Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar dakin ta sake budewa saiga Hulbasu
tare da matarsa Luzuraina da kuma jaruma siyama
tare da mahaifiyarta zalina har da sadauki ruhaisu
tsohon yaron hailur
koda ruhaisu yayi arba da hailur sai ya kamu da
tsananin mamaki kawai sai ya ruga gareshi suka
rungume juna cikin farin ciki mara misaltuwa suka kama
kyalkyala dariyar murna sannan ruhaisu ya janye
jikinsa daga cikin na hailur ya risina a gareshi
cikin
girmamawa yace ya shugabana ko a mafarki ban
taba zaton zan sake ganin wannan fuska taka
ba bare har na rungumi jikinka mai daraja ka sani
cewa har yanzu akwai sauran jama armu da yawa

suna rayuwa a boye cikin dazuzzukan wannan birni da muke ciki,
koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake lullube
hulkas yace nayi matkar farin ciki da jin wannan
albishir naka kuma lallai ina bukatarka tare da
sauran wadannan jama a tamu, ka sani cewa ga
shadila Allah ya dawo mun da ita don haka akwai
gagarumin aiki dake gabanmu wannan yaro da kake
gani wato yarima hulkas shine dan da nabar shadila
tana dauke da cikinsa
koda jin wannan batu sai hawayan farin ciki ya zubowa sadauki ruhaisu
ya ruga wajan hulkas ya rungumeshi
a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas ya dubi
siyama sa adda hawaye ya zubo masa sannan ya bude
hannayansa yace da ita ' ashe ke yar uwata ce ban
saniba?
Taho gareni yake yar uwata rabin jiki cikin matukar
murna siyama ta ruga izuwa ga hulkas suka rungume
junaa
A sannan ne zalina da shadila ma suka durfafi junansu
suna murmushin saduwa suna haduwa sai suma
suka rungume junansu
zalina na kuka tace yake gimbiya hakika kaddara ce ta rabaki
da mijin kwarai wanda babu kamarsa a wajena a cikin
dukkan mazajen duniya amma tunda gashi yanzu ubangijinmu ya dawo miki
dashi inaso mu hadu mu biyu nida ke mu bashi
farinciki irin wanda bamu taba bashi ba a rayuwa
ki dauka cewa yaune wannan dare na farko na amarcinku ehm keda shi don haka
na baki kwanaki goma domin jiya ta dawo yau
koda jin wannan batu sai shadila ta sake kankame
zalina a kirjinta da kyau cikin matukar farin ciki tana
mai yi mata godiya
Al amin Ahmed Dan mutan misau wato A square
nan take sarki hulbasu ya dubi matarsa luzuraina yace
dake da shadila da zalina ku tafi ku bamu wuri zamu
yi ganawa ta musamman mu shida dinn nan
ba tare da wata gardama ba kuwa sai matan uku suka
fice daga cikin dakin suka bar sarki hulbasu, hailur da
sadauki ruhaisu , siyama da hulkas da kuma barmas
sannan kuma sai Al amin Guyson saboda shine typer ehem
nan take dukkaninsu suka zauna tsawon yan dakiku
dayansu bai ce uffan ba can sai sarki hulbasu yayi
gyaran murya yace abinda yasa na taraku a nan shine
kowannanku ya san cewa gimbiya shadila tazo nan
birnina tare da tsaro na dakarun sarki shardas su
dubu bisa jagorancin SADAUKI MARZANU, yanzu ina
son na ajiye mulkina na tafi neman HULAR LAMSARA domin mu kare kanmu
gaba daya daga sharrin sarki shardas don haka ina
neman shawararku bisa yadda zamu yi dasu
sadauki marzanu a mataki na farko da kuma yadda
zamu kai ga cimma burinmu lallai ina son kowannanku
ya bude kwakwalwarsa yayi tunani mai kyau
koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai kowa

yayi shiru aka rasa wanda zai fara yin magana
koda ganin haka sai Hulkas yayi gyaran murya
ya dubi sarki hulbasu cikin natsuwa yace
ya shugabana ni shawarar da zan bayar itace kada muce
zamu kawar da su sadauki murzamu a nan cikin birninka kawai a bari a gama
kammala wannan gasa ta jarumtaka sai muyi
shiri gaba dayanmu a matsayin zamuyi musu rakiya
izuwa can karshen gari muna isa can saimu shammacesu
