gidan sarautar suna
masu jera kafada
tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice
uffan ba
sai sarki shardas ya dubi boka barwas yace
yakai abin dogaro na yakai shamakin dake
tsakanina da allolinmu ina son ka gaya mini
dukkan
dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da na umarci jama a dasu so wannan jariri na shadila
koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar
ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin
alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai
wannan abu da kayi shine babban kuskurenka na farko
a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne
cewa a duniya kaf baka da wani makiyi wanda
yafi wannan yaro? Shin ka manta ne cewa a halin yanzu
yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda suke son
ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a lokacin
da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular
lamsara
shine zai hau karagarka ta mulki kuma idan muka je muka
samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga kan
karagarka ba abu bane mai sauki duk da cewar zamu
iya hallakashi farat daya a wannan lokaci
saboda zamu fuskanci fishin jama a domin a sannan suna kaunarsa fiye da kai
kuma suna matukar jin dadin mulkinsa, dolene
sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu wanda
zai gane cewar dasa hannunmu, ni abinda nake so
dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka kuskura
wannan yaro ya san cewa ba kai bane uban sa ba har izuwa
tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi
akwai ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana
son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin idan
ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara saimun
sha bakar wahala kafin mu sami nasarar hallaka
wannan yaro
Auwzab nake Typing, kuskuren kuwa shine kada ka
kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga ranka domin hakan zata iya faruwa
don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga rai
Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha
bayan kowane kwana talatin, indai kana shan
wannan akan lokaci babu yadda za ayi son wannan yaro ya shiga ranka
shi kuwa kuskuren da zaka yi na uku ba yanzu
zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka
sani yayi
Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi
sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a
cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba
Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin
taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye, jarumai
da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya
boka barwas ne ya radawa jaririn suna
yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna
sai da aka kwana ashirin da daya kullum ana gabatar
da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa saida
akayi ta almubazzaranci tamkar a bola ake tsunto
su
hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya
walima tsawon wadannan kwanaki sarki shardas
a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima
Hulkas dansa ne na cikinsa wato jininsa ne hm
daga wannan rana wani abin mamaki ya fara
wanzuwa a cikin birnin
romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa
a cikin birnin suna tahowa daga manyan kasashe
na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu
a birnin
Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da bai taba yi ba a nahiyar
gaba daya nan da nan talauci da fatara suka yaye,
arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki
iri iri akayi ta shigowa da su birnin da hajoji kala
kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a nahiyar
fiye da shekaru daruruwa da suka wuce sai da
akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba dasu
al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin
sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata taba tsintar
kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar
ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato Hailur saita kefe kanta
a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda
sarki yasan halin da take ciki
duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan
magani wanda boka barwas ya bashi don kada
soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana
kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana wani ba
a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya
tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa da cewa
nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin
bai rigashi mallakar Hular Lamsara ba
a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki shardas
baya kusantar shadila don kada ma yayi arba
da Jarumi Hulkas hmm
Domin zai iya hallakashi nan take saboda zuciyarsa
tana tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin
kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa
na
tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe
jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar, A kwana
a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure duk irin abinda zuciyarsa
ke raya masa akan wannan yaro Hulkas har dai aka sami
tsawon shekara Uku
A sannan ne ya tsinci kansa a cikin tsananin so
da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar
ba zai iya yin rayuwa ba idan babu shi
wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya
shaku da sarki Shardas ya zamana cewa yama
shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa
Shadila har takai cewa ko abinci baya yarda yaci
sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai dai ya kwana da yunwa
shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi
kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan
da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana Hulkas yake dinka musu kullum
sai dai kaga sunyi anko sunzo fada tare sun zauna
akan karagar mulki duk da rana babu abinda
yake rabasu kullum ..
sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki shardas
sannan shadila ke daukeshi tayi masa shimfida
a kusa
da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka baiga
sarki ba sai dai ya fashe da kuka kuma babu mai
iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din
ita kanta shadila lokacin da taga shakuwar sarki
da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk
tunanin mai tunani sai hankalinta ya dugunzuma
ainun
taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta kuskura ta sanar da yarima
hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba idan
hulkas ya girma
A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka
na rufe wannan sirri dakuma
gargadin da sarki shardas yayi mata da
matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai
hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin
ciki........
Uhm Allah sarki Shadila Komai Lokacine
A nan ne Kuma Ni nake cewa Sai mun Hadu a part Na gaba
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part B.
.
Idan ta tuna gargadin da sarki Hsardas yayi mata
da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrinsa
sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin
ciki
haka dai aka ci gaba da wannan rayuwa har yarima
hulkas ya cika shekara shida ya zamana cewa
gaba daya mutanen kasar Romaniya suna
matukar kaunarsa kai ba ma yan kasar ba hatta baki
sonsa suke saboda kyawunsa da farin jininsa
da kuma kyawawan halayansa da irin hankalin
da Allah ya bashi tamkar bai kasance yaro
karami ba sannan ga shi Allah ya bashi jin kai da
tausayin talakawa sabanin sarki shardas wanda
ya kasance Kasurgumin Azzalumin bawa.