mu afka musu mu kawar dasu gaba dayansu, mu tabbatar
da cewar dayansu bai tsira da rayuwarsa ba amma
idan mukace anan cikin wannan gidan sarauta zamu yakesu
babu mamaki akwai yan leken asirin sarki
shardas
anan cikin garin wadanda suka sa ido akan su murzanu
wanda da zarar abu ya samesu zasu iya gaggauta
sanar da sarki shardas, koda hulkas yazo nan a
zancensa sai ruhaisu ya dubi hailur da sarki
hulbasu yace a matsayina na wanda ya dade yana
jagorantar mayakan hari na sumame na yarda da
shawarar yarima hulkas
dajin haka sai hulbasu da hailur suka yi murmushi
sannan sarki hulbasu ya dubi hailur yace yau nima
zan fara shirye shiryen wannan tafiya a sirrance ba
tare da kowa ya sani ba sai a ranar da zamu tafi ne
zan tara yan majalisata na sanar dasu cewar zan
raka gimbiya shadila izuwa ga kasarta don
tsoron kada a sami wata matsala
Akan hanya na fuskanci fishin mijinta kuma nan take
zan bar galadima jiran karagata saboda shine kadai
mutumin dana tabbatar da cewar zai iya rike amanata
idan kuma akwai wani mai wata shawarar ne a cikinku
ya fada
koda sarki hulbasu yazo nan a zancensa sai jaruma
siyama tayi murmushi tace ina so ku sani cewa sai munyi
taka tsantsan sosai akan dukkan shirinmu saboda
maso abinka yafika dabara, kuma ma su iya magana
sunce
kifi na ganinka mai jar koma, ina mai tabbatar muku da
cewa sadauki marzanu da sauran dakarunsa mutum
dubu biyu ba kanwar lasa bane domin sun zuba ido
sosai akanmu ko yaya suka ga wani mosti wanda basu
yarda dashi ba sai sun dauki mataki, abu na biyu kuma shine sarkin yaki sadauki
darkus ma yanzu dolene su sa ido akanmu gaba daya
musamman bisa ganin cewa sarki ya bani kariya nida
iyayena shin bakwa tunanin cewa zasu iya hada kai
dasu sadauki murzanu domin gano sirrinmu
koda jin haka sai sarki hulbasu ya girgiza kai yace tabbas hakan
zata iya faruwa amma zanyi amfani da damata ta sarki nima nasa amintattuna su
zuba ido akansu suyi nazarin dukkan motsinsu da shirye
shiryensu
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square

abinda nake so daku shine mu dukkannan jarumaine
don haka ina son kowa ya jajirce iya yinsa a ranar da
zamu gama dasu sadauki marzanu domin mu tabbatar da cewar gaba dayansu ba wanda
ya tsira mu bar ganin cewa
zan tanaji amintattun
dakaruna masu yawa a ranar da zamu fita wannan yaki
wadannan mutane suna da matukar hadari
da wannan furuci nake sallamarku amma banda
abokina hailur
koda jin haka sai kowa ya mike tsaye ya nufi
kofar fita daga cikin dakin amma banda yarima hulkas
domin tsayawa yayi yana ta kallon hailur har saida
sarki hulbasu ya dubeshi yace kada ka damu yakai
yarima yau tare da mahaifin naka zaka kwana don haka
kabi abokinka barmas nan da wani lokaci ma a cikin daren yau zamu sake haduwa
gaba dayanmu
koda jin wannan jawabi sai yarima hulkas yayi
murmushi sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin
dakin
fitarsa keda wuya sai sarki hulbasu da hailur suka mike tsaye Hulbasu ya kama
hannun hailur lafiyayyen ya jashi yana dingisa
daya kafar suka fice daga cikin dakin suka durfafi wani
bangare daban a cikin gidan sarautar yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wani
babban falo wanda aka kawatashi ainun da shimfidu na koren
kilishi da kuma korayen kujeru manya na alfarma
kai ! Hatta labulayen dakin koraye ne komai a wajen kore
abin gwanin ban sha awa
Al amin Ahmed Misau Guyson Ko A square sunana
babu mutum ko
daya a cikin wannan katon falo kuma ga shi tsaf tsaf
sannan an zuba kayan Alatu iri iri a cikinsa masu tsananin
ban sha awa akwai dakuna guda bakwai a cikin
wannan falo gami da kewaye guda biyar kowanne
daki an sanya luntsumemen gado a cikinsa mai dauke
da shimfidu masu taushin gaske, su kansu kewayen
sama da kasansu da jikin bangwayensu dutsen
lu'u lu'u ne kuma bahon wankan a cikinsu na zinare ne
cike da ruwa mai kamshin
turaren miski
ga furanni kala a cikinsa
sai da sarki Hulbasu ya zagaya da hailur cikin gaba dayan
wadannan dakuna da kuma makewayin duka
sannan ya dubeshi yace yakai abokina anan nake son
kaci amarcinka da matarka ta farko shadila
koda jin wannan batu sai mamaki turnuke hailur yace
haba ya shugabana ya nida nake talaka ba dan kowa ba
zakace na zauna a cikin irin wannan kasaitaccen daki
alhalin ni gaba dayan rayuwata ma a daji nayi ta
lokacin da sarki hulbasu yaji wannan batu sai nan
take yaji ya kamu da tsananin tausayin hailur har
lwallah ta cika masa ido amma sai ya dubeshi cikin
murmushi yana mai dafa kansa yace yakai abokina

shin ka manta ne cewa kai shugaba ne guda na
kabila babba
kaima sarkine kuma bana fidda ran cewa nan gaba zaka
zama sarki don haka komai kyan daki da cikar
kawarsa dai dai ne dakai, ni yanzu zan tafi izuwa ga
iyalina ka zauna a nan ka jira Uwargidanka shadila
ehem Al amin Guyson kenan sunana, zata zo ta
riskeka nan ba da dadewa ba amma ka sani akwai
walima ta musamman wadda na shirya a tsakanin iyalina
da naka iyalin kadai domin tayaka murnar sake
saduwa da danka da matarka a cikin daren yau don
haka kayi zaton amsa gayyata koyaushe, koda gama
fadin hakan sai sarki hulbasu ya juyaya fife daga cikin kasaitaccen falon ya bar
hailur a tsaye yanata kalle kalle cikin tsananin farin
ciki
domin ji yake kamar a yau an mallaka masa komai
dake cikin wannan duniya
'' '' ''
A can turakar gimbiya luzuraina kuwa wato matar
sarki hulbasu tuni ta zauna tare da gimbiya shadila
zalina da siyama an kawo musu gasashshen naman
kaji da yayan itatuwa suna ci suna hira cikin nishadi
amma kuma hankalin shadila a tashe yake domin ta
kasa cin komai ta sunkui da kanta kas tana tunani
a lokacinda zuciyarta ke ta bugawa da karfi
cikin alamun tsananin tsoro da fargaba
koda luzuraina ta lura da halin da shadila ke ciki sai ta kama
hannayanta ta rike
ta dubeta cikin alamun nutsuwa tace yake kawata
wai shin wane irin tunani mai zurfi kike yi ne
haka wanda har ya hanaki sukuni ?koda jin wannan
tambaya
sai shadila tayi doguwar ajiyar zuciya
Sannan ta dubi luzuraina dasu siyama tace a cikinku
kaf babu wanda yasan sharrin sarki shardas sama dani
yaki dashi dai dai yake da mutum daya jal yace zai tari
gaba dayan halittun duniya saboda karfinsa da
sharrinsa ya wuce tunanin mai tunani, ta yaya kuke
zaton cewa gaba dayanmu nan zamu iya tsira daga sharrinsa
alhalin ya fimu duk wani abu da muke takama dashi
koda jin wannan batu sai luzuraina ta numfasa
tana mai dafa kafadar shadila tace yake kawata kiyi
sani cewa masu iya magana sunce mai laya ya kiyayi mai
zamani !
Ko shkka bana yi cewar komai nisan jifa kasa zai fado
a saboda haka dole ne karen bana yayi maganin zomon
bana
ki sa a ranki cewa wannan yaki ne tsakanin Gaskiya Da Karya da karfin gaskiyar
mu ne zamu sami nasara akan wannan babban
azzalumi wanda ya dade tsawon shekaru yana
cutar da al umma
haka dai luzuraina tayi ta kwantar da hankalin shadila

tana lallabata har ta shawo kanta taci abinci ta koshi
suna kammala wannan cin abincine sarki hulbasu da hailur suka shigo
cikin turakar
koda ganinsu sai kunya ta kama shadila ta sunkui da
kanta kas ta kama murmushi na murna da farinciki
ita kuwa zalina sai ta mike da sauri ta tarbi su sarki
hulbasu tana mai yi musu barka da zuwa sannan ta
dubi hailur cikin raha da zolaya ta ce to ango saboda
doki ma ba zaka bari nakai maka amaryar taka ba
shine ka biyota ?