Gaba daya zaluncin da sarki shardas ke yiwa
talakawa sai da yarima hulkas ya hanashi kamar
matsa musu wajan karbar haraji mai yawa
kai sumame na mamayar bazato a kamo bayi a kwashe
dukiyar talakawa sai dai takai cewa duk inda yarima Hulkas ya gifta a cikin nahiyar
kasar sai dai kaga jama a suna yi masa kirari da
sarkin Gobe Yadda ake yi masa ladabi, biyayya, da girmamawa kuwa ko sarki
shardas ba a yi masa haka duk da cewa kuwa ana
tsananin tsoronsa hatta a cikin gidan sarautar
kwau
Bayi, barori, kuyangi da dakari ma suna bin
umarnin yarima hulkas tamkar sarki shardas
ne yake basu umarnin, kai sai da takai cewa yarima
hulkas yana zartar da abubuwa da yawa ba tare
da yayi shawara da sarki ba ko da kuwa shi sarki
shardas baya son wannan abu ba zaice uffan ba
bare ya hanashi
Ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin
sarki shardas da yarima hulkas boka barwas na lura
da shi amma sai yayi shiru baice kala ba
wata rana da yammaci sarki shardas na tsaye a can saman ginin wata baranda yake cikin
harabar gidan sarautar sai ya hango yarima
hulkas tare da mahaifiyarsa shadila sun fito
rangadi suna kewaye a cikin gidan sarautar sunta
rabawa bay dakaru barori da kuyangi kyaututtuka
na suturori kala kala
koda ganin wannan al amari sai ran sarki ya baci
zuciyarsa tayi bakikirin ya tuna cewa tunda fa aka
haifi wannan yaro hulkas rayuwar kasar gaba daya
ta sauya duk wani iko nasa
kwarjininsa da tsarin mulkinsa ya dakushe ya zama
kamar mutum mutumi sai abinda hulkas ya
zartar a fada shi ake bi
su kansu fadawan sarki shardas basa karbar umarnin
sa sai abinda yarima Hulkas ya zartar domin a gaba
daya sarakai, attajirai da talakawa sun dauki
hulkas fiye da kima wasu ma gani sukeyi kamar
ya cancanci a bauta masa kamar yadda ake bautawa sauran alloli na kasar saboda
ganin irin abubuwan al ajabin da suka faru daga sa adda
aka haifeshi kawo iyanzu
duk da cewar yarima hulkas ya sami wannan dama da daukaka bai dauki wani girman kai ba ya dorawa kansa
kuma hakan ba ta sa ya raina mahaifinsa ba sarki
shardas face ma tsananin sonsa da yake karuwa
a cikin ransa, duk abubuwan da yarima hulkas yayi a fada
ko yasa aka zartar a kasar sai yaje ya sanar da
sarki a yayin da suka kebe kuma ya tambayeshi
idan akwai gyara a cikin abubuwan da ya aikata domin yaje ya gyara
ko sau daya sarki shardas bai taba nuna cewar akwai
abinda hulkas yayi ba dai dai ba bare ma ya nuna
masa fishinsa a zahiri ko a badini, haka kuma duk abubuwan
da yarima hulkas keyi basu sa shakuwarsa da
sarki ta sami rauni ba face ma karuwa da takeyi a kullum
su kansu fadawan sarki shardas da duk masu
fada aji a kasar suna matukar mamakin yadda
wannan al amari ya kasance domin ko a mafarki babu wanda ya taba zaton
cewa akwai wani mahaluki wanda zai zo ya iya sauya halayan sarki shardas haka
sarki shardas na tsaye a can saman barandar
gidan sarautar yana hango yarima hulkas da mahaifiyarsa
shadila suna ta raba kyautar suturori ga hadiman gidan sarautar sai tsulum
yaga boka barwas ya baiyana a gabansa
take boka barwas ya risina ya kwashi gaisuwa
sannan ya juyo ya leka kasan barandar ya
dubi yarima hulkas da mahaifiyarsa, barwas
ya dago kai ya dubi sarki shardas yana mai ajiyar
zuciya cikin alamun takaici yace ya shugabana hakika in ba don ina kusa da kai da tuni ka
tafka babban kuskuren da zamu hallaka gaba daya
duk da cewa kana shan wannan magani dana baka
a karshen kowane wata, kaunar wannan yaro a
cikin ranka ta gama yin katutu idan baka yi
da gaske ba makiyinka zai samu nasara a kanka
koda jin wannan batu sai idanun sarki shardas suka
zazzaro zuciyarsa ta kufulo har fuskarsa ta kama
yatsine saboda fishi ya dubi boka barwas yace
yakai dirkar birnin romaniya kayi sani cewa har
gobe ban manta da asalin yarima hulkas ba na sani
cewa bani da wani makiyi a doron kasa wanda ya fishi
don haka duk wannan soyayya da nake yi masa ta
banza ce tunda lokaci kawai nake jira wanda zamu
tafi neman hular lamsara da ita ne kadai zan sami
nasarar hallaka wannan yaro kamar yadda ka fada
lokacin da sarki shardas yazo nan a zancensa sai boka
barwas ya tuntsire da dariyar farinciki sautin dariyar
tasa ne ya janyo hankalin yarima Hulkas da shadila suka
Hangosu
cikin tsananin farin ciki yarima hulkas ya baro
shadila a inda take tsaye ya ruga da gudu izuwa
kan matattakalar bene da zata kai shi inda su
sarki shardas suke
koda sarki shardas ya hango yarima ya taho
gareshi sai shima ya tareshi suka rungume juna
hulkas na hada idanu da boka barwas sai yaji zuciyarsa
ta buga da karfi
wani irin tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa dama
duk sa adda yarima yayi arba da boka barwas sai yaji haka
Hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas
yace yakai abbana kayi sani cewa yanzu nake shirin
na tafi zuwa turakarka bayan mun gama raba kyaututtuka ga hadiman gidan nan
na nemi wata alfarma guda daya a wajanka
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi murmushi
yace haba ya kai dana shin ka taba neman wata alfarma
ne a wajena na hanaka? Ai duk abinda kaji zuciyarka
tana da muradi kayi nayi maka izini
muddin wannan abu ba zai zubar mana da
kimarmu da mutuncinmu ba,

Please Login or Register in order to submit comment