Al amin Ahmed Misau Guyson ko A square sunana kenan
caraf sai sarki hulbasu ya tari numfashin hailur ya dubi zalina yace ke kuwa waya
gaya miki cewa ta zama amaryar tasa ai dole
ne da farko mu warware auren dake tsakaninta
da sarki shardas sannan a daura mata sabo da hailur
a sannan ne ta cika amaryarsa, tuni na gama shirya
yadda za a tafiyar da bikin wannan aure a yau din nan cikin
dare za a kara gabatar da gagarumar walima
koda jin wannan batu sai mamaki da farin ciki ya kama
hailur da shadila har dama yarima dasu siyama
sarki hulbasu ya dubi luzuraina yace dama wannan
sakon muka zo mu sanar da ku kawai don haka
idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi daku
izuwa can inda za a gabatar da ita, Al amin nake cewa
haka kuma idan
lokacin cigaba da wannan littafi yayi zakujini wato dai Gobe
kenan
kafinnan kuma
Nidinne dai Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
Dan garin Kaduna
nake cewa Mu zama
lafiya...TŠÅTŠµßÄ
Littafi Na Bakwai (7)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
.
Idan lokacin walimar yayi zamu turo manzo ya tafi
daku izuwa inda za a gabatar da ita, koda gama fadin
hakan sai sarki hulbasu ya kama hannun hailur suka
juya suka fice daga cikin turakar, fitarsu keda wuya sai

shadila ta rungume zalina tana mai cewa godiya a
gareki mara adadi yake abokiyar zamana domin na
san cewa duk wannan shiri naki ne tabbas kin dawo
mini da farin cikin rayuwata wanda ya fiye mini
komai a cikin wannan duniya kiyi sani cewa koda
zan sami dare daya ne jal na wannan farin ciki na
mutu ya fiye mini shekaru dubu da zanyi nan gaba na zauna tare da babban
makiyi shardas
koda zalina taji wannan batu sai tausayin shadila ya
turnuketa har hawaye ya zubo mata ta sake kankameta
a jikinta tace yake abokiyar zamana kiyi sani cewa dole ne nasoki kuma na
kaunaceki dari bisa dari kuma na san martabarki a cikin
zuciyarsa kece masoyiyarsa ta farko a rayuwa kece kika sha wahalarsa duk da cewa nima nayi
wahala dashi
amma ai kin kunshi bakincikin dako rabinsa ni ban kunsa
ba
sa adda shadila taji wannan batu na zalina sai taji
itama ta kamu da sonta fiye da ko yaushe don haka
sai ta kara kankameta a jikinta suka kama kukan murna
Al amin Ahmed Misau Inkiya Guyson ko A square
yayinda yarima hulkas da jaruma siyama suka ga
haka si suma suka kamu da tsananin tausayin iyayen
nasu har hawaye ya zubo musu a tare, kawai sai siyama ta
kama hannun hulkas ta ja shi suka fice daga cikin
dakin suka nufi wani bangare daban a cikin harabar
gidan sarautar
sai da suka iso wani fili mai fadi inda babu jama a wanda
ya kasance mai shirun gaske sannan suka zauna
tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba sannan siyama
tayi gyarar murya tace yakai dan uwana kayi sani
cewa nayi matukar farinciki dana san cewa ashe ina da
dan uwa a cikin wannan duniya wanda muke uba
daya
A farkon haduwata dakai naji ina sonka So irin wanda
mace ke yiwa namijin da take fatan zama abokin
rayuwarta
amma yanzu da na gane cewa kai muharramina ne
sai naji nafi kaunarka fiye da ko yaushe a matsayinka na jinina don haka
kukanka kukana ne kuma farincikinka nawa ne
mahaifin nan namu ya dade yana bani horon yaki
saboda kawai na dauki fansa akan ubanka na karya
wato sarki shardas ko a bayan ransa, shin yanzu zaka
bani hadin kai mu hada karfi da karfe domin
cika wannan bavvan buri na mahaifin mu?
Ka sani cewa raina ba a bakin komai yake ba akan
wannan al amari shin zaka iya cire soyayyar sarki shardas
dake cikin ranka ka kasheshi da hannunka
koda siyama tazo nan a zancenta sai idanun yarima
hulkas suka ciko da kwallah nan da nan hawaye ya
kama sartu akan kumatunsa, Al amarin da ya karya
zuciyar siyama ke nan ta rungumeshi kuma itama ta fara kukan
cikin sanyin jiki hulkas ya janye jikinsa daga cikin

nata suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu
ke zubar da hawaye Al amin Ahmed sunana
hulkas yace yake yar uwata kiyi sani cewa bazan iya cire
son sarki shardas daga cikin zuciyata ba amma
zan iya kasheshi da hannuna ba don komai ba sai domin
a halin yanzu babu mutumin da na tsana sama dashi a doron
kasa
na tsaneshi ne saboda zaluncin da yayiwa iyayena da kuma
munafurtata da yayi ya rinka wahalar da mahaifiyata
tsawon shekaru da shekaru amma yana nuna mini
cewa shi masoyinta ne na kwarai, ban taba sanin cewa
har dukanta yake yi ba a boye a bayan idanuna, shin
yanzu ke a cikin zuciyarki kina da yakinin cewa zamu
iya gano inda Hular Lamsara take har mu mallaketa
mu sami damar da zamu dauki fansa akan sarki
shardas alhalin bamu san a inda take ba kuma bamu san
wanda ya san inda take ba
koda yarima hulkas yazo nan
a zancensa sai jaruma siyama taja dogon numfashi
sannan ta kama hannayansa biyu ta rike suka
kurawa juna ido
sannan tace yakai dan uwana kayi sani cewa a cikin
wannan duniya babu abinda ba zai yiyu ba face
wanda ba a jarraba yinsa ba shin baka da labarin yadda
akayi JARUMI HANTARU ya sami nasarar dauko
Takobin SAIFUL LUJARA ? yasha bakar wahala kuma yasha
gwagwarmaya da manyan sadaukai irinsu RABBASU
wadanda suka fishi karfi amma saboda sa a da naci
gami da rabo sai da yakai ga gaci.
Al amin Kenan Mai
shararo muku Typing, shin baka da labarin jarumin
nan mai mashin GALILUL HARAS ? wato SADAUKI SHADDADU
shima yasha bakar wuya gami da gwagwarmaya kafin
ya mallaki wannan mashi to a yanzu ma ina ji a jikina
cewa kaine jarumin da zai mallaki HULAR LAMSARA sai dai kuma ......
Koda siyama tazo nana a bayaninta sai muryarta
ta shake da kakarin kuka ta kasa karasa abinda take
son fada ta fashe da kuka sosai al amarin da yai matukar
dugunzuma hankalin yarima hulkas kenan ya sake
rungumeta a kirjinsa yana mai cewa haba yake
yar uwata menene na kuka me zaki boye mini alhalin
ni dan uwanki ne na jini to ki sani cewa na san abinda
kike boye mini
wannan abu ba komai bane face duk wanda ya mallaki
wannan hula ta lamsara sai ya rasa rayuwarsa kuma a
tafarkin SOYAYYA zai hallaka kamar yadda ragowar
JARUMAN DUNIYA biyu suka hallaka
Tuni na dade da jin tarihin wannan manyan makaman
yaki guda uku kuma na sani cewa nine na ukun
Nasu nasan cewa mutuwa zanyi to amma ki sani cewa
ni yanzu nayi matukar farin ciki da ya kasance bake bace
masoyiyar da zan mutu a tafarkin soyayyarta ba

ke yanzu yar uwata ce ta jini wadda na tabbata da
cewar ko bayan raina zata iya kula da mahaifiyata
lokacin da yarima hulkas yazo nan a jawabinsa sai jaruma
siyama taji kaunasa ta kara linkuwa a cikin ranta don haka sai ta sake
rungumeshi suka fashe da kuka gaba dayansu
sai da suka dan jima kankame da junansu sannan
jaruma siyama ta janye jikinta daga cikin na
yarima hulkas ta mike tsaye kawai sai ta juya masa
baya tace wane shiri ka fara yi domin ka kai ga wannan
matsayi na zama JARUMIN DUNIYA na uku mai
hular lamsara ?
Yakai dan uwana kayi sani cewa ba a zama wane
a banza dole sai an sha bakar wuya da tarin
gwagwarmaya, koda jin haka sai yarima hulkas ya mike
tsaye yasha gaban siyama yace yanzu wane irin shiri
kike nufi zanyi ?
Jaruma siyama tayi murmushi tace dole ne ka cigaba da
baiwa kanka HORON YAKI har ka sami wanda zaka
iya zuwa inda hular lamsara take ka daukota
Al amin Ahmed Misau Guyson ko
A square sunana
a halin yanzu bincike ya nuna cewa kai da sarki
shardas kuna bukatar wannan hula ta lamsara kafin
dayanku ya sami nasarar hallaka daya shi dai sarki
shardas a halin yanzu yana da karfin da zai iya zuwa wannan wuri da hular
lamsara take bisa taimakon bokansa to amma inda
matsalar take shine dashi da bokan nasa basu san
a inda hular lamsara take ba sai dai kuma akwai wanda suka
nema
wanda shine kadai zai iya yi musu jagora izuwa wajen
ba wani bane ba wannan jagora nasu face wani
hatsabibin Tsohon Aljani wanda a halin yanzu
duk fadin duniya babu Aljanin da yafishi yawan shekaru
babbar magana Al amin nake typing
yafi kowa sanin sirrin wadannan manyan makaman yaki
guda uku wato takobin saiful lujara, mashin galilul haras
da kuma hular lamsara
shidai wannan tsohon aljani ana kiransa da suna
ARWASUL MASADUL
Aljani Arwasul masadul yana da tsananin karfin gudu
a cikin sararin samaniya domin daga birnin hindu yana iya zuwa birnin sin a cikin abin
da bai wuce sa a biyu da rabi ba don tafiyar
da bata wuce ta kwana talatin ba kuwa a cikin abinda
bai wuce wasu yan dakiku ba yake kammalata
ya kasance bashi da takamaiman wajan zama kuma
yana iya zagaye duniya kaf a cikin yini daya kuma
kullum sai ya zagayetan ma ana dai baya zama waje
daya tamkar shanshani
komai karfin sihirin tsafin boka bai isa ya iya ganin
a inda aljani arwasul masadul yake ba kuma bai isa ya
kirashi ya amsa kiransa ba haduwa da aljani arwasul masadul sai babban
rabo da sa a kawai

neman Aljani arwasul masadul dai dai yake da neman
jaki mai kaho
idan kuma har mutum yayi dace haduwa dashi tofa
duk abinda ya bukata daga gareshi indai akwai shi
a cikin wannan duniya to zai kaishi inda abin yake
a cikin kankanin lokaci
Inda matsalar take shine aljani Arwasul masadul baya yawo
a cikin siffarsa
Al amin sunana wato Guyson, gaskiya Littafin nan
nikaina da nake
typing dinshi duk da na jima da karantashi yana sake
kayatar dani uhm kufa ? Yakan rikida ne izuwa siffar
bil adama sau tari ko ta dabba ko ta kwaro don haka
sai mutum yaci jarrabawarsa sannan yake
taimakonsa babbar illar aljani arwasul masadul itace ba a rudarsa da dukiya ko mace ko mulki,
kuma bashi da
tausayi ko jin kai shi kawai yana da wadansu ka'idoji
ne wadanda sai ka cikasu sannan zai taimakeka kuma
dole sai ya zauna tare dakai tsawon kwana uku yaga
ka cika ka'idojin babu wanda yasan wadannan
ka'idoji na aljani arwasul masadul, baya ga haka aljani
arwasul masadul yana da karfin damtse na rikakkun
zakuna guda dubu dari da tamanin kuma duk duniya
babu mai karfin sihirinsa na tsafi amma wani abin
al ajabi a tare dashi shine babu abinda ya tsana sama da kudi
ko mulki kuma babu abinda yake so sama da jarumi
mara tsoro kuma mai sa a ya kai dan uwana kai mutum
ne mai tsananin sa a bisa duk abinda kasa a gabanka
sannan kuma na fuskanci cewa ko kadan baka da
tsoro bisa wannan dalili ne nake da yakinin cewa zaka
mallaki
hular lamsara kafin sarki shardas ya fita nemanta, ka sani
cewa sammako anema ba shine samu ba kai dai
kawai ka nemi sa a da dace, lokacin da jaruma siyama
tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya kamu
da tsananin mamaki ya dubeta yace yaya akayi kika
san duk wadannan al amura koda jin wannan tambaya
sai siyama tayi murmushi tace na taba haduwa da
Aljani Arwasul masadul kuma na cinye jarrabawarsa
a lokacinda nake yawon farauta a cikin daji kuma nayi mu amala da shi ta
tsawon kwana uku ba tare da na san ko shi waye ba
lokacin da yagabatar da kansa a gareni kuma ya
fito mini a siffarsa ta ainihi sai ya tambayeni abinda nake
bukata a cikin wannan duniya ya kaini inda abin
yake domin na mallakeshi, Al amin Ahmed Misau
koda naji wannan tambaya daga gareshi sai nayi
murmushi nace abinda nake bukata ba zaka iya
bani shi ba
cikin mamaki aljani arwasul masadul ya dubeni yace
ke yarinya kin yi babban kuskure da kika fadi haka
ki sani cewa komai yawan dukiyar da kike bukata zan
kaiki inda take kuma na kwasheta nakai ta inda

Kikeso a cikin dakiku kadan idan mulki kike so na
kowacce kasa a cikin wannan duniya zan iya baki
shi koda karfin tsiya a cikin dakiku kadan ke idan ma
duniyar gaba daya kike sonki mulka zan iya yi miki
sanadin hakan
to menene kuma abinda kike ganin cewa zai iya gagarata
sa adda naji wannan batu na aljani arwasul masadul
sai nayi murmushi a karo na biyu nace yakai wannan
aljani ka sani cewa duk abinda ka ambata bana bukata
ko daya daga cikinsu face ina son ka hana aikata zalunci
a doron kasa a tsakanin al ummar mutane da aljanu
da kuma tsakanin dabbobi da kwari sannan ka hana
zubar da jini a ko ina na duniya ya kasance duk
duniya kowa na son kowa ana zaman lafiya babu batun
sata ko kwace
babu fyade kuma babu bambanci tsakanin attajiri da talaka da kuma tsakananin bawa
da sarki wadannan abubuwa sune kadai cikar
burina na duniya
idan har ka har ba zan gansu da idanuna ba bana
fatar nayi doguwar rayuwa a cikin wannan duniya domin
takaicin rashinsu ne zai zama babban bakin cikina
koda nazo nan a zancena sai naga hawaye ya zubowa
Aljani Arwasul masadul yasa hannayansa biyu ya
dafa kafaduna ya ce kece bil adama ta farko a duniya data taba
burgeni
a cikin jinsin mata kuma ban taba haduwa da mai irin
wannan ra ayi naki ba ba wani abu bane yasa kika ga
na zubar da wannan hawaye baface takaicin kin
tambayeni abinda har na mutu ba zan iya samarwa da
wani shi ba
Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana
ina mai tabbatar miki da cewa aduniya ba za a taba
zama lafiya ba domin a hakan ta fara kuma a hakan zata
kare wannan shine tarihin da na riska a wajan kakana na
dari da ashirin
kuma nayi imani da wannan tarihi, yake wannan
jarumar mata hakika ba zan taba mancewa dake ba
a rayuwata domin ni a wajena kece jarumar jarumai
wadda bata damu da komai na duniya ba
yaune ranar karshe ta saduwata dake kuma ba zaki
sake ganina ba har izuwa ranar da zan mutu ko ke ki
mutu
amma ina fatan nayi miki taimako a sirrance ba tare
da kin sani ba kafin karshen rayuwata ina mai yi miki
fatan nasara da sa a a rayuwarki bisa wannan buri naki
da naji kin ambata daga yau nayi alkawarin cewar ba zan sake
zaluntar wani bil adama ba a doron kasa kuma
ba zan taba taimakon wani azzalumi ba amma lallai ki bar wannan al amari sirri karki
gayawa kowa face jarumin da kika tabbatar da
cewa shine zai kawo karshen zalunci , shugaban azzalumai
na wannan zami a cikin jinsinku na
bil adama da wannan furuci nake yi miki bankwana

na karshe
koda aljani Arwasul masadul yazo nan a jawabinsa sai
hawaye ya zubo mini na rungumeshi ai kuwa sai naji shima ya fashe da kuka
daga can kuma sai haji babu shi a jikina
ina bude idanuna na nemeshi sama da kasa na rasa
yau shekara uku kenan da faruwar wannan al amari
kuma ban taba baiwa kowa labarin

Please Login or Register in order to submit comment